Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jima tsaye a kofar dakin nan Ina Jin duk abinda kuke cewa,tabbas naji dadi Kuma na amince da abinda Ahmad yace tabbas ya cika dan halak daya rabu da mubeena Nasha nuna Masa yarinyar Nan bata ra'ayinsa Amma ya nace kullm cemin yake Wai kunya takeji dason boko amma d'aga zaran ta jona gaba da secondary komai zai daidai,na nagode Allah daya fahimtar dashi ya ganewa idanunsa me za'ayi da macen da Bata sonka,maman Ahmad tace tana karasowa cikin dakin.


Mikewa mubeeena tayi ba tare da tayi magana ba ta fita a dakin da Sauri gudu gudu ta fitoh a clinic in ta tsaya a bakin titi har lokacin hijab nata na Kare a fuskarta Rabin fuskar kawai ake kallo,Ruky ganin mubeena ta fita yasa ta mikewa da Sauri ta nufi kofar itama duk Kiran da Ahmad ke Mata bata tsaya ba,da Sauri ta nufi mubeena da ta soma tafiya da kafa tana rurufe fuskar ta Wanda Koh shakka Ruky batayi kuka mubeena keyi.

dan gudu gudu tayi ganin mubeena ta Mata rata mubeeena dakata don Allah ki tsaya Ina kike tafiya ne haka kindai san d'aga Nan zuwa gidanku bazaiyu da kafa bakan Koh?

dan tsayawa mubeeena tayi tana sassaita fuskarta gudun Kar Ruky ta fahimci abinda take ji,mubeeena nasan yanda kike ji Sarai Koh baka son mutum muddin akace wani ya karbesa sai kaji wani iri mubeena Ina Mai baki shawara daki kyautatawa Mai sonki haka zalika ki sassaita Masa sai Wanda kike mutuwa a kansa Shima ya sassauta Miki,Ki dubi abinda Kika ma Adewale dazun Sam baki kyauta ba yaya zakiji randa kikaji Lahab yace bai sonki gaba da gaba toh haka Shima Adewale yake ji,bazan gaji da baki shawara ba ki koma ku sasanta da Ahmad.

Kallon ta mubeena tayi sannan tace,wani irin mu sasanta bayan kinajin abinda mahaifiyar sa tace sannan Shima yace kuje kawai Nina hakura Allah ya zabawa kowa rabon sa.

Me kike nufi mubeeena kina nufin kema kin janyewa Ahmad in kenan?

Kwarai Ruky na janye Allah yasa hakan shine Mafi Alkhari a gareni.

Shikenan mubeeena Amma Ni bazanyi gangancin da kikayi ba nayi Wasa da damata a baya Amma a wannan Karo ban shirya cigaba da zaman gida ba Kamar yanda nayi a baya karfa ki manta kaf kawayen mu sai aure suke mu ba yaran manya ba bare ace za'a somu don kudin iyayen mu don haka Ni naji na gani Zan amince wa Ahmad ya aure Ni don banga wani aibu a garesa ba.


Juyawa kawai mubeena tayi ta tsallake titi tabar Ruky a wajen tare keken dayazo wucewa tayi cikin sa'a kuwa ya tsaya ba tare da tayi magana ba ta shiga tare da cewa muje Mai keke, Ruky da Ido tabi keken har Suka mile,mubeeena Kam wani irin kuka ta sake a cikin Keken Mai ciwo tama rasa meke Mata dadi a duniya gabaki d'aya Wai Ina zata sa kanta ne taji sanyi tayi iyya boye son Lahab Abu ya gagara gashi tayi rashin masoyi na gari innalilahi wa'inna'ilahu raji'un Allah ka kawo mini mafita.

Subhanallah Wai baiwar Allah lafiya haka kike ta rusa kuka a cikin Keke in ma mutuwa aka Miki kiyi hakuri kullunafsin za'ikatul maut,shine abinda Mai keke ya fada Mata don shi gani yake wani nata ne ya mutu take kuka shiyasa lokacin daya sauke tama yace ta tafe ya yafe Mata kudin sauka tayi tasa hannu ta Kara Jan hulan hijab in ta rufe fuskarta sosai tana tafiya hawaye na zuba tana gogewa a hakan har ta shigo gidan Koh sallama babu Inna dake zaune tana tsinka zogale da mamaki take tambayar ta ganin daga shigowar ta tayi daki kawai babu sallama bare na dawo,ke mubeeena ince dai lafiya Kam Koh kin shigo fuska a kulle Wai harkun dawo makarantan ne duk da yau asabar bansan me kukaje d'auka ba?

