Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Lahab,maza samarin kam tuni Suka matso kusa Suna basa hannu, sake fuskar sa yayi ya duka har kasa yana gaida mutanen dake wajen,sai Kuma sukace ya shigo falo sai ayi magana a ciki,binsu yayi Suka shiga ciki zazzaune suke akan kujera Lahab Kam Yana zaune a kasa sai Deyana data shigo hannun ta damke cikin na Meera tazo zata giftasu kwala Mata Kira Jaddu(kakan Nnenna ta wajen uba) yayi yana cewa Ina zata tazo ta zauna maganar daya shafeta ne suje Ina bayin Allah Nan Suka same ta"girgiza Kai kawai tayi tabar wajen.





Shigowa wani kyakkyawan balarabe yayi fari tas dashi sak Deyana(Abbas Ali)Zama yayi Lahab ya Kara gaidashi da murmushi ya amsa kana yace Hassan Koh"ba mamaki Lahab ya amsa don yasan yanayin aikin sa shiyasa mutane ke yawan sanin sa"Masha Allah yace kana ya nuna Lahab wa Yan falon a hankali yace"wannann shine mahaifin Abulkhari da Meera"da Al'ajabi jama'ar falon Suka Soma mamaki Suna cewa daman dan wasan kwallon nageria da suke gani a TV kullum shine mahaifin su Abulkhari Ashe ba abanza Meera keson sa ba,sun Kuma nemi dalilin kin fada musu da ba'a Yi ba sai yanzun Suka sani, Kuma sunsha mamakin ganin dan 31 dauke da yara Yan 13 year's,ana tsaka da maida magana saiga wani babban mutum a kalla zaikai 40 hannun sa rike dana wani yaro fari kyakkyawa Kamar dai Meera sun shigo daga ganin su hankalin su ba'a kwance yake ba dukan su biyu.





Yauwa Usman kaga Meera Kam an ganta Allah ya had'ata da mahaifin ta,dam dam haka Usman yaji zancen Nan,shikam Abulkhari da Sauri ya matso kusa da tsohon Yana tambayar sa Ina mahaifin nasu,nuna Masa Lahab dake sunkuye yayi Baiyi wata wata ba yazo ya rungume sa Yana cewa laii Abien mu Ashe ba tshoho bane .





Bayan an natsu Adewale ya maida musu yanda akai suka hadu,anan dai Jaddu yace su Lahab suyi hakuri gaskiya zancen auren sa da Deyana bamai daurewa bane don yanzun Yana bukatar jikansa a kusa dashi bazai iya barinta daga Nan har nageria ba tun tana yarinya batasan menene dadin iyaye ba bazai iya saketa sakaka ba, mahaifan Deyana(Nnenna)Basu so haka ba don su harga Allah Sunsan yarsu nason mijinta amma ka'ida ne a danginsu sai abinda babba ya yanke, kasa hakuri mamar Nnenna taso ta nausar da jaddu amman yace a Kira ita Deyana da kanta, shigowa falon tayi kanta a kasa ta zauna tambayar ta akai Nan tace itakam duk abinda suka yanke shi takeso daman kin raba auren da tayi Ada tayine don ta cika Masa ALKAWARIN data d'auka don haka duk abinda ya yanke yanzun daidai ne.






Adewale yasha mamakin chanjawar Nnenna zuwa Deyana duk da abubuwa da dama sun chanja shekaru sunja amma dai yayi mamakin Ina ta samu sabbin iyaye har Suna ikirarin diyarsu bazata koma naija ba sun manta irin wahalar da Lahab yasha da ita,Koh sun manta Nnenna Yar nageria ce kasa hakuri yayi ya tambaye su ta Ina Nnenna ta Zama diyar su"?nan jaddu ya Soma basa labari cewa shekaru 30 da wani Abu daya wuce sun kasance Suna da arziki sai dai rikicin akida sun musu katuntun sun hanasu sakar wata Rana kawai aka tashi da rikicin akida a Libya fada ya barke bana Wasa ba sun matukar tsorata,Daman a lokacin bakaken fata na shigowa wajen su Neman aiki na aikatau,cikin masu aikin gidan sune da mijinta ta damkawa Deyana tun tana jinjira ta Kuma Basu kudi tace su bar kasar da yarinyar ta don ita a lokacin ta zaci zata mutu ne kasancewar tunda aka Soma rikicin Koh asibiti ba'a budewa akallah an kashe family su kusan mutum ishirin, gashi tafara ciwo Wanda gabaki dayan mu Muka tsorata da ciwon nata tamkar bazata tashi ba Saida ta bada yarinyar kafun daga baya Muka sani na shiga tashin hankali bana Wasa ba na Kuma Yi takaicin daga karshe na fawwalawa Allah kome.




