Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana Masa magana,tashi Maza umaru muje mu duba sa muga ya jikin nasa Allah sarki dan maraya Koh garin yaya hakan ya faru ne?

Abbu daya mike tsaye yace Mata,nima wallahi bansani ba shiyasa nake son naje naji yanzun-yanzun naji garin yaya,kinsan nima uwan nasu ce ta kirani tace min itama dan uwansa ne ya kirasa.

Muje-muje Maza muga ya jikin nasa fita sukayi babban falo yaran ne zaune da iyayen su mata dayake ranan hutune Kuma sunyi baccin su harsun gaji suka fiffito falo Suka zauna,da mamaki suke kallon Abbu da Addayiya ganin su cikin Shirin fita kasa hakuri mamu tayi ta tambaye Abbu,lafiya kuwa Abbu na ganku haka cikin Shirin fita?

Koh amsa Mata Abbu baiyi ba don har yanzun haushin ta yakeji na abinda ya faru jiya,Uzaifa ne ya Kara magana ganin baban nasu da Addayiya na kokarin fita a falon, Addayiya sai ina?

Sai uwarka Kai asuwa da zan fita kace Ina zani?

Haba Addayiya sofa nake nima na biku don nasan fita da Abbu Alkhari ne yayi Mata dadin baki don ta samu ta fad'a musu,Abbu Kam Harya fita a falon Addayiya ta washe baki,Kai Uzaifa Maza zo mu tafi dan albarka bappan ka Lahab ne Yana asibiti ba lafiya zamuje,ai Jin haka yasa muneera mikewa da Sauri daman akwai gyale a jikinta takalmi kawai ta d'auka tabi bayan Uzaifa dayabi Addayiya a baya da Sauri.

Mikewa umaima tayi da dankwali a hannunta zata dau hijab nata akan kujera da niyar binsu daka mata tsawa mamu tayi,uwar Y'an iyayi sai Kuma Ina Zaki?

Jiki a sanyaye tace,mamu Zan bisu muje duba Uncle ne?

Uban kine shi ba uncle ba Yar iska Mara zuciya watoh abinda uwarsa tamin jiya harkin manta Zaki bisu kuje toh babu Inda zaku daga ke har Anwar da Shareef in,tsaki ummu taja ta Mike ta shiga dakin ta tad'au mayafinta tazo ta wucesu a falon tabi bayan mijinta da yaranta tabar na mamu a falon Wanda kallo daya zaka musu kasan suna son zuwa babu yanda Suka iyya ne,munafukar banza zai Kare a tsuliyan ku keda yaran naki ai indai Amina ne Muna Nan dake a gidan Nan Zangan ku a Rana kina binta a gindi a gindi babu uwarda take tsinana Maki,ita dai ummu Koh takanta bata biba ta fitoh compound lokacin Abbu da su muneera duk sun cika motar sa harzasu fita a gate sai gata ta fito tana d'ago musu hannu tsaya sukayi ta bude gaba ganin uzaifa yasata rufewa ta bude baya tare da Zama kusa da Addayiya don muneera ce ta gefen kofa Addayiya a tsakiya itama ta zauna a gefen Addayiya Abbu yaja motar Suka bargidan.




********************
Adewale yau tunda ya tashi da safe bai Fara karyawa da kome ba sai da bala'in papan sa ta Inda yake shiga ba tanan yake fita ba daga yace Masa ya shirya zasu tafi Church,shine Adewale yace bazashi ba baijin dadi,shikenan papa ya Soma ruwan bala'i daman baison zuwa church yaran hausa people na zugasa yabar addinin sa,Jin abinda yace yasa Adewale kasa hakuri ya tamka Masa,haba papa wannan wani irin magana ne haka Ni tunda nake da abokai na basu taba zagin addinina ba Koh suce wani Abu a ciki ba daidai ba Koh na daina.

Rufemin baki Wawa kawai stupid kawai Wanda baisan ciwon kansa ba yanzun ace duk yaran Christian basu isheka abota ba saika had'a da Yan iskan yaran?


