Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyawawan halayya suna taimakon ta.

Makarantan ba kowa shar kake ji sai maigadi hatta malamai babu.

Haka sukazo suka wuce suka fita get, tsayawa sukayi a bakin kwalta lahab ya tsaida keke, tambayar Nnenna yayi don shifa har yanzun bawai sanin sunan ta yayi ba,"baiwar Allah wai a wani unguwa kike ne"?

"Ka bar kudin ka kawai nagode zan iyya zuwa da kafa"

"Oh lallai ki tashi daga gadon asibiti kice wai zaki taka, bawai fa kinji garau bane Dr yace gobe ma zaki amshi ruwa"

"Nace ka bari zan iyya zuwa"

"Mtwss kinsan Allah kina bata mini rai ki shiga keke mu tafi"

Ba musu ta shiga ta zauna don daman karfin hali take kawai ba iyya takawar zatayi ba, shima shiga yayi tare da kallon mai keken"kaini GRA gidan mu xan kaiki tunda baki san gidanku ba"yace ma Nnenna.

Da mamaki Nnenna ta kalle sa"a GRA kake"?

"Oho bansani ba nima"

"Am sorry nima unguwan mu kenan amma mu muna layi na biyu"

Kala baice mata ba,itama shuru tayi mai keke sai tafiya yake, sunzo wajen round-about ga Go slow ya hade musu, gashi sai kiraye kirayen mangariba a ke hankalin lahab duk a tashe so yake ya samu sallah a gida, gashi sai kara cakud'uwa suke koh sunce zasu koma baya bazaiyu ba, gashi basu kusa da unguwan suba bare su taka da kafa Nnenna ma jikin nata kamar yanason tashi.


Kallon ta yake tayi ganin itama gabaki d'aya hankalin ta na gefen da take ta kurawa waje d'aya ido, shima wajen ya kalla wani dattijo ne fari tass a kallah zai kai shekara 90 ya tsufa sosai ga idanun sa manya masu girma d'auke da kwayar ido sky blue sak irin na Nnenna a duke yake kamar mai kusumbi yana rike da sanda, fuskar sa d'auke da farin gemu babu digon baki haka ma gashin kansa,hannun sa rike da roban bara, irin tsofafun nan ne masu bawa yara tsoro da tsufar su.

Had'a ido lahab yayi da tsohon ga mamakin sa kawai sai yaga tsohon ya nufo inda suke, da sauri Nnenna ta zabura ta juya ta kalli lahab suka had'a ido amma batace kome ba har tsohon ya kuda isa inda suke.

Bara ya soma yi a saitin lahab yana abasa na Annabi,tun ma bai iso ba, hannu lahab yasa a Aljuhu ya zaro gudan 200 zai mikawa tsohon, da sauri Nnenna ta damko hannun sa cikin rawan murya tace"karka basa"

"Akan me zakice karna basa" ?

"Akan nasan wanene shi wallahi ka basa abin hannun ka sai kayi dana sani, dana sani mafi muni a rayuwar ka, bako yaushe kyautatawa wasu yake zama Alkhari ba"



"Amma baki da hankali, oh haka akace muku a addinin naku bakyau kyauta"?

Kaga Ina maka maganar gaskiya kana d'aukar maganar addini, wallahi ka kuskura ka basa abin hannun ka toh ina mai tabbatar maka ka shiga tarko, yau ka fara shiga rayuwa ta, ka shigone da kyautatawa da tausayi a gareni bazanso kaddarata ta shafe kaba karka basa kudin nan"


Tsaki kawai lahab yayi yana mikawa tsohon daya iso kusa dasu kudin yana cewa,mu musulmai muna kyauta don Allah sannan babu abinda zai faru damu sai da izinin Allah, insha Allah Allah zai dubi niyata koma menene bazai basa ikon cutar dani ba.....................




✨Ruqeenjalal✨





*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 31&32
Bai idasa maganar sa ba Nnenna cikin zafin nama tasa hannu ta fizge kudin, cikin jin haushi lahab ya juya gareta"ke wai meye hakane? da babu kyau taimako da zan taimake kine da Allah ban kudi na"?

