Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake gashi fresh dashi idanu ya zaro daidai saman maran ta ta sama ba kome bane sai wani tattoo da ya gani na hoton skeleton (danger) shafa tattoo in yayi a hankali Yana Kara bin abin da Ido Kaine sai katsushuwan kafa da akayi cross dashi.



Lumshe idanunsa kawai yayi ya zare Mata pant in jikinta ya Soma Mata wankan Saida ya game jikinta da maganin tass kafun ya sanya Mata Sabon sutura duk idanunsa a rufe yake kome, gudun kada yaga abinda zai hanasa control na kansa yanzun in ma dauriyace kawai dagota yayi daga Kan taburman ya maidata Kan gado,ya kwantar tare da mikewa ya fita waje malam in ya Kira yazo ya basa no-no ya Bata Bata nonon yayi Mai magani"ka zauna a wajen ta ku kwana tare insha Allah zuwa can dare zata farfado saika Bata ruwan rubutun Nan tasha" amsa Lahab yayi Yana ta ma malam godiya.




Zama Lahab yayi bayan fitar malam ya dau kur'ani Yana karanta Mata a hakan har bacci ya daukesa zaune rungume da kur'ani a hannu baima San bacci ya fizgesa ba can dare ya bude Ido da Sauri Jin kakkarin amai mikewa yayi ya kunna Kwan fitila dake gefen gadon, Nnenna ce ke ta amai kur'an ya aje Kamata yayi ya saukar da ita a gadon Karan ya dukar da ita tana ta amai Aman no-no ne fari tass tana gamawa ya dauko Mata butan dake dakin ta wanke bakinta a daren ya goge wajen hade da fidda abubuwan da ta Bata Koh kyankyami babu.




Zaunar da ita yayi Yana Mata sannu gyada Masa Kai kawai take ya mike zai dauko rubutu da Sauri ta rike hannun sa, d'an murmushi yayi yace"ki kwantar da hankalin ki dare ne karkiji kome babu Inda zanje na barki gyada Masa Kai tayi ta koma ta kwanta shi Kam ruwan maganin ya d'auka yayi Bismillah ya kafa Mata a Baki sosai Tasha sannan ya janye ya maidata ya kwantar"Lahab meyasa ka yarda ka aure Ni ba tare da ka tuna abinda zai biyo baya ba"da mamaki yace"kina nufin kinsan abinda ya faru yau"?kwarai ma kuwa Lahab duk abinda ya faru Ina ji kawai bana iya sarrafa jikinane,Lahab kayi kasada a kaina da yawa Bai Kamata kayi wannan b......Bai Bari ta karasa ba yasa hannu ya rufe Mata Baki yana cewa"yanzun duk wannan surutun baida amfani burina shine ki samu lafiya haka zalika ki koma kallonki Kamar da wannan shine burina"




Gyada Masa Kai tayi ta gyara kwanciyarta shima kwanciyar yayi a haka idanun su biyu dukan su har asuba, sallah Lahab ya fita a masallaci yake sanar da malam ta farka daga Nan dakin in Suka shigo dukan su lokacin tana kwance Kamar Mai bacci da sallama malam ya shigo dakin ya nemi waje ya zauna sannan ya Kira sunan ta shuru tayi Bata amsa Masa ba matsowa kusa da ita Lahab yayi ya leka fuskarta sannan ya kalli malam yace"malam tayi bacci"girgiza Kai Mal yayi yace"idanunta biyu ki mike kimin bayani sanann ki amsa min tambayata wannan shine Karo na biyu Kuma na karshe muddin Baki gayamin alakarki da Mafia ba zaku tattara ku bar gidan Nan Banga amfanin zamanki a ciki ba"?




A hankali tasa hannu ta riko na Lahab gamgam ta rumtsa idanun ta da karfi kafun ta Soma magana"nice mataimakiyar shugaba a kungiyar mu haka zalika na kasance daya daga cikin su tun shekaruna bai.....................................





