Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ina Lahab?

Wani kallo Mami ta Masa Jin tambayar da ya Mata yasa ta kin kallon sama, sai mijinta daya basa amsa, muzammil Lahab Bai zo ba Allah dai yasa lafiya Koh?

Juyawa yayi fuuuuuu ya fita a gidan mami kam da dogon tsaki ta rakasa dashi.


*************

A makaranta yau Nnenna tayi ta zuba Ido da tsammanin ganin Lahab Amma shuru babu shi babu alamar sa gashi itama yau ta zubo Masa abincin gidan su ta kawo da zimmar zaizo.

A office in principal Muzammil ne da pastor baban Adewale sai bappa Ado,gabaki dayan su babu Wanda yazo da students in nan guda uku hakan ya Kara kular da malaman a ganinsu tunda har su Lahab basa Jin maganar iyayen su babu amfanin a bar musu su Lahab a makarantan.

Principal ne ya mike Rai a bace yace tunda har abin ya koma haka Ni d'aga yau bana son ganin yaran Nan a cikin makarantan naaaaaaaa




**************
Lahab na kwance Yana sharara bacci bashi ya farka ba sai kusan 10:30 na safe Nan ma yunwa ce ta tashesa bawai don ya koshi da baccin bane a hankali ya mike zaune Mika yayi a tsaye tare da hautsana gashin kansa Mai yawa da laushi,agogon dake dakin ya kalla,ganin 10 yasan yanzun babu kowa a gidan sai Mami hakan yasa sa fitowa a dakin d'aga shi sai wando 3quiter dake jikinsa bude kofar yayi ya fito falon Yana kaikaya gashin kansa.

Mami dake zaune akan kujera tana feeding na yaron ta Mai kimanin shekara 1 fari Sol dashi kyakkyawa, Lahab ne koh dai ba Kai nake gani ba?

"Dan tsayawa yayi sai Kuma ya shagwabe fuska yace nine mami"

Kardai kace min a gidan Nan ka kwana na bunu yayan ka yazo neman ka nace baka Nan?

"Matsowa yayi kusa da mamin ganin kaninsa dake Kan cinya ya sake no-no Yana ihu Yana Mika Masa hannu Wai ya d'auke sa,sa hannu yayi ya dauki yaron ya wurgashi sama ya cabe ai a take ya shiga babbaka dariya har hakoransa guda biyu na kasa suka bayyana.

Murmushi Mami tayi,kasan Yusuf ya d'auka Rahab ne harda marmarin ka dagasa,don kai dai bantaba ganin ka d'auke sa ba da sunan Wasa.

"Aikam Naga alama Mami na Yana maganar Yana Kara wullah yaron sama.

Kai Lahab ban yarona karka zoka kadamin shi a banza,tace tana kwace yaron,dariya yayi kawai ya zauna akan daya d'aga cikin kujeran da Yusuf a hannunsa don yaki sakema mamin shi,itama kitchen ta nufa abinci ta Iba ta kawo wa yaron ta Kuma dan farinta Mafi soyuwa a ranta,sarkin rigima Lahab,Jan center table dake tsakiyar falon tayi zuwa kusa da kujerar da Lahab ke Kai ta aje masa.

gyara zama lahab yayi da Yusuf a kafan sa ya soma cin taliyar da mami ta aje masa, itama mamin zama tayi a gefen lahab suka soma hira na tsakanin d'a da uwa, wai lahab meka yiwa muxammil ne yazo yana nemanka a fusace, Lahab kai me kake so ka zamane da bazaka natsu kamar dan uwanka ba?ka duba yanda kowa ke maganar rashin jinka Sam banajin dadin abinda kake,ga taurin kai ga kin zuwa makaranta.

Kwarewa yayi garin zai baiwa Mami amsa da Sauri ta mike ta ibo masa ruwa da kanta ta kafa masa kofin a baki, hannun sa ya daga ya daura akan hannun nata yana sha,Yusuf dake kan cinyansa hannu yasa akan plate in taliyan ya dumbula wai zaici, dan janye bakinsa akan cup in lahab yayi ya kama hannun Yusuf in.