Kin basa kudin tayi cikin jin haushi yasa hannnu zai fizge kudin da sauri Nnenna ta boye hannun ta mai kudin a bayan ta, hannayen nata duka biyu ya kama da karfi zai kwace kudin abu kamar kokowa har mai keke yasa baki su bari amma ina lahab naci na cinsa, sai da ya amshi kudin sa, juyawa yayi zai mikawa tsohon, amma me wayam babu kowa agun, bai kawo kome a ransa ba illah mutumin yayi wucewar sa.


Nnenna dake rike da kulenta garin fad'a harta yarda shi a kasan keke, da sauri tasa hannu ta d'auke sa tana kallon lahab, shima kallon ta yayi irin kallo mai hararan nan"ke lafiya kike kallo na gashi ma tsohon ya tafi"

Girgiza masa kai kawai tayi tare da nuna masa kulenta dake kwance kamar mara lafiya, da hannu cikin fuskan tausayi amma batayi magana ba.

"Mtwss kuna da aiki a gabanku ace mutum ya kama kiwon kule, har makaranta Allah ya kaimu gobe kikazo da kulen nan insha Allah zan kai karanki wajen principal"

Shuru ta masa again bata sake magana ba Shima gyara zama yayi ganin an sake hanya"don Allah mai keke kaja wuta sosai sauri muku"

Kai d'an samari ba gudun da zan kara Ehen ga mangariba yayi har kana cewa na kara wuta?

Ganin fa mai keken nan d'an jarabane yasa lahab yin shuru, ganin sai mita yake masa akan yace ya kara wuta.

Ana kiraye kirayen Sallah Mangariba suka shigo GRA, har kofar gidan su Nnenna mai keke yayi packing bayan kwatance da ta masa na gidan nasu, sauka tayi a hankali jiri na ibarta ta dafe karfen get nasu a take karnu kan suka zaburo, ganin ta ya sasu komawa suka kwanta.

Mikawa mai keken kudi lahab yayi shima ya sauka agun, jakan Nnenna ya d'auka ya rike, "muje koh"?

Da mamaki tace" zuwa ina"?

"Cikin gidan naku mana koh zaki iyya rikon jakan ne? muje nayi ma Mom naki bayani akan rashin cin abincin da bakiyi"

Girgiza masa kai tayi tana mika masa hannu"ka bani jakana bani da mama, duk uwa baza'ace mata diyar ta ba lafiya taki zuwa ba tun safe, ni nan ba gidan mu bane"

"Da gaske kike? toh meyasa baza kije gidan kuba"

"Kaga ka bani jaka na kawai"

Mika mata jakan yayi daker ta bakka sa a bayan ta ta juya tana kallon sa a sanyaye tace" Thank you for Everything"


Murmushi kawai yayi yana shafa kansa, itama batajira amsar saba ta bude get in ta shiga har tayi nisa taji yace mata"bakiji ba"?

Juyowa tayi tana kallon sa amma batace kome ba.

"Wai nace baki fad'amin sunan kiba"?

Kai tsaye tace" Nnenna Obinna"

Ya mutsa fuska yayi cikin raha yace, Labiba nice name"

Waro ido tayi jin sunan daya kirata dashi, hannunta ta ware Alamun tambaya.

Shima girgiza mata kai yayi hade dace mata"ki tabbatar kinsha maganin da Dr ya bamu yana jakan ki, sannan ki daure kici abinci ki huta"

Juyawa kawai tayi ta nufi falon duk yana tsaye har ta bude ta shiga, ganin ta bace masa yasa sa juyawa shima ya d'auki hanyar layin su, zuwa lokacin an shiga sallan mangariba hakan yasa sa yin Alwala ya shiga masallaci kawai bai isa gida ba.

Ana idar da sallah yabi 'yan gidan su zuwa cikin gida, zama sukayi a falo abba ya kallesa da kyau, lahab ina ka shiga yau?