Komawa Ade yayi bakin gado ya zauna papa na tsaye Yana jaddada Masa ya tashi ya shirya amma Koh gixau baiyi ba hakan shiya Kara kular da papa Harya sashi mikewa ya fizgo Bell in Ade dake yashe a kasan d'akin ya nufesa ai da gudu Ade ya mike ya rufi kofar bayangida binsa papan yayi tsabar rudewa kasa bude kofar yayi ganin papa ya kusa kamasa yasa sa nufar kofar dakin da gudu ya bude ya falfala a guje yayi falo,maman sa ce dake kwashe kwanuka a dinning ta nufosa tana tambayar sa lafiya? tsayawa yayi ya tsoma magana idanunsa nakan kofar dakin sa ganin har lokacin papa bai fito bama,mama nifa kaina na ciwo bazan iyya zuwa church ba this week gaskiya?


uhmmm haba Ade Kai duk weekend saika kirkiro abinda zai hanaka zuwa church kafasan dole ran papan ka ya baci Yana matsayin pastor ace d'ansa guda bai zuwa church abin zai Zama abin magana Koh ana cewa kafi karfinsa hakan baida kyau ka tashi kaje ka shirya shap-shap kazo mu tafi?

Zama yayi akan kujeran ganin papa ya fitoh Yana maida numfashin gudun da yayi daga dakin Ade zuwa falon,nifa kaina ciwo yake fa mama?


duk naji amma ka tashi haka zaka daure mu tafi abinda by 12:00 ma zamu tashi.

Kai mama har 12:00 Ina zaune ai sai ciwon ya Karu,tsawa papa ya daka Masa ganin sai lallabasa mama take shi Kuma sai botsarewa yake,Ade Zan mugun Saba maka a gidan Nan fa wallahi yau Koh zaka mutu sai kaje church.

Mikewa maman nasa tayi ta kamo hannun sa ta nufi dakin sa dashi Bata tsaya ba har toilet ta shigar dashi kafun ta basa umurni babu Wasa a fuskar ta,kaga Ade kayi wankan Nan na baka 15 minutes ka shirya ka samemu a falo wallahi in ba haka ba Zan Saba maka kanason ka jawa mahaifinka hawan jini Koh?


Kaya ya Soma cirewa ba tare da yayi magana ba hakan ya nunawa maman tasa zaiyi wankan kenan,fita tayi taja Masa kofa,bayan yayi wankan ya shirya Saida ya bata lokaci sosai don mama kafarta uku a dakin sa kafun ta samu ta fitoh dashi,anan ma Saida akayi daru don Ade 3quiter yasa papa Kuma yace bazashi church Yana d'ansa da gajeren wando ba daker dai aka samu ya canja,mota papan ya fitar Suka shiga sai church.





**********************
Lahab na sauke wayar a kunnen sa Nnenna ya mikawa"gashi kema ki Kira gidan ku"yace Yana Kara Mika Mata.

Mikewa tayi ta matsa kusa da jakanta tana harhada kayanta da takardun ta tana basa amsa"ban haddace number kowa a gidan mu ba"

dan zare Ido yayi kafun ya sake tambayar ta cikin dariya"hhhh kina nufin kaf gidan ku babu wanda Kika haddace number sa"?

Wani harara ta maka Masa tana rufe zip na jakanta tare da matsowa kusa dashi tana Mika Masa hannu"ban wayar na maida Mata innazo fita akwai Kaya a garden basu bushe ba,Mika Mata wayar yayi tayi Kamar zata karba sai Kuma yayi baya da wayar tare da Kama hannunta ya rike Yana bin fuskarta da kallo ya Soma magana a hankali"tafiya zakiyi ki bar patient"


Fizge hannunta tayi,"toh ba ka Kira Yan gidanku ba me Kuma Zan tsaya Yi maka"?

"Ki jira suzo saiku gaisa" Jin abinda yace yasa ta zaro ball eyes nata waje tana kallon sa tana magana"eh kace mu gaisa"?


