Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauri ya buge hannun nasa duk da bai d'ago yaga waye ba amma yasan tabbas lahab ne.

"Haba lahab yanaga kazo ka zauna a aji baka fita break ba koh so kake yunwa ya ramar dakai ne a banban tamu" lahab yace ma Rahab cikin zolaya.

Kallon sa kawai rahab yayi amma baice kome ba ya cigaba da danna wayan sa, bude laidan lahab yayi ya zaro takeAway ya aje akan loka "ga abinci kaci don wallahi yau dai wuni zakayi har yamma in ma bakaci ba jikin kane zai gaya maka, ga wannan yace yana mika masa 500.

Kin karba Rahab yayi ya masa banza, aje masa kudin lahab yayi"gashi kaci abincin Rana"yana maganar yana fita a ajin.

Misalin karfe 1:30 aka tadasu sallah, lahab ya hadu da rahab a masallaci amma baice masa kome ba, suna idar da sallah suka koma class.

Sai 3 cip aka tadasu muzammil ne yazo d'aukar su, daman Rahab kam baima fita a ajin ba don yasan yini xaiyi har yamma yana hango su suka shiga mota suka tafi, karfe 4 suka shiga Extra lesson, na awaya d'aya 5 suka tafi massallaci hadda bashi ya dawo gida ba sai kusan 5:40 na yamma.




***************
Dad kam daga wajen aiki gida ya nufa lokacin mom na dakin ta, ransa a bace ya bude kofar falon ya shiga ganin ba kowa a falon ya nufi d'akin Nnenna ya tura ya shiga.

Har lokacin zaune take da uniform a jikin ta tayi kuka har taji babu dadi gashi daren jiya ma bataci kome ba, kanta ciwo yake mata, girgiza kai yayi ya kirata, my daughter.

Da sauri ta d'aga kanta tana kallon dad sai kuma ta fashe da kuka dana durku sawa daga zaune da take.

Daughter menene in maganar zuwa makaranta ne ki kwantar da hankalin ki gobe goben nan zaki tafi makaranta da kaina zan kaiki kiyi shuru karki sawa kanki wani cutan kuma?

Cikin kuka ta mike da sauri tazo ta rungume Dad, tana sakin kuka haka kawai yau takejin kewan iyayeta da ace tana da iyayen ta a raye baza'a mata yankan kauna irin na yau ba.

Haba daughter ki kwantar da hankalin ki, yace yana bubbuga bayan ta.

Sake sa tayi ta koma bakin gado ta zauna tana mai dafe kanta don wallahi ciwo yake mata, daughter kinci abinci kuwa?

Girgixa kai tayi batare da tayi magana ba, fita dad yayi a d'akin yana kwalawa peace kira da sauri ta fitoh tana gaidashi, ba tare da ya amsa ba yace ta kaima Nnenna abinci.

Juyawa tayi ta koma kitchen in, shima dakin ya koma ya lallabata tatashi ta shiga wanka, yana fita bayan ta fito toilet in ta d'auki abincin da peace ta kawo mata taci, kadan ta baiwa kulenta saura kaya tasa a jikin ta, ta koma kan gado ta kwanta don tanaji yaukam bazata iyya aikin kome ba.

Dad yaje ya samu mom sosai ya nuna mata haukan sa tare da mata Warning mai kyau akan Nnenna, jennifer ma sosai ya zazzage ta ba kad'an ba wannan abu shiya karawa Mom tsanar Nnenna.

Har dare Nnenna bata fito ba abinci ma a daki aka kaimata amma bataci ba saboda nama da aka saka a ciki sai kulenta ta baiwa gashi yan gidan har yanzun basu fahimci batacin nama ba.



*********************
Lahab tunta ya dawo makaranta bai fita koh ina ba gudun kar a zarge shine lahab don Rahab baya yawo daga masallaci sai gida koh makaranta, hakan yasa sa zaman gida sosai ya kule a dakin su, yana ta bitan litattafai gudun kar azo a samu matsala a gane bashi bane.

A haka Rahab ya dawo goshin mangari ba ya same sa, yana turo kofar dakin kawai ya zube akan katifar sa yana maida numfashi don wallahi wahala kam yau yasha, wuni cur a makaranta ba lafiya bane.

