Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakin, shima lahab Shiga yayi da sauri yad'au uniform nasa yasa jakan sa da laidan abincin ya saba ya fita a dakin cikin hanzari ya maida kofar falon ya rufe, a sannu sannu take ratsa falon Nasu har kofar falon hannnu yasa ya bude kofar ya fitoh babban falon gidan.

Zazzaune suke kamar kullum akan dinning harya wuce su baiyi magana ba sai kuma ya dawo da baya tunawa da yayi da akwai fa uncle a dinning in,gashi ba addayiya bata fitoh ba, Dan rusuna wa yayi yana gaida Abbu"good morning yaya"?

Kallon sa Abbu yayi da mamaki yau shine sanye da uniform ba tare da anyi hali ba gashi wai harzashi makaranta, morning Lahab sai ina haka kake ta saurin nan?

Murmushi yayi ya dan tsosa keyar sa" wallahi yaya school zani Sauri nake na makara yana maganar yana kallon agogon dake manne a tsintsiyar hannun sa.

Dukan su suka zuba masa ido da mamaki wai yau lahab ke cewa zaiyi late, gyada kai kawai Abbu yayi bai kara magana ba, juyawa yayi ya gaida uncle dake hade da fuska yana cin abinci lahab yayi, kin amsa masa muzammil yayi sai nuna masa kujeran dake gefen sa da yatsa Wanda koh bai tambaya ba yasan me hakan yake nufi.

Kin zaman yayi cikin sanyi yace "uncle so nake daman na wuce da wuri ga abinci na nan a laida yana maganar yana daga laidan hannun sa.

Kallonsa muzammil yayi, kai wani Sabon salone cin abinci a kula ka fara koh me?

da Sauri ummu tace, Nima dai abin yaban mamaki yau tun asuba yake kitchen ya tasa muneera a gaba ta soya masa kwai da indomie.

Harara lahab ya maka mata a fakaice cikin jin haushi ya mike" gaskiya nifa ana samin ido a gidan nan abinci ne dai nace zan fita dashi kuma makarantane zanje sai kuma akama mini wani tambayoyi"

Kama baki mamu tayi"kema dai wallahi da naki Ina ruwan ki inyaga dama ma ya ya dau gas ya tafi school yana girki ashan me naki"

d'aga musu hannu Abbu yayi ganin in aka sake fadar zai koma na manya,kunga ya isheni, kai kuma lahab saika jira yan uwanka suci breakfast sai Ku tafi tare.

"Gaskiya ni yaya zan tafi da kaina wallahi banson tafiya dasu a mota zan hau keke"

Kasan Allah lahab in baka rufemin baki ba kaje waje ka zauna ba zan mugun saba maka shashasha kawai, muzammil yace yana masa mugun kallo.

Ba musu lahab ya sauka a falon zama yayi a one sita yana kunkuni ciki-ciki don shi so yayi yau su hade da Nnenna in so samu ne suje tare amma sunzo sun bata kome.

Bini-Bini saiya duba time yaja tsakin haushi a haka har suka kammala ci baima wani saurare suba ya fita daga falon, bin kofar falon yayi yana bin compound in da kallo har idanun sa suka sauka akan motar da driver ya packa yana jiran su, nufar motar yayi ya bude gidan gaba ya zauna koh gaida malam habu baiyi ba shima bai wani damu ba Inda sabo ya saba da halin lahab.

Ba'a jima ba munira da zulaihata da rahab suka fito daga falon kowa rataye da school bag Nashi, bubbude motar sukayi suka zazzauna, malam habu yaja motar bayan mai gadi ya wangale musu gate.

"Don Allah ka kara gudu zamuyi lattin fa" lahab yace yana kallon driver don shi ji yayi kamar motar bata sauri.

malam habu tafi a hankali mu ran mu na mana dadi, Rahab yace fuska a hade.

"Kaga malam sauke ni anan" lahab yace ma malam habu.

karka sauke sa in ba haka ba wallahi Zan Kai karanka wajen yaya, rahab shima ya maida martani yana kallon dan uwan nasa.

