Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu zuwa aiki ma sun wuce aikinnsu Amma sauran yaran nagida tunda yanzun ana holiday ne, bayan dakunan gidan ya leka anan ya tarar da goggoji Zama yayi babu boye boye ya zayyana Mata abinda ya faru da Kuma Nnenna dake gidan ta tare da tabbatar Mata Batayi kisan Kai ba sanan Dan Allah duk abinda zaije ya dawo kada ta sanar da kowa Nnenna na gidan ta sanann tasa Mata ido,babu abinda lahabbl zai nema Wanda Bai sabawa shariya ba goggoji ta kasa Masa don ya taimake ta a rayuwa badon Shiba da d'anta kwalli daya faruq daya Zama tarihi.





da yamma saiga Adewale da Nabeel hankali tashe sukazo gidan su Lahab Nabeel zai tsinewa Nnenna yake Wai ashe makashiyace Mai fuska biyu shi wallahi tunda ya ganta shikenan yaji ya tsaneta Allah yasa a Kamata a ratayeta wani irin Abu Lahab yaji ya tsoki zuciyarsa hatta yawun bakinsa wani daci daci yake Masa wani Abu Mai kamasa gundura tsana yaji ya dirar Masa a makwashi na Nabeel,Amma baice kome ba Adewale ma kallon Nabeel kawai yake Saida ya Bari ya kammala zaginta tas kafun yace"haba Nabeel kana da tabbacin ita tayi kisan ne wai meyasa mutane suke hakane gashi duk gari ya gume ta kashe Dan marikinta ka sani Koh ba haka abin yake ba"hayayyako Masa Nabeel yayi yace cewa za'a Mata karyane in tasan tana da gaskiya meyasa ta gudu ana Neman ta, mikewa Lahab yayi ya nunawa Nabeel kofa hade da cewa"tashi ka fitar min a daki Nabeel"? Da mugun mamaki Nabeel ya mike tsaye yace"Ni kake kora Lahab"kofar lahab ya Kara nuna Masa a zafafe yace"tun Kan Raina ya baci Nabeel kabar dakin Nan"mikewa Nabeel yayi yace"insha Allah bazan Kara shigowa gidan bama bare dakin ka ya bude kofar ya fita"mikewa Adewale yayi ya matso kusa da Lahab tare dasa hannu ya dafa kafadar sa Yana bashi Baki akan ya kwantar da hankalin sa taima ma duk abinda ake fada akan ta karyane,shidai Lahab baice kome ba Harya Gama surutun sa yabar gidan.






Bayan kwana biyu Da yamma bayan Lahab yaje ball ya dawo kamar zaibi gidan goggoji yaga ya Nnenna ta kwana sai Kuma ya dawo gida yadau laptop nata,bayan yayi wanka yaje gidan goggoji ya duba Nnenna Kuma yaji dadin yanda yaje ya sameta tayi wanka harma ta sa Sabon Kaya daya baiwa goggoji kudi ta sai Mata,Amma dai tadan rame kad'an Zama yayi a kusa da ita tare dasa hannu ya taba wuyanta buge hannun tayi,shikam Dan murmushi yayi ya aje Mata laptop in a gefen ta Bata kallesa ba ta juya fuskar ta gefe daban irin tayi fushin Nan,sai da yayita faman lallama kafun ya samu ta hakura ta sauka daga fushin da take dashi na kwana biyar dabaizo ya dubata ba, faruq ne ya shigo gidan da Sauri ya karaso Kan taburman ya dau laptop in Yana jujjuyawa.




