Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafun yace"Kaga Majid kaci abinci kawai ba'aci ana magana tsakanin ka da Lahab Kuma bansan Wanda yafi wani ba"yunkurin magana Majid yayi Abbu ya d'aga Masa hannu alamun ya mishi shuru kenan,shurun yayi Suka cigaba dacin abincin d'aga Ido Abbu yayi ya kalli mamu dake zaune fuska babu walwala hatta yaran Karan kansu sun fahimci akwai abinda ke damun ta,mikewa Abbu yayi cikin Sauri yadau jakan system nasa da Sauri muneera itama ta Mike hade da karban jakan ta nufi kofa,mikewa mamu tayi a fusace ta nufi sashen su ganin Abbu Harya nufi kofa baice Mata kome ba don jiya ma ba girkinta bane amma haka taje ta samesa akan kudin sayayya ya koreta gashi yau yayi ficewar sa bai bata ba,yaran Kam binta kawai sukayi da Ido Harta mule musu, amma basu ce kome ba duk da sunyi mamakin yau ranan kawo lefen umaima amma fuskar mamu ba walwala.





Mikewa sauran yaran sukayi Suna fiffitowa da d'ad'aya d'ad'aya Inka cire Majid da Lahab dake zaune har lokacin a dinning Kuma sune kadai bazasu makaranta ba(gagararu)Kamar an mintsine sa da Sauri ya mike gudu gudu Sauri Sauri ya fitoh a falon Aiko yayi sa'a su Rahab basu tafi ba, wajen sa ya matso yasa hannu ya jawo sa kusa dashi cikin kasa kasa da murya yace"don Allah Rahab so nake ka hadani da yarinyar da ta baka card jiya zamuyi magana ne a waya"wani juyawa Rahab yayi da kyau ya kallesa sai Kuma ya girgiza Kai ya shiga motar ya rufe baice kome ba aka ja motar Suka bar gidan komawa cikin gidan Lahab yayi ganin motar Dr ya shigo gidan nasu ya daura Masa ruwa da Allurai.



Mamu na shiga daki rai a bace ta zauna akan gadon ta tana kintsema irin wulakancin da Abbu ya Mata duk da tana da kudin itama Abba tanajin zafin kashe kudinta,Kamar ance ta d'aga Ido kawai taga card nasa akan pillow da Kuma pepar da Sauri ta matsa wajen ta dau card in take murmushin ya bayyana a fuskar ta ya yalwata sosai bude takardan tayi tana karantawa Kamar haka"toh sarkin son kudi Naga kin tashi sai wani harhada Rai kike waike Halima tunda nace Zan baki kina tunanin bazan bada bane toh ga card Nan banyar da ki kashe sama da dubu dari biyu ba don nasan ki"?da murmushi ta Mike ta dau wayar ta kiraye kirayen kawaye ta ta Shiga da kannen ta Akan suzo suje Mata cefene Kamar wani bikin ake.





Gidan su Lahab yanda kukasan gidan biki Kamar yau za'a daura aure saboda yawan kawaye da mamu ta gayyata karban Kaya sai zuzzuta zancen kayan take da kawayenta, Mami Kam batama San zancen kayan ba sai da azahar data shigo gidan taga Mata birjit gashi sai girke girke ake ana suyan kaji,da mamaki take gaida kawayen mamun da kannen ta amsa wa suke a daddage,Shiga cikin falon tayi hannunta dauke da laida hallo cikin ma da Mata gidasu tayi ta wuce sashen su Rahab zaune ta yarda Addayiya a falo sai ummu dake zaune Suna hira,karasowa falon tayi ta zauna Suka gaida sanan tace"Wai Addayiya meke faruwa ne Naga gidan a ciki"?meke Kuma faruwa banda Yar Nan umaima yau dangin yaron Nan sadeeq zasu kawo Kaya shine duk tazo ta cika Mana gida da jama'a Suna shewa Suna suya"da mamaki Mami tace"yanzun Addayiya haleema za'a kawo kayan yarta amma ba Wanda zai sanar dani"?ummu ne tace"Kinga Amina muma bamusan da maganar kayan ba sai da Addayiya ta fada"mikewa mamin tayi ta shiga dakin Lahab kwance yake hannunsa d'auke da ruwa shikadai ne don Majid ya fita,shigowa tayi ta zauna a bakin gadon tasa hannu ta taba wuyansa bude Ido yayi ganin Mami me yasa sa komawa baccin da yake.





Har zuwa yamma Mami na gidan duk da taso shiga ciki ayi aiki da ita Amma Jin yanda ake tsoka Mata magana yasa ta zame jikinta ta dawo tayi joining su Addayiya da ummu a falo Suka cigaba da zaman su,wanka yan Koran mamu sukayi akasha less da zanunuwa ansha d'auri ana jiran baki,da misalin karfe biyar na yamma lokacin yaran gidan wasu sun daddawo makaranta harsunyi wanka mazan Kam tuni Suka bar gidan bayan sunci lunch nasu.



Lahab sai hararan Rahab yake don bai hadasu da Nnenna ba bai kuma ce Masa kome ba,mami taso tafiya ganin har yamma ba'a kawo Kaya ba,amma ummu ta hanata gudun kada ummu tace hassada ce ya hanata Zama don tun safe zance daya mamu keyi yaudai makiyanta sai dai su mutu saidai su rufe idanun su yarinyar ta tayi goshi insha Allah kayan da za'a kawowa umaima har a gama aurar da yaran gidan baza'a kawo musu irin Shiba, danta Anwar ma akwatuna 12 ta had'a Masa za'a Kai wani sati Kuma tasan sadeeq zai had'a sama dashi.





Wangale gate na gidan akayi mota daya ya shigo rufe gate in Mai gadi yayi aka bude motar wasu matane guda uku Suka fito a motar,Jin mota ta shigo yasa mamu mikewa tabar falon ta shiga dakin ta Yan uwanta ne da kawaye suka tarbo bakin shigowa sukayi namijin daya kawosu shiya Fara shigo da akwatunan baza Ido manyan matan sukayi Suna kirga a kwatunan ganin mota daya ne ya shigo basu tsammace hakan ba Saida ma Suka ga an aje akwatunan duka,daidai Nan Mami da ummu Suka fito falon,kwata kwata guda biyar ne da karamin kit................................





🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*



Page 81&82

Zama Mami sukayi matan Suka Soma sauke kayan akwatunan, ba laifi sadeeq yayi kokari sosai zanunuwa kam masu kyau akwai na dubu hamsin da ishirin ga lace masu kyau babu laifi Kam, finda kayan suke su Mami na kirgawa sukam kawayen mamu Jan jiki sukayi Suna shan kamshi Koh kallon arziki basu ma bayin Allah Nan ba,mikewa kawar mamu tayi ta nufi sashen su Mamun zata Kai Mata rahoto da Sauri yayar mamu ta Mike tabi bayan matan Harta kusa isa kofa ta kwala Mata Kira tsayawa tayi har yayar mamu ta iso kusa da ita tana cewa"ina Zaki hajiya Hanifa badai wajen Halima Zaki ba"?wajen tane Mana zanje na sanar da ita abinda ke faruwa"da Sauri addanta tace"Kinga hanifa mu koma falo kinsan halin Halima Sarai zata iyya bamu kunya akan kayan nan muje ku ibo abinda aka tanadar musu ku Basu suyi Subar gidan kafun Haleema tasan zancen kayan lefen Nan"haba adda taya zamu d'au abinda muka had'a da kusan rabin kudin lefen da suka kawo mu d'auka mu Basu haba dan Allah"da Sauri Adda ta nufi kofar Jin ana kokarin bude kofar mamu itama Hanifa da Sauri tabi bayan Adda.



