Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta barta tana yawo,sulaiman yaro ne Mai hankali kowa ya shaida hakan shiyasa lokacin da Amina ta Soma sauraron sa sosai inno taji dadin abin.




Sulaiman dan makaranta ne yana karatun sa a birni na gaba da secondary abinda yasa Amina ke dada sonsa kenan kullum Suka hadu sai Hiran Makaranta take Masa daya koya Mata kaza kaza a hakan ya samu Shiga a wajen ta hardai Suka Soma soyayya kowa a kauyen ya sani ata dalilin Amina sulaiman ke komawa rugan su duk sati sati juma'a zaizo da yamma sai Kuma ranan lahadi ya koma da yamma,Inna kullum matsawa Amina take akan zancen sulaiman ya turo amma duk lokacin da ta kawo Masa zancen sai yace tayi hakuri ya kammala karatun in ya samu aiki sai suyi aure, in bai samu ba Kuma ya dawo kauyen su ya cigaba da kiwo kamar yanda ya taso.




Wannan shekarar ya kammala karatun sa ya muneeru da kansa yaje ya samu kawun sa sukaje wajen iyayen muneeru akan auren sa da Amina,amma sulaiman yace suyi hakuri zai tafi NYSC a kasar inyamurai a bar zancen auren saiya dawo insha Allah za'a Yi kome a gama sai ya cigaba da zaman sa a gida,badon ran inno yaso ba ta hakura,a takaice dai yanzun Amina na rugan su sulaiman na kasar inyamurai.



Bayan kabo ta fito wanka daidai lokacin muneeru ya shigo gidan da buhun masara a bayan wuyan sa daker daker yake tafiya da Sauri Inno ta Mike tsaye Tama gyara daurin xanin ta,tana magana,haba muneeru ya zaka dauko masara haka a kanka bazaka nemi amalanke ba,sauke masaran yayi Yana Bata amsa da fullacin"inno am hatou mi hebata ai dinka mi Ronda tam,da murna ya zaro kudin aljuhun sa wanda a kalla zaikai dubu goma ya nuna Mata Yana cewa ashan Aka Basu wani Mai kudine yazo kauyen nasu,da Sauri Inno tasa hannu ta fizgo kudin tana kirgawa tana washe baki tare da daukar 1k ta mikawa muneeru tana tsoka sauran a bakin zanin ta,girgiza Kai kawai Amina tayi ta shiga daki tana mamakin irin son kudin inno.



Bayan sallan la'asar saiga kawo shehu yazo gidan su kabo Bata San meya tattauna da inno ba tadai ga inno sai fara'a take tana Nan da nan da ita itadai Amina Bata tambaye ta ba,yaro ne ya shigo gidan Koh sallama babu ya Soma karade gidan Yana cewa Wai ana sallama da Kabo a waje,da murna Amina dake daki ta fito tare da zare gyalenta dake saman Zama ta yafa a zatonta sulaiman ne yazo hutu don yace Mata wata uku zaiyi yazo hutu Kuma gashi an cinye wata biyu.





Inno dake tsaye a bakin madafa da Sauri ta kwala Mata Kira ganin zata fita kofar gidan,dawowa Amina tayi cikin kunya don wallahi Bata zati inno na waje ba sunkuyar da Kai tayi,itakam inno cewa tayi akwai wani turare da muneeru yaje binne ya sayo min tafi wata na boyeta kije ki dauko a cikin kwalba ki fitsa ki shafawa kafar Nan Taki vasilin,da mamaki kabo ke kallon ta tunda take inno Bata taba sata fisa turare ba sai yau amma batace kome ba ta shiga ta dau turare ta shafa,mulkawa kafarta Mai da Sauri ta fito tana lekan labule ganin inno ta shiga bandaki da Sauri ta fito ta nufi kofar gidan.