Washe garin ranan da yamma Lahab ne zaune a dakin sa Yana karanta littafin physics don yanzun da gaske ya dage Yana karatu, yaji an turo kofar dakin sa da Sauri da Sauri ya mike tsaye ganin uzaifa ya shiga hankali tashe Yana cewa Lahab ya fito ana Neman sa,shekeke lahab yayi yace "don ana nemana saika min irin wannan shiga daki cikin tashin hankali"Bai rufe Baki ba saiga Abbu ya shigo dakin da kansa hankali tashe yace"Wai Ina Lahab inne ka fito Mana fitowa lahab yayi da Sauri Abbu ya kamo hannun sa har babban falo,sake Baki Lahab yayi Yana bin wa'inda ke falon nasu sai Kuma idanun sa ya sauka akan Dan uwansa da ke tsakiyar wasu mutane guda uku cikin dumbin mamaki,yaji Abbu na cewa bakun ga dayan ba Y'an biyu ne,gaLahab in wannan dake wajen ku Rahab ne ince dai lafiya kuke neman sa,babu walwala a fuskar dayan ya kalli Lahab yace"Kaine Hassan Al'hassan dogo Mai naira?gyada Kai Lahab yayi sai Kuma wani daga cikin mutanen ya zaro ID card insa ya nuna tare da cewa"Ni sunan wisdom timoti jami'in sirri na farin Kaya zamu tafi da Lahab office in mu akwai tambayoyi da mukeso ya amsa mana"Lahab yaci niiii"? Yes ur under arrest................................................




Alhamdulilah Alhamdulilah Alhamdulilah

🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Book 2

Page 1
Innace muku hankalin Y'an gidan su Lahab ya tashi toh yafi gaban tashi yayi sosai suka shiga rudani duk yanda Abbu yaso su Masa bayani tun a cikin gidan sukace ah ah saidai yabisu office nasu aiko take ya shiga ya dau keyn mota Rahab da tunda yaji ance za'a tafi da dan uwansa yake ta faman rusa kuka yazo ya rungumi Lahab,amma babu Imani aka fincike sa tare da tasa Lahab a gaba suka bar falon ji kawai sukayi timmmmmmm Rahab ya sulale a wajen,hankali tashe Abbu ya d'aga waya ya Kira ya jafar ya samesa a office in jami'an ya barwa su Shareef Rahab shi Kuma yabi bayan jami'an.



Bayan isar su Abbu anan ne yaji dalilin Kama Lahab akan wata yarinya da tayi kisan Kai Kuma ana zargin dasa hannun Lahab,aiko Nan Abbu yace uban kuturu yayi kad'an bare na makaho kaninsa Koh kuda bazai iyya kashewa ba bare tai guda,Kuma babu abinda ya had'asa da wata Yar arna,magana ta Zama babba Mami da Rahab na gado don gabaki d'ayan su faduwa sukayi,lokacin da labari ya riske mubeena Aljanunta ne Suka tashi rike-rike sai ihu take daker aka samu aka daddan neta Suka kwanta,daga baya Kuma sai aka koma asibiti ganin ciwo ne ya nufeta lokaci d'aya,su Inna sunyi mamakin surutun da tayi lokacin da take cikin kukan iska akan a fito Mata da Lahab kaza-kaza tunanin da yazo ma Inna taima tausayin sane ya sata haka tunda case na kisan Kai ba Wasa bane.




Papa Kam sosai ya dawo gida Yana ta masifa akan baga abinda yake gujewa Ade ba akan yaran hausawan nan makiyansu ne Amma baya ganewa gashi yaro ya kashe Cristian duk yanda Adewale yaso Kare Lahab a wajen iyayen sa abun ya gagara don Yana tare papa zaiji an buga Masa baki,kowa yaji zancen Nan sai ya karyata duk da Lahab bayaji amma wallahi kowa ya shaida Lahab bazai kashe mutum ba Koh taimaka wa wata ta kashe mutum.




Duk yanda Yan Sanda sukayi da Lahab akan ya sanar dasu Inda Nnenna take amma ya murza idanun sa akan shi baisan Inda take ba,gashi an Hana taba lafiyar sa da karfin iko da kudi yayun sa Suka daukaka Kara za'ayi shariya akan kazafin da ake son d'aurawa kanin su,duk wani masoyin Lahab ya Shiga tashin hankali lokacin da zancen yaje kunnen Nnenna goggoji ne ta dawo tana sanar Mata hankalin ta tashe ta Soma kuka tare da mikewa tsaye tana cewa zata,tace musu babu ruwan Lahab basai an Shiga kotu ba,hankali tashe goggoji tace bazaiyu ta barta ta fita ba Lahab bazai yafe Mata ba ta fahimci Yana kaunar yarinyar sosai ita da faruq Suka yita nutsar da ita tare da Bata tabbacin insha Allah Lahab xai fito ai Yan uwansa nada kudi Kuma Godwin bazai iya winning akan suba in zancen kudine zuriyan su Lahab sun damasu sun shanye daker dai da sudin goshi Suka samu ta yarda zata zauna laptop nata ta dauko ta baiwa faruq ya sitting na kome a ciki ta Fara Hawa yanar gizo tana kallon abubuwan dake gudana a duniya da Al'amarin case nata kowa na fadin Albarka cin bakin sa.