Hhhh kina tsoron karsu zo suga Wance ta tsagamin Kashi koh?toh ki kwantar da hankalin ki bazan fad'a musu ba kinji"?yayi maganar fuska a hade ganin Harta juya zata fita a dakin bata saurare Saba ma"bazaki min sallama bane sannan ga wayar nurse in ma baki d'auka ba Zaki tafi Kuma ki barni"?


bata Koh saurare Saba tasa hannu zata bude kofar sai Kuma ta koma baya da Sauri ganin an turo kofar da karfi, dady ne ya shigo sai mutane guda biyu dake bayan sa,waro Ido yayi da Sauri ya shigo dakin tare dasa hannu ya riko nata Yana dudubawa Yana magana, Nnenna meya sameki Ina Kika shiga meya kawoki asibiti iye talk to me Mana daughter?


dan sunkuyar da Kai tayi tama kasa magana d'ago Kai Dad yayi ya bin cikin dakin da kallo har idanun sa Suka sauka akan Lahab dake zaune akan gadon Kara kallon Nnenna yayi, daughter wanene wannan?ya nuna Lahab.

Calm down sir ka bari mube kome a sannu tunda dai mun ganta,sai Kuma ya kalli Nnenna Harya bude Baki zaiyi magana sai Kuma ya kalli kofar dakin Jin an bude, Dr ne ya shigo Yana binsu da kallo, Assalamu Alaikum?

Amsa Masa Lahab da d'aya mutumin sukayi dayake sune musulmai a dakin Dad Kam kasa hakuri yayi ya sake tambayar Nnenna nace wanene Kuma meya kawo ki hospital?


"Accident muka samu a Keke Muna dawowa makarantan daga lokacin bansan Inda Kaine yake ba Saida na farka na ganta ashe ita ba abinda ya sameta shine ta taimakeni tana jinyata"Lahab ya basa amsa ganin Nnenna ta kasa ma magana duk tabi ta sure.


What?don kayi accident sai akace ta zauna a wajen ka har 2 days Kai baka da iyayene?

"Ina dashi ranka ya dade shiyasa ma dazun na kirasu Suna Kan hanya"

binsa da kallo duk Yan dakin sukayi especially Dad don dagajin amsan da Lahab ya basa ya fahimci yaron baida kunya amma zai nuna Masa karshen rashin kunya,Kai Ina magana har kana da bakin bani amsa lallai Zan nuna maka karshen iskanci kallon d'ayan mutumin yayi sai na kulle yaron Nan Kan yata?


wani shegen dariya Lahab ya sake ya nuna kansa da yatsa"Ni za'a Kama Ina kwance cikin jinya sai Kuma ya kalli Dr kana ji za'a zo a ciccibeni a hospital naka toh wallahi daidai yake da ka shiga rigimar Nan"


ran Nnenna ne ya tsoma baci ganin Lahab nason raina Mata kanin mahaifi Kama hannun Dad tayi"kayi hakuri Dad bansan haka abin zaiyi zafi ba da ban tsaya ba na dawo gida tausayi ya bani babu Wanda yasan halinda yake ciki gashi Mai keken ya gudu gashi babu waya a hannun sa shiyasa na zauna dashi"


Police in dake sanye da suit shima ya goyi bayan Nnenna, gaskiya ne sir bai Kamata a halinda yake cikin Nan a kawo maganar kamasa ba,duba da baida wani laifi ga Kuma abinda ya faru dashi Kai Kuma Dr ya Kamata in kun samu jinya irin wannan kurin ga sa hukuma a ciki bawai ku karbi majin yaci ire iren na accident haka kawai,don Kuna private hospital.


da Sauri Dr yace insha Allah sir za'a kiyaye muma ganin su da uniform nayi tunanin abin bana accident bane.


Dad Kam kamo hannun Nnenna ya sake ya bude kofar ya fita Yana ta masifa don Koh Ido ba mudu bane yasan kima kallo d'aya Yama yanayin Lahab ya gane ba irin yaran da zai Kama Kuma a rufe bane.


suma mutanen binsu sukayi a baya Dr Kam matsowa yayi kusa da Lahab Yana tambayar ta,daman bakusan juna da yarinyar bane?


Kallon gefe Lahab yayi kafun ya basa amsa"bama accident nayi ba"

Ah ah Hassan daman karya kayi ba accident kayi ba sannan menene tsakanin ku da yarinyar Koh kasan uniform na wani school ne a jikinta?