Zama mami tayi ta aje kofin ruwan hade dasa hannu ta karbi Yusuf in tana cewa lahab, maza kaci abincin saika amsa min meka yiwa muzammil.

dan shuru yayi sai kuma ya aje spoon in hannunsa kallon mamin yayi a hankali hace"mami nasan kaf duniya koh zan fadi Abu Aki gaskatawa indai gaskiya ne na tabbata zaki yarda dani koh"?

Kwarai kuwa Lahab, Mami tace

"toh mami na fada miki wani Abu"?

Eh fadamin naji Lahab.

"Wallahi mami jiya farida matar da Anwar zai aura na gani a hotel taje party har 12 na dare"

Mikewa mami tayi tsaye har Yusuf na subuce mata a hannu ta tarosa ta soma tambayar sa, Lahab kai meya kaika hotel harka ganta karfe 12 na dare.........????



*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 49&50
sunkuyar da Kai Lahab yayi bai bawa Mami amsa ba,wanke sa da Mari tayi cikin bacin rai tace,bazaka fadamin mai ya kaika hotel a lokacin? Lahab me kake son Kan Zama ne,ashe shiyasa muzammil keta nemanka ruwa a jallu?

dafe kumatun sa yayi Yana kallon Mami dake ta surfa masifa meya kaisa hotel,mikewa yayi Koh riga babu ya Kama hanyar fita,kwala Masa Kira Mami tayi,Lahab Lahab Ina zaka Ni sa'ar kace da Ina maka magana zaka wuce ka fita,toh ka dawo Nan,ta nuna Masa kujerar daya tashi,kin dawowa yayi ya bude kofar falon ya fita ya maida kofar da karfi ya rufe,shi abinda yafi Bata Masa rai ba kome bane illah Marin da ta Masa Amma in badon haka ba da dakansa zai gaya Mata kome.

Fita gate na gidan yayi gashin kansa a yamutse jiki ba riga,a haka yayita tafiya duk Inda ya wuce sai an bisa da kallo mutum lafiyayye amma ace Yana yawo ba cikekken tufafi,a hakan ya gangaro kasan unguwan gidan su abokin sa da ranan Suka aje Keke ya shiga,ya karbi riga,Keke napep ya hau bai zarce Koh Ina ba sai gidan yayan mamin sa uncle muneer Keke na sauke sa a kofar gidan ya biya Mai keken ya shiga gidan.



*******************
Nnenna tayi ta tsammanin ganin Lahab amma shuru shuru har 2 na Rana bata gansa ba dole yasa ta cin doyanta,bayan an tashi makarantan ita kadanta ta Kama yanda da kafa tana tafiya tana tunanin Ina Abraham ya shiga kwana biyu bata ganin ziryarsa a gidan.



Lahab Kam baisa mu uncle a gida ba Yana kasuwa, wanka yayi yasa Kayan mansur dan uncle muneer ya fita a gidan direct hotel in daren jiya ya koma daker aka barsa ya shiga Hall in,amma Yana shiga ya samu an gyara Hall in an share haka yabi sit by sit Yana duba wayar amma bai gani ba,wajen manaja hotel in ya nufa, office in ya tura ya shiga bayan an basa izini, "Assalamu Alaikum"

Waalaikumu Salam Bismillah ka zauna?

Zama Lahab yayi Kamar yanda manaja ya bukata,an wuni lafiya"?

Lafiya Alhamdulilah ince dai lafiya Koh hall kazo kamawa?muna da hall masu girma da tsari Kama daga na birthday har na program in biki

"No ba hall nazo kamawa ba sir jiya nazo party a hotel Nan a cikin hall naku na kusa da packing space so na manta wayata ne ta Fadi a karkashin kujera shine nazo na tambaya Koh Allah yasa cleaner naku sun gani wayan is very important to me ne shiyasa na dawo.

a gaskiya banace ba saboda Ni da safe na tura cleaners suje su share Hall in sai dai bara a Kira su a tambaye su Koh sun gani?

"Ok toh ba matsala yallaboi"

Waya manaja ya d'auka yayi Kira ba'afi 10 minutes ba sai ga ma'aikata masu share share sun shigo su biyar ne,Suna shigowar suka gaida manajan kallon su yayi,a cikin ku su waye Suka share Hall in kusa da packing space?

