Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Masa a fuska ba sai bayan ya fita sosai tayita zagin umaima,washe gari da safe Rahab da sauran yaran Suka shirya cikin kayan makaranta suka tafi Abbu ya gama Shirin office NASA harzai fita Addayiya ta kirasa shida mamu ta musu bayanin akan za'a kawo lefen umaima gobe Tuesday sosai abin ya baiwa mamu mamaki ace Kamar ita uwar umaima bata San da zancen lefe ba sai da Addayiya ta Kira ta ta sanar da ita lallai yau zataci uban umaima,mikewa tayi a fusace zata bar dakin Abbu ya daka Mata tsawa tare da Bata izinin komawa ta zauna komawar tayi ta zauna Rai a bace Abbu yace"Abba haleema bazaki taba hankali ba tunda har yanzun Baki da hankali ya uwata na tsaka da magana Zaki tashi ki fita wannan ai raini ne"?

Rabu da ita ai haleema halinta sai Allah Inda sabo na Saba da shi nasan babu abinda ya Bata Mata Rai sai zancen lefe gobe Kuma ta Fara ji a bakina Addayiya tace tana girgiza Kai,Abbu yace haba Addayiya ai a tunani na Koh ke Zaki iyya tarban masu kawowan basai haleema tasa Baki ba Amma menene don kin sanar da ita Kuma ni naji dadin hakan Koh banza iyayen yaron Nan sun girmama mahaifiyata"bama su bane Umar yaron ne daya zo duba Lahab yau yake sanar dani akan Suna so zasu kawo Kaya Amma umaima tace karsu kawo sai Lahab yaji sauki.......ai bata gama magana ba mamu ta amshe da cewa"yanzun akan yaron Nan har umaima na cewa a d'aga kawo lefen don bata da hankali Ni na tabbatar wallahi Koh mutuwa nayi na tabbata yayan Amina bazasu fasa abinda sukayi niyar Yi ba akan me zatace haka wallahi yau sai ta gane kuranta.



Addayiya tace don Allah haleema inkin tashi Mata hukunci ki kasheta har lahira bake kince baki da kunya ba Bismillah jeki tabata Ni Kuma Zan nuna Miki karfin ikona a gidan Nan ShaShashar banza Mara hankali,Abbune ya Soma bawa mamar tasa hakuri itakam mamu mikewa tayi tabar dakin,tasan Koh hauka take yanzun dai bazata lakato wata maganar ba shiyasa ma bata bi takan umaimar ba Kuma batace Mata kome ba sai dai fuskarta kawai mutum zai gani ya gane tana cikin bacin Rai,d'aga waya tayi ta Soma kiraye kirayen kawaye da Yan uwanta akan gobe za'a kawo kayan auren umaima,duk Wanda ta Kira sai yayi Mata mitan akan sai yau za'a sanar dasu hakuri kawai take basu.



Abbu na fita a dakin Addayiya compound ya nufa zai bar gidan da Sauri mamu tabi bayan sa har ya shiga mota ya hangota yaso yaki tsayawa amma ya daure yaji dame tazo,abinka da Mai jiki dan Sauri da Tayi yasa ta sauke numfashi akai akai bayan isarta jikin motar sa ta Soma magana daker daker"daman Alhaji Naga fita zakayi bakace min kome ba?kallon banza ya Mata kafun yace toh me kike son nace Miki haleema?



Haba Alhaji kana fa zaune kanaji Addayiya tace gobe za'a kawo lefe amma baka bani kudin da zanyi sayyayyan abubuwan tarban Baki ba kasan wannan shine aure na farko da zamu d'aga a gidan Nan auren umaima da Anwar gaskiya bana son Abinda zaisa a Raina mu nafison kome a wadace,shikam Abbu Yana mamakin irin jaraban karya dason kudi da Haleema ke dashi a rayuwar ta amma baice Mata kome ba har Saida yaja dan lokaci ita dai tana tsaye tana kallon sa yace"Haleema wa'inda zasu kawo kayan Nan fa ba a gombe suke ba a bauchi ne Koh danko zaku dafa musu ai kye bari gobe yayi a dafa xuwa yamma ai ya dafu Koh?


