Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi ta yawon Neman mubeena Amma Bata ganta ba tana ta tambayar mutane,sai Kuma ta hango mubeenar ta shiga Hall na exam da Sauri tamike daaga Inda suke tsaye ta nufi hall in.....................




🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀





*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 77&78

Kauda idanunta tayi daga Kan na Ruky Jin an d'aga wayar tayi sallama, Adewale dake Kare da wayar a kunne amsawa yayi cikin Jin dadi Jin muryarsa yasa ta tamke fuska ta sabe jakanta a kafa hade dama lawiza nuni da hannu tana dawowa,tare ta Ruky dake tsaye tayi tace"haba mubeena yau throughout nayi ta neman ki a school Nan ban ganki ba sannan yanzun kin gannin Zaki wuce"?fuska mubeena ta sake Kamar ba kome tace"waya zanyi Kuma Ina bukatar sirri tana karasa maganar ta rabata ta wuce Ruky Baki ta sake tana binta da Ido hartabar hall in mamaki na cikata Koh Ahmad a gabanta mubeena ke waya dashi tunda suke mubeena bata tana zakud'awa da sunan amsa call ba koma waye ya kirata sai yau Zama tayi a kusa dasu lawiza tana sauke a jiyar zuciya kallon ta lawiza tayi sai Kuma ta tabe Baki batace kome ba.



Adewale dake Kare da waya a kunne Yana Jin duk abinda Suka fada, murmushi yayi yace"wake magana ne"?aikafi kowa sanin wake magana na d'auka wayar faduwa tayi tunda Yana hannun ka Inna dawo school na samu a gida"tace Masa cikin gara-gara shikam hade fuska yayi Kamar tana gabansa yace"kee Ni kike bawa umurni inkai wayarki gida kafun ki dawo toh in kikayi Wasa ma wayar tasha kenan Naga ta tsiya"waro Ido tayi tace"Kai Ni kake ma magana haka"?an Miki nace an Miki ke karfa ki Raina Ni don nace Ina so ki Ni ba irin mazan Nan bane bita zaizai"katse wayar mubeena tayi cikin bacin rai ta zauna a bakin baranda tana kitsema rashin mutunci da zata maka Masa duk lokacin da Suka hadu,mikewa tayi ta shiga Hall in har lokacin Ruky na ciki, mikawa lawiza wayar tayi Mata godiya ta juya tabar ajin.



Sauke wayar yayi a kunnen sa yakai duban sa ga Lahab dayayi tagumi hannu bibbiyu Yana kallon sa"Kai menene haka ka tasani agaba Kamar TV"?ba dole ba Adewale Ina ganin ikon Allah kalar soyayyar Nan taku tana ban dariya Kai a dole kayi waya da masoyiya sai Kuma ya kwanta ganin Ade Bai kulasa ba Yana sake Kiran number da mubeena ta kirasa dashi.


Lawiza ce ta zaro wayar tata tana kallon number Kamar bazata d'auka ba sai Kuma tayi picking call in ta Kara a kunne tare da sallama amsa mata Ade yayi Jin ba muryar ta bane yasa sa cewa"am dan Allah Koh mubeena na kusa ki bata wayar"lawiza tace"am sorry ta fita amma inta shigo na bata ta kiraka"no ki bari kawai basai kin bata ba in ba damuwa Zan iyya sanin time in da zaku kammala paper ku na yau"?dan shuru tayi tana tunanin ta fada Masa ne Koh karta fada Masa sai Kuma tace"3:30 afternoon zamu tashi, ok toh na gode katse wayar Adewale yayi ya mike tsaye Yana kallon Lahab sai Kuma ya nufi kofar Yana ce Masa"kaga nayi tafiya ta sai anjiman ka Allah ya Kara sauki"kala Lahab baice Masa ba Harya fita a dakin.




