Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dauke rayuwar sa, a Randa ya rasu na tattara kayana bamma kowa bankwana ba nabar gombe na koma kasarmu Amma abin ciwo iyalina Basu zo kauyen muba na tsorata sosai hakan yasa na dawo cikin gombe Babu irin yawo da banyi ba Amma bansame suba duk Inda nasan Zan gansu na duba Amma bangansu ba hakan yasa na Kama shago Ina xama a ciki Ina dan sana'a,maganan camera Kuma memory na saya Ina chanja record na vedio duk bayan shekara biyu duk abin kallo daya fito na yayi saina saya na tura a ciki na aje don nasan wata Rana xai min matukar amfani.





Kusan a Yan kwanakin Nan sai na ringa mafarki akan yarona Yana cewa na nemi gidan Alhaji naje nakai abinda ya bani,Koh bayan shekaru darine indai Ina da Rai unguwan bazai bace min ba saidai Kuma na kasa gane gidan dayake anyi gine-gine na zamani Kuma masu kyau don ashekarun baya kaf unguwan gidan Alhaji ne Mafi kyau sauran duk na talakawa ne Amma yanzun Naga ba haka bane,kutsam wata Rana Allah ya hadani da wannan yaro Adewale nake Masa kwatance gidan yace min yasan gidan don dan gidan abokin sane saidai babu lafiya don yaron gidan yasha guba Allah ya Masa rasuwa Nan yake bani labarin abinda ke faruwa,haka kawai naji hankali na ya tashi Kuma naji yaron ya kwantamin a rai anan nake basa labarin abinda ya kawoni,amma yace gaskiya zuwana gidan yanzun akwai hatsari, Inna yarda dashi muje ya nemamin gida na zauna zasu daukaka Kara akan lamarin ayi kome a gaban Sharia abi musu hakkin su, salati jama'ar dake code in suka sake,buga guduman sa Alkali yayi kowa ya nutsu,Neman ganin vedio akayi Mika musu wayan sa yayi aka zare memory,had'a kayan kallo akayi babba yanda kowa dake zaune acikin code in zai gani,ummu Kam sharkaf tayi da zuba,haka uzaifa hankalin sa ya tashi, wato mutumin da ya nuna baya kaunar wani Koh ance yama wannan Abu baza'a Yi mamaki ba da ace Mamu ce Babu Wanda zaiji dar don ansan Bata son mami Amma Wai ummu mikewa tayi ta Soma rantse rantse,malama Khadija Nan kotune ki kiyaye komawa tayi ta zauna hankali a tashe.







Haskene irin na films in da Babu colour amma ras ake ganin fuskar mutane,falone irin na da Alhaji sulaiman na tsaye sai Khadija daken zaune akan kujera cikin dari dari Suna magana"gaskiya kaf duniya Babu Wanda na tsana irin Amina"Kuma Zan iyayin kome don Naga bayan ta"gyada Kai Alhaji sulaiman yayi sai Kuma yace"karki damu nida kike ganina innan tsohon saurayin tane amma ganin Mai kudi yasa ta auresa ta barni don haka nima fansa nakeson d'auka a kanta Kuma Koh nawa Zan iya kashewa don ganin bayanta Ni aguna kudi ba kome bane"gyara Zama Khadija tayi tace watoh yanzun ka nemenine dan mu had'a hannu dakai mu raba auren nasu Koh yaya don nidai kome Zan iya Amma Banda kisa bazan iya kisa ba"





Karkiji kome Ina dai kin amince Zaki had'a hannu Dani"eh na amince"toh ke mekike so ayi Mata"Ni bani da buri daya wuce Naga Babu ita a cikin gidan, haka cikin dake jikinta babu shi shine burina,itace tazo a baya sannan tana kokarin mallake kome na gidan Kuma Ni na tsaneta so nake mu Kulla Mata sharri Wanda zaisa Alhaji da kansa yaji ya tsaneta Kuma ya saketa tabar gidan cikin jikinta Kuma so nake ya zube Babu shi"an gama karkiji kome basai an Mata sharri ba ni Ina da malami Kuma harma yamin aiki akanta,waro Ido Khadija tayi tace malami Kuma nida nace ayi Abu na sharri Kuma a samu maganin zubda ciki"?




Karkiji kome wannan zaifi yin aiki farat daya sai Kuma ya shiga daki ya fito hannunsa dauke da wani laida fito da wani yadi yayi ya Mika Mata Amma ba'a ganin wani kalane saboda Babu colour a vedion Amma sunajin tambayar da Khadija ta Masa"wannan Jan Kellen fa malam"?Mika Mata wasu layu uku yayi again bai Bata amsa ba ya sake Mika Mata wani sweet"karba tayi tana jujjuyawa a hannunta kana ta sake jefo Masa tambaya"wannan Jan sweet in ki tabbatar Alhaji yasha shi Koh a abinsha Koh a hakansa wannan kelle Kuma Zaki shimfida ne a kasan zanin gadon da zai kwanta saiki jera wannan layun duka uku a kasan filonsa ki tabbatar Babu Wanda ya kwanta akan shimfidar Koh Shan abinnan sai shi kadai"




Toh meye ma'anan hakan Kuma Ni a zatonsa ai Amina ce za'a ma magani ba Alhaji ba"wannan kikayi abinda nace Miki toh shikenan kaf duniya Babu Wanda Alhaji zaiji ya tsana sama da kome a duniya...............sai Kuma Sukaga Alhaji ya juyo ya kalle window Yana cewa waye a wajen sai Kuma Sukaga camera na gudu Yana haska kasa shikenan Kuma saiya dauke"innalilahi na shiga uku salati kawai ke tashi a kotu sannan lauya ya nemi ganin Khadija fitowa ummu tayi sai hawaye take tazo ta tsaya tambayar da aka jefo Mata yafi kome daga Mata hankali"watoh menene gaskiyar alakarsu da sulaiman Kuma zargin da ake gaskiya ne abinda sulaiman ya sata shita aikata washe gari Alhassan ya tashi da ciwon kafa"?





Tabbas nasan irin wannan Rana na zuwa shiyasa tun farko naso na sanar da hakikanin gaskiyar abinda ke damun Alhaji tun kafun yabar duniya amma sulaiman yayimin barazana da rayuwata mundin na furta ainahin abun saiya ga bayana"kotu ta tambaye ki hakikanin Al'amarin batace ki kamo wata jawabi ba"shin Menene alakarki da sulaiman? gaskiya bamu da wata alaka a tsakanin mu asali ma wata Rana Dana fita a gida ya tareni yace Yana so muyi magana naji tsoro ainun Amma lokacin da naji yacemin saurayin Amina ne nada, Kuma aiki yake so muyi tare zai biyani kudi masu makudan yawan gaske Jin zancen kudi yasa na amince muka saka rana da waje Muka hadu a Randa muka zauna muna tattaunawa yaron bubaja ya ganmu Kuma muka gansa munso ya tsaya amma haka yaki tsayuwa ya gudu hankali na ya tashi shiyasa nace Nina fasa aikin Amma yace Dole nayi abinda ya sani zancen d'an bubaja Kuma in zuba Ido zancen Nan babu Wanda Zai sani.





dana dawo gida nayita dari-dari dasu bubaja gani nake Kamar zasu tonamin asiri Amma hakan bai hanani narkar da sweet Inda sulaiman ya bani a shayin surkina ba haka zalika na shimfida Kellen Nan da laya a daren na langwabe da sunan rashin lafiya na dau uzaifa na kaiwa Addayiya a daren ta kwana dashi don nasan tabbas ba kwanan Amina bane Kuma Amina bazata yarda ta karbi uzaifa a hannun Addayiya ba Kuma haka zalika Addayiya bazata kwana da uzaifa ba daki d'aya da mijinta duk da lokacin yarone karami,Aiko hakata ta cimma ruwa washe gari ya tashi da ciwon kafa Amma haka ya d'aure yaje masallaci daman Ina fakonsa Yana fita na shigo sashen nasu Alhamdulilah Babu Wanda ya ganni harna Shiga na Ciro abinda nasa Masa sauran shayin ma na zubar a toilet,lokacin da nazo fita a dakin karaf Muka hadu da Addayiya Nan na Soma Kame Kamen Mara gaskiya kana nace Mata nazo duba uzaifa ne Yaya kwana"dayake ita Bata kawo mummunan Abu a ranta ba Kuma Bata tambaye ni Jan Kellen dake hannuna a nannade ba tace min in zanzo duba yarona Saida asuba zanzo uzaifan dan yayene,kana ta daukesa ta bani nabar sashen su.



Hankali na ya tashi lokacin da Naga surkina sai ciwa ce ciwa ce yake tun ranar dana saka Masa abubuwan Nan, hankali tashe na koma wajen sulaiman anan yake cewa ai maganin haka yake Nan da wata uku zanga abinda zai faru Aiko Nan da wata uku Alhaji ya rasu, hankali tashe naje na samu sulaiman akan gaskiya Ni Zan tona asirin gaskiyar abinda ya faru kudi sulaiman ya bani bana Wasa ba Kuma ya rantse da Allah Ina fadan gaskiya sai yayi ajalina,Ni Kuma haka na amshi kudin nazo naci gaba da rayuwata na watsar da kome Amma daga baya na fahimci dalilin amfani dani da sulaiman yayi watoh saboda Amina ta dawo garesa.





Uhmmmm ummu na gama bayani lauyan su Adewale ya mike Yana cewa" ya Mai shariya wannan Sharia da muke da Wanda ake yanzun Yana da banbanci an shigar da Sharia ne cikin shari'a Babu alakar kisan Abraham da Kuma wannan gabatar da shaidu da ake,gyada Kai Alkali yayi yace a tsare Masa sulaiman kana a cigaba da shari'an su Lahab shin lauya nada hujoji dazai Kare Wanda ake zargi"kwarai ma kuwa Ina dasu,toh Bismillah ka gabatarwa da code hujojinka"Kiran Nabeel lauya yayi dam dam haka zuciyar sa ta amsa mikewa yayi a dake yazo ya tsaya a Inda aka tanada"code zataso sanin cikekken sunan ka"Sunana Nabeel Muhammad"zaka iya sanar da kotu alakar dake tsakanin ka da Wanda ake tuhuma dasa hannun sa a kisan Abraham"abokina ne"abokin ka nada Koh na yanzun"Kamar ya nada Kona yanzun"calw down Mana Nabeel Wai nace abotar taku har yanzun anayi Koh an daina"?




Kaga Brr karka kawo wata manufa ta daban kawai in zaka min tambaya kamin abinda ya shafe kaina ba wani ba"kotu ta bashi dama kuma tana umurtar ka daka amsa Masa duk tambayoyin da zai jefa maka"a gaskiya Ina bukatar lauya nima Mai girma Mai shariya a d'aga shariyar Nan harsai na d'auki lauya" da murmushi brr yace"haba Nabeel tambaya ce fa Kamar yanda akama Khadija haka za'a maka ka koma ka zauna kaima toh, menene na d'aukan lauya Kuma"?dan shuru yayi sai Kuma yace eh abokina ne har yanzun.





a ranan............. Koh zaka iya sanar da kotu a wannan dare a Ina ka kwana"?dan rikicewa Nabeel yayi kafun yace kamar ya bangane a Ina na kwana ba"?eh a wannan daren dai a Ina ka kwana"gaskiya bazan iya tunawa ba don ya Jima sosai"toh shikenan tunda kace ya Jima sosai bari na tuna maka a ranan baka kwana a gidan ku ba Kama iyayen ka karya da sunan zaka kauyen su mahaifiyar ka zaka je ka gaida kakan ka ta wajen uwa sai Kuma da misalin karfe 1:23am na dare ka fito daga cikin gidan Godwin dake saman layin ku Kuma a daidai lokacin aka kashe Abraham Koh zaka gayawa code meya kaika gidan a daidai wannan lokaci?





Wallahi karyane Babu Inda naje Ina gidan mu wallahi karya ake min wannan ai kazafine"malam Nabeel ka kiyaye a kotu kake"shuru Nabeel yayi cikin tashin hankali ganin wankin hula nason kaisa dare,Dr Colin's kutu nason ganin ka don amsa wasu tambayoyinta mikewa wani magidan cin Cristian yayi yazo ya tsaya"Koh zaka sanar da kutu hakikanin abinda ka gani a wannan rana"kwarai ma kuwa a wannan Rana bayan na taso daga aikin dare da aka kirani na nufo gidana dake kusa da gidan Godwin tunda na sharo kwanar layin mu wutar mota ta ta haskamin mutum Kuma akwai hasken nepa duka, ya fito daga gidan hankali tashe jiki duk jini fuskarsa a rufe nayi matukar tsorata hakan yasani niyar juyawa na koma Inda na fito sai Kuma motar ta mutu yaki tashi wutar motar ma ta d'auke Nan nayi ta kokarin kunnata amma na kasa Saida yazo daf dani cikin duhu kawai saiya gwaru da motar tawa ba tare daya kula akwai mota a wajen ba Nan ya buge kafarsa da Sauri ya tsunguna Yana mammatse kafar Kana ya mike yabar wajen Saida yabar wajen nayi Sauri na bude motata na sauka Nan na kunna wayata Zan haska hanya na wuce gidana kawai saina ga wayarsa a kasa ya Fadi da Kuma mask na fuskar sa alamu ya cire mask inne,da banyi niyar d'auka ba amma daga baya saina d'auka kawai nayi gida tunda na koma gida haka na kasa natsuwa kwata kwata Saida na kunna wayan Nan amma wayar da lock a ciki sai dai screen in wayar akwai hoton shi Nabeel da Kuma yayarsa sun dau hoto tare Kamar ranan sallah ne ma hoton aka daukesa,lokacin dana ga hoton saina aje wayar da yakinin taima ya Kira yanason wayarsa,washe gari da safe saiga labari ya karade gari an kashe Dan Godwin babu Wanda naji ina zarginsa a Raina sai Nabeel amma Ina tsoron karna sa kaina a rikici bani da gamsheshen hujja Kuma naji tsoro Kar wani bincike yasa a bi diddigin layinsa,na kashe wayar gabaki daya,wata sabuwar labari danaji shiya dagamin hankali shine Wai Nnenna da Lahab su ake tuhuma sai dai ba'a Kama yarinyar ba har Shiga code nasu Lahab na farko naji labari da Kuma fitarsa Lahab na fita da kaina naje gidan su da sunan musu Jaje nace Ni malamin sune na makaranta anan Muka kebe da Lahab na basa wayar Nabeel Kuma na Masa bayanin ta Inda na samo wayar,Nan yamin godiya amma yace bazai iya kaiwa hukuma wayar ba,Koh bayani ba don Koh Nabeel ne yayi kisan Nan bazai iya tona Masa asiri ba"






tuni code ya kidime da hayaniya da Al'ajabin abinda ke faruwa kankace me jama'a sun Fara tofa Albarkacin bakinsu,bayani kotu ta natsu aka Kara tambayar Nabeel amma Nabeel ya karyata yace sai dai in sharri akeson lakaba Masa tabbas wannan wayan sane amma an saceta bai gani ba tun da Jimawa ganin Nabeel nason bawa lauya ciwon Kai aka dauko record na CCTV camera dake wani gidan shahararren dan kasuwa dake kallon gidan Godwin Nan aka haska tabbas gashi Nan Nabeel ya fito daga gidan awannan rana sabar toshiwan basira abinda yasa ya rufe fuskar tasa Yana fita kofar gidan ya cire Kuma camera ta d'auka dayake kofar gidan mutumin akwai hasken wuta radau.





