Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hudu suke kwana a dakin ga mata a sauran dakunann Koh bacci basa iyawa saban surutun jama'a daga asuba dana kuke kuken yara daman shi Anwar tuni ya koma gidan sa tare da zugan abokan sa don har sun Fara program na biki umaima ne sai gobe laraba za'ayi kamu.



daukar jakansa yayi Rahab dake zaune a gefe mikewa yayi ya dau NASA daya jima da hadawa,fita sukayi Suna ratsa jama'ar dake falon Suka fitowa tsakar gidan matane make tirim sai muneera dake zaune a gefe ga dukkan alamu kuka ta gama ga idanunta a kukkumbure,yafitota Lahab yayi da hannu ba tare daya tsayaba ya fita kofar gida.


Biyosu tayi har waje kallon ta Lahab yayi sannan ya tambaye ta meya faru wani kuka ta sake da karfi tana cewa"toh ba mamu bane ta aikeni tun safe Ina Kai katuna gidan kawayen ta shine fa ban samu lalle ba har Mai lallen ta tafi kafun na dawo, Kuma nacewa ummu ta ban kudi naje saloon Amin tace Wai bazata bayar ba.


"yanzun ke da girmanki Zaki tsaya kina kuka a gaban mutane amma wallahi kinji kunya duk yanzun ba wannan ba nawa ne kudin lallen"?cikin murna tace 3k ne uncle hannu Lahab yasa ya zaro 3k ya Mika Mata da murna ta karba tare da juyawa ta koma cikin gidan da Sauri zata dau mayafinta.



Gidan su ya jafar Lahab suka nufa don su nanne ma duk sun zo gidan su maza ne kadai a gidan ya jafar in, jakansa kawai Lahab ya aje Suka Shiga gari da Majid dinkin sa yaje ya karbo daga Nan Suka wuce cinima sai kusan 6 na yamma suka koma gida,abinci Suka samu an turo musu daga gidan biki Mai Rai da lafiya bayan sunyi dinner ne Majid ya kallli Lahab sannan yace"Lahab yaufa akwai casu"cikin rashin fahimtar Lahab yace kamar ya akwai casu ban gane ba"? murmushi Majid yayi ya mike tsaye tare da bude wardrobe nasa ya fito da wasu arnan jeans da longsleeve tare da wani jacket Mai uban kyau ya wurgawa Lahab a fuska Yana cemai"yau za'a Yi partyn ferry za'a kwana ana shashewa da Yan Mata Kai yau akwai casuuuuu



da Sauri Lahab yace"kana nufin yau za'a ayi partyn auren nata"?kwarai ma kuwa shiyasa na Mana shopping ba tare dana sanar da Kai ba gasu maza by 10 o'clock Muna hotel.



Mikewa tsaye Lahab yayi zai fita a dakin da Sauri Majid yace Ina Kuma zaka bayan nace maka karfe goma zamu fita yanzun Kuma Ina zaka"bazan Jima ba waje zanje Ina zuwa yanzun Nan,Yana karasa maganar ya bude kofa ya fita,da Sauri ya zaro wayar sa lalubo number Anwar yayi jikinsa har wani rawa rawa yake, ya Kara a kunne amma Harya tsinke Anwar bai d'auka ba Kara Kira yayi again har Saida Yama Anwar five miss call kafun yaji an d'au wayar abokin sane ya d'auka yace Yana wanka amma inya fito zai kirasa..........................................




🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 88&89

Komawa cikin gidan Lahab yayi ya samu har Majid ya shiga wanka, agogo ya kalla 8:30 ne na dare fitowa majid yayi Yana goge kansa yake cewa Lahab"kaga kayi Sauri wallahi tara yayi muna cikin gidan Nan fita zai Mana wuya kasan Daddy dasa Ido"?girgiza Kai kawai Lahab yayi ya bude bandakin ya Shiga Bai Jima ba ya fito Kaya ya sanya Suka fito har lokacin Anwar bai kirasa ba bini-bini sai ya duba wayar sa har Majid ya kasa hakuri ya tambaye sa meyake dubawa a wayan sane Wai"?akwai Wanda zai kirani ne Kuma har yanzun bai Kiraba"toh Kai ka kirasa Mana"na Kira baya d'auka ne"oh kawai Majid yace Yana tura gate in ya rufe tsallake titi sukayi,motar dake Parke a gefen titin Majid ya bude baya ya shiga shima Lahab budewa yayi ya shiga mutum biyu ne a ciki saurayin da ranan yazo ya dauke su sai wata budurwan dake zaune a gefen sa Tasha wanka cikin English wear.



