Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alkawarin jiran ka har karshen rayuwa ta mundin tsawon Rai Zan jiraka wannan *ALKAWARIN MASOYA* ne.





"Wai me hakan yake nufi kina nufin tafiya zakiyi ki barni"?Lahab ya Zama dole,kana ta karbi evalope in ta d'au ATM nasa ta Mika Masa ya karba,kudin dake cikin account nawa ya Isa in Kula dasu"no ki amsa in kika ki karba bazan ji dadi ba,maidawa tayi cikin akwatin kana ta dau macen ta Goya da majanyi hannu tasa zata karbi namijin,da Sauri Lahab ya mike tsaye Yana kallon ta kana yace"Wai da gaske tafiya zakiyi"Dole na tafi lahab"amma dan Allah kada kiyi nisa dani zamuyi waya ki Kama gida cikin tsohon unguwa da Muka Bari zanzo na sameki agun ki kular Mana da yaran mu sannan dan Allah inaso yarana su tashi cikin addinin musulunci Ina son su kasance musulmai ki Basu tarbiya daidai gwargwado,na Miki Alkawarin insha Allah kome zai daidaita wata rana ga wannan"ya Mika Mata wani golden box Mai sheki hannu tasa ta karba kana ta dau akwatinta a hankali sai Kuma ta tsaya tare da Mika Masa daya hannun ya bata yaron ta amma Lahab bai Mika mata nazeefi ba Kuma har lokacin yaron baibar kuka ba da ajiyar zuciya.



Lahab na maka ALKAWARIN yaran ka zasu tashi cikin musulunci Zan Basu tarbiya daidai gwargwado Zan sasu a makaranta da ake koyar da ilimin addinin ka,Koda Allah yasa bamu Hade yanzun ba, haka zalika Zan jira ka tsawon Rai amma bana tunanin zamu cigaba da rayuwa Nan kusa,nima inaso Koh bayan babuni dan Allah ka ringajin maganar iyayen ka Kama mahaifiyarka biyayya duk abinda tace maka kayi mata,kaga nida bani da iyaye wazai min Holo innayi ba daidai ba koh kuskure?babu bana dashi"



amma Labiba taya zakice bazamu ray..............bauuu kakeji an turo kofar da karfi mami ce ta shigo"toh karuwa an nuke da yaro a daki ana kitsa Masa magana ke Koh kunya bakiji ki rasa zaki bi sai wannan yaro"?Koda yake daman Ina Arne Ina kunya"maza shege ki fita tunda ba gidan ubanki bane,aje a nemi wani daderon bada d'ana ba,anga yaro yayi kudi ana Shirin d'auke Masa hankali"Mika Mata shegen ta ta Kara gaba dashi kin mikawa yayi da Sauri Mami ta karaso cikin dakin ta fizge yaron ta wurgawa Nnenna da karfi,saura kad'an yaron ya subuce baiwar Allah ta canke abinta salati Lahab y sake ya rumtsa idanunsa donshi a tunanin sa yaron ya Fadi akan tiles,a gaba Mami ta tasa Nnenna Kamar wata Shaniya tana zaginta tana turata da karfi ita da akwatin nata,Lahab na binsu a baya shima hawayen yake Yana rokonta.




Har wajen compound Mami ta fita da ita da Sauri Lahab ya sake kneel down batare da gajiyawa ba yahau baiwa uwar tasa hakuri amma Mami ta rantse bazata hakura ba"wallahi Lahab kaji yau sai rantsuwa nake ba? toh bazanyi a banza ba Koh bayan Raina hajiya Khadija ki shaida ban yarda ya Kara rayuwa da yarinyar Nan ba,haka zalika Inka sake Koh magana ya hadaka da ita Koh neman Inda take Koh a bayan idanunsa ne,Allah ya Isa Lahab Allah ya Isa,Kuma saina d'aga maka no-no in yaso kabi duniya,wani irin daskarewa Lahab yayi Yana tsaye harta fita a gate in,da gudu Ade yabi bayanta da niyar ya bita cakumosa Mami tayi tana zaginsa tana cewa babu Inda zaije wato zai bita su hadawa danta munafurci Koh? ai daman Arne bai iya samun waje ba"Lahab dai na tsaye Kamar gunki da Sauri Ade ya samu ya b'anb'are kwalarsa ana Mami da gudu ya nufi kofar gidan amma abin mamaki babu Nnenna Babu Mai Kama da ita,haka ya wuce hospital dake unguwan nasu amma Bata Nan,duk wani bus stop daya sani yaje amma Babu Nnenna.