Kuka Nabeel ya sake cikin tashin hankali"Muna sauraron ka malam Nabel"tabbas anyi haka nasan Koh naki Koh naso yaune ranan tonon asiri duk wata boye boye yau bazai boyeni ba"tabbas Nina kashe Abraham da hannu na"Inna Kam faduwa tayi a kasa sumemmeya take aka dauketa akayi waje da ita itama mubeena da Sauri tabi wa'inda Suka dau innan tana Kuka don dukan su Sunsan tabbas a ranan Nabeel baya gida,kenan gaskiya ne Nabeel dan uwanta kwalli d'aya a duniya Kamar tsokar nama daya a Miya shine yayi kisan Kai innalilahi wa'inna'ilahu raji'un.....................................................









*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*



Menene Abraham ya maka da harka kashesa Wanda a iya bincike da kotu tayi akanka Babu wani sanayya a tsakaninku"?share hawayen sa yayi bai iya daga Ido yaga jama'ar dake zaune ba tunda Inna ta Fadi gabaki d'aya yaji duniyar ta Masa zafi"tunda Muka taso da Lahab bani da abokin kishi irin sa saboda Ni Ina da bururruka a rayuwata masu yawan gaske amma abin takaici kullum Lahab shike nasara akan burina saiya samu Ni Kuma naci alfarmar sa wannan yasa na Fara Jin tsanar sa a raina tun Muna kanana,kokari ya fimu a makaranta tare Muke kin zaman class amma abin mamaki duk lokacin da zaiyi jarabawa sai yafimu samun Makin da Average Mai yawa"ban Kara Jin tsanar Lahab ba sai lokacin dana kyalle Ido na gansa da Nnenna yarinyar da kyawonta gabaki d'aya ya tafi dani naji duniya kaf babu Wanda nakeso sama da ita amma kafun ma na ganta Lahab Harya shiga rayuwar ta.




Na ringa bibbiyar ta harna gano gidan su Kuma naje nace Mata ta rabu da Lahab bata Mata rayuwa zaiyi amma budan bakinta sai tace bani da matsala da hakan sosai nayita shishige Mata a boye amma ta nuna bana kaunar Koh ganin fuskata abin yamin ciwo bana Wasa ba duk da nasan Bata sanar da Lahab abinda ke faruwa,gashi mu uku Muke abota Amma Lahab yafi sirri da Ade duk da Yana kokarin boye hakan a gabansa Amma Ni na sani, sai Kuma aka soma zancen jarabawan weac Karo na farko Lahab Bai bawa jarabawa na hankalin sa ba Koh zancen biyamin kudi bayayi lokacin sama bana samu sosai,hakan yasa na Soma binciken sa anan na gano yana tare da Nnenna naji tsoro kada shigowar ta rayuwar sa yasa ta kwace min shi.





Wata Rana Ina zaune a cikin gida aka turo yaro Yana kirana Ina fita abin mamaki farida(budurwar Anwar) na gani cikin mota Kuma daman na riga na santa nasan zancen fasa auren ta,shiga motar nayi taja mukabar layin,wani gida Mai tsananin kyau Muka Shiga har lokacin bata sake cemin kome ba faka motar tayi ta bude ta fito nima fitowa nayi Ina tambayar ta lafiya tace na Shiga mota Kuma zata kawoni Nan"?Mena gaggawa in mun Shiga zaka ga Koh menene ai,Koh tsoro kake ne"?girgiza Mata Kai nayi muka shiga cikin gidan,abin mamaki dadyn mahraz ne zaune Yana jiran mu Zama nayi na gaidashi anan yake cemin fatan na gane sa nace kwarai ma kuwa abinda ya biyo baya a zancen sa shine"yasan cewa Ina matukar jin tsanar Lahab Koh"?don ya lura Adewale ne kadai ke zaman tsakani da Allah da Lahab nikam zaman abin hannun sa nake dashi"da fari maganar daya fadamin ya batanin Rai saidai magana ta biyu taja hankali na"shine Wai zamu had'a hannu muyi aiki amma fa Zan samu kudi zai ban kudi kusan 10 millions.