Komawa Lahab yayi ya kwanta bai baiwa Dr amsa ba hakan shiya Kara kular da likita tare da kudurtawa a ransa bazai Kara Koh daura Masa ruwa ba sai ya koyi yanda zaima babba magana juyawa yayi yabar office in.



Su Nnenna na sauka a block na clinic in daidai lokacin motar Mami ke kokarin shigowa cikin gate na hospital in kusan tare Suka iso dasu Abbu parking tayi a lokacin suma su Nnenna motar su ya tashi gabaki d'aya Kamar ruwa ya cita ta tsinke da abinda zataje ta tarar a gida don taga Kamar abin ya bata wa Dad rai sosai.


Mami ne ta fito a mota tare da rufewa hannunta d'auke da key,Rahab ma budewa yayi ya sauka da Yusuf a hannunsa sai mustapha,tsayawa Mami tayi tana bin motar Abbu da Ido ganin sunyi parking,fitowa dukan su sukayi fad'ad'a murmushin ta tayi ta nufi Inda suke tana Isa ta mikawa ummu hannu tare da sallama, Assalamu Alaikum


amsa Mata sukayi gabaki dayan su gaggaisawa sakeyi ana jajanta abin mustapha ma ya matso ya gaidasu banda Rahab dake ta kakkauda fuska don shi saima yanzun yake Jin kunyar Abbu da abinda ya musu,shiyasa ma ya kasa gaidasu bare matsowa kusa dasu.


Muje ciki Amina Abbu yace shima yayi Kamar baiga Rahab in ba, Addayiya dake gefe ne ta matsa Inda Rahab yake hannuta tasa ta dau Yusuf dake hannunsa don yaron kowa ya gansa sai yayi sha'awar d'aukarsa fari tass gashi bulbul dashi,tayi gaba sauran suka bita a bay shima Rahab binsu yayi a hankali.


Suna shiga cikin hall in gabaki d'aya jama'ar dake wajen Suka bisu da Ido don duk hassadan Mai hassada inya ga ahlin Nan sai sun burgesu tun daga suturan su har ga fatansu ga matan dake d'auke da hakoran gwal a baki Suna dan Hira sama sama Suna tafiya,nurse uzaifa ya tsayar Yana tambayar ta Koh zata nuna musu layin majinyatan Kashi.


Dan shuru tayi kafun ta tambayesa,Menenen sunan Mara lafiyan?

Hassan Alhasan,ya bata amsa.


dan Jim tayi sai Kuma ta sake tambayar sa,wani irin rauni ne hannu ne Koh kafa Kuma yaushe aka kawo sa?


Fad'a Mata uzaifa yayi,shekaran jiya da Sauri ta ce kwarai ta ganesa,kubi wannan barandan direct har dakin Mai number 1.


Toh mungode yace Mata, itama ta wuce su Kuma Suka nufi barandan tafiya Sukayi kad'an kafun Suka iso dakin Mai number 1 hannu muneera dake gaba tasa ta Kama kofar zata bude,tura kofar tayi ta bude gabaki dayan su Suka sa Kai daya bayan daya Suna shiga dakin da sallama......................





🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀






*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 69&70

Mikewa zaune yayi daga Kan gadon yanabin familyn sa dake shigowar da Ido,gabaki dayansu shiga sukayi Suka tsatsaya Suna kallon sa Rahab daya shigo daga Baya da gudu ya nufi dan uwan nasa bai tsaya duba matsalan hannunsa ba ya ruga yaje ya rungume Lahab sai Kuma ya fashe da kuka, murmushi lahab yayi Yana kallon fuska irin nasa dake kuka su Mami ma matsowa sukayi bakin gadon cikin soyayya don kaf cikin su an rasa Mai magana sai kallonsa da suke,"Wai menene haka Rahab kana kuka kamar mace"?Lahab ya tambaye sa Yana Kara rungumar dan uwan nasa.

dan janye jikin sa daga na Rahab in yayi yad'aga Ido ya kalli Mami sai Kuma abba,murmushi Abbu yayi yasa hannu a Cikin tulin gashin dake kansa ya Soma magana,inkun gama rungume rungumen sai muma muyi magana,murmushi duk Yan dakin sukayi,ya jikin naka?"da sauki yaya"ya basa amsa.