*****************
Yayyafin aka Soma da karfi Mai hade da iska a hankali Lahab ya zame ya zauna akasan compound in Yana wani irin kuka maicin rai,sosai yaji tsoro ya darsu Masa a ransa kada Nnenna tashiga wani matsalar Kuma gashi baisan ya lafiyar dansa ba Ashe haka Y'ay'a suke da dadi? Mami tuni Suka shiga ciki Suka barsa a wajen tunda ya kafa idanunsa a gate tun fitarta har yanzun bai kauda ba,ruwa aka Soma dakarfi haka ruwan nan ke sauka akan Lahab amma Koh gezau ko alamun tashi baiyi ba,yanzun Kam kukan ma ya tsaya hawaye ya bushe,fitowa kawar Mami tayi tana cewa Lahab ya taso a wajen Kar wani ciwon ya kamasa"ki barsa inyaso ya mutu a wajen da irin wannan yaro ai gwara baka haihu ba"abinda Mami tace kenan taja kawarta Suka sake komawa ciki so take ta nunawa Lahab true colourn ta yanda gaba bazai Kara yunkurin tafka wannan kuskure ba.




Ruwan sama na kusan 2 hour's kaf suka Kare akan Lahab daman ba isheshen lafiya bane dashi gashi yaki rufe idanunsa har lokacin idanun nakan gate na gidan ruwa ya shishiga cikinsu sunyi jazur dasu,turo gate in akayi a hankali Adewale ne ya Shiga jikinsa a jike shima a hankali ya Soma nufo wajen da Lahab ke zaune a hankali lahab ya dago idanunsa ya kalle Adewale irin kallon Nan na tambaya?girgiza Masa Kai Ade yayi watoh baiganta ba, lumshe idanunsa Lahab yayi a hankali,kawai sai Ade yaga Lahab na sulalewa a hankali da Sauri ya tarosa da hannayen sa gudun kada kansa ya sauka da kasa,amma Ina Lahab Kam gabaki d'aya ya zube a jikinsa baya Koh motse.





A hankali ya Soma bude idanunsa sai Kuma ya maida ya rufe kirim ganin wani irin duhu daya mamaye dakin,Jin ana Kiran sunan sa a hankali yasa sa Kara bude idanun nashi dishi dishi ya Soma kallon sama sai Kuma ya Wulla idanunsa ga wajen da yaji ana Kiran nasa,Abbu ne da uncle muzammil sai Mami,maida idanun yayi ya rufe Koh tantama bayayi a gadon asibiti yake,toh amma yaushe su Abbu suka zo?Jin an rike hannunsa yasa sa Kara bude idanun,ya saukesa akan Addayiya dake zaune abakin gadon da yake,bude baki yayi a hankali yana Mata magana amma saboda dishewar da muryarsa yayi yasa Addayiya bataji abinda yake cewa ba matso da kunnenta tayi Kan bakinsa"Addayiya kwana na nawa anan"?



A hanakli Addayiya tace"yau kwanan ka uku Lahab a gadon asibiti"?.....................







*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*



Lumshe idanun nasa yayi ya koma ya kwanta,matsowa kusa dashi muzammil yayi yasa hannu ya taba wuyansa sai Kuma ya fita a dakin bai Jima ba sai gasa ya dawo tare da Dr, ta basa Dr yayi Lahab yaki bude idanun sa tambayar sa yayi akwai Inda yake Masa ciwo?girgiza Kai yayi a hankali ruwan Dr ya cire masa kana yace ya wanke Baki ya samu yasa Abu Mara nauyi a cikin sa,sannu Yan dakin Suka Soma wa Lahab shidai gyada musu Kai yake kansa na kasa don wani irin kunyar yayun nasa yake daman Mami Kam Koh kallon Inda yake batayi ba.