Kutsam Allah ya bayyana mana ita a London bayan ta hadu da Najib(Wanda Suka hadu lokacin Yan fashi Suka taresu a gombe har ta dau jaririn sa Yan uwansa na gombe suka Bata 500k)Ashe Dan uwan tane Kuma cikin yardan ubangiji yazo ganin gida Muka hadu da ita Allah ma yasomu Wai ashe da Bata sallah Saida ta zauna dasu ta fara"jinjina lamarin Allah Adewale yayi sai Kuma ya Soma zancen rashin dacewan raba auren amma Suka kekace babu Inda zata koma kawai in zai dawo ya zauna a Libya Bismillah in Kuma ba haka ba Saida ya sallame ta ita shi Kuma Lahab yace bazai bar kasansu saboda mace ba,harga Allah mahaifiyar Nnenna bataso hakan ba Amma batace kome ba,mikewa Lahab yayi a hankali ya musu sallama tare da juyawa zai bar falon a hankali Nazeefi(abulkhari)yace"Dady Zan bika"wani irin shaukine ya cika Lahab a karon farko yaji wani irin shauki da iyaye keji in aka kirasu da suna iyaye.





Da Sauri ya yafito yaron Aiko da saurin sa ya mike ya Kama hannun uban nasa,da mamaki nazeefa(Meera)tace Abul tafiya zakayi ka barni ne? Ai kema jiya tafiyar kikayi Kika barni "ai da Sauri itama tace nima Zan Bika dady gabaki d'aya yaran Suka Kama hannun uban nasu,kuka Deyana(Nnenna) ta sake don a zatonsa tafiya nageria zaiyi dasu,ganin haka Yasa jaddu(kakanta)tambayar Lahab shin Ina zashi da yaran Lahab yaso ya juya yace Masa ai yayan sane Koh bangon duniya zashi dasu Babu Mai bashi permission,Amma darajan tsohon yasa sa kasa magana sai Ade ne yace masa aiki sukazo insha Allah kafun su koma zai dawo dasu zancen makarantan su Kuma karsu damu zai iya kaisu daga nan,.






**********************
Suna komawa gida ba karamin masifa Lahab ya sake ba Yana cewa wallahi in Nnenna ta manta waye Lahab sai ya tuna Mana zai Mata bakin aiki harshi za'a nuna wa iko zasuga iko don wallahi daukar yaran sa yayi,washe gari yakaisu aka musu visa makarantan ma basa zuwa haka zai wuni dasu Suna Hira suna basa labari anan dai yaji labarin Yan gidan su Labiba Wai Usman cousin nata ne kuma son ummin su yake amma ummi Bata sonsa yasha zuga jaddu akan a raba auren a kotu kawai ta daina Zama ita ba aurareyya ba ita ba sakakiya ba karshe Saida ya gwabe Meera kafun ta dakata da labaran ta,yace baison gulma maganar ta Isa don kwata kwata nazeefi ya fita natsuwa.






ran sa ya Kara baci hakan yasa sa kuduri aniyar barin kasar da yaran wallahi sai dai ita ta nemosa,haka Koh akayi ya kammala kome nashi Kuma washe gari da safe zasu bar Libya,da misalin karfe uku na yamma kwance suke a falo Suna Hira Ade ke Basu labarin abotar su da Lahab tun yaranta hotonan su dake cikin system in Lahab ya d'auko Yana ta nuna musu, yaran sosai suke Jin dadi da marmarin zuwa NAGERIA don ya sanar dasu gobe insha Allah zasu tashi.