Mami tafi kowa Shiga tashin hankali Allah sarki uwa gabaki d'aya ta rame ta fige duk da an sallamota amma bata Jin garau Kamar dai mubeena itama ta Dan warware ga Kuma bikin Ahmad da Ruky da ake a wannan satin duk abubuwan sun hadu sun Mata yawa,Lahab ya wahala zaman gidan yari Koh babu duka ba zagi azabane, ya Kara Baki ya rame sosai sai Ido da hanci da tsawo duk sun fito sosai amma saboda taurin rai Lahab yaki ya basu duk information da ya sani akan yarinyar.




Monday morning kotu ya cika makil da Jama'a Koh matsakan tsinke babu sosai sai dan surutai dake tashi kasa-kasa shigowan Alkali shiya nutsar da Al'umma kowa yayi shuru tare da mikewa Harya zauna kafun jama'ar Suma Suka zauna Yan uwan Godwin (Dad) dana mom sai Family Lahab Suna da yawa sai Yan jaridu da Kuma Yan kallo after few minutes lauya ne ya Mike ya gatabar da kansa na lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma sannan lauyan su mom shima ya mike ya gabatar da kansa tare da Neman izini ya matsa kusa da Lahab ya tsaya sannan ya kalle sa yace" Koh zaka iyya fadawa kotu cikekken sunan ka"?




d'ago jajjayen idanun sa yayi ya kalli lauyan yace"Sunana Hassan Al'hassan dogo Mai Naira"jinjina Kai lauyan yayi sannan ya Kara jefo Masa tambaya"Koh zaka sanar da kotu wace alakace tsakanin ka da Wance ake zargi da kisan Kai Nnenna obinna"?sunkuyar da Kai yayi sai Kuma yace"bamu da wata alaka ta jini friend nawa ce a makaranta"wani shegen murmushi lauyan yayi ya gyara rigansa kafun yace"kana nufin bakwa haduwa sai a makaranta sanann duba da a'ladunku na Arewa babu friendship tsakanin mace dana miji"mikewa lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma yayi Yana cewa"objection my lo... barrister Yana kokarin cusawa Wanda ake zargi magana a baki taya zaice a Arewa babu abota tsakanin namiji da mace"gyada Kai Alkali yayi yace wa lauyan a kiyaye,sannan yaci gaba dama Lahab tambayoyi Yana basa amsa har aka gangaro Kan na Randa abin ya faru"Koh Hassan zai iyya sanar da kotu a ranan 30/1/202.........meya fitar dashi da misalin karfe 20:20am daga gidan su, alhali Kuma dokan gidan su yara basa fita muddin 9 na dare ya gotta.?




Sosai zuciyar Lahab ta tsinke bama Kamar lokacin da ya dago ya kalli Mami da Abbu da Suka zuba Masa Ido Suna jiran amsar da zai bada,a hankali yace"da misalin karfe biyu na dare Nnenna ta kirani a waya.......................tsab ya Fadi abinda ya faru a ranan har hotel Inda Suka sauka a ciki amma bai sanar dasu yasan ana tuhumar Nnenna da kisan Kai ba haka zalika baice musu ya kaita gidan goggoji ba yadai ce sun bar hotel in ya bata kudin mota akan zata koma garin su"jijiga Kai lauyan yayi sannan ya nemi izinin zama ya koma ya zauna.



