Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da jama'ar gari basu taba tsammani ba tabbas sunga ikon Allah daman akace Mai hakuri na tare da riba Allah ya kawo wa mubeena Miki balarabe Kuma saurayi ba magidanci ba,bugu da Kari Yana tsananin sonta da kaunar ta a bikin su ba karamin bajinta Lahab yayi ba duk da su basa kayan aure Koh gara Amma bikin yayi armashi kudi yayi kuka kome daya shafe mubeena Lahab ne yadau nauyin sa har aka kammala biki lafiya aka dagata daga naija zuwa Libya.






Iyayen Deyana sunzo bikin don haka Basu koma ba Suka nemi dady(baban Abraham) Wanda kunya ya hanashi Koh zuwa Inda Deyana(Nnenna)take,haka zalika momy itama tayi dana sani sosai,dady shiya dau iyayen Nnenna ya kaisu har Enugu daga nan Ya wuce dasu Edo state duk da dangin papa(marikin Nnenna daya rasu )Basu rike Nnenna ba amma iyayen ta sun musu goma na arziki wa'inda Nnenna ta sani da wa'inda Bata sani ba duk an musu abin Alkhari anan Nnenna take Jin labarin matar papa data rasu Ashe tunda ta dawo Libya da yarinyar(Nnenna)Kuma tace yarta ce ta Fara kudi Kamar na hauka yaranta data tafi Libya ta barsu su uku kaf Suka mutu saura Nnenna kawai Kamar tsafi saiga arzikin matar papa ya Soma karewa wata Rana kawai aka waye gari gidanta da ita ya Kama da wuta ta mutu murus Amma Nnenna Babu abinda ya sameta duk da kuwa tana cikin gidan wannan ne musabbabin rikon Nnenna ya dawo hannun papa,Kuma da iya gaskiya suka rike Nnenna Babu Wanda ya taba tsammanin ba yarsu bane.





Papa yasha tsangoma da tsana akan Nnenna saboda lakaba Mata maita da ake Amma Bai hanasa cigaba da rikon taba.






Bayan tafiyar iyayen Deyana Lahab yaje London ya tattaro duk wani Abu nasa dake can Mai amfani ya dawo nageria ball ma yace yanzun yayi girmeta bazai cigaba da bugawa ba ya barwa yara shi yanzun uban matasa ne, hospital babba ya budewa Deyana tana aiki ga yaran sa na zuwa makaranta duk karshen hutu zasu koma wajen Mami su Mata kwana biyu Su karasa sauran kwanakin a wajen Addayiya.






Labarin Alhaji sulaiman kutsam aka samu wata Rana,sakamakon wani tsoho daya kawowa Yan Sanda rahoto Kuma ya musu jagora,lokacin da aka shiga gidan dake dukar daji sulaiman aka samu rashe rashe dashi da Yan kungiyar su Suna Shan jinin jariri ga gawar yaron a kwance akan table nasu dukan su sanye da jajayen Kaya abin d'aga hankali Amma su Bako Imani, kamosu Yan Sandan sukayi a haka aka fito dasu cikin gari a kallah sun Kai su 10 Kuma dukan su Babu karamin mutan a cikin su, masu kudine sosai d'aga mazan har matan.







Makasu akayi a kotu a ranan dubun al'umma Suka shaida fuskokin mugaye da siffan mutanen kirki Mami tayi kuka bana Wasa ba lokacin da sulaiman ya Fadi dalilin sa na tsanar su Lahab Ashe tun lokacin da Al'hassan ya aure Mami yayi Alkawarin ganin bayan sa da duk abinda Mami zata Haifa Kuma saita Zama mallakin sa,amfani kawai yayi da kiyayyar su Lahab a zuciyar farida da Nabeel yasasu wannan aiki Wanda haka ya bayyana cewa Mami tafison y'ay'an Al'hassan akan nasa y'ay'an shiyasa yayi niyar kashesu yaga Koh in Babu su zata fi son y'ay'an sa sama da kome Daman tuntuni yayi niyar kashesun.






Zancen Nnenna Kuma Ashe kungiyar sune,asalin matar papa tana da mukami Mai tsoka a kungiyar don ta riga sulaiman shiga kungiyar tasu don shi sulaiman wani abokin sane dayaje service inyamuri suka hadu shine ya kawosa kungiyar,bayan matar papa ta dawo Libya kungiya ta bata mukami Mai girma sakamakon yaranta data bayar har uku,Saida Kuma rikici ya barkene lokacin da kungiya ta bukace,ta bata jinin Nnenna anan tace Nnenna Amana ce aka Bata bazata taba cutar da ita ba iyayen ta sun Mata halacci an buga an buga Abu yaki ta kafe akan bazata taba data jininta ba.





Hakan ya fusata shugaba su ya Aiko Mata da annoba Rana tsaka ya Kama gidan ta don duk barazanan da zasu Mata sun Mata amma ta nuna musu saidai tabar kungiyar akan ta bada Nnenna, amma abin Al'ajabi babu abinda ya samu Nnenna cikin yardan Allah saboda marabai dake jikinta sosai suke Bata kariya Amma da izinin Allah (tunda malam ya Bata magani shikenan Bata tare dasu yanxun)bayan mutuwar matar papa, sun gano jinin Nnenna ba karamin karawa kungiyar su shahara zatayi ba duk wani hanya da Suka San zasu bi suga bayanta sun bi Allah baya Basu sa'a lokacin da ta girma sai Suka Soma janta zuwa cikin kungiyya a nufin su ta gaji karagan mulkin matar papa Kuma ta dalmaya dasu saboda Karin shahara da daukaka da zasu samu amma sun rasa meyasa Nnenna tafi karfin su karshe ma duk lokacin da Suka yunkuro Mata sai sunga tashin hankali shiyasa suka sanya Mata kaunar Kule Kuma suka hadata da kiki Yana gadinta.