"Yaya ina makaranta ne"?


Wani irin makaranta lahab bayan 'yan uwanka sun dawo makaranta tun 3 na yamma, kai sai 6:00 sannan kace mini makaranta ka fitoh?

"wallahi yaya ka tambaye Rahab yau a school na wuni fa"

Muxammil ne ya tare abbu da sauri yace, Rufe min baki inka wuni a school sai akace kayi mangari ba ashan, ya za'ayi mutum na makaranta jakan sa ya dawo gida?

"Kash sai ma yanxun ya tuna da zancen school back nasa, kuma yasan Rahab ne kawai zai kawo masa" uhmm yaya nina bawa Rahab ya kawo mini nad'au littatafai a library"

Allah ya shirye ka lahab tashi kaje.

Mikewa yayi ya wuce dakin, wanka yayi ya sauya kaya, ya nufi daining yau kam harda shi ake dinner, umaimah ke raba abincin wa kowa, harta zo kan lahab tuwon shinkafa ne miyar Shuwaka ga kifi manya manya na yawo a ciki,tana gama zuba masa a hankali ya gusiri tuwon ya tallah miya harya sa tuwon a baki sai ya dakata yana tunanin Nnenna da yanzun ta fad'o masa a rai.

Koh tashi abinci yanzun?koh tasha maganin ta? koh me take iwar haka Allahu Alamu? sosai yayi zurfi cikin tunanin moment nasu na yau, ji yayi an kwace tuwon hannun nasa, da sauri ya d'aga kansa ya kalli wannan, Rahab ne dake zaune a gefen sa sai jama'ar daining in da suka bar cin abinci gabaki d'ayan su suka zuba masa ido suna mamaki yau Rana ta farko kenan da suka ga Lahab yayi zurfi haka a tunani, don shi kome nasa a watse yake baya ajewa kansa damuwa a xuciya gashi yau sunga sabanin hakan.

Binsu da kallo shima yake kamar yanda suke kallon sa har idanunsa suka sauka akan uzaifa, cikin eiiii eiiina yace"kai menene haka? ka wani zubomin ido kaci abincin ka mana maye"

Muzammil ne ya karbi zancen, ba maye zaka ce ba mayu zaka ce, watoh uzaifa ne marainin wayon ka shiyasa ka yabashe, tukunna ma tunanin uwar me kake?

Tambaye sakam koh wani abun ya b'aro koh wani masifan ya jawowa kansa waya sani, mamu tace cikin harare harare.

Addayiya dake xaune a falo tana jinsu da sauri ta mike tsaye, Keee halima masifa ya kare akan ki banda Amanar umar babu abinda zai faru sai Alkhari aniyarki ya biki mai mugun baki kawai.


Don Allah ya isa haka addayiya ke kuma Halima bazaki kama kanki ba ina hanaki shiga abinda ba ruwan ki kinayi koh? wata rana zakiga ba daidai ba, abbu dake wanke hannunsa yace yana mikewa a daining in.

Lahab kam abincin ma kasa ci yayi haka kawai yaji bazai iyya ciba batare da yasan halinda Nnenna ke ciki ba, kudur tawa yayi a ransa yana fita sallan isha zai kwace jiki yayi layin nasu, ana idar da sallah har yayi nisa yaji Muzammil na kwala masa kira ji yayi kamar ya zura a guje, wallahi da rana ne baxai tsaya ba gudun sa zaiyi, dawowa baya yayi har inda muxammil in ke tsaye a bakin get.

Lahab yawon dare ka fara ne koh me?

Girgixa kai yayi cikin haushi yace"Adewale ne ba lafiya shine xanje na duba sa"

Makarya cin banza Adewale dana gani da yamman nan a hanyar filin ball, nuna sa yayi da yatsa, wallahi lahab ina tausayin ka baka tausayin kanka, kafun na rufe idona na bude ka bace mini da gani.