*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*


🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



tun shekaruna bai kaiba amma wallahi ban taba Shan jinin dan Adam ba"wani kallo malam ya Mata babu Wasa yace"taya Zaki kasance cikin mabiyan Mafia Kuma kice min baki Shan jini"kuka ta Fara a hankali wani tsawa malam ya daka Mata ya Kara jefo Mata tambaya"nace ki min bayani menene alakarka da Mafia"?jikinta har rawa yake ta Soma magana"nima ban sani ba abinda na sani shine da Rana zanyi rayuwa a cikin Yan uwana mutane in dare yayi kuma na kwanta bacci sai na Kama rayuwa Kuma a cikin wasu mugayen mutane bansan yaushe na Shiga ba nadai San sunce Ni Yar uwarsu ce haka zalika sunce Ina da gadon mukami Mai girma a kungiya"





Kina nufin kice min Baki San kome akan kasancewarki a cikin su ba"da Sauri tace wallahi malam bansan kome ba tun da nayi wayo in dare yayi na kwanta sai na halakci taro duk ranan lahadi haka zalika ansha kashe mutum asha jini a gabana amma Ni tunda nake ban taba Sha ba bansan ya ake Sha ba haka zalika ban taba kashe kowa ba"da mamaki Lahab yace taya zakice baki kashe kowa ba Kuma kina cikinsu ana kashewa a gabanki"?hannu malam ya d'aga Masa sannan ya kalle Nnenna"inaso ki fadamin wanene ke kiban labarin ki"





dan kwantar da kanta tayi a kafadun Lahab tanajin wani irin ciwo a kirjinta a hankali ta Soma magana"Ni Karan kaina bansan wacece Ni ba abinda na sani kawai shine na tashi na tarar da papa na shine kome nawa yace mahaifiyata ta rasu tun Ina kankanuwa Ni ban ma santa ba Koh hotonta ban taba kallo ba,sannan kowa a kauyen mu guduna yake ana cewa Wai Ni mayya ce"malam tambaya ya Kara jefo Mata"meyasa ake ce Miki mayya"dan sunkuyar da kai tayi cikin zullumin tace"saboda duk lokacin da na Fadi mummunan Abu akan mutum sai ya faru dashi haka zalika Inka nemi cutar dani zaka mutu Wanda ni Banda wani masaniya akan mutuwar su"gyada Kai malam yayi sannan yace shin akwai wani abinda kike kiwo Koh dabban da kike tare dashi a gidan ku"?



da d'an murmushin damuwa tace"eh Ina kiwon kule"yakai shekara nawa a hannun ki"kusan shekara goma"yanzun Ina yake"?nima ban sani ba malm tunda nabar gidan mu ban Kara kallon sa ba"toh Ina so daga yau Koh kin gansa karki d'aukesa haka zalika karki sake kiwon Koh wani dabba a yanzun har sai jikinki ya warke rass"toh malam mikewa yayi ya fita kallon ta Lahab yayi yasa hannu ya taba gashinta sannan yace"kanki yayi datti sosai Koh muje waje na wanke Miki tunda kinji sauki"?




Gyada Masa Kai tayi ya Kama Mata hannu Suka mike,waje Suka fita ta zauna a gefe yaja ruwa ya dau babban kwarya yazo ya aje a bayan ta omo da matar malam ta basa ya jika ya saukar da Kan nata ya Soma wanke Mata, tass ya wanke Mata Kai sannan ya debo wani ruwan yakai Mata bandaki ya dauko Mata wani wankeken Kayanta ya makala Mata kafun ta fito wanka ya wanke Mata kayan data cire da nasa da Wanda ta bata duka ya Shanya matar malam sai tsokanarsa take Wai tun ba'a lale amarya ba an Zama mijin hajiya shidai sai dariya yake,bayan ta fitone ya Kama hannunta harkan shimfidar da ya Mata a waje, kwanciya tayi shi Kuma ya zauna a gefenta Suna dan Hira kad'an kad'an malam ne ya shigo gidan hannun sa d'auke da kaza mikewa Lahab yayi yace ya tashi ya gyara Kazan mikewa yayi matar malam ta tafasa ruwan zafi ta basa bai taba gyara kazaba sai yau haka yayita fama matar malam na tayasa Suka gyara Kazan ta daura Masa a wuta Yana daka tana hura wuta,malam ya kawo magani ya Basu Suka dafa dashi lumus Suka dafa Naman juyewa sukayi a kwano Suka kaiwa malam amma sai yace wa Lahab ya kaima Nnenna taci da mamaki Lahab yace"malam ka manta batacin nama"?