Mune sir wasu guda biyu sukace mace dana miji,kallonsu again manaja yayi kafun yace,akwai phone da aka manta a hall in koh akwai Wanda ya d'auka a cikin ku?

duk kansu biyu girgiza Kai sukayi da Sauri macen sai wani zare Ido take tana tsinne kai,mikewa kawai Lahab yayi ya fita a office in Jin manaja nace Masa su Basu ga wata waya ba taima ma a cikin wa'inda sukazo party wani ya d'auka,Yana fita a hotel in machine Lahab ya hau zuwa makarantan su har sun kusa da makaranta ya hangi mace na tafiya sanye da uniform Kuma Yana kyautata zaton Nnenna ne d'aga tafiyan ta ya gane ta sauka yayi a keken ya biya Mai keken kudinsa yabi Nnenna a baya ba tare da ya Mata magana ba.


dan dakatawa Nnenna tayi haka kawai jikinta ke bata ana kallonta juyawa tayi tana kallon bayanta,Kamar a mafarki idanunta ya shiga cikin nasa waro Ido tayi cikin happy tana kallon sa,Shima kallonta yake Yana murmushi ji yake Kamar yayi shekara Bai ganta ba sosai yake kewanta.

matsowa yayi kusa da ita har lokacin fuskar sa d'auke da murmushi,hannun damansa yasa ya Kama haggunta,da Sauri ta zabura tare da kokarin fusge hannunta Amma Ina ta kasa don riko ya Mata na gam gam,sakeni shine abinda take cewa tana dad'a fisge wa,"kee ki natsu Mana"Jin abinda Lahab yace Mata yasa ta d'aga Idonun ta tasa a cikin nasa sosai take bin fuskarsa da Ido,ka sakarmin hannu yamma yayi Zan koma gida.

bai bata amsa ba sai hannu daya sa ya dau jakanta dake kafadarta ya bakka a bayansa har lokacin bai sake Mata hannu ba ya Soma tafiya tana binsa a baya tafiya suke babu Mai magana,tsallake titi sukayi ya nufi wani babban restaurant kallon wajen Nnenna tayi sannan ta sake kallon sa,Inane Nan?

Koh ma inane muje in mun shiga Zaki ganewa idanunki,shiga wajen sukayi har lokacin hannunta na cikin nasa Zama yayi akan kujeran dinning dake wajen yaja Mata nata"ki zauna"

"Nifa bana Jin yunwa"

"Uhmm Koh bakiji sai kinci"

Abinci aka kawo musu fried rice sai ferfesun kaza,plate biyu aka jera musu,shokali Lahab ya d'auka ya Mika Mata ganin bata d'auka ba karba tayi ta rike tana bin abincin da kallo, Lahab Kam harya Soma cin abinsa Amma hankalinsa na kanta ganin har lokacin bataci kome ba yasa sa magana,"Wai bazakici abincin bane in Kuma bai Miki ba sai kiyi magana a kawo abinda kikeso"

girgiza Masa Kai kawai tayi ta saka shokali a plate in shinkafan ta Iba sosai takebin shinkafan da idanu sannan a hankali ta matso dashi kusa da hancinta da Sauri ta maida shi cikin plate in"ni nace maka na koshi fa"

abincin sa Lahab ya cigaba daci sai Kuma ya dakata Jin tambayar da Nnenna ta Masa,shin "meyasa bakazo makaranta ba yau"?

"Hakan kawai"shine abinda yace Yana daukar cinyar kazar yanaci.

"Naji jite jite ance Wai an koreku"?

Hhhh korata Kuma Labiba?Aiko an koreni anyi a banza bayau aka Saba ba Kuma nake komawa.

"Kamar ya kenan bangane ba"?

"Jira nake case in yayi sanyi saina dawo"

Uhmm meyasa toh kaki komawa gidan ku?Nnenna ta tambaye sa again

da Sauri ya kalleta da mamaki yace"waya fadamiki bana gida?

dan sassaita kanta tayi shuru,Kara tambayarta yayi shuru ba amsa Shima bai wani damu ba don yasan bazai wuce a bakin Yan gidansu Koh malamai zancen ya fitoh ba.