Hankali na ya tashi Jin makudan kudin da ake zancen za'a bani Nan naji cewa Babu abinda za'a sani na kasa Yi akan kudin Nan anan yake sanar dani cewa kisan Kai zai sani nayi"Abune da ban Saba ba ban Kuma San dalilin dayasa ya zameni a matsayin makashi ba,amma kudin Nan bazan Bari ya kubuce min ba"nunamin farida yayi yace wannan yarinya fansa takeso ta d'auka akan Lahab Kuma ta gano Lahab ba karamin kaunar Nnenna yake ba don haka daurawa Nnenna sharri ba karamin broken na heart nasa zaiyi ba,daman ba kaunar Lahab nake ba hakan yasa banyi wani gardama ba anan Muka shirya plan namu,farida ita taja ra'ayin Abraham kamar yanda Muka tsara a club kwaya ta basa masu karfin gaske kana ta hada Masa dana tada sha'awa Mai tsanani Kuma tace Masa yaje dakin Nnenna tayi Masa waya tace yaje su Kwana tare,dayake ya bugu da kanta ta maidashi har kofar gidan su ta saukesa ya fita da layi ya Shiga cikin gidan nasu cikin tsakar daren Nan"daidai lokacin nima na shiga cikin gidan saidai ban shiga flat in ba Zama nayi a bayan window Nnenna, Inajiran abinda zai faru Aiko Kamar yanda Muka tsara haka yagudana,tabbas Nnenna buga masa lamp tayi ihunsa shiyasa ja hankalin y'an gidan Wanda yasa Nnenna tsorata ta bude window ta dirka Kuma duk abinda take Ina labe Ina kallonta tana fita dayake karnukan sun Saba da ita basu Mata haushi ba.





Window data bude shina bi na Shiga dakin nata wuka na d'auka na caka Masa a ciki kafun na fita dakin da gudu a lokacin karnukan Suka Soma Bina Suna haushi Wanda yaja hankalin Yan gidan suka zaci Koh Nnenna ne,suka zagayo..........................






"toh Nabeel Koh zaka sanar damu abinda Rahab ya maka ka kashesa bayan sharri dakasa aka ma Lahab meye Rahab ya maka shida babu ruwan sa baida wata alaka dakai saita mutunci amma ka bisa har London ka kashesa Kuma camera ya tabbatar da shigarka layin nasu a wannan Rana"?tabbas naje London Amma kafun naje na cikawa farida aikinta watoh na d'au wayar Ade a ranan danaje gidan su lokacin daya dawo hutu,bayan nace Masa Ina so ya kawomin abinci sai kawai nadau wayarsa bincike nayi sosai harda chatt nasu Nan na gano Lahab har aure yayi nayi farincikin haka na tura hotonan a wayata,na turawa farida ita Kuma ta yad'a,kudin da Alhaji sulaiman yamin Alkawari ya cikamin yaban kudaden Amma yace Dole Zan dan Kama sana'a Wanda zai d'au hankalin mutane karsu zargi kudin danayi dare daya.





duk da aikin farko da mukayi bamuyi nasara ba amma ana biyu munyi nasarar da tasa gabaki d'aya family su Lahab a damuwa amma Kuma sai naji hakan bai wada ceni ba ganin d'aukaka da Allah Yama Lahab sosai abin ya tsayamin a wuya naji Babu Wanda na tsane cigaban sa sama da Lahab,nida farida mukaje London Muka had'a Baki da Waitern dasu Lahab ke ordern abinci a wajen su,munfi wata biyu a London muna jiran randa za'a Yi order amma shuru Lahab baya ordern kome,kutsam saiga shi ranan yayi,sam ban kawowa raina Rahab bane zaici harga Allah duk da nasan gida daya suke amma tunani baizomin kila Rahab Koh Addayiya suci ba Muka saka poison Mai hatsarin gaske Rahab yaci ya mutu"





Aiko Nan code ta cika da mamaki aka hau salati bana Wasa ba ganin waje yaki natsuwa yasa alkali wanke peace tare da bimata hakkin ta ga Kuma tara da Nabeel zai biya ta.






