Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu lesson, tama d'ayar Assigment nata sai kusan 9 suka kwanta.

Washe gari da asuba shayibu yazo ya buga musu kofa yaran sukayi Alwala sukayi sallah Nnenna wanke-wanke ta had'a shayibu yasai musu omo da yawa yaran sukayi shara shi kuma ya musu karyawan taliya dafa duka da manja.

Suna karyawa yasa yaran a gaba zai kaisu makaranta, daga nan zai wuce GRA neman gidan Coulis Appa, Suna barin gidan Ma'u ta ibo kayanta masu datti dana yaranta tazo ta jugawa Nnenna a gaba hade da bata boket ta jido ruwa ta wanke musu kaya.

Haka koh akayi Nnenna tayi jidon ruwa tun daga rijiyan unguwan har ta cicika randa kafun tazo ta dukufa akan daurayan harda na shayibu ma'u ta had'a saban mugunta, Nnenna ba ita ta gama Aikin ba sai kusan 5:30 lokacin ta gama wankin jikinta duk yayi tsami gashi ma'u bata bata na rana ba tanaji tana gani ta gama dafawa ta zubama yaranta da suka dawo makaranta Amma ita kaman ajalinta, ga gajiyan d'auraya.

Shayibu na dawowa ya tawo mata da kyakyawar Albishir yau wuni yayi yana binciken gidan Coulis kuma ya samu a kasan GRA yake har kofar gidan yaje sai gobe in Allah ya kaimu zai kaita da safe.

Nnenna murna sosai tayi ba kad'an ba har Allah Allah take gari ya waye tabar gidan nan, da dare ma Albarkacin shayibu ta samu dan tuwo ta saka a bakinta.

***************
Lahab da jama'an gidan sune zaune a babban falon gidan kowa na sha'anin gaban sa, Lahab ne zaune yanacin Ferfesun kifi da tuwon gurka(akoro),a kwano d'aya shida Addayiya suke zaune a tsakar falo suna ci suna fad'a, wai Addayiya na shan miya Ah ah tana cin kifi da yawa.

Sai fad'a suke yayinda abbu ke zaune a kujera yana karanta jarida sauran matan hira suke yayinda Su Anwar ke zaune da laptop a hannu munira kam Assigment nasu suke, Umaimah ne ta kalli Abbu sai kuma ta marairaice murya, Abbu Na ayya nace ba?

Zare glass in idanunsa Abbu yayi yana kallon umaimah toh mamata menene fadi ina jinki?

Yauwa Abbu daman Ina son a bani kudi ne xanyi abu?

Wani kudi zai baki yar batalon uba, uwarki bazata baki kudin da zaki yiwa saurayin ki cefene ba sai ubanki ya baki tsabar makon uwarki, Addayiya tace cikin masifa.

Hade fuska umaimah tayi, toh Addayiya ina ruwanki nasa bakin ki a ciki ne?

Kul mamana banason haka yaushe kika fara zama mara kunya mamar tawa kike fadawa haka?

Shuru tai sai kuma ta mike cikin fusata tayi hanyar falon su.

Zo nan mamata?Abbu yace

Dawowa tayi ta tsaya a gefe, ki shiga falona akan center table akwai ATM nawa ki d'auka in Allah ya kaimu gobe lafiya sai driver yaje miki kasuwan don banason yawo.

Cikin murna tace thank you Abbu na.

Shima dariya kawai yayi, yana kallon Rahab dake ta fama da haddansa na Alkur'ani a gefe koh shiga sabgar su baiyi hankalin sa naga abinda yake.

Tsaki Addayiya tayi cikin fad'a fad'a tace kaidai ka jiyo umar da sakarwa y'ay'an ka kudi sakaka har Atn(ATM) kake basu su cire abinda sukaso batare da ka ka'ide musu ba.

Kiyi hakuri Addayiya Ummu tace yayinda Mamu ta hade fuska sosai jin yanda Addayiya keta zazzaga masifa, don an baiwa Umaimah card.