Misalin karfe 3:30 Ade ne cikin mota zaune a haraban makarantan Yana wowola Ido ata Ina zai ganta Kamar daga samq yaga ta fito a class tana Sauri ga dukkan alamu akwai Wanda batason ya ganta ne, fitowa yayi a mota ya tsaya Yana jiran karasowar ta itakam ma baka kula dashi ba hartazo zata gifta ta gaban sa,yace"malama dan dakatawa tayi sai Kuma ta kallesa wani harara ta watsa Masa tacigaba da tafiyar ta binta yayi Yana magana amma fir taki sauraran sa kasa hakuri yayi yasa hannu ya riko nata,da Sauri ta juya hade da d'aga hannu zata watsa Masa Mari sai Kuma ta tsaya tana bin fuskarsa da kallo ganin yanda ya rumtsa idon Yana jiran tsammanin ma rabbuka.



dai dai lokacin su Ruky Suka fito da sauran friends nasu tsayawa sukayi Suna kallon show in dake gudana a tsakanin Ade da mubeena sauke hannunta tayi taso fusge hannun da ya rike amma ta kasa saima janta da yayi da karfi ya bude gaban motar ya jefata,ya maida murfin ya rufe kokarin bude motar take amma ta kasa da Sauri ya zagaya ya bude driver sit ya zauna tare da tada motar bai kula da masifar da take Masa ba.


Tafiya suke shuru babu Mai magana hannu tasa ta bude jakan makarantan ta ta zaro memo nata tana lissafe lissafe tare da list in abubuwan da zata saya kwata kwata 3k ne kadai ya rage Mata shima cikin Wanda Ahmad ke bata tana Tarawa ne so take Tama Lahab delicious Mai dadi insun tashi zuwa dubasa takai Masa,tama rasa mezata saya tasan kaza dai intace zata saya da sayyayyan sa sai yafi 3k Yanke shawaran saya masa ice fish da sweet potatoes list takeyi tana gogewa sai ta gama inta buga calculate sai ya bata sama da 3k tsaki kawai taja ta cilla paper gefe ta dafe kanta tama rasa Mai zata saya na marmarin tasan kome ta sayo Masa akwai fiye da hakan a gidan su.




Adewale da duk hankalin sa na kanta Yana kallon duk wani movement nata"tsaya Zan sauka anan tace daidai lokacin Suka iso titin kasuwa tsayawa yayi yasa hannu ya dau paper kokarin kwacewa tayi yayi Sauri ya boye Yana murmushi yace"ke behave yourself Mana me haka"batayi magana ba sai kokarin fita da tayi tana fita shima ya fita ya rufe motar tare dabin bayan ta ganin ta nufi tsallaken titin,binta yayi a baya Yana kallon list in dan dakatawa tayi Harya karaso kusa da ita tace"Wai ya haka ne Mena Bina a Baya"kin kulata yayi Yana Kuma tsaye Kara footsteps tayi again ya bita abun haushi ya Bata sosai hakan ya sata Neman waje ta zauna shima zaman yayi Koh a jikin sa,ganin lokaci na gudu har ana Neman 4 na yamma yasa ta mikewa bata kulasa ba tayi cikin kasuwa Yana binta a baya,rumfan dankwali ta nufa tare da zaro 1k tace a Bata,kallon Mai rumfan Ade yayi yace a zuba Mata na 5k Aiko da Sauri Mai rumfan ya Fara zubawa kallon list in Ade yayi Yana Masa lissafin kayan gwari dake rumfan sa Wanda ta rurubuta,Kuma da yawa yawa yake saya itadai mubeena yunkurin barin wajen tayi yasa hannu ya damko hannunta zaro Ido tayi ganin yanda idon mutane ya dawo kansu abinka da cikin kasuwa tsoro ne ya kamata tahau rokon sa da Allah bai sakar Mata hannun ba Saida tamar alkawarin bazata tafi ba.