Kamasa muzammil yayi a hankali ya mike tsaye sai Kuma yace uncle ka sakeni Zan iya zuwa toilet in da kaina sakin sa muzammil yayi Aiko saura kad'an Lahab ya zube a kasa ya tarosa Yana cewa ba bayaji ba shiyasa ya barsa yaga gudun ruwan sa mutum kwana uku a kwance har Yana da kuzarin cewa zai mike ya taka,Kai muzammil ka bisa a hankali Mana kafun yaji saukin tukunna"Addayiya tace tana mikewa tabi bayan su cikin toilet in ruwa ta hadawa Lahab yayi wanka ta basa Sabon toothpaste da brush ya wanke bakinsa Sabon uniform na hospital in da aka aje musu a goge Addayiya ta dauka ta basa ya sanya Wanda ya ciren Kuma aka saka a basket.





dawowa Lahab yayi ya zauna a bakin gadon gabaki d'aya ya zube,ya Kare kowa ya gansa yaga Wanda yakejin jiki,tea Addayiya ta had'a Masa tare da Mika Masa,gizgiza Kai yayi kana yace"Addayiya banajin yunwa bazan iya Sha ba"aiko Dole kasha Taya zaka zauna babu kome a cikin ka har kwana uku Allah yaso ma ana daura maka ruwa"duk yanda Addayiya tayi Lahab yaki Shan tea Nan gajiya Mami tayi ta daka Masa tsawa akan ya karbi shayin yasha hannu Lahab yasa ya karbi shayin bawai don tsawar data buga Masa ba sai don kudurin da ya daukarwa kansa akanta,tunda ya kafa kofin shayin Bai sauke ba Saida ya karar duka Yana aje kofin amai ya tasar Masa kafun ma ya Isa toilet tuni ya kwarara a tsakar dakin.





Sai da Lahab yayi kwana biyar a hospital kafun aka sallame su Kuma abinda ya bawa kowa mamaki shine,tunda ya farka baiyi zancen rashin ganin Ade ba Koh Kuma zancen Nnenna asalima Lahab gabaki d'aya ya sauya inya zauna ya lumshe idanun sa sai yakai awa uku Koh hudu Bai bude ba sai ka gama surutun ka akansa bai d'ago ya kalleka ba,indai ba Mami bace ta Masa magana Koh Abbu Koh muzammil wannan Kam Koh Bai Basu amsa ba yanayin abinda sukace Koh abinci Suka basa Koh baison ci ci yake inyaso amai ya biyo baya,bazai hanasa sake ci ba.




Gabaki d'aya jikin dangin sa yayi sanyi yau aka sallame sa,zaune yake Akan gadon hospital in ya chanja uniform nasu zuwa kayan sa kallon sa Addayiya tayi, guri daya ya kurawa Ido zuru magana take Masa Amma baimasan tanayi ba hannu tasa ta tabasa,da Sauri ya zabura sai Kuma ya kauda fuska,shigowa dakin Abbu yayi yace ya tashi su tafi an sallame sa,mikewa kawai yayi kansa a kasa har Suka fita,mota Suka hau sai gidan Lahab.





Suna Isa anan Lahab yaga sauran yayun nasa sunzo ya jafar da addan sa matar sarkin katsina duk Suna tare a falon ga Ade ma zaune yake Wanda rabonsa dashi tun Randa akai ruwa,nuna Masa waje Abbu yayi ba musu ya zauna Yana bin falon da kallo wasu abubuwan na dawo Masa kunyar kansa,Mami ce ta shigo falon da mijinta Suka neme waje Suka zauna har lokacin Lahab bai cewa kowa kome ba haka zalika Bai daga Ido yaga kowa ba,gyaran murya Abbu yayi kana ya Soma magana Kamar haka"Lahab ka gan mun Nan kaf namu badon kowa Muka taru anan ba sai don Kai Muna so ka Mana cikekken bayanin da zamu gansu,shin mun taba maka wani Abu daya sa kaji cewa bamu cancanci kayi shawa damu ba"?hawaye ne ya cika idanun sa sai Kuma ya girgiza Kai"magana zakayi ba body language ba"ya jafar yace"ah ah baku taba ba"toh meyasa kayi abinda kayi kasan kana tare da yarinyar Nan ka samu muka tashi tsaye ka fito daga hannun hukuma sannan kazo ka zauna da ita kana Zina Lahab Zina fa yanzun abinda zaka saka Mana dashi kenan saika tara yaran da bata hanyar aure aka samesu ba ka Mana daidai a matsayin mu na marikanka?