Kallon Lahab Addayiya tayi d'an kusan wa ka tashi ka karo mana miyan, duk kazo ka kanainaye mini abinci gashi duk ka cinye mini kifi kabar kayuka d'an kwad'ayi kawai.

"Wallahi bazan karo ba wani irin na cinye kifi?Ai naga dai Abincin gidan mune kene ma zan ma gori miji ya mutu anki a koma inda aka fitoh"

Nashiga uku nida gidan d'ana dan uwarka ina zanje kaida uwarka ta kasa zama daku tayi auren ta abinta, ta watsar daku badon niba ai da yanzun kun watse.

"Wallahi badai mu watse ba sai dai ki watse"

Ungo naka Lahab wallahi zanji maka tashi ka karo mata miyar, bana son shirme Abbu yace yana ma Lahab gargadi da yatsa, ba musu lahab ya mike da kwanon miya a hannu yana zuwa kitchen ya aje kwanon abinsa ya wuce sashen su bai karo miyar ba.

Daki ya wuce abinsa yayi wanka ya chanja kaya, ya kwanta wayan sa ya d'auka ya kunna data ya shiga groups nasu na whatsApp suna hira da Abokan sa, har kusan10:00 sai da Rahab ya shigo d'akin kafun ya kashe wayar suka kwanta tare kamar kullum.

Washe gari da safe yaran gidan gabaki d'ayan su sun tafi aiki wasu kuma sun tafi Office in aka cire Anwar da baiya zuwa saboda ciwon sa, Lahab ma tun safe daya karya ya fita bai dawo ba.

**************
Ta bangaren Nnenna ma da safe bayan ta gama aikace aikacen gidan tayi wanka tama yaran ma'u, suka tafi makaranta tana karyawa ta cicibi kulenta ita da shayibu suka fita a gidan.

Bakin titi suka nufa Nnenna na rike da laidan kayan ta, da Shayibu yasai mata jiya, Tare musu keke napep yayi suka shiga.

Kwatance yama mai keken har unguwan GRA daidai kofar wani gida mai kyau sosai, amma irin gidan nan na Christian ne ba'a kewaye flat in ba gashi gidane mai kyau gidan sama da kasa gashi yasha glass na Ameniun sai shuke-shuken flowers sai karafuna da aka kewaye gidan dashi, karnuka ne manya manya kwakwance a tsakar gidan wasu na shawage.

Nufo get in karfen dake rufe sukayi suna taba get in karnukan suka mike da gudu suka nufosu cikin haushi........

**************

Umaimah da kanta taje kasuwa tare da driver tayi sayayya sosai, saboda saurayin ta da zaizo yau tare da iyayen sa, za'azo tambayan Auren ta, amma sai gobe iyayen zasu shigo gidan don har bauchi suke kuma in suka iso a yau zasu sauka a hotel su huta sai gobe zasu shigo, Amma Angon yace mata zaizo wajen ta da yamma.

Sayayyya tayi sosai harda wanda gobe za'a dafa musu, ba ita ta dawo ba sai 11 tana, ta tsunduma akan girkin da kanta ba ita ta kammala ba sai la'asar, wanka tayi shafshaf ta zauna ta fara tsantsara kwalliya.

Lahab da suka fitoh yawo tun safe ga yunwa gidan su Adewale suka fara biyawa Amma basu shiga ciki ba gudun masifa don iyayen sa sun tsane su, gani suke duk taurin kan Adewale su lahab ke koya masa, Abinci ade yaje ibo musu Amma momin sa ta koro sa akan bazata basu ba har dashi ma baxaici ba.

gidan Inna suka biya Amma basu samu ba, karshe dai gidan su lahab suka nufo don lahab baida koh sisi a hannunsa bai fita da kudi ba bare su sai abinci, suma basu da koh sisi a hannu a waje suka tsaya shi kuma ya shige cikin gidan, yana shigowa direct kitchen ya nufa.

