Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tsararshi?,yakanyi saurin qaryata zuciyarsa da kwabar kanshi,yana ganin kamar maganganun wasu daga cikin abokansa dake maza hasashen yiwuwar rashin samun bilkisu suke son tasiri a ransa.


Baibar wajen ba har sai daya daina hangota,saiya saki ajiyar zuciya yana juyawa don barin layin da niyyar randa zaije zai tafar mata da ita,don a ganinsa ya kamata zuwa yanzu ace tana riqe waya a hannunta,kodon yasamu damar jin muryarta koda baya nan.


Saura kadan yaci karo da abokinsa dake tsaye bayanshi yana kallonshi,suna hada idanu yasaki murmushi mai kama da dariya
"Irin wannan kallo haka?,ko daukota kawai zakayi ku wuce?" Dariya hamza yayi yana dan dukan kafadar mudassir
"Mtsweew,bari kawai abokina,yarinyar tashigemin rai da yawa,fatana kawai shine nagama samun kanta,tana da dan wuyar sha'ani da rashin saurin sabo,har yanzu ta kasa sakin jikinta dani bare na fahimta komai" yana maganar ne lokacin da suka fara tattakawa tare shida mudassir
"Top class mace kenan,haka akeso ai,bawai kawai tashin farko ta sallama komai da komai ba,kamar wata haaja a kasuwa" hannu yabawa mudassir suka tafa
"Allah mutumina?"
"Allah kuwa,kaidai kaci gaba da jumuri" sake tafawa sukayi cikin dariya kana sukaci gaba da takawa tare suna ci gaba da tattaunawa kan bilkisun da irin halayenta daya fuskanta.


Bayan sallama datayi a tsakar gidan nasu sai kuma tasoma binsa da kallon mamaki,kullum abun mamaki bai qarewa cikin gidan nasu,baqine dangin abbanta daga nijer,qannenshi biyu sai yayarsa da kuma qanwar mahaifiyarsa wadda take tamkar a maxaunin mahaifiyarsa tunda tajima da rasuwa.


Ba zata iya tuna lokaci na qarshe da suka zo gidan dan uwan nasu ba da sunan ganin iyalinshi ba,koda yaushe idan ka gansu to baban nata ya tashi qara aure ne,abun yana daure mata kai,tamkar basu damuwa da rayuwarshi,kamar bashi da mafadi?,kamar basu bibiyar al'amuransa,haka siddan duk lokacin daya tashi qara aurenshi zai gayyatosu ne,su kuwa tinqis tinqis haka zasu taso su taho biki,batajin akwai wadda ta taba tuhumarshi ko tambayarsa labarin matarsa da sukazo biki wancan karon meye rabashi da ita?,amma abinda ta fuskanta shine,kamar yana riqa maqudan kudade ne yaje yamusu yayyafinsu.


Jiki a mace ta jingina da bangon da yasha fentin farar qasa albarkacin zuwan amarya,wanda iya tsakar gidan akwai yayiwa,dakunansu kuwa ko oho,tazame tanemi gefan tabarmar da suke kai tazauna.


Cikin nuna girmamawa tayi musu sannu da zuwa,saidai sam babu wani sabo ko sakin jiki a tsakaninsu,don hatta yaran sun sansu dai a idanu amma basu wani saba ba,don ba ganinsu din suke ba bare ace wani shaquwa ta shiga tsakaninsu,don haka itama tana gama gaidasun tamiqe,tana jin yadda suke yaba girmanta da kyanta,saita jefesu kawai da murmushin yaqe,harta shiga dakinsu bataji motsi ko taga gittawar umma katti ba,batasan cewa tana qule a daki ba,baqinciki da bacin rai kawai ke sakadarta,shi yasa tunda tabasu tabarma suka shimfida nan tsakar gidan bata sake bi ta kansu ba.


Abun mamaki da daddare saiga kular abinci lafiyayya ana shela kowa yafito ya karba,tana zaune inda take bata ko motsa ba amma ta tura yaran su su karbo suzo suci su kwanta,har suka gama ci suka gama santinsu tana kallonsu bata motsa ba,sai data tsinto muryar mahaifinta yana qwala mata kira kana tamiqe a sanyaye tafita da faranti a hannunta.


"Yarinyar nan bilya babu inda tabaro maimunatu,ai bilya kayi asarar mace,har yau baka maida kamar maimunatu ba"
"Hmmm,bari kawai binto,ai maimunatu diyar albarka ce,bansan dame zan saka mata ba,maiminatu 'yar aljanna ce na shaida hakan tun kafin ta rasu"itadai tana tsugunne mariya qanwarshi na zuba mata abincin batace komai ba har aka zuba matan tamiqe zuwa daki.