tafiya suke Majid da abokan Shashancin sa sai Hira suke akan party yau da kayatuwar da zaiyi,wani kayatatten Hotel Lahab yaga sun nufa gate aka bude Suka danna hancin motarsu ciki,tun Kan su Isa parking space sukejin yanda kide-kide ke tashi Kamar ba dare ba ga matasa na shigowa da mota wasu da machine harda Wanda masu xuwa da kafa ma, parking sukayi suka sassauka dukansu nufar Hall in sukayi Lahab na binsu a baya har Suka danna ciki wa'iyyazu billah Mata da mazane shakude ansha wanka cikin banzan Kaya bama Kamar matan Wanda Rabin tsiraicin su ke waje,Zama su Lahab Sukayi don ita uwar gayyar Bata shigo ba.



Tsabar kid'an dake tashi shiya Hana Lahab Jin ringing in wayarsa dake Aljuhu,mikewa tsaye matasan sukayi suna ihu ganin shigowar farida cikin wasu shegun Kaya wando damamme sai riga da kwata kwatansa kasan kirjinta ga Rabin mamata ta sama a bude kannan yasha attachment ga eyelashes fuskar nan d'auke da makeover,tafiya suke ita da saurayinta da akayi birthday partynsa ranan hannun su cikin na juna da Sauri Lahab yasa hannun sa a Aljuhu ya zaro wayarsa sai a lokacin yaga miss call in Anwar,vedio ya Soma Mata har sukaje suka zauna har lokacin hannun su a cikin na juna sai wani lillikewa a jikin juna suke saving in vedio yayi ya mike da Sauri ya fita a Hall in.



Saida yayi nisa da hall in yanda zaiji abinda Anwar zaice Masa Kiran Anwar in yayi bayan yayi picking yace Masa"Lahab ka kirani d'azun Ina wanka dana fito muhsab yake cemin ka Kira Niko ban kiraka ba sai dazun baka d'auka ba ince dai lafiya"lafiya Anwar don Allah kana Ina"?


da mamaki Anwar yace"kace lafiya Kuma kana tambaya ta Inda nake"Kai dai ka fadamin kana Ina yanzun"?kallon agogo Anwar yayi yace Ina gidana"ok toh ayya in baka wani Abu zanzo akwai maganar da zanyi da Kai"dan shuru Anwar yayi sai Kuma yace"a daren nan zaka fito? kadai Bari gobe da safe kazo Mana"nidai dan Allah kace min eh babu ruwan ka da dare yayi"shikenan sai kazo,katse wayar sa Lahab yayi da Sauri ya nufi gate Keke ya tsayar tare da fada Masa unguwan da Anwar yake.




Sauka yayi a keken ya zare 500 ya Mika ma maikeken tare da bar Masa changen gate na gidan ya tura yaji a rufe hannu yasa ya ringa dukan gate in da karfin gaskiya don unguwan sabuwar unguwa ne ba mutane sosai,bude kofar akayi Anwar ne tsaye Yana kallon Lahab dake kallon sa shima"Wai da gaske zakazo Lahab"?



"Eh man Anwar da gaske nake yana maganar ya bi gefen Anwar ya shiga gidan Anwar ma bayan sa yabi,juyawa Lahab yayi ya dawo wajen gate in yasa hannu ya bude babban kofa ya wangale,zaro Ido Anwar yayi yace Wai kanka daya kuwa ana Neman karfe 10 kana wangale gate Aiko da Rana ba'a irin wangale wannan"Ina key motan ka"?shine tambayar da Lahab ya Masa"wani banzan kallo Anwar ya Masa yace kana nufin abinda ya kawoka kenan kazo ka amshi mota a daren nan toh wallahi badani ba bazaka jazamin masifa a wajen yayunka da Addayiya ba.



Had'a fuska Lahab yayi yace"ba Aron mota nazo ba zuwa nayi in d'auke ka muje wani wajen da zaka Sha mugun mamaki"hararan sa anwar yayi yace kaga nifa yanzun haka a kule nake fa"meya faru toh Lahab ya tambaye sa"d'an tsaki yaja sannan yace"waifa Saida muka gama arrangements na kome farida tace Wai bazatayi bidi'a a auren taba taki yarda da kamun da za'ayi gobe,gashi na tara friends.


zaro Ido Lahab yayi cikin Al'ajabi lallai farida ta shahara kuma insha Allah yau asirinta sai ya tonu,lallaba Anwar Lahab ya Fara daker da sudin goshi ya samu Anwar ya amince zai bisa wajen Amma da sharadin bazasu Kai 20 minutes ba,nuna Masa hanya Lahab yayi Suna tafiya a mota da mamaki Anwar yace ganin hotel Inda Lahab ya nuna Masa Wai su shiga yace,mezan dauka a cikin wajen Nan Kuma,anya hankalinka kalau kuwa"?kaidai muje mana bakace minti 20 ka bani ba Abu Zan nuna maka sosai ran Anwar ya baci don shi gabaki d'aya ransa ya baci ganin shirmen da Lahab ke Masa paka motar sukayi ya fito hannunsa kawai Lahab ya Kama Yana tafiya Anwar na binsa a baya har suka iso bakin hall in Shiga sukayi gabaki d'aya hall in ya hargitse da hayakin wewe,farida na tsakiyar wasu maza biyu gabaki d'aya sun sata a tsakiya sai mammatseta suke,wani Kara Anwar ya sake da karfi ya dafe kirjinsa.





Jikinsa har rawa yake ya suma ratsa mutane Yana son karasawa Inda farida take Lahab Kam wayarsa ya kunna Yana vedio,fincikota Anwar yayi daga Kan cinyar guy in kafun ta Ankara tuni ya wanketa da wani irin bahagon Mari,muryarsa na rawa ya Soma magana"farida kin cuceni da ace nayi gangancin auren ki danayi nadamar da bantaba tsammani ba ashe ke munafuka ce Mai fuska biyu Allah ya Isa Allah ya Isa min,gabaki d'aya Hall in ya d'auke shuru DJ ma ya kashe kid'an dake tashi saboda abin ya d'au hankalin jama'a jin ango da kansa ne a wajen.




saurayin tane yasa hannu ya zaro wukar dake kugunsa ganin mutuwar tsaye da farida tayi bana zafin Marin bane illah na tashin hankali data saka kanta a ciki,ya kaiwa Anwar yanka da Sauri ya tare da tsintsiyar hannun sa wukar ta samu Naman wajen shaa jini ya ballo da Sauri Lahab ya katse vedio ya kusa cikin taron ganin wasu gayu sun kakkama saurayin,ganin yana da niyar karama Anwar yanka, Anwar da mugun shock da farida ta sashi da Kuma yankan daya Sha shiya sakasa Kama Kai da karfi sai Kuma ya sulale ya yanke jiki ya Fadi a wajen da gudu Lahab yayi kansa cikin Kara yana kuka.




Security ne Suka shigo Jin hayaniya a hall in da gudu sukazo Suka ciccibi Anwar ganin jini a hannun sa gashi ya Suma ga saurayin farida da wuka a hannu sosai Suka tsorata sun d'auka Koh kisan Kai akayi,Aiko ganin abinda ya faru daman police station na kusa waya sukayi lokaci kankani Yan Sansa Suka shigo wajen Aiko take aka Soma guje guje wasu sun gudu wasu an kamasu cikin wa'inda aka Kama harda farida da saurayin ta,Majid dai ya matso wajen Lahab sukace Yan uwan Anwar ne Kuma Yan sandan sunga Kama na jini sosai sukayi asibiti,da isarsu aka karbe Anwar hankali tashe Lahab ya d'au wayarsa ya Kira Abbu karawa yayi a kunne Harya tsinke bai d'auka ba agogon hannun sa ya duba 11 saura na dare yasan war haka Abbu ya Jima da kwantawa,




Zama yayi a reception na asibitin Majid dai har lokacin Yana tsaye Yana aikawa da Lahab mugun kallo wallahi baisan farida itace matar da Anwar zai aura ba da bazai yarda ma Lahab yasan da zancen party ba, number Shareef ya Kira d'auka Shareef yayi baiyi magana ba sai Lahab ne ya Fara sallama amsa Masa yayi Yana tambayar sa lafiya?,ce Masa Lahab yayi Anwar ba lafiya Yana hospital tare da tura Masa address in asibitin.





cikin kankanin lokaci Shareef ya iso tare da tambayar ba'asin cutar nasa anan Lahab yake sanar dashi abinda ya faru"Kan bala'i lallai wannan yarinya ta cika algunguma Ina vedio yake"?Mika Masa wayar sa Lahab yayi da Sauri Shareef ya karba Majid dake gefe cikin damuwa yace Shareef me zakayi da vedio?Koh kallon sa Shareef baiyi ba ya d'au wayar sa ya tura vedion a take ya sake a internet tare da Karin jawabi,ya mikawa Lahab wayan sa.



Lahab Koh a jikin sa a asibitin Suka kwana su uku,washe gari maganar farida Wasa-Wasa Saida ya baza online Koh Ina ka Shiga zancen ake Kota Ina zagin farida ake wasu mazan na comments akan Koh Mata sun Kare in sune Anwar bazasu aure taba bare ma da Shareef ya had'a da hotonan ta na islamiyyar da labarin ta da irin yabonta da ake.




A gidan su Lahab Kam tun daren jiya Yan Mata Suna Fara gani kankace kala tuni magana ya baza unguwan daga zaran wani ya bawa wani labari sai ace a nuna vedio Koh a tura musu a haka abu ya Fara yaduwa sai ga Kiran Shareef yake sanar da Abbu nasu Anwar na asibiti bayan Abbu take asibiti lokacin Anwar na bacci gabaki d'aya gidan bikin ya Zama wani iri kowa ka gani fuska ba walwala,11pm Anwar ya farka nurse ta fito ta sanar dasu daman ba'a fadawa matan gida halin da yake ciki ba,Abbu da Lahab sai Majid da Shareef ne Suka nufi dakin,Suna shiga Anwar ya fashe da kuka ganin mahaifin nasa,matsowa kusa dashi Abbu yayi da Sauri ya rungumesa Yana magana yana kuka yace"don Allah Abbu karka sani auren ta Dan Allah Abbu a fasa auren Nan wallahi inna aure ta Zan mutu ka taimaka min Dan Allah.





Duk da ya bawa Abbu tausayi amma sai ya maze yace"ah ah Anwar hakuri zakayi mu rufa Mata asiri yanzun inka fasa auren Nan nasan kaida aure kuma sai wani ikon Allah yanzun fa karka manta kana da shekaran 35 ba aure, yaushe zakayi kenan in ba'a Yi yanzun ba don hakan zancen aure ba fashi"da Sauri Shareef yace haba Abbu dan Allah Mana in dai aka ma ya Anwar haka wallahi ba'a Masa adalci ba na rantse"




Shuru Abbu yayi baice kome ba"kuka Anwar ya sake Yana cewa"wallahi Abbu na amince zanyi aure Koh Mata hudu ne na amince amma dan Allah banda farida"kana da Wance kake so a hadaku ne banda yarinyar"?



Girgiza Kai yayi yasa hannu Yana share hawayen dake bin fuskarsa ganin Abbu ya sauka babu zancen farida yace"ah ah amma Ni Koh Wance ka aura min Koh zaka aura min na amince wallahi"sosai yaron ya baiwa mahaifin sa tausayi sosai"toh shikenan yanzun dai tunda ka farfado Bari likitan yazo yayi discharge naka mu tafi.