Shima lahab baice kome ba yaja bakin sa yayi shuru tunawa ma da yayi koh ya nace ya sauka ba dole bane ya samu Nnenna by this time.

A haka har suka isa makaranta a bakin gate malam habu yayi packing dukan su suka sassauka kamar yanda sauran students dake ta Shiga school gate in, suma Shiga sukayi, da Sauri lahab ya wuce clinic direct don shi a tunanin sa Nnenna tazo tuntuni.

Rahab daga nesa yake kwala masa kira ganin ya nufi hanyar clinic har hankalin sa ya tashi koh d'an uwan nasa baida lafiya ne?

Tsayawa Lahab yayi jin Kiran da Rahab ke kwala masa, baice kome ba har Rahab ya karaso kusa dashi, lafiya lahab ina zakaje kuma naga ka nufi clinic?

"Mtwsss kai d'an sa ido yau kuma ni ka tsare da tambaya kamar wani kanin ka kaji Dan Rai nin since kawai"

Juyawa kawai Rahab yayi ba tare dayace kome ba, shima lahab kara gaba yayi abinsa ya wuce clinic in, yana isa bakin block in ya Haura steps dake barandan yana Hawa a hankali ya taka har bakin kofar hall in ya tura tare da Shiga ciki.



***************
Ta bangaren Nnenna ma da Sauri ta Shiga dakin uniform ta d'auka Harta tube kayan ta zata sa rikan uniform sai kuma da Sauri tai"shiiiiii"tare da duba hannnun nata jin wani rad'adi agun, alluran ne ya tsoketa tun lokacin da mom ta ja hannnunta ta damke ga jini na malala, kuka ta sake a hankali ta aje rigan dake hannnunta tasa d'aya hannnun a hankali ta zare Allurar ta aje a kasa da Sauri ta dauko dankwalin ta tasa raiza ta yanka ta daure hannnu, kafun ta lallaba ta Sanya kaya a jikin ta, jakanta ta d'auka ta sanya magangunan ta tare da tattare cake Inda yayi fata-fata da cake Inda ya wargaje a kasa.

Kulenta ta d'auka tasa a jaka tare da tattara magangunan ta duka tasa a jakan da Sauri jin Abraham na kwala mata kira daga falon.

Da Sauri ta fita sai kuma ta soma tafiya a lalube a hankali ta shigo falon, ganin ta yasa Abraham nufar kofa yabude mata a hankali ta fita ya rufa mata baya ba tare da ya saurare warning Inda mom ke buga masa ba suka fita hannun Nata ya kalla tare da karban jakan dake hannun ta ya rataya ba tare days kula da ciwon taba.

Bude kofar gaba tayi ta Shiga shima ya bude drive sit ya zauna tare dajan motar suka Lula.

Suna isa school in ya sauke ta a kofar makaranta tare da zare 2k ya mika mata amma kememen Nnenna taki karban kudin Sam yayi yayi amma taki karshe haka ya barta ta fita a motar ta nufi gate, har lokacin bai tafi ba yana tsaye har yaga shigan ta.

A hankali take tafiya kamar iska zai hure ta saboda ciwon kwana da kwanaki dake cinta sosai ta rame, maimakon ta nufi clinic kamar yanda Dr yace, saboda ita Sam batason missing na class in yau ma.

Lokacin data bakin class ma first period ne har anyi nisa dole yasa ta tsayuwa a kofa bata shiga ba.

Uncle maths dake teaching juyawa yayi ya ganta sai kuma ya yafitota da hannu, ba musu ta karasa cikin ajin ta tsaya a gefe Yana gaidashi, cikin tsawa yake tambayar ta ba tare daya amsa gaisuwar ba, kee meyasa kullum kike lettin ne?

"A hankali tace, sir am sorry bansan zanyi Lettin ba"?

Oh late in ma sai an sani ake?

Durkusawa tayi da gwuwowin ta a kasa tana basa hakuri daker dai ya hakura tare da nuna mata bench dake can tsakiya, go an sitdown my friend.