Mamu da taji surutu na tashi kadan kadan a corridor nasu shiyasa ta fitowa ganin ba kowa ya sata koma daki,su Karan kansu Yan uwan sadeeq jikin su yayi sanyi ganin yanda aka tarbesu Sam basuga fuska a gunsu ba saisu Mami dake Nan da Nan dasu Mami ce ta bude jakanta tadau gudan dubu duba sabbi guda ishirin ta Basu a matsayin kudin tukuici,Adda ce ta Mike ta shiga kitchen da kanta ta Soma d'auko Robobin kaji dasu donot da eggroll tana shigowa dasu falo ganin hakan yasa sauran Yan uwa mikewa da Sauri Suka shiga kitchen in daman robobi biyar suka shirya musu ganin Adda ta fitar da uku yasasu zuwa Suka dau biyun Suka saka a store Suka rufe duk yanda Adda tayi tayi dasu akan su bada biyu a Kai amma Suka ki,mikewa bakin sukayi sunata godiya Mami da ummu da Adda su Suka rakasu har mota.



Mamu najin tashin mota daman tana bakin window da Sauri ta fito a dakin ta ta nufi falo,idanunta ne Suka sauka akan kawayen ta da Sauri ta karaso saboda Zama da sukai Suka tasa akwatunan a gaba shiya hanata gani magana ta Fara"Alhamdulilah yaudai Zan kwanta cikin kwanciyan hankali an kawo kayar diy...........kasa karasawa tayi kanin akwatunan da Sauri ta karaso tsakiyarsu tana nuna kayan da hannu tana tambayar su"wannan fa menene?Ina sauran akwatunan dakina fa za'a kai?da dariya Mai Kamar tura haushi Mami tace"kayan umaima ne da matan gidan Nan kaf bazasu samu irin Shiba shine aka kawo Kuma iyya kacinta kenan"jikin mamu har rawa yake tasa kafa tayi ball da akwatunan Kamar mahaukaciya tana rantse rantse wallahi sai an maida musu kayan su ita yarta ba Yar agwagwa bane da zasu aurar da ita haka da wasu shegun Kaya.


Mami Kam tafiyarta tayi Koh a jikinta ummu Kuma tayi dakinta taje ta kwanta,sauran kawayen Mami abincin Robobin suka deddeba Suka bar gidan Suna kananun magana bayan sun zuzzuga mamu akan karta yarda karsu karbi kayan,Koh sallama basuma mamu ba saboda haukar da ta ringa zubawa akan kayan auren karshe ma tace baza'a Kai Mata daki ba Addayiya ce tadau kayan takai dakin ta,har dare mamu na dakinta ta kulle kanta bata tabajin kunya irin na yau ba da tasan kayanda za'a kawo wa umaima kenan wallahi da bata gayyi kowa yazo ba dama bazata bawa kanta wahala wajen kashe kudin dafe-dafe ba,Abbu da yara tunda Suka dawo basu ga Mamu a waje ba Wanda hakan yasasu sanin tabbas akwai damuwa kasa hakuri Anwar yayi Saida ya tambaya,mikewa Addayiya tayi tabawa su zulai da muneera umurnin su dauko Mata akwatunan dake dakin ta,ba musu Suka daddauko ajewa tayi a tsakar falon Yan gidan duka na zaune a wajen umaima ce kawai Bata nan.


Nuna kayan Addayiya tayi tace"kaga kayan Nan umaru shi aka kawowa umaima shine uwarta ta d'aga hankalin ta har tana rantsuwa za'a maida musu"da mamaki Abbu yace a maida musu akan me kenan"?da Sauri ummu tace"akan bai Mata ba Mana Alhaji"girgiza Kai kawai Abbu yayi yace wa Addayiya"Ina ga yaran Nan zasu dau kayan sukai sa sashena su aje Zan rufe kayan a wajena bana bukatar wasu suzo da Suna ganin Kaya a gidan Nan bakuma za'a fitar da kayan ba sai ranan da aka daura auren"Yana gama maganar ya mike rai a bace yabar falon,Shareef ne ya ciccibi akwatunan da kannen sa Suka Kai dakin mahaifin nasu suka rufe.