"Wallahi Yaya banyi haka don in zubar muku da mutunci ba Kuma ba Zina na aikata ba"da Sauri Mami tace toh Meka aikata nace Meka aikata Koh ba'a gidanka nazo na sameta ba ka samu Sabon uwa"? d'aga Mata hannu muzammil yayi rai a bace yace"Kinga Amina ki rufe Mana Baki karki sake saka bakinki a maganar Nan sai ansaki"Kai muzammil bazan rufeba ya za'ayi kace sai an sani a ciki Zan Shiga d'ana ne fa"?



Kallon ta sumayya tayi tace"Ke da Allah ya Isa ke duk abinda aka sakaki a ciki sai anga rikici tun farko ai Saida akace ki hakura da zuwa London ki jiramu mu shirya Amma dayake idanunki sun rufe kikazo kikayi abinda ranki yakeso Kika dagula kome sannan zakizo kina nuna ma mutane Isa"ke dakata sumayya karki kuskura ki sake saka bakinki a magana ta badake nake ba Kuma Babu abinda na dagula wato so kuke na zauna a likawa yarona sharrin shegu.




Wani irin sharri wani irin sharri Koh makaho ne ya shafa hoton yaran Nan yaga jinin mu,Kuma Koh yaran Nan shegune mu bazamu kasa rikesu ba Kuma bazamu ji kunyar nunawa duniya su ba,tunda keda kike uwarsa bazaki iya ba"



"Dan Allah ya Isa haka Dan Allah nace, kaina zai fashe"shine abinda Lahab yace Yana kuka a hankali mikewa yayi zai bar falon da Sauri Abbu yace Masa ya koman ya zauna"Lahab baka bamu amsa ba menene dalilinka na aikata wannan d'anyen aiki Kuma riban me kacin ma"?




Share hawayen sa yayi a hankali ya Soma magana"wata Rana da safe a makaranta.......................................tsab ya zayyana ma Yan uwan sa dalilin haduwarsu har abubuwan da Suka faffaru har kawo abinda Mami ta Masa kwana biyar daya wuce Yana karasa labarin Yana hawaye, girgiza Kai Abbu yayi Yana cewa"haba Lahab haba Lahab meyasa baka tinkare da zancen Nan ba meyasa tun farko baka sanar Dani ba kayi gaban kanka Lahab kayi kuskure yanzun dame zamu gansar da Jama'a da dangi akan auren ka bamu da wani shaida"?



Zaro wayar sa Ade yayi ya mikawa Abbu vedio dauren aure ne gabaki d'aya falon Saida kowa ya kalla Mami kam tabe Baki tayi, gaskiya Amina abinda kikayi bai dace ba kwata kwata hukuncin da Kika yanke yayi tsaurin yanzun kikasan halinda yaran Nan zasu shiga Koh irin hannun da zasu shigo Koh irin riko da zata musu"?don haka ki janye furucinta akan Lahab kana musa a nema Mana yarinyar Nan inyaso mu amshi yaran a hannunta in ma rabasu za'ayi gwara a karbi yaran mu murike namu itama ta Kama gaban ta,tunda zargin kisane akan ta"




Mikewa Mami tayi wallahi bazai sa'u ba Akan me za'a amshi yaran maganata Kuma bazan canja ba duk lokacin da Lahab ya nemi yarinyar Nan Allah ya Isa"waike Amina hankalinki daya Kuma Anya kanki daya kuwa menene haka Wai meyasa bazaki chanja bane Infa Rai ya baci hankali Bai gushe ba"Alhaji sulaiman ya fad'a ganin rashin kunyar da matar tasa take zubawa"kaga Babu ruwan ka ai Dole kace kaina ba daya ba,tunda ba danka mahraz bane Dole kace na natsu kaga ma tsaya kada ka sake sa bakinka a maganar Nan"?




