Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba Suna tafiya Suna Hira kallon ta yayi yace"shikenan yanzun bazamuna haduba sai an dawo hutu"?tana Wasa da yatsan hannunta tace"eh man Inba haka ba toh a Ina Zan ganka"toh waike Baki zuwa Koh inane"ah ah bana zuwa daga gida sai makaranta Kuma kaga yanzun babu zancen makaranta Kuma sai zaman gida.



Gyada Kai yayi yace"Aiko gyara Miki ma da Baki yawon,bare yanzun kin samu laptop saikiyita using na abinki"gaskiya ne"shurune ya ratsa sakanin su ganin shurun yayi yawa Lahab yace"bayan weac namu wani school kike da burin shiga"?dan shuru tayi Kamar Mai nazari sai Kuma ta juya ta kallesa ta sake kauda fuska sannan tace"Ina son na karancin medicine sannan na Zama soja"waro Ido Lahab yayi sai Kuma ya Soma dariya har Yana dafe cikinsa




Kallon sa tayi ta had'a fuska tace"toh dariyan Kuma na menene kake min"dole na Miki dariya hajiya ke kince Zaki Zama Dr sannan soja a hakan"ya nunata a gatsine nifa tambayar ki nayi wani makaranta kikeson shiga after graduate kiwani cemin soja da Dr"ganin yanda ta had'a fuska bata basa amsa ba yasasa dan tsakaita dariyan yace"toh Yi hakuri yanzun dai fadamin menene dalilin ki nason Zama soja dama-dama Dr Zaki taimake Mata"?


"Zan Zama soja ne saboda Ina da sha'awar Zama security yanda zanna hukunci a dokance"harara ya Mata mata Ya tamke fuska yace"toh ke Kika Zama soja wazai aure ki a hakan"nima ai bance Ina son aure ba,a takaice ma Ni bazanyi aure bama"shuru yayi baice kome ba Amma fuskar nan babu fara'ar d'azun a hakan suka ringa tafiya harsaida sukazo daidai kwanar layin su Nnenna kafun ya tsaya saboda rokonsa da tayitayi akan ya koma Kar Yan gidan su su ganta da ita kwalin laptop nata ya Mika Mata daman Yana hannun sa kin amsa tayi tace"ka rikemin a gunka Inna tashi Zan karba"akan me Zan rike Miki Kuma Baki da hannune Koh Kuma gidanku babu wajen ajiya"?






Bata basa amsa ba ta cigaba da tafiyanta Bata saurare abinda yake cewa ba Wai zai bar Mata kwalin a wajen shima yayi tafiyarsa, baibar wajen ba Saida ya leka yaga ta shiga gida kafun yadau laptop in yayi gidan su dashi,daga isan sa gida yaga yanda Addayiya keta washe baki tana nan da nan da shi sai a lokacin ya tuna ashe fa yazo na daya yau babu kamarsa duk tarihin karatunsa report card nasa Bata da kyaun gani saboda rashin maida hankali ga karatu dakin zaman rubuta jarabawa, amma yau ya baiwa kowa mamaki,sai wani huhura hanci yake a dole yau babu kamarsa.




Abbu daya dawo yaji labarin abinda ya faru Nan Dadi ya kashesa tare dama su Lahab da Rahab Alkawarin muddin sukayi weac da neco nasu yayi kyau yamusu Alkawarin zai Basu damar zabar duk kasar da sukeso suje suyi karatu Nan Dadi ya Kama Rahab sabanin Lahab da jikinsa yayi sanyi yasan tabbas baida buri da ya wuce yaga Yana buga ball a kasar waje Amma bazaiso ace ya tafi karatu yabar abokin Saba yasan Adewale zasu iyya tafiya tare tunda iyayen sa nada kudi Nabeel da Nnenna sune yake jimamin rabuwa dasu a karon farko an kasafa Masa abinda bazai iya biya wa Nabeel ba don makarantan da suke ciki shida Ade suke had'a kudin hannun su su biya Masa school fees batare da Yan gidan su sun sani ba sai nasu nabeel kawai,daman ba zuwa makarantan suke ba tunda Suka biya Masa su kum ma daga gida ake biya musu ana asara basa zaman aji.



ganin yanda Abbu yaga rashin murna a fuskar lahab Kamar yanda yayi tsammani,hakan yasasa kasa hakuri Saida ya tambaya"Lahab Koh baka murna ne Koh akwai Inda kake son karatun ne"da Sauri Rahab yace"Abbu ya wuce akan ball ne kafa San shi inso samune yafison ya Kare a bautawa kwallo"mikewa tsaye Lahab yayi yacewa Abbu"insha Allah zanyi karatu Kuma Zan dage sosai ganin na cinye jarabawan"Yana karasa maganar ya bar wajen da Ido Suka bisa Suna mamakin Koh meke damun sa oho.





**********************
Nnenna na Shiga gida ta samu Jennifer zaune dasu mom tunda ta shigo zaginta suke batabi ta kansu ba daki ta shiga ta aje jakanta tare da d'aukar kiki dake tsakar dakin ganinta yasasa,rugawa yazo yahau jikinta ita Kuma ta daukesa ta rike a hannu,sai Kuma ta saukesa ta shiga bandaki,Jennifer ce ta shigo dakin don laptop da aka baiwa Nnenna a makaranta ya saya Mata a wuya shigowa dakin tayi ganin ba kowa ya sata sa hannu ta bude jakan Nnenna ta juye kayan jakan akan gado Allah yasa Nnenna bata ajiye wayarta a cikin takandu Yana aljuhun jakan shiya Hana Jennifer gani ball tayi da kiki ganin bataga laptop in ba don tayi niyar d'auke sa.




Fitowa Nnenna tayi sai Kuma ta tsaya tana kallon Jennifer da mamaki tace"mekike nema da Zaki shiga daki kina wargaza min Kaya"mtwsss Naga dai gida da dakin duk na ubana ne Ina da ikon shiga duk Inda nakeso"amsar da ta baiwa Nnenna kenan hakan yasa ta kin kula Jennifer tazo ta bude wardrobe nata tana maida kayan da Jennifer ta wurwurgar a kasa"keee Ina laptop in kin Isa ubana ya saki a makaranta Kuma ki samu kyauta kiri ke,ke kin Isa ki rike laptop ban rikeba?




Kala Nnenna Bata ce Mata ba ta gama tsayuwar ta ta bar dakin,har dare Nnenna na daki a kwance bayan ta kammala duk abubuwan da ya zame Mata jiki,wayar ta ne yayi Kara d'auka tayi ganin lahab ne tayi pick up ta Kara a kunnen ta sallama ya Mata ita Kuma tace Hello, murmushi kawai yayi yace"Wai harkin Fara bacci ne"?ah ah ban kwanta ba"ok ki hau online"toh tace tana katse wayar WhatsApp ta hau ya tutturo Mata hoton su na yau Suna ta Hira sai kusan 12 ya Mata sallama shima badon ya gaji ba sai don bacci datace Masa tana ji Yana yanke wayar ta gyara kwanciyarta sai bacci.




Kiki dake kwance mikewa yayi ya koma bakikkirin ga idon sa ya Kara zarowa sunyi jajer dasu,tafiya ya koma da kafa biyu na baya ya tashi Yana tafiya da kafarsa yana Isa kusa da window ya Manne da jikin glass na window take ya bace batt,misalin karfe 1 na dare aka bude kofar Nnenna a hankali shigowa akayi cikin tsanda aka nufi Kan gadon nata,hannu Wanda ya shigon yasa zai tabata cikin duhun dakin,da Sauri tayi wani irin zabura ta farka daga baccin da take tare da matsawa gefe hannun nasa ya sauka akan gadon.............................................





🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀



*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*

Page 100

Kafa tasa ta hankade sa tare da mikewa da Sauri ta kunna wutan dakin ga mugun mamakin ta ba kowa bane illah Abraham cikin maye yasha ya bugu,faduwa yayi sai Kuma ya mike cikin maganan Yan iska yake cewa tazo kusa dashi ya take gudun sa sonta fa yake Yana Kara matsowa kusa da ita Yana layi sosai.


Nnenna sosai taji tsoro don tunda ta kamasa da peace shikenan taji Koh magana batason Yana hadasu,ganin yanda ya maso kusa da ita yasa tayi Baya da Sauri,hannu yasa ya fizgota da karfi ya maka akan gado tare da fadowa a kanta,wani irin juyi tayi ta wantsalar dashi a gefe ta tashi tsaye jikinta ne ya Soma bari bana Wasa ba karkar Kar haka Naman jikinta yake Bari hannu ta d'aga tana nuna sa dashi hankali tashe take cewa"Abraham fitamin a daki ka fita tun kafun na illataka"rigan jikinsa ya Kwabe ya Soma kokarin cire wando da mugun gudu ta nufi kofar amma kafun ta kiftashi yasa hannu yaja vest in jikinta da nufin jawota baya rigan ya barke take kirjinta rabi ya fito subhanallah aiko take hankalin Abraham ya Soma tashi itakam hannu tasa ta tare kirjin nata cikin wani irin Hali na bakin ciki.



da gudu ta nufi kofar Amma kafun ta Isa tuni ya Sha gabanta tare dasa hannu ya damke damtse hannunta Yana kokarin janta sai layi yake lokacin da ya d'aura hannun sa a jikinta a lokacin idanunta ya rufe tama manta waye a gaban ta bed lamp ta d'auka ta kwada Masa a Kai take kannan ya fashe tare da lamp in duka jinine ya fantsama Wanda tashin hankali yasa Abraham fasa wani irin giggitancen ihu Mai amsa amo duk Wanda yaji ihun Abraham a lokacin yasan Yana cikin wani irin zafi na radade faduwa yayi akasa ya Kama Kan yana shure-shure.


Su mom dake sama da gudu suka sauko Jin muryan gudan jinisu Yana ihu bilhakki da gaskiya sai Kuma ya soma gurnani Basu tashi ganin tashin hankali ba Saida suka jiyo sa a dakin Nnenna Kama kofar sukayi zasu bude amma kofar taki buduwa,ashe lokacin da ya shiga dakin ya maida kofar ya rufene ta ciki.



Cikin tashin hankali Nnenna ta sabe wayarta da boron makarantan ta Koh riga Bata tsaya ta d'auka ba don tashin hankalin da take ciki bana Wasa bane, window dakin ta ta waje shita bude,tana bude glasses in ta hau ta dirko ta waje tana dudduba kiki don Bata gansa a dakin ba,take karnukan Suka hafto Jin motse da gudu tabar gidan Suna binta Wanda kukan karnukan shiya jawo hankalin su mom dake falon kasa Suna tsattsaye a kofar dakin Suna bugawa tare da kwalama Abraham Kira, Suka hankalta da kukan karnuka a waje.



da gudu Nnenna tabar layin karnukan basu bar binta ba har Saida ta Shari kwanar barin layin kafun suka koma baya Bata damu da dare bane gudu kawai take tana sa hannu tana Kare kirjinta don gudun da take kirjin zafi yake Mata,layin su Lahab ta Shiga duk da Bata San gidan su ba amma haka kawai jikinta ya Bata Nan ne layin nasu tunda yace mata unguwan su daya,amma Bata canki gida ba a kofar wani gida ta tsaya Inda babu wuta don sauran gidajen kofar gidan solar ne aka kafa haske Kamar Rana ita Kuma a yanda take Bata bukatar tsayuwa a haske Koh dankwali babu daga ita sai wandon bacci da yageggen vest,rasa Ina zata tayi babu Wanda ya Fado Mata a Rai sai Lahab.



So take ta kirasa amma Kuma inta kirasa tace Masa meye?a daren nan,wayarta ta d'auka ta danna Masa Kira Harya Fara ringing da Sauri Kuma ta kashe, mannuwa tayi da ginin tana tunanin in wani Abu ya samu Abraham Ina zata Shiga in Dad ya koreta daman ya Mata kashedi tun farko zuwan ta Amma bazata iyya zuba Ido ya keta Mata mutunci ba..



Lahab dake zaune akan sallaha idar da sallansa kenan don yau mummunan mafarki yayi shiya farkar dashi daga bacci,yayi Alwala yazo yayi sallah raka'a shida,Kamar ance ya d'aga kansa kawai yaga wayarsa dake gefen katifar sa tana wuta don wayar na silent ne, da mamaki ya mike toh wazai kirasa war haka agogon dakin ya haske karfe 2:20 ne na dare mikewa yayi ya dau wayar,ganin Nnenna ne yasa sa bin Kiran.



da Sauri ta dau wayar ganin kirann sa kafawa tayi a kunnen ta"Nnenna"ya Kira sunan ta fashewa tayi da kuka a hankali tace"na'am Lahab"meya faru Kika kirani yanzun lafiya Kam"shuru ta Masa tana nazarin ta fada Masa gaskiya ne Koh ah ah"Jin shuru batace kome ba yasa sa duba wayar ganin tana Kan layi ya sake tambayar ta"lafiya Nnenna"kasa basa amsa tayi saboda gaskiya yau taji tsoro fiye da lokacin da yan fashe Suka taresu yayin shigowar ta gombe,hankalin sa ya tashi wanda ya Sasa mikewa tsaye"lafiya Nnenna kina inane"a hankali tace Ina layinku.



Waro Ido yayi yace"layin mu fa kikace are u out of ur sense kinsan karfe nawa yanzun"?kikace kina layin mu?eh Ina Nan Lahab ka taimake Ni kaf duniya banda Wanda zai taimakamin sai Kai"?ai baisake cewa kome ba ya bude kofar su a hankali cikin tsanda ya fita a dakin tafiya yake a hankali a hankali,Harya iso kofar falon nasu budewa yayi ya fita da Sauri ya karaso bakin kofar gate nasu gate in a rufe yake kirim,hannu yasa yana kokarin bude sakatan gate in irin Mai karfin Nan ne in ka taba sakatansu zasu tona maka asiri.



Maigadi dake bacci da Sauri ya zabura tare da lalubar toshinsa Mai hasken gaske ya fito a dakin nasa Yana cewa wayene daidai lokacin Lahab ya bude kofar ya fita Aiko da gudu Mai gadi ya biyosa a baya tsayawa Lahab yayi ya jirasa Harya karaso kusa dashi Yana tambayar sa Inda zashi"kaga rufe gate Nan Ina zuwa Zan dawo yanzun yanzun Kuma bance ka fadawa kowa ba kanajina Koh baba"amma in............baibari ya karasa maganar ba ya d'aga Masa hannu yace "don Allah kaje nace Koh"ba yanda maigadi ya iya haka ya koma cikin gidan ya rufe gate yayi zamansa bai koma bacci ba Yana tsammanin dawowar Lahab da Kuma Inda zashi.





Lahab na fita ya kunna wayarsa kiranta yayi tana Masa kwatance Harya karaso Inda take kallon ta yayi sau d'aya Bai Kara marmarin kallon taba sai korin shaid'an yake a zuciyarsa jallabiyar jikinsa ya zare ya Mika Mata,karba tayi ta saka,"meya fitar dake a daren nan Kuma a haka babu suturan kirki"?hawaye ta share ta sanar dashi duk abinda ya faru da mamaki yake tambayarta daman Abraham ba yayanta bane Dad ma ba babanta bane,gyada Masa Kai tayi,tunani ya shiga yasan Koh hauka yake bazai dau Nnenna yakai gidan su ba Kuma tace Masa daga Enugu tazo.




A wajen Suka nemi dutse suka zauna sai misalin karfe uku na asuba Lahab ya mike tare da cewa ta jirasa Yana zuwa,gida ya koma lokacin da ya shigo har lokacin idon Mai gadi biyu da Sauri ya shiga dakin nasu har lokacin Rahab na bacci wandon baccin jikinsa ya cire yasa wani wando da riga ATM card NASA ya d'auka,ya bar gidan shidai maigadi sai Ido babu halin tambaya gashi yace Masa Koh Abbu zai nemesa yace Masa ya fita sallan asuba da wuri,da kafa Lahab Suka ringa takawa da Nnenna har wani karamin hotel dake gaban unguwan su kad'an, kama musu Roomi and falo yayi na kwana daya lokacin da suka shiga dakin ce Mata yayi taje ta kwanta a bedroom tunda jiya Bata samu bacci ba shima kwanciya yayi a falo.



