Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shareef da Hashim Suka turasu abroad karatu gabaki d'aya bama sun sanar da mahaifin nasu ba Saida yaran Suka tafi,sosai Alhassan yaji ba dadi Amma baice kome ba, gidan ya kasance yarane kananu kadai a cikin sa masu wayon duka basa Nan.





Amina tayi sanyi kad'an Kuma ta Soma kula Alhassan harma suyi Hira hakan ya samu mafari ne da takardu Koh jaridu dayake kawo Mata Yana karanta Mana tare da koya Mata yanda ake wasu abubuwan a boko shikenan ta Soma sanyi haka zai sayo littatafai in yana gida su zauna Yana karanta Mata Yana fassara masa,ganin yanda take kaunar karatu yasa sa shigar da itama makarantan secondary akaita a daukota, a sannu sannu soyayyar sulaiman tayi sanyi aranta bawai son alhassan ta Fara ba ah ah tanajin farin ciki yanzun in tana tare dashi a hankali hankali zaman su ya sauya daga tsana zuwa kulawa.





Bayan wasu watan Ni saiga ciki kusam ya fito daga wajen Amina abinda ya zamo abin mamaki da Al'ajabi da kunya a wajen ahlin gidan Inka cire uban gayyan dayafi kowa murna murna yake Kamar Bai taba samun Y'ay'a a duniya ba sai Nan Nan yake da Amina kome take so jiki na Bari yake Mata,itakam Amina kunya sosai yake damunta haka zata kunshe ciki musamman lokacin da ya fito tayita boye boye batason Koh fita tsakar gidan.





Lokacin da cikin ya girma hatta tafiya Amina bata iyyawa sosai duk tsanar da Addayiya da sauran yan Gidan Suke Mata Saida Suka dawo tausaya Mata Amma Banda Mamu dake ta radawa mutane cikin jikin Amina bana surkinta bane,saurayinta ke binta makaranta daga Nan su wuce iskancin su shine tayi ciki ana cewa Wai na alhassan ne,magana fa ya fito fili Wanda yasa alhassan mugun fusata tare da jawa Umar dogon layi akan ya Shiga tsakanin matar sa da Amina maganar datayi girma Saida Umar ya sake halima,ganin yaka yasa jafar tattara matarsa da yaransa Suka koma cotes na ma'aikatan gonnati Suka bar gidan.






daker da sudin goshi mamu ta dawo dakin ta,cikin Amina ya girma girma bana Wasa b,sosai alhassan yake kula da ita da abinda ke cikin ta baya duba tsufansa Koh girma yake tattalan matar sa,lokacin da cikin Amina ya shiga wata tara,Alhassan ya Soma ciwon da ba'a gane kansa ba,da fari ciwon ciki ya Fara anje asibiti sukayi gwaje gwaje aka basa magana Koh sati baiyi ba sai Kuma tashi ya gaggara haka aka ciccibesa aka Kai asibitin likitoti sukace su basuga ciwo ba,hankalin family Nan ya tashi bana Wasa ba dawo dashi gida sukayi ganin yanda yake ramewa.





Alhassan ya rame ya Kade gashi a kwance sai abinda aka Masa magana ma ya daina saidai kawai aga yana zabura Yana Shure Shure hawaye Nabin kumatun sa,abun fa ya d'agawa Amina hankali ganin tunda ya kwanta sai aka hanata shiga Koh dakin da yake,mamu ta Soma zuga Addayiya Wai Koh Amina ce da saurayin ta Suka Masa asiri,Nan fa Addayiya ta tada hankalin ta aka Fara Neman maganin hausa,Koh wani malami aka kawo daga yace iska sai yace asiri aka Masa,Nan danan magana ya Fara nisa Amina ce ta Masa aSiri ai Fulani daji me(shiyasa akeson Koh baka son mutum ka boye kiyayyar a idanun mutane inko ka bayyana toh Koh Abune ya samu mutumin in badai Yana da tauyidi ba kana cikin matsala).




Yau Amina ta tashi da nakuda sosai take cikin halin ciwo,tun safe tana daki tana fama da jikinta don tunda Alhaji ya kwanta ciwo babu Wanda yake bi ta kanta abinci ma kuku zata kawo Mata ta aje Mata ta fita duke take a bakin gado sai jujjuya kanta take tana damke da bakin gadon sai salati take tana kuka.