Jin wa'innan labaren ya d'aga hankalin jama'ar NAGERIA Inda wasu gaggan matasa Suka bankawa motar su sulaiman petur da wuta lokacin da aka fitar dasu daga kotu Basu ma Bari shariya ta kare akan su ba,mutuwar su Babu abinda jama'a ke tofawa sai Allah ya Kara nauyin kasa,mahraz da kannen sa harma da Mami ha karamin kuka sukasha ba uba ubane Koh yaya mutum zaiji zafin abin a ransa.








Su Lahab sun koma rugan su malam Inda Suka tarar Allah Yama malam rasuwa Lahab ya d'auki dawainiyar matar malam nayau da kullum ya gyara Mata gidan ya koma na zamani haka zalika ya kaita haji duk wata Kuma sai ya turo Mata da kayan abinci,mama da Muhammad Ashe iyalan bubaja ne mama ta sake aure ne,lokacin da Suka hadu ba karamin kuka mama tasha ba shima bubaja ya Barta da Sabon mijinta don yaji matukar dadi daya hadu da gudan jinin sa,sannan mijinta ya rike dansa Kamar na cikin sa,ashe lokacin da Suka fita a gidan haka kawai Suka manta da kome da kowa nasu sai mutuwar su sulaiman ne abubuwan Suka dawo musu.







Rayuwa ta koma sabuwa sai abinda ba za'a rasa ba daman shi dan Adam kulum cikin jarabawa da tawakkali yake yau dadi gobe akasinsa,mubeena Amarya ta haihu Allah ya azurta ta da samun ya mace,haka zalika matar Ade ma ta haifi namiji,amma Deyana shuru kake ji har yara sun gima kusan 15years kafun Allah ya saukar Mata da rabon ta,itama ta Kara haihuwar namiji yaro yaci sunan Rahab duk da ba tagwaye bane amma Lahab yasa Masa Hussain Kuma ana Kiran sa da Rahab,saboda har lokacin Kewan Dan uwan sa da har gobe yake damun sa Bai barsa ba, Y'ay'an Mami kaf sunyi sure Yusuf autane kad'ai ya rage shima ya Zama saurayi.






Abotar Adewale da Lahab sai Kara gaba gaba yake har Kuma lokacin iyayen Ade basu musulunta ba sai dai hakan baisa eshat da yaranta sun guje jinin ubansu ba haka suke zuwa wajen kakanayen nasu Kuma Alhamdulilah Suma Suna kaunar y'ay'an d'an nasu(jikokin su) Kamar me ga yara Kamar larabawa kamannin uwar su Suka d'auka hatta launin fatar su.






Yau tun safe gidan Lahab ke cikin farin ciki ata dalilin bakin da zasuyi daga Libya,ba karamin shirya gidan Nnenna da nazeefa sukayi ba Lahab de na kwance a daki don kwata kwata yau da mutuwar jiki ya tashi shiyasa ya Shiga daki yayi kwanciyar sa sai yaran da mamar sune keta murna,wayar sane yayi ringing amma ya kasa d'auka turo kofar akayi Dr Deyana ce ta shigo dakin nasu kallon Lahab tayi sai Kuma ta girgiza Kai kawai,wayar tasa daya tsinke ta d'auka ganin miss call in waye yasa ta bin Kiran,sai Kuma ta matso kusa da mijin nata ta manna Masa a kunne amma tana Jin duk abinda na cikin wayar ke cewa.





Waro Ido tayi Jin muryan Ade na dariya Yana cewa sai dai fa suyi hakuri su mubeena a gidan sa Suka sauka yanzun haka ma Suna Kan dinning ita da Usman Suna cin abinci da yaran sh,"what wallahi basu Isa ba Suka sani tun safe Ina Kan kafata kana suzo suce Wai sun sauka a gidan sa"tace cikin Jin haushi dariya kawai Lahab yayi ya katse wayar da Sauri ta Mike bude wardrobe nata tayi ta dau hijab bata saurare tambayar ta da Lahab yake Ina zata ba ta fito falo kallon yaron nata tayi tace"Kai Rahab maza mike,kee nazeefa fito a dakin Nan kwalliyar ta Isa haka kizo ki dau Abdul-Rahim mu tafi gidan big uncle naku,sai Kuma ta dakata tana cewa Kai nazeefi d'au kulolin abincin Nan muje baza'a sani asara ba,shidai Lahab fitowa yayi Yana kallon abin mamaki Nnenna ta tasa kuloli da yaranta a gaba suka fita a falon gidan.........................




*ANAN NA KAWO KARSHEN LABARIN KUSKUREN DAYA YI A CIKI ALLAH KA YAFE MIN MASOYA INA MANA FATAN ALKHARI*





*Alhamdulilah Alhamdulilah Allah nagode maka daka nuna min Rana ta yau jumma'a 25/2/2022 Na kammala labarin ALKAWARIN MASOYA godiya Mai tarin yawa gareku Fan's na ALKAWARIN MASOYA nagode da kaunar da kuka nunamin ubangiji ya Kara bude Aunty's masu cewa har yanzun ba update me toh yau dai Zan kwanta sakayau Dani Babu tunanin update,duk da naso labarin yafi haka tsawa saidai Alhamdulilah hakan ma nagode wa Allah daya bani iko da basiran kammalawa lafiya Bissalam*








🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀

Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment