Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ware mu barka.

"Hhhh yan iska meyasa baku shigo ciki ba, kuma uban wa yace muku ina gidan tun safe"

Hh ai tunda mukaji kace xaka gidan mami nace badani ba, don nasan inkaje baka ga ta dawowa yanzun ba.

"Kai nabeel baka da mutunci mamar tawa?

Sorry aboki wallahi mamin kan nan nasan yau saita kare mana tanadi a gidan ta shiysa nace bazani ba.

"Naji yanzun ina muka nufa"

Adewale ne yace Masjid mana bayau friday ba?kuma naga time ya kusa almost 1:00 yanzun fa?

"Ok yanzun ya zamuyi da keken nan don nidai sai dai na ware na barku kuhau machine"

Wallahi nan ne kuma baka isa ba, sai dai mu shiga gidan su duwaisu mu aje keken in mu tafi duka a keke napep in?

Ba musu lahab ya yarda suka aje keken a gidan wani abokin makarantan su, suka shige masallaci lokacin da suka iso masallacin a bakin titi suka bar adewale bakin wani shago ya zauna, yana jiran su yayin da su kuma suka wuce cikin masallacin.

Bayan an idar da sallah kasuwa suka wuce, don sam nabeel da ade basu sayi jesen ba aje kudin sukayi sai lahab ya samu saisu had'a su saya tare.

Jese suka sasayawa kansu kala d'aya, lahab ya had'a da socks da takalmi duka, haka suka ringa yawo basu sukayi niyar komawa gida ba sai kusan 5 na yamma, nabeel da lahab harda ade wale kowa na rike da laidan kayansa, sukabi gidan su Duwaisu suka karbo keke.

Ade suka fara rakawa gida, a bakin get suka tsaya, kallon su yayi sai kuma ya mikawa nabeel kayan sa, gashi nabeel ka rike mini gobe in zamu tafi zanzo na karba?

Hhh"kace dai kana tsoro"lahab yace yana dariya

Shuru kawai yayi ya shige gidan da kekensa ganin motar baban sa na nufosu alamu dai dawowar sa kenan, ade na shiga gida, suma su lahab suka juya zasu tafi da sauri baban ade ya sauke glass na motar sa, hiii kuzo nan ya kirasu cikin turanci.

Da sauri suka karaso inda yayi packing gai dashi sukayi bai amsa ba sai binsu da yayi da kallo idanunsa suka sauka akan lahab, kaiiii yaron nan daga ganin idanunka baka da kunya.

Shuru lahab yayi baice kome ba yana jinsa ya cigaba dacewa, toh bara kuji daga yau sai yau karku sake koh da sunan wasa naji koh na ganku da yarona especially kai bakin nan,ya nuna lahab, watoh ku gaku yaran hausawa muslim zaku mayarmin da yaro irin ku ku cutar mini dashi koh?yan ta'adda toh yafi karfin ku mugaye ku wuce ku bani waje munafukai kawai?

Sumui sumui suka juya suka kama hanyan layinsu gabaki d'ayansu basu sake magana ba koh gulman baban ade, don su haka suke gabaki d'ayan su suna girmama iyayen abokan su, sam don d'aya daga cikin su don iyayen su sun zage dayan su baya damun su duk da zagin da baban adewale ke musu yayi yawa harya wuce iyyaka.

Gidan su nabeel suka je aje kayan sa shima lahab yayi a wajen nabeel kafun ya nufi gida.

Tafiya yake hankalinsa kwance harya iso kofar gidan su, hannu yasa xai tura kofar get, sai kuma yaja da baya ganin ana kokarin bude kofar ta ciki, Abbu ne ya fitoh cikin jallabiya hannunsa rike da calbi sai yaransa dake binsa a baya harda Rahab dagani dai masallaci zasu don an fara kiran sallan mangariba, sunkuyar da kai yayi ya basu hanya.

Dubesa kamar mutumin kirki, shige mu tafi masalaci, Abbu yace yana masa pointing da yatsar sa, ba musu lahab ya juya yabi bayan su.


Bayan an idar da sallah haka Abbu ya sakasu a gaba suka kamo hanyar gida don masallacin baida nisa da gidan su, asalima ginin gidan su manne yake da masallacin, tun a hanya yaga yanda Rahab yayi banza dashi sai wani shamasa kamshi yake amma koh a jikinsa.


Don shi harya ma manta da zancen 11k na safiya wallahi sai yanzun dayaga yanda rahab ke had'e da fuska ya tuna amma dai baice kome ba har suka shiga gida.

Bude kofar lahab yayi don wannan karo shine a gaba, mamu da ummu ne zaune a falo dukan su suna sanye da hijab dagani dai sun idar da sallan mangari bane, wuce su lahab yayi, ya nufi kofar daya fitoh da safe.

Tura kofar yayi ya shiga wow babban falone mai dauke da manyan kujeru na gani na fad'a sai d'akuna sama da bakwai dake falon, nufar d'aya daga cikin kofofin dake falon yayi, tura kofar yayi ya shiga d'akin da sallama.

Dakine babba mai d'auke da kayyaya ki irin na samaru kan zamani, wardrop ne guda biyu sai manyan katifu guda biyu d'aya a kusurwar daki, dayan ma haka an gyara katifun sun matukar kayatu da zanin gado, sai mirrow dake d'auke da kayan kamshi irin su turare da mayuka, labuleye sun kewaye rabin d'akin, shiga yayi ya tura kofar ya rufe.

Toilet direct ya nufa wanka yayi babu jimawa sai gasa ya fitoh, wardrop in ya bude wando da riga na bacci ya d'auka ya saka fisa turare yayi ya koma d'aya daga cikin katifar dake kwance akasan tiles na d'akin ya kwanta, lumshe idanunsa yayi kawai yayi shuru duk da yasan yanzun ne lokacin cin Abincin dare Amma bayaji zai iyya cin kome gaskiya.

Turo kofar d'akin Akayi da sallama, bai bude idanunsa ba ya amsa.

Tsayawa umaimah tayi tana kallonsa ganinsa da kayan bacci kuma a kwance, small uncle wai inji Abbu kazo muci abinci?

Kallonta yayi irin kallo mai kama da hararan nan"ke kuma munafuka watoh gidan mamina kike zuwa kina kai gulma koh"?

Hhh dariya ta sake da karfi tana rufe bakin ta, ashe yau gidan mami akaje shiyasa ya shareef yace min yaganka da jallabiya kum......da sauri ta kwala kara ta ruga a guje ta bar d'akin, ganin lahab ya mike harya sabi bell nasa zai nufota.

Kwafa kawai yayi cikin jin haushi ya koma ya kwanta, sai kuma ya mike da sauri jakan makarantan Rahab ya bude takardunsa ya fitar English And maths ya d'auko yana dudubawa.

Bude kofar d'akin akayi, Amma bai dago ya dubi waye ya shigo in ba, ji kawai yayi an fizge littafin Hannun sa, da sauri ya d'ago yana dubansa, Amma baice kome ba.

Wallahi karka sake taba mini littafi lahab?daga yau sai yau tunda baka da mutunci bakasan idon sani ba harni zaka fizgewa kudi? don kaje ka kashe a banza da abokan banzan ka?in karatu kake so kaje makaranta ni ba bawanka bane.

"Don Allah ya isheka haka d'an iyayi kawai zakazo kana tsayamin akai zaka mini rashin mutunci, lahab sosai ya rufe D'an uwansa da masifa, shuru kawai Rahab yayi ya koma kan katifarsa da littata fansa, Aje littatafan yayi ya d'au system yana dannawa.