Da sauri lahab yayi cikin gidan direct kan kujeran babban falo yahau ya kwanta, likimo yayi kawai yama rasa meke masa dadi yau jinsa yake wani incomplete, kamar yanda aka saba duk dare za'a zauna a falo babba ana hira kafun aje a kwanta sai asha fruit, yauma hakan take d'aya d'aya ake zuwa har aka cika falon kowa na abinda ke gaban sa, lahab na kwance ya juyawa mutane baya yana fuskantar kujeran harde kafafun sa yayi waje daya yayi filonda hanneyen sa.

Yau fa jama'an gidan na ganin sabon salo agun lahab, nitsuwar sa na yau ya dame su koh don bai saba nutsuwar bane, koh baida lafiya lahab baya nutsuwa waje d'aya.



*******************
Nnenna na shiga falon su taci karo da jennifer dake tsaye a bakin window sai mom dake kan kujera koh kallon su bata kara ba tayi hanyar dakin ta, dukan su da tsaki suka rakata.

Tana shiga dakin daman ji take kamar xata mutu da sauri ta kwanta akan gadon koh uniform bata cire ba, kulen ma ajesa tayi duk da shima ba lafiyar bane dashi lahab ya halbi besa, har kusan 9 na dare tana kwance bata koh rimtsa ba gashi bakin ta ba dadi maganin ma bata sha ba, maganar lahab ne ya fado mata, ta mike da sauri towel nata ta zaro a saman kofar toilet ta shiga wanka, ta dauro towel in ta fitoh tare da jika kayan makarantan ta a boket Allah ma yasa kala uku aka dinka mata.

Koh mai bata shafa ba ta bude wardrop na kayan ta, wani siket pencil mai tsagu a baya ta saka sai riga mai yale-yale, socks ta sanya a kafarta ta fitoh daga d'akin, tafiya take a hankali-hankali harta fitoh falo amma yanzun babu kowa a ciki.

Kitchen ta shiga bubude kulolin tayi ta mayar ta rufe, tare da jan d'an karamin tsaki, tukunya ta d'auka ta tare ruwa ta d'aura a gas, binciken liptop tayi ta zuba a ciki sai sugar ta rufe, tana tsaye a wajen har ya tafasa juyewa tayi a cup tasa shukuli, d'auka tayi ta nufi barin kitchen in.


Tsayawa tayi ganin jennifer a bakin kitchen in sai girgiza kwankwaso take cikin masifa ta soma magana,wannan gidan ubanki ne koh?da zaki dafa abinda kika ga dama, oh watoh a binda aka dafa bai miki ba shine zaki dafa naki daya ke ubanki ke cefene.

Rana Nnenna ya baci sosai amma sai kokarin danne wa take ba tare da ta kula Jennifer ba ta nufi gefen ta zata wuce, shan gaban ta jennifer ta sake tare dasa hannu zata kwashe cup na tie in, jan cup in tayi Nnenna kuma taki sakewa, kara ja da karfi jennifer tayi, a zuciya Nnenna ta sake mata cup in, a bazata kawai ruwan tie tafasheshe ya watsu mata a kafafu, abinka da jikin mai shafe-shafe take ta sake kara da karfi, wanda yasa mom da sarah rugowa daga d'aku nan su suna tambayar meya same ta.

Nnenna gefe ta koma ta tsaya batace kome ba, cikin kuka jennifer kece musu Nnenna ce ta zuba mata ruwan zafi, a hassale mom ta nufe Nnenna cikin zafin Rai zata kwad'a mata mari, cikin zafin nama Nnenna ta cafke hannun ta cikin xafi tace"karki kuskura kice zaki sa hannun ki a jikina don abin bazai miki kyau ba.

Tana gama maganar ta hurgar da hannu mom ta fita a kitchen in, gabaki d'ayan su da ido suka bita suna mamakin wannan Al'amari daman Nnenna nada bakine haka?ake ganin ta salaha.