Kwance Lahab yake akan katifar sa sai Rahab dake gefe Yana assignment"yanzun Rahab da gaske baka kirani ba ka hadani da yarinyar Nan"tsaki kawai Rahab yaja baice kome ba sai Shan Kuma yace"eh ban hadaku ba in kanason magana da ita kaje da kanka Mana ba maka Kama da Dan aika ne"shuru Lahab yayi baice kome ba daidai lokacin Majid ya fito daga wanka don har lokacin bai koma gidan su ba bude wardrobe na Lahab yayi ya dau kayan baccin sa ya saka,sannan ya dawo Kan katifar tasa ya kwanta kallon sa Lahab yayi yace"Wai don Allah Majid kasan yarinyar Nan farida"?Jin maganar mace yasa Majid sauren tashi zaune Yana washe baki yace"wace yarinya kenan"am yarinyar Nan da mukaje birthday party saurayinta"Jin maganar da suke yasa Rahab barin abinda yake ya juya Yana kallon su da kyau.




Oh baby ferry kake magana haba Lahab me zakayi da wannan second hand in, karka bada kanka Mana bazaka nemi yarinya fresh one ba d'anta sai kilakin Nan ai taimaka girma wallahi abokai na da yawa sun hayeta fa"waro Ido Rahab yayi sai Kuma ya girgiza Kai yamike ya bar dakin tare da bugo musu kofa da karfi,Suma basu bi ta kansa ba sai Lahab yace"Kai tambayar ka nake ka santa bawai dogon magana Koh bayani nake so ba"




Eh na Santa mugun sani ba,amma Kai meyasa kake maganar ta"?tashi zaune Lahab yayi yace so nake na ganta don Allah Koh akwai wani party dakasan zata very soon"?eh toh gaskiya babu kasan fa ta wanke wani gara aure zatayi amma naji friends nawa nacewa za'a Mata na bankwana a Ranan za'a murzata na karshe"amma Kai meyasa kake son ganin ta?gyada Kai Lahab yayi ya cije baki baiso ace tonawa farida asiri yayi nisa har kusan aure ba, yaso ace tun yanzun kome ya kunce"karka damu kaide duk lokacin da aka saka date da venue na wajen ka sanar dani"ok shikenan ba yawa lahab, kwanciya sukayi dukan su biyu don Rahab Kam tunda ya fita a dakin Bai dawo ba.



Washe gari da safe sai ga goggoji Mai aiki ta dawo bakin aikinta daman girkin mamu ne gashi bata fito ba tun jiya hakan yasa tana zuwa ta fada kitchen bayan sun gaisa da mutanen gidan,bayan sunyi breakfast Abbu da kansa ya mike ya nufi dakin mamu hannu yasa ya tura kofar dakin ya shiga zaune take a bakin gado ta zuba tagumi sosai tayi nisa a cikin kogin tunani da ta shiga,Zama yayi a gefenta hakan ya sata dan birkita sai Kuma ta koma ta zauna tana kallon mijin nata Kamar yanda yake kallon ta,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya Soma magana a tausashe yace"Halima meke faruwa ne"?


Kamar ya?tace Masa tana dad'a tamke fuskar ta"Kamar ya Kuma zakice ai a tunani na kinfi kowa sani miya faru, na tambaye ki Wai meke faruwa ne Naga tunda na dawo jiya har yau ban saki a idanuna ba gashi yanzun nazo na sameki acikin damuwa"?shuru tayi sai Kuma ta fashe da kuka ta Soma magana"gaskiya Ni wallahi a maida musu kayansu taya za'a ce yarka guda za'a kawowa lefe akwatuna biyar da wani banzan kit daya haba haba don Allah kofa zanin sama da dubu hamsin babu a ciki"?




da mamaki Abbu yace"toh Halimatu yanzun ya kike so ayi indai maganar lefen ne baiyi ba babu damuwa Ni Zan iyya Kara Mata wasu set ma a had'a Mata da wannan,wani irin kayane umaima bata daura ba a gidan nan,abinda nakeso dake dan Allah ki kwantar da hankalin ki inke kin nuna irin wannan dabi'ar ita Kuma diyar taki ya kike so tayi kenan,amma in Kika nuna Mata albarkan aure yafi kayan tarkacen Nan na tabbata itama bazata nuna bai mata ba"