Muzammil dasu Anwar da labarin ciwon Alhassan ya riskesu duk da Muzammil na fushi da abinda mahaifin nasa ya Masa Amma halinda akace yake ciki ya tada Masa da hankali bayan isarsune suka tsinci zancen ai Amina ne ta Masa asiri abinka da maza su Basu wani yarda da zancen ba,amma Mata Kan sosai suke zuzuta abin,cikin wannan halin da Amina take ciki badawiyya(matar Hussain)ta shiga falonta da sallama don ita Sam yau hankalinta Bai kwanta da shurun Amina tun safe Koh tsakar gida Bata fita ba.



tana shigowa falon taga kulan abinci a aje budewa tayi taga Koh ci batayi ba sallama ta Soma Mata Amma shuru ba amsa bkin kofar taje ta tsaya tana Kiran Amina,Nishi dataji Yana tashi shiya mugun d'aga Mata hankali,haihuwane gadan gadan janta tayi sukayi bayan gida wahala iyya wahala Amina tajishi har Allah ya dauketa lafiya ta haife yaranta tagwaye kyawawa masu Kama da mahaifinsu sak hatta skin nasu Basu dau hasken taba.



Bayan badawiyya ta Gama kimtsa yaran kwantar dasu tayi ta taimakawa Amina tayi wanka bayan fita da tayi taje part nata ta daura ruwan zafi tazo ta kimtsa ta da yaranta,Allahu Akbar lokacin da badawiyya ta sanar da haihuwar Amina duk da Muzammil baya kaunar Koh ganin Mai Kama da Amina amma jini yafi ruwa kauri,Saida ya taka kafarsa har dakinta ya dau jariran sosai jikin familyn Alhassan yayi sanyi ganin yaranda Amina ta Haifa like father like son,anan take muzammil ya d'au yaran ya Kai har dakin mahaifin su,da hannu ya nunawa muzammil ya nuna Masa yaran, facing nasa yayi ya nuna Masa yaran a take hawaye ya cika Masa Ido,tare da Mika hannu daga kwance dayake ya karbi yaran ya kwantar dasu duka a kirjinsa,a hankali ya bude bakin sa ya Soma magana"muzammil kiramin Amina"da mugun mamaki muzammil ya mike Yana cewa"Abbi magana kake kaji sauki"?gyada Masa Kai Alhassan yayi da gudu muzammil ya fita Kiran Amina cikin gaggawa duk da Bata da karfin jiki Kuma hutu take bukata amma hakan bai hanata gaggawar mikewa zuwa Kiran mijinta ba.





Tunda ta shigo dakin ta fashe da kuka ganin yanda Alhassan ya koma in baka Masa kyakkyawan sani ba bazaka ganesa ba,daga tsaye da take yasa hannu ya rike nata tare da jawota kadan ta zauna a bakin gadon har lokacin yaransa na jikinsa sai bacci suke yatsan su a baki"Amina na gode da wannan kyautar da Allah ya Mana ke Kuma Kika Haifa mini, Amina Koh a yau na mutu Banda asara tunda har Kika haifamin yara a tsotsonki,Ina sonki Amina Allah ya Miki albarka ga yara Nan na musu huduba da Sunan Hassan da Hussain Kamar yanda nake nida dan uwana"Kuka ta fashe dashi tana rufe Baki sai Kuma ta zamo bakin gado ta Soma rukon sa gafaran abinda ta Masa, murmushi kawai yayi yace"Niya dace na nemi yafiyar ki Amina na cutar dake na aureki na dole badon ranki naso ba Baki tabamin wani Abu na bacin Rai na kwanta dashi ba ba tare da na yafe Miki ba Amina ki yafe min..........Bata Bari ya karasa ba ta rufe Masa Baki da hannu tana hawaye tace"babu abinda kamin bare ka nemi yafiyata Alhaji Allah ya baka lafiya"Ameen ya amsa Mata Yana lumshe idanunsa dake cike da hawaye.