Sai da ya jima a kwance har an fara kiran mangariba kafun ya shiga wanka daidai ya fitoh ma har lahab ya sanya jallabiya ya tafi masallaci, da sauri ya sanya kaya yabi bayan sa, ana idar da sallah suna fitowa masallaci sukayi kicibis da yaya jafar watoh yayan uncle muzammil kanin Abbu, gaisawa sukayi sosai yana ta yabon Lahab a tunanin sa Rahab ne don yanzun rahab koh musawa mutane bayayi am mai dashi lahab karfi da yaji.

Gida suka shiga Aka zauna cin abinci ana hira gwanin sha'awa, ana kiran isha'i gabaki d'ayan su suka nufi massallaci sallan isha, tunda aka idar da sallah Aka duba ba'aga Rahab ba, amma tabbas tare dashi aka idar da sallah amma an nemesa ba'a gansa ba sosai ran uncle ya baci ton shi a tunanin sa lahab ne ya tafi yawo.

Shima lahab ya damu don yasan Rahab baya yawon Rana ma bare dare, gida suka shiga Muzammil sai masifa yake yana kwatanta irin dukan da yau zaima lahab inya dawo shidai lahab na zauna yana bitan qur'ani a gefe zuciyar sa a tsinke.

Yaya jafar karan kansa wannan tashin hankalin bai bari ya tafi ba, har 9 na dare shuru-shuru babu Rahab ba labarin sa, gashi sun kasa zaune sun kasa tsaye, bare ma lahab yafi kowa shiga tashin hankali kiran waya aka fara gida-gida ana neman Rahab koh yazo amma shuru, a take Amwar ya fita neman sa har gidan su nabeel yaje lokacin yana kwance kafa ba lafiya.

Anan ma sukace basu gansa ba rabon su da lahab tun jiya, yauma da sukaje dubosa tsaraban duka suka samu jin haka yasa baima je gidan su Adewale ba.


Uncle muzammil ne zaune akan kujeraya harde kafa hannunsa rike da bell jira kawai yake aga Lahab jikin sa ya gaya masa, don shi yafi ta'allaka abin akan gudu Lahab yayi don yaga yana takura masa koh kuma wajen shashancin su yaje


Ji sukai an turo kofar cikin sallama, mikewa sukayi suna amsa wa har suna had'a baki, mami ce ta fara shigowa sai Rahab dake binta a baya yayin da mijinta ke jiran iso, da sauri muzammil ya mike cikin zafin rai yake nuna Rahab, yau zakasan kasa kafa kabar gidan nan lahab watoh gidan uwarka kaje koh?toh yau babu mai hanani dukan ka a gidan nan koh a gaban tane sai na bugeka.

Kallon uku saura mami ta masa don daman tun husul basa shiri da muzammil, tun suna yara lokacin tana matar baban sa, don Allah dakata mini malam akan me zaka dakar min d'a? baijiba bai gani ba aiko abu yama Albarka cin idona zaka sassauta masa saina tafi bare bai maka kome ba.

Ok iko zaki gwada mana akan yaranki maryam, kinsan kina son sune kika tafi kika barmu dasu?

Na nuna ikon kaji tunda nina haifi abuna babu wanda ya haifa mini?koh duk abinda kake musu na taba saka bakine?ina tambayar ka nace na taba saka bakine, saboda da nasan kanayi ne akan gyara lahab, Amma taya zaka kama Rahab kana azabtar dashi abanza da sunan lahab wannan Adalcine nace adalcine?dabazan nuna ikona na uwa ba saina zuba ido ka bugesa akan abinda ba laifinsa ba.

Da sauri Abbu ya dakatar da cece kucen ganin muzammil na son bata amsa, kai muzammil wallahi ka kuskura naji kace wani abu saina nuna maka bacin Raina? Sai kuma ya kalli mami maryam bamu gane zancen ba kimana yanda zamu fahimta mai lahab in yaje yace miki?

Kallon lahab tayi dake sanye da jallabiya yana tsaye a gefe sai fiki-fiki yake da idanu,ya bata tausayi sosai abinka da uwa da 'ya'yan ta, don tasan yau Allah ne kad'ai zai kwacesa a hannu muzammil.............







✨Ruqeenjalal✨




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ

✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ

Free page🀧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*

page2⃣7⃣&2⃣8⃣
Bafa Lahab yake hukunta wa ba Rahab ne?

Sake baki muxammil yayi yana kallon Lahab dake tsaye, lahab da gaske ne abinda maryam tace?

Shuru lahab yayi baice kome ba, aiko abin ya mugun kara batawa muzammil rai fizgo lahab yayi ya wanke sa da lafiyayun mari guda biyu, amma ko gizau lahab baiyi ba bare ma ya bada hakuri.

