Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

b'anb'ara bakin get tun daga nesa yake kwalawa mai gadin get akan ya bude masa kofa.

Jin hakan yasa Rahab shima yiwa mai gadin warning akan karya bude kofar, Amma ina mai gadi kam duk ya rikice, driver dake tsaye yana jiran yan makaranta da ido ya bisu ganin yanda sukazo suka wucesa kamar walkiya da gudu lahab ya bankade kofar get in ya fice a tamanin.

Turus Rahab ya tsaya rai a bace yana maijin bakin cikin abinda lahab ya masa, gashi yasan tunda lahab yafita a gidan shikenan badai ya iyya kamasa ba.

Kamar zai fashe da kuka haka ya koma cikin gidan cikin bacin Rai,Abbu ne ya kallesa Rahab waton rashin hakuri koh? Rahab kiranka muke Amma ina zuciyarka ta kasa hakuri koh?ai da wannan zuciyar kullum lahab ke galaba akan ka.

Shuru yayi fuskar nan tayi kirim Kamar zaiyi aman wuta, Addayiya dake gefe har yanzun tana salati akan hayo mata kai da Lahab yayi tace, wallahi Allah ya isa tsakanina da uwar yaran nan ta cuceni data aure mini miji.

Cikim haushi RAHAB ya juya gareta,kinga wallahi kimin shuru Addayiya karki sake zagar mini uwa banaso wallahi bala'inku ya tsaya iyya kan Lahab ba mamata ba.

Baki suka sake gabaki d'ayan su suna kallonsa da mamaki, sau dubu lahab zai masa abu in aka zagesa sai kuma ya nuna bacin ransa.

Babu wanda ya sake magana sai tashi da sukayi daga kan daining Area in, shareef ne ya mikawa Rahab 10k, gashi uncle ka sai littafin?

Karba Rahab yayi yana sabar jakarsa ya fita a falon, su munira sukabi bayansa dayake duk school d'aya suke dasu lahab.

Motar school da Ake kaisu suka shiga, Rahab ya shiga gaba munira da zulai suka shiga baya, driver yaja suka bar gidan, shareef da Anwar mototin su suka hau, haka ma umaimah da dan uwanta duk suka wuce school.

Lahab kam da gudu ya fita a gidan haka bai tsaya ba saida ya dangana da karshen layinsu, kafun yaja birki yana numfashi, sai kuma ya sake dariya tunawa da yanda yanzun Zuciyar Rahab ke tafarfasa.

Boom yaci ya kama tafiyarsa kamar bashi ba tun daga nesa ya hango Adewale tsaye sanye yake da uniform, wando da riga, wandon pencil ya d'amesa sosai sai rigan uniform in koh botur bai rufe ba wuyansa sanye da sarkan cross mai sheki sai hannunsa dake sanye da abin hannu na maza.

Yana kallon Lahab daga nesa ya kama baki cikin tarin mamaki, jesus nashiga uku me zan gani haka Lahab ina kayan makarantar yake dan iska?duk cikin hausar sa dabai nuna ba ya tambaye lahab.

"Kallon banza lahab ya masa kai na fasa zuwa school in"

Wannan wani irin iskancine lahab kace mana jiya zaka school kasa yau na buga uniform zaka wanice baxaka ba?

"Eh bazani bane kawai yau in ma"

Amma baka da mutunci yanzun so kake nayita yawo da uniform ai danasan bazaka ba bazan saka ba.

"Basai ka koma ka cire ba"

Aikin banza momy na gida zakace na koma na cire uniform?

"Sorry ina Nabeel yake wai bai fito bane har yanzun, nifa na samo kudin jesen nan"

Kallonsa Adewale yayi, nima ai na fito dasu yace yana zaro kudi a Aljuhunsa ka gansu nan 10k ne cip.

"Kai anya ba satosu kayi ba daga magana jiya harka samo"

Kowa barawo ne irin ka, an gaya maka ni dady ne ya bani dana ce masa a school aka bukace kudin kaga kuma uniform na saka ga kekena ma, shiyasa ya yarda makaranta zani, yace yana nunawa lahab kekensa dake gefe a fake, kekene mai masifar kyau da tsada.