Addayiya ne ta mikawa muneera Yusuf itama ta matso wajen Lahab in tasa hannu ta Kama hannu Mai ciwon dan Kara Lahab ya sake yace"haba Addayiya ya haka ai saiki karasa ni"?

Uhmm sannu ya jikin naka?

"da sauki"sauran Yan dakin duka suka masa ya jiki yayin da Rahab ya d'ale Kan gadon ya kwanta Kamar shine Mara lafiya gasu uzaifa da muneera duk sun d'ad'd'ane Kan gadon sun Sasa a sakiya sai Hira ake,Mami Kam kasa cewa kome tayi sai bin Lahab in take da Ido a y'an kwana biyun nan har wani Yar rama yayi tace,Wai Lahab garin Yaya ka samu raunin Nan ne Allah dai yasa ba a filin kwallo bane?

A wajen ne Mana kinsan babu Inda zai samu irin raunin Nan in ba a wajen ba, Addayiya tace Lahab ne ya had'a fuska kafun yace"da Allah dakata Addayiya nifa ba a wajen kwallo naji ciwon Nan ba karki min sharrin da Kika Saba"Jin abinda yace yasa Mami Masa dakuwa da yatsun hannunta tace,ungo naka Addayiya ke maka sharri don baka da kunya.


Addayiya tace uwarka ce Mai sharri bani ba,sannan Kai umaru ka wani tsaya tsololo dakai kanajin abinda yaron Nan Mara kunya Yake gayamin bazaka bubbuge min bakinsa ba tunda uwarsa ta kasa bugewa, murmushi Abbu yayi sannan yace,kiyi hakuri Addayiya Kinga ba lafiya bane dashi amma inyaji sauki duk abinda ya Miki Ina tarawa muzammil xai maganin sa kinsan daman akwai punishiment dake jiransa.

Hade fuska Addayiya tayi Jin abinda Abbu yace tace,kaga ba wani ponushmant(punishment)da za'a Masa abinda ya wuce dai ya riga ya wuce Kuma in maganan abinda yake min ne Ni bana rikesa na yafe masa,langwabe Kai yayi Jin abinda Addayiya ta fada sai Kuma ya kalli yayan nasa"Yaya nifa gaskiya na gaji da zaman hospital Nan kawai a sallameni,wani kallo Mami tayi masa tace,wani irin a sallame ka a yanda kaken Nan kasan jinyan Kashi kuwa?toh babu Inda zaka,ummu ce tace,ah ah Amina da dai an sallame San in yaso yayan nasa sai ya dauko Dr n Kashi Yana zuwa har gida Yana dubasa,da Sauri Addayiya tace,Anya za'ayi haka kuwa in ba hospital ba Anya Lahab zai zauna a Masa jinya har yaji sauki?insha Allah zai zauna in ma bai zauna ba hannun sane zai lalace bari naje office in Dr muyi magana,Abbu yace Yana fita a dakin,mikewa uzaifa yayi yabi bayan sa.

Abbu yaje office in likitan ya nemi sallama duk da Dr baiji dadin haka ba amma yanemi alfarman shi zaina zuwa duk safiya kafun ya fito clinic yazo ya dubasa afternoon zaizo Koh da evening,ba musu Abbu ya amince sanan aka sallame sa,dakin ya shigo yana cewa muneera ta hada kayan dakin zasu tafi,kallon ta Lahab Yaya yace"Kinga akwai garden a hospital Nan inkin fita akwai Kaya dake shanye guda biyu wando da riga na mata dana Maza sai abaya baki,kallon sa duka Yan dakin sukayi har Mami ta kasa hakuri harta tambaye sa,kayan mace Kuma meya hadaka da kayan Mata Kuma,shuru yayi bai bata amsa ba har muneera ta fita a dakin,turo kofar akayi nurse innan ce ta shigo wanda koh sunanta bai sani ba, gaida su Yan dakin tayi kafun ta kalli Lahab tace,Hassan ya jikin na....makalewa maganar yayi lokacin da Rahab ya fitoh daga toilet in da Sauri ta kallesa ta kalli Lahab,d'aga Mata gira Lahab yayi Yana murmushi,bude Baki tayi zatayi magana Lahab ya rigata da cewa"Hussain sunan sa"Hussainin ka?ta Kara tambayar da?