Wani zabura mamu tayi ta tashi tsaye ta Soma magana a harzuke"kasan Allah Alhaji nifa bazan yarda ba haba don Allah akwatuna 6 Kamar Wanda zai aure Mai tuyar awara da sakel gaskiya da sakel a maida musu da kayan su in Kuma bazasu Karo wasu ba saidai a sauke maganar auren Nan ai bashi bane kadai autan Maza kanaga fa,wannan yarinya Jamila ita da ba kyau ne da ita ba kaga gidan ubanta Koh gate babu amma ka dube kayan auren da aka kawo Mata sai tawa Yar za'a kawowa wannan tarkacen"shima Abbu tashi yayi ya nuna mamu da yatsa yana magana cikin fada"kee halima bafa tsoron ki nakeji ba karkiga Ina binki da lallama kice Zaki takani yanda kike so zancen aure Kuma Koh kiso Koh kiki wallahi baza'a fasa ba Koda kuwa yaron baiyi Kaya ba bare yayi sai in shine yace ya fasa,Yana karasa maganar yabar dakin cikin bacin rai.





Lahab Kam fita yayi a gidan hannun sa daure sai Mai lafiyar dake d'auke da kulan mubeena da niyar zai kaimata, ya gangara layinsu Nnenna da kafa don bazai iyya tuka Keke ba gwara ma in hannun hagune yake da matsala ba dama ba,Zama yayi a kofar gidan dake kallon nasu Nnenna sosai ya zurawa tsakar gidan ido Yana jiran fitowar ta duba agogo yayi karfe 7:12 ne daidai,Harya Soma tunanin Koh dai Harta wuce makaranta ne,amma saiya tsinci kansa da kasa tafiyar,sai kusan 7:30 yaga an turo kofan nasu tunda daman gidan nasu ba'a kewaye yake da gini ba, karafuna ne mutum na tsaye a wajen Yana hango cikin gidan.



Abraham ne ya fito yasha wanka cikin wasu arnan wando da riga na gogaggun Yan iska masu tashen kwaya, Nnenna na binsa a baya rataye da jakan makarantan ta bude mota yayi ya shiga itama ta bude gefe ta zauna yaja Suka bar gidan har sunzo saitinsa zasu gifta Kamar ance ta kalli gefen glass sukayi Ido hudu dashi da mamaki ta waro idanunta,shima bai tashi ba ganinta da yayan ta,har Suka share kwanar layin Yana zaune bai tashi ba"brother nayi mantuna nabar assignment book nawa a gida gashi yau zanyi summit pls ka tsaya Zan koma na d'auka"tsayawa yayi ya juya Yana kallonta yace"basai kin sauka ba bari mu juya mu koma saiki d'auka"da Sauri tace"ah ah ka tsaya dai na koma da Sauri Zan dawo karna baka wahala Bata jira mai zaice ba ta sauka da Sauri ta nufi layin su hangosa tayi a zaune har lokacin ya sata Kara Sauri tana dan gudu gudu kad'an hakan ya baiwa sassan jikinta daman kadawa da kyau,ganin ta yasa sa mikewa tsaye Yana murmushi Harta karaso Inda yake fuskar ta d'auke da murmushi itama tace"Lahab Kaine kaji sauki kenan"?hararan ta yayi irin na wasan Nan yace"eh nine lallai baki da kirki Labiba ace kin karyani amma baki nemi sanin yanda na Kaya ba nasan Koh Shakka banayi baki koma asibiti dubani ba"



Marairaice fuska tayi tace"kayi hakuri wallahi kana raina naso zuwa amma saboda abinda ya faru yanzun ba'a barina nafita makaranta Ni kadai"da gaske Ina ranki"ya tambaye ta Yana d'aga Mata gira daya,shuru tayi tana dai tsaye tana kallon sa"oh kina nufin makaranta kawai kike zuwa ne Koh Yaya"?dan rufe fuska tayi tace"eh wallahi tunda nazo garin Nan sau d'aya nayi yawo a gari amma kullum makaranta nake zuwa"Ware Ido yayi Wanda ya zame Masa jiki yace"cap kifin rijiya kenan"?


