Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Soma ci a hankali saukowar yayi shima yadau spoon yazo ya zauna a kasan carpet in yasa ya Soma ci,dago Kai tayi Suka had'a Ido sai Kuma ta maida kanta kasa tana cigaba dacin abincin nata 5 spoon tayi ta aje spoon in tana daukar ruwa da Lahab yasha ya aje ta Sha mikewa tayi tsaye tare da aje Masa plate in a gaban sa"ka tashi ka bude min kofa Zan tafi gida Dad nawa zai nemeni yamma yayi sosai"



Kin mikewa yayi yaci gaba dacin abincin sa har lokacin Ade bai fito ba,komawa tayi ta zauna tayi mugun hade rai wayarta ne yayi ringing hannu tasa ta dau jakanta dake kasa ta bude wayar ta zaro ta duba Mai Kiran nata Abraham ne tsaki kawai taja ta maida wayar a jaka, indomie ya cinye tass ya dau plate in yakai kitchen dakin Ade ya shiga zaune ya samesa ya tasa wayar sa a gaba Yana kallon screen.



Hannu yasa ya fisge wayar dake hannun Ade da Sauri ya zabura sai Kuma Yana tsaki tare da kwace wayar NASA"dariya Lahab yayi yace"wato Kai haryau kana fama da wannan makauniyar soyayyar"?in soyayyata makauniyace toh kaima ka Fara makancewar"da shekiyanci Lahab yace"Kamar ya nima na Fara makancewar"?




Wani murmushin gefen Baki Ade yayi ya nuna kofa yace Masa gata a falo"da Allah waya cema soyayya nake"in ba rami Lahab meya kawo zancen Rami ai nima bance ba"juyawa kawai Lahab yayi Yana cemai kaga na tafi sai kaci gaba da kallon hotonan nata ban ma San a Ina ka samo pictures in ba nadai San ba ita ta baka ba malam"



Fitowa sukayi a gidan boronta Lahab ya bude yadau wayar ta number sa ya saka ya Kira wayar sa ya maida Mata itadai tana kallon sa batace kome ba tsallake titin sukayi har lokacin Yana binta Suka nufi layin su,tayi tayi dashi ya koma amma ya ki tun daga nesa ta hangi Dad Mom da sauran Yan gidan tsaye a compound na gidan daga ka gansu kasan hankalin su ba'a kwance yake ba Abraham nata surutu,da Sauri Nnenna ta dakata tare da rokon sa akan ya koma kada iyayenta su gansu tare.




Tsayawa kawai yayi ita Kuma ta wuce amma Yana iyya hangota tunda ta nufi cikin gidan gabaki d'aya Suka zuba Mata Ido tana shiga Dad ya wani zabura cikin bacin Rai Suka rufeta da fada mom Kam tsinketa da mahaukacin Mari tayi Nnenna ta dafe kumatun ta tana hawaye,ashe abinda su Lahab basu sani ba lokacin da ya rike hannunta Abraham dake cikin mota ya hangosu harda shiga gidan su Ade da sukayi shine ya dawo ya sanar da iyayen sa ya kirata Kuma taki d'agawa sosai Dad ya zazzage ta tare da cewa duk randa ya Kara ganinta da wani dan hausawa sai ya cireta a makaranta Kuma ta bar Masa gida.




************************
Friday gidan su Lahab yau Koh matsakin tsinke babu yau ne d'auren aure, jama'a ne kamar kasa,kayatattun abincin dauren aure ake shiryawa a takeAway Masa ne da miyar ganda sai drink's ana arrange na abubuwa da gift na d'aurin auren sosai gidan ya hargitse da jama'a especially da yanzun kwata kwata bai wuce 3 hours ya rage a daura auren ba bayan sallan juma'a,Lahab dake daki ya fito wanka daure da towel,da mamaki yace"Rahab ya na ganka har yanzun da towel baka shirya ba harna fito wanka"?