Mikewa tayi da Sauri ganin mubeeena bata bata amsa ba tabi mubeenar cikin daki,samun ta tayi zaune ta Kwabe hijab in jikinta abinka da farin fata lokaci daya idanun ta da fuska sunyi jawur ganin Inna ya sata Kara fashewa da kuka,jikin Inna har bari yake ta matso kusa da mubeena,ke mubeena menene meke damunki?saurin rungumarta mubeena tayi tana wani irin marayan kuka ita Karan kanta Inna ta shiga damuwan tunda take bata taba ganin mubeena cikin wannan tashin hankalin ba don Koh rasuwar iyayen ta bata da wayo sosai,don Allah mubeena ki natsu nasan ke yarinya ce Mai zurfin ciki Ni na haife mahifinki Kuma Nina raine ki tun kina da shekara biyar a duniya mahaifanki Allah ya musu rasuwa keda dan uwanki duk a hannuna kuka tashi ban rareku da kome ba duk abinda na samu bana Fara sawa a bakina har sai Naga ku kunci meyasa meyasa mubeena Baki d'auke Ni a matsayin wance zakiyi shawara da ita ba wance Zaki fadawa damuwan ki kuyi Alhini tare tun kina yarinya Koh Abu na damunki baki fadamin sai dai Inna gane nayi kokarin magance Miki Amma bazaki fadamin da bakin kiba sai Kuma ta fashe da kuka Mai tsuma rai tana Zama a bakin gadon tasa bakin zaninta ta rufe fuskar tata.

da Sauri mubeena ta sake rungumar Inna cikin kuka take magana,kiyi hakuri inna bawai haka bane wallahi kaf duniyan Nan bani da Kamar ki na tabbatar Koh iyayena ne Suka dawo bazan musu son da nake Miki ba dake na Saba Ina boye Miki damuwa tane don gudun sakaki kema a damuwa.

in dai bakison sani a damuwa toh mubeena ki daina boye mini damuwar ki hakan na mini zafi gani nake Kamar akwai wani abinda nake Miki Wanda yasa kike gudun naji sirrin ki.

girgiza Kai mubeena tayi sai Kuma a hankali ta soma magana hawaye na bulbulowa,Inna Ahmad ya rabu dani s...sa...saboda.......sai Kuma ta kasa karasawa saboda kuka daya ci karfinta,mikewa Inna tayi cikin bacin rai tace,kaii badai akan wannan yaro kike zubda hawaye haka ba tukunna ma maiya hadaku daman duk son da yake gwada Miki na shekaru duk karyane munafukin Allah toh wallahi babu Wanda ya Isa ya yaudari jikata ya kwana lafiya tana karasa maganar ta gyara daurin zaninta hade da daukar hijab a jikin kofa tasa tana kokarin fita a dakin sai surutai take,shagon sa zanje saina ci Masa mutunci sai yasan ya taba kayyu yau Innan don ubansa har gun uwarsa sai naje na shata Mata layi Ni za'a rainawa wayo in gama tattali Ina jiran biki zaizo yace ya fasa.


Inna ki dakata don Allah,Amma Ina Inna bata saurare mubeena ba sai takalmin ta data saka tsabar Sauri ma hagu ta sama dama dama ta sawa hagu ta nufi kofar gida.


Inna ki dakata nace Miki Koh kunje shagon sa bazaki samesa ba haka zalika gidan su saboda yana asibiti,dakatawa Inna tayi ta juya tana kallon mubeena,wani asibitine kenan har can Zan bisa Koh Yana danjan mutuwa ne saina nuna Masa bacin Raina harni zai cutarwa Jika,ta juya abinta zata fita.


Inna ki dawo Nina ce bana sonsa bana sonsa ne don bashi bane a zuciya.............