Zuwa Rahab yayi ya zauna kusa dashi baice ma nurse in kome ba sai Addayiya data nuna Mata mami"ga maman su Ni Kuma matar baban suce saida na tsufa mijina ya aureta ga y'ay'an su shararren dan kasuwane in gaya Miki yaran Nan tun Suna kanana Allah yama mahaifinau rasuwa Allah sarki,murmushi kawai nurse in tayi ta kalli Mami, gaskiya hajiya kin iyya haihuwa Allah ya rayasu nima kisani a Addu'a Allah ya ban tagwaye irin su masu Kama wallahi Suna ban sha'awa?

Insha Allah kawai Mami tace juyawa nurse in tayi tana kallon Lahab tare da tambayar sa jiki.

"da sauki sister amma sallame mu"zaro Ido tayi da mamaki tace,an sallame kafa kace Hassan?amsa ya bata"eh an sallameni za'a cigaba da dubani a gani,sai Kuma ya dau waya da abayan ta ya Mika Mata harda sallaya,gashi mungode sister Allah ya bar zumunci"hannu tasa ta amshi wayar tace,kabar sujud in da abayar na bar mata.

"Ah ah ki amsa sister ai ta riga ta tafi"da mamaki tace,ta tafi Kuma Hassan tafiya babu sallama? murmushi yayi ya shafa kansa a hankali yace,tafiyar ce tazo babu tsammani,Mika Masa wayarta tayi ungo kasamin layinta sai muyi zumunci,amsar wayar yayi yasa Mata layin sa don baisan me zaice Mata ba karbar wayar tayi ta musu sallama ta fita Y'an dakin Kam sai mamaki suke don su basu gane wa ake nufi ba Amma Basu ce kome ba,har bakin mota nurse da Dr Suka rakasu,kallon Abbu mami tayi tace,yayan su nace Koh Zan wuce da Lahab Ina kula dashi a wajena daidai yaji sauki?


Wani kallo Abbu ya Mata amma baice kome ba sai Addayiya ce tayi magana,lallai Amina Baki da mutunci harmu Zaki nunawa son d'a da iyya kula dashi watoh mu bazamu iyya ba kenan Koh me?toh bara na tuna Miki inkin manta tunda Kika yaye yaran Nan Kika dawo Mana dasu nake kuladasu dani da yarana sai yanzun Kinga ya samu matsalan Kashi Zaki wani jajubo jiki Wai a baki shi kiyi jinya toh baza'a bada ba,hannu tasa ta tura keyar Lahab da karfi tana cigaba da masifa,wuce muje bazaka bita ba Shi dayake binta yaje can yayita bin nata kaidai bazaka ba munafurcin banza da wofi, baki ummu dasu muneera Suka sake Suna kallon ikon Allah kasa hakuri Abbu yayi cikin alhini yace,haba Addayiya itace fa ta haifi abinta ta fimu iko da yaranta tana da ikon tafiya da Lahab ta kula da lafiyar sa don haka ki barsa ya bita.


tsayawa Addayiya tayi amma har lokacin bata sake Lahab ba saina rike Masa kafadu da tayi da kyau Kamar xa'a kwace ta a hannunta tace,wallahi bazai bita ba ai da mahaifinku zai bar duniya yasan da Amina a duniya ai yace Kai ya baiwa amanar y'ay'an sa ka kular Masa dasu, toh akan me zaka barsu a gidan uban wasu wallahi bazan bayar ba ai Ni da Y'ay'ana aka barwa yara ba wata b'akutuwa ba tana karasa maganar ta Kama marfin mota tana kiciniyar budewa amma saboda bala'i tama kasa budewar shidai Lahab baice kome ba Kuma bai tayata budewa ba sai da ummu ta bude Mata Suka shiga Mami Kam kala batace ba ta bude motar ta ta shiga ita dasu mustapha Suka bar asibitin.