Kai muxammil sake yaron nan koh mutuwa na kunyan idon uwa bare kai ka sake sa, Addayiya tace ganin yanda muzammil ya finciko lahab zai fita falon dashi.

Kin tsayawa muxammil yayi sai jan kwalan jallabiyan lahab yake, amma lahab koh hakuri koh alamun nadama babu a fuskar sa.

Yaya jafar ne ya tsaida muzammil,sake yaron nan kadai san duka baya gyara koh?lahab yanzun ya girma ace shekara 18 namiji ana dukan sa aiko mace ne ta wuce duka.

Addayiya fashewa tayi da kuka, wallahi muzammil ka sake yaron nan marayan Allah zaka cakume kaje ka illata sa.

Kyalesa yaje ya kashe sa addayiya koh an bar lahab baxai hana gobe yayi abinda yafi haka ba, tunda dai zai iyya kwakwayon d'an uwan sa har ana gallaza masa, mami tace tana share hawaye bawai abinda xa'ama lahab ne yasata kuka ba sai tuna mahaifin su lahab, da ace yana raye babu wanda ya isa ya d'aura hannu akan 'ya'yan sa.

Muzammil koh kulasu baiyi ba kawai ya bude kofar zai tura lahab, da gudu Rahab yazo ya kama kafar sa tare da dukar da gwuwar sa a kasa cikin kuka yake magana don Allah uncle kayi hakuri na rokeka ka taimaka, wallahi ni naje na fad'awa mami ne badon a buge lahab ba, kuma nayi farin ciki daya gyara halin sa a kwana d'aya ya zama kamata, dan Allah uncle kayi hakuri karka bugesa gobe nama Alkawari zaije makaranta.

Tsayawa muzammil yayi yana kallon lahab dake tsaye ya wani lonkosu ya rike kwankwaso da hannu d'aya, d'aya hannun kuma ya dafa jikin gini, kana ganin sa kaga taceccen gagare koh alamun nadama babu a fuskar sa, duk da akwai tsoro aran sa amma sam baima bari an gane ba..

A gaskiya Rahab yau in ban ma lahab duka ba zan zame hannu na a lamarin yaron nan, don naga duk abinda yake kuke d'aure masa gindi yake duk abinda yaso.

Shuru duka falon sukayi don wallahi sun san mundin sukace a kyale lahab toh muzammil ya daina saka sa a gaba kenan don sun san muzammil kaifi d'aya ne, basu san wazai jawa lahab birki ba.

Mami ce ta kalli mijin ta Alhaji muje koh tana maganar tana nufar kofar falon, koh kallon muxammil batayi ba tanajin wani irin zafi a ranta, daman haka uwa keji mundin za'a taba lafiyar d'anta koh da kuwa shine da laifi sai dai ta danne xuciyar ta a hukunta shi.

Binta mijinta yayi a baya suka bar gidan uncle jafar ma tafiyar sa yayi Rshab kam sai kuka yake a falo, ganin muzammil yaja lahab zuwa sashen sa.

Extra room na falon sa yakai lahab bell ya d'auka ya dinga laftar sa, amma abin bakin ciki lahab baya kuka kuma baya bada hakuri sai dai kare kansa da yake, sosai Muzammil ya bubuge lahab bana wasa ba ga sashi tsallen kwado da ya ringayi da machine in yamasa taurin kai ya rufasa da duka.

Lahab fa iyya jikita ya jinkita amma taurin rai bai bari ya nuna nadamar sa ba, ruwan sanyi muzammil yaje ya ciko a boket yazo ya kwara masa a jiki cikin daren nan, haka yana zaune bayan wahalar dashi da yayi a haka lahab ya kwana a zaune kuma a jike bashi ya sake saba sai kusan 4 na asuba.

Kasa tashi lahab yayi da rarafe ya ke tafiya kamar yaro mai tete , a haka ya fita a falon ga jikin sa duk ya farfashe amma fuskar sa bai samu kome ba sai idanun sa da suka kumbura na wahala da rashin bacci, a haka har ya ido kofar falon su duk a bude aka bari sanin da akayi yana wajen muxammil, a zaune yasa hannu ya bude kofar da rarrafe ya isa kofar falon su, yana shiga yaga Rahab zaune har lokacin kuka yake d'aga fuskar sa yayi da yayi mugun kumbura ya kalli Lahab da sauri ya mike ya isa garesa.