tsaye yake a jikin zanan kofar gidan ya jingina da bishiyan cabbulle dake manne da zanan,tunda ta fito yake binta da kallo ganin sai kalle-kalle take had'a Ido sukayi ta kauda fuska tana cigaba da dube-dube Kamar tana Neman wani Abu,cikin taushin muryar sa yayi Mata sallama,amsawa tayi sama-sama tana cigaba da abinda take,Gimbiya Aminatu kabo nine bakon da kike nema"



Wani irin juyowa tayi a kaikaice tana Kara kallon mutumin Wanda a haife yayi jika da ita Wai shine Wanda ya tura a kirata toh Koh Tayi Masa laifine ita da ba sanin sa tayi bama bare,toh Koh ta Masa Kama da Yar aikane da zai turo a kirata ya aiketa kenan........................ .................




*In na samu charge zakuga update da dare*
🤸🤸🤸🤸🤸🤸🤸🤸🤸🤧


🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 94&95

tsayawa tayi daga nesa tana kallon sa da mamaki sai Kuma ta durkusa har kasa ta Soma gaidashi"Kaka Ina wuni"d'an murmushi yayi yace taso Mana Aminatu mun wuni lafiya"tasowa tayi tana tambayarsa da lafiya yake Kiran ta,babu d'ard'ar Koh Jin kunya anan take ya bayyana Mata soyayyar sa da Kuma niyar sa na auren ta,wani irin harara Amina ta maka Masa sannan tace"yanzun Kai banda rashin tsoron Allah bawan Allah daga kawai kazo garin mu ka Mana kyauta sai Kuma ka Soma bin yara gida,Kai Koh kunya Bakaji ba tsofe-tsofe da Kai kazo kace kanason yarinya Kamata amma dai wallahi anji kunya girma ya Fadi Niko yanzun me zanyi dakai gemu duk furfura toh wallahi Bari kaji tun ban nuna maka halina ba ka kwashi kafafun ka kabar Mana kofar gida.




Sosai Alhassan yayi mamakin yanda Amina ke zuba Masa tsiwa amma a maimakon yaji d'ar akan son da yake Mata saima yaji son ya karu sosai yake Jin son Amina a ransa bana Wasa ba shi Karan kansa yasan yazo neman aure a Inda bai dace dashi ba yarinya kankanuwa Kamar wannan yasan abun kunya ne zai jawa yaransa da matansa amma ya zaiyi,shi so haden Rabbi ne lokaci d'aya yake shiga amma fitar sa Bata da iyaka,yanda takejin yarinyar kaf duniya banda iyayen sa da Suka mutu babu Wanda zai hanasa auren yarinyar Nan sai wani ikon Allah babu ruwan sa da abin kunya tunda addini bai haramta ba.



tsaki Mai karfi Amina ta sake ta juya fuuu ta koma cikin gidan nasu ranan haka ta kwana Koh abincin dare bataci ba washe gari da safe ta tafi makaranta tana dawowa tadauki tallan nonon ta,da yamma bayan ta dawo daga tallah ta nufi gida tun daga nesa ta hange mutum zaune a kofar gidan su abin mamaki ba kowa bane sai mutumin jiya,Yi tayi Kamar Bata gamsa ba tazo zata wucesa da Sauri ya mike yabi bayanta Yana Mata magana ganin tana Shirin shiga gidan"haba minatuwa Baki ganni a tsaye bane tun fa 12 na Rana nake zaune anan bayan nazo akace min kin tafi tallah nake zaune Ina jiranki amma shine Zaki ganni ki wuce.