Ka Kai mata nace Kuma ka tabbatar taci toh Lahab yace ya dau kwanon aje Mata yayi a gaba sannan yace ta Mike mikewar tayi yasa hannu ya yago Naman cinyar ya nufi bakinta dashi da Sauri ta rike Masa hannu tana girgiza Kai amma batayi magana ba"kici malam ne yace"?ba yanda ta iya haka ta amshi Naman cikin tsoro ta Soma taunawa tana rumtsa Ido tunda take a rayuwata Bata taba cin nama ba haka zalika ma batasan dandanon nashi ba sai yau kwata kwata sai taji Bai Mata ba Bai Mata Dadi ba ranan dataci shinkafa Mai miyar nama a gidan goggoji ciwonta ya tashi toh yafi Naman saukin rashin dadi"kauda fuska tayi tana yamutsa fuska sai Kuma amai ya biyo baya Aman Naman tayi na naman data ci sosai take amai Kamata yayi Saida ta Gama Aman kafun ta koma ta kwanta Naman ya tasa a gaba bai damu da maganin dake ciki ba ya cinye tass ya aje kwano.





da malam ya tambaye sa taci,cewa yayi ita taci malam bai Kara magana ba tun kallo d'aya daya Masa, washe gari baru malam ya yanka aka sake dafa Mata da magani aka bata Nan ma taci tayi amai amma baikai na jiya ba akalla Saida akayi sati ana bawa Nnenna nama a hankali ta Fara daina Aman Kuma dandanon ya Fara Mata kad'an kad'an sai dai har gobe idanunta Basu budu ba,yau malam ya kirasu dukan su bayan sallan isha'i kallon Lahab yayi yace"ya Kamata ka koma gida Lahab Bai Kamata ka cigaba da Zama anan ba yanzun haka ana Neman wata biyu da wani Abu jikinta yayi sauki sai abinda baza'a rasa ba bazan iya cewa kome akan taba? dan Ni Karan kaina bazan iya cewa wani abuba tunda bansan gaskiyan lamarin taba abinda na sani kawai d'aya ne tana da alaka da Mafia haka zalika abinda ta fada gaskiya ne Kuma insha Allah wata Rana kome zai warware muku kafun Nan Ina so ka koma gida Zan baka maganin da zaka dinga diga Mata a Ido sai Kuma ya juya harshen fulatanci yaci gaba da magana don baison Nnenna taji"idanunta bazasu bude ba har sai ranan da kuka rabe juna a matsayin ma'aurata Kuma cikin tsigar shauki da sha'awar juna dukan ku dan haka bazan tilasta muku ba duk randa kuka ji zaku kasance da juna in Allah ya yarda kome zai daidai ta"sunkuyar da Kai Lahab yayi wani irin mugun kunya ya lullubesa itadai Nnenna sai Ido don bajin abinda suke fada take ba haka zalika hausar ma ba iyawa tayi ba duk abinda malam ke tambayarta cikin turanci yake Wanda Lahab yasha mamakin iya turancin malam Harya kasa hakuri ya tambaye matar malam anan take cemai babu Inda malam baya zuwa bada magani amma ada sai yanzun da tsufa ya kamasa kafun ya zauna waje d'aya,sosai malam ya musu Nasiya bana Wasa ba,ya hadasu da maganguna harda Wanda Lahab zaina yiwa kansa na wanka na hayaki harda nasha Dana digawa haka zalika yace duk abinda zai sake tashi suzo su sanar dashi godiya sosai Lahab ya ma malam cikin Jin Kewan rugan washe garin tun safe sukayi wanka sukabi gida gida Suna ma 'yan rugan sallama sabo tirken Wawa d'an wata biyun nan sosai Lahab ya Saba da jama'ar garin.