Haka kikace Amina?kwarai ma kuwa ta basa amsa Kade rigansa yayi yabar falon gabaki d'aya yabar gida mikewa muzammil yayi yace"zakiyi iko da d'anki Amma mu zamu nemeta mu karbi jinin mu"a karata lafiya"shine abinda Mami tace tana bin bayan mijin nata don Daman tunda yazo tabar gidan Lahab,sauran Yan falon duk mikewa sukayi Suka shishiga dakunan da Suka sauka a cikin gidan, shima Lahab mikewa yayi a hankali Yana tafiya yana kallon dishi-diahi,dakin ta ya shiga a hankali ya maida kofar ya rufe tare dabin dakin da kallo Yana tuna abubuwan da dama da suke gudanarwa a ciki bude wardrobe nata yayi kayantane a jere tsaf ya rufe tare da Zama a bakin gadon idanunsa suka sauka akan hoton su da Suka d'auka su hudu hannu yasa ya dau hoton Yana kallo sai Kuma yaji hawaye ya tarun Masa a idanu hannu yasa ya shafa hoton"Dan Allah Labiba karkiyi nisa dani bazan iya jurewa ba"sai Kuma ya mike da Sauri wayansa ya d'auka da hanzari messager ya Shiga yaga babu alert na alamun bata cire Koh sisi daga cikin account nasa ba wayar tata ya Kira Amma yaji a kashe dukawa yayi a kasa ya Kama kansa da karfi.





turo kofar akayi Adewale ne ya shigo Amma Lahab Bai d'ago ya kallesa ba matsowa yayi kusa dashi kana yace"Lahab kayi hakuri da duk abinda ya faru sannan ka cire wannan damuwa da take ranka duk da bansan dadin d'a ba Amma Bai Kamata kasa kanka a damuwa har haka ba? zakaje ka daurawa kanka cuta Nnenna Kuma insha Allah Allah zai kareta indai kayi Imani da ubangijinka"tabbas haka ne Ade duk da Kai ba musulmi bane Amma kafi wani musulmin sanin ya Kamata,Allah ya muku albarka abinda Addayiya tace kenan ta aje kwanukan hannunta abinci ta Iba ta mikawa Ade Amma yaki amsa tare da cewa shi zai wuce Daman yazo Yama Lahab sallama ne"d'ago Ido Lahab yayi ya kallesa da tsigar tambayar Ina zashi"Dan yake Ade yayi yace"Lahab yanzun bana cikin gidan Nan na Kama gida a waje inaga hakan zaifi"gyada Kai Lahab yayi don yasan Daman irin zagin da Mami Tama Ade ba lallai bane ya Kara Zama a gidan fita yayi bayan sunyi bankwana da Addayiya.





***************
Haka Lahab ya cigaba da rayuwa cikin kadaici da damuwa inya tasa hoton yaransa a gaba saidai kawai yaji hawaye na zuba ba tare da sanin Saba duk Inda su Abbu suka shiga aka Kai bincike ganin Nnenna ya gagara anje airport an bincika amma akace Babu jirgin da Nnenna ta hau,rayuwa tama Lahab daci karatu da ball in duk baya tabuka musu kome Yama ajesu a gefe Daman Yana exam na final year nasa abin ya faru gashi yai missing na wasu paper dolen sa yayi losing na one year,family sa sun hakura sun koma nageria Addayiya ce ta cigaba da Zama dashi tana kula dashi don Babu Inda yake zuwa yanzun gabaki d'aya Lahab ya sauya daga Lahab nashi zuwa wani sabo.




Rahab yaji labarin abinda ya faru Kuma hankalin Sa ya tashi yaso zuwa London Amma jarabawan ya tsaidashi da Kuma Mami"Alhamdulilah Rahab da Ade sun kammala digree nasu cikin yardan Allah tare da sakamako Mai kyau, yanzun Rahab cikekken accountant ne da kwalin digree nasa, Adewale Kuma engineer,Rahab na karban result nashi gudu yayi ya dawo London Suka zauna tare da Addayiya Suna kula da lafiyar Lahab gudun kada ya samu wani ciwon Kuma daban, masters Rahab ya nema a school nasu Lahab kana yasa Lahab ya koma makaranta da lallama yaje ya karasa final nasa dayayi losing,Ade ma ya join suka cigaba da bawa abokin nasu kulawa duk da yanzun Ade baya zaune dasu gida daya,haka Mami Bata sake zuwa London ba Kuma Bata takura Lahab yazo NAGERIA ba kasancewar zargi na kansa Kuma Koh yau ya dawo magana zai sake tashi sabo,labarin Nnenna Babu shi har gobe ba'a San Inda ta shiga ba.