Kuloli ya gani a jere sai kamshi ke tashi bubude kulolin yayi Abinci ne mai kyau da kayatarwa a ciki, da sauri ya sabi babban kulan mai d'auke da Rice sai d'ayan kulan dake dauke da Soyayyen kaxa da miya.

D'aukar guda biyu yayi da sauri ya fita a kitchen in, nufar falo yayi zai fita sukayi kicibis da zulai, da sauri ta tsaya tana kallonsa sai kuma tace uncle kulanda ka d'aukan nan fa abincin Aunty umaimah ne tama Yaya sadeeq yau xaizo.

Hararan ta yayi cikin masifa yace "wallahi ki ban waje na wuce kona bangajeki yar banza mai gulman tsiya, a gidan uban wa sadeeq in ya zama yayan ki kalen dangi koh"ya karasa maganar da tureta sai da ta fadi akan 2 sita.

Ihu ta sake tana kwalama umaimah kira, wayyo Aunty ga uncle lahab ya d'aukar miki kulan Abincin yaya Sadeeq, mamu kuzo kuzo zai gudu.

Ai jin haka yasa umaimah rugowa a guje daman yanzun take kokarin fitowa ta tarbo sadeeq dake compound, ai da gudu ta kwala kara ta bude kofar da sauri, tana kiran mamu.

Jin muryar umaimah yasa Lahab rugawa a guje da kuloli a hannunsa yayi kofar gida yayinda Sadeeq ke jingine a jikin motar sa, da sauri ya tashi tsaye daga jinginar da yayi ganin mutum ya banbaro a guje yayi kofar get, sai kuma ya juya da sauri jin muryar wance ta bisan tana had'asa da Allah ya da...............

✨Ruqeenjalal✨





πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ

Free page🀧

*EXQUISITE WRITER'S FARUM*


page1⃣9⃣&2⃣0⃣
Akan dan Allah ya dawo, Amma ina Lahab koh juyawa baiyi ba harya fita a get, yayinda Umaimah ke tsaye a bakin baranda kamar ta hadiye zuciya ta mutu,haka ta ringaji bare ma sai yanzun da taga sadeeq gabaki d'aya ta manta yana compound ta biyo lahab.

Murmushin dole ta kirkiro hade da karasa wa kusa dashi, tana tsunkuyar da kai suka gaisa irin na masoya tambayar ta yake mai ya had'ata da Rahab yau koh tsayawa baiyi sun gaisaba.

Cikin yake take ce masa su shiga ciki pls,bata basa amsa ba, ba musu yabi ta a baya hanyar da suka saba zama, watoh garden xama sukayi da sauri ta turawa Rahab dake cikin gida sako akan Lahab ya d'aukar mata abincin bako ya taimaka ya fita ya sayo mata shinkafa da miya da kaza a restaurant.

Yana dawowa aka juye a wani kulan, mai aiki takai musu garden, Amma cika kam Mamu da umaimah sun shaka, jira kawai yau mamu take Abbu ya dawo ayita ta kare ta gaji da hakuri da Halin Lahab.


Lahab yanda ya fitoh a guje haka su nabeel suka rufa masa baya don sun sam tabbas akwai abinda ya b'aro kenan shiyasa ba tambaya, gudu yake da kuloli suma suna binsa a baya har suka shari kwana, kafun Lahab ya tsaya aje kwanukan yayi yana maida numfashi.

Kai menene haka duk kabi ka d'aga mana hankali ka sakamu gudu kaman barayi?

kallon sa Lahab yayi sai kuma ya kyalkyale da dariya"aiko wallahi barayin ne don sato mana abincin umaimah nayi saurayin ta zaizo ta masa delicious"


Habba Lahab meyasa zaka d'aukar mata?kai shikenan kullum gidan ku ana case naka.

Tsaki lahab yayi yana bude kulan shinkafan yace"don Allah rufe mini baki munafuki in zakaci kazo kaci banason munafurci"

Zama koh sukayi a wajen ruwan fanfo suka tara suka wanke hannunsu, had'a miyar yayi a shinkafan ga kaji suka soma ci hankali kwance.