Gyada Masa Kai tayi ta fizge hannunta tare da jingina da kantin sayayya tana tsinewa Nabeel a ranta daya hadata da wannan fitina,sayayya yayi sosai sannan ya kalleta hade da cewa muje Koh binsa tayi a baya har wajen Mai kifi kusan guda shida manya manya na dari biyar biyar ya saya musu,tafiya suke bayan sun fito a kasuwar babu Mai magana har Suka iso unguwan nasu har kofar gidansu ya kaita Yana parking ta Mika Masa hannu hade da cewa"ban wayata Adewale"kin bata yayi sai bude motar da yayi ya sauka hade da bude boot Yana sauke laidodin cefenen juyawa kawai tayi ta nufi cikin gida batabi ta kansa ba dayake ta kwala Mata Kira akan ta tsaya ta dau cefenen amma Bata saurare Saba.



Bayan shiga gidan mubeena tsaye yake a kofar gidan nasu Sam ya kasa shiga haka kawai yaji baison shiga yafi 20 minutes a wajen ya hangi Nabeel ya fito matsallaci yana nufo gidan nasu tun daga nesa ya hangosa karasowa yayi cikin fara'a ya dake kafadar Ade hade da cewa"mutumina ya na ganka tsaye da laidodi baka shiga ba Kuma"



Kaga Nabeel mubeena na dauko daga makaranta muka tsaya a kasuwa tayi tsayya Wai kawai don na biya shine taki karban kayan,wani kallon tuhuma Nabeel ya Masa yace"kana nufin ka koma ka daukota kenan"?dan cijewa Ade yai gudun karya bada kansa yace"eh na koma na dauketa saboda wayarta data Bari a motar Yana maganar ya Mika ma Nabeel wayarta karba kawai Nabeel yayi sannan Bai gamsu da zancen ba amma dai baice kome ba ya karbi cefenen ya shiga gida sauke ajiyar zuciya yayi ya shiga motarsa yabar arean nasu.



Aje cefenen Nabeel yayi a gaban mubeena dake cin abinci a tsakar gida hade da d'osana Mata wayarta akan cinyarta baice kome ba ya shiga dakin sa,mikewa Inna tayi tana tambayar mubeena hade da bude laidan tace"ya haka Nabeel zaka kawo Abu bazaka Mana bayani ba saika aje ka tafi Kamar ka samu wahalallu washe baki tayi ganin kifi manya da dankali ga kayan Miya enough"ah ah ikon Allah Nabeel wannan tattakwashin fa na menene Koh dai laidan cefenen wani ka sato don nasan Kai tsoron Allah Bai wadace kaba"?



Lekowa yayi daga cikin dakin NASA fuska a daure yace"waini me Kika maida nine toh cefene dai ba nawa bane na mubeena ne sako aka ban na kawo Mata in Kuma bataso ki amsa kawai rabonki ne"juyawa Inna tayi ta kalli mubeena da kyau Jin abinda Nabeel yace tace"kee Yar nema waye Kika aika Koh ya bada sako a baki,Ni ban aike kowa ba,da mamaki Inna tace Nabeel kanaji Wai Bata aike kowa ba toh Kai waya baka"?fitowa yayi gabaki d'aya daga dakin nasa yace"Adewale ne yace sunje kasuwa shine tayi cefene ya biya itakuma taki amsa"


Mikewa kawai Inna tayi ta shiga daki tabar cefenen a wajen shima Nabeel keken sa ya hau ya Kama dinki bai sake magana ba tana gama cin abinci sallah tayi tadau cefenen tayi kitchen dashi ta Soma girki.





********************
5:26pm mota ce tayi parking a tsakar gidan sauka Yan makarantan sukayi duk a gajiya kowa na goye da school bag nasa a baya zulaihat ce a gaba Kamar zataci da Baki saboda fitsari daya cika Mata Mara Kuma batayi a makarantan ba Saida Suka shiga mota ta farajin sa sosai shigowa falon sukayi ita da muneera sukayi sashen su,shima Rahab nasu sashen ya nufa tura kofar yayi ya Shiga wanka yayi ya sanya kayan gida da Sauri ya fita a dakin kitchen ya shiga Suka kusa cin Karo da muneera d'auke da plate na abinci a hannunta matsa Masa tayi ya shiga kafun itama ta fita abinci ya zuba a plate ya dau drink Mai sanyi ya fita a dakin Zama yayi a babban falo Yana cin abincin sa,Saida ya gama tas kafun ya mike baidau kwanon bama ya tafi ya barsa a wajen.