*****************
tafiya suke akan keken Shanu daya d'aukosu daga cikin rugan jugudun Lahab yayi cikin damuwa da zullumi sai yanzun yake tsoron abinda zaije ya tarar a gida,saukesu akayi a wani kauye da zasu samu machine ya fito dasu cikin local government in Hawa sukayi sanan Lahab ya d'au wayarsa kunnawa yayi ganin network ya dawo ya bugawa Adewale amma bai d'auka ba Saida ya Masa kusan five miss call kafun ya d'auka baidai ce kome ba Lahab ne ya Soma magana"Ade Dan Allah Koh zaka shigo local government in Nan kazo k d'auke mu"a gatse Ade yace au baka San hanyar gidan bane Koh baka da kudi"?Dan sauke ajiyar zuciya yayi ya kalli Nnenna dake rike da hannun sa gangataran tamkar Wance akace zai gudu ya Barta yace"Adewale kasan Shiga gari da Nnenna tare dani akwai matsala ka dai zo dan Allah"katse wayar Ade yayi baice zaizo ba haka zalika baice baraizo ba.







Mikewa Lahab yayi ya dago Nnenna da niyar su shiga mota kawai koma mezai faru ya faru tunda yanzun har yamma yayi Suna tsallaka titi ya hango Adewale ya bude marfin mota ya fito karasawa yayi kusa da Aden Yana rike da hannun Nnenna kallo daya Ade ya Masa sai kuma ya kauda fuskar sa,Lahab baiyi zuciya ba yana rike da hannun Nnenna ya bude bayan mota ya sata kana ya bude gaba shima ya shiga ya rufe bai cewa Ade kome ba Ade bude kofar yayi shima ya shiga kawai yaja motar Suka Lula dan juyawa yayi Suka had'a Ido da Lahab murmushi Lahab yayi yace Adewale kanajin haushi na Koh"?girgiza Kai Ade yayi yace"akan me xanji haushin ka Kuma bayan abinda kaga dama kake"haba Ade ka juya kaga halinda yarinyar Nan take ciki yaci a tausaya mata"




Ade dai baice kome ba tafiya Suka cigaba dayi cikin hukuncin Allah har Suka Shiga gombe ba'a gane Nnenna ba kwata kwata saboda shigar Fulani dake jikinta ga gashinta da kitson dake kanta, parking Ade yayi Kamar yanda Lahab yace tunda Suka nufo cikin tsakar gari sauka yayi tare da cewa Ade yakai Nnenna gidan goggoji Jin hakan yasa Nnenna kiransa da Sauri bude kofar yayi ya shiga ya Soma Mata magana a hankali cikin lallama"Kinga ki bisa kuje gidan goggoji Ni gidan mu zan nufa Kuma Banda tabbacin zamu gana Nan kusa ki kula da kanki Allah ya Baki lafiya magani na Booth"gyada Masa Kai kawai tayi hawaye na taruwa a idanunta,Ade Kam Jan motar yayi baice kome ba.





Lahab tunda ya tare machine ya shiga ya nufi unguwan su zuciyarsa ta Soma bugawa wallahi baisan amsar da zai Basu gamshashiya ba akan Inda ya Shiga gashi bayason musu karya Koh kad'an a hankali ya sauka a keken Yana bin kofar gidan nasu da Ido kudi ya baiwa Mai keken a hankali ya nufi kofar hannu yasa ya kwankwasa sai Kuma ya tsaya Jin muryar Mai gadi na cewa wanene Yana bude kofar sai Kuma ya tsaya Yana kallon Lahab da kayan jikinsa sai Kuma yayi shuru kwata kwata yanda Lahab ya fige Bai Masa kama da Rahab Inda ya gani d'azun a cikin gida ba da Sauri yace Lahab?




Murmushi Lahab yayi ya gyada Masa Kai aiko da Sauri ya bude kofar ya Soma salati cikin Al'ajabi ya ruga cikin gidan da gudu Yana kwalama Abbu kira da iya karfinsa Lahab Kam binsa yayi a baya a hankali,Yana tura kofar ya dan tsaya ganin kattafanin jama'ar gidan su a tsaye Suna jiran karasowar su don Mai gadi tuni ya kusa ya tsaigunta musu sunkuyar da Kai yayi lokacin da yayi Ido hudu da Abbu bawan Allah har wani Rama yayi na rashin amanar sa,da gudu Rahab ya tawo yazo ya rungume dan uwan nasa dan dukawa Lahab yayi a hankali ya Kara makale dan uwan nasa da karfi kowa yaga kaunar Nan yasan na sakanin jini da jini ne,da Sauri ya sakesa Jin Addayiya na salati fitowarta kenan daga dakin ta hannunta rda canula.






Kuka ta fashe dashi ganin Lahab a hankali ta Soma takawa tana nufo su da Sauri Lahab ya mike ya nufeta fadawa kawai yayi a jikinta ya sake kuka Wanda shima baisan kukan menene ba,zazzaune suke sun tasa Lahab a gaba tun ana lallaman sa ya fad'a musu Inda ya shiga har ran muzammil ya baci Wanda zuwan sa kenan yau don B'atan Lahab in tun ana daukar Wasa Abu ya Zama gaskiya sannan anzo ana Masa tambaya ya mannawa mutane hauka mikewa yayi Rai bace Yana zare bell in jikinsa ya Soma magana"wallahi Lahab inka kuskura ka batamin Rai jikinka ne zai gaya maka dan iska kawai"da Sauri Abbu ya d'aga Masa hannu tare da cewa kada Wanda ya sake tambayar sa Inda yaje duniya ce duk abinda ka shuka shi zaka girba sudai sunyi iya bakin kokarin su a kansa duk Wanda ya zagesu Allah ya Isa sai Kuma yace daga yau Kar Wanda ya sake tambayar Lahab Ina zashi duk Inda yaga dama yaje duk lokacin da yaso ya dawo Yana karasa maganar Rai bace ya mike yabar falon da d'add'aya kowa ya watse don Abbu baiya fushi amma in yayi abin Baya kyau Sam.





Zama Lahab yayi akan katifarsa lokacin da ya Shiga dakin nasu lumshe Ido yayi rabonsa da ganin haske haka Harya manta sai Kuma ya mike ya shiga wanka wanka yayi sosai ya kimtsa jikinsa cikin kayan baccin sa wando da riga kwanciya yayi ya lumshe idanun sa,turo kofar dakin akayi Addayiya ce d'auke da plate na abinci sai drink's mikewa yayi da Sauri ya karbi plate in ya aje a gefe itama Zama tayi tasa hannu ta shafa kansa a hankali ta Soma magana"Lahab Sam banji dadin abinda kayi ba ka d'aga Mana hankali haka zalika kasa mu a damuwa karka Kara Mana irin haka Kamar yanda yayan ka yace karmu sake tambayar ka bazan tambaye kaba amma dan Allah karka sake irin wannan?gyada kansa yayi ya kwantar da kansa a cinyarta hawaye na taruwa a idanun sa hannu tasa ta dauko abincin ta bude tare da d'aga kansa tana cewa ya tashi yaci ba musu ya karbi plate in ya Soma cin abincin daya Dade baici ba.





tunda ya kwanta yake juye juye Sam ya kasa bacci tunanin matar sa yake"Lahab yaji Rahab dake katifar sa ya kirasa"amsawa yayi tare da mikewa zaune shima Rahab mikewa yayi ya ce"bakayi bacci ba har yanzun"eh banjin bacci ne dan uwa"uhmmm kasan me"ah ah saika fada"Abbu ya Mana registration na weac da neco insha Allah zuwa next week za'a Fara waro Ido Lahab yayi yace kana nufin yanzun an rufe biya kenan"?kwarai ma kuwa.