***************
Alhaji sulaiman da Mami da yaranta ne zaune akan dinning dayake yau weekend ne babu makaranta gabaki dayan su abinci suke ci Kuma d'aga yanayin cin kadai zaka gane Suna Jin dadin sa,sabanin Mami dake ta sai jujjuya shukali take abin duniya ya dameta gabaki d'aya jin abincin take Kamar mad'aci,Mami Mami Mami mahraz ya kirata har baki uku Amma shuru Bata ma San yanayi ba.

Mufeeda dake kusa da itane tasa hannu tadan tabata,Mami ya mahraz nata Miki magana baki amsa Masa ba?dan firgigit tayi cikin yake ta kalli mahraz , na'am mahraz Meka ce?

Mami meke damunki ne Koh Baki da lafiya ne?

Ah ah mahraz lafiyata klau Meka gani?

Uhmm kawai yace bai Kara magana ba don Shima yanzun ya Fara wayo sosai yasan me ake Kira tunanin shiyasa daya fahimci bata son tambayar ya Barta kawai badon ya yarda ba,Alhaji sulaiman Kam girgiza Kai kawai yayi tare da kallon mamin,mamin mahraz tunda yau weekend ne sai kije gidan su lahab in ki barmin yaran a gida.

Dan dago Kai tayi ta kallesa watoh Koh bata fada Masa ba ya fahimci matsalar Lahab ne,toh shikenan dadyn mahraz,tsagal wasila tayi tace,nidai gaskiya Mami Zan biki kinji?

kallon ta Mami tayi Jin mahraz da mufeeda ma sunce Suma zasu,Kinga bafa jimawa zanyi ba Kai Kuma mahraz da girmanka zaka wani cewa zaka bini toh Yusuf ma a gida Zan barsa,Aiko Yusuf dake Kan cinyar wasila Kamar yasan me mamin ta fada Kwabe fuska yayi sai Kuma ya sake kuka da karfi Yana kokarin sauka d'aga Kan kafar wasila Yana mikawa Mami hannu,gabaki dayan su Saida sukayi dariya hannu tasa ta dau Yusuf in ta daura akan kafarta Aiko take yayi shuru abinsa Costan sa da aka dama Masa a cup ta janyo daga gaban wasila tana Iba tana basa.


Suna gama cin abincin mufeeda ta goya Yusuf ganin yayi bacci a bayanta yasa Mami ta tashi ta shirya fitowa tayi hannunta d'auke da car key's,toh Ni Zan wuce sai na dawo tace tana kallon Alhaji dake zaune rike da jarida ga yaransa a kusa dashi,toh a dawo lafiya Mami yaran suka had'a baki,yauwa Yan Albarka sannan Kai mahraz ka karbi Yusuf a bayan mufeeda ka kwantar dashi a tsakar gado kasa Masa filo a gaba da bayan sa Karya fadi?

toh Mami saikin dawo,Allah yasa tace tana bude kofar falon ta fitoh compound na gidan parking space ta wuce ta bude motar ta ta shiga tare da maida murfin ta rufe ta tada motar.

da Sauri gate man ya walgale Mata gate Yana Mata a sauka lafiya.



*****************
a gaskiya sadeeq kayi hakuri maganar kawo laifen Nan a ajesa a gefe yanzun hankalin gidan mu ba'a kwance yake ba bare ayi wata maganar lefe,umaima dake jingine da motar sadeeq a cikin compound na gidan su tace fuskar ta babu walwala.

Sadeeq dake zaune a gaban mota kofa a bude fitowa yayi gabaki d'aya a motar Yana kallon umaima,Wai umaima Mike faruwa ne na kasa gane kanki tun fa jiya na shigo garin ku na kiraki a waya akan ina zuwa da daddare Zan Miki Albishir na musamman saboda maganan Nan na taso daga baushi nazo gombe amma har zakice Wai a sauke maganan kawo laife ranan Monday bangane me kike nufi ba?


Unmmmmm sadeeq kenan bazaka gane bane shiyasa amma nidai na riga na gama magana.