Addayiya ne ta shigo dakin tare da Muzammil dasu Umar daman sumayya(goggon katsina) ma na gidan,karasowa sukayi Jin muzammil yace muzu Alhassan na magana Aiko gashi sun ganewa idanunsu Zama sukayi Suka kewaye sa saiga Hussain ya Shiga dakin shida matarsa Hawa Kan gadon yayi ya rike hannu dan uwan sa cikin tsananin tausayin sa,suke Masa sannu hannun dan uwansa ya Kara damkewa a nasa,a hankali alhussan yasa hannu ya d'aga yaran akan kirjinsa shima ya rikesu a hannun sa,gyara kwanciyar sa Al'hassan yayi ya Soma magana Kamar haka"Umar ya Kira sunan babban dansa da Sauri Umar ya matso kusa dashi hawaye na cika Masa Ido,nuna Masa jariran yayi yace"Umar Koh bayan Raina zanyi Alfahari dakai mundin karike min y'ay'ana ka Basu tarbiya ka kularmin dasu Kamar yanda kake kula da yaranka,gasunan Amana na bar maka"kuka Umar ya fashe dashi Yana cewa mahaifinsa bazai mutu ba insha Allah zai tashi da kansa zai kula da yaransa.




"Ah ah Umar banajin haka a jikina muzammil jafar inaso kumin alkawarin Koh babu Ni banason ku Ware yaran Nan a cikin ku Koh ku nuna masu banbanci, Alhussan ga Umar da kannen sa na barmaka ragamar kula dasu a hannunka ka zame musu uba tamkar kaika haifesu duk abinda kaga sunyi ba daidai ba ka sawatar musu,gabaki dayan ku Allah ya musu albarka duk abinda kuka min Wanda na sani da Wanda ban sani ba duk na yafe muku duniya da lahira yayana nima kuskuren dana muku kuyi hakuri..............Bai karasa ba sumayya tace"babu abinda ka Mana Abbi insha Allah babu abinda zai sameka, Addayiya Kam kuka take lokacin da taji mijinta na cewa ya yafe Mata duniya da lahira itama ta yafesa,sosai Alhassan ya karya musu da zuciya kuka Kam shi suke Alhussan kasa hakuri yayi har Saida ya zubada kwalla karban yaran Alhassan yayi daga hannu Hussain ya kwantar akan kirjinsa Suma yaran Koh kuka basuyi ba Suna bacci,shima baccine ya daukesa Yana kankame da yaran,ganin haka yasasu Fara fita dakin d'aya bayan d'aya Kama Amina badawiyya da sumayya sukayi Suka fitar da ita a dakin aka Kira likita har gida tazo ta dubata tare da daura Mata ruwa.








da misalin karfe 1 na rana Addayiya ce ta leko a Karo na uku tun baccin Alhaji da yaran Nan Bai farka ba har yanzun,Hassan(Lahab)ya farka sai kuka yake yasata shigowa hannu tasa a hankali zata dau yaron tana mamakin wani irin nauyin baccine ya d'auke mijinta yaro na sanyara kuka amma baiko motsa ba bayan Kuma tasan sa da yawan ji Koh bacci yake mutum ya shigo dakin sai ya farka, janye hassan(Lahab)daga jikinsa tayi sai taga hannun dayasa ya rungume yaron yayi baya ya sake Yana Lilo a Bakin gado waro Ido tayi jikinta na bari ta Soma maimaita kalmar innalilahi wa'inna'ilahu raji'un sai Kuma tasa hannu ta dau Hussain (Rahab) shima ta kwantar dasu a gefen gadon Aiko take ya farka suka Soma kuka su duka biyun a tare da Sauri tasa yatsanta biyu a bulin hancin Alhassan (mahaifinsu) sai Kuma ta sulale a kasa ta sake wani marayan kuka.



*********************
Allahi Akbar rayuwa kenan yaudai Alhaji Alhassan Muhammad dogo Mai naira ya zamo tarihi,Allah daya hallice abinsa yau ya dau kayansaAlhassan an kaisa gidan sa na gaske,mutuwar Nan tayi mugun dukan Amina ashe haka rayuwa take Koh baka kaunar mutum Randa aka waye gari babu shi sai kayi alhini bare ita dake kyautata masa sosai ta Shiga wani irin Hali na atausaya Mata,dole tasa inno zuwa akan zata tafi da ita kauye Amma Umar ya Hana yace ta zauna a dakin ta tayi wankan jego,Aiko dole tasa inno zama a gidan tana kula da 'yarta.