Yago kazar yayi ya nufi bakinta Yana cewa"haiii bude Baki na saka Miki"kin bude bakin tayi sai wani kallo da take Masa Shima yaki sauke hannun nasa dake d'auke da tsokar kaza,a hankali ta Soma magana"nace maka banaci banaci dole ne"?

Sauke hannun nasa yayi Kamar ya hakura sai Kuma ya shammace ta da Sauri ya tura Mata namar a Baki,ai a take tasa hannunta ta buge hannun nasa sai da ya Fadi daka kan kujerar zuwa kasa yayin da ita Kuma ta duke a wajen tana tufar da kazar dake bakin nata,sai Kuma ta dago da Sauri Jin yanda Lahab ke Nishi abin mamaki kwance yak har lokacin ya kasa tashi sai wani had'a zufa da yake Yana rike da hannunsa.


***************
Juyawa su mubeeena sukayi da Sauri Suna duban Wanda ya fadin ba kowa bane face Ahmad kwance a kasa ya Suma uhu mubeena ta sake ta nufesa da gudu tana kuka,dukawa tayi a kusa dashi tana girgiza sa tana kuka,don Allah ka tashi Ahmad in wani Abu ya faru dakai bazan yafewa kaina ba.

Rukayya Kam da gudu tayi gate na makarantan nasu Keke napep ta tare ta shiga Suka dawo makarantan har wajen da mubeena suke Suka matso sauka tayi tare da rokon Mai keken napep in akan ya taimaka masu asa Ahmad a aciki,da taimakon Mai Keke da wasu samari aka sa Ahmad a Keke napep Suma su mubeena suka shiga,asibiti aka wuce da Ahmad direct d'aga zuwansu aka basa gado,gashi su mubeena nada paper gashi sai kuka take daker dai rukayya ta lallabata tare da karban wayanta daman akwai number kanwar Ahmad Kira Rukayya tayi ta sanar da ita an Kama yayanta a gadon asibiti,basu Kai Koh 20 minutes ba saiga kanwarsa da mamansa da babansa sunzo,Suna tambayar abinda ya samesa mubeena ta kasa magana sai kuka sun ma rasa me zasuce sai rukayya ce tace musu Suma Basu sani ba kawai ganin sa sukayi ya yanke jiki ya Suma a makarantan su.


Ok toh Allah ya basa lafiya shine abinda baban sa yace,Suma Su mubeena Addu'a samun sauki Suka Masa sannan Suka fita a hospital in mubeena taso ta koma gida amma Rukayya tayita lallabata daker ta amince Suka koma school Suka rubuta paper,sai yamma lilis mubeeena ta nufi gidan su tunda ta sauka a Keke napep ta hangesa tsaye a kwanar layinsu,Yi tayi Kamar Bata gansa ba har tazo saitinsa zata geftashi taji ya Kira sunan ta,mubeena mubeena.

Shuru tayi bata amsa Masa ba takowa yayi Suka Soma jerawa tare har lokacin bata kulasa ba,dan Allah mubeena ki saurare ni mana wannan wulakancin duk saboda nace Ina sonki ne?

dakatawa tayi tare da Soma magana,kaga Adewale ka fita d'aga harkata da rayuwa ta banason dogon zance in Kuma kaki wallahi saina shimfida maka dana sanin da zakayi nadama.

Nadama fa kikace mubeena menene abin nadama a sonki da nake.

dan Allah dakata son banza kenan toh bari na fada maka Ni bana sonka bana sonka bana sonka wannan kalma jinsa yayi tamkar kifiya haka yajita a Randa sosai maganar ta Masa zafi Wanda yasa sa kasa binta sai Ido daya zuba Mata har ta shiga gida.

Da sallama mubeena ta shigo gidan nasu, Assalamu Alaikum

Waalaikumu Salam mubeena sai yanzun?

Eh wallahi Inna kinsan exam muke shiyasa ban dawo da wuri ba.

Toh ki Shiga ciki ki Kwabe kayanki ga abincin ki Nan saiki zo ki d'auka.