Juya fuska Rahab yayi yace"Ina ruwanka ne Wai ma"?babu ruwa na Kam shine abinda Lahab yace Yana shafa Mai a jikinsa bayan ya goge, wayar sa dake gefe ya d'auka ya Kara Trying number ta a Karo na ba adade Kamar yanda ya Saba haka yaji a kashe,mikewa yayi ya bude wardrobe nasa farin shaddan sa ya zaro sabo gal dashi sai maiko yake zura wando yayi yasa rigan have joppa ne, liss yasa a hannun sa baki yad'au takalmin sa sabo shima Baki ya sanya bayan yasa socks Baki hula ya saka Baki ya sanya ya daura agogo kallon kansa yayi a madubi yayi wani mugun kyau ga kwarjini daya bayyana kirikiri a fuskar sa ga sajen Nan NASA ya taju yayi kyau turare ya d'auka ya feffesa,had'a Ido sukayi da Rahab dake kallon duk abinda yake,hararan sa kawai yayi baice kome ba ya sa Kai ya fita a dakin,ganin har 1:30 yayi.



A hankali yake tafiya Harya nufi corridorn Abbu Yana dube dube gudun kada wani ya gansa dayake sashen Abbu babu Baki a wajen gashi abbun ya tafi masallaci,bude dakin yayi da Sauri ya Shiga wajen drowern mirror ya nufa ya bude Key's na car insa daya sabuwar ya d'auka da Sauri ya nufi kofar Harya bude kofar sai Kuma ya koma baya da Sauri ya nufi cikin cotton na dakin ya boye ummu ce ta shigo dakin hannun ta d'auke da food flask Mai kyau d'auke da abinci ta aje a dakin ta juya ta fita da Sauri shima ya fito tare da nufar kulan ya bude kazane aka soya Masa sai tuwon shinkafa da akayi miyan shuwaka aka tsoma Kazan a ciki spoon yasa ya dauko cinya daya ya maida kulan ya rufe fitowa yayi a dakin bayan ya cinye cinyar ya bude kofa ya fita Inda Allah ya Sosa Harya iso babban falo ba Wanda ya gansa kofar baya ya nufa ya bude sai gashi ya fito a bayan flat nasu.






garejin ya nufa ya bude,wata babban Jeep ya nufa ya bude duk da akwai Kura kad'an haka ya kunnata bayan ya shiga yayi reverse yaja motar,ya ratso tsakar gidan da mamaki mamu tace"ah ah waya dau motar Alhaji Kuma bayan ya fita amma wallahi Shareef bayajin magana Sam Sam kullum ina fada Masa ya daina daukar motar baban sa Amma bai dainawa"sai Kuma ta nufi motar ganin ya tsaya Mai gadi na bude Masa gate.




da Sauri wata kawarta tace"haba Amina yaufa daurin auren yayan sane ki barsa Mana Kika sani Koh zai d'auko Yan daurin aure Jin abinda sukace yasa ta komawa ta zauna Suka cigaba da hiran su ana kimkimtsa abinci.




da gudu Lahab yake fasa unguwa duk Inda ya wuce Saidai kaga Kura fuuuuuuuuu yabi motan a baya jama'a sai kallon motar suke Suna salati a guje ya nufi kofar gidan su Nabeel tun daga nesa Suka Fara dariya don su wallahi kallo daya suke ma motar da Lahab ke tukawa su gane shine daga gudun motar kawai zaka gane, parking yayi Saida motar tayi gaba kadan ta dawo baya kafun ta tsaya,matsowa kusa da motar sukayi Nabeel Yana cewa"don girman Allah ka baiwa Adewale key ya tukamu wallahi Lahab tsoron hawan motar da kake tukawa nake ji nake Kamar ajalina na tinkaro a cikin motar .




glass baki Lahab ya dauko ya kwaba a fuskar sa yace"kaga Ade shigo muje lokaci na kurewa don Allah karna rasa sallah bude gaban Ade yayi ya shiga,Nabeel Kam badon ransa yaso ba ya bude baya ya Shiga ya zauna har Lahab ya tada motar saiga mubeena ta fito daga gida da Sauri ta nufi motar cikin zakuwa dason ganin abinda take so tunda taji Nabeel yace Lahab zaizo su tafi masallaci tayi wanka ta zauna tana jiran sa"Lahab Ina kuka nufane"da Sauri Adewale yace masallaci zamuje in akwai Inda kike son zuwa shigo mu sauke ki"