Rumtsa Ido Lahab yayi yaci burin ya biyawa Nnenna duk da Bata kallo sai ya bada a Mata duk da yasan hakan prohibited ne a exam,komawa yayi ya kwanta Rahab ma kwanciyarsa yayi Bai Kara cewa kome ba ba,a cikin kwanakin Nan da Lahab yayi babu Wanda ya Kara tambayar sa Inda yaje Mami ma batazo ba shima ya kasa zuwa wajen ta saboda tsoro gashi yau satin sa daya ya muzammil ma ya koma a yau Suka Fara jarabawar neco babu Wanda ya sanar dashi zancen jarabawar Koh yaje yayi sai Rahab don yanzun Abbu baya Masa magana Koh gaidashi yayi baya amsa wa,sun cigaba da zuwa school harda Adewale Nabeel ma duka Yana zuwa duk da Lahab baisan waya biya Masa kudi ba yadai ganshi shima a hall Kuma ya tambaye sa Inda ya shiga sharesa kawai Lahab yayi Bai ce Masa kome ba Kuma sosai yaji ya Kara son Ade watoh duk da sun samu rashin jituwa akan Nnenna amma babu Wanda ya sanar wa da labarin auren sa.






Kamar kullum yau sun tashi jarabawar har yamma Suna fitowa lahab ya dan kalli Adewale ganin Nabeel hankalin sa baya kansu yasa sa kama hannun sa Suka zagaya bayan exam Hall shidai Ade Ido kawai yake binsa dashi Jin abinda yace"dan Allah so nake ka daukomin Nnenna ka kaimin ita garden City mu hadu a acan bayan mangariba dan Allah"wani kallo Ade ya Masa kafun yace"Kai me yasa bazaka je ka dauketa ba?kaga Lahab ka daina Sakani a shirgen ka da yarinyar Nan fa bana so"





Kawa Allah kayi hakuri Ade kasan Abbu yace naje duk Inda Naga dama ya cire security na gidan mu Amma abinda na gano wallahi yasa ana bibiyata duk Inda na shiga muddin aka ganni naje gidan goggoji za'a sawa zuwan ayar tambaya"shuru Ade yayi sai Kuma yayi tsaki ya juya yabar wajen murmushi Lahab yayi ya shafa kansa sannan yabi bayan abokin nasa, Nabeel ya hango tsaye Yana dubasu ganin su yasa sa matsowa kusa dasu yana cewa "muje gidan mu ka gaida Inna duk ta damu a kanka ga Adda mubeeena kamma ba'a magana"girgiza Kai Lahab yayi yace"kayi hakuri Nabeel bana fita tunda na dawo amma in Allah yasa muka gama exam lafiya zanje.






Ba kome shine abinda Nabeel yace Yabi bayan Ade Suka bar school in Lahab Kam gida ya koma wanka yayi ya tafi sallan mangariba daga Nan wani mall ya wuce sayyayyan Kaya ya Mata sosai ya had'a da kayan ciye ciye laida guda daidai ya fita a mall in ana Kiran isha'i tsayawa yayi yayi sallah kafun ya nufi wani tukuban nama yasai kaza sukutum guda biyu Keke napep ya hau Yana kallon motar dake binsa a baya tsaida keken yayi a kafar wani gida ya bude gidan ya shiga suturan jikinsa ya Kwabe yasa wani sabo daya saya sanin da yayiwa gidan Mai kofa biyu ne irin gidan Nan guda biyu da ake musu kofa a katangan tsakiya bude daya kofar yayi ya fita abinsa ta wani layi ma ya fito Yana dan dube dube ya tare Keke sai garden City.






Yadan jima kad'an kafun Adewale Suka karaso rike yake da hannun Nnenna had'a fuska Lahab yayi Yana kallon hannun har Ade ya karaso,cikin masifa ya Soma magana"wannan wani irin Abune ya zaka rike Mata hannu"?da dariya a fuskar sa duk da baison Yi amma wallahi Lahab ya basa yace"idan ban rike Mata hannu ba Lahab Ina Zan rike gani nayi Bata amfani da Sanda Kuma haka zalika bazan barta haka ba Koh ya kake so nayi maka ne Wai"hararan sa yayi ya fizge hannun ta ana Ade ya rike Yana magana kasa kasa Yana cewa matar aure zai rike kaza kaza shidai Ade wani table ya nema ya zauna nesa dasu ya zaro wayarsa Yana dannawa.




Zaunar da ita yayi akan dardumar daya shimfida musu a kasa Yana bin kayan jikinta da Ido kayan ya kode sosai,gaidashi tayi ya amsa Yana cewa"Labiba kiyi hakuri ki Kara hakuri da jarabawar ki Allah ya bamu ikon cinyewa kinji"amsa Masa tayi da toh kana ya bude laidan Kazan,Naman ya yago yasa Mata a baki bude bakin tayi ta amsa ta Soma ci,ya Kuma dauko hanken ya goge Mata gefen bakinta sannan ya sake yago wani Naman Yana Kai Mata Baki daidai lokacin yaji tsayuwar mutum a kansa da Sauri ya d'aga Kan nasa sai Kuma ya zaro Ido cikin mamaki Wanda ya gani agun............................








*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*


🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



Farida murmushi tayi tace lallai ma Lahab Ni ka shekemin tawa soyayyar Kai Kuma kana raya taka Koh? sai Kuma ta gyada Kai tare dayin kwafa tabar wajen binta yayi da Ido harta mule kafun ya maida kansa ga Nnenna data jefo Masa tambaya "Wai wacece?shuru yayi Yana daukar drink ya kafa Mata a Baki kin bude bakin tayi ta rufe sa gangataran d'an dakatawa yayi Yana kallon ta da mamaki yace"bazaki karbi juice in ba"?nace maka wacece"?dariya ya Soma cikin dakewa yace "kishi Koh"?





babu wani kishi kawai dai naji yanayin da tayi magana Kamar tana Jin haushin Kane duk da ba yarenku nakeji sosai ba"ba kome shine abinda yace Mata sannan ya Kara da cewa"Nnenna mun Fara exam naso na biya Miki amma Allah baiyi ba"ba kome Lahab hakama na gode matukar babu abinda zance maka sai godiya kamin goma Sha akan wannan basai ka ce kome ba"amma naso na biya Miki wallahi"dariya ta danyi tace toh Inka biyamin ka fadamin da wani idon zanyi exam"?kamo wani hiran yayi sukayita Hira har Saida Ade ya gaji da Zama ganin 10 na dare yayi yazo yace ma Nnenna ta tashi su tafi,kayan Lahab ya bata da sauran tarkacen Ade ya d'auke sai gidan goggoji.






Lahab bai koma gida ba sai kusan 10:30 na dare babu Wanda yace Masa kalallahu haka ya shiga ya kwanta,sannu sannu kwana nesa su Lahab harsun kammala exam nasu Suna jiran result har yau Lahab baije gidan su mubeena ba Kuma bai hadu da itaba haka zalika bai yarda yaje wajen Mami ba in ma yaji tazo baya fita nukuwa yake a daki harta tafi sosai yake Jin shakkar haduwar tasa da ita dan baida amsar da zai bata,duk lokacin da take son kallon Nnenna Yana rokon Ade ya d'auko Masa ita, in Kuma yaji Yana son Jin muryarta wayar goggoji yake Kira ta hadasu sosai soyayya Mai zafi da tsafta ya shiga tsakanin su daidai da rana daya Lahab bai tabajin dana sanin tarayyar su da Nnenna ba Yana sonta bana Wasa ba duk da kalaman soyayya

Please Login or Register in order to submit comment