Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a jikinta,kayansa ya Soma tsinewa binsa tayi da kallo sannan tace"ya haka Abraham kafasan halinda nake ciki shine zaka tafi ka barni a hakan"wani dogon tsaki yaja tare da barin dakin baice Mata kome ba,damke lips nata tayi na kasa ta cija cikin Jin takaicin abinda Nnenna ta musu gabaki d'aya ta katse musu jindadi.

Cikin sati daya sosai Nnenna ta sauyawa Abraham bana Wasa ba ga gudunsa da take don kwata kwata Bata yarda su hadu makaranta ma tun asuba take saka uniform Koh karyawa batayi ta tafi da kafa kafun 7 na safe ta Isa,gabaki d'aya taji zaman gidan Bai Mata ba ga takurin mom a gida gana Jennifer a makaranta,ga wani irin kiyayya da peace ke gwada Mata especially da Abraham ya fita a harkanta tun daga randa ta kamasu red hand yaji gabaki d'aya ya tsane kansa da peace in gabaki d'aya.



**************
Lahab ne tsaye a dakin su Yana Santa uniform don yaune za'a Fara CA Kamar yanda Yama Nnenna Alkawarin zaizo gashi yazo shiyasa tun jiya ya ishi Dr dake dubasa har Saida sukaje hospital aka kunce hannu Kuma Alhamdulilah hannun yayi kyau sosai saidai baya iyya aiki dashi sosai sai dai a hankali.

Fitowa yayi a dakin ya nufi dakin gidan zazzaune suke ana karyawa amma babu mamu da umaima don a cikin satin nan gabaki d'aya sun sauya a gidan shigowa Lahab yayi ya zauna akan dinning in tare da d'aukar plate da spoon ya ibi abinci cup na tea ya d'auka ya Soma karyawa,kallon sa Abbu yayi yace"yau Kuma school zaka kenan"?eh Yaya makaranta xani"dan murmushi Anwar yayi yace"ka manta an koreka a makarantan ne"kallon sa Lahab yayi shima yayi murmushi hade da kallon Abbu da Sauri Kuma ya kauda kansa ganin shima kallon NASA yake yace"ai da babban Yaya zani"wani kallo Abbu ya Masa sai Kuma ya mike tsaye ummu ta dau Masa jakansa Suka nufi kofar,ganin haka yasa Lahab mikewa da gudu yabi yayan nasa a baya har compound Saida ya bari ummu ta aje Masa jaka ta juya kafun Lahab ya nufesa da Sauri ya bude gaban motar ya Shiga.


Fitamin a mota Lahab?"Ni gaskiya Yaya muje ka bawa principal hakuri kafa San yau za'a Fara CA"?CA fa kace CA nawa ne yazo ya wuce da exam bakayi ba"?wallahi Yaya da gaske nake don Allah kaje ka basu hakuri daga wannan jarabawar fa sai dai mu Kira weac"


Shuru Abbu yayi na d'an wani lokaci kafun ya d'aga waya ya Kira su Rahab dake falo su fito yau da kansa zai kaisu makaranta cikin happy muneera ta Mika har Suna rige rige Suka fita Rahab na binsu a baya,bude motar sukayi Suka shiga Abbu yaja suka bar gidan,Suna Isa makaranta sauran yaran Suka nufi class nasu,Abbu a gaba Lahab na binsa a baya Kamar Wanda kwai ya fashe Masa a ciki Yana binsu a baya,har cikin office na principal Suna Shiga Suka tarar da bappa Ado da Nabeel sai papa da Adewale,fuskar kowa ba walwala Kamar hadin Baki gabaki dayansu yau Suka tattaro 'ya'yan nasu a gaba,Zama Abbu yayi Yana fuskantar principal da fuskar sa dake d'auke da fushi kwata kwata babu walwala a fuskar tasa toh haka Suma kaf babu fara'a.