Kafun azahar an sallamo Anwar a asibiti amma an dinke hannun sa don wukar ya shiga karfin haline kawai gidan suka koma saboda tsananin damuwa dayake ciki ga abokan sa dake ta maida zancen amma dai Alhamdulilah tunda ba'a d'aga biki ba,mamu tafi kowa shiga tashin hankali ganin ta samu Anwar zaiyi sure ga Kuma abinda ya faru amma Koh banza taji dadi sosai da Allah ya taimake ta ba'ayi auren ba.




Family meeting na gaggawa Abbu ya had'a duk Wanda ya dace Kuma d'an uwa Koh Yar uwa na kusa-kusa duk an hallara zazzaune ake manya nakan kujera yara na kasa,da Addu'a Abbu ya Fara bayan an shafane ya Soma jawabi Kamar haka"Alhamdulilah yabo da godiya su tabbata ga Allah mad'aukakin sarki daya kawo mu wannan Rana Mai albarka,Wanda yake kunshe da abubuwan mamaki da Kuma jimami,a gaskiya abinda ya faru tsakanin Anwar da yarinyar Nan farida a gaskiya bamuji dadin abinda ya faru ba dukan mu,haka zalika yad'a abin a kafan sada zumunta.




Anwar ya nuna bazai iyya yarda da auren yarinyar ba, Wanda Koh baifad'a ba nida nake mahaifin sa da yan uwana bazamu amince ba,nida jafar munje takanas ta kano har gidan su mahaifin ta Kuma mun Musa bayani,bai nuna wani bacin ransa akan abinda muka je dashi ba don dama labari ya riga yaje musu,ga akwatunan sa sun hadamu dashi mun dawo.




Nida d'an uwana tare da goyon bayan kanwar mu sumayya mun yanke hukuncin had'a Anwar aure da Yar uwar sa A......................................






🍀 *By Ruqeenjalal* 🍀




*Littafin nan na kudi ne gamai so naira 300 ne vie* 2185602275 *Rukayya Ibrahim UBA bank koh card na MTN zaki tura ta wannan layi 0816 464 2820 tare da shaidan biyan ki*


Page 90&91

Zamu had'asa aure da Yar uwarsa Aisha"Koh rufe Baki Abbu baiyi ba mamu tayi wani irin zabura ta Mike zatayi magana"Abbu bai bari ta furta kalla daya ba ya d'aga Mata hannu da Sauri fuskar nan tasa babu fara'a Sam don tunda take dashi Bata taba ganin bacin Rai a kwance a fuskarsa irin na yau ba sosai tasha jinin jikinta hakan yasata koma ta zauna"kuka Aisha ta sake da karfi tana rufe fuska Jin abinda bappan nata yace kamar a mafarki Wai za'a aura mata Anwar,rufe fuskar ta tayi da hijabin dake jikinta,Anwar Kam tunda ya sunkuyar da Kai Bai d'ago ba har Abbu ya kammala jawabin sa tare da cewa Suje su cigaba da buki aure ba fashi.



Jiki a sanyaye Anwar ya mike yabar falon bayan fitan mahaifan nasa, Aisha Kam tama kasa tashi a wajen har lokacin bata bar kuka ba wasu daga cikin yan uwa ne Suka Soma bata baki Suna nuna Mata muhimmaci da ribar biyayya ga iyaye,nanne da wasu Yan uwansu Suka d'au Aisha Suka nufi gidan ya jafar da ita aka kafa Sabon biki a gidan dole yasa Yan uwa rabuwa Kashi biyu wasu Suka koma gidan jafar,sosai Yan uwa sukayi murnan wannan hadin shikam Anwar daga Nan gidan sa ya koma ya kwanta duk nacin abokan sa Bai saurare suba illa bar musu dakin da yayi ya Shiga wani dakin daban ya kwanta gabaki d'aya ya kasa manta abinda farida ta Masa.


Misalin karfe 4 na yamma mototine cike a kofar gida Koh wace Mata Koh Yan Mata zaka ganta cikin anko ansha wanka iya wanka ana shishiga mota,alAmarya umaima dake d'aki, Masha Allah tayi wani irin kyau cikin material dinta Golden colour dinkin buba akayi zanine normal sai riga da aka d'aura zani akai kannan yasha d'auren turban ga wani yadi Mai sheki da aka rufe kanta dashi sosai tayi kyau kowa ya ganta yasan kudi yayi kuka a cikin suturan dake jikinta Banda golagolai dake wuyanta da hannu da kunne.