Amina ta Zama abin tausayi sosai tayi sanyi bana Wasa ba tayi nadamar abubuwan da tayi Masa a rayuwa,Allah sarki duk irin kiyayyar da aka nuna Mata a gidan Albarkacin y'ay'anta ta samu sassauci sosai suke nuna kaunar yaran nata bana Wasa ba,kullum matar Alhussan haka zatazo ta daukesu su wuni a part nata no-no kawai ke dawo dasu wajen uwar su.




Tunda Alhassan ya rasu shikenan lafiya tazamo sai a hankali a wajen dan uwan NASA sosai ya Soma ciwace ciwace na ba gaira babu dalili yaje asibiti likitoti sun gargadesa akan damuwar da yasawa ransa ya rage,Amina ta kammala jego cikin koshin lafiya Amma babu zacen barin gidan Umar yaki inno ta koma kauyen su,tabarta anan,shekaran Yaran d'aya Allah Yama Alhussan rasuwa,rasuwar da ya tada ciwon mutuwar Alhassan mutuwar ya zamo musu sabo fil,don shikadai ya rage musu suke kallo a matsayin uba,Amma ya Suka iyya babu Wanda yake ja da hukuncin ubangiji.




Bayan rasuwar Alhassan, badawiyya ta Soma laulayi Ashe rabo ya shiga duk tsawon shekarun Nan Bata taba koh batan wata ba,sai bana dahar sun cire tsammani Allah ya Bata taso ace kafun mijinta yabar duniya yaji wannan albishir amma harya bar duniya baisan da cikin ba......................





🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*



Page 98&99

Bayan rasuwar badawiyya Amina taso ta cigaba da shayar da yarda badawiyya ta Haifa ta rasu ta barta aka maida Mata sunan mahaifiyarta ana kiranta da Amrat,Amma su Yan uwan badawiyya sunki sun nuna Akan zasu rike yarinyar a wajen su Tasha Madara,Kuma ba musu aka barmusu yarinyar a wajen su.



Bayan Amina ta yaye yaran ta anan tace zata koma gidan su don rasuwar mijinta shekara biyu kenan,gadon su Lahab a kallah yakai million biyar biyar Koh wannen su ga gidaje biyu biyu da Suka tashi dashi,da gonaki,Amina an Bata kasonta Saidai na yaranta ta barma Umar a hannun sa,ya sanya Dana muzammil Yana juyawa a cikin kasuwancin sa kudin na dad'a habbaka,ta dau tata gadon ta ta koma garin su, y'ay'anta ta barsu a hannun Addayiya ita tacigaba da kular Mata dasu.




Hassan da Hussain wa'inda aka lakabawa Lahab da Rahab har sunan su na ainahi ya buya don kowa kunyan Kiran yake sunan iyayene,yaran sun tashi kowa da halin sa, Lahab yarone Mai hakuri ga Wasa ga saurin yafiya ga rawan Kai dogon hakuri farfar da mutane babu ruwan sa talaka Koh Mai kudi shikam duk daya suke a gunsa Amma akwai rigima da taurin kai,sabanin Rahab daya tashi da sanyin Hali amma akwai zuciya ga riko ga saurin fusata gashi d'an ba ruwana ne sai yaga dama yake shiga harkan mutane in baiga dama Amma akwai yawan gaisuwa kam, Lahab akwai Wasa fara'a rawan Kai hakan yasa yafi Rahab yawan jama'a da wuya kaje unguwan kace Lahab wani baice yasan Saba.






Amina na komawa garinsu Daman sulaiman ya kammala makarantan sa babu aiki haka yaci gaba da kiwo a kauyen su,zuwa lokacin ya hakura da zancen Amina Amma Bai Kara zancen aure ba dawowar Amina ita ta sake tada Sabon sonta a ransa,Suka cigaba da soyayyarsu suka daura daga inda suka saya.