Kallon su principal yayi cikin masifa yace"Kunga bayin Allah ku tattara yaranku nidai nace ya isheni bazan iyya ba akwai makaranta a gombe kuje ku nemi wani ku sasu"da Sauri bappa Ado yace"haba malam wani irin mu sasu a wani kwata kwata wata nawa ne ya rage su kammala karatun shekara biyu da wani Abu kuke fama dasu sai saura Yan watannii ku rabu ma gabaki d'aya shine bazaka iya hakuri su dawo ba"?wani shegen kallo principal ya Masa yace"in zamu rabu sai akace muyi rabuwar tsiya dasu coper fa Suka buga gabaki d'aya kace nayi hakuri akan me? sunan makaranta ta suke so su b'ata Koh me"?Kai nifa na gaji da wahala Nan daman team Nan ya rage musu kawai suje suyi zaman gida su jira register weac da neco in yaso kwa musu a wani makarantan ba nawa ba"sosai principal yayi ta zuba tijara su Lahab bazasu dawo makarantan ba har Saida ran papa ya Soma baci sukayi kaca kaca yayi zuciya zasu koma gida shida d'an nasa, Abbu ganin abin ya Zama haka yasa baki akan zancen dayake mutum ne Mai natsuwa da dattako lokaci d'aya principal ya sauko Suka daidai ta amma fa da sharadin su Lahab na Kara jawo wani abin zasu bar Masa makaranta,papa Kan cewa yayi a raba Adewale dasu a class kowa da ajinsa haka Koh akayi daman Lahab ya koma B aka bar Adewale a A shi Kuma Nabeel aka kaisa D class.



Zaune take tana duba text book in biology data d'auko a Lab tana checking nasa,Zama yayi a kusa da bincin ta har lokacin Bata d'aga Kai ta kalli wanda ya zaunan ba don kwata kwata hankalinta ba'a Kam class yake ba yana ga littafin tane,hannu yasa yaja book in da Sauri tasa hannu zata kwace,sannan ta dago Kai ta kallesa,had'a Ido sukayi da Sauri ta sakar Masa littafin da mamaki tace"yaushe ka shigo"taya za'ayi kisan na shigo hankalinki Naga book duk karatun da kikayi a gida bai isa ba sai kinzo kin dad'a anan,duk nacin kidai baza kici 💯 ba"murmushi kawai tayi batace kome ba shima gyara zaman sa yayi ganin malamin su ya shigo,mikewa sukayi dukan su Suna gaidashi amma banda Lahab shima malamin Bai damu da gaisuwar nasa ba shiyasa yayi Kamar bai gansa a zaune ba,Zama Yan ajin sukayi ya Soma raba musu Questions paper dake hannun su da answer shep,zaro pen sa Lahab yayi dake Aljuhu ya Soma rubutu da hannu Mai ciwo.



30 minutes after yara Suka Soma fita Suna summit shidai Yana zaune Yana rubutu sai Kuma ya aje pen in yayi zaman sa, Nnenna data gama rubuta amsan ta dan masowa tayi kusa dashi murya kasa kasa tace"ka bani papern ka ka karbi nawa bansa Suna akai ba,tana maganar tana Mika Masa papern ta kasa.



Kin juyowa yayi sai magana take Masa har malamin biology su ya ganta ya kwace papern nata bayan ya sata ta rubuta Sunanta ya karba tare da korarta waje da d'add'aya da d'add'aya Yan class suke tashi har aka bar saura mutum biyu Lahab da wata yarinya,lokaci ya kusa karewa Nan da minutes uku Zan karba paper"shine abinda malamin ya fad'a Yana muzurai da Sauri yarinyar ta tashi ta Mika Masa nata ta fita,bayan minutes uku da kansa yaje Kan table in Lahab ta kwaco nasa ya fita.



Mikewa Lahab yayi ya fita a ajin,kusan cin Karo sukayi da Nnenna da duk tabi ta shiga damuwa ganin bai gama ba aka karba"Lahab meyasa Ina ta maka magana ka karbi paper ta kaki"?shine abinda ya Fara fita a bakinta, d'an gyara tsayuwar sa yayi yace"ke ai abin kunya ne Ina namiji mace taban Satan amsa don hakan maganar CA ajesa a gefe muje restaurant muci abinci nasan wata kila baki karya ba Kar ulcer ki ya tashi"ah ah nagode Lahab zanje na maida biology Nan na Kuma duba Civic kasan shine second paper mu"?shuru yayi sai Kuma yace"ok asha karatu lafiya ya wuce,itama tafiyar ta tayi tana Isa lab in ta aje biology tadau Civic da notebook Inda ke hannunta tana dudduba wa,aje Mata laida yayi a Kan table Inda take rubutu yaja kujera Mai facing nata ya zauna tare da harde hannun sa"itama barin rubutun tayi tana kallon sa,hannu yasa ya bude laidan Pizza a kwalin sa babba dashi bude kwalin yayi ya dau yanka daya yasa a Baki tare da tura Mata sauran ya soka ear_P insa a kunne ya aje wayar a gabansa Yana latsawa.



Jawo pizzan tayi duk da bata Saba ci ba hakan bai hanata son ci ba don yanzun batajin shakkan cin Abu a gabansa tunda sukayi zaman asibiti.




*****************
Yau satin sadeeq d'aya kenan baiji muryan umaima ba da farko inya Kira layinta bata d'agawa daga Baya Kuma sai aka kashe wayar gabaki d'aya,abinda ya d'aga Masa hankali kenan ya dawo gombe ba shiri yaji Koh lafiya amma abinda ya Kara basa mamaki yau kwana biyu Yana zirga zirga a gidan su Lahab baya ganin umaima daga ace Masa bata da lafiya bazata iya fitowa ba sai ace Masa Batanan tana makaranta dayake itama tana final Exam nata zuwa next week zasu Gama sai ayi bikin da sati biyu kenan yanzun kwata kwata bikin nasu saura sati uku.



Yaje makarantan su amma Baya ganin ta abinda Bai sani ba shine duk lokacin da umaima ke makaranta in yazo mamu zatace ace Masa Bata da lafiya in Kuma tana gidan sai ace tana makaranta haka bawan Allah Nan yayita gantali a gidan nasu akalla a Rana zaizo sau uku kamar yau ma yazo da safe akace Bata Nan,yanzun ma misalin 12 na Rana Yana compound na gidan tun d'azun yazo ya aike Mai gadi aka cemai Bata da lafiya bazata samu fitowa ba"don Allah baba Koh zakaje kayi musu iso Zan shigo na dubata"dan shuru Mai gadin yayi don yasan harga Allah babu abinda ke damun umaima haka zalika yasan sadeeq tunda sun jiya da umaima Yana zuwa gidan Kuma Halo yaron ya basa tausayi.



daurewa yayi yace toh bara naje na sanar dasu,horn na mota da akayi ne yasa baba maigadi juyowa daga kokarin Shiga falon da yake zuwa wajen gate,da Sauri ya Kama gate in ya bude,motar su Lahab ce ta parking gabaki d'ayan su Suka fitoh,dukan su Suka gaida sadeeq sukayi da fara'a ya amsa hade da baiwa Rahab hannu sukayi musaba'a Yana Masa ya jiki,nuna Masa Lahab daya kusa Isa kofa yayi yace Masa gashi can Mai jikin"dan Allah toh in ba damuwa kamin magana dashi"gyada Masa Kai kawai Rahab yayi yabi bayan su zuwa ciki,har Lahab ya Kwabe riga Rahab ya shigo dakin Yana sanar dashi sadeeq nason magana dashi,Jan dogon tsaki yayi yace"nifa na Fara gajiya haba akan me zaina takuramin inyana da matsala ya nemi yayan yarinya Mana bani ba"da Sauri Rahab yace"haba Lahab Kai kana ga duk gidan Nan banda Kai wazai taimake sa kana tunanin Anwar Koh Shareef zasu sauraresa Kamar yanda zakayi Masa ne"?fita a dakin kawai Rahab yayi ransa a bace don shi harga Allah sadeeq ya Soma isarsa,karasowa yayi kusa dashi ya jingina a jikin motar sa.