Lahab sannu wallahi tunda uncle ya wuce da kai ban samu bacci ba, gashi mami ma sai kira take akan ya barka ka dawo amma bai barka ba sai dukan ka yake koh?

"Kamani muje d'aki"lahab yace ba tare daya basa amsa ba, da sauri Rahab ya kamasa da taimakon sa suka shiga dakin daman ba kaya a jikinsa sai wando muzammil ya kwabe jallabiyar.

Har toilet Rahab ya kaisa, " jona mini kettle Rahab"

Da sauri Rahab ya d'au butan ya cika ruwa a ciki ya jona, wandon jikin lahab ya taimaka masa ya cire, ya rage daga shi dai gajeren wando, ganin yanda jikin sa ya zama yasa Rahab kara fashewa da kuka yana d'aukar wayar sa dake ring mami ce.

Hello mami rahab yace cikin muryar kuka

Da sauri mami tace Rahab lahab in ya dawo ne?

Eh mami gashinan wallahi duk uncle ya faffasa masa jiki koh tafiya baya iyyawa mami.

Bashi wayar, mami tace tana hawaye.

Mika ma lahab wayar yayi amma kememen lahab yaki amsar wayan sai ma mugun kallo daya watsawa Rahab.

Kashe wayar kawai lahab yayi yana zare socket na ruwan zafin ajewa yayi ya zaro karamin towel ya aje a gefe, tura kofar yayi ya fita da sauri ya nufi babban falo, Yana shiga kitchen boket ya d'auko a store da roba karami sai gishiri, yana fitowa sukayi kicibis da addayiya.

Da sauri take tambayar sa lahab ya dawo? gyada mata kai kawai yayi ya cigaba da tafiyar sa,itama da sauri tabi bayan sa har dakin su lahab, rahab ya tura kofar toilet in suka shiga.

Ganin jikin lahab yasa addayiya kama baki ta fara kuka tana dafa kirjinsa, wayyo na bonu amanar umar ne haka, amma muzammil anyi azzalumi haka yayi maka lahab tana maganar tana had'a ruwan zafi.

Kala lahab baice ba kansa na sunkuye koh d'agowa baiyi ya ganta ba don itama yau wani mugu-mugun haushin ta yake ji.

Addayiya da rahab su sukayi ta wanke lahab suna gasa masa jiki zuwa 5 na asuba jikin ya d'anyi sauki, Alwala sukayi dukan su a dakin Rahab ya sanyawa lahab wando 3quater addayiya ta shimfida masa sallaya ta fita a dakin.

Daga Rahab har lahab ranan kin zuwa masallaci sukayi a daki sukayi sallah abbu na dawowa sallah ya shigo dakin nasu, a yanayin da yaga jikin lahab yasa sa saurin kiran likita, yazo ya basa maganguna da allurai a take bacci ya d'auke sa, shima Rahab baccin ya koma don jiya baiyi bacci ba kuma yasha Alwashin koh kashesa za'ayi yau bazashi makaranta ba sai lahab yaji sauki.

Gari na waye wa muzammil ya nufo dakin nasu da niyar ya korasu makaranta, yana budewa ya gansu kwakwance a kan katifa, sai addayiya dake gefe a zaune tana gyangyadi jin an budo kofa yasa ta saurin zabura ganin muzammil ne yasa ta mikewa tsaye tana masa nuni da hannu akan ya fita a dakin, fuska a d'aure shima baija zancen ba ya juya ya tafi abinsa.

****************
Ta bangaren Nnenna yau ta tashi a sab'ule koh d'okin zuwa school in batayi ba, tana tashi tayi ayyukan ta kamar ko yaushe kayan makarantan ma bata saka ba sai da Abraham ya shigo ya kara jaddada mata yau zata school.

shiryawa tayi jiki ba kwari ta ibi abinci taci kad'an Dady da kansa ya d'auke ta xuwa school, , jennifer kam kin binsu ma tayi tace bazata bi dady ba mom zata kaita.

Nnenna tunda suka nufi makaranta zuciyar ta ke tsinkewa, wanda bata san dalili ba tana ji kamar akwai wani abu mai muhimmanci dake tinkaro rayuwar ta anan gaba.

Makaranta ne na manya in akace manya ana nufin yayan masu akwai sosai, makaranta mai kyau da tsada daga yanayin ginin makarantan da uniform inda ke sanye a jikin su kome clean ne, ajujuwa ne sama da kasa bini mai hawa uku gashi reshe-reshe gefen science daban Art ban, Amma senior ne kawai babu primary koh jenior.