"Masallaci zamu Kuma mun makara don haka kawai big Aunty ki nemi motocycle,bude bayan motar tayi ta shiga tana cewa"wallahi sai ka kaini Zan sauka a kofar gidan su Fati dake hanyar tudun wada Kuma ai Naga sai kunbi wajen kafun ku Isa massalacin"kala Lahab baice ba yaja motar Suka cillah,tafiya suke motar shuru babu hayaniya sai wakar da Lahab ya sake duk ya cika musu kunne Nabeel Kuma Allah Allah yake su sauka lafiya bini bini mubeena sai ta kalli madubin gaban motar amma abin takaici maimakon taga Lahab sai su had'a Ido da Ade.




Sun aje mubeena a tudun wada kafun suka wuce masallaci Ade kawai Suka Bari a mota,su suka Shiga ciki after jumaat prayer,kofar gidan su Lahab mazane a cike tim don auren Aisha ma anan za'a d'aurashi dole waje ya cika d'auren aure biyu za'a Yi gashi d'aga bikin na farko ne,bayan an daura auren kowa ka gani fuskar nan Kamar gonar auduga kada ma sadeeq yaji labari Wanda aka daura nasu akan sadaki naira dubu 100k cicib,Anwar kam yake kawai yake Amma kowa ya gansa zai zaci baida lafiya ne gabaki d'aya yayi sanyi sai yawo yake a cikin gare.




Tund'a zun da Lahab ya Parka motar Abbu Abbu ya gansa kawai yayi shuru ne Albarkacin idon mutane amma kaffa kaffa yake da Lahab kada ya bar wajen da motar sa Lahab dake rarrabawa jama'a laidodi daya d'auko daga cikin gida a cike a basket babba duk Wanda ya baiwa sai kaji ana cewa wannan ba dan Alhaji Al'hassan dogo Mai naira tsohon minister,Kai Masha Allah tagwaye sun girma yau da gobe yafi karfin wasa,shikam Lahab rabon sa kawai yake da kalandun daurin aure Kamar ance ya kalli gabansa Rahab ne ya fito da basket gifts a hannun sa, sak irin shigar da Lahab yayi shine shima yayi Inka gansu a lokacin karyar ka banbantasu kome na Lahab Rahab yasa hatta turaren sa sai yanzun Lahab ya fahimci dalilin dayasa Rahab yaki saka Kaya Harya bar dakin, Adewale dake gefen sa shima Yana rabawa mutane takeAway yaji an fizgo sa da Sauri ya juya sai Kuma ya sake laidan hannun sa ganin Wanda ya rikesan ba kowa bane illah..........................




🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page92&93

Papa ne ya wanke Ade da wani irin Mari ya hau masifa hakuri jama'a Suka Soma basa ana cewa yayi hakuri ya bar Ade amma Ina keyar Ade ya tasa a gaba Suka bar wajen,Lahab Karan kansa ransa ya baci bana Wasa ba Sam baijin dadin irin yanda papa ke nuna masu kiyayya Kiri-Kiri babu Koh boye-boye,rarraba abinci suka cigaba dayi shida d'an uwan sa Koh Ina Suka wuce sai kaji Wa'inda Basu sansuba Suna cace Kai tagwaye masu Kama wa'inda suka sansu Kuma sai suce ga yaran Al'hassan marigayi yara sun girma.




bayan d'auren auren karfe 3 akayi walima a babban hall had'a Aisha da umaima akayi aka musu walimar har lokacin Aisha taki yarda Koh lalle a Mata sai hauka take,bayan an tashi a waliman saiga mototin Yan bauchi da niyar a ranan zasu wuce da Amarya,dagewa kawayen mamu sukayi sai dai a bari gobe da safe a wuce,su Kuma dangin sadeeq sukace yau zasu wuce basu shirya kwana ba anan dai akayita kace nake karshe Abbu da kansa ya fito ya dau umaima ya danka musu bayan Nasihat da ya Mata ya Kira mamu sukayi sallama da Addayiya da sauran wa'inda Suka face.