Wata babbar mace ce ta shigo dakin tare da cewa Amarya inta gama Shirin yanzun za'a fitar da ita ganin ta a shirye yasa ta fita sai gata ta dawo da wasu matan biyu Suka dau Amarya kawaye dake cikin anko Suka Mara musu baya a haka aka ratsa gidan da ita har bakin gate,zazzafar mota baki dake tsakiya aka nufa da ita, budewa akayi ta Shiga sannan matan Suka shiga,Suma kawayen mota daban Suka shiga ba wannan ba.




****************
Lahab daya gudu daga gidan ya jafar ya dawo gidan su Jin hayaniyar tafiyar kamu ta lafa yasa sa mikewa wanka yayi ya sanya Sabon shaddan sa Ash colour sabuwa Kal da ita takalmin soso ya zura ya fito daga gidan gabaki d'aya gidan shuru sai daddaiku da baza suje bane aka bari amma gabaki d'aya gidan babu hayaniya nufar gate yayi sai Kuma ya dakata Jin ana kwala Masa kira,juyawa yayi da mamaki yake kallon Mai Kiran nasa uzaifa ne"tsayawa yayi har uzaifan ya karaso kallon sa yayi da mamaki yace"Lahab baka tafi ba ai na zati ka tsufa a wajen"tunda aka Fara program ka gannin a wajen"?shine tambayar da Lahab ya Masa.


Ah ah ban ganka ba Kuma nayi mamakin haka kwarai"yauwa toh ka gannin Nan bazan iyya zuwa biki, duk Inda na juya Ina had'a Ido dasu Mami ba, ban Isa ba Ni Jiran dinner nake da d'aurin aure su zanje"Kama Baki uzaifa yayi Yana dariya kafun yace"Aiko dadai ka jira daurin aure kawai,dinner Kam bana tunanin zaiyu"?



"Akan me dinner bazai yuba"eh in gaya maka ya Anwar da Aisha wallahi dukan su kin zuwa sukayi ba yanda abokan ya Anwar basuyi ba yaje kamu yaki itakuma Aisha anyi anyi tayi Koh lalle ne taki sai hauka take musu ran nanne ya baci taci kaniyarta"hhhhhhhhhhhh wani bazawarin dariya Lahab ya sake Yana bude gate in ya fita baikara cewa uzaifa kome ba,Yana tsallake titin layinsu kaman ance Masa ya waigo kawai ya hangi Nnenna na tafe sanye da uniform.



da sassarfa ya bita a baya a hankali-hankali,har lokacin bata juyo ba,Yana Isa bayan ta unexpectedly yasa hannu ya rufe Mata Ido,tsayawa tayi kana tasa hannunta ta tattaba nasa,sai Kuma ta hade fuska hade da cewa"Lahab sakar min Ido a bakin titi muke mutane na kallon mu"da mamaki ya sakar Mata Ido juyowa tayi garesa Suna facing in Suna"amma dai daman kin gannin Kika wani fusge Kamar baki ganni ba"da murmushi a fuskarta Wanda tunda ta hadu da Lahab tasan tana da yawan murmushi tace"banganka ba amma dana taba hannun ka na gane wanene Kai sai Kuma ta Soma bin kayan jikinsa da kallo Kamar Mai nazarin wani Abu shidai yayi shuru yana binta da Ido Kamar yanda take bin kayansa kana tace"aure ake a gidan kune"?da mamaki yace"ah ah me Kika gani "girgiza Kai kawai tayi tace"babu kome"amma me yasa Kika ce ana aure a gidan mu"ba nace bane na tambaya dai.