A gaba tasaka kwanon abincin,tunanin mahaifiyartata ya bijiro mata,kewarta ta bijiro mata,zataso sake rabarta,zataso tasake jin duminta,ta jingina a jikinta ta gaya mata damuwarta,saidai tasan ina,mai rabawar ya riga daya raba,babu wani sauran abinda yarage sai haquri dangana da kuma binta da addu'a.


***** ****** *****


A nutse yake fitowa daga dakin nashi sanye da farar riga mai dogon hannu da rufaffen wuya,farace tas ta kama jikinsa duk da cewa tana da dan kauri,sai wandon jikinsa shima farine kamar rigar daya zarta gwiwa duk da cewa sanyi akeyi,fuskarsa tayi fresh babu wannan fushin ko digo daya shigo dashi dazun,saidai wannan daurewar da miskilancin na tattare dashi.


Zuciyarsa ta rage nauyin datayi,saboda yasamu cikin baccinsa yayi mafarki wanda hakan ya qara mishi relief,kai tsaye falon yanufo hannunshi riqe da wayarshi yana neman layin safwa,don yasan halinta sarai,yanzu haka qilan tana nan a dame.


Mutum biyune zaune a falon jabir da mustapha suna kallo,hada idanu sukayi da jabir saiya dauke idanunshi gamida mazewa,yayin da azeez ya jefeshi da wani kallo wansa shi jabir din yasan ma'anarsa sarai,kuma yasan laifinsa,dauke kansa azeez din yayi yanufi kitchen,a can yasamu abinci a cooler,yasan aikin mustapha ne,don kaf gidan shi kadai yake da juriyar dafa musu abinci suci,saidai yau an samu akasi sam baya sha'awar abinci kowanne iri ne,don haka ya hada coffe mai zafi yajuye a wani qawataccen qaramin flask wanda yafi kama da butar shayi,yadauki cups dinsa guda biyu bayan yazuba dambun nama daya taho dashi tun daga gida nijeria a wani dan qaramin plate sannan yafito zuwa falon.


Yana shirin zama mustapha yace
"Kafito kenan" kaiya gyada mishi daidai lokacin da safwa tadaga wayar tashi,kamar kuwa yadda yazata hakance ta kasance,kukan shagwaba ta sake masa,shuru yayi idanunsa a lumshe yana saurarenta kana yana neman daukin Allah,sai daya barta ta rage qorafinta sannan yadakatar da ita cikin sanyin muryarsa fiye da yadda take ada saboda yanayin jikinsa da babu qwari kamar yadda yasaba jinsa,ko mustapha dake gefansa baijin me suke fada
"Don't stress your self sweetberry....duk tyn din da kiks kira kikaji banyi picking ba to ina da uzurine zan duba kiran kuma zan biyo ,i made it clear?"ya qarashe maganar da sigar tambaya,daga haka suka dan taba hira duk da batayi tsaho sosai ba,yace mata baijin dadine yau sosai,amma idan yasakeyin bacci yatashi zaiji fresh then zai kirata,yasauke wayar daga kunnensa yajawo kofin shayinsa yasoma shan a hankalin yana hadawa da dambun.


Akaran kanshi shurun azeez din yasa yasake tsarguwa,cikin sigar jan hankali yakirashi
"Prince" shuru yamasa kamar baiji ba,bayan wasu mintuna yasake maimaita kira,sai azeez din ya aje kofin hannunsa ba tare daya dubi sashen da jabeer din yake ba yace
"Wannan shine lokaci na qarshe jabir,karka kuma maimaita abinda kayimin yau"
"What?....daga yin abu don na taimakeka?" Sai a sannan yadubeshi ya watsa mishi wani kallo kana yace
"To hell with your taimako,banaso kuma kar ka sakemin irin wannan" yasan qwarai ya fusata,yana qoqarin danne dariyarshi ya hada hannyenshi biyu waje daya yace
"Is ok,ba za'a qara ba,am so sorry" saiya janye idanunsa daga kanshi,kana yamiqe a nutse yasoma takawa ya isa gaban socket din kayan kallo zai cire charger din system dinshi,yanaso yayi amfani da ita cikin daki
"Amma yarima.....kamal fa,kayi haquri yadawo" sake waiwayowa yayi yadubeshi fuska a dinke
"Abokin cin mushe?" Kai ya girgixa dariyar nasake cinsa
"Nooo....tunda kamasa haka surely zai sauya"
"Ba yanzu ba" ya bashi amsa yana takawa zuwa dakinsa abinsa ba tare daya waiwayo ya dubeshi ba.


"Prince taurin kai,prince kafiya,kai wannan mutum...." Jabeer yafada yana tsalle gamida tsallakowa zuwa inda azeez yatashi yaja cup din tea din yasoma surbewa yana hadawa da sauran dambun,kafada mustapha ya daga
"Yadai fiki gsky magana ta haqiqa,kawai kuyi qoqari kuma ku sauya a karan kanku kodon mutuncin addininku"
"Zamu sauya amma ba yanxu ba,don banga dalili ba hakanan da quruciyata,da dukiyata da kyauna nazauna ban mori rayuwata ba,shima yanaso,tsabar iya takura kaine" dubanshi kawai mustapha yayi,da alama shima yafara sallama lamarinsu,dukkan alamu sun bayyana wanda yayi nisa bayajin kira saidai gyaran Allah kawai.