Yan uwa Suka Mata rakiya sosai zata baka tausayi in kaga irin kukan da take Kamar ana yankata,rabuwa da iyaye akwai jimami,aka wuce da ita Lahab Kam tun a wajen daurin aure ya d'au mota abinsa bai tsaya a gida ba yawo Suka ringayi da Adewale Nabeel tunda ya samu Suka dawo massalci yace wallahi bai sake Hawa don Sam,shikuma Lahab yaki yarda ya koma gida gashi anata Kiran sa a waya amma yaki d'auka.



da misalin karfe takwas na dare Lahab ne da Adewale a mota sai bada wuta Lahab yake, unguwan su ya jafar ya nufa tun daga nesa ya hangi mototi a cike da kofar gidan tim, parking shima yayi a gefe wasu Yan Mata suka bude Suka shiga don su sun d'auka motar d'aukan aure ne Saida mototi Suka cika kafun aka Fara tafiya,Amarya Aisha aka Kai gidan mijinta angonta Anwar har lokacin kafarta fari fat ba lalle daker aka samu aka fitar da ita don kuka take bil hakki da gaskiya,Lahab haka ya ringa daukar mutane Yana juyewa Yana dawowa har kusan karfe 9 na dare.




bai koma gida da ba Koh maida motar ba saima gidan ya jafar ya koma yaje ya fakata sanann ya hau Keke napep,gidan su Nabeel ya nufa agun ya kwana,washe gari da safe bayan sun dawo masallanci ya koma bacci don a gidan kaf babu Wanda yasan ya kwana Saida asuba da Inna ta fita sallah ta gansa a duke yana Alwala.



***************
ringing in wayarsa shiya farkar dashi bude idanun sa yayi a hankali yasa hannu ya lalubo wayar dake gefen dollof,daukar wayar yayi bai wani kalli screen in ba ya danna tare da karawa a kunne,da Sauri ya mike zaune Yana Ware Ido tare dasa kafa ya shurar da kafar nabeel daya daura Masa a kafada Jin muryar Maminsa ta cikin wayar cikin bacin Rai take tambayar sa Inda ya kwana"Mami Ina gidan su Nabeel nefa"ka taso yanzun yanzun Nan kazo ka sameni a gidana wallahi ka Kara minutes 20 baka zo ba sai nayi mummunan Saba maka nonsense kawai"tana gama maganar ta yanke wayarta.



Sake Baki Lahab yayi Yana bin wayar da kallo cikin mamaki sai Kuma ya mike zaune da Sauri wandon sa dake Kan kayan Nabeel ya jawo ya sanya Akan gajeren wandon dake jikin sa wankan da yake son yayi ma fasawa yayi ya d'au rigansa da Sauri ya bude kofar dakin ya fita,cikin kankanin lokaci ya Isa unguwar su Mami gate na gidan ya buga da karfi Mai gadi ya bude Masa,cikin gidan ya shiga da sassarfa don shi Sam yasan bawai Kwanan sa a wani waje bane ya d'aga Masa hankali illah yanda yaji Mami tamar magana ne yasan babu lafiya.



tura kofar falon yayi ya shigo sai Kuma yayi turus ya tsaya ganin Wance ke tsaye a tsakar falon,a hankali ya karaso ciki mamin sane zaune akan kujera sai Alhaji sulaiman shima a zaune yake ga Rahab a zaune akan carfet,farida(budurwar Anwar na da)ce tsaye kallo daya zaka Mata kaga ainahin Kamar ta na rashin mutunci gabaki d'aya ta zafge sanye take da lafcecen hijab har kasa sai nikaf data daga shi sama fuskar ta a bayyane,nuna farida yayi da yatsa Yana yamutsa fuska yace"wannan Kuma wacece Mami me take a gidan Nan ba auren ance an fasa da ita ba metake mana anan"



Juyowa farida tayi fuska jawur idanunta a kumbure sumdum ta Soma magana Kamar haka"wallahi tallahi Lahab tunda ka rabani da farin ciki ka rabani da walwala ka Haddasa min bakin ciki na rantse da Wanda Raina yake hannun sa Koh zanyi yawo tsirara Lahab saina Haddasa maka kaima bakin ciki ka rubuta ka ajiye nazone na baiwa uwarka sallahu tunda har kayi sanadin da bakin ciki ya kashe mahaifiyata ta bar duniya jiya Kuma akan abinda kayi bazan barka ba.