Da Sauri taje ta zauna a take yaran dake zazzaune kusa da bench in duk suka marmatsa abinsu.

************
Lahab kam yana shiga hall in direct ya wuce corridor dake dama da falon sannan ya tura kofa mai number 4 Wanda a ciki jiya aka kwantar da ita, yana Shiga da mamaki ya tsaya yana bin dakin da kallo.

Ba kowa asali ma dakin tsap yake an gyara an kimtsa kome alamu dai bama mutum a ciki, Fita yayi ya nufi office in likita, yayi knocking sai da aka basa izinin shiga kafun ya tura kofar ya Shiga da sallama,"Assalamu Alaikum"

dago kai Dr yayi tare da amsa masa" waalaikumu salam ah ah lahab shigo mana get a sit?

Zama lahab yayi a hankali ya soma gaida Dr "good morning Dr"?

Amsa masa yayi, morning lahab yamai jiki?

"da sauki Dr daman nazo naji koh an chanja mata dakine"?

Da mamaki Dr yace, Ah ai bata iso ba,ai dana ganka ma na d'auka koh tare kuke?

"au Dr bata zo bane"

Murmushi Dr yayi, maybe lahab an kaita wani hospital inne.

"Anya kuwa Dr munyi da ita fa jiya nan zata dawo"

Kai lahab ka sani koh iyayen ta sun bukace kaita gaba, koh dai koh dai??ya karasa maganar yana dagawa lahab gira.

Tsotsa keyan sa yayi tare da mikewa tsaye cikin kunya yace"toh Dr mungode"

Ba kome lahab daga nan dai ka wuce aji karka ce zaka fita school yanzun don nasan halinka Sarai?

Gyada masa kai lahab yayi tare da bude kofar falon ya fita, kujerun dake hall in na silver,akan guda daya ya zauna don shi yafi ta'allaka rashin zuwan nata da late tayi shiyasa yace bari ya jira ta.


Lahab na zaune har 9:12pm na safe shuru babu Nnenna babu mai kama da ita haka ya miki ya fita a block in, harya nufi gate sai kuma ya dakata, da Sauri ya juya ya kama hanyar block na SS class.

A window ss 1A ya tsaya ba tare daya damu da malamin dake ciki ba ya soma jejjefa ido yana duba ta, amma bai ganta ba haka dai bai karaya ba ya ringa bin class by class yana checking nata har yazo kofar ajin da aka maidashi ss 3B kamar a mafarki yana laika Kansa ya hangota zaune kanta akan dex tana rubutu.

Ai da sauri ya nufi kofar class in ba tare daya nemi excuse ba kawai ya Shiga abinsa hannun sa danke da laidan takeAway nasa.

Uncle physics dake note a board ya juyo yana kallon sa yana mamakin rashin kunyar yaron, ace banda iskanci ya gansa a tsaye a cikin class amma haryana da confidence na shigowa kai tsaye.

Lahab kam koh takan sa baibi ba da Sauri ya nufi wajen da Nnenna ke zaune, yayin da yan ajin gabaki d'aya suka bar abinda suke suka zuba masa ido harda Nnenna data daga kai zata ga board kawai sukayi 4 eyes da lahab a take fara'ar dake fuskar ta bayyana, Barin rubutun tayi tana jiran karasowar sa, ganin wajen ta ya nufa.

Aiko yana isa gareta dayake binci mai d'aukar mutum daya ne kowa da lokansa da sit nasa hakan yasasa, tsayuwa a kanta ba tare daya zauna akan binchin dake kusa da nata Wanda yara suka marmatsa suka barta.


Nufar sa teacher yayi rai a bace cikin tsawa yace, kaiii stupid ways baka izinin dazaka shigo aji ba tare da Neman izinina ba who I u ya karasa maganar cikin hargowa.

Nnenna Kam ta sure sosai sabanin lahab dako a jikin sa saima Zama yayi akan bincin dake gaban nata yayi cross lag...........