Abinci sukaci dayake ba kad'an bane har suka rage ga kaji duka, Almajirai Lahab ya gani a bakin titi ya kirasu ya juye musu sauran Abincin.

Kulan ya sab'a su Adewale suka rakasa har get na gidan su ya kwalama mai gadi kira.

yana fitowa ya basa kulan ya shigar cikin gida shikam baici ta shiga gida yanzun ba.



*****************
Nnenna bata gudu ba tsayawa kawai tayi tana kallon karnukan dake tinkaro ta yayinda shayibu ya ruga a guje ya koma kwanar layin ya tsaya yana kwalawa Nnenna kira akan ta gudu.

Kin gudun tayi ta tsaya don ita ba tsoron kare take ba sam, abune da sun riga sun saba dasu duk da wa'innan mazajen karen, ta fahimci suna da fad'a da zafin nama.

Turus suka tsaya a gabanta suna maida numfashi yanda karnuka keyi ba tare da sun mata kome ba, juyawa tayi tana kallon shayibu sai kuma ta nuna masa da yatsa akan ya tawo su shiga, ba musu ganin babu abinda yan iskan karnukan suka mata, ya karaso wajen Yana mamakin yanda kule yaga kare Amma bai wani razana ba, suma karnukan badu nuna yunwar su ba.

Nnenna ne a gaba hannu tasa ta tura kofar karfen shayibu na binta a baya karnukan ma suka bisu, tsayawa Nnenna tayi a tsakar gidan tana bin koh ina da kallo wai wannan gidan ne zata xauna a ciki?koh a mafarki bata taba tsammani ba.

Kofar falon shayibu ya isa yayi knocking kusan sau uku kafun suka koma gefe suka tsaya, sai da aka jima kafun sukaji ana kokarin bude kofar, ana budewa dukansu suka dubi na bakin kofar mace ce Christian budurwa a kalla zata kusa 25 sanye da zani guntu sai t-shirt koh ba'a fad'aba daga mutum ya ganta yasan yar aiki ce.

Da sauri taja baya tana kallonsu suma da sauri suka gaidata, Amsawa tayi a yangace tare da tambayar su lafiya me suke bukata?

Kallonta shayibu yayi cikin turanci yake ce mata ta musu iso a wajen pastor Coulis Appa wajen sa sukazo, kamar bazata ba sai binsu take da kallo, kafun ta koma ciki sai da ta jima kafun ta dawo tace musu su shigo ciki.

Ba musu Nnenna tabiyo ta a baya shayibu na binsu har suka shigo falon, wow falone mai kyau d'auke da Jere na zamani kujeru da kayan Alatu daidai karfin masu gidan don baza'ace azabebben kyau ba, zama yar aikin tace suyi a falo ita kuma ta wuce kitchen.

Daga Nnenna har shayibu a kasa suka zauna watoh kasan tiles, basu hau kujera ba, sai kallon falon Nnenna keyi daga ka ganta kasan bakauyiya ce.

Sai da suka d'auki akalla 1 hour a zaune duk sun gaji kafun suka ji karan takalmin mutum a upstair's, Gabaki d'aya suka bi matakalar da kallo, wani mutumi ne baki d'an lukuti ga tumbi ke saukowa daga ka gansa kasan lallai irin pastotin nan ne rikako, kamar yanda suka zura masa ido shima haka ya zura musu ido yana kallonsu har ya gama saukowa musamman ma daya ga shayibu don dagani babu tambaya Annurin musulunci daban ne.

Kallon Nnenna yake ganinta babu d'an kwali ga wando a jikinta na gwanjo da t-shirt sai dai basu kamata ba, hakan ya tabbatar masa ba musulma bace kuma yayi matukar mamakin kamarta kyaun nata na taban ne koh nace na musamman.