Lahab ya kammala digree nasa Amma zancen kwallo ya aje gefesa a gefe su Rahab ma Suna shirye shiryan had'a masters nasu shida Ade,yau tunda safe lahab ya tashi da zazzabi Mai zafi Yana kwance Adewale da Rahab sun tafi makaranta sai shi da Addayiya ne da har yanzun Taki komawa tana zaune dasu tare,tana kula dashi,turo kofar dakin nasa ta shigo karasawa tayi bakin gadon tasa hannu ta yaye blanket in a hankali kwance yake gabaki d'aya sai had'a zufa hake,Kai innalilahi wa'inna'ilahu raji'un Lahab zaka kashe kanka a banza Lahab duk nasiyar da nake maka bazaka fawwalawa Allah lamuran kaba kayi hakuri da kaddarar ba"sanin bazai amsa Mata ba yasata mikewa ta shiga toilet ruwa ta Iba a baf ta saka towel a ciki tazo ta Kwabe Masa riga dagashi sai 3quiter ta Soma matse towel in tana goge Masa jiki Koh zazzabin zai sauka don sun gaji da jagelen asibiti.







da yamma da Rahab ya dawo daukar Lahab yayi sukaje hospital aka Masa allura da magani kana suka dawo gida kwance yake a falo Rahab na matse Masa jiki Yana Masa hira wani ya amsa wani yaki amsawa a hakan de suke hiran Addayiya nasa musu baki,door bell aka danna kallon juna Lahab sukayi sai Kuma Rahab ya mike Yana cewa"taima order danayi ne ya karaso"kallon sa Lahab yayi yace wani order Kuma bayan Banga kayi ba"Kai d'azun wayanka na d'auka nayi Mana order abincin dare Addayiya yau na hutar dake"ah ah Rahab bana bukata bazan iya cin abincin turawan Nan ba gudawa yake sani garamin na dafa abuna da kaina.





Murmushi Lahab yayi Wanda Rabon yayi irinsa tun ranan da Nnenna tabar sa,dukan su kallon sa sukayi sai Kuma Rahab ya hau dariya ya nufi kofa zaikarbo abin Yana cewa"in bazakici ba ai nida kanina zamuci,mikewa Lahab yayi da gudu yadau pillow yabi Rahab Wai zai buga Masa duk da ba karfin jikinsa yakeji ba Amma haka kawai yau yakejin kaunar Dan uwan nasa sama da da, yaji baida buri daya wuce ya gansa cikin happy shiyasa yana mikewa ya Soma bin Rahab dariya Rahab ya Fara Suka ringa zagaya falon Addayiya Kam sai magana take sun bar mutum tsaye a kofa,sosai Lahab ke gudu Yana bin Rahab shima gudun yake Yana kakkaucewa da Sauri ya bude dakin su ya Shiga Yana kokarin rufe kofa,Lahab ya turo kofar da karfi Aiko Nan yasa Kara yayi Kan gadon binsa Lahab yayi ya dannesa kana yad'au filon Yana ta buga Masa Yana cewa"nine kaninka ni"?da Allah kayi hakuri toh ba Kai bane haba"d'an sayawa Lahab yayi yace toh kacemin Yaya"da Sauri Rahab yace Yaya dan Allah gani ka matsemin hannu fa zafi yake min,mikewa Lahab yayi shima ya mike zaune Yana duba hannun nasa,hannu Lahab yasa ya rike hannun dan uwan nasa Yana dubawa.