Murmushi kawai lahab yayi yace"aiko kudin Rahab na rarumo"

Toh kaikam Allah ya shiryeka?

"Ameen shige Ade muje mu dubo nabeel koh tsohowar nan ce ta tsayar dashi"

Kekensa Adewale ya hau Da sauri lahab ya rike bayan keken ganin Adawale na kokarin jan abinsa"wallahi Ade baka isa ba ka wuce a sama ka barni a kasa"

Turesa ade yayi yaja kekensa da karfi ya bule lahab da kura ya kara gaba.

Cikin jin haushi lahab yake bin kuran bayan keken ade har kofar gidan su Nabeel, irin gidan nan ne na block da block sai d'an karamin kofar falange ga ade a tsaye a kofar gidan yana jiran isowar Lahab.

Koh kallon ade baiyi ba ya tura kofar gidan, da sauri Adewale yabi bayansa.

Da sallama suka shigo tsakar gidan, amsa musu mubeena dake zaune a tsakar gidan tana wanke wanke, sanye take da xani na Atamfa riga daban zani daban, sai hulan bacci data soka gashin kanta a ciki, amma hakan bai hana ganin gashinta dake kwance a gaba goshinta ba.

Sai kakar Nabeel inna dake zaune a taburma tana tsefe kanta, Kallon Su lahab inna tayi sai kuma Adewale, dake gaidata Amsawa tayi ciki ciki ganin lahab bai sanya uniform ba, tasan daker ne yau su leka makarata.

Jin yanda ta wani Amsa ma Ade gaisuwarsa yasa lahab kin gaidata, d'akin ya nufa Adewale na binsa a baya.

Ku dawo nan karku kuskura ku shiga d'akin nan yan iskan yara fitinannu Addan Nabeel dake wanke wanke tace.

Koh kulata lahab baiyi ba ya wuce d'akin, yayin da Ade ya tsaya kamar yanda Mubeena tace, jingina yayi da jikin ginin dake gefen wajen wanke wanken nata.

Mikewa Inna tayi ta sabe bokatin wankan ta ta shiga ban dakin, batace musu uffan ba.

Ganin ba kowa yasa Adewale fisgo Mubeena dake tsaye tana kokarin d'aukar kwandon kwanukan ta, had'ata da bango yayi ya rufa mata jiki da nasa, ya kasance tana jikin bango yana gabanta, yasa hannu akan ginin dake bayanta.

Da sauri ta kallesa sai kuma cikin bacin rai tasa hannu ta ture sa amma koh gezau baiyi ba, yana mai duban cikin kwayar idanunta, a hankali ya bude baki yace, Akan ki na koyi sallama a gidan koma waye in zan shiga mundin musulmine,Amma na fahimci ke baki ganewa koh?kin matsamin.

Cikin jin haushi tace karka kuskura banason wasan banza don Allah sakeni?ni sa'arkace nifa Aunty kuce?

Hhh dariyanya sake tare da cemata, auntin nabeel da lahab dai, badai niba kuma shekara nawa kika bawa nabeel in? Amma sai son girma.

Hannunta tasa ta make masa kumatu da mari amma irin mara zafin nan.

Da sauri ya riko hannayen ta cikin zafin nama ya murd'a mata su.

Ihu tasa da karfi

Kamar daga sama sukaji ance mezan ganin nan haka

Da sauri ya saketa yana kallon mai maganar................

pls Subscribe!!!!


๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€
๐Ÿคน๐Ÿฟโ€โ™‚๏ธ *ALKAWARIN MASOYA* ๐Ÿคน๐Ÿปโ€โ™€๏ธ
~ Na ~

๐Ÿƒ *Rukayya Ibrahim*๐Ÿƒ

Free page๐Ÿคง

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*


Page5โƒฃ&6โƒฃ
Lahab ne tsaye yana kallonsu cikin mamakin Abinda Ade yake ma Mubeena, fuska ba walwala ya tako wajen da suke tsaye, Itakam jikinta sai rawa yake don ta tsorata bata d'auka lahab bane.