Tsaki lahab ya sake ya koma ya kwanta cikin bacin rai don shi ya tsani abin haushi a rayuwar sa, shi gabaki d'aya ma ya manta da zancen fad'arsu na safiya, tuni ya watsar Abinsa, kwanciya shima yayi yana kallon d'an uwansa dake rike da system haushi yakeji sosai don sam Kin saya masa akayi, aka saima d'an uwansa kome aka tashi Rahab ake bawa koh a basa abu, Amma shi ba'a masa.



*************
Nnenna zaune take akan kujera, kwalli d'ayan dake falonsu,littatata fanta take dubawa Ta rasa me zatayi ga yunwa ga kewa, ita kad'anta take rayuwa a d'akinsu Babu uwa ba kawaye Babu kowa sai kulenta dake gefe a zaune,ji kawai tayi an banko kofar falon.


Da sauri ta mike papane ya shigo cikin mayye Yana tangadi hannunsa rike da laida baki karami,cikin magana irin na Yan kwaya yake k'wala Mata Kira,Nnenna!!

"Yes papa"tace tana toshe hanci Jin irin gasar da mahaifin nata keyi ga wari,Mika Mata laidan yayi da sauri ta karba don Wallahi yunwa takeji Tana Kai hannu ta Amshi laidan kawai ya kwararo Mata Amai a jiki da sauri ta matsa gefe tana fashewa da kuka ganin Alelen Akwai dake laidan ma ya Fadi a kasa Amai ya tabasa ga jikinta duk Amai,da kuka ta fita waje da gudu.

Papa dabaya cikin Hayyacin sa kiranta kawai yake Nnenna!!Nnenna!!Ina zaki??


Kasa basa Amsa tayi da sauri ta kwabe rigan dake jikinta. Tabar vest don ita ba brz bane da ita,ruwa ta iba da sauri tayi bandaki.

Tana wanka tana kuka a hakan harta kammala, ita abinda yafi Bata Takaici Abinda zataci Daya baci da Amai yafi kome Mata ciwo,falon ta shiga tana kallon Papa dake kwance Kamar macece Ga Amai a zube a gefe.

Tsumma ta d'auko da ruwa ta share simintin don d'akin ba kome a kasa sai simintin kwashe Aman tayi ta rufe musu kofar falo,kulenta dake gefe a rakube ta d'aukosa hawaye na cika Mata ido, yau hakan zasu kwana da yunwa kenan.

Kwanciya tayi tare da zare glass nata ta aje a gefe,kulen ta d'auka ta kwantar a gefenta,A sannu sannu har bacci ya d'auke ta.


Misalin karfe 1:30am na dare,dare ya tsaga, A hankali kulen Nnenna(Kiki)ya mike daga kwance, sauka yayi akan taburmar ya girgiza jikinsa da karfe a take ya sauya Kama daga fari zuwa baki kirim, kwayar idanunsa ya sauya shima zuwa jajazur,da hanzari yayi hanyar kofar d'akin fita yayi Zuwa falo, kallon Papa yayi sai Kuma y..............









✨Ruqeenjalal✨




πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ


Free page🀧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*


page 9⃣&πŸ”Ÿ
Sai kuma ya ruga yayi kofar falon ganin papa na motsi kamar xai farka, yana isa kofar kamar walkiya a take ya bace batt.

Nnenna dake bacci jin wani irin sarawa da kanta yayi wanda yasata farkawa a gegece kama kan tayi gam tana Kiran jesus, ji take kamar ana tsikara mata kwakwalwa da Allura, gashi d'akin duhu don koh touch basu dashi mai kyau sai fitila shima ya mutu.

Jin abin ya saketa kad'an yasa ta mikewa a hankali hannu tasa a duhun tana lalubar glass nata har Allah yasa ta gane, d'auka tayi tasa a idanunta Amma abanza don kamar yanda bata kallon kome da bata saka ba haka ma yanxun.