Iyayen sulaiman sunso Hana d'ansu auren Amina a matsayinta na bazawara Amma sulaiman ya nace tare da rantsewa in ba'a Bari ya aure Amina ba bazai taba aure ba,babu yanda iyayen Suka iya haka aka daura musu aure da Amina bayan d'aurin auren nasu ne Amina tadau million daya daga cikin gadonta ta baiwa yayanta muneeru akan ya cigada da kula da gidan su sauran biyun ta baiwa mijinta sulaiman tare da rokonsa su koma cikin gombe yanda zata ringa ganin y'ay'an ta akai akai Allah sarki akace Mai sonka dole yaso naka,baiyi musu ba Suka tattaro Suka dawo cikin gombe haya ya Kama musu,da kudinta data basa ya Kama shago Yana Saro Kaya daga kasar inyamurai Yama zubawa Yana sairuwa.





Cikin kankanin lokaci Sulaiman yayi kudi na ban mamaki sosai harziki ta bude Masa Harya biya Amina(Mami)kudinta ya tsaya da kafafunsa,Amina ta koma makaranta ta cigaba da karatun ta sannan duk sati tana zuwa taga yaranta inta tashi tafiya haka zasuyita kuka zasu bita,wata Rana ta daukesu suje su kwana wata Rana Kuma saidai ta barsu.



Amrat(badawiyya karama)ta taso a wajen dangin mahaifiyarta cikin rashin isheshen kula don yarinyar ta taso ba'a Mata kwaba Bata da kunya wani zuwa da jafar yayi dubata a can garin su badawiyya(Adamawa)yaje ya tarar da irin rashin kunyar da Amrat ke zubawa a ranan ya tattarota Suka dawo gombe da karfin Isa don dangin sunso hanawa ya nuna musu suke da iko da Amrat,daga lokacin rikon Amrat ya dawo hannun jafar wanda a lokacin sun bar cotes ya dau daya daga cikin gidajen da ya mallaka na mahaifinsu ya koma ciki.




Mami ta sake haihuwa bayan auren ta da sulaiman,sun samu Yaya hudu bayan su Lahab,Mahraz mufeeda wasila sai Yusuf karami da ake shayarwa yanzun,rayuwa tama wannan masoya dadi kudi iya kudi sulaiman nadashi tuni yabar harkan kasuwa ya tsunduma a gomnati ana damawa dashi sosai ya kera gida Mai kyau suka koma ciki,itama Amina yanzun ta Zama Hajiya Matan manya ga business nata da take a cikin gida kudi na shigowa hannunta sosai, d'aga inno da dan uwanta tayi ta dawo dasu cikin gombe gida ta sai musu Mai shegen kyau daman muneeru ya Jima da aure tun kafun a haifi su Lahab Yana d'a daya mustapha,da matarsa salamatu sosai zaman salamatu da inno ya kasance wani iri abun ba dadi Sam lokacin da Mami ta kawosu birni sai abin yafi lokacin da suke kauye sosai inno ta tisa salamatu a gaba ranan da salamatu ta kasa hakurin zagin da inno ke Mata ta shiga ramawa.



Shigowar muneeru kenan ya tsinkayi zagin da salamatu kema uwar sa Nan ransa ya baci yace saita bar Masa gida ganin irin kukan da dansu dayayi wayo yake Jin abinda baban sa yace,yasa muneeru hakura amma fa ya tattara yanasa-yanasa da salamatu da dansu sunbar gidan,karamin gida Mami ta basa kudi ya saya suka koma ciki,daman Yana kasuwan ci,suka cigaba da zaman rufen asiri da matarsa bakin su alekum.


Iyayen sulaiman sunki dawowa birni a ganinsu bazasu iya barin tushen suba gida ya kera musu a can rugansu Mai kyau Suka koma rayuwar birni a kauye.




*******************
Inda asalin abotar su Lahab ta samune ata dalilin unguwan su daya tun Suna yara Lahab nason zancen ball haka yake Sasa kullum sai ya zame jiki ya fita arean su Nabeel suje suyita buga ball kullum in sun hadu da Nabeel sun buga ball basa gamawa lafiya sai sunyi fada Wasa Wasa har abota ta Fara atsakanin su suyi fada su shirya Lahab kullum in sun gama Wasa sai yabi Nabeel gidan su suci abinci wata Rana Kuma Addar Nabeel mubeena ta koresa.