Karasowa yayi kusa da Adewale a daidai lokacin wani farin matashi bazai wuce sa'ar su lahab ba, sanye da kayan gida a jikinsa wando 3queter da riga duk da kayan da gani sun d'an sha ruwa, kallonsu lahab yayi cikin tuhuma ganin su a tsatsaye harda Addansa ma, kai lafiyarku?

Har suna had'a baki wajen basa Amsa ba kome, da sauri mubeena ta sabi kwandon wanke-wanken ta har lokacin jikinta na bari ta shiga kitchen nasu dake gefe.

Kofar gidan suka nufa har sun iso bakin kofa sukaji muryar inna data fito daga bandaki, kai nabeel!!

Da sauri dukansu suka juyo gareta suna kallonta.

Ina zaka??banaji kace makaranta zaka da safen nan ba? yana ganka a haka sannan dumamen dana aje maka bazaka d'auka bane kaci sai ulcer ya kamaka.



gaskiya Inna ki basar kawai ni bazani makarantan nan ba.


akan me bazaka ba?koh don uban gidanka(lahab) baxaije bane? ai tunda na gansa ba uniform nasan za'a rina, toh ka tsaya na fad'a maka gaskiya, tun duniya bai fad'a maka ba, kaga wannan yaro lahabu da wannan d'an yorobawan?su suna da gata iyayen su nada hali koh basuje makaranta ba, rayuwa bazata musu tsami irin naka ba, Amatsayin ka na maraya ka rike maraicin ka kayi karatu ka samu na tallafawa rayuwar ka damu duka, in bakayi karatuba ka samu madogara wazai zamo gatan mu nida yar uwarka nabeel?



jin kalar fad'arda akema nabeel yasa Su fita a sulale suka bar gidan, suna fita kallon Ade lahab yayi"Adewale menene tsakaninka da mubeena Addar Nabeel"?


shuru ade yayi sai kuma ya ce ba kome.

cin serious lahab yayi, karka fara karka kuskura duk rashin jin mu baikai nan ba, koh zamuyi iskanci banda Ahlin mu a ciki, dangin nabeel tamkar nawa nake ganinsu kuma bazanso wani abin ya samesu ba, haka naka dangin bazan yarda a tuzartasu ba, don haka karka kuskura ka bari nabeel yaga irin abinda kayin nan, don Wallahi nasan karshen relationship naku yazo karshe kenan, kadaisan halinsa"?


Promise u hakan bazai kara faruwa ba, amma fa bada niya nayi ba kawai abinda tamin ne banji dadi ba?

"sai kuma aka.......shuru lahab yayi bai karasa ba ganin nabeel ya fitoh daga gidan fuska a hade.


Ade ne ya kallesa toh ina dumemen(dumame)yake koh bazaka fito mana dashi bane?


daga lahab har Ade dariya suka sake tuno Yanda abokin nasu ya tsane dumamen tuwo.

kallon banza ya musu ya kama tafiyar sa, da sauri sukabi bayansa ganin ya nufi gangaren layinsu, " kai nabeel ina zakane"?


kamar bazai amsa ba sai kuma yace, shago


"wani shagon"?

shagon dinki mana


da mamaki lahab da Ade sukace shagon dinki?har suna had'a baki, don rabon nabeel da shago ai an kwana biyu duk da ya iyya dinki, Amma fa banda had'a kura babu abinda ya iyya inya kakkarba kayan mutane sai ya daina zuwa shago" Amma dai yau mafarki kayi wata zata karka akan kudinta koh"?


kallon Lahab yayi sai kuma yayi murmushi kawai hade dacewa, kun manta kudin jesen jiya da mukayi daku zamu saya.

"eh mun tuna"


toh shiyasa yau zanje shago tunda mun fasa shiga school in naga koh Allah zaisa na samu kafun yamma.

amma Nabeel taya zaka samu 10k a rana d'aya kuma a d'inki gaskiya da wuya.

lahab kam baice kome ba jin Amsar da Ade ya bawa nabeel yasa sa ciro 11k innan a Aljuhunsa mikawa Abokin nasa kudin yayi, "gashi 11k ne ka d'auki dubu goma kuje da Ade kusai jese shima kudinsa na hannunsa 1k in ku hau transport"


da mamaki Ade ke kallon lahab daman haka kullum yake mundin D'ayansu baida abu tsakanin shi da Nabeel haka lahab zai d'au nasa ya basu, toh yanzun kai ina zaka?


da sauri Nabeel ma ya jefo masa tambayar sa shima, toh lahab inna karbi kudin nan kai kuma ka saya dame?