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 37&38
Damko kwalan Lahab yayi rai a bace ya Soma jansa Yana buga Masa tsawa,I say get out from my class?

Kowa yasan yanda ss 3 suke feeling lokacin da suke Sabon Shiga gani suke kansu daya da malamai ne yanzun gasu da gemu,gashi a lokacin yaran ke tashen balaga ji suke kashin su na daidai dana kowa,toh hakan take a wajen Lahab daman gashi da karfi Kamar doki Koh uncle muzammil dake jibgarsa albarkacin kanin uba yakeci,kwace kwalar sa yayi da karfi tare da bangazan coper in don bazai wuce 25 ba"Akan me Zan bar class in"?Lahab ya tambaye sa Yana haki.

Mari coper in ya wanke sa dashi tare da cewa,saboda bana ubanka bane.

Habawa daman Lahab a duniya ba abinda ya tsana irin a zagi ubansa Koh don uban bai raye ne oho,Amma shi gwara ka zagi uwarsa daka zagi ubansa,kafun coper(uncle physics) ya sauke hannnun sa tuni Lahab ya d'aga hannu ya sharara Masa Mari,a take suka rungume juna da fad'a.

Kacemewa ajin yayi da ihu Nnenna sosai ta tsorata ganin irin dambe da ake bugawa gabaki dayansu fada suke da dukkan karfin su Kuma bamai kwaran wani, Lahab bai basa daman da zai bugeshi,Kuka take tana tattara jakanta dana Lahab da laidan, ta ruga gefe ganin sun koma fadan akan bencuna.

Ihun dalibai shiya d'auki hankalin malamai dake makarantan da dalibai duk take sauran classes Suka fifita a ajujuwan su Suka nufi Nasu Lahab ciki harda su muneera dasu Adewale da Nabeel da rabon su da Lahab tun jiya,ganin fada ake da Lahab yasasu shigar Masa,take su ukun Nan Suka Soma jibgar coper Nan da karfin da Allah ya musu,daman ance sarkin yawa yafi sarkin karfe,zuwa lokacin Kare kansa coper Nan ya suma Amma baya iyya maida martani ganin malamai sun nufi ajin Yasa sauran students fara ihu suna ga principal ga disple Master.

da gudu Suka sake bawan Allah Suka nufi windonan hannnun daman ajin Suka hau Suka tsallaka daidai lokacin malamai Suka shigo da gudu suma Suka nufesu,Amma Ina kafun ma su sauka tuni su Lahab sunyi Nisan zango,sun dosi cikin gonakin makarantan Amma duk da hakan Basu hakura ba Suka rufa musu baya suma.

Ta bangaren class Kam kuka Nnenna take tayi don ita ta gama sadakarwa shikenan yau Lahab ya shiga ukun sa,daidai lokacin Rahab ya iso wajen bayan su muneera sunje sun Kai Masa rahoto sosai Shima ya shiga damuwa sanin da yayi lallai yau jikin Lahab zai gaya masa in aka kamasu,Yana Isa ya samu sun ma gudu juyawa yayi bai shiga ajin ba ya Kama hannnun zulai tare da muneera Suka bar wajen,warning ya musu akan karsu kuskura yaji sunyi hiran abinda ya faru Koh da Wasa Koh fadawa wani a gida,munira ce ya kallesa,insha Allah uncle bazamu fada ba Amma ni ina tsoron matakin da xa'a d'auka akan uncle Lahab?

Girgiza Kai Rahab yayi,karki damu munira abin zaizo da sauki Allah ya Mana Mai kyau.

Zulai dake kuka sai share hawaye take akai akai ita tayi magana,ni toh uncle Mai yasa yake haka ne.

Kin cika surutu zulaihat ya Isa haka kudai duk lokacin da kukayi sallah kusa uncle naku a Addu'a Allah ya shirye sa.

dukan su da Ameen suka amsa Masa kowa ya koma class nasu.