Zama yayi akan kujera yayi bake-bake yana binsu da kallo da sauri shayibu ya sunkuyar da kai yana gaidashi, Amsawa yayi kamar bayaso, hade da tambayar su lafiya suke neman sa?

Gyara zama shayibu yayi ya koro masa bayanin haduwar sa da Nnenna tare da takardan da ta basa tana neman d'an uwan babanta daga Enugu, rike baki yayi yana kallon Nnenna sai kuma ya nunata da yatsa, kee kece yar Obinna taya kika zama Yar Obinna dubeki fa.

Kuka ne ya kwace wa Nnenna a tunanin ta koh in tazo zata samu tarba mai mutunci itama karshen wahakar ta kenan ta huta da wahalan rayuwa ashe ta gudu ne bata tsira ba.

Mika hannu yayi, ku bani takardan ai zan gane rubutun Obinna duk da shekaru da dama rabona dashi Bana tunanin zan manta?

Ba musu Shayibu ya zaro paper ya basa, ba musu ya karba yana bin rubutun da ido sai kuma ya d'aga kai yana kallon Nnenna, yaren Egbo ya fara mata don tabbatar wa kansa yar d'an uwan sane, tambayoyi yake mata tana basa Amsa harda tambayar ta mahaifiyar ta fa, tace masa bata san taba, amma bata sanar dashi ana mata kazafin maita ba, hade da mamakin halinsa na koh in kula da jin labarin mutuwar Obinna gashi dai ita tunda take bata taba ganinsa a kauyen suba, Amma ga kaman nin papa nan a fuskar sa.

Koh godiya baima shayibu ba na kula da Nnenna da yayi jiya sai ma kwalama mai aiki kira yayi, Akan tazo ta nunawa Nnenna d'akin baki dake kasan falon, yana maganar ya haura sama abinsa, da sauri ta fito hade dama Nnenna iso suje ta kaita dakin.

Mikewa shayibu yayi bayan fitan coulis hannu yasa a Aljuhu ya zaro kudin ya mikawa Nnenna girgiza kai tayi a hankali cikin dauriya tace,"Am sory sir da abinda Uncle nawa ya maka nasan bai kyauta ba, kudin nan kuma ka rike a hannunka kayi business dashi na baka rabi kudin nima ka juya mini nawa nima, wata rana in bukatar kudi ya kamani nasan gidan ka zanzo"

Kin karba yayi sai da tayi da gaske kafun ya karba yana mata godiya tare da mata Alkawarin zuwa ya dubata hade da mata nasiha akan hakuri da rayuwa aduk yanda yazo mata.

Rakasa tayi har kofar get in hannunta d'auke da kulenta ta dawo falon, kofar da taga mai aikin ta shiga tun d'azun gun ta nufa ta bude, dakine d'an madaidaici mai d'auke da gado daidai na mutum biyu, sai labulaye da aka zaga d'akin dashi, fita mai aikin tayi, da sauri Nnenna ta matsa jikin labulen ta kama ta yaye sai kuma ta rike baki ashe glass dake wajen nan cikinsa ne, dakin ta tan kallon unguwan baki d'aya daga dakin ta inta yaye labule, sosai taji dadin dakin koh banza zai rage mata kewa.

Turo kofar akayi da sauri ta juya tana kallon mai aikin hannunta d'auke da tiren abinci aje mata tayi akan tiles tare da nuna mata wardrop dake gefe akan tasa kayanta dake laida a ciki, tare da nuna mata bayan gida da yanda zatayi amfani da kayan ciki fuska ba walwala yar aikin ke mata magana, tana gamawa ta fita daman ita Nnenna koh fuska bata sakar mata ba daman ita ba ma'abociyar fara'a bace bare ta damu.

Aje kulen tayi akan gado da sauri ta bude abincin Arish ne da kwai sai bread da tie sosai taji dadi wallahi gyara zama tayi ta fara cin abincin ta har lumshe ido take don ba sabawa tayi da cin suba, daga ita har kulenta sukeci tare a kwano d'aya.