"kallonsu yayi toh tambayar wa zan fara amsawa a cikin ku"?


dukan mu suka basa amsa.


" toh gidan mamina zanje koh zaku rakani ne"?


da sauri sukce Ah ah

ok toh sai kuma maganar kudi, ina da wasu kuje kawai da wannan in, kai kuma Ade bani keken nan naka naje dashi a cikin 1k innan Nabeel ya saya abinci tunda bai karya ba.

godiya nabeel ya masa, bai amsa ba sai harara ya dallara masa, cikin wasa yace"babu godiya a tsakanin mu Abokai ai yiwa kaine, ya karasa maganar da hawa kan keken yaja ya kara gaba, suma da ido suka bisa sai kuma suka wuce bakin titi suka tare keke napep zuwa kasuwa.


lahab kam unguwan da maminsa ke aure ya nufa, unguwane mai kyaun gaske packing yayi a kofar wani tangamemen get, gidane mai kyau Amma baikai gidan su kyau ba, hannu yasa ya bubbuga get in hade da danna hon na kekensa.


maigadi dake zaune a d'akinsa jin bugu ba gaggautawa yasa da sauri ya mike takalminsa ya saka cikin sassarfa ya nufi kofar, kokarin bude kofar yake hade da tambayar wanene.


shuru lahab yayi baiyi magana ba, mai gadin nad'an bude kofar zai leka yaga waye ne da gudu lahab yaja keken yayi cikin gidan saura kad'an ya kade maiganin, da sauri ya basa hanya tsayawa kawai yayi yana bin lahab da ido hade da mamakin ganinsa yau don duk da baya ganesu da d'an uwansa, Amma mundin lahab yazo saiya ganesu a d'abi'a da d'an uwansa ne yana zuwa gaidashi zaifara ba kokarin kad'esa ba, komawa kawai yayi ya rufe kofar ya zaune a benchin dake gefen d'akinsa.


lahab bai tsaya da keken saba har ya wuce compound na gidan sai da ya iso har bakin kofar falon in ya tsaya da kekensa, sauka yayi ya jingina keken ya haura baranda, tura kofar falon yayi koh sallama babu ya duro kansa ciki.


mami dake zaune Akan kujera tana shan fruit salad ne ta bisa da ido harya karaso tsakar falon, fuska ta hade tana kallonsa, koma kayi sallama.


tsayawa yayi kikam yana kallonta ganin yanda ta had'a fuska, bazaka fita bane koh yaya?ta sake maimaita wa.


juyawa yayi a hankali wallahi badon bukatar sa bace ta kawosa da inya fitan nan badai ya kara shigowa ba, komawa yayi ya tsaya a bakin kofar, da karfi ya kwala sallama.

Girgiza kai kawai mami tayi jin mannin hauka da lahab yake, amsawa tayi tare da bashi izinin shigowa, ba musu ya shigon, zama yayi a cikin d'aya daga cikin kujerun falon yana kallonta"ina kwana mami"?

Lafiya lahab ashe ana ganin ku?

"Eh mami bagani ba"

Ah ah bukatar ka dai ta kawoka ba zuwan Allah Annabi bane wannan, yasu Addayiya da sauran yan uwan naka da iyaye?

"Suna lafiya mami sun mace suna gaidake"

kadaiji tsoron Allah wallahi taima ma babu wanda yasan kayi hanyar gidan nan, gashidai safiyar jumma'a ce kowani yaro yana makaranta war haka amma kai kana gantali da abokan shashancin nan naka?

"Wallahi mami yaune na tashi kafad'ata na ciwo shiyasa Abbu yace kar naje makaranta"

rufemini baki shashasha kawai Abbun kake ma karya koh sa'anka ne taya za'ace kai kullum cikin case kake, kai ba zuwa makaranta ba kai ba sana'ar baki ba bare fari, sai yawon kamar kare, da ball kai koh kishi bakaji yanda kowa ke yabon yalin d'an uwanka Rahab.