Toh Inna shine amsar da mubeena ta bata tana shiga dakin Kwabe kayan jikinta tayi ta daura fellen zani a kirjinta ta fitoh a dakin kitchen ta shiga ta dauko kwanon abincin nata ta zauna a gefen taburman da Inna ke zaune akai bude kwanon tayi dan wake ne yaji burkono da Mai gaurayawa tayi tayi Bismillah ta soma ci a hankali bawai don tana ra'ayi ba sai gudun kada Inna ta zargi wani Abu,ta danci kadan kafun ta rufe kwanon alamun ya isheta.

Badai Harya isheki ba mubeena?

Wallahi Inna na koshine.

Wani irin kin koshi mubeena abincin da kikafi sone fa na girka Miki sannan Koh shokali biyar lafiyayye bakiyi ba kicemin kin koshi?

Mikewa tayi ta dau bucket ta nufi rijiyan dake tsakiyar gidan ta zura guga tanajan ruwa ba tare da ta baiwa Inna amsar taba itama innar bata Kara magana ba sai binta da kallo da take gabaki d'aya yarinyar ta susuce ga tarin damuwa a fuskar ta amma tasan halin mubeena da zurfin ciki shiyasa bazata sake tambayar ta damuwar taba sai in tayi ra'ayi da kanta ta fada Mata, bucket in na cika ta shiga daki tadau kwandon sosonta ta sabe bucket in tayi cikin bayan gida.


Bappa Ado ne ya doko cikin gidan Koh sallah babu tsabagen yanda ransa ke bace,ah ah Ado menene haka ya kana girma kana Kara shiga daji aka sallamar ma ya gagara zaka Fado Mana cikin gida Kai tsaye.

dan Allah Inna kiyi hakuri raina ne duk a bace.

In ranka ne a bace Ado sai ka shigo waje ba sallama,Zama yayi agefen ta wajen da mubeena ta tashi tare da cewa Inna,wallahi Inna yaron Nan Nabeel ya raina mu?

Meya faru Kuma me yayi akace maka a makarantan?Inna ta tambaye sa.

Inna Wai kinji abinda shugaban makarantan su yace Ashe Nabeel da Yan iskan abokan San Nan Suka hadu Suka bugi malamin su.

Da mamaki Inna ta ce,dukafa kace Ado Kai Amma wa'innan yara anyi marasa kunya shi Kuma Nabeel ShaShaSha su duk abinda Suka aikata Suna da gata shi Kuma fa Ado kana ganin kudin makarantan su yaron Nan dubu darine fa duk tam(team) su suke biyan Masa maimakon ya tsaya ya more su yayi karatun sa saiya tsaya shashanci su sukiyi Shima yaki.


Gyara Zama Ado yayi,wani irin karatu ma Inna bayan an koresu.

An koresu fa kace Ado?

Kwarai ma kuwa anan ya fada Mata duk yanda akayi da principal sosai Inna tayita mita kawo Ado sallama yayi Mata ya tafi abinsa.


Nnenna Kam kuka ta sake sosai ganin halin da Lahab ke ciki sai had'a zufa yake Yana dafe da daya hannun nasa yama kasa Koh mikewa zaune,da Sauri ta matso wajensa tasa hannu ta dagosa zaune, customers dake cikin restaurant in gabaki dayansu hankalin su ya tashi ganin halinda Lahab ke ciki ga kukan da Nnenna keyi su Karan kansu ma'aikata sun tashi hankalinsu ganin wani ya Shiga matsala a cikin shagonsu.

Mutumin dake zaune kusa da table in su Lahab ne ya mike a hankali ya nufi Nnenna ganin mutanen wajen sai zaginta suke akan kome ya samesa itace sanadin kome harda cewa su fitar musu a shago,karasowa yayi kusa dasu yasa hannu ya dago Lahab tare da kallon Nnenna dake ta kuka jikinta sai rawa yake harga Allah Bata bugi hannunsa da niyar cutar dashi ba mutumin da ya taimaketa a rayuwa yau an waye gari ita ta cutar dashi,dau jakanki muje asibiti don ina tunanin ya samu matsala a hannun sa,shine abinda mutumin yace Mata Yana tafiya da Lahab bayan ya tallafesa.

