Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bata masan wake kanta ba lokacin da yadau maganin zai Bata bayan kammala tofi da yayi a ciki,likitotin sukace afatau bazai Bata ba ai hanjinta a nade yake bazataci abincin yanzun ba haka zalika in yasan zai Bata traditional medicine meyasa bai mata a gida ba Suka kawo ta hospital, Lahab yabuga ya buga sunki daga karshe dai Saida ya musu hauka kafun Suka barsa maganin ya shafa Mata a Kai da fuska kana ya zuba Mata kad'an a Baki ta hadiya,da Sauri Kuma ya nufi dakin yaran balla roban zamzam yayi ya juye a kofi duk abinda yake innan jikinsa rawa yake karkar Kar don shi kadai aka bawa daman ganin su,zame oxygen in yayi ya bawa yaran ruwa da Sauri namijin ya Soma tsotsa Yana hadiye wa,kwantar dashi yayi yadau macen itama ya Bata baima mayar musu a oxygen in ba Yana dai rike dasu a hannunsa sai Addu'a yake shafa musu gabaki d'aya yau yaga abinda ake Kira tsinkewar Rai,a sannu sannu numfashin su ya Soma daidai ta sai Kuma ya sama sauka Normal,bacci ya daukesu kwantar dasu yayi Yana Mai Addu'an fatan gamawa da duniya ga malam,da Sauri ya nufi dakin Nnenna Alhamdulilah jini ya tsaya ya Soma zuba kad'an kad'an Wanda sosai abin ya baiwa likitoti mamaki Basu tsammaci hakan ba.





Alhamdulilah jikin Nnenna yayi sauki na ban mamaki har an chanja Mata daki an had'ata da yaranta waje daya lokacin da ta farka taga Lahab rungume da yaran ba kunya tace saiya aje mata yaranta Aiko Lahab bai biye mata ba tana ta masifa har Saida Dr yazo ya Mata allura don su sun dauko irin farkawar Nan ce da mutun yakeyi da shirme, Muhammad ya koma gida ya sanar da mama Aiko Nan ta musu girki Mai kyau da dare ta tattara kayanta a jaka ta biyo Muhammad hospital lokacin Nnenna Bata farka ba,anyi anyi ta koma gida tace ita Ina da Nnenna zata zauna kafun maman su Lahab tazo,anan Muhammad ke sanar da ita ma'aurata ne ba Yan uwa ba,aiko gyara Zama tayi tace babu Inda zata gashi asibitin basason mutum ya wuce daya Mai jinyar Mara lafiya dole Lahab badon yaso ba yabi su Ade suka koma gida.







Washe gari tunda ya idar da sallan asuba yayi wanka tare da ibawa Nnenna magangunan su,ya fita a gidan ya wuce mall zai sai Mata kayan shayi amma ya samu Basu bode ba babu yanda ya iya haka ya jirasu har kusan 6 kafun ya sassayi kayan karyawa duk da yasan da wuya taci wani Abu yau,da abinda zata bukata na yau da kullum ya jido musu,7:30 ya samesa a hospital in,lokacin da ya tura kofar ya shiga mama ce zaune da hijab da gani sallah ta idar bata tashi a Inda ta zauna ba,Kai dubansa yayi ga matar tasa bacci take,matsowa yayi kusa da gadon yaran hannu yasa a hankali zai dagasu sai Kuma ya tsaya Jin gyaran murya da mama ta Masa dan juyowa yayi suka gaisa kana tace"kaga bawan Allah karka dagasu don daren jiya bamuyi bacci ba sai koke koke suke,Kai Koh kunya bakaji Yan farine fa xaka dagasu a gabana"?





Koh sauraranta baiyi ba waishi da yaransa za'a ma iyayi xama yayi a bakin gadon ya dagosu duka ya rike sosai ya kurawa fuskokin yaran Ido yanajin kaunar su na kara nutso a ransa, Addu'a ya tofa musu a ruwa ya ibi maganin ya basu,kana ya musu huduba daidai lokacin akayi knocking na kofa Adewale ne da Muhammad Suka shigo sai jidda dake d'auke da kula,karasowa sukayi duka Suka zauna ana gaggaisawa Ade ya zaro wayansa ba tare da ya bari Lahab ya gane ba yayi musu hoto dukan su dashi da yaran harda Nnenna dake bacci,kana ya maida wayar sa Aljuhu"malam zaka bamu yaran mu rikene Koh yaya"?inji Ade ganin Lahab baida niyar Basu yaran.