Kasa bacci Nnenna tayi har 8 na safe idanunta biyu,Lahab dake bacci Jin Karan knocking in door ya farkar dashi mikewa yayi ya Isa bakin kofan, room service ce ta kawo musu breakfast amsa kawai yayi ya maida kofar ya rufe har ya koma zai kwanta sai Kuma ya mike ya nufi bedroom in,da mamaki yake kallon ta ganin ta a zaune ta zuba tagumi kallo daya zaka Mata kasan tana cikin damuwa.



Xama yayi a kusa da Ida tare dasa hannu a hankali ya Kama nata yace"Labiba ki kwantar da hankalin ki kinji insha Allah Zaki koma gidan ku"?gyada Masa Kai tayi tace"daker ne wallahi mom ta barni na Kara xama tare dasu kaga yanda kansa ya fashe kuwa"?mikewa yayi tsaye yasa hannu ya mikar da ita bandaki ya shigar da ita ya ajeta a toilet sit ruwa ya Iba ya wanke fuskar ta sosai yajawo towel ya goge Mata tare da cewa"tunta bazakiyi bacci ba ai shikenan sai kizo kici karyawa ga yanda idanunki Suka kukkumbura fa"?



Banajin yunwa,da Sauri yace ai Baki isaba wallahi shige muje da karfin dole ya fito da ita falo har lokacin jallabiyar sane a jikinta abincin ya bude Mata shinkafane da doya,tura Mata yayi a gaba hannu tasa badon taso ba ta Soma Sakura tanaci shikam komawa yayi zai kwanta sai Kuma yaji wayansa na ringing daukar wayar yayi ya Kara a kunne amma baice kome ba sai Kuma yace"ah ah Ade ban hau online ba meya faru"?ok ok kawai yace ya katse wayar tare da mikewa yadau remote ya kunna TV.





Kara Nnenna dake zaune ta sake da karfi tana ihu jikinta na rawa shi Karan kanshi Lahab yasha jinin jikinsa bana Wasa ba gawan Abraham ne kwance cikin jini kansa a faffashe ga shatin wuka da aka daba Masa a ciki,tare da Karin bayani akan an kashe matashi Mai Suna Abraham Godwin a cikin gidan su sai Kuma aka nuna mom tana kuka tana cewa Nnenna ta kashe Mata d'a sannan ta gudu a cikin daren ba'a San Inda take ba sai Kuma aka Nuno hoton Nnenna boro boro a screen in TV, innalilahi wa'inna'ilahu raji'un shine abinda ya Fara fita a bakin Lahab ya mike tsaye tare da nuna Nnenna da yatsa Yana cewa"keee Daman kisan Kai kikayi kikeson ki sani a matsala"wani irin kuka tafashi dashi tana kafa gwuwowinta a kasa tana cewa"bani na kasheshi ba Ni ban kashe Shiba buga Masa lamp nayi aka Amma wallahi ban soka Masa wuka ba,tana kukan jikinta na rawa tana cewa"shikenan nikam rayuwata ta lalace,gwara ma kawai na mutu na huta da ganin wannan bakin cikin.





tana karasa maganar ta Mike da gudu ta zaro wukar dake Kan center table akan plate na fruit da aka had'a musu dashi zata cakawa kanta da mugun gudu Lahab yayi kanta hannun yasa ya Kwabe wukar da karfin gaske ya murza hannun nata tare da had'ata da bango ya bita ya danne da jikinsa har Suna Jin numfashinal juna da Sauri Sauri kuka Nnenna ta Soma tanayi tana ihu akan ya Barta ta kashe kanta shi Kuma Lahab tashin hankalin sa d'aya shine Halin da ta fada ga Kuma kuka da take Masa gudun kada wasu suji a shigo dakin,wani ihu ta sake tana cewa ya saketa saita kashe kanta turasa tayi yayi baya Kamar xai Fadi da gudu ta nufi wajen wukar dake kasa tana dukawa ta dau wukan.