Had'a fuska yayi don shi a duniya ya tsani in za'a masa fad'a ace ya kwaikwayi Rahab abin haushi yake basa.


Ka had'a fuska da kyau, gaskiya na fad'a ai yaron nan ya fika hankali babu ranan jumma'a da yamma daba zaizo wajena ba ya gaidani, yanzun kai tsakani da Allah rabonka da gidan nan tun yaushe?


Fuska a hade yatsungunar da kai, shuru yayi baice kome ba shidai sai Allah Allah yake kartazo ta hanasa kudin nan,"kiyi hakuri mami zanna zuwa kullum insha Allah"


ALKAWARIN KA ai ba Alkawari bane sau nawa kana mini Alkawari kana karyawa, Yanzun sau nawa kanace mini xaka daina saka Addayiya surutu Amma ka daina inne? hatta jiya da Umaimah tazo gidan nan saida ta bani labarin abubuwan da kake musu a gida anya lahab zakayi hankali kuwa, shekara 18 ace mutum baisan inda ke masa ciwo ba?


Shuru yayi yaki tanka mata don shi irin mutanen nan ne da holo baya damunsu sam ga rashin zuciya, koh fad'a kukayi da lahab zuwa anjima ya watsar abinsa, ya cigaba da rayuwar sa baya sakawa kansa tention.

Ganin yanda yayi zuru yana sauraronta kamar radio yasa ta yin shuru kawai, tana kallonsa.

Shima d'aga ido yayi ya kalleta jin ta daina fad'ar had'a ido sukayi da sauri ya sunkuyar da kai yana kaikaya gashin geyarsa"uhmm ayya mamina my only mother ki taimaka mini da 20k mana momcy"ya karasa maganar cikin Alamun a tausaya masa.

Kama baki mami tayi tana kallonsa, uban me zakayi da 20k lahab?


"Wallahi mami so nake na sayi wasu kayane"

Kaya lahab?wani irin kayane baka dashi a gidan ku?daga na banza harda na kirki sanan kazo kace na baka kudi, badai kaya bakam kadaisan me zakayi da kudin, toh bara na fad'a maka lahab bazan baka koh sisi ba kaji na fad'a maka, bazaiyu Yayan ka yana kirana yana mini masifa ina bata ka da kudi b, a badani ba kaji na fad'a maka.


Mikewa lahab yayi tunda yaji mami tace bazata bayar ba toh fa magana ya kare kenan, tafiya ya fara cikin jin ba dadi.

Dawo nan lahab, ba musu ya dawo ya tsaya ka karya kuwa?

"Ah ah"

Toh wuce kitchen akwai abinci ka iba.

Girgiza kai kawai lahab yayi alamun bazaici ba.


Ina wasa da kai?

"Ah ah mami"

Toh karkasa na maimaita kalamaina wuce akwai abinci a kitchen ka iba kazo ka zauna kaci nasan tunda ka fito ba uniform toh nasan baka karya ba, Shiyasa nake Allah Allah muzammil ya dawo shine daidai da kai wuce ka bani waje...


Wucewa yayi cikin kitchen in, bude kulanda ya gani mai kyau a zaune a kitchen in yayi plate ya d'auka ya iba, dankalin hausane soyayye da miyar tattasai sai shayi a kofi ya had'a da soyayyen kwai akai, fitowa yayi da plate da cup in a hannunsa zai zauna akan daining.


Kawo abincin na gani lahab?mami tace tana kallonsa.

Tsayawa yayi yana zullumi had'e da kallon plate in, dankaline da bai wuce yanka bakwai ba, sai kwai da biya kad'an.

Bakaji me nace bane?

"Naji mami ina zuwa na manta ban saka miya ba"yace da sauri yana komawa kitchen in karo dankalin yayi da yawa saida plate ya cika ya fito a kitchen in, ya nufo wajen da mamin ke zaune.

Mika mata plate in yayi, ba tare da ta kalli plate in ba tace, zauna kaci a kusa dani na gani.