dan dakatawa kawai tayi Saida ya gama maganar sa kafun tace"wallahi tsoho ka rabu dani Koh bakaji menace maka bane Wai"?naji Mana amma Ni bazan iya hakura dake ba gaskiya"sosai Amina taci Masa mutunci iyya mutunci kafun ta barsa tsaye a wajen ta Shiga cikin gida inno dake labe tana Jin duk irin cin mutuncin da Amina ke Masa,tana shiga daki inno ta bita da sharbeben d'anyen Kara duka ta rufe Amina dashi tana cewa"ke Harkin Isa kimin bakin ciki in Kika Kore wannan in wazaizo ya aure ki Koh so kike kiyita jazamin magana a gari,toh wallahi Bari kiji Koh sulaiman ne ya dawo bazai Hana a fasa auren ki da Alhaji Nan ba Yar banza hutu yazo Mana Zaki min bakin ciki tunda mahaifinku ya rasu Nike jegele da gida yanzun da Allah ya amshi Addu'a ta Dana Dade inayi shine Zaki min hassada,da gudu muneeru dake dakin sa ya shigo yazo ya kwace ta, ganin irin dukan da inno kema Amina kamar zata yankata ga Amina da taurin Rai Koh ana dukanta Bata gudu.





Fizgota yayi da Sauri ya shigar da ita dakin sa ganin inno nason karyo wani Sabon bulalan rufe kofar bukkan nasa yayi,Zama Amina tayi tana kuka sai rarrashin ta muneeru keyi yana bata baki shidai baice Mata kome Akan Alhaji ba, yadai nuna Mata tayi hakuri insha Allah kome zai daidaita sai Wanda takeso zata aura insha Allah zai tsaya Mata, Jin hakan yasata ta danjin sanyi-sanyi Saida fa zazzabi ya rufeta ainun kwanciya tayi a katifar yayan nata, shikam fita yayi ya dauko Mata jikekken maganin su dake gindin Randa ya tsiyaye Mata a kwanon Sha ya kawo Mata kin sha tayi don ita Bata kaunar jikekken magani sam.




Wasa Wasa Abu ya Zama gaske tun Amina na d'aukan abin a shirmen Abu ya Fara girma sosai Alhaji ke surfa Mata naci ba ranan da baya zuwa Koh karyan ciwo tayi sai inno ta tasata a gaba harsai ta fita inta fita babu abinda ke had'ata dashi sai cin mutunci sosai take Masa rashin kunya shikam Bai karaya ba Sam,muneeru baison aure saboda harga Allah yasan ba'a ma Yar uwarsa adalci ba ya tinkare inno da maganar amma ta rumtsa Ido tace aure sai anyi,abinka da magana a ruga lokaci d'aya zance ya karade gari Amina ta samu Alhaji zai aureta baza'a bawa sulaiman ba sosai iyayen sulaiman Suka Soma gaba da gidan su Amina,Allah sarki Amina Kam hankalinta yafi na kowa tashi Bata San ya zatayi ba gashi sulaiman baya na.




A bangaren gidan minister Suma sunsha mamaki da sukaji an baiwa Alhassan Mata a zaton su ma babbace tsohowa Kamar Addayiya,amma duk da hakan Addayiya ta nuna kin amince warta akan me zai Karo Mata Amarya bayan Saida Suka riga Suka tsufa da Yaya da jikoki wannan ai abin kunya ne Amma me rumtsa Ido yayi yace yaji ya gani y'ay'an sa gabaki d'ayansu sun nuna basa kaunar auren Amma yaki hakura dan uwan sa Saida ya bashi shawaran hakura ganin gidan nason rikicewa,amma yace babu Mai hanasa auren Amina.




Zancen aure ya kankama Kaya na Alfarma minister yayi ma Amina Wanda yasa Yan kauye Suka ringa CeCe kuce akan inno zata saida Amina saboda tsabar son kudi irin nata amma inno ta toshe kunnen ta ta musu ta uwar shegu,saura sati daya biki duk Wanda yaga Amina sai ya tausaya Mata ta rame ta zabge tayi kuka tayi kuka harta fawwalawa Allah lamuran ta amma fa bawai ta hakura bane, sosai take Jin wani irin tsanar Alhaji a ranta tare da kudurta irin abubuwan da zata shuka Masa in yayi gangancin auren ta.




tirkashi ana wani ga wani cikin wannan Hali sulaiman ya Fado a cikin rugan su yazo ya tarar da wannan mummunan labari sosai ya birkice Kamar tababbe da kansa ya shigo har cikin gidan su Amina yazo ya dafa kafar inno Yana rokonta akan kada su rabasa da Amina amma inno tace aikin gama ya gama wajen kawu shehu yaje amma Ina babu alamun nasara don ba karamin kudi Alhaji ke sakarwa inno ba,yaso ya rusa gidan su Amina kafun aure ya musu na zamani amma inno tace a Bata kudin kawai abin magana baya kad'an a kauye har jikokin su sai amma gori.