ta baya ya rungumeta da karfi jikinsa na rawa yasa hannu zai fizge wukar suka Soma kokowa sosai suke ta dambe a kasa cikin tashin hankali ya fizgota ya maka a bango daga zaune da suke,tana bude Baki ya danna lips NASA acikin nata,take jijiyoyin jikinsa Suka mimmmike Naman jikin na wani irin rawa,a zabure ya damke lips nata na kasa ya Soma tsotso da zafi zafi Yana maida numfashin dake kokarin barin jikinsa gabaki d'aya.





Hannunta dake damke da wukar batasan ya akai ta sake wukan da kanta ba hankali tashe ta Soma sauke kanta kasa har lokacin bakinsa na cikin nata Yana aikin tsotsar tausashen lips nata dukar da kanta take a hankali shi Kuma Yana Kara tallafo Kan sama da hannun sa,a hankali ya zame bakin sa daga Kan lips nata a hankali Yana tsude damshin yawonsa dake manne a lips Natan,a sanyaye ya zamo Kansa daidai kirjinta ya kwantar tare da Kai hannunsa ta bayanta ya mannata sosai a jikinsa Yana Jin yanda kirjinta ke mugun bugawa ya Soma magana cikin mutuwar jiki"Labiba duk abinda ya samu vawa jarabawace daga ubangiji meyasa bazakiyi hakuri da jarabawar ki ba,nasan ke ba musulma bace Amma babu addinin duniya daya hallata kisan Kai don an Shiga kuncin rayuwa na yarda dake na amince bazaki iya kashe kowa ba,Koda duk duniya zasu gujeki Ni Zan kasance a gefenki na Baki kariya.


Kwantar da kanta tayi a bango ta rumtsa idanunta da karfi,Sun Dan Jima a haka kafun ya zare jikinsa a nata,ba tare da ta kallesa ba ta Mike tsaye sai Kuma da Sauri ta dafe bango Jin jiri nason ibanta,ta nufi kofar da Sauri yasha gabanta tare da Kare kofar da jikinsa,ba tare da ta Bari sun had'a Ido ba tace"ka ban hanya na wuce"Ina zakije"?shima ya tambaye ta.




"Zanje na gayama su mom bani na kashesa sa"cikin damuwa Lahab yace"tun farko kin Bata kome da ace lokacin da abin ya farune Kika tsaya Baki gudu ba duk abinda zai samesa kina da bakin kare kanki,amma yanzun kin taka sahun barawo ne kina zuwa saidai a yanke Miki hukuncin kisa"ban damu ba don rayuwa ta daman Bata da wani amfani"da Sauri ya rungumeta sosai ya manna bayansa da jikin kofar tana jikinsa dan dagata yayi a hankali Bai damu da fizge-fizge da take ba,har Saida ya dangana ta da bedroom turata yayi da Sauri ya dawo da kofar ya rufe ta Baya sannan ya fita a falon.




Fita yayi a dakin ya tsaya a bakin dakin dake kallon nasu in Bai manta ba jiya kusan tare Suka Kama dakin da couple in Suka shiga dakin su Kuma suka shigo Nan, knocking yayi Saida ya Jima kafun aka bude dakin mutumin ya tsaya Yana tambayar sa lafiya,dan kaikaya keyansa Lahab yayi a hankali yace"Dan Allah madam ta taimaka min da veil daya Dan Allah,kallon sa sosai mutumin yayi sai Kuma ya girgiza kansa Yana mamakin abinda ya had'a yaro da Bai wuce 18 years ba da mace a Hotel Amma baice kome ba ya koma dakin Yana kitsema iskancin yaran yanzun daga xaran balaga yazo musu dai macece a ransu.