Jin abinda yace yasa ta hade rai tace"haba dan Allah kafa San yau nake son naje nayi sayyayyan kayan aiki irin su kaji da sauran su kaga gobe in Yan uwa Suka hallata sai su Fara aiki kawai,zaro Ido yayi ya nunata da yatsa yace"yanzun haleema da bakin ki kike cewa Zaki kasuwa sayyayyan kayan abinci wallahi karki kuskura Kuma kudi ne dai bazan bayar ba saina dawo office Yana karasa maganar yaja motarsa yayi gaba ya barta a tsaye agun tana juyawa zata koma cikin gida Kamar ance ta kalli bini sukayi Ido hudu da ummu dake saman bini tana kallon su,a fusace mamu ta shiga falo ta nufi upstairs don wallahi yau saita nunawa ummu bacin ranta na sa Mata Ido da take a gidan.



Ummu dake sama da Sauri ta Soma saukowar daga saman jin takun steps a fusace yasa ta bude dakinta dake sama ta shiga tare da maida shi ta rufe da karfi ta murza key harga Allah masifar mamu ya isheta haka bata son cecekuce a gaban yara.




********************
tun da sassafen mubeena ta kasa nutsuwa yau Monday sunada paper batason zuwa makarantan balle ta hadu da Rukayya ita Soma tayi Inna ta tashi suje su duba Lahab amma tace sai ta dawo makaranta sai suje ga Nabeel dake ta surfa Mata nacin ta shirya yau da kansa zai Rakata makaranta lura da yayi duk jikinta a sanyaye,ruwa ta Iba taje tayi wanka shima Nabeel wanka yayi ya goge kayan sa bayan ta shirya dumamen tuwon daren jiya sukaci,Nabeel ya dauko kayan daya dinka jiya da niyar kaima Mai kayan tunda jiya bai samu ya karasa da wori ba sallama Suka ma Inna dukan su Suka fita a gidan tafiya suke Suna dan taba Hira kowa ya gansu yaga Yan uwa gasu farare tass farin nasu daya ne ga Kama na jini,sunkai almost 30 minutes basu samu Keke da zai kaisu makarantan su mubeena ba in Kuma Suka ce drobe basa samun Wanda ba mutane kowa yasan yanayin garin gombe in gari ya waye especially ranakun makaranta akwai go slow sosai hakan ya taimaka wajen Kara lattin nasu sosai hankalin ta ya tashi ganin lokacin shiga jarabawan bai wuce 40 minutes ya rage ba,Nabeel wayar sa ya zaro a Aljuhu ya lalube number Ade ya Kara a kunnen sa.