"Next week zamu Fara CA test pls kazo makaranta"ke makaranta zanzo a haka da hannu na"ya tambaye ta,ka dai daure pls bari na wuce ana jirana byeee"ta juya tana d'aga Masa hannu da Sauri ya riko hannun nata zai Mata magana sai Kuma yayi shuru ganin Dad dake tsaye a kusa da motar sa Rai a bace Yana kallon su.



Ganin sa yasa Nnenna fizge hannunta ta kwasa a guje tabar layin shidai Lahab na tsaye hannunsa d'auke da kula,harya karaso kusa dashi yatsa ya nuna wa Lahab a fuska a mugun bace yace"Kai Kuma again a kofar gidana Kuma da daughter ta bana maka last warning akanta ba tuna hospital don Kai baka da mutunci shine zaka biyota har Nan kana rike Mata hannu"?



Juyar da Kai Lahab yayi Yana karewa layin kallo Yana magana"wannan ne kofar gidan ka"?wannan ai kofar gidan wani ne nake tsaye kofar gidan ka gashi chan tsakanin sa da Inda nake tsaye akwai titin gonnati ma a sakani don haka kaji da kyau Nan ba filin ka bane,Yana karasa maganar ya juya ya Soma tafiyarsa Dad na binsa da Ido Harya bar layin sosai yaji mugun tsanar yaron a ransa.




*******************
Tura kofar maman nasa yayi ya shiga,zaune ya tarda ita a gaban mirror tana shafe shafe cikin shigan suit na aiki ga jakanta a gefe sai Sauri take tana shafa powder Jin an bude kofa yasa ta juyawa ta kalli kofar ganin sa yasata maida kanta ga mirror hade da d'aukar agogo tana daurawa a hannunta,matsowa yayi kusa da ita yayi Hugging nata ta baya ya daura kanta akan kafadarda Yana kallonta ta mirror hannu tasa ta ture sa ta baya amma yaki barin jikinta yace"Kai mama ki Bari na lale bayan Mana"


Rankwashin ta sake masa ta kansa da Sauri ya saketa Yana Susa wajen Yana turo Baki,mikewa tayi tsaye ta dau jakanta tace"kaga Adewale Naga baka da aikin yine yau shiyasa kozo kana likemun gardi da Kai matsamin na wuce papan ka na jirana a compound"haba mama magana fa nazo muyi fa shine Zaki shareni ki wuce"?tsayawa tayi tana kallon sa sai Kuma ta zauna a Inda ta tashi tace"toh Fadi naji in maganan kudine bani dashi in Kuma wani maganar ne kayi Sauri"


Yauwa mama na daman nace ayya Koh Zaki gidan su Lahab ne ki dubasa ayya mamata kije don Allah kije mamata ki dubasa tunfa jiya nasanar dake amma bakice kome ba"?


Kaga Adewale ni Karan kaina Ina son zuwa dubasa amma banson samun matsala da mahaifinka,shiyasa ban Masa zancen zuwa ba tunda yace bayason ka da yaran Nan ai ya Kamata kaima kaja jiki dasu"had'a fuska yayi yace"haba mama don Allah ace ke kome zakiyi Saida izinin papa gani nayi tunda Zaki office maizai Hana inkin tashi ki shiga ki dubasa shafshaf Mana"



Ah ah Adewale maganin Kar ayi Kar a Fara kadai bari Inna dawo saika Kira Lahab in na gaidashi a waya ai zaifi amma bazan bi abinda kake so nazo na samu sabani da mahaifin ka ba"?