Packing Dad yayi a packing space na makarantan a hankali Nnenna ta bude marfin motar ta fita Dad ma fita yayi, yana kallon ta tare da sakar mata murmushi, daughter muje koh yanzun fa Almost 7:39pm gyada kai tayi tabi bayan sa har office in principal.

An gama kome harda interview aka mata kuma sun yaba da kokarin ta, ga speak a bakin ta, a take Dad ya mata registration, aka bata takardun makaranta tare da sanar da ita akwai Labrary basai an bata textbook ba, sai da aka gama mata kome kafun aka mikata a sss 3 A.

Tunda Nnenna ta shigo ajin gabaki d'aya 'yan ajin suka bita da kallo sosai suke kallon ta kamar sun samu wata sabuwar halitta, a bench na gaba aka ajeta itama karan kanta ta sargu ganin yanda yara keta binta da ido daga maza har mata.

Wata yar inyamura ce ta matso bench da take cikin yare ta soma mata magana ganin ta Christian kuma kykkyawa haka, atunanin ta Egbo ce, duk da kyawun nata yayi yawa sosai, cikin yare take sanar da ita sunan ta Amarachi?

Gyada kai Nnenna kawai tayi tana kallon yarinyar amma batace kome ba, don dad yau saida ya kara ja mata warning sosai akan mu'amala da mutane ta kuma iyye bakin ta.

Sake tambayar ta yarinyar tayi ita kuma menene sunan ta? mikawa yarinyar takardan ta tayi, ba musu yarinyar ta karba ta duba, sai kuma ta d'ago tana kallon Nnenna, ok ur name is Nnenna obinna from Enugu state abie?

Gyada kai again Nnenna tayi batace kome ba itama Amarachi bata damu ba koh banza zatayi kawance da kyakkyawa,wasu yara biyu ma duk suka zo sukayi joining na Amarachi sai hira suke ma Nnenna, tana binsu da ido kawai duk cikin turanci suke wasu har takardu suka fiffitar, note nasu suka bata wai ta copy aiko da sauri ta karba tana copy abinta.

A haka Jennifer ta shigo class in fuska ba walwala kallon Nnenna tayi dake rubutu sai yara dake gefen ta mata uku maza biyu sai hira suka mata sosai, ranta ya baci ganin daga zuwan Nnenna zata kwace mata jama'a a ajin su,tsawa ta dakawa Nnenna tare da nunata da hannu ke yar kauye tashi mana a bench banza mabaraciya kawai.

Mikewa Nnenna tayi yayin da d'aya daga cikin mazan yace ma Jennifer amma dai ke mahaukaciya ce, ya daga zuwan yarinya zaki wani fara zaginta ubanki yazo da benchi daga gidan kune.

Badai gidan mu ba sai dai gidan ubanka.

Ai kankace me fad'a ya barke tsakanin Jennifer da yaron , sosai yake bugun jennifer kafun aje akira teacher tayi laushi sosai, kafun akazo aka jidesu dukansu akayi staff room dasu.

Ranan koh darasi d'aya jennifer bata samu ba saboda hukunta su da akai a staff aka barsu wuni kas don su school in basa duka sai dai su horar.

***************
Lahab basu suka farka ba sai kusan 11 na safe suna farkawa suka tarar da addayiya na zaune har lokacin a d'akin, watoh dai gadin su take, Lahab jiki yayi sauki da kafar sa ya shiga toilet duk da kafar bawai ya daina tsami bane, wanka yayi da ruwan zafi da addayiya ta had'a masa yana fitowa ya samu ta zuzzuba musu abinci a plate.

Zama yayi a bakin katifar tare da jinginar da jikinsa a jikin ginin dakin, da sauri ta kawo plate in ta aje masa a gaba, kallon plate in yayi shinkafa ne da salad sai miya,"gaskiya nifa addayiya bazan iyya cin abincin nan ba bakina ba dadi"

Ok toh lahabu mekake son ci?

"Kwai kawai zaki kawo mini soyayye sai ruwan tie ba madara"

Da hanzari ta mike ta fita a dakin, abincin da lahab yaki ci shi Rahab ya d'auka ya kama ci, koh 30 minutes ba'ayi ba saiga addayiya da tiren abinci aje masa tayi a gaba ga dukkan alamu yanzun ma ta d'aura tie in harda suyan kwai.