Zaune Lahab yake gabaki d'aya ya tattara hankalin sa Akan TV dake aiki a dakin ball take kallo gabaki d'aya wasan ya tafi da imanin sa aka turo kofar dakin,d'ago kansa yayi ganin Rahab ne yasa sa maida Kan ga TV,Zama Lahab yayi a gefen sa Yana kallon sa a hankali yace"aikin kenan baka bawa kome muhimmaci sai ball wallahi Lahab gwara ka gyara rayuwar ka wannan bayi bane"wani kallo Lahab ya Masa sannan yace"Kai da Allah dakata nifa kana kallo na innan insha Allah abinci na na cikin kwallon kafa Kuma Kai da kanka ka San na iya"da mamaki Rahab yace shi kwallon kafan ne abinyi"?kwarai ma kuwa Kai kasan kudin da yan kwallon suke samu kuwa Kuma Ni Koh ba kudi yake kawowa ba nidai Ina da sha'awar Yi"?




Mika Masa card nasa kawai Rahab yayi yasan duk abinda sai gaya Masa Lahab ba ganewa zaiyi ba"amsar card in Lahab yayi da mamaki yace"a Ina ka dauko ATM nawa"?


Tashi tsaye Rahab yayi yace"ita ta bani a school"zaro Ido Lahab yayi yace"ita wa"?Wance ka baiwa card in Mana Koh kana nufin baka bata bane"?shuru Lahab yayi bai amsa Masa ba shima Rahab bai motsa ba sai Kuma ya koma ya zauna tare da fuskan tar dan uwan nasa yace"wacece don Allah"? remote Lahab ya d'auka ya Kara volume na TV ya mimmmike kafa ya cigaba da kallon sa Bai saurare Saba.


Bayan mangariba zazzaune suke akan dinning Suna dinner gabaki dayan su Lahab da Addayiya ne kawai basa dinning in don tunda Lahab ya dawo basu cika cin abincin da aka dafa ba shida tsohowar tsabar irin girke girken da ake kawo musu na namomi gashi yauma mamin sa ta turo su mahraz sun kawo Masa pepper chicken,ya jafar ne da iyalan sa Suka kwada sallama a falon amsa musu akayi gabaki d'aya cikin farin ciki zazzaunawa sukayi a falo mamu ta Mike taje ta dauko musu drink's da water ta aje musu gaggaisawa akayi Majid ya mike direct ya nufi dakin Addayiya don sunyi waya da lahab,tura kofar yayi Koh sallama babu zaune Lahab yake Yana cin kwai dafeffe,mikewa Addayiya tayi da plate na nama a hannunta ganin Majid yasa ta sakin tsaki amma batace kome ba ta koma ta zauna tana holo yashigo ba sallama Kamar dan kafurai shidai bai kulata ba sai zaman da yayi akan gadon ya kwace plate na kwai dake gaban Lahab ya d'auka ya Soma ci,da Sauri Addayiya ta kwace tace"Kai majidu baka da kunya Meka kawo Mana bare kazo ka samu dan marayan Allah Yana fama da jiki ba tausayi ka dau kayan jinya kana lashewa ai wannan mugunta ne?


Kala baice Mata ba sai kallon Lahab dake kallon sa yayi ya kalli Addayiya sai Kuma ya mike tsaye yace"don Allah ka tashi muje dakin ka menene na Zama a dakin tsohowar nan duk warin tsufa"uwarka da ubanka ne masu warin tsufa bani ba dan banza kawai gagare"ganin fad'an nason girma don sai CeCe kuce suke yasa Lahab mikewa ya nufi kofar Yana ma Majid magana akan suje sashen su,Majid Saida ya Bari Lahab yabar dakin kafun ya fizgo laidan kazar dake gefe ya fita da gudu a dakin.