Mikewa yayi yazo ya mikawa Muhammad daya ya baida jidda daya kana ya dau yarinyar Muhammad ya koma ya zauna,Kai Masha Allah yara Kam sak ubansu tabar kallah yara Kamar larabawa Allah ya rayasu ta farkin musulunci"jiki a sanyaye duka Yan dakin Suka amsa da ameen zuciyar Lahab Saida ya amsa sai yanzun yake tuna makomar yaransa shin ya zaikaya dasu yau Suka girma Suka tarar da uwarsu Bata sallah shin a matsayinsa na uba zai iya da tarbiyar su ta farkin islama shi kadai babu sa hannun uwa a ciki,tabbas ba auren ahlil kitab bane tarbiyar addinin ka shine babba tunda ita ke tare dasu kullum a matsayinta na uwa,Hira Yan dakin suke a hankali har Nnenna ta farka,Suka Mata ya jiki kana Ade da Muhammad Suka wuce makaranta ya rage sai jidda da mama sai Lahab.






****************
Kwanan Nnenna hudu aka sallamota zuwa gida saboda jikin nata yayi sauki Alhamdulilah abinka da tiyatan waje Koh na gida ma baya wuce haka a yanzun,mama gabaki dayanta ta tattaro ta dawo gidan Lahab tana kula da Nnenna sosai tayi musu goma Sha ita ke kula da yaran dan Saida Suka kwana uku kafun ruwan no-no yazo Lahab ya koma bangaren Ade Suna kwana tare Kuma har yau babu shiri a tsakanin su don tunda Nnenna ta haihu ta dau son duniya ta daurawa yaranta Kuma bai Isa ya taba yaran Nan ba sai sunyi rigima da ita Saidai ya aje Mata yara.





Bayan sallan isha'i da sallama Lahab ya shigo falon nasu,zaune Nnenna take akan pillow a kasa,tuwo takeci miyan ganda yaji pepper sosai sai jaririn dake kwance akan kujera idanunsa biyu amma ba kuka yake ba dan Sam yaran Basu da yawan kukan banza sai in dare yayi su Hana uwan su bacci,amsa Masa tayi ciki-ciki bata Koh daga Ido ta gansa ba takalmin sa ya cire ya aje laidan hannunsa ya zauna akan kujeran da babyn ke kwance tare dasa hannu zai daukesa da Sauri Nnenna ta daukesa Bata damu da hannunta akwai Miya ba,"ke Wai me kike nufi ne Ya ni da y'ay'ana ki hanani sakar Koh a garin gaba-gaba naji irin wannan"suwaye yaran naka"wani banzan kallo ya Mata kafun yace"au yaran ne Baki san nawa b"?






Nidai wa'innan nasan nice uwarsu amma bakaine ubansu ba"me kike nufi banine ubansu ba"kwarai ma kuwa koka manta ne"ai wallahi baki Isa ba? da Allah bani yarana"hannu yasa ya fizgo d'ansa da karfi tayi tagal tagal zata Fadi da Sauri ya tarota hade da saurin rungumarta ya had'a da babyn duka a kirjinsa,kokarin banbare jikinta take amma yaki Bata daman haka a hankali ta Soma zamewa shima ya bita Suka zauna akan kujeran tare da zare babyn ya daura Mata akan cinya Jin yaron ya Fara kuka,hannu yasa zai daga Mata riga da Sauri ta make Masa hannu,Aiko yasa hannun nasa duka ya Kama nata ta baya ya rike kana ya zame rigan tare da fitar da breast in ya baiwa yaron da Sauri ya amshi abinsa ya Kama Sha,sosai kirjinta Suka dad'a cika Suka kumbura dam dam,dan zamewa yayi ya kwantar da kansa akan kafadar ta.