Koh lauyan dake Kare Wanda ake tuhuma Yana da tambaya Koh shaidan da zai nunawa kotu Hassan bashi da hannu a kisan Abraham?mikewa lauyan yayi ya sake rusunawa kafun ya dawo wurin Lahab ya Soma magana"a ranan da akayi kashe Abraham Wanda ake zargin Yar uwarsa Nnenna obinna ce ta kashe sa,abisa binciken likita sai da aka raunana gawar da duka akai kafun bayan Yan minutes aka daba Masa wuka daidai karfe 1:30 na dare Wanda anan Kuma Mai gadi ya tabbatar ma da kotu karfe 2:21am Lahab ya bar gidan su,kotu in tayi duba da wannan al'amari Lahab bayida hannu a kisan Abraham duba da cewa Saida aka kashe Abraham kafun ya bar gidan su.




Yana karasa maganar Alkali yace Yana da takardan hujjan likita amsawa yayi ya mika aka mikawa Alkali,sannan yaci gaba da bada gasheshen bayani akan babu abinda ke tsakanin Lahab da yarinyar sai abota Kamar yanda yace duba da cewa ajinsu daya a makaranta,haka zalika yarinyar da aka bibiye tushen taa korarta akayi a kauyen su saboda zargin maita da ake binta dashi,Kai a takaice dai an fafata shariya sosai kowa yanason yaga ya kada d'aya, Alkali ya d'aga shariyar sai Nan da sati shida sannan lauyan su mom ya tabbatar daya nemo hujoji masu karfi Wanda zai tabbatar wa da kotu Lahab nada hannu dumu-dumu Koh boye Nnenna,bayan kammala shariyar aka maida Lahab Inda aka d'auko sa don Abbu yayi yayi a sakosa su dawo gida Amma kotu Bata bada dama ba.


Bayan sati shida Zama na biyu,tsaye lauyan su Abraham yake a gefen Lahab daya gama kodewa ya Zama wani iri dashi ya jefo Masa tambaya"shin Koh zaka sanar damu dalilin da yasa kuka fasa kwana a hotel in alhalin Kuma kudin kwana ka biya tun farko"?gyara tsayuwar Lahab yayi yace"saboda a hotel in ba'a Kama wuni sai kwana sannan na jawota ne don na ajeta daidai safiya na maidata gidan su Don ni bansan cewa ba iyayenta take tare ba"



Kana nufin duk abotar ku da ita bata sanar dakai cewa ba iyayenta bane Mr Godwin da matarsa ba"?



"Kwarai Ni Bata sanar Dani ba"


Amma me tace maka bayan sanar dakai cewa ta bugawa Abraham lamp"?cemun tayi ya shigo dakin ta cikin dare Yana kokarin afka Mata shine garin Kare kanta ta buga Masa lamp"ok a lokacin kasan cewa ba yan uwa bane Koh Kuma tace maka menene a tsakanin su"a kufule Lahab yace nace maka bansan bada parents nata take tare ba Saida abin ya faru.


Murmushi barrister yayi sannan ya nemi izinin gabatar da shaid'an sa na biyu, peace ya Kira ta taso tazo ta tsaya gabaki d'aya idanunta a kumbura kallo daya zaka Mata kasan cewa wannan mutuwar ta shigeta ta Soma amsa tambayar da aka jefo Mata,shin akwai wani Abu na rashin fahimta Koh tsana Koh Kara tsakanin Abraham da Nnenna,girgiza Kai tayi sai Kuma hawaye ya cika Mata Ido tasa hannu ta share ta Soma magana a hankali"babu wani Abu a tsakanin su sai dai Kuma Nnenna batason shishige Mata da Abraham keyi Kamar ma ta tsane sa,sosai dai akayi ta fama da shariyar aka Kira mom Dad Jennifer Sarah sukazo sukayita bada shaidan gaskiya da karya akan Lahab bayan kammala nuna hujjojin barrister Solomon jefau ya koma ya zauna,mikewa lauyan Dad yayi ya matso kusa da lahab.