Kad'an lahab yaci ba yawa ya koma ya kwanta tare da d'aukar wayar sa, nabeel ya kira amma har ya gama ring bai d'auka ba haka ma adewale abun ya basa mamaki don da wuya ka kira d'aya baka samesa ba.
Aje wayan yayi kawai ya lumshe idanun sa yana sauraron hiran da addayiya keyi da rahab.

****************
Nnenna a rana d'aya tayi winning na heart in yara, daga malaman har daliban saboda kwakwalwar ta da kyaun da Allah ya bata gashi students mata sai janta labrary koh cafe suke ayi ciye-ciye, koh suce suje ta musu wani Assigment, duk da ba fuska ta sakar musu ba tana d'ari-d'ari da kowa kuma abinda ya bata mamaki shine sam yaran musulmai basu rabeta ba gwara maza wasu sun mata magana albarkacin zaman tare, amma matan kam kowa d'aga kai tayi abinta kamar basu san da ita a class in ba.

Yayin da bakin ciki ya gama gashe jennifer ganin rana d'aya Nnenna ta kwace mata kawaye, da aka tashi makaranta da driver yazo d'aukar su jennifer hanata shiga tayi driver yaja mator ya barta a tsaye.

Haka Nnenna ta ringa takawa da kafarta tun daga school har gida, gashi 3 aka tashi koh karyawan kirki batayi ba gashi taki cin abinda students suka sai mata, ga tafiya duk da hanyar sabone a wajen ta hakan bai hanata gane gida ba sai kusan 4:30 ta isa gida.

Tana tura kofar falon ta tarar da Mom zaune a falo sai sarah dake duba book nata koh kallon ta mom batayi ba, harta shiga d'akin ta wanka tayi ta ibo kayan uniform nata ta wanke su a waje ta shanya, kitchen ta nufa zata ibi abinci haka mom ta hanata iba, akan tunda Jennifer ta dawo makaranta ta kulle kanta a d'aki koh abinci taki ci sai kuka take don haka itama bazataci ba.

Sai dare aka samu Jennifer ta bude kofa anan take sanar da mom nata abinda Nnenna ta mata aiko mom ba karamin bacin rai taji ba, amma tace ta bari gobe in Allah ya kaimu zasu je school in tare ayita ta kare.

Haka koh akayi washe gari da safe Mom da kanta taje school in su Nnenna ita da jennifer yayin da suka bar Nnenna a titi tana takowa da kafa, Nnenna batasan me su mom sukazo suka kulla mata ba, tadai tazo school late har anso korarta gida, m amma daga baya principal yace a barta jin dalilin late in nata, sannan ya shaida mata tabar A class an maidata B.

Haka ba musu ta koma B da zama, amma sam ta daina jin dadin makaranta saboda mugun tsanar ta da aka soma ba gaira ba dalili gashi wulakanci jennifer take mata sosai, wani lokacin sai dai ta buya tasha kukan ta koh zaman aji bata iyya wa in aka fita break saboda ihu da ake mata da hausa wanda bata san mema suke cewa ba amma ta tabbata zagine.

A haka ta ringa zuwa school a kafa kuma a wahale kullum sai ta buga late allah ma ya sota ba'a duka a school in sai dai horo mai tsanani irin su wanke toilet da dai sauran su.

Daga an buga break kuma sai dai ta tafi bayan ajujuwa wajen gonakin makaranta ta xauna abunta ita kadai sai kulenta har a dawo break.

Gidan ma ba dadi yake mata ba sai in Abraham nanan koh dad suke d'an shiga harkar ta kad'an, nan ma ba sosai bane ga yunwa dake cinta abinci ba koh yaushe take samu taci abinda ranta ke so ba, har wani tari ta fara wanda bata san kansa ba in tanayi kirjinta har zafi yake mata haka numfashin ta ke fita da sauri sauri.

****************
Lahab sai da ya kwashe kwana 3 Rahab da addayiya suna jinyansa kafun ya samu ya murmure har yana zuwa masallaci da kansa muzammil yaso su koma makaranta amma addayiya tayi kukan kura ta dire tace jikin lahab bai warke ba, shikam da wannan yayi amfani wajen kara longo bewa don da gaske ciwo kan sun bushe sai dai baza'ace sun warke ba.

Yau dai yana fita sallan asuba bai zarce koh ina ba sai gidan su adewale, Amma maigadi yace masa adewale baya

Please Login or Register in order to submit comment