boron ta dake bayanta yasa hannu ya cire yana cewa"ke kullum makaranta makaranta ana revision in ma bazaki sassautawa kanki ba"hade fuska tayi ta Kama tafiya tana cewa"in banje makaranta ba Ina zanje kenan"?kamo hannunta yayi kawai ya nufi kofar gidansu Adewale dake gabansu,waro Ido tayi cikin tsoro tace"Ina zaka kaini sakarmin hannu menene haka banason"kin sakin nata yayi yasa hannu ya tura gate in ya shiga,ihu ta Soma Masa tana cewa ya saketa bazata shiga ba amma yaki sakin nata maida kofar yayi ya rufe ya nufi bakin flat in hannu yasa da karfin cin tuwo ya bugawa, kofar falon,Adewale dake kwance a falo ya mike da Sauri don shi kad'aine a gidan iyayen sa sunje garin su.





da Sauri ya mike Yana masifa Akan za'a balla musu kofar ne,budewa yayi sai Kuma ya sake baki da Sauri Yana cewa"kutt Kai sai Kuma yayi shuru ganin mace a bayan Lahab Yana rike da hannun ta"da Sauri ya matsa ya Basu hanya shigowa Lahab yayi har lokacin Yana rike da ita,shigowa sukayi ta fizge hannunta da gudu ta nufi kofar da har lokacin Adewale na tsaye rike da kofa baki bude idanun sa har lokacin nakan su,ganin yanda ta nufo kofa a guje yasa Ade matsawa da sauri,Lahab daya biyota shima a guje ya fincikota tare da matseta a jikin ginin kofar da karfi Yana zagin Adewale akan meyasa zai masa Mata ta wuce.




da masifa Adewale yace"Wai uban mi zakayi da itane ka shigo Mana gida sannan kana wani matse Yar mutane da Allah saketa"saketa Lahab yayi da Sauri ya nufi kofar ya rufe harda makulli Zama yayi akan kujera har lokacin Adewale da Nnenna dake manne a bango Rai bace Basu zauna ba"malam yau tun safe banci kome ba ka ban abinci"amma dai Lahab bakajin tsoron Allah ba ana biki a gidan ku ba yanzun ma haka Shirin tashi nake nashirya zuwa wajen kamu".



Mtwsss Lahab yaja tsaki yace"shikenan don ana biki a gidan mu sai Kuma naki cin abinci, Koh me kake nufi dan Allah kawo mun abinci"yanuna Nnenna sannan yace mata"kizo ki zauna Bari ya kawo Mana abinci"kin Zama tayi"Adewale kam kitchen ya shiga duk da baida kome dafaffe a gidan Kuma badon Albarkacin Nnenna ba bazai saurare dafa Masa abinci ba,Lahab Kam kwanciya yayi yadau remote ya chanja tasha Nnenna har lokacin tana tsaye a Inda take.



30 minutes saiga Adewale ya fito da plate d'auke da dafaffen indomie sai tururi yake kowa yasan yanda yaran yorubawa suke girki,dangolawa Lahab yayi a gaba ya koma ya zauna,mikewa Lahab in yayi ya dau plate na indomie Yana cewa Ade"Kai haka zaka kawo abinci babu ruwa ba drink's Kuma plate daya ita Kuma fa"?shuru Ade yayi baiko kalle Saba sai Kuma ya mike yabar falon,shima Lahab mikewa yayi da Sauri ya nufi Nnenna ganin haka ya sata rugawa zata gudu daga wajen da sauri,binta yayi Suka ringa zaga falon a guje aje plate na indomie yayi ya kwala ihu Yana nuna Mata kofa kamar irin yaga abin tsoron Nan,juyawa tayi zata ga Inda ya nuna matan kawai ya damkota damka bana Wasa ba.



Jawota yayi ya aje akan kujera yunkurin tashi tayi ya maidata zaune daukar indomie yayi ya daura Mata akan cinya Yana bin kafafunta dake waje da kallo,hade rai yayi yace"yanzun meye amfanin wannan sutura ace mutum yasa Kaya kafa a waje cinya a waje Wai Ansa uniform"hannu tasa ta tura kirjinsa baya tana cewa"Wai meye hakane don Allah d'agani Ni banjin yunwa bazanci ba Kuma babu ruwan ka da kayana.



"Komawa daya kujeran yayi ya dau indomie ya Kara daura Mata a kafa"wallahi saikin ci kici kawai sai mu tafi Ni babu abinda Zan Miki kinji"hararan sa tayi ta dau plate in ta bude ta

Please Login or Register in order to submit comment