Su Lahab Kam da gudu Suka fasa cikin gonakin makarantan ganin har lokacin ba'a daina binsu ba yasa su Kama katangan makarantan Koh tsoron wayan danger dake mammakale basuji ba Suka d'ale da gudu Suka dirka ta bayan makarantan,Inda Allah ma ya sosu yashine a bayan wajen suna dirka Suka Kara gaba abinsu ,dole tasa malaman juyawa ganin su Lahab dai sun tsira.

Koran yara a ajin su Lahab teachers in sukayi sai Yan aji kawai aka Bari,Kama coper dake sheme akasa sukayi don gaskiya ya daku wallahi dole tasa aka nufi clinic dashi.

Nnenna Kam komawa tayi kan des nata ta zauna har lokacin jikinta baibar rawa ba don it's Sam duk abin tashin hankali bason sa take ba.

Su Lahab Kam d'aga Nan hankalin su kwance don harma sun manta sunyi fada tsakanin su su biyu da Nabeel,hirane ya barke tsakanin su sunayi Suna dariya,Amma wallahi Lahab baka da mutunci wai ma tsaya uban me ya hadaku ne wai?

Cikin dariyan shekiyanci Lahab ya dubi Nabeel dake Masa wannan tambayar"Kai za'a tambaya d'aga kanin Muna fada sai kawai kuzo ku shiga abinda ma bakusan kansa ba.

Hararan sa Adewale yayi toh sai mu Bari a jibgeka ne Koh Yaya?

"Wallahi kunsan nafi karfen muyi dambe aci zalina"ya karasa maganar Yana kallon Nabeel Yana dariya Shima Adewale kwashewa yayi da dariyan tunawa da dukan da Lahab yamasa last time.

Aiko Nabeel ya Shaka sosai har ya kasa hakuri ya yunkura zai kaiwa Lahab naushi da gudu ya zura tare da fashewa da dariya Nabeel ya Mara Masa baya Suka ringa guje guje a titi Kamar tababbu.


tun da abin ya faru ba teacher d'aya daya shiga ajin su Nnenna, don malaman sun rantse bazasu sake shigaba harsai an dauki kwakwaran matakin akan su Lahab don bazai yu suna matsayin malamai har dalibi ya samu daman dambe da malami abarsa ba hakan raini ne sosai Kuma in aka bar abin a haka toh tabbas an bawa dalibai satan amsa ne,duk Wanda malami ya buga zaice zai rama tunda Lahab ma yayi ba'a Masa kome ba,suma daliban Koh a jikinsu saima Dadi da sukaji yau babu lesson,sai hirar abinda ya faru suke duk an cika ajin da surutu group group akayi wasu mata zallah wasu Maza da Mata,wasu na zagin Lahab wasu nacewa ya burgesu daman copern haushi yake Basu wasu Kam labarin gagarancin Lahab suke musamnan Yan kusa da Nnenna Kuma sunayi Suna gaurayawa da turanci hakan yasa tana dan fahimtar abubuwan da suke cewa.

10:00pm dai dai aka buga break duk daliban ajin Suka Fara fita da d'ad'aya har gabaki dayan su Suka fita,sai Nnenna dake zaune rakube Kuma wallahi sosai takejin yunwa rabonta da abinci Mai kyau tun Wanda Lahab ya saya Mata jiya sai Kuma cake da taci shikuma ba abinci bane Mai nauyi bare ma ita data tashi d'aga jinya Koh magani anfison aci a koshi kafun asha,kwantar da kanta tayi a des in sai Kuma ta tashi jakanta ta bude ta fito da kulen nata a hankalin ya ajesa akan bincin da Sauri Kiki ya sauka ya nufi laidan Lahab dake aje a kasan bincin tun lokacin da ta sje batabi ta Kai ba kansa yasa Yana tsuntsuna laidan Yana soka kansa.