Knocking na door in akayi,bada izinin shiga Ade yayi Mai gadi ne yace wata ce tazo tace a Mata sallama da Lahab, balance Lahab yayi don haka kawai jikinsa ya basa itane kallon sa Ade yayi ganin baida niyar magana gamai gadi a tsaye yasa sa cewa a ce Mata ta shigo,da sallama ta bude kofar mikewa yaran sukayi suna Mata oyoyo bude hannayen ta tayi ta rungume su da karfi sannan Suka Karasa ta zaune akan kujera a hankali ta ce"Ina wuni Adewale"?dariya ya sake kana yace"nifa yanzun Sunana Nabeel kawai mijinki ke kirana da Adewale Dan Allah kekam ki Bari da Nabeel Kinga yaran Nan na samu Suna kirana uncle Nabeel karkusa su koma cemin uncle Ade Mana"kai Ade Naga dai sunan Kane bana wani ba don haka nikam dashi Zan kiraka"Kuma ai bakai bane Nabeel Ina Nabeel inne"?





ganin Ade Bai Bata amsa ba,Mikewa Lahab yayi yabar falon dakin sa ya shiga ya kwanta Bai fi 20 minutes ba yaji an turo kofar daga Ido yayi ya kalleta sai Kuma ya maida idon ya rufe Yana girgiza kafarsa,karasowa tayi a hankali ta nemi bakin gadon ta zauna"Ina wuni"?kin amsawa yayi batayi fushi ba ta sake cewa"daman nazone na dau yaran mu koma gida Naga yau kusan 1 week basa zuwa makaranta malaman su na complain zasu Fara jarabawa"Nan ma Bai Bata amsa ba haurawa tayi Kan gadon a hankali tasa hannu ta taba kafarsa"maganafa nake maka' wani irin mikewa yayi da karfi ya fizgota da iya karfinsa ya makata akan gadon kana yayi gaggawa hayewa kanta zaro Ido tayi tana kallon sa sai Kuma ta kalli kofa da Sauri bai koyi gizauba illah fuskar ta dayake bi da kallo kawai cikin Al'ajabi tace"in yaran Nan Suka Shigo fa"?





Sai suga abinda uwarsu da ubansu suke"shine abinda yace mata Yana sauke numfashi cikin haushi"harni Zaki nuna wa iyaka ta watoh kinyi kudi kinyi ilimi har kina da bakin da Zaki ce in sake ki Koh?gaji Mai dangi"watoh Ada saboda rashin kowa yasa kike biyayyar Dole badon kina sona ba Koh?toh wallahi zanyi maganin ki in an hanani ke ai baza'a hanani yarana ba"?hawaye ne ya taru a idanunta kana tasa hannu a hankali ta shafa fuskar sa cikin sanyi Hali tace"ka Kara girma sosai dear"?





Make hannun nata yayi sannan a hankali ya kwantar da kansa a wuyan ta wani irin unexpected kiss ya sake Mata Wanda ya sata mikewa da Sauri shima ya maidata kwancen yayi ya danne,Yana cewa wallahi bakin ce na sakeki ba watoh ke aure Usman Koh"?





da Sauri ta girgiza kanta tana maida numfashi a hankali saboda yanayin kwanciyar nasu ba karamin cinnata yake ba"kawai dai Ni yanzun kaga a NAGERIA Ni Mai laifi ce duk da a yanzun Ina da karfin gwuwar tinkarar shariya,Kuma dangin ka basa kauna ta tunda har mahaifiyar ka tayi ikirarin kasheni ai babu wani zancen cigaba da zaman aure da Zan sake a kasarku,tunda Alhamdulilah yanzun na samo asalina".