Sulaiman tunda ya dawo yake bin Koh wani hanyoyi don ganin ya hadu da Amina amma inno ta datse Amina Koh Nan dashan Bata fita ta kasa ta tsare,sulaiman bai samu ganawa da Amina ba sai a daren da za'a daura Mata aure misalin karfe Sha biyu na dare ta farka don da Rana kanwar sulaiman tazo ta sanar da ita akan yayan ta zai jirata a Sauro da daddare ta fito zaiyi magana da ita a sirri karta fadawa kowa,tun karfe 9 na dare take son fita tana tsoro, gudun kada wasu su ganta Koh inno ta farka ta Kamata zata fita.




tafiya take a hankali cikin duhu gudun kada a jiyota kofar gidan su ta nufa a hankali taji muryar mutum a bayan ta da Sauri ta juya hade da kwala ihu da Sauri sulaiman yace nine Amina karkiyi a jiyo mu,jikinta ne ya daina bari anan Suka zauna Suka soma tattaunawa Suna muhawara don sulaiman cewa yayi ta tashi su gudu daga rugan suje suyi aure a can Inda yake NYSC,ita Kuma tace bazata jawa iyayen ta abun kunya ba akan me zata bisa suje suyi aure su shiga duniya ita bata yarda ba amsar da ta basa shiya kuntata Masa Rai, anan fad'a ya barke a tsakanin su sosai sulaiman ya gaggasa Mata magana akan itama tana son auren Alhaji shiyasa ta Fadi haka Ashe ba soyayyar gaskiya take Masa ba taga Mai kudi zataje birni.




Komawa cikin gidan tayi tana kuka ta shiga dakin ta ta kulle wani irin zafi takeji a ranta har Addu'a take Allah ya dauke ranta kafun gobe ta huta Kar taga wannan Rana da za'a ce an daura Mata aure da tsohon nan,.





*********************
Rana bata karya saidai uwar d'iya taji kunya ayau dubban al'umma Suka shaida dauren auren Alhassan Muhammad dogo Mai naira tare da Amaryar sa Aminatu kabo jibril Akan sadaki naira dubu Ashirin,tunda aka kafa rugan ba'a taba daurin aure irin na ranan ba jama'a mn Kamar kasa Yan birni sosai Suka cika kauyen hatta yaran ango da jikokin sunzo daurin auren kakan su,Amina dake daki,kafa yasha yaben bakin lalle da hannu sai kuka take tunda gari ya waye Koh wanka taki tashi tayi Jin lasfikan masallaci iska ya kado zancen daurin auren nata dib taji ta d'auke wuta bata Kara sanin me ake ciki ba Saida ta farka ta ganta a cikin mota ana tafiya da ita,watoh ashe data Sumama bata tsira ba a sumen aka sata a mota bama ta lafiyar ta ake ba ta zancen aure suke sai yanzun take takaicin rashin yarda da abinda sulaiman yace Mata tayi,data bisa Koh bangon duniya ne suje.





****************
tafiya suke sosai ganin haka yasa ta hakura da iFace iFace da take ta nutsu waje d'aya har lokacin hawaye baibar bin kumatunta ba idon Nan Kamar garwashi,tsayawa motar yayi itakam har lokacin bata dago taga Inda suke ba bude motar akayi da Sauri wata goggon ta ta lulube Mata fuska Wai gudun kada a ga fuskar tata ba'a sayi Baki ba.