Am daman akwai wata Alfarma da nake nema ne Lahab nasan na dameka Koh"?kallon sa yayi babu walwala a fuskarsa yace"in ma ka dameni sadeeq Yana iya kana ga dai makaranta na fito Kuma yunwa nakeji amma ba kome fad'a muji"ajiyar zuciya sadeeq ya sake sannan yace"Lahab wallahi bansan meke faruwa ba kwata kwata umaima yau sati banji muryarta Koh ganinta ba nazo garin Nan ma ganin ta ya gagareni"?




a gajiye Lahab yace"toh Ni yanzun mekake so nayi maka ai wannan magana Abbu zaka tinkara dashi kaga maganar lefe ma daka min karshe abin ya Zama babba ance Wai daga bakina magana ya fito ba daga bakin umaima ba"?da damuwa sadeeq yace toh yanzun Lahab Yaya za'a Yi akan Yar maganar Nan in sake ya tafi har wajen manya bai dace ba ya Kamata mukashe maganar iya nida ita basai iyaye sun shiga ba".




dan shuru Lahab yayi sai Kuma yace"toh ya kake so ayi"?yauwa Lahab nida so nake dan Allah duk yanda za'a Yi Ina son ganinta ne nazo ance min bata da lafiya in ma fitan ne bazata iya ba Ni Zan iya shiga"karkata Kai Lahab yayi sai Kuma yace Ina zuwa,ciki ya koma har dakin umaima Saida ya dudduba amma baiga Koh Mai Kama da ita ba dakin su muneera ya shiga ya tambaye su sukace Bata dawo makaranta ba fita yayi Yana tunanin mezai cewa sadeeq don harga Allah baison karyata mutanen gidan su ya zubar musu da kima a idon surkinsu tunda sunce bata da lafiya Kuma yasan mamu ce, alhalin Kuma tana makaranta,karasowa wajen sadeeq yayi Yana tunanin mezaice Masa gabaki d'aya basirar sa ta kwace in yace tana ciki sadeeq zaiso ya Shiga in Kuma yace Masa tana makaranta wato Yan gidan sun Masa karya kenan,a hankali ya bude Baki yace"eh sadeeq daman dai umaima......sai Kuma yayi shuru ganin motar da ya shigo cikin gidan.......................





🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀


*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 86&87

Motar umaima ne yayi parking bude kofar tayi ta sauko tare da daukar school bag nata ta rataya Yi tayi Kamar Bata gansu ba ta Kama hanyar shiga ciki,baki sake sadeeq yake binta dashi don gaskiya tayi mugun rame Masa sosai ta Kara haske Kamar dai maijin yan gaskiya Alhalin Kuma damuwa ce kawai ke cinta,ai ganin ta giftasu yasa sa binta da Sauri yasha gaban ta cikin damuwa yace"umaima lafiya kwana biyu bana samun ki ya jikin"?a gajarce tace lafiya da sauki sosai"sai Kuma ta yunkura zata Kara step da Sauri Kuma ya sake tareta haba umaima ya Kamata mu samu waje mu zauna akwai maganar da nake so mu tattauna dake ne"?



Shekeke take kallon sa tace"yanzun dai makaranta na fito Kuma Banda isheshen lokaci bazan iya magana da yawa ba"da saurin sa yace toh shikenan amma dan Allah meya faru Inna Kira wayarki Baki d'auka daga baya Kuma na jisa a kashe na shiga damuwa sosai wallahi"wayar ce ta Bata ban ganta ba shiyasa"da mamaki yace haba umaima in waya ya Bata bazaki d'au Koda na muneera bane ki sanar dani in yaso na Aiko Miki da kudi kisai wani"wani kallo ta Masa a fakaice,Wai ya turo kudi ta sai sabo Ina shi Ina saya Mata wayar da take rikewa tunda ya kasa had'a kayan auren azo a gani"ka Bari kawai Abbu yace nabar maganar wayar zai saimin sabo"ah ah umaima Nina dace Dana saya Miki,yanzun dai duk ba wannan ba so nake muje mu samu waje kiban Koh 10 minutes ne muyi magana akan programs Inda zakiyi anan gombe da Kuma kudaden da Zan Baki na gyara da dinki"shuru ta Masa Saida ya gama maganar kafun tace"basai ka kashe kudinka ba na gode duk abinda nake bukata an riga an tanadar mini dinki ma na riga na Kai maganar programs Kuma guda uku zanyi Kuma duka ango baya zuwa so ba bukatan ka sani tana karasa maganar ta zagaye sa ta wuce abinta har lokacin Yana tsaye Yana kallonta Harta bude kofa ta shiga ta maida ta rufe.