Duk wannan maganar meya hadashi da auren mu wannan alakar dake tsakanina dake Zaki tsaya akai bawai akan zancen dangina da kasata ba in Kuma akace duka sun chanja ra'ayi a kanki fa"gaskiya Ni yanzun na maka girma Kuma ma Taya Zan iya cewa Wai Kaine mijina wa mutane gaskiya da kunya wallah.........a hankali ya danna bakinsa a nata a hankali ya Soma kissing nata irin kiss Nan ne da ake cewa ci da zuciya watoh cikin zafin Rai da haushi zame bakinsa yayi a nata kana ya tashi akan nata,ganin haka da Kuma yanayin sa yasata rarrafawa da Sauri zata d'auka akan gadon kafafunta farere tass ya Kama tun daga bakin gado ya jata fiiiiiiiii har tsakar gadon jikinsa na rawa ransa sosai ya baci ya Soma magana yana cewa"ki kace kin fi karfin zaman aure Dani koh..........................











*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*



dan Allah kayi hakuri karka min haka"tace cikin tashin hankali ganin ya danne kafafunta da nasa kafafun ya Soma Kwabe riga"kaga dan Allah ka maida riganta karfa ka manya yaran mu na falo"zare wandon jikinsa yayi Kara tayi a hanakli ta fizgo jikinta a nasa tana kokarin sauka akan gadon kamota yayi da karfi Yana cire Mata kayan jikinta had'asa ta somayi da Allah amma Saida ya zare dogon rigan jikinta a hankali"yana bin hips nata da kallo ganin yanda kwata kwata yanzun ta sauya Kamar ba Nnenna ba ta Kara cika ta Zama babban mace"






"dan Allah ka bari wallahi ban shirya d'aukan ciki a gidan mu ba dan Allah dai"?au aikin fi karfina ne yanzun Koh kikace"ah ah dan Allah kayi hakuri ka bari banaso dan Allah dai kokawa Suka Fara a hankali ta koma ta kwanta tana hawaye ganin da gaske yake son kasancewa da ita,yayin da ita Kuma bata shirya karbar sa a wannan lokacin ba,sallama da ake kwad'awa a bakin kofar shiya dakatar da Lahab daga abinda yake,a hanakli ya mike zaune gabaki d'aya jikinsa Babu kuzari mirginawa yayi ya kwanta agefen ta.




Itakam murna fal cikinta mikewa tayi kayanta ta sanya da Sauri ta bude kofar dakin,nazeefa ce Wai Uncle Nabeel(Ade) yace Lahab yazo su tafi masallaci ana Kiran mangari ba"nufar hanya tayi tare da cewa su mike suzo su tafi kin binta sukayi kai da fata,karshe dai haka ta tafi Babu Shirin don Bata son Lahab ya fito ya sameta mikewa Ade yayi ganin ana kokarin tada sallah Lahab bai fitoh ba har lokacin gashi nazeefi yayi Alwala shi kawai suke jira dakin ya shiga anan ya gansa kwance har lokacin bai mike ba girgiza Kai kawai Ade yayi tun lokacin da yaga kwayar idanun sa sunyi mugun rinewa gashi gadon kaca-kaca shiyasa shi juyawa kawai yabar dakin.






Washe gari Lahab Suka nufi NAGERIA Koh sanar dasu Abbu basuyi Suna zuwa ba Rabon Lahab da NAGERIA an Jima sai yau lokacin da suka iso ba karamin mamaki familyn Lahab Suka Sha ba gashi gidan ya Zama daga Abbu sai Addayiya data tsofa sosai sai Mamu don ummu tana fita a gidan yari Abbu ya sallame ta, yara kuma kaf nasu sunyi aure hatta zulai auta itama ta Jima da auren ta.





dangin Lahab sunyi matukar farin ciki na ganin walwalan Lahab ta dawo kowa na dangin su Saida Suka zo kallon yaran Nan kowa yazo, saiya Yaba da tarbiyar yaran ga saurin Shiga Rai,Mami lokacin da tazo kuka ta sake don yaran sun tuno Mata da d'anta Rahab Allah sarki da shima yanzun yayi aure kila.





Lahab ya mayar musu da yanda akai harma dakin auren su da dangin Nnenna basayi Kuma suka nuna akan bazata dawo dakin taba,Abbu da kansa shida Mami sukaje har Libya amma jaddu yace Ina zance dai d'aya ne Nnenna bazata dawo nageria ba an buga an buga Abu yaki haka Suka hakura Suka dawo,shikam Lahab makaranta yasa y'ay'an sa suka cigaba da karatun su shima ya zauna a kasarsa abinsa Yana kula da yaran sa Babu abinda Suka nema Suka rasa.