"Labiba Labiba"bakin sa biyu Yana kiranta Bata amsa Masa ba illa tallafar d'anta da tayi da kyau tana feeding nasa,"duk fushin Nan na menene"?ya Kara tambayarta again Bata Masa magana ba"hhhhh shine da Kika ga Zaki mutu a dakin haihuwa kike ta cewa a kirani na yafe Miki"Nan ma shuru ta Masa Bata basa amsa ba,in akan abinda ya farune kiyi hak..............Bata Bari ya karasa ba tasa hannu ta rufe Masa Baki hawaye na cika Mata Ido ta Soma magana a hankali"baka cancanci ka bani hakuri ba,bakamin abinda zaka bani hakuri ba,Niya dace na baka hakuri Lahab"?da Sauri ya mike zaune yace"hakurin me Zaki bani alhali Kuma nine Banda gaskiya"?Mata a wajen mijinta kullum ita ke daukar hakuri ai bare nida ka zame mini kome Kaine kadai Wanda Zan daga hannu na nuna a matsayin nawa sai Kuma wannan kyauta Mai girma da tsada da ka bani"ta nuna yaran, bani na Miki kyauta ba Allah ne ya Baki Ni Kuma na Zama suka, Amma duk da haka Kuma shine kike fushi Dani"murmushi tayi tana kokarin sauka a Kan kujeran Zama tayi ta Soma cin abincin shima zaman yayi yasa hannu suka Soma ci kafun tace"duk abinda namaka nayi ne bawai Dan Ina Jin haushin kaba sai don kada ka sake zancen zubar da ciki"gaskiya da nayi nadama har karshen rayuwata da nayiwa kaina wauta wannan kyautar da Allah yamin nasa subi flushing ga zunubi"




"Yanzun kana sonsu kenan"?Nnenna ta tambaye sa"ke yanzun harsai na fada miki"nasani Koh ganin idon mutane kake nuna........................................Bata karasa ba saiga mama ta fito daga dakin nasu d'auke da yarinyar alamu wanka ta Mata sai cinyara kuka take"ah ah angon karni Kaine"eh mama mum wuni lafiya"?lafiya Alhamdulilah,ke ungo bata no-no tasha sai Kuma take"hannu Lahab yasa ya dau namijin dake Kan cinyar mama tasa Mata macen Aiko Nan na mijin ya sanya kuka da karfi da Sauri mama ta had'a Madara ta baiwa Lahab ya kafa Masa a Baki shuru kakeji yaran sun natsu.




Zama mama tayi tana kallon su sosai taji sun burgeta yaro karami da Mata da yara Kamar babba bayan Kuma koshi ba'a gama rainon sa ba"Wai d'an ball ya sunan yaran ne in ban mantaba yau kwanansu biyar a duniya Koh"?gyada Mata Kai yayi kana yace"eh nazeefi da nazeefa"ah ah tabar kallah ubangiji ya musu Albarka"Ameen mama ga wannan ya dauko laidan daya shigo dashi ya Mika Mata amsa tayi ta bude nama ne da yawa gasasu,Hira sosai suke sai kusan 11 na dare ya musu sallama ya wuce flat na Ade.




Ana gobe Suna kasa hakuri mama tayi ganin babu wani daga dangin Lahab Kona Nnenna da yazo yasa ta aje Nnenna ta Soma Mata tambaya"Wai Yar Nan in tambaye ki Mana"?Ina jinki mama Nnenna tace tana ninke kayan yara da mama ta wanke"kin daukeni a matsayin uwa Kamar yanda na daukeki"?barin abinda take tayi ta juyo tana kallon mama Jin tambayar da ta Mata alamu dai abinda zata fadamata Mai muhimmaci ne"sosai ma mama"shikenan tunda kin daukeni a matsayin uwa Ina so ki fadamin tsakanin ki da mahalicin ki?gyada Mata Kai Nnenna tayi"shin keda yaron Nan Anya aure kukayi kuwa"?