Wai tsaya umaima bangane Kin gama magana ba akan me zakice Kar a kawo Kuma baki gayamin gamsheshen amsa da Zan Kai gidan mu nace ba, meke faruwa ne?Koh dai son nawa ne Kika daina d'aga jiya zuwa yau?


dan murmushi tayi tana kallon sa watoh shi tanan ma tunanin sa ya sako Masa Kenan,sadeeq dan uwan mahaifina yau kwana biyu bai kwana a gida ba sannan ba'asan Inda ya shigaba taya hankalin mu zai kwanta har a karbi kayan auren ka?

Subhanallah wanene a cikin su ya batan?ya tambaye ta don yasan bazai wuce small uncle's nata ba.


Wallahi hubby Lahab ne ya bata ta basa amsa tana kallon gate Jin horn na mota Mai gani ne ya taso ya bude kofar.


ton Allah ya bayyana sa,sannan Kayan aure na Koh na auren ki ai inta nine a yafe kayan.

Shuru tayi bata basa amsa ba tana kallon Mami data shigo da motar ta gidan parking tayi a kusa dasu ta fitoh a motar tsungunawa sadeeq yayi har kasa ya Soma gaidata.

Amsa wa Mami tayi umaima ma ta gaidata ta amsa sama Sama ta nufi flat nasu don hankalin ta ba'a kwance yake ba da sallama ta bude kofar ta shiga Addayiya ce zaune a kasan cafet sai rusa kuka take yayinda muzammil dasu Abbu keta bata hakuri amma Ina sai Kara volume take Jin sallamar Mami yasa ta share hawayanta tare da amsa sallamar Kamar yanda sauran Yan falon Suka amsa shigowa Mami tayi ta nemi waje ta zauna gaggausawa sukayi anan ake ta jajanta lamarin.

toh Ni anawa shawarar uncle Mai zai Hana akai case Nan hannun Yan sanda babu amfanin muyi shuru da sunan gudun magana shifa mutum ba'a iyya masa kome aka Masa baza'a gujewa maganar sa ba,shareef dake zaune Akan 1 sita yace Yana kallon uncle.

da Sauri Mami ma tace eh wannan gaskiya ne nima nayi tunanin haka Kar Muna tunanin wuta a makera mu ganta a masaka Muna tunanin Lahab gudu yayi Alhalin Kuma b'ata yayi Koh wani abin ne ya samesa don Ni wallahi jikina ya bani ba lafiya bane jiya Koh bacci ma banyi ba.

Wani dogon tsaki mamu tayi cikin makirci ta soma magana,Haba Amina wani irin magana akai ga Yan sanda waye baisan halin Lahab ba aje asa hukuma a ciki karshe a kamasa a logi(hotel) Koh club ya kunyata mu abarshi dai ai duniya ce tafi gabaruwa jimawa Kuma duk Wanda yabar gida da kafarsa zai dawo.

Wani irin bacin rai ne ya ziyarci Mami Jin munanan kalamai da take fadawa gudan jikinta,keee Haleema dakata banason shshigi ai basai kinyi haka Zaki nunawa duniya baki kauna ta da y'ay'ana ba wannan Kam kowa ya Jima da sani,Ina d'aga Miki kafane Albarkacin yayan ki amma wallahi wannan karon in Kika Kara shiga harkata wallahi Zan nuna Miki shuru shuru ba tsoro bane.

Itama mamu mikewa tayi Koh kunyar su Anwar batayi ba,keee Amina inkin fasa baki cika yar halas ba sannan menene abin ki a tsotsonki banda kwadayi dason abin duniya in ba kwadayi ba meya shigo dake tsakar rana cikin ahli Kika Haifa musu masif........tas tas kake ji Mami ta wanke fuskar Mami da wasu mahaukatan Mari guda biyu daidai lokacin umaima ta shigo falon mikewa Anwar yayi jikinsa har rawa yake ya nuna Mami da yatsa,mahaifiyata Kika Mar..............