hijab in ya kawo Masa babba har kasa sosai Lahab yayita godiya da Sauri ya shiga dakin bude kofar dakin yayi ya Shiga zaune ya saketa sai kuka take,jakanta dake yashe ya d'auka ya dau wayar ta ya maka da bango don yasan daker ne in ba'a bi diddigin layi ba shiyasa ya cire sim in ya karya yadau hijab in ya zura Mata akan jallabiyar dake jikinta irin hijaban Nan ne da akece musu Mai Corona ya rufe Mata Rabin fuska hannunta ya Kama ya goyi jakan nata a bayansa Wanda babu kome a ciki sai tarkacen takardunta fita sukayi a hotel in da Sauri ya tare musu Keke Suka shiga Yana tunanin Ina zai kaita to yasan dai yanzun fita a gari bazaiyu ba,kallonta yayi a cikin keken yace"akwai Wanda Kika sani anan ne"?girgiza Masa Kai tayi"Mika Mata wayan sa yayi yace kisa number parents naki muyi magana dasu don ya Kamata Susan abinda ke faruwa.





Kuka ta Soma a hankali Wanda yasa Mai Keke Dan juyawa ya kalleta,da Sauri Lahab yace"kimin shuru karki taramin jama'a"shurun tayi tana shesheka,"tsaya anan"Lahab yacema Mai keken ganin yanda yake juyowa Yana kallon Nnenna Bini-Bini duk da ba Dole bane mutum ya ganeta ba,sauka sukayi ya basa kudin sa wani keken ya tare ya fada Masa Inda zai kaisu,Suna Isa bakin layin Bai yarda ya shiga da Mai keken ba ya zare kudin sa ya basa hannu yasa ya kamo na Nnenna Suka Soma tafiya har Suka iso kofar wani gida Mai Jan tabo sosai irin gidan Nan na talakawa tsayawa yayi a bakin kofar gidan Yana sallama.




Amsawa akayi daga ciki babu Jimawa saiga yaro saurayin a kalla zaikai 25 ya fito sai Kuma ya waro Ido yace Rahab sannu da zuwa,shafa kansa Lahab yayi yace"Lahab ne"Aiko da Sauri yaron yace masa su shigo ciki Bismillah ba musu Lahab ya kama Nnenna Suka shiga ciki shimfida musu taburma yayi Suka zauna bin gidan Lahab yayi da Ido sai Kuma ya kalli yaron yace"goggoji ta tafi aiki ne"da Sauri saurayin daya mike ya ibo musu ruwa a kofi ya aje Yana amsa Masa da eh Lahab Bai barota a gida ba"?share tambayar Lahab yayi sannan ya nuna Nnenna yace"Dan Allah faruq in babu damuwa Ina son ta zauna anan zanje gida nayi magana da goggoji don Allah Kar a barta ta fita sannan ta zauna a daki banason mutane Suna shigowa Suna kallonta ga wannan ya Mika Masa 5k ka sama Mata abinda zataci pls,da Sauri faruq yace haba Lahab abinda zataci sai ka bani kudin karfa ka manta daga gidan ku goggoji ke zuwa da abinci haba haba wallahi bazan karba ba,duk yanda Lahab yaso faruq ya karbi kudin ki yayi,mikewa yayi zai tafi da Sauri Nnenna ta Mike hade da tsayawa a gefensa zaro Ido yayi yace"ya haka"?wani kallo take Masa duk da bataji abinda sukace ba don bajin hausa take ba Amma ta fahimci a gidan yake nufin zata zauna Taya zata zauna gida daya da faruq ba Mata a gidan.




da turanci take fada Masa bazata zauna gida babu mace ba,anan Lahab ke ce Mata ai matar gidan na tafiya aikine shima faruq Yana zuwa shago don haka ita kadai zatana wuni kin yarda Nnenna tayi da zaman sai da Lahab yayita Mata masifa kafun ta amince a idanunsa faruq ya bude Mata kofar dakin goggoji ta shiga shi Kuma yabi Lahab a baya ya rufe gidan ta baya kamar yanda Lahab yace Masa.





Lahab na Isa gida ya tarar da har Yan gidan sun karya

Please Login or Register in order to submit comment