***************
Kafun mangariba mubeena ta kammala girkin ta dankalin turawa ne ta soya sai ferfesun kifi ice fish,duba kwanukan nasu tayi gabaki d'aya sun tsufa Basu da kula sabo raba abincin tayi ta zubawa Inna nata da ban Nabeel da ban tasa nata sauran data keda niyar kaiwa lahab,hijab nata ta rufa ta fita gidan wata amarya dake kusa da gidan su,Kuma tayi sa'a ta samu Sabon kula guda biyu na tuwo dana Miya,sabo gal Mai kyau dawowa tayi ta zuba dankalin daban kifin daban ta aje a kwando,ita dai Inna da Ido kawai take binta,wanka tayi Koh abinci ta kasa ci bude akwatinta tayi ta dau wani less nata Mai kyau purple zani da riga gyale fari ta d'auka da takalmi ta yafa fitowa tayi a dakin a Karo na hudu tana duba Inna amma abin haushi har lokacin batayi niyar mikewa ba kasa hakuri tayi ta tama inna magana tana cewa"haba Inna dare fa nayi don Allah ki tashi mu tafi Mana Ina da karatun da zanyi fa"kallon ta da kyau Inna tayi tace Wai ke yaushe kuka Fara shiri da Lahab in har kike rawan kafa zakije ki duba sa ga wani uban cefene da kikayi Kamar Zaki gidan surkunaye"gabanta ne ya yanke ya Fadi Jin Inna ta jefo jirginta amma ta dake tace"shikenan nama hakura da zuwa"tayi Kamar zata koma daki amma a cikin zuciyar ta Allah Allah take kada Inna taki tsaidata.




Wallahi baki Isa ba tun yamma kike uzzuramin sannan yanzun kice kin fasa zuwa, bari ma nadau hijabina muje,dakatawa mubeena tayi ta hade rai ta tsaya tana jiran Inna data shiga daki dauko hijab nata,kulan abincin ta d'auka ganin Inna ta fito rurrufe kofofin su mubeena tayi Suka fita a gidan,tunda Suka dotse gate na gidan su Lahab gabanta ke faduwa rabon ta da ta Shiga gidan Harta manta tun wani Shiga da tayi Mami taci Mata mutunci tun Suna yara Bata sake taka gidan ba sai bana da zata yanda suke nufo gidan haka dukan da kirjinta keyi yake daduwa,wutan lantarki ne Kamar rana yake tsaye a kofar gidan ga flowers dake shiki,hannu Inna tasa ta bubbuga gate na gidan....................................................





🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 79&80

da Ido Mai gadin ya bisu sannan ya bude gate in tare da matsa musu saboda ya gane Inna ba yau ta Saba zuwa ba Akan Case in Lahab da Nabeel tun Suna yara,tafiya suke mubeena na binta a baya duk inda Suka wuce sai mubeena ta Kara waigawa ta kalla da kyau gidan gabaki d'aya ya chanja Mata ganin irin daular da yake ciki yanzun sama da da,tsayawa sukayi a kofar falo Inna nata kwada sallama dayake daman kofar in ba bell aka danna ba ba Jin mutum za'a Yi ba in Yana magana hannu mubeena tasa ta danna kararrawan.



Kallon ya Umar ya jafar yayi yace"gobe in Allah ya kaimu za'a kawo lefen yarinyar Nan umaima Koh"?kwarai ma kuwa gobe ne insha Allah"toh Allah ya kaimu saiku tashi mu tafi dare nayi sai Allah ya kaimu gobe in zaku dawo ma saiku dawo,mikewa dukansu sukayi harda nenne duk da yaran sunso a barsu su kwana amma ya jafar yaki yace gobe akwai school,kallon nanne yayi yace"Ina Majid in da Aisha kuma"mamu ce tace wata kil Majid na wajen Lahab ita Kuma Aisha bazai wuce tana can tana like da umaima ba, kasanta da zancen zuwa biki daga auren mutum ya tashi zata Fara like Masa"Addayiya dake zaune ne tace,kaji Shashashar banza ke zulai shiga ki kirata Kai Kuma uzaifa kirawo Majid in yazo mu tafi"ring na bell Inda sukaji shiyasa Anwar mikewa ya nufi kofar kamawa yayi ya bude sai Kuma ya waro Ido yace"innan Nabeel yau Kuma me Lahab yayi kin fa San baida lafiya Koh fita bayayi karma kice Yama Nabeel kaza"?hararan sa tayi da murmushi a fuskar sa ya matsa Mata ta shige mubeena na binta a baya tad'anji sanyi ganin yaran gidan har yanzun Basu da girman Kan masu kudi in ka cire Shareef yafi kowa mugun hali da murd'adden hali a gidan.