***************
Nnenna na fita a bakin asbitin ta samu wani shagon Kaya shiga ciki tayi ta zabi riga da wando kala uku na Lahab sai itama ta dauko wando kala biyu da riga biyu sai vest ta saya Masa da boxes ita Kam bata samu vest na Mata ba towel ma duk ta saya mikawa Mai shagon ATM nasa tayi yasa a POS ya cire kudin sa wani shagon dake gefe ta shiga tasai maclen brush da soso harda sabulu da turare abinci Kam tama rasa wanne zata sai Masa wajen Mai shagon bakin asibitin taje ya had'a Mata shayi a flask Kofi biyu sai kwai daya soya Mata, tasai bread sai doya soyayye data musu takeAway,komawa cikin asibitin tayi hannunta Niki Niki da Kaya ta tura kofar dakin ta shiga kwance yake Kuma Sarai yaji shigowar ta amma bai wani motsa ba Yana kwance a yanda tabarsa,aje kayayyakin hannunta tayi tare da daukar laidan suturar da ta sai musu ta matsa bakin gadon"Lahab ga kayan na sai maka ka duba Koh ya maka"?



Kala baice Mata ba sai mikewa da yayi daga zaunen da yake sandal Nata yasa a kafarsa ganin haka yasa ta saurin dauko Sabon silifas Inda ta sayo ta aje a gaban sa,cire sandal in yayi yasa silifas in,mikewa yayi a hankali ga hannu an daure harda igiya aka daura Masa a wuya zuwa hannu saboda hannun kada ya ringa Lilo sauka yayi a gadon ya finciko laidan hannun nata da hannunsa Mai lafiyar wando ya d'auka da vest ya Kama hanyar toilet in da Sauri Nnenna ta kallesa sai Kuma tace"Amma dai ba wanka zakayi bako"?


Har lokacin baiyi Mata magana ba sai kokarin bude kofar da yake da hannun sa na hagu Yana jinta Sarai yaki tamkawa,"Lahab kasan ba'a wanka in aka samu rauni irin wannan Koh"?

Bauuuu kakeji ya maida kofar toilet in da karfi ya rufe shuru kawai Nnenna tayi takoma ta zauna sai Kuma ta Mike da Sauri Jin Karan faduwar a toilet tare da ihun mutumin nata.........






Page 57&58



da gudu ta shiga bandakin zaune ta gansa akan tiles kayan daya shigo dasu a watse a kasa tsayawa kawai Nnenna tayi tana kallon Lahab dan sauke ajiyar zuciya tayi ganin babu abinda ya samu hannun nasa dan ita tama tsorata ta d'auka Koh hannun ya samu matsala ne"menene ya faru kake ihu"?

dan dagowa yayi ya watsa Mata wani kallo cikin masifa-masifa yace"oho ban sani ba yanzun a yanda Kika gannin Nan Har kina tambayar meya faru? Koh ma meyafaru aikece sila".

Shuru kawai tayi bata kulasa ba har lokacin tana tsaye"bazaki kamani na tashi bane"?da mamaki take kallon sa Jin abinda ya fada Wai ta kamasa matsowa tayi a hankali ta duka a gabansa ta sanya gwuwuwinta a tiles in hannunta ta zura a hakarkarin sa a hankali,dan zabura yayi don wallahi sai yaji Kamar jakulkule ta Masa"ya haka malama Zaki wani ciccibeni Kamar Zaki d'aga dan yaye Kama min hannu zakiyi"Lahab yace cikin d'an rawa rawan murya don dan tabasa da tayi yanajin wani iri a tattare dashi.

Nnenna bata kulasa ba unexpectedly ta dagosa daga zaunen da karfin Allah,zaro Ido yayi"keee Wai Naman jaki kike cine Koh me mutum sai karfi Kamar shariya Kamar ba mace ba haba "

tura Lahab in tayi Kamar xai Fadi sai Kuma tasa hannu ta rikosa tare da pushing nasa ya zauna akan toilet sit,ba musu Shima Lahab in baiyi kokarin tashi ba sai hannun sa na hagu daya sa Yana kokarin cire vest in jikin sa amma ina ya kasa saboda hannun sa dole sai dai a yaga vest in"Wai tsayuwar me kike ne da bazaki taimake Ni ba Koh jira kike na Kwabe kayan nayi wanka a gaban ki"?Lahab ya karasa maganar yana hararanta.