*****************
Adewale na tsakiyar falo da papansa sai jaraba yake zubawa akan rashin zuwa makarantan da Ade yake"Wai papa mekake so nayi ne ba dai an koreni a makarantan ban menene Kuma zai kaini"? papa yace mezai kaika kake tambaya na ai in mukaje na Basu hakuri albarkaci na za'a Mai dakai amma dayake Kai Wawa ne kafison kayita yawo a gari kana galantoyi kaida abokan shashancin ka"ringing in wayar Ade shiya dakatar da papa ganin Mai Kiran yasa Ade picking ya Kara a kunnen sa Yana sauraron abinda Nabeel ke cewa Kamar haka,"pls Ade nace kana gudane so nake ka aramin machine naka wallahi Auntina ce tayi late gashi Suna da exam Nan da 40 minutes"ba kome Bara na fitoh wait for me Ina zuwa yanzun Nan Yana karasa maganar ya katse Kiran tare da kallon papa yace"nifa gaskiya papa na gaji gani nayi mu yanzun sss 3 ne Kuma Muna second term no need na dame kaina da karatu Koh zuwa makaranta Koh naje Koh Kar naje duk daya ce revision ake fa Kuma Koh ban samu Avr ba ban damu ba tunda bazai hanani registration na weac ba,Yana maganar Yana tafiya Harya bude kofa ya fita binsa a baya papa yayi Yana zagin sa Ade bai wani tanka masa ba ya shiga garejin gidan su key machine dake aljuhun sa ya zaro ya tsokawa machine in zai tayar papa daya iso wajen hannu yasa ya zaro key machine in tare da juyawa ya koma cikin gidan,da Ido kawai Ade ya bisa sai Kuma ya dake banban machine in da karfe ya sauka akai bude gate yayi ya fita da kafa Yana Kara duba time ganin kusan 6 minutes da Kiran sa da Nabeel yayi ya shige gidan su David ya shiga da Sauri ya nufi flat nasu Allah ya Sosa sun fito kenan zasu fita sai gashinan alfarman machine na kanin David ya nema ya basa aro amma bai samu ba saboda zashi makaranta dashi sai mota da David ya basa,karba Ade yayi duk da Suna koyan mota da Lahab Kuma sun Kai kusan shekara amma bai taba Hawa ya fitoh cikin gari ba,amsar key yayi ya bude motar ya shiga tare da kunnata yayi reverse yaja zuwa bakin gate Mai gadi ya bude Masa ya fita,tafiya yake Yana duba time ga kirjinsa dake bugawa na rashin Sabon tuki da yake yanzun Yana taka tsamtsam gudun karyayi kuskure,gangarawa kwaltan su Nabeel yayi tun daga nesa ya hangosu Suna takowa da kafa har round about nasu.



Parking yayi a gaban su gabaki dayan su Suka ja baya tare da basa hanya Suna kaucewa zasu wuce sake Shan gabansu yayi Wanda hakan ya fusata Nabeel har ya Soma dura zagi akan Mai motar nason kadesu,sauke glass Ade yayi yace"toh sarkin masifa washe baki Nabeel yayi yace"durun wa Kaine mutumina irin wannan harka haka wannan motar fa"Kai shigo da Allah time na tafiya,da Sauri Nabeel ya bude gaban motar yana kallon mubeena dake hade da fuska tunda ya Kira Ade take wani ciccin magani ita a dole bai Mata daidai ba yace"Aunty kizo ki shiga ya kaiki lokaci na wucewa Ni Kam Zan wuce gidan su Nadiya na Kai Mata dinkin nata.



ranta badon yaso ba ta shiga gaban motan tana hararan kanin nata,shikam Nabeel ya maida murfin ya rufe Bai damu ba Ade Kam sai wani murmushi yake yau zasu kasance tare da juna Kuma a kadaice matsawa baya Nabeel yayi Yana musu a sauka lafiya har Suka bacewa ganin sa shima tsallaka titin yayi ya nufi gidan su Nadiya customern sa.



Adewale tuki yake amma gabaki d'aya hankalin sa na kanta wankan ta gabaki d'aya ya tafi dashi duk da ba walwala a fuskar ta amma ba laifi tafito ras da ita dan gyaran murya yayi ya juya ya kalleta kadan,juyawa tayi ta kallesa amma batace kome ba ganin har lokacin kallon ta yake maida kanta kan titi tayi sai Kuma ta zare Ido jikinta na rawa tasoma Kiran innalilahi wa'inna'ilahu raji'un da Sauri tayi super ta rungumesa tare da rumtsa idanunta jikinta na mugun b'ari...........................




🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀








*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 75&76

Wani irin Jan birki Ade yayi Wanda har Saida Kan mubeena dake Kan kirjinsa ya koma gaba ya bugu kara ta sake da karfi bawai na zafin buguwar bane ah ah na tsoro ne,sauke ajiyar zuciya yayi ganin Allah ya takaita abin saura kadan ya buge motar dake gabansa,bude Ido tayi ganin babu abinda ya faru yasa ta sauka a jikinsa cikin bacin Rai tace"Wai menene haka wannan ai hauka ne in kasan baka iya driving ba ya zaka d'auke Ni a mota ka nemi kashe Ni a banza,kala baice Mata ba bai Kuma tada motar ba bai Kuma fasa kallon ta ba a fusace tasa hannu zata bude motar amma ta ji a rufe gim da Lock,juyawa tayi ta kallesa suka had'a Ido ta cilla Masa harara cikin Jin haushi tace"malam ka bude min Mota na sauka nayi late,bai saurare taba yayi ma motar key,fusata tayi ta Soma Masa ihu ya sauke ta Koh kulata baiyi ba sai zuba gudu da yake a kwalta bini bini Yana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannun sa,saura minutes 6 a shiga jarabawa Kuma daidai lokacin suka iso gate na makarantan itama Karan kanta mubeena hankalinta a tashe yake"ta Ina ne department naku,nuna Masa tayi da mugun gudu ya kwasa Wanda Saida yaja hankalin dalibai dake geftawa, parking yayi a gaban block nasu mubeena saban Sauri bude motar tayi ta ruga da gudu tayi cikin hall na exam nasu hango lecture dake tawowa zai shiga,tana sa kanta a hall in taga Rukayya tsaye hankalinta tashe da waya Kare a kunnen ta ganin mubeena yasa ta saurin nufota tana cewa"mubeena lafiya kinsan halin malamin Nan baida mutunci sannan Kika buga late gashi saura minutes 2 fa a fara,Koh rufe Baki batayi ba malamin ya shigo hakan ya sata hakuri da Sauri ta nufe kujeran da ta Kama musu ita da mubeena,kauda fuska mubeena tayi ta zauna a wani kujera daban ba tare da tabi ta kanta ba sai kokarin boye bacin ranta take Bata son bayyanawa.


Ade da Ido kawai ya bita ganin yanda take gudu cikin tashin hankali dariya kawai yayi sai Yana shafa kansa sai Kuma idanunsa suka sauka Akan wayarta daya Fadi lokacin da Suka kusa accident tashin hankali Bai Bari ta d'auka ba dukawa yayi yadau wayar Yana jujjuyawa sabuwa ce Kiran hot 6 kunna wayar yayi ganin akwai Lock yasa sa jan tsaka ya aje wayar tare dajan motar yabar school in.




*****************
Tun da sassafe Nnenna ta Soma share share don peace ta dawo ta karbi aikin kitchen share tsakar gida take hankalinta ba'a kwance ba ga idanunta da Suka kukkun bura jiya Koh isheshen bacci bata samu ba na rashin Kiki abin ya mugun d'aga Mata hankali sosai sabo, da kule harna tsawon shekaru ace yau an waye gari baka gansa ba dole zakaji ba dadi kwashe sharan tasoma tana zubawa a basket dake gindin bishiyar goiba tacan bayan zaro Ido tayi ganin Kiki a cikin shara yayi lame lame dashi gashin jikinsa duk ya yamutse ya yarda kai Kamar macece hannu tasa ba kyama ta dagosa hawaye na zuba a idanunta Koh ba afada ba daga gani ruwan da akai shekaran jiya akan sa ya Kare kenan? da Sauri ta nufi cikin gidan dashi Allah ya sota ba kowa a falo da gudu ta Shiga dakinta.