Mikewa Mami tayi tace"ke karamar Yar iska, ya kashe Miki uwa Koh bakin cikin ki ya kasheta shasha Sha karamar Yar bariki zakizo kice bazaki bar dana ba a gabansa, toh wallahi bazan bar maganan Nan ba sai mun danganta da kotu sai an rubuta Kamar yanda Kika ce duk abinda ya Sami d'ana kece sula ba Baki da mutunci ba Zan gwada Miki yanda ake rashin mutunci Mami na karasa maganar da Sauri ta shiga dakin ta,ganin hakan yasa farida barin gidan da Sauri tana rantse rantse bazata barsa ba.


Lahab Kam da Rahab duk shuru sukayi suna mamakin yanda farida tasan Lahab ne ya tona Mata asiri,fitowa Mami tayi a dakin tana waya da wani barrister akan zata Kai kara station yanzun za'a turo su kotu,kofar falon ta nufa hannun ta d'auke da hijab har lokacin hannun ta Kare da waya a kunne,da Sauri Alhaji ya mike Yana dakatar da ita akan babu Inda zataje ta koma ta zaune bude Baki Mami tayi tace"taya zanyi na zauna wannan shegiyar yarinya Harta Isa ta shigo gidana a gabana tana ma yarona warning harda Shan Alwashin bazata barsa ba kasan me zata Masa gaskiya ban yarda ba wallahi dole nasan abunyi.



Nace ki dawo ki zauna Amina Kika San Koh zafin mutuwar mahaifiyar tane yasa ta fadin haka dame zataji yanzun da mutuwar Koh da abinda Zaki Mata yanzun"d'aga Masa hannu Mami tayi cikin masifa tace"wani irin Bata hayyacin ta Bata hayyacinta ne zata gayamishi haka watoh nabar maganar ta wuce,daga baya nazo Naga d'ana cikin wani Hali bada Ni ba"



Kinji na rantse Amina babu Inda Zaki na gaji nagaji wannan wani irin abune haka fisabililahi,ban Isa dake ba kenan Koh ban Isa nace kibar Abu ki Bari ba,sai Kuma ya mike tsaye cikin bacin Rai yasa Kai yabar gidan,komawa tayi Kan kujera ta zauna ta dafe kanta,da Sauri Lahab da dan uwan sa Suka nufi mahaifiyar tasu ganin Kamar kuka ta Fara rungumar ta Lahab yayi a rikice,da Sauri ta turesa tare da wanke sa da Mari ta Soma magana cikin kaushin murya"matsa min daga jikin Lahab ya zanyi da Kai ya zanyi da Kai duk abinda na fada maka bashi kake aikatawa ba kwata-kwata Bakaji Koh don mahaifin ku baya rayene,ni Kuma bana tare dakune shiyasa kuke abinda kuka ga dama so kake hawan jini ya Kamani nima na mutu na barku.............




da Sauri Rahab ya rufe Mata Baki hawaye na bin kumatun sa yace"don Allah Mami kada kice haka, ki sanya Mana albarka don shi mukafi bukata a Yanzun insha Allah Koh babu mahaifin mu a duniya zamu zamo abin kwatance da Alfahari bazamu taba yin abin Allah wadai ba Abbu ya jafar ya muzammil Suna iyya bakin kokarin su wajen ganin sun tsaya a Kan tarbiyar mu Mami in bazaki yaba musu ba,Bai Kamata kiga gazawar su ba akan muba.