Hassan shin mutanen dake zaune da Nnenna sun taba kallonka Koh sanin wani alaka a tsakanin ku"amsa Lahab y basa"kwarai ma kuwa uncle Nata ya taba ganina a asibitin haka zalika cousin nata Jennifer mate namu ce don haka Ina da tabbacin sun sanni"gyada Kai Barrister yayi ya Kira peace tambayar da ya Fara jefo Mata shine menene alakarta da Abraham,dan rikicewa tayi cikin eii eiiina tace babu"dan murmushi barrister yayi yace a bincikin da kotu tayi tagano cewa akwai soyayya Mai zafi a tsakanin ki da mamacin kafun Nnenna ta dawo gidan da Zama,sai gabaki d'aya hankalinsa ya Soma komawa kanta,daga Nan ya shiga kyautata Mata ke Kuma tun daga lokacin kikaji kaf duniya babu Wanda Kika tsana Kamar ita"da Sauri tace Ah ah ni babu wata soyayya a tsakanin mu"karkiyi Wasa da kotu don Nan bamusan Wasa ba sannan ya Kara jefo Mata tambaya wata daya kafun mutuwar Abraham kunje hospital dashi saboda zazzabi da kike na shigan ciki,gane hakan yasa ya Miki dadin Baki akan zai kaiki a Baki magani daga Nan aka baki na zubar da ciki Wanda shi ya sani kece Baki sani ba Saida cikin ya zube,Kika koma kauyen ku jinya Saida Kika Kai wata Kika dawo"kukane ya kwacewa peace ta tsunguna tana kuka"amsa Zaki bawa kotu"kwarai haka akayi Kuma naji matukar zafin zuban cikin.




toh Zaki iya komawa ki zauna ganin irin kukan da take komawa tayi ta zauna sannan aka Nemo mom tambayar farko da aka jefo Mata shine waya Fara Jin kukan Abraham Kuma waya Fara Shiga dakin da Kuma waye karshen shiga a lokacin da abin ya faru peace na Ina dakuma dalilin da yasa Abraham Shiga dakin Nnenna cikin daren Allah,duk amsa daya ce peace ce tayi bayan shiga sannan itace farkon fitowa na jiyo kukan NASA haka zalika bata San abinda ya shigar dashi dakin Nnenna ba



Ina son wannan kotu Mai adalci data dubi hujojin da aka gabatar a gaban kotu in tayi duba da cewa Abraham ya shiga dakin Nnenna tsakar dare Kuma cikin maye Wanda bincike ya tabbatar Mana daga dakin peace ya fito don yabar hulansa da wayarsa a dakin peace tare da goran syrup daya Sha bugu da Kari peace bata shiga dakin ba sai bayan minti uku da mutuwar sa haka zalika Nnenna tayi kokarin Kare kanta na yunkurin raping nata da take kokarin Yi,mikewa Barrister Solomon yayi yace Barrister Yana yanke magana babu hujja,sosai akayita shariya daga karshe aka wanke Lahab daga zargin da ake Masa tare da Kama peace a matsayin Wanda ake tuhuma kuka peace ta fashe dashi tana rantse-rantse ba ita ta kashe Shiba,sannandasa Ido Mai tsanani wajen ganin hukuma ta shafko Nnenna obinna.




Wanka Lahab yayi yaci abinci kafun ya samu ya farfado gabaki d'aya zuriyan su ranan sun cika gidan ana ta maida zancen abinda ya faru wasu Nasiya suke Masa akan abinda ya faru ya Zama iznah a garesa Mami Kan cewa tayi duk Randa taji labarin an gansa da wata wallahi sai tayi mummunan Saba Masa zata basa mamaki,Abbu Kam security ya zuba a gidan sunfi goma ya Karo mototi haka zalika yanzun shiga gidan su Lahab baida sauki haka zalika fita ma banda Shareef babu Wanda ake Bari ya fita shi kadai sai da driver da security zakaje ka dawo malami aka dauko musu Yana karantar da yaran Arabic a gida gashi daman ana Holiday gabaki d'aya Lahab yaji Kamar zai mutu an kwace Masa waya an hanasa fita gwara kowa ma za'a barsa yadan fita shikam Koh kofar gida bai zuwa damuwa sosai yake ransa sai dai Yana d'anjin labarin Nnenna a wajen gogoji amma hakan bai wadace saba so yake ya ganta face to face Koh xai danji dadi gashi abokansa ma duka an hanasu shigowa gidan babu Mai shigowa sai family su Koh gogoji Mai aiki da sauran ma'aikatan sune keda daman shiga da fita ta sauki.