Cire glass in kawai tayi ta lallaba ta mike tsaye da sauri ta dafe kanta jin juya mata da kan keyi, ga wani irin jiri dake dibarta, da sauri ta dafe jikin falangen d'akin nata, da babu shakka zatasha kasa.

Kuka ta fara a hankali ta rarrafe zuwa kan katifar ta, kwanciya tayi sai kuma ta mika hannunta zata taba kulenta, amma bata jisa ba kiransa tayi cikin muryarta mai dadin sauraro cikin rauni"kiki!!kiki!!"

Ke Nnenna bazaki mini shuru ba saikin cikamin kunne aikin banza, taji muryar papa daga falo cikin magagin bacci.

Shuru tayi tana tunanin taima kulen ya chanja wajen kwanciya ne.

Haka tayita fama da motsen kai har 3 na dare kafun ta samu bacci ya d'auke ta.


****************
Asuban farko Lahab dake kwance a katifarsa lulube da blanket ga sanyin AC dake dukansa, ware idanunsa yayi a hankali ya yaye blanket inda ke kansa, bakinsa d'auke da Addu'an tashi daga bacci ya mike zaune.

Hannu yasa a drower dake gefen katifar ya kunna hasken wayansa,zuro kafarsa yayi a kasan cafet inda ke shimfid'e a kasan tiles na d'akin, mikewa yayi tsaye a hankali hade da mika, toilet ya nufa, ya bude ya shiga kunna hasken ban d'akin yayi,brush yayi ya hada ruwan dumi ya watsa a jikinsa, Ya d'auro Alwala ya fita a bandakin.

Kan katifar da d'an uwansa ke kwance ya matsa sai kuma ya koma toilet in da sauri, ruwa ya tara a buta yana zuwa yaja kafar Rahab kasan tiles ya dundula masa ruwan sanyin.

Ihu Rahab ya tsake hade da salati ya mike tsaye ganin Lahab ne, ya masa wannan rashin mutunci daman ya saba masa.

Tsaki kawai yayi ya juya ya wuce toilet don shi sam bai iyya fad'a irin lahab ba sai zuciya.

Shimfid'a sallaya lahab yayi ya sauya kaya zuwa wando da riga, hawa sallayan yayi ya tada sallan nafila,Rahab na fitowa a daidai lokacin yajin An fara kokarin shiga masallaci hakan yasa Lahab sallamewa.

Masallaci suka wuce dukansu mazan gidan, basu dawo ba sai 6:30 Abbu kam komawa bacci yayi haka yaran giyan kaf daga matan har maxa inka cire tagwaye sai ma'aikata ke zarya, Rahab zaune yake yana bitan haddansa, yayinda lahab ya sanya kayan ball wandone dogo na roba, sai riga da boot ya sanya sai towel ya rataya a wuyansa fita yayi a d'akin.

Firij na falo ya bude ruwa gora d'aya ya d'auka ya nufi kofa da jogging, gudu yake a hankali harya fita a gidan su a haka ya gangara layinsu har kofar gidansu adewale.

Aiko yana tsaye sanye da wandon ball guntu da riga sai takalmi alamu shima jiransa yake hannu ya bawa lahab suka kashe, tare da tambayar ya suka waye garin yau, daga nan gidansu Nabeel suka nufa da sallama suka shiga gidan.


Addar nabeel ne xaune a tsakar gidan tana banbaran masara, Amsa musu tayi ba tare da ta d'aga ido ta kallesu ba, lahab ne ya wuce d'akin yayin da Adewale ya koma kofar gida ya tsaya ganin irin kallon banza da mubeena ke masa,lahab na shiga ya samu nabeel sai bacci yake koh sallan asuba bai tashi ba, Ruwa ya ibo a randan inna yazo ya kwara masa a jiki, mikewa yayi cikin masifa yake zagen lahan, shima yana ramawa, sai da yayi da gaske kafun ma suka samu yayi sallah suka fita tare.