Waro Ido Nnenna tayi sai Kuma taji ranta ya baci wato ma kokonton zaman nasu ake kenan"mama wani irin magana ne haka"kiyi hakuri yata in maganar ta Miki zafi Naga tunda nake daku Banga wani naki ko nasa dayazo kasar nan da sunan zuwa duba yara ba haka zalika babu Wanda ya bugo waya a idanuna"kuka Nnenna ta Fara ahankali sai yanzun tunanin yazo Mata lallai Suna da Kura a gaban su shin Menene makomar yaranta,mama Kam shuru tayi Bata Kara magana ba har Nnenna tayi kukan ta ta gaji.





Washe gari Suna babu kowa a gidan sai Muhammad dasu Lahab da iyalinsu sune Suka hadu sukaci abinci tare da gifts da Suka baiwa yaran,bayani Suna Lahab ya cigaba da zuwa makaranta haka ma ball ga Mama na zaune Masa da matar sa tana baiwa yaran kulawa sosai da gyara Masa Mata kome ya daidai ta a tsakanin su sun koma Kamar da ana Raha Wasa da dariya yaransu na samun kulawa na ban mamaki,a sannu sannu kwana na tafiya har Nnenna ta kammala wankan jegon ta Lahab ya koma dakin matar sa yayin da mama ta koma kasar nageria da tsaraba Mai yawa da Lahab ya mata,badon ranta yaso ba sai don Kiran da tsohon mijinta ke Mata akan taje ta zauna a tsakiyar yara,yanzun rainon yara ya koma wajen Nnenna da jidda da Suka kasance makwanta kawaye Kuma masu zumunci sosai,don wani lokaci in Lahab yabar kasar sai jidda ta dawo gidan Nnenna su zauna suyi girki su wuni sai dare ta ibi abinci a kula ta wuce gidanta dashi.





Yaran Lahab sun girma sosai yara kubul kubul dasu Kamar yaran turawa ga haskensu sosai ya karu fuskar Nan Kamar na mahaifinsu, don yanzun har tafiya Suna Yi babu Inda bada gudu Lahab ya Zama cikekken mutun magidanci Dan shekara 20 a duniya da yara Yan shekara 1, Nnenna tayi kiba ta waye duk Wanda yasan ta a Nnenna obinna a kauyen su inya ganta yanzun ba lallai ya gane ta ba,su Lahab sun samu hutun karshen shekara yanzun haka sun kammala part 2 saura musu shekara daya su kammala digree nasu anyi hutu Adewale yayiwa Lahab zancen tafiya nageria Amma Lahab ya murza Ido yace sai ya kammala makaranta zai je nageria,babu irin yanda Ade baiyi dashi ba yace bazashi yabar matar sa da yaransa ba.




Yau Ade baije Koh Ina ba kwanton Lahab yake yabar gidan Amma Ina dayake yau baida Wasa Koh training Yana gida da iyalan sa don haka yake in baida abinyi baya fita in Kuma zai fita toh da family sa,Jin motse a compound yasa sa mikewa yazo bakin windown sa ya bude labulen,Lahab ne tsaye da Nnenna Suna sanye cikin kananan Kaya gabaki dayan su jeans ne da t-shirt sai yaran su dake sanye da Kaya irin daya Lahab na rike da daya Nnenna na rike da daya ya sanya facemask a fuskar sa don haka yake indai zai fita da family sa sai ya rufe fuska gudun kada a daukesu hoto a yada a duniya ya Shiga uku,tsaki Ade yayi ganin sun shiga motar sun bar gidan tsake labulen kawai Ade yayi Yana mamakin halin Lahab nason Kai ace mutun nason yayan sa da matar sa haka Amma bazaiyi tunanin ya tasa mahaifiyar take kewar sa ba a zatonsa in Lahab yaga yaransa zaiyi hankali ya Fara natsuwa Amma baiga alamu ba Sam.