Maida kofar bayin tayi ta rufe ruwan zafi ta had'a a bucket ta Soma wanke kiki Kamar mutum harda soap tass ta wanke gashin jikinsa tadau towel nata ta lullabesa da gudu ta fito a toilet in ta ajesa akan gadon fita tayi a d'akin da Sauri har Suka kusa cin Karo da peace dake kokarin fita a kitchen ita Kuma tana kokarin shiga matsa Mata peace tayi cikin Jin haushin ta ita Kam Nnenna batabi ta kanta ba ta shiga kitchen in fridge ta bude ta dauko milk ta fita,zubawa Kiki tayi a ciki plate na abincin sa data aje a daki tana zuba Masa abinci kullum wanke plate in tayi ta tsiyaye madaran da Sauri tahau Kan gadon ta dauko sa tura Masa plate in tayi a saitin bakin sa amma dib kakeji kiki ya kasa latsar madaran,bude Masa Baki tayi ta dau Goran ta kafa Masa a Baki daker da tsuden goshi yasha kadan rufe Goran tayi da Sauri ta shiga ban dakin shashaf tayi wanka tazo ta zura uniform nata jakan makaranta ta d'auka ta cicibi kiki dake cikin towel har lokacin Kuma ita Bata cire Masa ba ta nufi barin gidan, Abraham dake kokarin shigowa ne a gate ya tsaya Yana kallonta da mamaki yace"ba Dad yace zai dauko Miki driver ba ki daina fita ke kadai"brother cat nawa ba lafiya so nake nakaisa clinic a dubasa"uhmm kawai yace ya bude Mata kofar motar tare da Bata izinin Shiga ba musu ta shiga ya data motar Suna barin layin su waya ya d'auka ya Kira Dad ya sanar dashi yadau Nnenna zai Kaita makaranta,Suna gama wayar ya tambaye ta"Hope de da Kika tashi fita clinic in dabbobin kinsan a Ina yake Koh"?girgiza Masa Kai tayi amma Batayi magana ba shima baice kome ba ya cigaba da tukin cikin kankanin lokaci yayi parking a gaban wani shago Kamar chemist,sauka sukayi dukan su Suka nufi cikin shagon glass in kofar ya bude Suka shiga.



Sosai akayi treatment in kiki harda allurai aka Masa Dr n yace a bar Masa shi taje school ta dawo, Abraham ne ya biya duk kudin da aka kashe a clinic in daga Nan makaranta ya kaita tare da sanar da ita akan ta jirasa zaizo ya dauketa in aka tashi,zaune take a class tana tunanin yanda Lahab ya kwana da jiki taci burin zuwa ta dubasa sannan ta Kai Masa card nasa amma Bata samu hakan ba gashi tsoro take ji kada ace bazata Kara ganin sa ba tunda ance an koresu gashi yanzun batasan gidan su ba,ga Dad zai nema Mata driver tunawa da zulaihat data taba zuwa ta karbi jakan Lahab a hannun ta in bata manta ba Yar junior set ce Kuma ba shakka zata game fuskar ta da Sauri ta Mike ta fita a class in ta sauka a barandan su.


Block in junior ta shiga class by class amma koh Mai Kama da zulaihat bata gani ba sauka tayi a baranda har tazo tsakar compound na makaranta motar gidan su Lahab ta danno Kai cikin makarantan muneera ce ta balle marfin motar sai Rahab daya fitoh a gidan gaba sosai Nnenna ta daskare a wajen tana bin dan uwan nasa da kallo cikin Al'ajabi don ita a zatonta Lahab ne yazo makaranta da Sauri ta nufesa ganin zai hau block in class nasu tace"Lahab tsayawa yayi Yana kallon ta da mamaki duk da yasan ba shi ta sani ba amma ya cika da mamakin Inda tasan Lahab don shidai bai taba ganinta a school in ba"ya jikin naka Wai har an kunce hannun ne"?ta ce tana kallon sa, murmushi kawai yayi yace Mata"da sauki sosai amma baizo ba"waro Ido tayi kenan wannan ba Lahab bane lallai kam,card data dauko da niyar baiwa zulai ta Mika masa tace"gashi na Lahab ne Inka koma ka basa" hannu yasa ya karbi ATM in Yana jujjuyawa juyawa tayi tana tafiya shidai Yana tsaye har lokacin Yana binta da kallo Harta shiga aji shima juyawa yayi ya wuce nasu ajin.



***************
Adewale na barin makarantan su mubeena gidan su Lahab ya wuce,zaune suke a daki Suna Hira kallon Adewale Lahab yayi yace"Wai Ade lafiya yanaga duk kabi ka ramene ga wani fara'a daka shigo dashi Kamar Wanda aka baiwa auren mubeena"kyelkyelewa da wata bazawaran dariya Ade yayi shima Lahab dariya yayi a hankali Yana kallon abokin nasa Addayiya ce ta turo kofar dakin fuska a hade tace"Kai Kunga banson hauka ya zaku zo ku zauna min a daki kunamin ihu bare ma Kai Mara lafiya surkuwar haleema tazo dubaka tana falon su zata shigo sannan kazo kana dariya a sama sama Kamar zararu"shuru sukayi gabaki dayan su basu kulata ba itama juyawa tayi ta bar dakin.



"Bazaka gayamin meke maka Dadi Yana saka rama be Wai"?cikin murmushi Adewale yace"kasan yau Nina Kai mubeena makaranta a mota"waro Ido Lahab yace mota kwal uba yaushe ka samu mota Ni ban samu ba ai wallahi da sakel"kaga kwantar da hankalin ka Lahab ba nawa bane na David ne"?


"Toh ya akai ta yarda ka dauketa wannan sarkin taurin Kai"murmushin dake fuskar sa har lokacin na Nan yace"Nabeel ya kirani Nan take ya sanar dashi yanda Suka Kaya,sosai Lahab yaji dadi ganin abokin nasa na cikin farin ciki yace"aiko aiki ya sameka Ade sai kayita fama aiki ya sameka soyayya ne Koh wahala"hararan sa Ade yayi ya zaro wayar ta ya nunawa Lahab yace"tabbas zata kirani kaga na samu hanyar communication da ita"gyada Kai kawai Lahab yayi Yana murmushi don shi soyayyar su dariya yake basa.



muryan Addayiya sukaji tana cewa"Bismillah ki shigo Yana ciki shigo farida Sannu da zuwa,sai Kuma aka turo kofar Addayiya na gaba farida dake sanye da hijab har kasa babba sai socks dake kafarta kanwarta na gefe sanye da gyale,Suka shigo Zama farida tayi a kasan carpet in dakin duk yanda Addayiya taso ta zauna a kujera ki tayi shikam Lahab tunda ta shigo ya mugun hada rai Yana Mata wani kallo na bacin rai gata dai a fuska mutuniyar kirki har kwatance iyaye keyi da ita akan yaransu suyi koyi da halinta a unguwan amma basusan Kura bace da fatar akuya,ita Karan kanta jikinta yayi sanyi don kaf gidan Banda Anwar babu Wanda yake supporting in soyayyar su sosai irin Lahab so dubu in Suka hadu ya ringa tsokanar ta kenan San bai rike girman sa na surkinta bappan mijin da zata aura ba,amma abin mamaki yau Koh kallon arziki bata samuba amma ta alakanta abin da ciwon dake damunsa ne kawai amma ganin yanda ya juya ya Kama hira da Ade sai taji ranta ya baci sallama Tama Addayiya Suka tafi.





Bayan fitar su juyawa Ade yayi ya kalli Lahab yace"Wai Lahab wannan ba Amiran islamiyyar ku bace ustaziyar unguwan Nan Kuma matar da Anwar zai aura Kodai ba ita bace"ita ce Ade Meka gani"?da mamaki yace gani nayi kana Mata magana kamar maijin haushin ta Kuma Naga ba hakan kuka Saba magana ba last haduwar da nasan munyi da ita ma in ban manta ba ta fito islamiyya mu Kuma mun fito ball har kake cewa dole a auren su ayi program Kai babu ruwan ka da ustazanci ta ajesa sai bayan aure"?



Kai wallahi Ade yanzun nayi mugun tsabar yarinyar munafuka ce Mai 2face ce"Kamar Yaya ban gane ba ya Kara tambayar sa nan Lahab ya zayyana Masa duk abubuwan da suka faru tare da kudurinsa akan wargaxa auren sai Kuma warning da Mami ta buga Masa akan zancen"rike Baki Ade yayi yace"gaskiya Lahab ba haka zakayi ba kawai ka rabu dashi ya aureta taima watakil auren ya zamo tsular shiriyarta sai kaga ta shiryu"wani kallo Lahab yayi Masa yace"kana nufin auren ta da Anwar zai nutsar da ita macen da aka sa date na auren ta har zata iyya fita hotel tsakar dare tana can akan me Koh kaffara bazanyi ba Anwar ba mazinaci bane akan me Zan bude Ido Ina kallo ya aure Mai dattin Mara tazo ta Haifa Masa yara Yan iska karfa ka manta duk abinda mace ta aikata zata gani a kwartar tuwon ta sai Wanda Allah ya sosu suke ganin daidai amma mace batayi iskanci bama ya ta Kare bare tayi Kuma Ni abinda ke dad'a batamin Rai shine fuskar mutanen kirki da take dashi wallahi saina tona Mata asiri don ubanta"


Sosai Ade ke kallon Lahab Yana mamakin soyayar dake tsakanin su da Yan uwan sa yace"kaga nifa yanzun shawaran da Zan baka d'aya ne karka tona Mata asiri a bayyyane baka da hujja in dai baka iyya Kama barawo ba shi saiya Kama ka Mami nada gaskiya gwara kayi shurun kawai"wallahi bazanyi shuru ba"Lahab yace,ok in bazakayi shuru ba toh kasani indai zaka Hana auren ka Hana a zahiran ce ba a nuni ba kasa Anwar ya ganta da kansa"sosai Lahab ya zagu yace toh ta Yaya kenan"Baki Ade ya bude zaiyi magana saiga Kira ya shigo wayar mubeena dake aljuhun sa zaro wayar yayi Yana kallon screen in waya.



Mubeena mikewa tayi tayi summit na paper ta da wuri tana Allah Allah Kar Rukayya itama ta Mike tana mikawa da Sauri gudu gudu ta fita a class in rataye da jakan ta bayan hall Inda ba mutane sosai ta nufa don ta tabbatar in taje cafe Ruky zata iyya ganinta itakuma yanzun batason wani alaka ya sake shiga tsakanin su da juna tafison tayi rayuwarta Kamar da Kamar batasan Ruky a duniya ba Zama tayi akan kututturen itace dake gindin bishiyar leam dake wajen jakan ta ta bude tasa hannu zata dau wayarta wayam kake ji bataga waya ba hankalin tane ya tashi ta shiga dube dube tana zaro material nata dake cikin jakan dan dakatawa tayi tana wani nazari in dai bata manta ba Kamar lokacin da suke tawowa Yana hannunta time to time tana duba lokaci sai Kuma kusan accident in da sukayi daga lokacin Kuma ta kasa tuna yaya wayar ma yayi "Allah dai ya Soni Kar a wani wajen na yatsar da wayar" da Sauri ta Mike ta Kama hanyar hall tana shiga lokacin an gama summit gabaki d'aya ajin sai dalibai daidaiku dake tsattsaye wasu a zaune Suna jiran next paper ganin ba Ruky a cikin hall in ya sata karasowa wajen da ta zauna tana dudduba wajen Koh Ta bar wayanta a wajen amma babu,lawiza dake zaune ita da wani Suna duba jotter ta matso wajen su tayi da sallama tare da rokon lawizan ta Ara Mata wayarta zata Kira wayarta,Mika Mata lawizan tayi da Sauri ta amsa ta loda number ta a ciki tare da karawa a kunne,daidai lokacin Ruky da tunda mubeena ta fita itama ta kammala da Sauri tabar ajin sosai

Please Login or Register in order to submit comment