Peace na tsaye a kofar dakin ta tana sauraron duk abinda ke faruwa amma bata iso cikin kitchen in ba, Nnenna ma yi tayi kamar bata san da mutum a tsaye ba, dakin ta shiga ta maida kofa ta rufe harda makulli.

Kwanciya tayi tana jin babu dadi na missing in lesson data yi yau, jakan ta dake gefe ta jawo takardun ta, soma cirewa tayi 1 by 1 tana ajewa akan gado da niyar bitan su don ta gaji da zaman kad'aici,hannun ta ta dakatar dake cikin jakan jin ya tabo laida, jawo laidan tayi tana kallo da mamaki glass nata ta gyarawa zama, tana bude laidan ganin laidan kaman na wajen sai da kayan ciye-ciye, bude laidan tayi taga laida babba a ciki bude laidan tayi tare da ware ido, cake ne babba d'an madaidaici Amma baikai na birthday girma ba, sai d'an card a gefe a manne.

Bude card in tayi letter ne Lahab ya bar mata, anyi rubutu mai shegen kyau da black pen " FOR YOU"maimaita wa tayi for u, b'are laidan tayi ta aje cake in akan gado, ta d'au wukar dake makale a gefen ta yanka, tana d'aukan kad'an-kad'an tana ci sosai cake in ya mata dadi bana wasa ba, tana tsaka da ci ta tuna da kulenta yayyanka masa tayi ta aje masa amma kememen yaki ci, har tayi mamakin hakan amma ta basar.

Ta samu taci cake in da yawa sauran ta lulube sa da laidan sa ta aje a cikin drower, wanke hannunta tayi ta shiga toilet ta taro ruwa a pampo tasha maganin dashi, kwanciyar ta tayi hade da kashe wutar ta lumshe idanun ta a hankali har bacci ya d'auke ta.




********************
Lahab kam jin surutun su ya ishesa yasa sa mikewa da sauri yayi cikin d'akin, kwanciya yayi kawai yama rasa meke masa dadi, kara wayar sa yayi ya d'auka ya duba, ganin Adewale ne yasa sa daukar wayar ya kara a kunnen sa" hello guy"

Hiii ykk?

"Normal friend yasu mom"

Klau suke, yau an tashi school mun nemeka bamu ganka ba, gashi kuma har geto munje shuru?


"Oh naje wani waje ne"

Ina kenan?

"Mtwss rabu dani dasa idon nan naka ka isheni"

Amma dai Lahab bawai fad'an ku da nabeel bane yasa ka ware mu gefe bako? haba lahab ban sanka da riko ba bayau kuka fara samun damuwa ba, daga karshe kaje ku sasanta amma naga koh damuwa da fad'ar ma bakayi ba?

"Kaga Ade ina da abubuwan yi da yawa ka barni naji da abinda ke damuna karka karamin zafi kan zafi haka kawai"?


Allah baka hakuri daman kawai na kirane naji inda ka shiga, gobe in zaku school na biyo kane mu wuce?

"no ku tafi a binku"

Kashe wayar kawai Adewale yayi bai sake cewa kome ba.

Lahab ma kwaciya yayi har Rahab ya shigo duk yana kwance, gefen sa yazo ya zauna hade da da zuba tagumi yana kallon lahab.

"Kai lafiya kazo ka zauna ka zubamin na mujeya"?

Hmmm lahab ba dole na zuba maka ba, yau gabaki d'aya naga kamar wani abu na damunka ne?

Shuru lahab ya masa sai surutu yake amma lahab bai kulasa ba, harya gaji don kansa ya koma ya kwanta.


Bashi ya samu bacci ba sai kusan 1 na dare ya samu bacci ya d'auke sa.


Tsaye yake a cikin wani gursungumin daji mai d'auke da manyan itatuwa hade da korayen ganye masu ban tsoro da duhu, ga kogi a gaban sa mai girman gaske yayin da ruwan cikin sa ya kasance jaaaaa kamar jini,da karfi yaji an hankad'a sa cikin ruwan cikin ikon Allah ya kauce bai fadi ba ya fadi a gefe.