***********

Yau satin Lahab d'aya da dawowa ba laifi yadan murmure sai fama da jinya yake tunda ya dawo abinka da Wanda ya Saba da dadi yaje wahala,kwance yake akan katifar sa Addayiya na gefe a zaune,ruwa Dr yake daura Masa bayan ya gama ne ya fita a dakin Addayiya ma fita tayi Lahab dake kwance bude Ido yayi Jin an turo kofar Rahab ne ya shigo sanye da jampa sai qur'ani a hannun sa yanzun malamin ya sallame su,aje Qur'ani yayi akan sett ya matso bakin gadon da Lahab ke kwance,hannu yasa ya taba goshin Lahab, dan bude Idon da ya lumshe Lahab yayi ya kalli dan uwan nasa sai Kuma ya maida idanunsa ya rufe.




tagumi Rahab yayi yanda Lahab ya rame haka shima ya rame sabar damuwar da yagani a fuskar dan uwan nasa,kasa hakuri yayi yace"Lahab ya Kamata kayi hakuri akan abinda ya faru ka manta da kome ka dawo da fara'ar ka Mana dan uwana Koh nima Zan dawo yanda nake,Kama hannunsa lahab yayi a hankali ya Soma kokarin mikewa zaune tashi Rahab yayi ya taimaka Masa ya tashi xaune,a hankali yace"Rahab dan Allah ka taimaka mini"wani kallo Rahab ya Masa sannan yace"wani irin taimako Zan maka amma fa ka sani indai akan karya dokan da Abbu yasa a gidan Nan ne bazan taimake kaba"fuskar tausayi Lahab yayi yace"dan Allah Rahab ka taimaka min da waya zanyi Kira"da Sauri Rahab yace dan Allah rufemin baki akan me Zan baka waya kayi Kira wallahi badani ba shiyasa ma Abbu ya raba Mana daki yanzun kwana kawai yake kawoni Nan".




Hawaye ne ya cika idanun Lahab a hankali yace"shikenan Rahab tunda kowa zai nunamin fifiko a gidan Nan cikin Suma harda Kai bakome Randa na mutu ai kun huta"da Sauri Rahab ya mike tare da zaro wayarsa ya mikawa Lahab Jin Lahab ya ambace mutuwa cikin damuwa yace"gashi nan karba kayi Kiran dan Allah ka daina min Wasan mutuwa bana fatan ka mutu ka barni na daina ganin Mai irin fuskata a duniya"?karbar wayar kawai Lahab yayi a hankali ya mike tare da zare ruwan dake hannun sa,ya mike tsaye a daddafe ya bude toilet ya shiga tare da maida kofar ya rufe shidai Rahab Ido ne nasa yabisa dashi Harya rufe kofar.




d'an jingina yayi da tiles na toilet in ya loda number Adewale don shi Sam baida number goggoji a wayan sa Kira yayi Saida ya tsinke ya Kara Kira na biyu kafun Ade ya d'auka karawa yayi a kunnen sa yayi sallama amsa Masa Ade yayi daga Jin muryar tasa ya shaida shi da Sauri yace"Lahab nayi missing naka so much wallahi babu ranan da bana zuwa kofar gidan ku amma security sun hanani shiga duk na shiga damuwa wallahi gashi layinka bata shiga"a hankali Lahab yace"nida fita Kam bansan ranan Saba Abbu ya rantse bazan Kara fitaba sai lokacin weac Ina kammalawa results na fita yace bazan Kai sati a kasan Nan ba duk banjin dadin rayuwa ta wallahi"dan shuru Ade yayi Saida ya gama sauraron sa kafun yace"toh yanzun Lahab ya zakayi dolen ka kabi abinda yayan ka yake so,dan Allah karka sake shigar da kanka wani rigimar Kuma kayi hakuri saura wata nawane kwata-kwata muyi weac in, kaga in mukabar kasan Nan karyan dai ace za'a sa Mana Ido.