Kallon sa Rahab yayi yace"ya Allah ka dauwamar da zuciyar d'an uwana cikin gaskiya da aminci"d'ago Kai Lahab yayi ya kallesa tare da amsawa da Amin"Lahab ka rame sosai kayi hakuri da kaddarar aduk yanda tazo maka Mai kyau Koh Mara kyau kayi hakuri kome ya faru jarabawa ne daga ubangiji zanji dadi Inka kasance cikin happy Kamar rayuwarka tada"girgiza Kai Lahab yayi kana ya zame ya kwanta a cinyan Rahab Yana cewa"Anya kuwa wannan geben zai cika abinda ya wuce ya wuce bazai taba dawowa ba, Rahab yanzun Kaine kad'ai farin ciki na Kuma nawa dake kusa dani"shafa kansa Rahab yayi yace toh inka waye gari babu Ni ya zakayi bazaka iya hakuri ba kenan"?





d'ago Kai Lahab yayi da sauri yace"banason haka karka karamin wasa irin wannan banason ai duk Randa Babu Rahab Babu Lahab Koh ka manta Abu dayane mu guda biyu"?haka ne Lahab Allah ya baka hakuri kaji"nuna min hoton yaran namu na Kara gani naji ance Suna Kama damu Niko sai Inga Kamar sun fimu kyau"da Sauri Lahab ya mike system nasa ya d'auka ya mikawa Rahab Aiko Nan Rahab ya kwanta Lahab ma ya kwanta tare da daura Rabin jikinsa ana Dan uwan nasa,kallon hotonan Rahab yake Yana yaba kyawon yaran da tsamtsam kamannin su dasu sai dai yaran farare ne"smma sunan da ka sawa yaran baimin ba Ina laifin kamin tagwara Lahab"?




Kasan fa sunan mu sunan iyayen mune kana nima na sake sawa yarana haba abin yayi yawa shiyasa nasa Musu nazeefi da nazeeefa Ni sunan yamun Kuma Ina Jin dadin sa"kyebe Baki kawai Rahab yayi Yana cewa lallai masu yara manya Allah nifa dariya kake bani Inna ganka na tuna Wai yara biyu gareka,make sa Lahab yayi shima yasa hannu ya hambare Lahab in Saida ya Fado daga Kan gado zuwa kasa,turo kofar Addayiya tayi hannunta d'auke da laidan ordern ajewa tayi tana cewa Kai ga abin naku nidai bazanci ba"mikewa Rahab yayi yazo ya amshi laidan ya koma Kan gado ya zauna bude laidan yayi ya dau roban takeAway in ya mikawa Lahab amsa Lahab yayi shima Rahab ya dau sabo ya bude sai Kuma ya kalli na Lahab ya kalli nasa.





"Yaya dai haka"?tsaki Rahab yaja yace nace takeAway uku biyu shinkafa daya gasheshen nama Kuma Ni Naman nafiso fa"kallon takeAway gabansa Lahab yayi sai Kuma ya dauka ya mikawa Rahab Yana cewa"anything for u brother gashi daman Ni nama bai wani dameni ba yanzun ban shinkafan naci,Mika Masa Rahab yayi sai Kuma yadau takeAway Naman ya aje a gabansa ya ibi guda bakwai ya sama Lahab a cikin shinkafan sa,iba a spoon Lahab yayi zaikai Baki haka kawai sai yaji abincin ya fita akan sa yaji baya kaunar cin abincin sauke spoon in yayi Yana kallon Rahab dake ta cin nama Yana kada Kai irin ya Masa dadin Nan,had'a Ido sukayi Rahab ya d'aga Masa gira daya"?




A hankali Lahab yace"Rahab na rasa meyasa nakejin wani iri a jikina Kamar Zan rasa abinda nafi so"?amsa Rahab ya basa,sai kayita astagafurullah na rasa meyasa Lahab ka kasa hakuri da abinda ya faru yanzun dai kaci abinci tukunna sai muyi magana dan Ni yunwa nakeji"shuru Lahab yayi Yana ta kallon dan uwan nasa"bazakaci bane Lahab girgiza Masa Kai yayi da sauri Rahab ya cire hannusa a naman Yana tambayar sa meyasa Koh Naman yakeso ba shinkafa ba sai Kuma ya tura Masa Naman duka a gabansa"toh gashi karba kaci"hawayen da Lahab baisan na menene bane ya cika masa Ido yace"nima bansan meya faruba haka kawai nake jina incomplete wallahi"





Murmushi Rahab yayi sai Kuma ya yamutsa fuska kana Kuma ya Fara

Please Login or Register in order to submit comment