Kallon bayan sa yayi don gani wanene ke son turasa ruwa,wani mummunan hallitane sanye da kaya jaaajazur koh kyaun gani bai dashi, hannu yasa zai kamo sa da gudu ya mike tsaye ya ruga da gudu yayi cikin dajin,


Wannan mummunan halintan ya rufa masa baya gudu yaje yana ganin dajin na jujjuya masa, ga wasu manyan kuleluka bakake dake takawa hallintan nan baya, wasu na saukowa daga saman itatuwa suna kai masa hari yana kaucewa.

A kallah yakai 2 hour's yana gudun kafun yaja birki ganin tsoho mai farin furfura a gaban sa tsohon da in bai manta ba ya hadu dashi kafun nan, tsayawa yayi yana dariya tare da nuna sa da hannnu sai kuma ya hurgar da sandan sa, ya wani nannade jikin sa ya zama mukeken maciji ya nufi kansa shima.

Riki cewa yayi ya rasa ina zai nufa gaba maciji, baya kuma hallintan nan da kulelu kan nan suna kara kusanto sa, tsungunawa yayi kawai ya kama kansa yana Ambaton innalilahi wa'inna'ilaihi raji'un.

D'aga kansa macijin nan yayi zai sare sa, a take ta bayyana cikin shiga na mayaka, wukar dake hannun ta ta d'aga da karfi zata sare kan macijin, kafun wukar ya same sa tuni ya bace batt.


Da sauri ya d'ago kansa jin hannun mutum a kafad'ar sa ya taba sa, zaro ido yayi ganin wance ke gaban sa, cikin tsawa take ce masa"ka tashiiiiiiiiiiii ka tashiiiiiii naceeeeee makaaaaaa kaa...........





*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


*Kuyi hakuri babu yawa sai in Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya yau ma da yamman nan na daure nayi typing duk saboda far in cikin ku don naso sai gobe zanyi*

Page 33&34
Ka tashiii naceee???ta yi maganar tare da dafa kafadunsa duka biyu ta girgiza sa da karfi.

Hasbinallahu wani'imal waken shine abinda lahab ya furta lokacin da ya farka daga wannan mumunan mafarki mai cike da rud'ani, abinda Nnenna tace masa ne a cikin keke napep ya dawo masa akan karya baiwa tsohon nan sadaka toh wanene shi wannan tsohon, dahar yayi mafarkin sa yau kai akwai dai abu a kasa.


Jin motse ta wajen window yasa shi lalubar wayar sa da sauri ya kunna tare da haska wa, baiga kowa ba sai glass in windon su dake bude wandan yake da tabbacin rabon su dasu bude glass harya manta,mikewa yayi da sauri ya isa wajen windon zai rufe, amma me? yana isa ya hango kule baki a tsaye a bakin window, gaban sane ya fadi amma bai wani nuna razana a fili ba, don tsoro na d'aya daga cikin abinda yasa ake galaba akan mutum.

Window ya rufe da bismillah ya sake labule, jima yayi baccin ma ya daina ji kwata kwata, toilet ya bude ya shiga Alwala yayi yazo ya shimfida darduma, lokaci ya duba karfe biyu ne daidai na dare, tada sallah yayi.

Rahab da fitsari ya ta dashi mikewa yayi ya sauka a katifar sai kuma ya tsaya da mamaki ganin Lahab na kiyamun laili yau harda kiyamun laili?Shiga toilet in yayi yayi uzurin sa ya dauro Alwala shima yazo ya tada sallan.


Raka'a shida yayi ganin sallan lahan in bana karewa bane yasa sa sallame wa ya koma katifar sa ya kwanta abinsa.

Sallah lahab yayi tayi har kusan hudu na asuba kafun ya sallame, yana idarwa ya saka sports wear nasa ya Riga uncle FIta abinsa, jikin sa yau duk a sanyaye na mummunar mafarkin da ya Afku jiya abin ya tsaya masa a rai.