Washe gari lahab ya fita training hakan yasa Ade nufar kofar lahab ring na door ya Danna kana ya tsaya Yana jira ta bude Saida ya Jima sosai Harya juya zai tafi sai Kuma ya tsaya Jin an bude kofar"ah ah Uncle in twins Kaine sannu da zuwa shigo Mana"tace tana matsa masa,shigowa yayi da fara'ar sa ya karaso falon Zama yayi da sauri nazeefe dake zaune a kasan phalorn Yana Wasa ya mike da gudu Wai zaizo wajen Ade sai Kuma ya Fadi take ya sanyara Kara da Sauri Ade ya mike ya dagasa yana rarrashen sa"ba rawan Kai ba haka yake a Rana saiya Fadi sau uku ma"dariya Ade yayi Jin abinda tace yace"kin manta jinin Lahab ne in baiyi ba sai Allah ya tambaye sa"had'a fuska Nnenna tayi tana tafiya kitchen tace"gaskiya Uncle bazamu shirya dakai ba husband nawa kake fadawa haka"?sai Kuma ta shiga kitchen abinci ta ibo Masa ta dawo falon aje Masa tayi da drink's,Jin nazeefa tana sanyara Kara a daki Daman bacci take yasa Nnenna mikewa ta shiga daki jawo abincin Ade yayi ya Soma ci Yana baiwa nazeefi dake ta sa hannu a plate in Wai zai Iba Daman gashi yayi hakori hudu.





Fitowa Nnenna tayi da ita ta zauna akan kujera tana Bata Madara a feeder,ture plate na gaban sa yayi ya kalleta"mun wuni lafiya maman twins"? lafiya klau"Masha Allah Daman akwai wata magana da nake son muyi dake ne in ban takuraki ba"babu kome Ina jinka Allah yasa lafiya"?




Gyara Zama yayi yace lafiya kalau kawai dai aKan mutumin ne nace bari nazo ta wajen ki Koh Allah zaisa kisa baki,wallahi Nnenna Lahab baida hankali tunda mukazo kasar Nan waya wannan in ba Yan nageria ne suka kirasa ba sai sa'i da lokaci yake Kiran su,wancan shekara akayi hutu yace bazai koma ba saboda cikin ki daya girma toh ga wannan shekara yace bazashi ba,abinda Ni nagani Kamar abinda yake Bai Dace ba ace shekara biyu baka koma gida ba bayan Kuma kana da dama,hakan zai jefawa family sa cikin tunanin Abu biyu"na farko ko don Lahab yayi kudi shiyasa yake kokarin zame kansa a cikin su Koh fifita aikin sa akan su hakan Kuma zai iya saka manyan yayunsa sa Ido akansa a cikin kasarnan tunda Suna kudi ba Basu dashi ba, Kinga za'a gane kome akanku,Abu na biyu Kuma mundin aka gano kina tare dashi ne za'a daurawa alhakin rikon nasa Akan ki,Kuma daker su barku tare tunda sunga yanda ya iya Zama dake ba tare da yayi tunanin gida ba Wanda ada ba haka yake ba,don haka nazo na Baki shawara ki sa Baki Koh Allah zaisa yaji naki tunda yanzun kun riga kun Zama daya"?



Ajiyar zuciya Nnenna tayi ita kanta tana tsoron randa asirinta zai tonu"yanzun Ade kana ga duk Randa family sa suka San da auren mu zasu barmu tare kuwa wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba"?uhmmm kedai kiyi Addu'a kawai shine abinda yace Yana mikewa da nazeefi a hannun sa,Aiko da Sauri nazeefa tasa kuka ganin zasu bar falon Wai itama a dagata"dawowa yayi ya ciccibeta da boron madaran su harda feeder da flasks a ciki na ruwan dumi karami ya bar falon dasu duka.





Goshin mangariba Lahab ya Isa gida tura kofar falon yayi ya shiga da sallama falon tsabtsab sai kanshi dake tashi Nnenna ce ta fito kitchen hannunta d'auke da kuloli tana jerawa a dinning,sanye take da guntun siket da riga karami kannan nata yasha gyara sosai wallahi mutun ya ganta zai zaci Koh Bata had'a jini da kasar bakaken fata ba,saukowar tayi Akan steps biyu dake wajen dinning in,ta karaso kusa da mijinta dake zaune akan kujeran falo tsungunawa tayi tana warware Masa igiyoyin dake makale a takalmin ball dake kafar sa ta zare dogon socks in,kana ta Mike ta sabe jakan sport nashi ba tare da tace Masa kome ba ta haura upstairs,binta yayi da Ido harta Haura saman Ya shafa kansa yana mamakin wannan cicin maganin da take innan fa yasan dai lafiya suka rabu, gashi yaga yau sama ta haura alhalin Kuma tunda yaransa Suka Soma tafiya yace Mata bayason amfani da upstairs gudun kada yaransa suce zasu hau Koh a hau dasu suce zasu sauka suje su illata a banza a wofi.