Tana gama ci toilet ta shiga tsintsiya ta d'auko tazo ta share dakin ga basket a ciki ta juye sharan, wanka tayi ta gyara gadon ta kwanta abinta tana maijin dadin sauyin rayuwa data samu da fatan kasancewa cikin kwanciyan Hankali.


Har dare tana d'akin bata tashi ba duk da taji tsayuwar mota a tsakar gidan don duk abinda ke faruwa a waje tana d'anji kad'an-kad'an saboda glass.

Yar aikin ne ta shigo tare da sanar da Nnenna tafito ana nemanta a falo, da sauri ta mike sanye take da dogon riga d'aya daga cikin wanda shayibu ya sai mata, kofa ta nufa zata fita ai da sauri kulenta dake kwance a gadon ya mike zai bita.

Da sauri ta nuna masa gadon cikin yare tace masa ya koma ya kwanta, ba musu kuma ya koma ya kwantan Abinsa kamar yanda tace, bin yar aikin tayi har falo, ji tayi zuciyar ta ya tsinke ganin mutanen dake falon, uncle Coulis ne zaune akan 3sita da wata tasha bleching ga attech akanta, sai wasu yara mata biyu dake zaune da kananun gajerun wanduna d'ayan zata kai shekara 23 sai karamar mai shekara 17, sai namijin dake zaune a 1sita daga ka gansa kaga dan iska bakin nan bakikirim irin na yan kwaya sai ido jajazur zai kai 30, daga ka gansu kaga irin shagwababun yaran nan babu kob'a, gashi tunda Nnenna ta fito yake binta da wani mayace cen kallo yana lasar baki.

Rakuba tayi a gefe cikin rawan jiki take gaida matar"good Evening ma"?

Amsa mata tayi hade da sanar da ita ba ma zatace ba mom yaranta ke kiranta, ta karasa maganar cikin yanga kai kawai Nnenna ta daga mata alamun taji gaida sauran yaran tayi harda uncle nata.

Kallon ta Dady yayi cikin yare ya nuna mata mom, ga wife ina sunan ta chidimma Doctor ce, sai wannan ya nuna na mijin sunan sa ibraham yana karatu a kasar waje Amma yanzun ya dawo hutu, my first born.

Nuna yaran matan yayi wannan sunan ta Sarah ta kusan kammala digree inta sai mai binta jennifer tana sss 3, ni kuma pastor ne, na fada miki ne don ki san mu da kyau, kuma zansa a je amin bincike a kauye kamar yanda Dr tace saboda na tabbatar dake din yar uwa tace, ganinki da nayi da muslim nan hankali na bai kwanta dake ba?

Gyada kai tayi hawaye na taruwa a idanunta tsoro take ji kar yaje yaji zancen mayyace ita shima ya korata a gidan nasa, bata dawo daga tunaninta ba mom ta kalleta cikin gatse tace ke tashi kije ki jera mana abinci a daining ba zaman banza zakiyi a gidan nan ba dole yanzun na sallame Lakwanti ke ki maye gurbinsa a ayyuka, keda peace kun isa tayi na kitchen kiyi na gida.


Gaskiya ne mom bazayu tana yar kauye muci mu kwanta ita ma haka ba, sarah tace tana yamutsa fuska cikin rigima, guy innan kam maida Nnenna yayi madubi sai kallonta yake yayin da jennifer taji wani irin tsanar Nnenna a ranta ganin yarinya yar kauye tazo ta fita kome da kome gata kyakkyawa, bare ma yanzun dataji dad na cewa bayan anyi bincike ya tabbtar yar obinna ce har makaranta zai saka ta.

Da murna Nnenna kece masa takardun ta na gidan su pls in za'aje garin nasu a d'auko mata.

Tsawa mom ta daka mata ke yar kauye dakata menaji kike cewa? ta tambaya tana nuna Nnenna, yaushe kika samu waje har zaki bada order shege ya.