Esha(cousin na Nnenna) Adewale ya Fara soyayya da ita yarinyar bazata wuce 17 ba ba karamin mamaki Lahab yasha ba ganin tsawon shekarun Nan Adewale baya zance wata mace Saida ya hadu da eshat Ashe shikam tuni sun Soma tsula soyayyar su lokacin daya tare sa da zancen mubeena budar bakin Ade yace yanzun mubeena tafi karfin sa rai bace Lahab yake cewa shida yake da Mata age mate nasa meya samesa, Kuma a haka Yana son suci gaba da rayuwa tare Bai taba Jin sha'awar wata ba.





Amsar da Ade ya bashi shine aisu sunci kurucciyar su shifa? Kuma da ace shima mubeena ta nuna Masa so da har gobe bazai kalli wata ba Ada yayi hakuri Amma Banda yanzun Kam, murmushin takaici kawai Lahab yayi don yasan har gobe mubeena na zuciyar abokin nasu don yayi bincike sosai ya gano Adewale yaci gaba da biya Mata makaranta harta kammala karatun ta har matakin digree aikin da take ma shiya nema Mata kuma duk wata sai ya tura Mata da sakon Kaya Koh wani Abu,amma da sunan Lahab yake amfani Wai Lahab ke Mata sako, don tuni ya gane Wanda mubeena keso shiyasa shima ya sanyayawa zuciyar sa hakuri ya Zama Yana kyautata Matane saboda Allah da Kuma abotar su.





Lahab yadau yaransa har wajen mubeena ya kaisu Allah sarki so ranan sosai tayi Kuka bama kamar daya ce Mata zai aureta don ta matukar basa tausayi gabaki d'aya unguwan su Babu macen data kaita girma a budurwan sai ita kadai,gaskiya so bala'i ne wani lokacin.







Auren Adewale da eshan ya tashi wannan Karo jaddu yace bazai bada eshan ga tubabbe ba Amma eshan tayi fito na fito da jaddu iyayen ta Kuma suka Goya Mata baya don jaddu kakan tane ta wajen uwa Nnenna Kuma ta wajen ubane,Yan uwan Ade Cristian ne shiyasa su Abbu suka tsaya Masa a zancen auren nasa sai dai duk abinda ake anayi ne da izinin iyayen sa papa girma yazo Kuma Ade ba karamin kudi yake dashi ba don yanzun gidan su ma abin kallo ne ga kauyen su daya koma yana d'aukan yara Yana zuwa Yana sasu a makaranta wasu boarding Koh day Suna karatu sosai,wa'inda suka kammala karatu ba aiki duk Yana nema musu aikin yi hakan yasa kiyayyar da suke Masa a dalilin musuluntar sa tuni ya washe a idanun su daman akace kyautatawa tana rage kiyayya.







Zacen auren Ade daya tashi Saida mubeena ta kwanta ciwo sosai ta gane kuranta a rayuwar tayi kuka tayi kuka daga karshe tafawwalawa Allah kome Kamar yanda ta Saba,don zaman gidan bappa Ado ba dadi ne dashi ba sai d'an Karen bakin ciki, yanzun Addu'a take Allah ya Bata Miji komai ruwane(garuwa) tayi aure ta huta itama ta samu zuriyar da zasu debe Mata kewa,Allah sarki mazan jiya su Nabeel(real)an Zama tarihi da farida rayuwa kenan duk abinda ka shuka shi zaka girbe Inka biyewa zuciya zata kaika ta baroka kayi Wasa da Daman ka na rayuwa.