Ah ah sannu da zuwa wa nake gani Kamar Inna kayyu?da murmushi Inna ta karaso cikin falon ta zauna akan kujeran da Addayiya ta tashi tana nuna Mata ta zauna mubeena Kan kanta a kasa tazame ta zauna a kasan carfet"nice hajiya Asma'u"gaskiya ne barkanku da zuwa haba Yan Mata ya da Zama a kasa ki hau Kan kujera Mana kin hawan mubeena tayi sai wani susunkuyar da Kai take komawa zaune ya jafar yayi Suka gaggaisa dasu Inna, fitowa umaima tayi da hijab a jikinta sai Aisha dake gefenta Suna magana a hankali Suna dariya tare da muneera da aka aika ta Kira Aisha kallon umaima mamu tayi tace"ke Kuma meye haka Ina Zaki"dan rausayar da Kai umaima tayi batace kome ba sai Aisha ce tace"mamu Wai zata bimu gidan mune kinsan gobe za'a kawo Kaya shine Wai tanajin kunya"rike Baki Addayiya tayi tace"kunya Kuma Koh munafurci koma menene kwadaiji dashi,mikewa ya jafar yayi again Yana kallon uzaifa daya fito babu Majid kallon sa yayi ya tambaye sa Ina majid in?Wai shi Anan zai kwana"shuru kawai Addayiya tayi Albarkacin su Inna dake falon da wallahi Majid bazai kwana musu a gida ba,fita ya jafar da iyalan sa sukayi su ummu da sauran yaran Suka rakasu compound har gaban mototin su, Bismillah kuzo muje kugansa Yana dakin su,mikewa sukayi Suka bi bayan ta tana gaba Suna bayan ta har lokacin hannun mubeena d'auke da kwandon kwanuka gabaki d'aya jikinta yayi sanyi zuwa da tayi ta tarar da plates na kaji Baja Baja a falon da abinci Mai Rai da lafiya Wanda aka kawowa su nanne,sai taji ta muzanta ita da ferfesun kifin ta da dankali.


Zaune suke da Majid Suna Hira system na Rahab ne a gaban Lahab Yana chatt nasa sai Majid dake Masa Hira Yana cin kazar daya d'auka a dakin Addayiya,turo kofar dakin a kayi Addayiya ta shigo Inna na binta a baya waro Ido Lahab yayi da Suka had'a Ido da mubeena"Bismillah ku zauna ga waje Addayiya tace musu Zama sukayi"kallon Inna Lahab yayi ya gai data ta amsa tare da Masa ya jiki mubeena ce ta Fara Masa ya jiki ya amsa hade da cewa"big Aunty mekika kawo minine haka Naga kulan sabbi alamu dai abun ciki ba karamin dadi zaiyi ba"?dariya Inna tayi tace aiko ka canka daidai kasan Ni bazan tsaya bata lokaci wajen maka girki ba"da murmushi Lahab yace"kaiyya Inna Ina ma Kika iyya bare yayi dadi"dariya dukan su Yan dakin sukayi Majid Kam Inna kawai ya gaidar idanunsa Kam akan mubeena Wanda yasa Lahab sa hannu ya mintsine Naman cinyan sa dan Kara ya sake ya sauka akan katifar ya koma kasan carfet ya zauna Yana jama Lahab Allah ya Isa,kallon kulan Lahab yayi sai Kuma ya mike ya dawo kusa da mubeenar hannu yasa ya bude kulan sai Kuma da Sauri ya kalli mubeena,mikewa yayi ya dawo bakin gadon da kulan ya aje sai Kuma ya sake budewa yadau marfin ya zuba dankalin akai yasa miya ya Kama ci,Yana gyada Kai sosai mubeena taji wani mugun dadi ganin Lahab yaso abinda ta kawo duk da sunada fiye da hakan a gidan su,duk kankantan kyauta da mutum Yama Lahab baya botsaresa sosai yake nuna Masa ya kaunace abin Koh da kuwa bai Masa ba baya nunawa.