Ba musu lahab ya zauna akasan cafet in, cin abincin yake cikin rashin walwala don sam basirar sa ta toshe baisan ina zai samo kudin jese ba, yana kammala ci mikewa yayi ya kai kwanukan kitchen, yana fitowa ya kama hanya zai bar falon.

Kiransa mami tayi, ya Amsa yana kallonta, wuce kitchen kaje ka wanke mini kwanukan da sukayi datti oya.

"Wanke wanke kuma mami?ni ina na wani iyya wanke wanke don Allah fa"

Toh yau kai zaka mini koh baka iyya ba ka koya.

"Amma dai mami gaskiya ni kuma, ina yan aikin naki toh"?

Oho wuce kitchen ka bani waje, ba musu ya shiga kitchen in, zaman sa yayi ya zaro wayarsa yana chatting abinsa.

Mami dake falo kamar tasan abinda yake aikatawa mikewa tayi da saurinta ta nufi kitchen in, tana tura kofar da sauri ya mike tsaye yana kokarin boye wayar, amma ina tuni harta raftosa, ban wayar nan?tace tana mika masa hannu.

Ba musu ya mika mata wayar, nuna masa kwanukan tayi da hannu wanke.

Zare rigan saman shirt nasa yayi ya soma wanke kwanukan, shiyasa bayason zuwa gidan ta akwai matsawa mutum, a haka ya ringa wanke kwanuka harya gama haka mami tasaka sa sake wankewa wai bai fita ba.

Yana gamawa haka tasaka sa aikace aikacen kitchen, tana girki yana mika mata kayayyaki har suka gama abincin rana tare, lokacin kusan 12:00 saura na rana, Abincin ma kinci yayi gashi duk kaurin girki yake.

Wanka yayi a d'akin kaninsa mahraz, bayan ya fito d'aure da towel, bude wardrop in yayi yana duba kayanda zai saka don bazai iyya maimaita kaya mai datti a jikinsa ba bayan yayi wanka, rasa ma kayanda zai d'auka yayi don duk kayan sun masa kad'an, daker ya samo wata jallabiya fara sol ya zura sai wando baki pencil dayabi jikinsa ya kwanta irin roba-roban nan ne.

Turare kawai ya fisa ya fita a d'akin falon ya shiga zuwa lokacin mami ma har tayi wanka tana zaune akan siter.

Baiyi mata magana bama kofa kawai ya nufa itama in batayi magana ba, harya fita baranda sai kuma ya dawo tsayawa yayi a gefe ba walwala yace"mami a bani wayan"

Mara kunya aida wuceni kayi, don haka koma ka sako hula a kan shegen gashin kan nan naka.

Baison magana kawai juyawa yayi ya koma ya d'auko hula ya saka akan sa, fitowa yayi ya tsaya ba tare daya ce kome ba, wayar ta mika masa.

"Hannu yasa ya amshi wayar hade da kallon mamin nasa"ayya mami kitaimaka mini mana mami na ki bani koh 10k ne don Allah"?

Wuce mini daga gani in abin arziki zaka saya zan baka Amma banda na shirme.

"Don Allah mamina kiyi hakuri na tuba alalubo abani"

Lahab bazan bayar ba kaji koh nace bazan bayarba.....shuru mami tayi jin an turo kofar falon.

Wani d'an dattijo ne ya bude kofar sanye yake da suit baki, sai yara dake binsa a baya sanye da uniform su uku da gudu suka rugo cikin falon ganin lahab da sauri suka rungumesa suna oyoyo yaya Rahab, don su sam d'auka sukai akan Rahab ne ganin yau shigen mutunci ne a jikinsa.

Da dauri ya turesu a jikinsa cikin masifa yace "don Allah ku matsamin a jiki karku batamin farin kaya.

Da mamaki yaran ke kallonsa suna mamakin meya faru da yaya Rahab donsu basu kawo lahab bane.

Kallonsa dattijon yayi, ah ah Rahab yau ziyaran jumma'ar da wuri akazo mana kenan, aiko saika jiramu mu tafi tare koh?

Kauda fuska lahab yayi ya nufi kofa baice kome ba.

Kwala masa kira mami tayi lahab dawo nan...........