***************************
An daura auren eshan da Ade Ade sai rawan Kai yake an aure balarabiya lokacin da akazo za'a d'auki auren eshan mutanen NAGERIA guda bakwai ne Suka je maza uku sai Mata biyu d'aya goggon sa dayar kuma goggon su Lahab sai ango da abokan sa uku cikin su harda Lahab sai su Abbu da Suka karbi auren,a lokacin jaddu yace Deyana ta tashi tabi mijinta Allah ya Basu zaman lafiya Kuma yaji dadin biyayya data masa ubangiji ya Basu zaman lafiya Kai ranan nan Deyana tayi kuka Kam bana Wasa ba kafun Suka rabu da iyayen ta daman yaranta tuni suna nageria Lahab baki har kunne aka karkato naija.







Hadadden dinner aka had'a a washe garin ranan da Suka dawo da daddare Ade yaso Lahab ya shiga cikin dinner ayi dasu amma Lahab yace dashi da matar sa sun girma, Addayiya ma daker tabar Nnenna (Deyana) taje dinner don tace baza'a tare ba sai Lahab yamata Sabon gida gidajen sa na naija sun tsufa Nnenna tafi karfin su Kuma ya Mata lefe.







Zazzaune ake akan kujerun ga jama'a Kamar me an cika Hall in dam Adewale ne Akan floor da Amaryar sa Esha kyakkayawar yarinya ajin farko, saidai fa Bata Kai Deyanan muba,Lahab na zaune a Inda aka tanadar wa Baki shida matar sa sai yayan su dake zaune kusa dashi daman table ne Mai daukar mutane hudu abokan su tunna secondary school duk sun hallara harda na London duka,hall innen yayi shuru sakamakon sanarwa da MC (Dj) yayi ayi shuru akwai wani abin mamaki da za'a nuna musu,yaye labulen dake jikin gidan hall in akayi.





Farin kyelle ne ya bayyana sai Kuma abinda mutane bazasu zata ba hoton Lahab ne tsaye da Rahab sunyi ne a cikin gida su a wancan shekarun,Nan wa'inda Basu San Lahab tagwaye bane suka Soma tambaye wannan Kam shine dan uwan sa kenan,hoton ne ya bace aka nunu na Lahab sanye da uniform sai Nnenna da itama tana sanye da uniform a jikinta tsaye suke a unguwan su Basu ma San anyi hoton ba,sai Kuma hoton Lahab da Adewale da Nabeel na ainahi,sai Kuma hoto na gaba shine Randa Suka kammala secondary school sukayi hotuna dukan su da mate nasu harma da coper dasu Lahab Suka duka.




Abin Al'ajabi sai ganin vedio dauren auren Lahab akayi sai Kuma aka Kara nuna hoton Nnenna da Lahab again lokacin da take da ciki,kana aka sake Nuno hoton su dayaransu harda Ade a cikin hoton,sosai mutane ke jinjina soyayyar dake tsakanin su, Ada sai gulmar su ake tunda Suka zauna Amma tunda aka ga hoton sai jikin mutane yayi sanyi hotona sosai aka yita nuna wa, mubeena da tayi karfin Hali tare da ma kanta ALKAWARIN insha Allah zata zo bikin Ade Koh don d'awainiya da yayi da ita a boye don taje ta samu Mai kawo Mata kudi da sauran abubuwa tsawon shekarun nan tace ya fad'a Mata tsakani da Allah wake d'awainiya da itan Nan yace Mata Adewale ne.






Hawaye ne ya cika idanunta a hankali ta Mike tana kuka ta fita a Hall in Babu Wanda ya hankalta da fitar ta sai Lahab shima baisan tana hall in ba Saida tazo fita ya ganta,a hankali ya mike tsaye tare da cewa Nnenna Yana zuwa fita yayi a hall in Yana bin bayanta ganinta yayi zaune ta kifa kanta tana kuka,sosai jikin sa yayi sanyi gabaki d'aya ya rasa meyasa yanzun ya damu da lamarin mubeena sosai ya damu akan lamarinta ace mace har 33 Babu aure gaskiya abin a tausaya Mata ne,tsaye yake akanta yafi minti goma amma mubeena bata sani ba a hankali yasa hannu yad'au purse nata data Yar a kasa daga Ido tayi Suka had'a Ido murmushi yayi kana yace inkin gama kukan ki goge hawayen naki ya Isa haka mubeena kiyi hakuri da rayuwa aduk yanda tazo Miki nasan tabbas kina Jin ciwo a ranki amma hakuri ake kome zai wuce.