Mikewa kawai yayi ya bita saman dakinsa na saman ya bude ya shiga a gyara yake Kamar Yana kwana a ciki alhalin Kuma sai yafi wata bai hau sama ba,Jin motsinta a bandakin yasa sa tura kofar ya shiga,wanka ya fito daure da towel kana daya na hannunsa yana goge ruwan dake kansa,mikewa tayi tazo ta karbi na hannun nasa shi Kuma ya zauna ta Soma goge masa,kafun ya tashi ta Mika Masa zallabiya da wando Yasa ta shimfida Masa sallaya ganin lokacin sallan mangariba ya kusa calbin sa ta sauka ta dauko a dakin kasa ta kawo Masa lokacin Harya Fara sallah ta aje Masa a gefe,ta koma ta zauna akan kujera ta jawo wayar sa tana dannawa.





Yana idar da sallan Addu'a yayi kana ya d'aga Ido ya kalleta sai Kuma yace"Wai Ina yaran Nan ne tunda na dawo Banga su ba Koh bacci suke kuma kinsa nace Miki banason kina barin yaran Nan Suna baccin yamma bashi da amfani kwata kwata Kuma baida kyau"bafa bacci suke ba Kuma tunda kace bakason Suna baccin yamma nadaina barin su Suna bacci Koh sunyi ta dasu nake"gyada Kai yayi"in kawo maka abincin Nan ne"?no Zan sauka naci a dinning Amma Baki bani amsa taba Ina suke kinsan banson yaran Nan kina kaisu gidan Muhammad da sunan barma jidda raino fa"?





Mtwsss ikon Allah waika ka fini son yaran Nan ne Inka tashi sai kayita min fada Kamar nika Haifa Basu ba,kafasan Ni na girmeka baikamata kana min magana haka ba"wani zabura Lahab yayi ya tsaya Yana Mata wani kallo kana yace"keee niii Kika girma inji wani makaryacin..............................











*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 08084453785 tare da shaidan biyan ki*




dariya Nnenna ta sake da karfi ganin yanda Lahab ya had'a gabas da yamma don shi a duniya Kam ya tsayi yaji kalmar girma daga wajenta,mikewa tayi a guje ganin yayo Kan gadon da niyar kamota,da gudu ta sauka ta nufi kofar amma kafun ta Isa har Lahab ya Kamata d"agata yayi da karfi ya maka akan gado tsorata tayi ta kwala Kara duk da kadon Mai laushine Dan Saida katifar ta lotse ta Kara tashi da ita binta Kan katifar yayi ya danne kana ha had'a fuskokin su waje daya Yana wuci Kamar wani kumurci,fuskar tasa take bi da Ido tana kallon mijin nata sai Kuma tasa hannu a hankali ta shafa gemun sa daya cika dam da gashi,buge hannun yayi irin bayason Nan yace"wallahi wallahi daga yau Kika Kara min maganar girma Zan Baki mamaki,yaushe Kika girmeni a gidan uban wa"?




"Hhhh ka manta Naga date of birth naka nafa baka wata biyu"wallahi karyane babu wani wata da Kika bani Kuma Kika Kara cewa kin ban banyafe ba wallahi"ganin fad'an nason Zama babban magana Kuma gashi taga ya hau zuciya,a hankali ta Kama lips nasa ta tsotsa lumshe Ido yayi sai Kuma ya zame lips nasa a bakin ta ya Kara maidawa shiya Kama nata Yana tsotsa duk lokacin da ta yunkura zatayi amshi nasa sai yayi saurin Zame nasa a nata inta yunkura zata kama sai Kuma ya d'aga kansa a nata"hannu tasa ta kamo Kan da karfi hade da capkar dan tsukekken lips in nasa ta hau tsotso.