Da misalin karfe 8:00 lahab ya nufo gida jikinsa duk ya jike da gumi alamu dai dawowarsa kenan daga jogging, kofar get nasun ya bude ya wuce cikin gida, tura kofar falon yayi koh sallama babu, Rahab ne dasu munira da zulai ke karyawa cikin uniform na islamiyya yayinda rahab ke sanye da jallabiya fari da hula, su kad'ai ke zaune akan daining in, dayake Al'adan gidan su ne ranan weekend kowa na baccin safe sai su yara dake zuwa islamiyya, da ma'aikata hatta Addayiya bata tashi a weekend.

Good morning uncle?

Kallon xulaihat Lahab yayi kamar baxai Amsa ba Amma kuma saiya basar ya amsa mata da "lafiya " don karya yarfata, kawai ya wuce Abinsa.

D'aki ya shiga direct ya wuce toilet wanka yayi ya fitoh daure da towel wando kawai ya saka dogo, yad'au waya yakira mai aikinsu, ta kawo masa Abinci.

Ba'afi 5 minutes ba sai gata d'auke da tire zata kai shekara 50, da sallama ta shigo D'akin Amsa mata yayi, har gaban katifarsa taxo zata aje masa abincin.

"Subhanah Gogoji lafiya kuwa"Lahab yace da mamaki ganin saura kad'an ta xubar da abincin.

A sanyaye tace lafiya klau ta juya tana tafiya, harta fita A d'akin lahab kallonta yake, haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damunta.

Abincin ya bude macaroni ne da miyar kaxa sai ruwan tie, karyawa yayi yana kamawa ya d'an xauna kad'an Abinvin ya sauka before ya kwanta abinsa, A hankali har bacci yayi Ahon gaba dashi.




****************
Nnenna bata farka ba sai kusan 7 na safe dayake yau babu school share d'akinta da falo har waje tayi, tsummo karansu ta tattaro masu datti, bunu guda ta aje a waje, ta dawo falon kallon papa tayi dake xaune a kujera" good morning papa"

Morning daughter?

"papa abani kudi nasai omo zan mana wanki"?

Ah ah daughter ina naga kudin omo yanzun sai dai ki bari gobe na baki kudin in mun dawo church sai ki wanke?

Ok papa kawai tace tana mikewa tsaye.

Daughter ga wannan ki dafa mana doyane da manja sai magi?

Hannu tasa ta karbi laidan dake hannunsa sai doya dake gefe ta d'auka ta fita waje, kara-karan dake bola shita ibo tazo ta hura wuta dashi, d'aura tukunya tayi ta zuba ruwa tasa magi da manjan ta rufe, fere doyan tayi shima ta zuba.

Bayan ta sauke girkin ta ibawa papa nasa itama ta saka nata sai kulenta dake gefe ta zuba masa nasa, zama tayi a wajen tanaci tana kallon jama'ar dake zuwa wucewa in sun ganta a zaune sai su koma, gabaki d'aya tausayin kanta da kanta take don Abincin ba dadine dashi ba, in kuma bataci ba waxai bata.

Papa na karyawa yasa kafarsa ya fita a gidan, d'aki ta koma ta kwanta tama rasa me zatayi haka ta wuni har dare a d'akin sai kusan 11 papa da yadawo a buge Yau koh Abincin bata samu ya sayo mata ba haka ta kwanta.

Washe gari Sunday da safe lipton ya sai musu da sugar suka sha shayi baki, Nnenna na sanyi da wani kod'aden siket iyya gwuwa da riga, sai sandal na makaranta dake kafarta don bata da Wani takalmi sai wannan, kanta babu hula sai tsifeffen gashinta dake kwance babu gyara, hannunta d'auke da bable.

Papa ma sanye yake da kodeden suit nasa na gwanjo da wata kifefeyar takalmi da hula a kansa, rufe gidan sukayi zasu churchi, da gudu kulenta yataho kusa da ita ya tsaya,da masifa papa yace.