Lahab dake tsaye a bayan su kad'an kallon su kawai yake Bai zakud'a daga wajen da sadeeq ya barsa ba,juyowa yayi ya dawo wajen da Lahab ke tsaye yace"Wai Lahab akwai abinda ke faruwa ne Koh yake damun umaima"?kafada Lahab ya d'aga Masa irin shima Bai sanin Nan ba,karban number wayan sa sadeeq yayi kafun ya tafi.


Komawa cikin gidan Lahab yayi direct ya nufi kitchen abinci ya Iba a plate shinkafa da Miya sai cabbage Zama yayi akan dinning Yana ci,goggoji ne ta fito daga sashen Addayiya d'auke da kwanuka masu datti tazo zata shiga kitchen ganin Lahab a dinning yasa ta tsayawa Suna gaisawa tambayar ta labarin d'anta yayi da jikin sa tace Masa da sauki harma an basa Mata a garin su sosai ya Taya ta murna harda tsokana Wai zata Zama uwar Miki Banda sawa surkuwa Ido"da Wasa da dariya ta wuce kitchen.



Bayan isha'i zazzaune suke gabaki dayan su a falo Abbu ya karkato su dukan su,sai dai har yanzun umaima da mamu Basu fitoba,wayarsa dake gefe ya d'auka cikin bacin Rai ya Kara a kunnesa Saida ya kusa tsinkewa mamu ta d'auka"keda yarki ku fito yanzun Nan maza kafun na Bata muku rai"Bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar sa, ba'a dau lokaci ba saiga Mamu da umaima sun fito Zama mamu tayi a daya kujeran Kamar yanda ummu da Abbu da Addayiya ke Kai umaima a kasa ta zauna,Anwar Shareef uzaifa ku fita compound ku bude booth na motar dana shigo da ita akwai Ghana must go manya guda uku kowa ya dau d'add'aya ku shigomin Nan dashi,mikewa sukayi da Sauri Shareef sai zumbura Baki yake Yana hararan tagwaye dake zaune su ba'a ce musu suje ba.




Shigo da kayan sukayi Suka aje a tsakiyar falo umurni Abbu ya Basu su bude bags in su fiffito da abinda ke ciki,zannuwa ne manya manya masu tsada hadaddu da lufaya lace harda materials a daya Ghana must go in dayan Kuma shadodene tirim da hula da takalmi sai Kuma daya bag in dake d'auke da zannuwa colour uku Amma sun Kai turmi hamsin a ciki,kallon Addayiya yayi yace ta xabi turmin zani a cikin bakko dayan da bana anko ba matsowa tayi ta xabi zanuwa masu kyau kala uku Abbu yace Mata ta Kara Amma taki tace wannan ma ya isheta Allah yayi albarka itakam zanuwa ai Wanda take dasu ba'a dinka bama yawane dasu gasu can make a wardrobe.