Sosai Nnenna ta razana don itakam harga Allah batason tsawa, nuna mata kitchen mom tayi wuce kije ki taya Peace aiki, ba musu ta mike a hankali take tafiya Ibraham sai binta yake da ido kamar tsohon maye.

Tana shiga kitchen in ta tsaya tana kallon peace dake shirya Abinci a kuloli, tana gama zubawa ta bawa Nnenna umurni akan taje ta jera a daining don duk abinda ke wakana a falon tana ji, ba musu ta cicibe kulolin takai daining ta jerasu, tare da su plante suna gamawa kimtsawa, familin suka zo suka zazzauna akan daining, saving nasu peace take Amma Ibraham yace lallai sai dai Nnenna tazo ta zuba masa.

Ba musu Momy tace tazo ta zuba masa matsawa tayi fuska ba walwala sam, tazo ta d'auki plate kaman yanda taga peace tayi haka itama take, zuba masa tuwon tayi da miyar naman Alade, sai kauda fuska take saboda bata koh son ganin naman.


Shikam kafa yasa ta karkashin table in ya taba mata tsintsiyar kafa, sake plate in tayi jikinta na wani irin bari kamar mazari, da sauri ta juya ta dafa jikin bangon Area in kanta na wani irin sarawa kamar zai rabe biyu.

Da sauri suka mimmike suna tambayar ta menene..............







✨Ruqeenjalal✨





πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
πŸ€ΉπŸΏβ€β™‚οΈ *ALKAWARIN MASOYA* πŸ€ΉπŸ»β€β™€οΈ
~ Na ~

πŸƒ *Rukayya Ibrahim*πŸƒ

✨Tsokaci ALKAWARIN MASOYA na kudi ne gamai bukata naira 300 ne kacal ki tuntube ni ta layin nan whatsApp only 07044407979πŸ‘Œ

Free page🀧


*EXQUISITE WRITER'S FARUM*


page2⃣1⃣&2⃣2⃣
Kasa Amsa musu tayi saboda tsananin ciwo da kanta keyi ga wani irin fushi dake taso mata tana kokarin dannewa.

Tsawa mom ta daka mata,kee ba magana ake miki ba kin wa mutane banza?


Shuru kawai Nnenna tayi jin jirin ya lafa mata yasa ta nufi barin Area in cikin damuwa, sukam da ido suka bita suna mamakin halinta na ko in kula ga had'a fuska da mannin hauka.

Tura kofar d'akin ta tayi ta shiga da sauri ta zauna a bakin gado, ranta a jagule ta kwanta tare da lumshe idanunta, anya zaman nan zai mata dadi kuwa?wai itakam bazata samu farin ciki bane a rayuwar ta, shikenan bata da sukuni, wai menene a jikinta da yake rud'ar maza harsu kasa hakuri sai sun nuna maitar su a fili tayi tunanin koh in ta dawo Birni zata ga change ashe abun ba haka bane.


A haka tana kwance har bacci ya d'auke ta ba tare dataci na dare ba daga ita har abin kiwon nata.



********************
Lahab kam gantali suka tafi abinsu bashi ya dawo gida ba sai yamma kamar kullum yau ma xama yayi a masallaci, agun yayi Alwala ya shiga harsu Abbu ma suka shigo suka same sa daga yanayin kallon da abbu ya masa sai da yaji cikin sa yayi kuka.

Suna idar da sallah yabi bayan su har cikin gida tsaya yayi a falo yana bin falon da kallo, mamu ne zaune ita da umaimah inka gansu a lokacin kad'ai ya isa ya sanar da kai akwai matsala, tsawa abbu ya buga masa, Lahab nemi waje ka zauna.

Ba musu ya nemi gefen kujera ya zauna kamar na Allah ya hade kafa waje d'aya, zama Abbu yayi haka ma su Uxaifa, saiga Addayiya ta fitoh sanye da hijab, yauwa Umaru jarabebben ya samu isowa kenan, ai tunda naji muryarka nace d'an kusan wa ya dawo, ta

Please Login or Register in order to submit comment