Kenan mama ace kullum sai abinda papa yake so zakiyi menene a ciki Nan Nan baki da hanci bazaki ki dubasa ba"eh bazata dubasan ba Mara kunya Mara hankali duk abinda kake cewa Ina jinka sannan ke Kuma wallahi kin fanshe kanki don dako labari naji kinje gidan su yaron Nan ninasan abinda Zan Miki shige mu wuce kin sani nayi late a banza Kai Kuma saikayita zaman banza daka Saba stupid kawai,papa na karasa maganar yabar dakin mama na binsa a baya Suka barsa a tsaye Baki bude.


turo kofar gidan yayi ya Shiga bako sallama,mubeena dake zaune da takardu a gabanta tana bita don yau basu da pepar Koh dankwali babu akanta da Sauri ta d'au gyale dake gefe ta yafa a kanta,karasowa yayi cikin gidan yaja kujera ya zauna tare da kallon Nabeel dake ta faman dinki baima San da shigowar sa ba Saida yaja ya zauna tukunna ya tsaida dinkin Yana kallon Lahab da mamaki harma ya kasa hakuri yace"Wai Lahab Kaine ka fito a haka kaida baka da lafiya"


Kayya Nabeel wallahi na gaji da Zama waje daya,Inna zauna har wani zafi zafi nakeji a mazaunai na haba"mikewa mubeena tayi tana Jan tsaki don harga Allah maganar ya bata kunya Kuma ta fahimci Lahab bai dashi,dariya Lahab ya sake fahimtar abinda yasata shiga dakin,hararan sa Nabeel yayi yaci gaba da dinkin sa Inna ce ta fito daga bandaki tana kallon Lahab sai Kuma ta girgiza Kai tace"Lahab nake gani Koh bashi ba"?


Nine Inna ga kulanku na dawo muku dashi gaskiya abinci yayi dadi,d'aukar kulan Inna tayi ta shiga dashi kitchen,har yamma Lahab na gidan nasu daga Nan yayi gidan su Adewale,sai goshin mangariba ya koma gida sosai Abbu yayita Masa fada don ini kas baisha magani ba bare Allura kafar Dr biyu a gidan bai samun sa.





*******************
da misalin karfe 2 na dare Nnenna ce ta farka daga bacci saboda matsanancin kishin ruwa daya farkar da ita,mikewa tayi daga Kan gadon nata ta sauka,taka tiles na dakin take a hankali tasa hannu ta dau wayar ta,kunna wutan wayar tayi,tana sanyi da kayan bacci wando da riga hannu tasa ta bude kofar dakin ta ta fita,tafiya take a hankali kasancewar falon shuru ba motsen kowa kasancewar daman ita da peace ce kadai a downstairs sauran mutanen gidan Suna upstairs ne, kitchen ta shiga har lokacin bataji motsen kome ba ta bude fridge ta dau ruwa Mai sanyi a cup tasha ta maida cup in ta aje,mikewa tayi takama hanyar dakinta Harta gifta kofar dakin peace sai Kuma ta dawo baya, Jin surutai na tashi kasa kasa ga Nishi Nishi da take ji.



Matsawa kusa da kofan tayi ta kasa kunne sosai tana son ganin mike faruwa toh Koh dai peace bata da lafiya ne,Jin Karan mutum yasata Sauri sa hannu ta bude dakin tare da haska ciki,wani irin ihu ta sake da Sauri ta juya da gudu ta nufi barin wajen a guje har tana tuntube da flower dake zaune a kusurwar step in sauka a dakin................................




🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀





*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*

Page 84&85

da Sauri Abraham ya mike hade da daukar gajeren wandon yasa shima da gudu yabi bayan Nnenna data Jima da Isa kusa da kofarta a hankali yake kiranta gudun kada iyayen sa Koh Yan uwansa dake sama su jiyosu,dakin ta shiga da gudu jikinta na rawa ta maida kofar ta rufe harda murza ki tayi Kan katifarta ta kwanta hankalinta tashe.


Yakai 10 minutes a tsaye a bakin kofar gabaki d'aya jikinsa yayi sanyi tunda yake Bai tabajin kunyan abinda yake aikatawa ba irin na yau ba, juyawa yayi jiki a sanyaye ya nufi dakin peace ya bude ya shiga,har lokacin tana kwance ba sutura a jikinta don gabaki d'aya babu kuzari

Please Login or Register in order to submit comment