lokacin da aka juyo za'a Kama Alhaji sulaiman wayam kamar walkiya ba'a gansa ba,babban magana su dai police dake gadi basuga wucewar Saba,Nan aka Soma kus kus Ashe Dan kungiyan asiri ne, Nan aka d'auki ummu da Nabeel aka wuce dasu tare da d'aga shariya sai Nan da sati biyu kotu ta bada belin Lahab zai iya komawa gida, mutane da yawa sun babbawa peace kyautar kudi masu mugun yawa ana Kuma tsinewa su Nabeel Sunsa yarinya zaman yari harna shekara biyu cip ba tare da hakkin taba dady shima hankalin sa ya tashi baisan a wace duniya Nnenna ta Shiga ba ya kasa riketa a matsayinta na Yar dan uwan sa Wanda ya turota wajen sa gashi yanzun baisan Inda zai sameta ba,Mami Kam saida aka fitar da ita don kasa fita tayi sai kuka take tana ta Cuce kanta.





Kutu ta bada umurnin kafun shariya ta gaba tanason a durkusar Mata da Alhaji sulaiman da Kuma farida a kotu a duk Inda Suka Shiga Yan Sanda su Nemo su.




Mami Saida ta kwanta a gado gabaki daya ta gama rikicewa sai cewa take ta cuci kanta ta ruguzawa yaronta rayuwarsa ta rabasa da matar sa da yayansa Anya Allah zai yafe Mata kuwa sulaiman ya cuceta,ana ta Bata hakuri shidai Lahab ba uhmmm ba uhmmm uhmm Amma dai yaje ya dubata sai cewa take Hassan ka yafe min ban maka adalci ba a matsayina na uwa shidai kansa a kasa harta gama surutun ta ya mike ya fita.






Yaje wajen Inna gaskiya halinda ya ganta ita da mubeena ya saka sa a damuwa sosai Inna ke fama da ciwo bana Wasa ba asibiti ya chanja musu zuwa Mai tsada yadau d'awainiyar jinyar ta ita dai mubeena duk lokacin da ta gansa sai dai kawai mutum yaga tana kuka.




Cikin sati biyun Nan abubuwan da dama sun faru ciki kuwa harda rasuwar Inna da Kuma kamo farida da akayi amma Alhaji sulaiman ba'a Yi nasarar Kama sa ba haka kotu ta yanke mutu hukunci daidai da abinda Suka shuka Allah sarki mubeena Suma Kan Suma ta ringayi ta rasa dame zataji da mutuwar Inna ne ko da rabuwa da Nabeel dan hukuncin kisa aka yanke Masa ta hanyar rataya shida farida ita Kuma ummu a bisa lura da akai Bata da niyar kashe Alhaji Kuma bata San zai mutu ba a dalilin abinda ta saka Masa, yasa aka sassauta Mata hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai,ga maraicin rashin uwa da uba,lokacin da yazo Kan gawan Inna zai Mata bankwana ba karamin kuka yaci ba ya nemi yafiyar mubeena duk da yaso ace Inna na ra'ayi yazo ya nemi tata yafiyar amma sai ya kasance shine ajalinta,tabbas duniya budurwar Wawa ce shikam tasa ta Kare,duniya tama mubeena zafi jau yayin da Mami ma ke fama da rashin lafiya Wanda hakan ya Hana Lahab komawa London.




Mubeena maraici ya Mata yawa sosai yanzun tana gidan bappa Ado ana fama da rayuwa amma kwata-kwata rayuwar ta baya Mata dadi kwata-kwata tana cikin bakin ciki da damuwa bama Kamar inta tuna saura kwana kaza a rataye dan uwan nata.





Mami taji sauki kana ta tattara ta koma gidan da ta sayawa mahaifiyar ta da yaranta donta rantse bazata Kara Zama a gidan sulaiman ba yaran ma badon badon ba da dangin sulaiman zata mayarwa suje can su karata amma data tuna Y'ay'a dai nata ne Kuma itace gatansu hakan yasa ta rungume abinta,Lahab ya taso da zancen komawa London Wanda Mami ta nuna Bata son hakan ya zauna a Nigerian in ma karatu zai cigaba yaci gaba anan don ita yanzun kaf duniya Babu Wanda takeso a kusa da ita irin Lahab yanda taga ya chanja gabaki d'aya

Please Login or Register in order to submit comment