Dole nayi kuka Lahab Dole ne rayuwar da nake ciki a yanzun ban taba tsammanin Koh hasashen Zan taba shige ta ba,Babu duka Babu zagi sanan Ina da albashina Mai tsoka sai dai rashin aure yamin cikas ka duba fa ka gani Ranan kawai Na fito gida saiga Yar Ahmad (14year's)Wai hartana nuna Ni Wai ga budurwar baban ta har yanzun batayi aure ba sai Kuma ta sake kuka da karfi don harga Allah yanzun so take tayi aure Amma tunda aka ganoo abinda Nabeel ya aikata ta nemi manema ta rasa.





tashi muje na kaiki gida"girgiza kanta tayi a hankali tana cewa"no basai ka kaini ba nida kaina Zan koma ka koma wajen iyalinka"girgiza Mata Kai yayi a hankali yasa hannu ya rike nata ya Soma magana"mubeena ki manta da kome daya wuce a baya mu fuskance gaba Koh da Inna Koh Babu Inna mun riga mun Zama Yan uwa pls feel free with me kinji big Aunty"?




A hankali ta gyada Kai tana share hawayen idanunta sake Mata hannu yayi kana yace suje ya maidata 9:00 na dare yayi tuntuni, tafiya suke Lahab Kamar ance ya d'aga Ido kawai ya had'a Ido da Nnenna dake tsaye a bakin hall in tana Masa wani irin kallo da Bai taba ganin ta dashi ba haka kawai yaji mugun shakkanta ya shigesa,amma ya basar bude motar sa yayi mubeena ta shiga kana shima ya Shiga yaja Suka bar wajen,har unguwan su ya kaita lokacin da zasu rabu kudi kusan 100k ya Bata Amma mubeena taki karba yayi yayi taki.






Lahab na dawowa yaga wani kallon harara da Ade ke aika Masa,kallon yaran nasa yayi yace su taso su tafi Nnenna kin tashi tayi har Saida nazeefi ya Kara Mata magana kafun ta tashi Albarkacin yaron nasu kada ya fiskanci akwai wani abu,shikad'an sa yake Hira da y'ay'an sa itakam bakinta kus Kama wata hanyar taga yayi hakan yasa ta kalle sa Amma batayi magana ba,gidane Mai kyau Kuma kerarre bude kofar sukayi dukan su Suka shiga haurawa upstairs yayi da yaran Koh wannen su ya nuna Masa dakin kwanan sa Babu abinda Babu a dakin nasu Kama daga man shafawa zuwa sutura duk ya tanadar musu.





A ranan bacci ma Lahab basuyi tare da Nnenna ba saboda masifar data yitayi Masa akan mubeena harda cewa in son mubeena yake bazai burgeta ba sai taga ya aureta abu dai baiyi dadi ba ranan.






***************
Washe gari da safe Addayiya ta turo ma yaran kayayyakin su don ta fahimci Lahab Kam ya Kai matar sa dakin tane sun koma gidan su,Yan uwan Nnenna da suka zo aure dukan su sunzo sunga gidan ta Kuma gaskiya sun yaba wa Lahab,Mami tazo tayi ta Neman gafarar Nnenna amma Nnenna tace Mata Babu kome yanzun kome ya wuce ai Suma da laifin su a wancan lokacin,vedion auren Ade da aka had'a dana Lahab Sosai mutane suka ringa tofa Albarkacin bakin su.








Bayan aure bai Jima ba saiga Usman (cousin in Deyana)daga kasar su ya taso har NAGERIA gidan su Lahab yazo da hoton mubeena Wanda a cikin hotonan biki aka d'auka Bata ma sani ba tana zaune akan kujera ga hawaye cike a idanunta,yace fa shi duk duniya yaga matar aure ta tafi dashi,ai ba karamin dadi Deyana(Nnenna) taji ba Koh hankali ta zai kwanta saboda yanda Lahab ke shiga harkan mubeena abin na jaza musu rikici akanta.







Anyi bikin mubeena bukin da d'angi

Please Login or Register in order to submit comment