dan zame jikinta tayi a nasa ganin abin nason wuce gona da iri ajiyar zuciya ya sauke kana ya d'aga Ido ya kalleta ganin tana kokarin maida riganta jikinta"ya haka"kaga"ta nuna Masa agogon bango tace"isha'i yayi ya Kamata ka tashi kayi wanka kayi sallah kaci abinci"hararanta yayi yace wankan da nayi kafun nayi mangari ba fa"?hhh ai wani zaka sake wancan ya baci"kana ta Mike ta bar dakin,zaune suke akan dinning Suna cin abincin ya Kara tambayarta a Karo na uku Ina yaran sa"Suna wajen Ade kasan yaran Nan tun azahar har yanzun banji duriyan su ba"tura abincin hannunsa yayi Baki kana yace"ai su indai da Madara baka da matsala dasu"?




"Gaskiya ne Kam",bayan sun gama cin abinci Lahab ya zauna a falo tare da kunna TV Yana kallo,zuwa tayi ta zauna akasan cafert in dake kusa da kujeran,hannu tasa ta d'aga kafarsa ta daura akan cinyarta ta Soma matse Masa kana ta Soma magana Kamar haka"mijinta"daga Ido yayi ya kalleta Suka had'a Ido sai Kuma ya d'aga Mata gira daya"?akwai maganar da nake so muyi da Kai"uhmm Ina jinki"akan maganar koma warka nageria ne gaskiya banji dadi ba Kuma banso abin ya faru ba kwata kwata"meya faru Wanda Baki so ba"ya tambaye ta Yana kwace kafarsa daka Kan cinyar ta"





"daman akan maganar tafiyarka nageria ne a ganina bai Kamata kaki zuwa ba kodon abinda zaije ya dawo dear baka tunanin randa asirin mu ya tonu kada ace saboda Ni kaki komawa gida"had'a fuska yayi kana yace"watoh karana Ade ya kawo Miki kenan? ke kuma gaki uwata"kayi hakuri ba karanka ya kawo ba yadai zo ya ban shawara akan abinda ya dace ne, Kuma kaga duk duniya wallahi bana tunanin zaka samu abokin da yakai Adewale tsakani da Allah yake sonka Kuma Yana so maka abinda yake sowa kansa"shuru Lahab yayi na dan wani lokaci kafun ya kalleta yace"toh shikenan in Allah ya kaimu Rana ita yau zamu tafi nageria Amma fa ki sani zanyi kewar ku"dariyan yake ta Masa itama tace"ai Suma sunyi kewarka"?





Amma fa innaje sati biyu zanyi na dawo"waro Ido tayi tace shekaran ka biyu kaje ka musu sati biyu ka musu 2 months dai kawai"Kee in tafi in bar yay.................... knocking in door shiya hanasa karasa maganar sa mikewa Nnenna tayi sanin wake bugawar ta shiga daki,Lahab bude kofar yayi ade ne d'auke da yara harda bag nasu ya shigo falon fuskar Lahab Koh walwala babu ya koma ya zauna,fitowa Nnenna tayi sanye da hijab Kamar yanda Lahab yace Mata ta daina Zama da mutane babu hijabi shiyasa haryau su Muhammad basu San ba musulma bace ita,"uncle sai yanzun gaskiya sannunka da kokari wallahi"tana karasa maganar ta ciccibesu sukayi daki,Zama Ade yayi Yana dariya kana yace"daga gani dai hajiya ta bada umurnin tafiya ne"



Shuru Lahab ya Masa shikam Koh a jikinsa haka ya zauna Yana Masa hira daga baya Lahab ya sauko sukayita Hira har Suka Saida ranan tafiya.




***************
After one week,yau ne ranan tafiyar Lahab tun safe yake zaune a dakin sa Nnenna nata shirya Masa Kaya haka yaransa Suna manne dashi ya d'aga wannan ya aje ya dauke wanan ya Goya haka Yan nageria yau ba karamin farin ciki suke ba

Please Login or Register in order to submit comment