Pls subscribe

https://youtube.com/channel/UCsYHQSbZF_5kKSbjvZTYXHg






๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€
๐Ÿคน๐Ÿฟโ€โ™‚๏ธ *ALKAWARIN MASOYA* ๐Ÿคน๐Ÿปโ€โ™€๏ธ
~ Na ~

๐Ÿƒ *Rukayya Ibrahim*๐Ÿƒ

Free page๐Ÿคง

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*


page 7โƒฃ&8โƒฃ

Ba musu lahab ya dawo ya tsaya cikin had'a fuska yake kallon kannen nasa dake gefe sunyi xuru suna kallon sa.

Lahab waye wannan?mami ta tambaye sa tana nuna masa Dattijon.

Kallon mutumin lahab yayi sai kuma yace"dadyn su mahraz ne"

Eyeee watoh dadyn su mahraz kai ba dadyn kaba kenan koh?shiyasa dake kallosa kamar banza?anya lahab kana da tunani kuwa mahraz ba kaninka bane koh bani na haifesa a cikina ba dabaza girmama ubansa ba?


Shuru kawai yayi baice kome ba.

Gaidashi lahab?

Ba musu lahab ya dubi dattijon"ina wuni Dady"?

Lafiya lahab yasu Yayan naka da d'an uwanka, kwana biyu kayi mana retaya baka zuwa?

"Lafiyan su klau dady"yace sai kuma yayi shuru baice kome ba.

Mahraz dake gefe zaikai shekara 13 tun d'azun sai kallon Lahab yake tunda yaji momy tace ba Rahab bane yaja gefe ya tsaya abinsa gudun karyasha duka a banza.

Sai kayi tafiyarka ai koh na rike ka ne?

"Bai bawa mami amsa ba kawai ya juya zai fita sai kuma ya sake kallon mamin yanzun mami bazaki bani ba"?

Mami koh Amsa masa bata sake yiba,tayi shuru abinta,dady ne ya dube lahab in, mekake so lahab?

Da sauri mama race,Kaga Dadyn mahraz kuwuce muje ku shirya time na gudu yaufa have day ne, kusamu ku shirya kafun a fara tafiya jumma'a.

Kallon lahab dady yayi me kake so ta baka?

"Kudine dady kuma tace bazata bani ba"

Nawane kudin lahab?

"Murmushi yayi yana kallon mami,yace 30k ne"

Ok jirani ina zuwa kawai dady yace yana shigewa ciki, da mamaki mami tace lahab yaushe zaka fara tsoron Alalh ne?yanzun na karyata ka agabansa yace banason yana kyautatawa yarana,Amma lahab allah ya shiryeka.

"Ameeen mamina"

Ba'a jima ba saiga dady ya fito daga sashin sa,kudi ya mikawa lahab, da sauri yasa hannu ya Amshe kudin cikin murna yake masa godiya ganin kudin kamar zaifi 30k ma.

Fita yayi a gidan keken sa ya d'auka, tuda mai gadi ya gansa ya fitoh da sauri ya bude get in ya basa waje ya wuce, bai fita ba saida ya kirga kudin 50k ne cipcip da murna ya soka kudin a Aljuhunsa na jallabiya, wayarsa ya duba aiko kamar yanda ya tsamma nine kusan 10 miss call na Adewale da nabeel suka kirasa bai d'auka ba, buga kekensa yayi ya kara gaba.

Yana fita a get in gidan, haryayi nisa a layin kamar daga sama yaga ade da nabeel zaune a kofar wani gida su biyu dukansu sun shanja kaya alamu dai jiransa suke.


Tun daga nesa da suka hangosa gabaki d'ayan su suka mike suna kallonsa ganinsa sanye da jallabiya harda hula abinda ba d'abiyarsa bace saka kaya manya ba, durun wa, kaji manyan gari nebeel yace ganin lahab ya kusa isowa kusa dasu.

Da gudu lahab yayo kansu da keke ai a dari suka watse suna zaginsa shege d'an iska meye haka kaje ka wani zauna ka barmu a tsaye, munata kiran wayan ka ba'a picking, wallahi saura kad'an mu

Please Login or Register in order to submit comment