Da Sauri tadau jakanta tabi bayan mutumin daya riga ya fita waje,amma abinda ya bata mamaki shine tana fita kawai ta nemi mutumin da Lahab ta rasa,hankalinta a tashi ta Soma tambayar mutanen dake tsatsaye a bakin restaurant in Koh sunga wani mutumin sanye da farin jamfa da wando Yana rike da wani dan makaranta?amma kowa cewa yake baigansu ba dawowa tayi cikin restaurant in ta tambaye su Koh mutumin bai fita bane amma Suka tabbatar Mata ya fita Mana harma tabi bayan sa,dafe kanta tayi da karfi jikinta na rawa sai Kuma ta Mike da mugun gudu ta fita a cikin restaurant in.................




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 51&52
Sosai ta rikice tana bin wajen shagon da Ido sosai jikinta na rawa kallon wani Forest dake gefe da shagon tayi,da Sauri ta nufi dajin tayi cikin bishiyoyin kaman ance ta dubi damanta kawai taga mutumin nata Sauri da Lahab Kamar ma baya hayyacinsa,da wani irin mugun gudu ta nufi mutumin unexpected tasa hannu ta bangajesa har Saida Lahab Shima ya Fadi timm a Kan wasu ciyawe wuyan mutumin ta shake da karfi sosai ta had'a bayansa da jikin wani bishiyan zaiti,sosai ya shaku Wanda a take kamanninsa Suka Fara sauyawa zuwa na wannan tsohon sosai jikinta ya Kara d'aukar rawa Shima sai kokarin kwatar kansa yake a wuyanta ga tari na caarkesa Kamar xai mutu,ki taimaka karki illah tani ki sakeni ki sakeni Zaki cutar dani akan wannan yaro,shine abinda tsohon yake fada har lokacin ya kasa kwatar wuyansa.

Hawaye ne sun cika idanun Nnenna ta soma magana"na maka gargadi na sake na maka gargadi akan Hassan ka fita daka hanyan sa amma kaki na fada maka kabar zuwa Masa a mafarki kaki sannan yanzun ka koma farautar sa"?

Jin abinda tace yasa sa zabura cikin zafin nama yasa kafa ya tunkudeta sai da ta Fadi a kasa a take ta Mike tsaye tana binsa da mugun kallo,tabbas dole na bibiye sa tsawon shekaru muna baki kariya akan me rana tsaka zaizo ya chanja Maki zanen kaddarar ki d'aga tsarin mu zuwa nasa.

"rufemin baki ku kun Isa ku zanamin kaddarar rayuwata kun Isa babu Wanda ya Isa ya tsara wa mutum abubuwanda zai faru dashi bace abinda God ya tsara wannan karyane"

Bari kiji bazamu lamunce Hassan a rayuwar ki ba bazamu lamunta ba tsawon shekaru kin rayu bisa tsarin mu baki Isa ki kauce ba ata dalilin sa ba ki kaurace Masa muddin kina sonsa a raye.

"taya Zan rabu dashi tunda nake bantaba samun Wanda ya damu da damuwa ta ba ban tana haduwa Koh Samun Wanda yakeson kasancewar dani a tare dashi ba,sai yanzun Hassan ya rabeni ya nuna min tausayi shida shayibu mundin kanason kanka da lafiya ka fita harkan sa ka fita harkansa ka fita wannan ne gargadi na karshe da Zan maka na rantse ka Kara rabarsa nice ajalinka kaji ka fada musu iyya wuya Ina tare da shi"tana karasa maganar ta tsunguma ta cicibi Lahab abin mamaki ba tare da ta wani ji nauyinsa ba abayanta ta goyasa ta dau jakanta ta juya tana tafi ba tare da ta sake kallon Inda tsohon yake ba har ta bar Forest in.

Maharbi dake tsaye tun d'azun a cikin wasu ciyawe da Ido yabi Nnenna Harta bace sannan ya dawo da kallonsa ga tsohon amma Ina baigansa ba girgiza Kai kawai yayi yaci gaba da tsintar maganin sa.