Rungumar dan nata tayi Lahab dake zaune a kasa tunda ta turesa daya sunkuyar da kansa har yanzun bai daga ba,Saida yaji abinda mamin nasu ke cewa"Lahab tun farko Nika Fara kawowa zancen farida nace maka ka bar zancen ashe Lahab baka bari ba Saida ka bibiye yarinyar Nan,ka tona Mata asiri yanzun Kuma tazo tasha alwashin bazata barka ba meyasa kake son damuwa da wa'inda basu damu da kaiba kake son gwaninta wa wa'inda gwanintar taka ba ganin sa zasu Yiba meyasa-meyasa nace meyasa Lahab"ta tambaye sa da karfi.



dagowa yayi idanun sa jajer yace"Saboda d'an d'an uwana ne bazan so mugun iri a cikin zuriyar mu ba Kuma na tabbata Koh nine Anwar shine Ni sai Inda karfin sa ya Kare wajen Hana wannan aure, murmushin takaici Mami tayi tace"lallai yaro baisan wuta ba saiya taka da ace kasan wacece Halima da bazaka d'aga Ido ka kalli yaranta so biyu ba Halima ta musguna min a rayuwa Halima tamin sharri kala kala bata da makiyiya kamar Ni,amma nasan baka San tarihin gidan ku ba illa Suna da ka sani da yan uwan ku,a yau Zan baka labarin tushen aure na da mahaifin ku da Kuma dalilin auren nasa yana babban mutum Ina yarinya.





****************
WAIWAYE ADON TAFIYA...............


Alhaji Al'hassan dogo Mai Naira shine cikekken sunansa ainahin su Fulani gombe ne haifafun cikin gombe Alhaji Al'hassan tagwaye ne dattabai masu sananin Kama da junan su Wanda a lokacin zaiyi wuya kaga tagwaye tsofafe masu Kama irin shida d'an uwan sa Al'hassan tare Suka taso kome iri daya suke Hatta karatu course d'aya Suka karantaAlhaji Al'hassan nada Mata d'aya kwallin gwal,Hajiya Aisha Wanda yaranta suke kiranta da Addayiya auren saurayin da budurwan sukayi da ita har Allah ya azurtasu da Y'ay'a guda biyar Umar(abbu) sai da Umar yayi wayo ya Soma zuwa makaranta kafun aka haife jafar saboda haihuwar Aisha tana da tazara sosai Saida jafar ya girma kafun ta haifi sumayya (goggo) sai autan ta Muzammil (uncle).




Alhaji Al'hassan kudi sun zauna sosai haka ma Al'hussain shima yayi aure amma har tsawon shekaru matarsa bata taba haihuwa ba,duk da Al'hassan yasha basa shawara akan ya Kara aure amma kememen yaki yace haihuwa na Allah ne Kuma Koh baida rabon Y'ay'a a duniya y'ay'an Al'hassan Suma sun isheshi da haka yake kashe Masa Baki.



Umar yayi aure bayan ya kammala karatun sa har mahaifin nasu ya gina Sabon kamfani Kuma ya basa manager a company in yana gudanar da ayyukan ciki,Umar nada yara uku da matar sa Halima(mamu)d'ansu na farko Anwar sai Mai binsa Shareef da kanwar sa umaima,bayan haihuwar umaima ne ya Kara aure ya aure ummu ta Haifi d'anta na farko uzaifa a lokacin.




Jafar yayi aure shima ya aure Khadija (nanne) Yana aikin gonnati,Yana da yara hudu Hashim Fatima sai Aisha(Amaryar Anwar)sai auta Majid a lokacin ma Yana jinjirin sa,sumayya(goggo)tayi aure ta auri sarkin katsina tana zaman aure a shan, muzammil lokacin an Fara Zama saurayi har an shiga jami'a ana karatu a cikin gombe.