Ga kuma tsananin son sanin halinda Nnenna take ciki, gangarawa layin su yayi har kofar gidan su Nnenna, ya tsaya yana tsumayin zata fito ya ganta.

Har kusan Biyar amma fara kiraye kirayen sallan asuba yana tsaye a kofar gidan su har lokacin, kamar mafarki ya hange uncle muzammil ya nufo Layin, ai da gudu ya kara gaba ya sake zagayawa yayi Layin su.


Jan birki yayi a kofar gidan su yana haki don ba karamin gudu yasha ba, amma kuma duk da haka yaki shiga gidan sai da ya bari muzammil ya shigo Layin kuma ya tabbatar ya gansa kafun ya tura kofar ya Shiga hankalin sa kwance.

Tura kofar falon su yayi cikin Sauri ya Shiga falon direct kofar sashin su ya nufa yana Shiga dakin ya tadda lahab na kokarin Sanya jallabiya a jikin sa.


Jin mutum ya shigo dakin bako sallama yasa Rahab saurin juyawa, lahab INA ka shiga da asuba uncle yazo Neman ka?

"Kala lahab baice masa ba don shi a ganin sa manna masa hauka Rahab yayi ya zai gansa da Mayan sport kuma yana tambayar sa INA ya fito, shiyasa baice kome ba kawai ya wuce bayi abinsa wanka yayi yayi alwala yazo ya zura kayan ya wuce masallaci.


Bayan sun idar da sallah gabaki dayan su yauma Kamar kullum Suka jero a jere xuwa cikin gidan,gabaki dayan su dakin Addayiya Suka shiga Suka gaidata sannan kowa ya wuce dakin sa zai d'an kwanta daidai lokacin fita sun dan rintsa.

Kasan cewar gogoji(Mai aiki)Bata dawo aiki ba har yanzun don abbu yace ta Bari har d'anta ya samu cikekkiyar lafiya tukum,dole tasa mamu da ummu Suka Fara shiga kitchen da kansu, Kuma yau girkin ummu ne shiyasa ta shiga kitchen bayan idar da sallan asuba.

Lahab dakin su ya shiga shida dan uwan sa, harya kwanta a katifar sa da sauri ya Mike ya fita a dakin,Rahab Kam da Ido ya bisa ya rasa meke damun dan uwan Nasa ba, daga jiya xuwa yau duk yabi ya susuce baida cikekkiyar nutsuwa Kamar yanda yake, duk da Mai rawan Kaine Amma wannan azarbabin NASA yafi nada yawa.


Shikam lahab Yana fita a dakin kitchen ya wuce ya tura kofa ya shiga, ganin ummu a ciki yasa Shi tsayawa Shi baiyi abinda ya kawo Saba Shi bai fita ba.


Ummu Kam ganin ba gai data zaiyi ba yasa ta watsa Masa mugun kallo cikin Jin haushin sa, da Kuma haushin kin dauko wata Mai aikin da abbun yayi gashi su umaima kiwiya ne dasu dakin aikin asuba sam,Kai lafiya kazo ka tsayamin a gaba Kamar an baka sallahu Akaina?


Dan tsotsa Kansa yayi sai Kuma ya jingina da jikin kitchen in cikin murmushin Nan nasa maikyau ya bude Baki ya Soma mata magana"Aunty me ake girka Mana ne yau munji dadin mu"?

Wani shegen kallo ummu ta Masa irin kallon Nan na ka Raina mini wayo cikin haushin tace"Kai da Allah gafara mini anan kullum da ake girki baka taba tambaya ba sai yau Don Neman iyayi kome?

Cikin dariya-dariya na wuce haushi lahab ya kamayi"Haba Big aunty daga tambaya sai kuma ki sauke a kaina naga dai bani nakar zomon ba rataya aka bani"?

Kala batace masa ba ta cigaba da aikin ta Shima bai sake magana ba ya wuce cikin store Nasu yana tunanin shin mai ya dace ya dafa mata

Please Login or Register in order to submit comment