Nnanna har bakin titi ta fitoh da Lahab a bayanta Keke ta sayar Mai keken tsayawa yayi Yana tambayar ta Inda zai kaita ganinta d'auke da mutum a bayanta ga hannunta rike da jaka.

"Asibiti nake so ka kaini" Nnenna tace cikin turanci.

Ke in zakiyi hausa kimin hausa.

Shuru Nnenna tayi don bata fahimce me yake nufi ba gashi bata iyya hausan ba,Mai Keke Kam Jan kekensa yayi ya Kara gaba ya na masifa.

Ta Jima a wajin kafun ta samu wani Mai keken dan niga-niga dashi,tace Masa asibiti zai kaita.

Cikin dan gaya gayan turancin sa yace mata meya samesa naga baya motse.

Kawai malam ka kaimu asibiti,shine abinda tace kenan tana kallonsa.

shiga muje,a hankali ta sa Lahab a cikin keken itama ta Shiga,wani asibiti Zan kaiku?Kowan ne ma maikyau sannan don Allah kayi Sauri.

Karki dawo da gudu ya fege keken bai tsaya Koh Ina ba sai wani Private hospital ya faka.

Sauka Nnenna tayi tare da rokonsa ya Kama Mata Lahab su shiga ciki.

dazun waya d'auka Miki shi da yanzun Zaki wani ce na rike Maki shi da Allah ban kudina na Ware.

Waro Ido tayi sai ma yanzun ta tuna bata da ko sisi a hannunta,kaga ka taimaka ka Kama mini shi mushiga saina karbi kudinka na baka,cikin masifa yace daman kudin nawa bake Zaki bani bama kenan?

Shuru tayi taki kulasa Shima cikin haushi yazo ya Kama hannun Lahab da Sauri ya zabura domin hannun ne Nnenna ta buge Masa,"Kai malam menene haka nace maka hannunsa zaka kama ne"

don Allah rufemin Baki Yar banzan inyamura In ba hannu ba Ina kikeso na Kama Masa,Bata kulasa ba tasa hannu ta cicibi hakarkarin sa ta cirosa a keken wani cleaner ne yazo da gudu ya taimaka Mata ganin Kamar zata fadi.

Cikin asibiti Suka shiga da gudu akazo aka karbi Lahab akayi wani daki dashi,Zama tayi a hall in Mai Keke sai masifa yake akan ta basa kudin sa kin kulasa tayi har hankalin mutane ya dawo kansu wani mutumine ya tambaye sa kudin sa yace 200 ne yasa hannu a Aljuhu ya zaro 500 ya Mika Masa.

Canji Mai keken ya basa Amma yace Masa ya bari kawai, sosai Mai keken yayi ta godiya ya juya ya tafi,kallon ta mutumin yayi,Kinga Yaya karki Kara shiga abin mutum in baki da kudin biyansa hakan babu kyau gwara ki roka ya kawoki a kyauta kinjiko?

Kallonsa Nnenna tayi Kamar Mai gane abinda yake fada tadai fahimci Holo yake Mata hakan yasa ta gyada Masa Kai ba tare da tayi magana ba ta Mike Jin ana niman Wanda ya kawo patient asibiti,mikewa tayi tace itace kiranta nurse in tayi tare da Mika Mata takarda ta Sayo abinda aka lisssafa,daukar jakan makarantan ta tayi ta karbi takardan tana sake saken ina zata samu kudi ita Kuma har tayi nisa sai Kuma ta dawo tunawa da d'azun taga Lahab yasa hannu a Aljuhu ya zaro kudade a restaurant da Sauri ta shiga nurses station ta roki nurse in akan tanaso taga lahab.

Kee yanzun dai doctor na ciki Kuma tsagewan Kashi ya samu za'a daura Masa hannu sannan kizo kice Zaki gansa bama ta abinda akace ki siyo kike ba.

dan rusunawa tayi tace"sorry ma bani da kudi a hannusa shiyasa nake son ganinsa Zan dau kudi a Aljuhunsa"Jin abinda Nnenna tace yasa nurse

Please Login or Register in order to submit comment