Kullum in ya fita haka Abbu zaiyita fada akan a daina barin sa Yana fita hakan bazai hana gobe ya fita ba,a hankali suka Fara wayewa da juna Nabeel nad'an zuwa gidan su Lahab shida addan sa,Amma haka Mamu zata koresu ta hanasu shigo musu gida Wai y'ay'an talakawa,makarantan su Nabeel government ne tana manne da private Inda Lahab ke ciki wata Rana da aka kawo Lahab makaranta aka saukesu a gate saiga Nabeel da addan sa zasu Shiga makarantan su Aiko abin nema ya samu tun daga Nan Lahab ya gane gudu a makarantan su yazo nasu nabeel,su Kuma malamai su korasa akan ya koma makarantan su daga ya fita Nabeel zai sulale ya bisa su shiga yawo unguwa unguwa,kutsam aka kawo Sabon dalibi dan yarobawa a ajin su Lahab Mai shegen taurin kai.





Lahab Adewale Nabeel abotar su taci gaba dakin karatunsu sai yawan yawo tun Suna primary 4,duk irin tsanar da baban Ade ke gwada musu da kyankyami da Mamu ke nuna musu baisa su sun rabu ba kullum abotar su Kara gaba dake,saidai Kuma duk yanda kake da mutum biyu Dole zakafi Jin d'aya sama da d'ayan toh hakan take a wajen su Lahab yafi kaunar Adewale haka yafi yin sirri dashi Abba baya nuna wa a gaban idon Nabeel dan Adewale ba karamin kauna yake ma Lahab ba.




An dawo labari......
*****************
Lahab Kam shuru yayi kansa a kasa har Mami ta gama zayyana musu labarin Family su,sai yanzun ya gane dalilin dayasa ta aure mahaifinsu Wanda kullum Addayiya da Mamu ke goran ta musu mamin su Yar kwadayine,Amma yawancin abinda ta fada yasassan su.




Mikewa yayi a hankali ya nufi kofar,kiransa Mami tayi ba musu ya juyo ya dawo kallonsa tayi tace,Lahab ka fita a harkan yaran Mamu Ina rabaka da yaran matan Nan,sannan ka dawo anjima zamu fita bafa Zan hakura da zancen Nan yasha a banzaba"?gyada Mata Kai kawai yayi yabar gidan Yana fita a kofar gidan ya durkusa ya Soma kuka bilhakki da gaskiya sosai yakejin wani irin tausayin mahaifin su don duk da ya rasu Suna da hotonsa dashi da baban Amrat(Alhussan),ashe haka babansa yasha wahala akan Mami sanan har Mami tanada bakin cewa Mamu Bata kaunar ta,duk irin abubuwan da ita ta Mata ai tun farko ita ta Fara jawo fadan.



Alhaji sulaiman daya sharo layin nasu ganin Lahab duke Yana kuka yasa sa parking na motarsa ya sauka a motar in,karasowa yayi kusa da Lahab yasa hannu ya dago kansa da yayi shabe shabe da hawaye a tunanin sa Rahab ne"haba Rahab ya zakazo ka zauna kamar an maka wani Abu Koh mamin taku tace maka wani Abune"?girgiza Masa Kai kawai Lahab yayi baice kome ba"toh Koh akan Hana maminku Kai Kara ne kake kuka"rasa abin cewa Lahab yayi kawai ya d'aga Masa Kai alamun eh"toh tashi muje ciki saimu fita da mamin naku,ba musu ya mike suka Shiga cikin gida har lokacin Rahab da Mami na falon.






Anje station Mami ta shigar da korafi akan abinda farida tace wa danta, police da kansu Suka shiga mota sai gidan su farida amma Kash da zuwan su Suka tarar da mutuwar mahaifiyarta ana zaman makoki sannan annemi farida an rasa,karshe dai dole Mami tayi hakuri da maganar bayan yarjejeniyar da aka aje duk wani mummunan Abu daya faru da d'anta alhakinsa na wuyan farida za'a neme mahaifinta.