Nifa na fara gajiya da wannan cat in naki ace tsawon shekara goma kina tare da Abu bai mutu ba, sanan har magana ya fara ji, I swear bazaki fita dashi ba.


tsungunawa tayi tana shafasa"kiki zamuje church ka xauna a gida saina dawo", aiko kamar maijin magana haka ya koma gefe ya tsaya yana kallonsu har suka wuce, a tare suke tafiya da yarsa duk inda ta wuce sai a ringa gudu wasu su shanja hanya.

Da suka isa church in ma kin bari pasto yayi Nnenna ta shiga, Papa ya buga ya buga Amma yace bazata shigo ba, karshe haka ta koma gefe da bable inta dake hannunta ta zauna, Amma duk da haka pasto nan yace sai dai ta koma bayan church ba gaba ba kartana kallon yaran mutane daga nesa.

Ba musu ta koma shan bayan church ta zauna a kan wani dutse tana kuka ta rasa me yasa mutane suka tsaneta ne wai haka?

Ba'a taso church ba sai 12:38 su kuma basu suka bar church in ba sai da jama'a suka watse duka wannan umurnin pasto ne.

Sai kusan 1 suka kama hanya har gida yauma bata samu na rana ba sai omo da papa yasai musu na 50 ya bata ta dawo tayi wankin a gida zai wuce , saida ya jaddada mata kar taje kogi wanki, amsa masa kawai tayi da "toh"ta karbi omo tace

Tana komawa gida wankin ta harhad'a gayyane guda tana tunanin ina omon hamsin zai isa Amma tuna a kogi zata wanke koh ba omo zata sa a ruwa ta cire, don basu da ruwa a gidan in kuma zatana ibowa a kogi harta cika jarakuna, Abin ya mata yawa gwara ta tafi da wankin kawai.

Tattara wankin tayi ta sabi kulenta tasaka sa cikin kayan wanki ta d'aura akan ta,kogi ta nufa kamar yanda tayi tsammani hakance watoh jama'a a tare a kogin kamar me,daga masu wanki masu kama kifi, gefe daban ta samu babu kowa sai yashi mai kyau da haske juye kayan tayi a gefe , tad'au boket ta ibo ruwa ta dawo ta zauna agun tana wanki ga kulenta a gefe yana zaune.

Sosai take wanke kayanta bata damu da marmatsawa da wasu masu dauraya sukayi daga gefenta ba, duk da suna da nisa da ita Amma haka suka kara marmatsawa sosai, tana cikin wanki kamar daga sama taga an tsaya a kanta.

Da mamaki ta d'ago tana kallon yaran, yan matane guda hudu, katti katti irin inyamurai manyan nan gasu bakake, gabanta ne ya fadi tunawa da yaran ba mutunci bane dasu gashi a kauyen su taji papa na cewa Yan zaman gindin dutsene sai sufi wata basu dawo kauye ba.

Kee kece mayyar da ake magana koh?

Shuru tayi bata basu Amsa ba sai raba ido take.

Haushi rashin Amsa wata taji a cikinsu, hannu kawai tasa ta kifar da ruwan omon Nnenna.

Da sauri Nnenna ta tsunguna tana tsine kayanta dake cikin ruwan omon kuma sun zubar a yashi, sai da suka bari ta tsine duka ta saka a boket, sai wata ta sabi boket in da gudu ta nufi kogi.

Da gudu Nnenna ma ta bita tana kuka tana bata hakuri don a cikin kayan harda school uniform nata, kuma shi kad'aine da ita tasan papa bazai taba sai mata wani ba gashi weac ma kasa biya mata yayi haka ta sake maimaita ss 3 don batason zaman gida kullum kewa na damunta shiyasa take zuwa makaranta, an koreta har an gaji an barta.