Jidai kawai tayi Suna tafiya amma Bata San Inda take sanya kafarta ba har suka nufi cikin sashen nata ajeta sukayi akan gado Suna jin Mata sai shigowa suke Suna fita ana gaggaisawa da Yan uwa ta,abinci aka kawo musu aka aje duk matan dakin Suka fita aka bar amarya dayan uwan ta sosai Yan uwan nata Suka Soma cin abinci basu Koh damu da halin da Amina ke ciki ba Suka hau zagin mutanen gidan Wai Suna musu kallon wulakanci Kamar sunga Kashi ga wani d'add'aga hanci da uwar gidan take,ai maganin inno kenan ba kwadayi ba sai ta Kai yarta ga mahallaka Koh wajen yan Yankan Kai,inji wata tsohowa a cikin su itadai Amina har lokacin tana lullube Bata yaye mayafin ba.




da yamma akace za'a Yi budan ka gidan minister sosai ya cika da Baki duk da auren sirri yayi amma bai buyaba zancen auren Kuma kowa yaji sai yace zaizo yaga matan da Alhassan ya Kara da gangan aka kirkiro budan Kai don ayi maganin tsohowar d'aya aura,wanka Amina ta sake Alhassan ya turo matar Alhussan tazo ta kawo Mata kayan da zata sa don duk gidan babu Mai supporting auren Nan nasu sai ita hatta dan uwan sa baiso.



Ba karamin mutuwar tsaye goggo badawiyya tayi ba data ga Amaryar tsohon nan,amma batace kome ba haka ma bata fadawa kowa ba ta kawo Mata zani da Sabon mayafi ta yafa,tanama Yan uwan Amina da aminar jagora har tsakar gida wajen budan Kai,lokacin da aka bude Kan Amina kowa ya Sha jinin jikinsa Addayiya kuka ta fashe dashi tana cewa Alhassan ya kunyatata ya rasa wance zai kawo Mata a wannan shekarun sai jikarta?da jikarta zatayi zaman kishi sosai fa magana ya bazu a gari akan zancen auren nasu.




Bayan kwana biyu baki masu zuwa kallon Amina da Yan gulma duk sun dan ragu Addayiya har ciwo tayi akan zancen auren Amina kafun daga baya ta fawwalawa Allah,tsakanin Amina da Alhaji babu abinda zamuce sai dai muce rabon wahala ne ya sasa auren ta don ba karamin rashin mutunci Amina ke Masa ba a gaban kowa nuna wa take bata sonsa auren dole aka Mata ga rashin kunya takewa kowa a gidan,duk da ba halinta bane amma auren duk shiya birkitata sosai take nuna Masa kiyayya shima abin na Masa ciwo amma hakuri yake Yana danne zuciyar sa don duk abinda zata Masa bazai fasa Zama da ita a hakan yake sonta.





Alhassan fa yaga ta kansa don gabaki d'aya Amina ta birkita masa gida rashin kunya takewa mutane na bugawa a jarida Inka cire Alhussan da matar sa badawiyya don su basa ma zuwa Inda take bare tagansu tace zata musu rashin kunya, muzammil yayi mugu mugun tsanar yarinya ga Kuma abinda take musu,ummu bata fada da ita Saida babu abinda ke hadasu sabanin Addayiya da mamu sosai suke gaba gashi duk lokacin da akayi fada sai Alhassan yadau gaskiya ya bata cewa yake duk Mai son zaman lafiya dashi toh ya fita harKan Amina.