Parking Abbu yayi Suka bubbude kofar motan Suka fiffito har lokacin Addayiya batayi shuru ba sai mita take,in ma bakin cikin kajin da za'a kakkawone take hassada tace zatayi jinyar Lahab, kashinsa da fitsarin sa lokacin da nake dawainiyar su Ina ita Aminar take da uwarta sai da yara Suka kawo Kai za'a nuna muna fin karfi,badai Wanda ya kulata shikaran kansa Lahab baice kome ba har Suka Shiga cikin gidan, ba kowa a falo har lokacin Addayiya na makale da kafadar sa,bude kofar dakinta tayi Suka shiga su Abbu Suka zauna a falo,Suna Shiga dakin da Sauri ta sake sa tasa hannu ta rufe kofar harda makulli bude wardrobe nata tayi ta Ciro Sabon zanin gado ta feffesa Masa turare ta yaye nakan gadon ta shimfida Sabbi tana chanja pillow tace,ai gwara na canja Kar azo dubaka aga zanin gadon ba yanda yake tana gama shimfidawa Lahab ya kwanta, sake share dakin tayi ta feffesa turare,matsowa tayi kusa da gadon tace,Kai lahabu Mai Zan dafa maka Naman kazane Koh ganda Koh kifi Zan maka kasan ance in mutum ya samu matsalan Kashi so ake a ringa dafa Masa nama Amma karfa kaci Kashi?


Shuru Lahab bai amsa Mata ba leka fuskar sa tayi taga yayi bacci fita tayi a dakin taja kofar ta rufe tare da nufar kitchen dake babban falo,har yamma mamu da yaranta basu shiga sun duba Lahab ba sai Anwar daya fake idanunta ya shigo ya duba Lahab in tare da Masa ya jiki yayi zaman sa a bakin gadon Yana daddanna wayar dake hannun sa jifa jifa Suna Hira da Anwar in,Addayiya ce tayi sallama tare da leko cikin dakin amma bata shigo ba,had'a Ido sukayi da Anwar sai Kuma ta had'a fuska tare da turo kofar ta shigo hannun ta d'auke da food flask Mai shegen kyau guda biyu ajewa tayi akan table dake dakin ta had'a rai ta zauna akan kujera tana hararan Anwar tace,Ni don Allah tunda mutum yazo dubiya Kam basai ya duba ya tafi ba me na Zama Kuma zai sawa mutane Ido aka abincin ma mutum bazaici ba sai an wani zuba Masa na mujiya salon ya kware,murmushi Anwar yayi ya mike tsaye yace,toh Addayiya basai kince na tafi bakison naci amincin da Kika Masa ba ai shikenan Yana maganar ya bude kofar ya fita,kallonta lahab yayi kafun yace"Wai ke Addayiya menene haka"?


Hararan sa tayi tana d'auko kulolin tana ajewa akan gadon tace,uwarka ce amsar da ta basa kenan tana bude kula babban tuwon shinkafa ne fari tass gashi ya dawo sosai laida biyu ta dauko ta bude tare da ajewa a plate in dake gefe karamin kulan ta bude lumshe Ido Lahab yayi,kazane tayi ferfesun sa sai kamshin citta da tafarnuwa yake zubawa tare da tsokokin a kwanon Miya,ta aje a tsakanin su tare da mikewa ta taro ruwa a roba ta Mika Masa,hannun sa yasa ya wanke a roban kafun taje ta zubar ta dawo ta zauna kusa dashi Suka Soma cin abinci hankalin su kwance.




mami na barin hospital in bata tsaya dasu mustapha ba duk da yaso su tsaya ya sauka amma Mami tace ah ah sai dai ya bita suje gidan ta,Suna shiga gidan dukan su suka sauki a motar sukayi cikin gidan zaune Alhaji yake da yaransa a falo Suna Wasa da sallama Mami ta shigo falon yaran na binta a baya gaggaisawa sukayi Rahab da mustapha Suka zazzauna gabaki d'aya Rahab so yake ya koma gidan su,amma ya rasa ta Yaya Yana son Zama da dan uwansa waje d'aya,hijab Mami ta cire

Please Login or Register in order to submit comment