Kamata sauran yara ukun sukayi tana kuka tana rokon d'ayan akan ta dawo mata da kayanta Amma ina sai da ta juye su a ruwan kogi, tana juyewa suka saketa suna dariya haka jama'an dake kogin dadi sukeji ana wulakanta ta.

Da gudu tayi cikin kogin tana bin kayanta zata cire Amma ina ruwa kam sai tafiya yake da kayan ta, haka tanaji tana gani ruwa ya gudu da tufafinsu sai na papa data samo kala uku,Amma itakam na jikinta ne kawai ya rage mata.

Dawowa bakin kogin tayi tana kuka ga jikinta na tsintigon ruwa, boket nata biyu dake gefe ta d'auka zata tafi, da sauri suka fizge boket in,har suka jimata ciwo da karfen boket in a hannu,d'ayan ta had'ashi da dutse a take boket in ya fashe, cikin dariya tace bake mukaji anacewa mayya ba toh mu mun fiki Hassabibanci.

Kuka ta sake da karfi don ita a duniya babu abinda ke bata mata rai irin a kirata da mayya, abin na mata ciwo, hannu kawai tasa ta sabi kulenta, fizgo kulen wance ta zubar mata da kaya tayi ta wurwura kulen zata jefar a ruwa.

Da karfi Nnenna tayi tsalle ta taka kirjin yarinyar da kafarta, A take yarinyar tayi wani irin zubewa a kasa saida kasan wajen ya girgiza take ta sandare babu Alamun Rai a tatare da ita.........



✨Ruqeenjalal✨





πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ

Free page🀧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*


page 1⃣1⃣&1⃣2⃣
Sam yarinyar bata motse idanunta sun kakkafe a sana ga hancinta na xubar da jini, ihu jama'a suka kwala aka rufu akan yarinya.

Hankalin Nnenna a tashe Don yau tasan ta shiga uku, gashi papa ya hanata xuwa Amma taki ji wai ita tabi sauki, gashi taje tasa kanta a masifa, da sauri ta sabi kulenta da ya jefo a gefe, ganin hankalin mutane baya kanta yana kan yarinyar dake kwance.

Yasata banbarawa a guje jikinta sai rawa yake tunda take bata taba jawo rigima kiri kiri irin na yau ba, sai dai taga an mata Aiki Amma yau ta baiwa kanta mamaki mai girma.

da gudu ta baro kogi har ta shigo cikin kauye direct gidan su ta nufa tana xuwa ta bude kofa ta mayar ta rufe jikinta na rawa tayi cikin dakin aje kulentayi ta zauna dabas a kasa ga kayan jikinta a jike.

Kuka take sosai gabaki d'aya hankalinta a tashe yake ta rasa meke mata dadi yau dai tata ta kare ta shiga uku.



*****************
Lahab bashi ya farka ba sai kusan 11 na rana, mikewa yayi daga kwancen ya d'auko laptop na Rahab ya kunna data, har 12 yana dakin jin muryar su rahab a falo yasa kasa mikewa da sauri ya kashe system in ya mayar ya aje.

Fita yayi a d'akin ya wucesu a falo babba suna xaxxaune Ana hira, kitchen ya nufa yana bude kofar kitchen in sai kuma ya tsaya ganin gogoji mai aikin su tana duke Tana kuka.

Harya karaso cikin kitchen in bata ma san ya shigoba shima dukawa yayi a tiles in kamar yanda yaga tayi, ya dafata tare da kiran sunan ta"gogoji"?

Da sauri ta d'ago tana kallon lahab sai kuma da sauri ta kama goge hawayen ta da bakin dankwalin ta.

"Gogoji tun da safe nasan akwai abinda ke damunki, Amma haka kika boye mini dana tambaye ki kikace lafiya, ke ba'a mai aiki na d'auke ki ba kawai a gidan nan, a matsayin uwa nake kallonki tunda nayi wayo na bude ido na ganki a

Please Login or Register in order to submit comment