Bayan bikin su Anwar gida ya koma Kamar yanda yake sai Kewan mutane biyu da ake musamman umaima,gwara Anwar ana gari d'aya,Hankalin Mamu ya kwanta yanzun babu kowa a gabanta sai Shareef shi Kuma ya girma,su Lahab sun Fara jarabawan second term,yau Friday ayaune sukayi last paper nasu na English Kuma kwalli daya sukayi.



Bayan sati daya da jarabawan yau Tuesday ayaune sukazo karban report card nasu gabaki dayan su SSS 3 Suka taru waje d'aya ana hotona photographer musamman aka Kira ana d'add'aukan hoto harda malamai masu manyan waya irin su Lahab duk sunata d'auka da nasu, coper da Lahab Suka Masa duka Yana staff room su Lahab Suka nufi staff in dukansu uku Suka duka suna basa hakuri don daga wannan Rana ba lallai bane a sake haduwa don wasu ba'a makarantan zasuyi paper ba, shima coper in zai koma garinsu ya gama service sukaran kansu ss3 daga wannan time babu tabbacin zasu dawo third time babu grante Don a lokacin zaman gida ake turasu suyi ace su jira register waec,sosai copern yaji dadin hakurin da Suka basa Harya zaro wayarsa ya fito waje yace suzo su tsaya, ya baiwa wani malami ya daukesu zai aje na tarihi, Lahab ma wayarsa ya bayar a d'auka dashi sosai sukayi hotona bana Wasa ba.







Zame jiki Lahab yayi a cikin yara ya nufi ajin su, Nnenna ne zaune waje d'aya kowa ka gani da abinda yake wasu na Wasa wasu na hotona wasu na karban number juna sabanin ita zaune babu wanda yace tazo suyi hoto Koh taje suyi,karasowa Inda take yayi yasa hannu ya Kama nata tare da mikar da ita ya Soma tafiya tana binsa,daman jakanta na bayan ta"Ina wayarki"shine tambayar da ya Mata Mika Masa wayar tayi"har Kan floor insu yajata Suka tsaya wayarsa da nata ya bayar yace a daukesu sosai aka shiga daukar su sannan wasu na shiga hoton anayi dasu kankace me duk yawancin class mate nasu duk sunyita daukar hoto da Nnenna da Lahab,su Adewale ma sunzo sun shiga hoton Nabeel nata mamakin alakar dake tsakanin Lahab da Nnenna duk da ya tambaye Lahab Lahab yace Masa friendship ne a tsakanin su amma baice kome ba saidai shikam Sam Bai kaunar Nnenna da Lahab kwata kwata amma tunda dai school life ne dole wata Rana zasu rabu.




Ba karamin bakin ciki ne ya kashe Jenifer ba,sai kusan 10 na safe aka had'a musu assembly abinda yayi mugun bawa mutane mamaki da Al'ajabi shine first position da Lahab ya d'auka a ajinsu sosai abin yayi ta saka jama'a a mamaki,sai Nnenna tazo na biyu wayyo Allah Ina wuta Jennifer ta jefata,daga Nan aka Shiga rarrabawa wa'inda suka dau position na daya zuwa na uku kyaututukan Lahab ya tashi da kyautar Award Wanda aka Mika Masa yayinda dalibai ke kashe sa da cameran wayansu,bayan an basa award na jajirtancen dan kwallo,don yafi kowa hazaka a makaranta in akace za'a buga ball da wasu school,aka had'a Masa da kyautar Keke sabuwa Mai kyau duk da yafi karfin Keke amma akace kyautar bajinta daban yake acikin sauran kyauta, Nnenna an bata kyautar laptop sabo,sauran ma aka babbasu nasu,Lahab a ranan murna Kam Baki har kunne,lokaci d'aya aka ringa post na hotonan su da sukayi da keken da aka basa,mikawa Nabeel yayi yace ya Kai Masa gidansu award in Kuma ya baiwa Rahab yakai Masa gida.




Tafe suke da Nnenna yau Koh abin Hawa Bai tare musu

Please Login or Register in order to submit comment