Hhhh dariya Nnenna ta sake a karon farko shima yaga dariyar ta sosai dariyar ta Mata kyau ga wasu cute white teeth nata da suka bayyana,girgiza Kai tayi cikin dariya ta fizgo vest in jikinsa har sai da ya barke ihu lahab ya sake Yana ce Mata"Wai menene haka ke Baki da hankali ne ki natsu Mana"Amma Ina zare Masa yagegen vest in tayi Lahab Kam da hannu daya yake ta Kare jikinsa Yana daka Mata tsaka ganin tasa hannu ta Kwabe botul in wandon jikinsa tana kokarin zaresa d'aga waist nasa,jikinsa har wani irin rawa yake yasa hannun sa Mai lafiyar ya fizgota har Saida ta fado a kansa"wash yace Yana Kara sa hannu ya mannata a jikinsa sosai Yana wani irin sauke a jiyar zuciya akai akai.

Jinta a jikin namiji a karon farko a rayuwar ta mutumin da take sakewa dashi fiye da mahaifinta da ace wanine ya rungumetan Nan da sai wani ikon Allah badai Shiba,dan muskutawa tayi tana son tashi d'aga jikin sa Jin yanda gemun dake fuskarsa ke taba Mata wuya gata dama-dama akan kirjinsa Mai d'auke da kwantancen gashi baki duk da bamai yawa bane sosai amma ga dukkan alamu shekaru yake jira su dan Karu Shima ya Karu saboda kallo daya Zama ma Lahab kasan irin mutanen Nan ne masu halittan gashi da yawa a jiki"so kike kimin tsirara da gaske"?Lahab ya tambaye ta Yana kwantar da kansa a wuyanta.

Kokarin turesa take amma Ina ta kasa saboda da karfi sosai ya riketa,cusa hannunsa yayi ta wajen cikinta ya zagayo dashi bayan ta tare da rike waist nasa,ihu ta sake tana cewa ya sake ta ya saketa amma Lahab gam ya riketa sosai Yana dad'a mannata a jikinsa.


ganin da gaske bazai saketan ba yasata dan sake jikinta kadan a nasa tare da dago kanta ta kalli fuskar sa hannu ta d'aga a hankali ta shafa fuskar tasa da Sauri ya lumshe idanunsa Wanda tun dazon yake kanta,dan bude Ido yayi Yana kallonta itama kallon nasa take"yunwa nakeji"Lahab yace Yana Kara bin fuskarta da kallo.

Uhmmm kawai tayi ta lumshe idanunta kafun ta basa amsa"nida Kai wa aka rike?

"Ke kike rikeni"ya Kara amsa Mata Yana dan shashafa Mata waist,hannunta tasa akan nasa tana turewa"ka sakeni Mana sai kayi wankan kaci abinci kaji"?

Dan muskutawa yayi yace"so kike na sakeki watoh Kinga Banda hannu ki kwabemin Kaya Koh"?

"ah ah Wasa nake maka mezaisa na Kwabe maka Kaya a gabana Kuma ai saina makance"


Jin abinda tace yasa sa sa hakorin sa yadan ciji kafadarta da dan karfi"Jesus ka kasheni"tare da ture hannunsa ta sauka a jikinsa tana shashafa wajen tsungunawa tayi ta kwashe kayan daya shigo dashi bandakin suka zube a kasa ajewa tayi a bandakin cikin boket da Sauri ta bude kofar ta fita shikam da Ido ya bita Yana dan murmushi,bata jima ba sai gata ta dawo da wani Sabon wando da rigan harda towel ajewa tayi ta ciki ruwan dumi a boket in ta aje Masa a gabansa tare da daukar karamin towel tasa a cikin ruwan hade da bude sabulu ta aje Shima juyawa tayi zata bar wajen,hannunsa yasa da Sauri ya rike nata,tsayawa tayi bata juyo ta kallesa ba ganin hakan yasa sa Kwabe fuska"kizo ki Kama min wando ki cire wallahi kafar baya fita sai da laida"(kaji iskanci dazun da za'a cire mekace😏)