Mamu itace na biyun zaba kala bakwai ta d'auka harda less dasu materials ta hada,sai ummu ita Kuma tadau kala biyar,anko abbu yace muneera ta zulaihat suzo su d'auka duka kala ukun Suka d'auka Koh wanne d'add'aya sai lufaya da Suka d'auka cikin bakko su Mamu da gyale da takalmi,sauran ankon Abbu yace su d'auka su rabawa Yan uwa gida gida kafun bikin su tabbatar sun kaiwa su nanne nasu gobe goben Nan sai Anwar ango kala goma Abbu yace ya d'auka shadda dasu boyel sauran yaran Suka daddauka Lahab Saida yadau kala biyar biyu nasu Adewale uku nasa,umaima ki Kira goggon ki na tura Mata kudi saikuyi magana zata Miki order Kaya daga Kano za'a dinka Wai a Shan don haka saiki kirata ki gaya Mata kalan kayan da Zaki saka a biki da Wanda za'a Kara Miki ta waya,sannan wa'innan Kuma Haleema kidau goma kema haka ummu sai ku baiwa Addayiya sauran zata rarrabawa kawayen ta Kuma haka sai kudin dinkin daya Basu Amma Anwar yaki karba shida Shareef sunce zasu biya a aljuhun su, Yana karasa maganar ya mike yabar falon Addayiya na binsa da sanya albarka.



Mikewa Lahab yayi ya dau shaddan ya Kai dakin su ya aje wanka yayi ya kwanta,washe gari a makaranta sunyi Math's da chemistry dayake sunada paper uku ne harda Islamic aka had'a musu,dayake makarantan basa bada paper a rarrabe sai an gama CA duka suke hadawa gabaki d'aya a raba a Rana daya.


Bayan ya dawo gida da yamma sadeeq ya kirasa tare da rokon sa akan ya fito wajen gate don baison shiga gidan sako zai basa ya baiwa umaima zai wuce bauchi ne,bayan ya fito kwalin waya ya Mika Masa tare da rokon sa akan ya taimaka ya baiwa umaima sannan dan Allah ta kirasa,ba musu ya karba hade da Masa alkawarin insha Allah zata kirasan,bayan wucewar sadeeq cikin gidan Lahab ya dawo har dakin umaima ya shiga hannu yasa ya tura kofar dakin nata zaune take cikin kayan bacci wando da riga sai dai ba Mai bayyana tsiraici bane Yana da duhu da laushi,kanta d'auke da holan bacci rike take da wayarta Kiran iPhone 11 chatt suke da goggon ta sumayya da Abbu yace ta nemeta suyi magana hotonan materials da zata sai Mata dasu purse da sauran surutun da zata saka a program's take turawa,taji an turo kofar a tunanin ta muneera ce Koh zulai don Mamu bata cika shigowa ba saidai ta kirata ita taje ta samesa hakan yasa bata bar abinda take ba har Lahab ya shigo dakin Zama yayi kusa da ita yasa hannu ya karbi wayar hannunta Yana jujjuya wayan hade da kallon ta.



Mika Masa hannu tayi fuskarta babu walwala tace"ka bani wayata baka ga Abu Mai muhimmaci nake bane"?eh Naga abinda kike amma fa ki sani duk muhimmacin sa baikai sadeeq bakoh"?



Mikewa tayi Rai bace zata bar dakin da Sauri shima ya mike ya Isa kusa da kofar da Sauri ya rufe hade da zare key in ya rike a hannun sa yace"umaima zauna magana zamuyi dake"hararan sa tayi tace Kai asuwa da Zan tsaya na saurare ka kaga nifa banson damuwa yanzun"hhh bakison damuwa nidai yanzun kawai ki zauna muyi magana malama"Zama tayi tana kallon wani direction daban"umaima Zan fada Miki gaskiya duk da da ciwo amma fa ki sani kaf duniya babu masoyin ka sama damai fada maka gaskiya Zan tambaye ki tsakanin ki da Allah umaima meyasa Kika chanjawa sadeeq"?