Amina bata da aiki a gidan sai dai taci ta kwanta tasha gwada gudu amma security ne birjit KoNan dacan bata iya zakudawa a cikin compound sai sun bita da Ido Suna duba Inda zata,Alhassa nada hakuri shiyasa yake zaune da Amina Yan garin su nadan zuwa kadan kadan ya musu hisani su tafi akwai wata Rana kanwar sulaiman tazo gidan ta a boye da letter (wasila) ta Bata akan sulaiman ne yace ta Bata sannan itama ta rubuta Masa reply kanwar tasa ta koma Masa dashi, Amina ta karbi wasikar shikenan tun daga ranan sai sulaiman ya dau kanwar sa suzo cikin gari don yaki komawa service,yan kitsa Mata rashin mutunci da zatana ma Alhaji ta yanda zaisa shi sakenta amma Abu ya gagara harsai wata Rana mamu ta Kamata suna magana da kanwar sulaiman plan in yanda zata fita su hadu da sulaiman, anan take ta sanar da Alhassa sosai ransa ya baci bana Wasa ba Kuma ya bincike dakin Nan ya samu wasikun da take Tarawa na sulaiman a ciki da durowan ta sosai Yama Amina fada akan martabar aure,da Kuma Hana security barin kowa daga kauyen su indai ba mutane uku bane, kawu inno da muneeru tunda har waya aka kawo aka Bata.





Yau surkin Alhassa sarkin katsina ya shigo gombe sannan ya iso gidan surkin nasa sauke sa a babban falo Alhaji yayi cikin mutunci kowa na gidan sai haba-haba yake da surkin nasa ana kawo abin Sha daci ana jerawa kowa Saida yazo ya gaidashi daman alhassan ya gargadi Amina don Allah kada ta kuskura tazo ,Aiko ita daman abinda zai kuntata masa shi take so tayi Masa,Suma tsaka da magana ta Fado falon mikewa Alhaji yayi Yana tare ta da cewa suje waje sai suyi magana amma Amina taki ta fita,saima ta hau Kan kujera ta kame.




Kunya Kamar ya kashe Alhaji sai lallabata yake ta tashi su fita surkinsa ne karta kunyata shi amma abin bakin ciki mikewa Amina tayi tasa kafa ta shurar da kulolin abincin dake gaban sarki ta Soma masifa akan bazata tafi ba saiya saketa bazata zauna dashi ba,dafe kansa yayi cikin takaici sai Kuma ya sulale ya Fadi Koh motse bayayi salati muzammil daya shigo gidan kenan dawowar sa daga makaranta Addayiya ke sanar dashi sarki na falon babansu yaje ya gaidashi,ya jima a bakin kofar Yana Jin duk abinda ke faruwa amma baice kome ba don yasan Koh yayi magana baban sa zai gwatsele sa akan Amina.





da gudu ya shigo dakin yayi Kan mahaifin nasu sai Kuma ya sake kuka yana kwalama mutanen gidan Kira ya mike da gudu yabar falon sarki ma mikewa yayi yana salati ya matso wajen alhassan in bayan ya dauko ruwa yana shafa Masa amma ina shuru,saiga muzammil da fadawa da suke tsatsaye a kofar flat in da sauran Yan gidan suka shigo falon da gudu cikin tashin hankali Amina dake gefe da Sauri tayi hanyar kofa jikinta na rawa bata taba Shiga tashin hankalin da ta shiga ba, karfa mutuwa Alhaji yayi.





Mikewa muzammil yayi yabi bayan ta da gudu tana kokarim dannawa kofa sakata ya bango kofar ya shigo bell nasa lafiyayye ya Soma lafta Mata da iyya karfin sa Daman ya girmeta da shekara biyar a lokacin Yana da 21year,mugun duka ya rufeta dashi baji ba gani duk takaicin da take dura Masa a gidan yau shiyake sauke Mata, dukanta Yake Yama cewa kafun ta kashe Masa uba shi zai Fara kasheta har lahira inyaso ana binne ubansa ana tona kabarinta a gefe.................................