Da Sauri Nnenna ta d'auke sa sai Kuma ta hada fuska ganin sai kokarin sauka yake zai koma wajen laidan"Kai Kiki menene haka ka daina Mana"tana maganan tana sake rikesa gam abinka da dabba maijin yunwa da kwadayi take ya Soma kukan Nan nasu na kuleluka,tsorata tayi gudun Kar wani yaji ta shiga matsala da Sauri ta dauki laidan ta bude da mamaki abinci ta gani sai dan paper karami dake d'auke da note,haka kawai taji ranta nason karanta abinda ke rubuce,hannnun tasa a hankalin ta dau paper warwarewa tayi,"wow shine abinda ya fito a bakin ta Ganin wani nice note dake rubuce, rubutune Mai shegen kyau Kamar na computer.

"Good morning Labiba(Nnenna)"

Shine abinda ta Fara gani a farkon shafin,murmushi tayi don tasan kaf duniya babu Wanda ya taba kiranta da sunan Nan sai mutum daya, amma Bata tsammani lettern nata bane.

"How was your night hope kintashi lafiya ya karfin jiki,meyasa Baki koma clinic ba alhalin kince min Zaki dawo a Kara duba lafiyar ki"?

"Ok fine ga break na kawo miki Yana laidan Nan pls karkice no and promise me zakisha maganin ki,nasan indai har na shigo ajin Nan ba lalle in samu magana dake ba shiyasa na tsaya na rubuta miki letter na shigo dashi""


"Kici abinci Kisha magani and kije clinic"

"See you tomorrow byeeeeee"

Hannnunta tasa ta rufe bakinta tana murmushi watoh abinda ya faru Nan daman Lahab ya riga ya tsara kenan kafun ya shigo,Jakarta ta bude a hankalin ta aje papern a cikin litattafanta, cire barrect nata tayi ta aje a gefe laidan ta bude tana maijin dadi Sam ta rasa meyasa indai Lahab ya Bata Abu har marmarin karba take,Koh Abraham dake dan uwanta bata karban abin hannunsa.

takeAway in ta fitar duka biyu budewa tayi ganin daya indomie ne dayan Kuma kwai hakan yasata aje kwai in ganin akwai bread ma,indomie ta bude ta zubawa Kiki a marfin roban ta aje Masa akasan binci ya sauka ya kamaci,flask in ta bude don tasan yanda ake budewa akwai irinsa a gidansu.

Tsiyaye coffee tayi a cup fork ta d'auka Shima na roba ne ta Soma cin indomie cikin happy tana hadawa da coffee inta hankali kwanci sosai taci indomin Harta rage don daman Saida ya cika roban dam,karshe rufe sauran tayi ta maida cikin laidan ta,Ana dawowa breakfast haka sukaci gaba da Zama babu malami har azahar musulman suka fita sallah itakam kwai da bread ta d'auka taci ta koshi.

Misalin karfe 3 na yamma aka tashi makaranta dayake yau ba extra lesson kasancewar abinda ya faru yasa su tun karfe ukun akace su tafi gida,duke take tana tattara litattafanta data fitar tana bitawa saboda ita dai abinda ya faru bai Mata dadi ba da asaran lesson nayau dabasu samu ba,Amma ta lura yan ajin Koh a jikinsu Basu wani damu ba.

Excuse me senior,taji muryar wata yarinya dake tsaye a kanta d'aga Ido tayi ta kalli yarinyar black beauty ce kyekkyewa sosai Yar doguwa bazata wuce 15 ba Koh kasa da haka"yes" shine abinda Nnenna tace tana kallonta don d'aga gani juniorn sune.

Am daman nace Koh jakan dake zaune a gaban des Nan naki ne?

Girgiza Mata Kai Nnenna tayi"no ba nawa bane na class mate nawa ne.

Murmushi zulaihat tayi,ok sister na uncle nawa ne Bari na d'auka.

"La ba kome Nnenna tace tana d'auka da kanta ta Mika ma zulaihat in don ganin yanda ta tsaya sai kallonta take Kuma tana magana idanunta akanta.

da Sauri zulaihat tasa hannu ta karbi boron tana kallon laidan abinci dake gefe Amma dai batace kome ba tama Nnenna sallama tabar ajin,Nnenna ma jakanta ta d'auka tare da laidan ta fita a ajin.