Juyawa tayi ta kalli kafar wandon ta sake kallon fuskarsa"Wai menene haka kike wani kallona toh ma waya raunanani ne ai kece don haka ki kula dani malama"kala batace ba Shima mikewa yayi ya zare wandon a kugunsa ya saukar kasa rumtsa Ido tayi da karfi ganin boxes nasa a waje ga cinyoyin sa masu tsoka gasu bakikkirin ga gashi a kwance akai"kijamin kafar wandon Mana hai"?

tsungunawa tayi ta kamo kafar Lahab in ta daura akan cinyarta kallon yatsotsin tayi gasu dogaye tsirara dasu ga kafar Mai tudu da nama Kamar kafar mata hannu tasa ta Kama wandon tana ja ja take da karfi amma Ina wandon pencil Kam yaki fita sam"Wai menene amfanin sayan wando Alhalin Kai Mai kudin baka huta ba ace ka sai wahala da kudin ka Wai da sunan gayu"Nnenna tace tana Jan wandon da karfin gaske Wanda har lahab dake zaune ya biyo wandonsa Suka zubu a kasa daga shi har Mai cire masan"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un wayyo hannuna yace kamar irin ya bugen Nan cikin tashin hankali ta Mike tana dubasa"sannu sannu Lahab Inga hannu Jesus hannu Mai ciwo.

sassake jikinsa Lahab yayi yana wani irin narkewa Kamar maijin jiki,da Sauri Nnenna ta Mike ta nufi kofar"bara na Kira likita suzo su dubaka hannunka ya fame"kizo ki gyaramin jikina bazan iyya ba sai mu fita a bandakin kafun kikirasu"dakatawa tayi Jin abinda Lahab yace da Sauri ta dawo ta taimaka Masa ya tashi ya zauna bucket in ta jawo sai Kuma ta fita da Sauri ta dauko laida Baki da aka sa Mata su soson wankan a ciki ta dawo bandakin ta tsunguna a gaban Lahab ta sanyawa kafarsa a laidan kafun wandon ya fita aje wandon tayi a gefe ta tsoma hannunta a bucket In ta tsamo towel dake ciki ta matse sosai kafun ta sanya towel in a gadon bayan sa tana goga Masa lumshe Ido Lahab yayi,a sannu sannu tayi ta goge Masa jiki sai dai bata goge kafa ba iyya sama kawai ta wanke, hannu tasa ta lakace sabulu tana goga Masa a fuska a hankali gudun Kar ruwa ya taba Masa hannu har lokacin idanunsa a rufe Yana ji tana tattaba Masa gashin fuska wanke Masa fuskar tayi tasa towel ta goge Masa fuskar sosai take kallon fuskar NASA gashin gemunsa ya jike tare da sajensa ya wani irin kwantawa gwanin sha'awa.

Aje towel in tayi"ka karasa sauran da kanka Zan jira ka a waje kayi Sauri abincin na sanyi"ta fita a ban dakin ta barsa.


kallon abin wankan Lahab yayi sai Kuma ya cire gajeren wandon sa ya karasa wankan da kansa towel ya daura ya fitoh a bandakin,mikewa Nnenna tayi ta bude laidan kayan ta Mike Masa karba yayi ya koma bandakin ya sanya wando dogo na roba vest Kam bazai Shiga ba saboda yanayin hannunsa fitowa yayi ya aje rigan dake hannunsa ya zauna a bakin gado"meyasa baka saka rigan ba Koh vest"?sai naje na Kira Dr ya duba hannun tunda ka fame.


"bazan sa ba a hakan kikeso nasa kayan ne Koh Yaya nidai kiban abinci naci"mikewa Nnenna tayi ta dau cup guda daya ta Iba Masa tea in tasa spoon ta Mika masa,"make kafada yayi tare da kallon ta Yana Wani shugwabe fuska"nifa bazan iyya Sha da kaina ba Kinga dai hannun damana ne"?Kika tsagamin.

Zama tayi a kusa dashi a bakin gadon ta aje cup ta dau takeAway in kwai dana doya soyayye da Miya duk ta kawo ta aje masa tayi sosai sannan ta dau cup in tasa Masa a Baki kurba yayi a hankali Yana kallon fuskarta itakam Koh kallon sa batayi ba ta yago wainar kwai in

Please Login or Register in order to submit comment