Shuru tayi bata basa amsa ba har lokacin bata Kara kallon sa ba"umaima tambayarki nake meye faru a tsakanin ku har Zaki Masa karya kice wayarki ya bata Alhalin Kuma gashi a hannunki kin Sasa ya sai Miki wani haba umaima duk wannan na menene"?Koh akan kayan auren ne kema Bai Miki ba"?hawaye ne ya cika Mata Ido a hankali tasa hannu ta goge wa'inda Suka zuba Mata cikin shesheka tace"haba Lahab ya zanyi da Raina ne Taya za'a ce sadeeq zaimin Kaya haka a ganina Yana da kudin da zaimin fiye da hakan amma ya kasa"toh ke umaima yanzun abinda ya dameki shine kankantan kayan?a tunanina babu kayan da za'a Miki ya d'aga darajan ki bayan Wanda Kika saka a gidan Nan sannan kinsan dalilin sa nayi Miki kadan inne"?kuka ta fashe dashi tana magana"Ni duk ba kankantan kayan bane yafi Bata min rai Kamar d'aukan kayan da akayi a waya aka had'a da hotona ana yadawa a online Wai duk girman kaina ga lefen da aka min,sannan haka maganar yake ta yawo a school namu abin shiyafi mini ciwo wasu kawayena ma don su tabbatar yasa su zuwa da sunan kallon Kaya,amma Basu samu kallo ba don Abbu yahana a fitar,shine suke cewa Wai kunya ya Hana a fitar jama'a su gani"





girgiza Kai kawai Lahab yayi yace"ke dai umaima sai kace yarinya karfa ki manta yanzun fa 25years kike dashi Amma kin kasa magance dan matsalan Nan"ke Banda abinki yanzun a tunanin ki in sadeeq ya Miki wannan Kaya har abada bazai Miki Wanda ya fisa bane Nan gaba karfa ki manta Mata da yawa sun samu kayan aure na bugawa a jarida amma auren baiyi lastic ba meye amfanin sa,ba yawan Kaya bane aure ah ah albarka ake nema kawayen ki masu Miki dariya yanzun haka a cikin su wata da sadeeq zai nemi auren ta Koh babu lefe ba goro sadaki kawai in zai tabata da gida wallahi tanason,kina ga guy kyakkyawa dashi ustaz ki tsaya kina Masa yanga,amma shikenan in Baki so ni Zan iya zuwa na samu Abbu a fasa bikin kawai sai yayi lefe 24 box's shikenan"?ya karasa maganar tare da jefa Mata kwalin wayar akan gado da wayan ta duka.


Da Sauri ta Mike tsaye ganin zai fita a dakin a shagwabe tace"toh Ni yaushe nace maka bana sonsa Kuma ai Vance a sauke sarti ba"?juyawa yayi ya kalleta cikin Serious yace"nifa na gama magana mundin sadeeq ya kirani yace Baki kirasa ba wallahi tallahi saina gayawa Abbu,Bai saurareta ba ya fita a dakin ya maida kofar ya rufe.



Washe gari Lahab ya d'au Kaya yakai dinkin duka kala ukun sa ya baiwa Adewale da Nabeel nasu Suma Suka Kai dinki don kowa da telan sa saboda yawan rikicin su da teloli daman Nabeel telan matane vana maza ba,zancen Ruky da Ahmad har manya sun shiga iyayen Ahmad sun kawo kudin goro naira dubu 50 cicib aka saka musu sarti Nan da wata biyu masu zuwa Nan take ahlin gidan su Ruky da Ahmad Suka Soma shirye shiryen biki,mubeena data tsinci zancen zuciyarta ne kawai Bata hadiye ta mutu ba amma har ciwo Saida ta kwanta na kwana biyu tsabar damuwa.



kuma rukyn ce ta tura Mata message ta what'sApp akan an saka ranar auren ya zancen anko da zasu fitar, Bata Mata reply ba sai ma blocked inta da tayi don ita gani tayi Kamar cin fuska Ruky ke Mata, daman sun riga sun kammala exam nasu Suna hutu yanzun.




*******************
Yau Alhamis saura kwana daya a Fara biki gidan su Lahab cike yake tam da jama'a bakin da sukazo aure abinka da d'aga bikin farko a family sosai Yan uwa ta kowani kusurwa Suka allara gida ya cika makil da Yan uwa Mata,Lahab ne ke shirga kayan sa a jaka zai bargidan saboda karancin dakuna da sukayi kadan dan su

Please Login or Register in order to submit comment