🍀*By Ruqeenjalal*🍀




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 96&97

babu Wanda hankalin sa ya kawo wajen dukan da muzammil kema Amina asibiti aka wuce da minister,mamu ce ta hankalta bayan an wuce da Alhajin asibiti Kara zuga muzammil tayi,shikuma yayi ta kirban Amina ba karamin duka Yama Amina ba Saida ya faffasawa Yar Fulani jiki kaca-kaca kafun ya Barta korata shida mamu sukayi a gidan har bakin titi mamu ta yafa mayafinta ta kora Amina muzammil na rike da bulala, sulaiman daya maida kofar gidan wajen zaman sa tunda aka Hana kanwarsa shiga shikenan ya maida wajen wajen zaman sa kullum Yana tsumayen wata Rana Amina zata fito Kamar a mafarki yaga Mai Kama da ita an hankadota daga cikin gidan,hankali tashe ya mike ya bi bayan su daidai lokacin muzammil ya watsa Mata bell da Sauri ya tare dukan tare da cakumar muzammil da dambe security dake kofar gidan da gudu Suka nufosu ganin wani na dambe da Dan minister a takaice dai daga Amina har sulaiman ranan jikin su yayi tsami bana Wasa ba.




Allah yaso sulaiman yana da kudi a wajen sa,dashi Suka hau mota zuwa kauyen su gabaki daya zance ya baza kauye sulaiman ya kashewa Amina aure inno batayi binciken kome ba ta hau fushi da Amina Koh sauraron raunukan dake jikinta batayi ba,sai muneeru dake Kai kawo a kanta.





ta bangaren gidan minister sai bayan tafiyar Amina sukaji labarin dukan da Muzammil Yama Amina,Amma babu Wanda ya damu don ba sonta suke ba Daman Kuma abinda tama mahaifinsu ya musu zafi,hawan jini ya samu sosai Koh hayyacin sa Bai dawo ba sai bayan kwana biyu ya Fara bude Ido,a ranan daya bude Ido da zancen Amina ya farka sosai ran Addayiya ya baci ita ta sakasa a wannan Hali sannan har Yana da bakin Kiran sunan ta bama yaki taba,baida magana saina Amina batazo ta dubasa ba Koh Bata da lafiya ne,da haushi ya ishi muzammil Anan yake ce Masa tana garin su ya koreta Aiko ranan sunga me ake Kira bacin Rai iya bacin Rai rikice musu yayi akan lalle lalle sai an sallamesa yaje ya dauko matar sa a kauye.







Abin fa ya wuce tunanin Mai tunani dole tasa alhussan tashi tare da basa Baki akan shi zaije ya daukota shi Kuma yayi hakuri ya zauna a asibiti sai jikin sa yayi sauki kafun yace zai bar asibitin.



Alhussan badon ransa yaso ba yaje garin su Amina,sosai inno tayita basa hakuri lokacin da ya zana Mata abinda Amina ke musu, daki ta Shiga ta jawo Amina tare da Mata kashedi Koh bayan ranta ta sake Masa makamancin abinda akace, indai ta rabu da Alhaji Allah ya Isa Bata yafe Mata ba Amina tasha jinin jikinta bana Wasa ba especially furucin inno gareta haka ta bi alhussan har asibitin halin da taga bawan Allan a ciki sosai jikinta yayi sanyi shikam cewa yayi ta zauna a asibitin kin Zama tayi saboda yanda kowa yazo sai taga irin tsanar da yake nuna Mata abayyane, komawa gida tayi sai dai tazo ta dubasa ta koma shikam yad'anji dadi kad'an ganin ta dan sauya Hali tayi sanyi ba Kamar da ba, ba'a San garin Yaya ba wani ya sanar da Alhaji dukan da Muzammil ya Mata sosai ya birkice yace muzammil kada ya sake taka Masa gida ya tattara yanasa yanasa ya koma hostel,wannan shine mafarin gabar da muzammil keyi da Amina ata dalilinta mahaifin sa ya bude Baki yace kada ya tako Masa gida akanta.




Alhaji yaji sauki inno da muneeru sunzo sun dubasa Kuma sun Kara basa hakuri akan abinda ya faru,su Umar hankalin su ya tashi haka zalika ransu ya baci na abinda mahaifin su yayi na korin muzammil,gashi yaran duka sun tsani Amina sosai,Umar jafar su Suka tattara yaran su da Suka Fara wayo sosai, muzammil Anwar

Please Login or Register in order to submit comment