Zulaihat Kam tana fita ajin su Rahab ta nufa ta Kai Masa jakan Kamar yanda ya umurceta kafun ta wuce masallaci domin sallan la'asar suci abinci kafun su Fara hadda by 4 O'clock.

Harta nufi gate sai ta tuna Lahab yace taje clinic juyawa tayi ta nufi clinic in,tana Hawa block in ta samu wasu Yan coper guda biyu sun fitoh d'aga ciki suna yare, alamu dai ya nuna wajen uncle physics nasu Suka fitoh shiga clinic in tayi direct ta nufi office in likitan knocking tayi shuru ba'a Bata izinin Shiga ba,gajiya tayi da tsayuwa kawai saita yanke shawarar tafiya abinta, juyawa tayi saura kadan suci Karo da Dr daya kawo Kai,da Sauri tayi baya hade da dukawa, "good afternoon Dr"?

Afternoon Nnenna Koh?

gyada Masa Kai tayi, toh muje ciki sai muyi maganar,Yana karasa maganar ya bude kofar office in ya shiga,biyosa tayi a baya Zama yayi a kan kujerar sa tare da nuna nata kujeran kaban Des nasa,sit down Mana Nnenna?

gyada Masa Kai tayi hade da Zama akan kujeran dake gaidashi tayi Shima ya sake amsawa kafun ya daura da cewa,gaskiya Naga jikin yayi kyau sosai ashe shiyasa ban ganki da safe ba.

"Sorry Dr naji saukine sosai shiyasa"

Ok Amma ai zakizo mu cire kanula in Aiko,ya karasa maganar Yana kallon hannnunta.

"Dr Na zare Allurar ai"ta karasa maganar tana kallon sa

What???meyasa Zaki cire kina aikin asibitine ban hannun mu gani.

Mika Masa hannun tayi,da kansa ya warware tsumman zare Ido yayi Ganin yanda hannnun ya kubura alamu ma sun nuna jini ya zuba,Aiko take yahau masifa irin dai yanda Dr kema majinyata in suka jika musu aiki,take yadau waya yayi magana ba'ajima ba sai Suka ji knocking izinin Shiga ya bada,aka turo kofar wata kyakyawar budurwace sanye da kayan asibiti.

Cike da girmamawa tace,sir gani

Yauwa sister farida ga wannan kuje da ita pharmacy kusai Allurar Nan saiki Mata tare da dressing in hannun nan nata Kisa Mata plaster,yakarasa maganar da Mika Mata Dan paper daya rubuta Mata allurar.

da Sauri ta karba cikin girmamawa.

Am sannan ke Nnenna kina Shan magani akan Kari Kam Koh? karki kuskura kiyi Wasa da magani kinji Koh?

Gyada Kai Nnenna tayi tare da mikewa tabi nurse in a baya,fuskarta a hade don wallahi ta tsane Allura.

Haka ba yanda ta iya ana kammala Mata allurar aka wanke hannun nata aka manna Mata plaster ta fita a clinic in, lokacin kusan 3:30 yayi haka ta fita a makarantan Koh sisi Bata dashi haka ta ringa takawa da kafa har gida duk tabi ta gaji ta jirkita gabaki d'aya.


Ta bangaren su Lahab haka Suka ringa yawon su har rana yunwa data Kama Lahab abinci Suka saya dukansu Suka ci,d'aga Nan sai Kuma yamma Suka Kama hanyar gidan su Nabeel.

Da sallama dukansu suka shiga gidan Inna ce zaune tana kwaba lalle zata daura sai yayar Nabeel dake rataye da jakan makaranta a kafadar ta sanye take da dogon riga na atamfa Wanda yasha wanki da guga duk da yasha ruwa Amma tas yake sai gelenta fari medium rataye a kafadar ta,ta rataya hand bag nata maikyau a kafadarta fuskar ta ba kome sai powder data shafa,tunda Suka shigo Adewale ke binta da kallo itakam kallo daya ta musu ta

Please Login or Register in order to submit comment