Al'hassan mutum ne Mai hakuri dattako dajan nasa a jiki sosai, An basa minister of labour and employment,kudi ya zauna sosai hakan yasa sa gina babban gida yadau 'Ya'yan sa da d'an uwan sa(Hussain)ya maida su cikin gidan,gidane da ake zaman lafiya Kuma babban gida sai abinda baza'a rasa ba mamu(halima)macece Mai masifar tsiya da kasa hakuri yayin da ummu ta kasance Yar ba ruwa na hakan yasa zaman su yayi sanyi don Koh mamu ta hau ummu Bata kulata, Addayiya akwai gajeren hakuri sai dai macece Mai tausayi matuka tana kaunar mijinta da Masa biyayya sosai sannan babu ruwan ta da sawa surkunaye Ido daman part nasu daban tsakanin tama dasu akwai rata shiyasa ba'a Jin kansu,gogo badawiyya(matar Alhussan)daman ita macece Mai sanyin hali ga yawan shuru shuru shiyasa gidan baida hayani Kamar gidan yawa.




A wata Litinin Alhaji Al'hassan da tawagan sa Suka je wani kauye na Fulani usul dake karamar hukumar bajoga dake cikin gombe,wani rikici ne daya hafko tsakanin Fulani da manoma,sosai akama Fulani barna Kuma ya mugun tausaya musu shiyasa ya taso takanas yaje rugan,minister ya mike ya shiga rarrabawa jama'a kudi sosai Yan kauyen Suka cika da murna ga kayan masarufi da aka sauke musu mota babba ana rarrabawa buhuhunan shinkafa da masara,tun daga nesa ya hangota d'auke take da Robobin nonon ta akai dawowar ta kenan daga cikin gari ta Kai tallan no-no tana dawowa su uku ne suke tafe tana tsakiyar su,ganin yanda ake rabon abinci da kudi yasa sauran abokan tafiyar tata Suka aje Robobin su da gudu sukayi wajen motar da Kuma dattijon dake raba kudi,tunda ta d'aga Ido ta kalli wajen bata Kara kallo ba tafiyar ta kawai ta cigaba dayi.




Mikawa PA nsa kudin hannun sa yayi ya cigaba da rabawa,ya nufi barin wajen da Sauri security Suka mimmmike zasu bisa,ganin hakan ya Sasa shiga mota kawai ya zauna amma bai rufe murfin ba Yana kwanton yaran da suke tare da ita,yafito security yayi ya sanar dashi akan ya Kira masa yaran da suka d'au buhun shinkafa ta gwannati akan sun Nan su biyu,Kiran su security sukayi duk da kowa yasan yan kauye da tsoro hakan bai hanasu zuwa ba,Jin Wanda ya raba musu kudine ya kirasu aje shinkafan sukayi da Sauri Suka nufi motar.




Kabo na Isa gida ta aje roban nonon ba tare da ta saurare masifar da innon ta ke Mata ba akan ta San ana raba Abu bazataje ta karbo ba ai in bata samu ba,yayan ta zai samu in Kuma Suka samu dukan su karuwan sune,daki kawai kabo ta shiga ta fito da soson ta sai sabulun sodan ta dan kankani taja ruwa a rijiya cikin k'walla ta nufi kewayen nasu,Aminatu shine cikekken sunan ta yarinya ce da bazata wuce shekara 16 ba kyakkayawar bafulatana ce Fara Sol da ita sai kauyanci daya Kara boye sirrin kyawun nata sosai.




Amina(kabo)y'ace ga malam jibril marigayi Mai Almajirai da matar sa Rabi(inno)tun Amina na karama Allah ya ma mahaifinta rasuwa su biyu iyayen ta Suka Haifa ita da dan uwan ta muneeru,Aisha irin yaran Nan ne masu tsananin son karatun boko hakan ya sa ta sanyawa ranta son karatu sosai,duk da bata makarantan amma haka take sanya uniform data sayawa kanta tana zuwa tun ana koranta saboda iyayen ta basuzo sun sata ba har malaman Suka hakuri abinka da makarantan kauye taci gaba da zuwa(kuyi hakuri Yan kauye karkuce Ina ci muku fuska labari ne)




Sulaiman shine kadai saurayin kabo(Amina) sulaiman na tsananin son Amina fiye da tunanin Mai tunani da farko Amina Bata sauraron sa don ita kwata kwata soyayya baya gaban ta kowa yazo zata saka bori tace Bata sonsa sa'o'inta duk an aurar dasu sosai ake zagin inno a rugan su akan taki aurar da ita

Please Login or Register in order to submit comment