Ajiyar zuciya Lahab yayi sannan ya Kara kasa da murya yace"Ni duk ba wannan bane damuwa ta"da mamaki Ade yace toh menene damuwarka Banda Wanda kake ciki har akwai wani abin ne"eh akwai Ade so nake kaje gidan goggoji....Ade Bai bari ya karasa ba da Sauri ya sake jefo Masa tambaya wace goggoji Kuma"?a hankali Lahab yace Wacce ke Mana aiki har muka taba zuwa gidan ta muka duba yaonta"?da zullumin Ade yace"toh mezai Kaine gidanta Kuma"



Sauki ajiyar zuciya Lahab yayi yace"yau kwana biyu batazo aiki ba hankalina ya kasa kwanciya Ina ji a jikina akwai abinda ya same Nnenna duk da Addayiya tace min wai faruq ne ba lafiya kasan sickle cell ne"da mugun mamaki Ade yace"wace Nnenna Kuma"?a sanyaye yace Nnenna da aka ikirarin tayi kisan Kai"wani dogon salati Ade ya sake kamar wani musulmi ya Kara da cewa"kana nufin duk ukubar da ka shigan Nan yarinyar nan tana wajen goggoji toh wallahi babu ruwana bazaka sani a matsala ba in gaya maka babbu Inda zani Yana karasa maganar ya yanke call in......................................




🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



Cike da damuwa ya Kara Kiran Adewale amma sai ya danna Masa user busy,baiyi zuciya ba ya tura Masa message dan Allah ya d'auki wayar sa daker dai ya samu Adewale ya dau wayar sannan ya amince zaije ya dubo Nnenna amma daga wannan kada ya sake sakasa a shirgen Nnenna babu ruwan sa,katse wayar Lahab yayi Yana hamdala sannan ya koma cikin dakin har lokacin Rahab na zaune yana jiran sa,yana fitowa ya Mika Masa hannu wayan nasa ya basa sannan ya maida ruwan jikin sa ya kwanta.



da daddare Koh abinci Lahab ya kasa ci sai tsumayen Kiran Adewale yake amma shuru sai kusan 8 na dare Adewale ya Kira Rahab Rahab ya kawo Masa wayar amsa yayi da Sauri ya tashi Kamar d'azun ya shiga ban dakin Kara wayar yayi a kunne ya Soma mita sai yanzun Adewale zai kirasa tun d'azun Yana zaune Yana tsumayen Kiran nasa amma shuru"?yanzun zaka tsaya na fada maka abinda na ganone Koh zaka tsaya min mita na kashe wayata"?da Sauri Lahab yace toh kayi hakuri fadamin inji meya faru"?




Ajiyar zuciya Ade yayi yace ka duba WhatsApp na tura maka hoton ta kaga halinda naje na sameta a ciki zuciyar Lahab Saida ta buga cikin tsoro yace meya sametan,baidai basa amsa ba kawai ya katse wayar,jikinsa har rawa yake ya bude data ya shiga WhatsApp zubewa yayi a kasa ya zauna tabas saban shock Nnenna ya gani kwance Kamar gawa Ido a rufe jikinta gabaki d'aya ya sauya daga fari zuwa yellow sosai ga bakinta yayi jajer dashi rabin fuskarta har wajen wuyanta jijjiyoyine bakekkerin Suka fito rudu-rude jikinsa ne ya cigaba da rawa ya fita da Sauri wayar Ade ya Kira Yana d'auka ya Soma Masa magana"Adewale mutuwa tayi ne meya sameta"kaga Lahab karka sa kanka a matsala nidai goggoji tacemin yau kwana biyu kenan da Fara ciwon Nan nata sun tsorata ainun don numfashin tane kawai zai tabbatar maka tana da rai"innalilahi wa'inna'ilahu raji'un kawai Lahab yace ya katse wayar da gudu ya fito daga ban dakin wardrobe ya bude ya fito da kayansa sakawa yayi ya zaro takalmi zai sa yaga Rahab ya shigo da mamaki yace"Lahab sai Ina zaka a haka Kuma"?




"da Sauri Lahab yace fita zanyi"fita fa kace wani irin fita kake nufi

Please Login or Register in order to submit comment