Mikewa Inna tayi tace toh hajiya mu zamu tafi Allah ya kiyaye na gaba"Ameen Suka amsa duk da mubeena bata ji dadin tafiyar da Inna tace zasuyi yanzun ba amma ba yanda ta iya haka sukayi sallama da mutanen gidan Suka tafi,Suna fita a dakin Lahab ya aje plate in don harga Allah ba yunwa yakeji ba kawai dai yayi hakan ne don nuna Mata Jin dadin sa Sarai yasan halin mubeena haka zalika karon farko data dau Abu ta basa cikin mutunci babu masifa"da Sauri Majid ya dawo kusa dashi Yana bin kofar da kallo har lokacin sai Kuma yace"Kai wannan fa wacece Ni fuskar tama familiar ne gareni"hararan sa kawai Lahab yayi baice kome ba naci sosai Majid ya ringawa Lahab a Kan mubeena amma bai kulasa ba gajiya Lahab yayi yace Masa"kaga Majid banason surutu haba don Allah Kai baka Isa kaga Mata ba jikinka sai ya ringa rawa toh ka kiyaye kanka wallahi"tsaki kawai Majid yaja da Sauri Lahab yace"yauwa don Allah Ina so ka taimake Ni"wani banzan kallo Majid yayi Masa shima baice kala ba matsowa kusa dashi yayi Yana rokon sa.






Hannu Majid yasa ya hankada Lahab Sora kadan yafadi akan hannun sa mikewa Lahab yayi ya shiga toilet bucker ya cika da ruwa Majid na kwance kawai yaji an kwarara Masa ruwan sanyi kafun ma ya dawo hayyacin sa Lahab yabar dakin da gudu yayi dakin Addayiya tare da maida kofar ya rufe yahau Kan gadon ta ya kwanta sai bacci.





*****************
Zaune take rike da wayar da Abraham ya kawo Mata tare da dogon gargadi kada ta bari kowa ya gani sosai take jujjuya wayan babba be babu laifi Kiran Tecno danna wajen da yace Mata zatanayi in zata kunna tayi take haske ya kawo sosai take kallon screen in wayan tama rasa ta Ina zata Fara wannan shine Karo na farko data rike waya nata na kanta papa nada waya amma karamace ba irin wa'innan ba,shige shige ta Fara kasancewar ta Yar makaranta waya bazai bata wahala sosai ba shige shige tayi tayi har dare sosai,kafun ta kashe wayar kiki ta d'auka ta basa magani ta kwantar dashi itama ta kwanta abinta.





Washe gari da safe tun asuba ta tashi share gidan tayi da wuri Kamar kullum ta Gama aikin ta na safiya ta shirya ta tafi makaranta Kamar jiya yauma Abraham ne ya kaita duk da mom bata so amma babu yanda ta iyya ganin yanda Dad ya Soma chanjawa a Yan kwanakin Nan.




**********************
Bayan sallan asuba gabaki d'aya Yan gidan sun koma bacci sai kusan 7 Suka hallara akan dinning yaukam harda Lahab abinci sukeci Majid ya kalli Abbu yace"Abbu wallahi jiya Lahab jika katifar da Zan kwanta yayi ya jikani da ruwa karshe ma dakin Shareef na kwana"shuru Abbu yayi nadan wasu minutes

Please Login or Register in order to submit comment