______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.

To kuzo ga dama ta samu💃ðŸ»ðŸ’ƒðŸ».

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________
7/11/21, 4:30 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA*👑



*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya ki tuntubi wadan nan lambobin_*


0903 234 5899
Ko
09033181070




11



Rashin samun damar malamin na halartar darasin sa a ranar yasanya daidai period din ajin yazama dandalin hira ga daliban,duk da cewa yawanci koda malami bazaizo ba to akwai wanda zai riqe mishi hissarsa ta ranar,to amma yau hakan bata samu ba,kasancewar yau da gobe sai Allah,hakanan tafi gaban wasa.


Rukuni rukuni ne na dalibai kowa ya kama dabarshi,wasu na saman wajen rubutu wasu na kan kujerunsu na zama,kusan group din afnan Abdallah mu'az yafi kowanne cika da yawa,saidai kana dubansu kasan kowacce tana jine da kanta,duk da hira suke haiqan amma babu wata hargowa a ciki,duk wannan abun da ake bilkisu na saman nata kujerar karatun,ta dora kanta saman wajen rubutu takwantar tamkar mai bacci,saidai ba bacci take ba,littafi ne a hannunta tana nazarin c.a da za'ayi musu a gobe.


Duk yadda ta maida hankalinta ga karatun hakan bai hanata jiyo hirarrakin group din afnan ba,kusan kowacce tana bada labarin yayyenta maza ne na gida da sauran abubuwan daya shafesu,afnan din tana tsakiya batace komai ba sai binsu da kallo da take tana kuma saurarensu,yayin da wani tsagi na hankalinta kuma jifa jifa yake kan bilkisu,haushinta na kamata,itakam tana mamakin yadda mutum yake iya rayuwa baya magana,yadda mutum yake iya rayuwa shi kadai,babu 'yan uwa ba abokai bare qawaye,ta tabe bakinta lokacin da hanan tace
"Princess baki bamu labarin naki yayun ba,nasan it will be sweeter than ours" wani murmushi tasaki tana tuna miskilin yayan nata,ya azeez mai aljanun miskilanci,miskili kafi mahaukaci ban haushi,sa baka dariya sai hamma tatuna wasu daga cikin kirarin da ammi kan masa musamman idan yabata haushi
"Yayana guda daya ne,prince abdul'azeez" ta qarasa maganar cikin nuna alfahari,sautin muryarta na cike da nuna qauna da kulawa ga dan uwanta,da kuma wasu alamu dake nuna tana matuqar ji dashi,sai dukka suka sake bata kunnuwansu,don dama bata taba musu wata magana makamanciyar wannan ba,kowa ya zaqu yaji me zatace
"Uhmmm....tell us about him" hanan da kusan tafi kowa zaquwa tafada tana murmushi.


"Komai zance akan yaa prince na dabanne kamar yadda yake na daban,i have never ever seen mutum kamarshi,shi na musamman ne koda cikin gidanmu ma,tun daga yanayin halittarshi zuwa attitude nashi,kyakkyawa ne yayana,har wataran nakanyi buri dama nice nake da kyanshi" zaro idanu hanan tayi tana cewa
"Wow!,duk yadda kike din nan afnan?" Kaita gyada tana dubanta
"Yes,kyansa ba irin nawa bane,ya hade da kwarjini,kinga banson miskilancinsa,i hate miskilanci"sai kuma tayi shuru tana duban bilkisu a sace,wanda ta tabbatar bilkisu taji abinda tace
"Yana iya wuni shi daya,koda yana cikin mutane kina iya irga maganan da yayi qwara nawa ce,mma duk sanda naso inyi masa mita ko qorafi....u know what?" Duka sai girgixa kai
"Daya kalleni saina kasa cewa komai,there is something special in his eyes,kwarjini....yayana badai kwarjini ba"
"Wow...wow" hanan tasoma fada tana tafa hannayenta kana tasake matsowa gaban afnan sosai
"Pls friend....ki bani yayan nan naki mana,wallahi har naji nakamu" ihu duka wanda yake team din yasaki wanda yashiga har tsakiyar kan bilkisu,ta runtse idanunta don sam batasan hayaniya,saita kifa littafinta saman kan nata,amma duk da haka bata tsira daga jiyo cecekucensu ba,kowacce tana fadin saidai ita.


"Wait.....relax 'yammata" afnan tafada tana duban kowaccensu
"He already taken out" duka sai sukayi shuru suka zuba mata idanu,yayin da itakuma take murmushi
"By who?"
"Miss Safwa ibrahim khalilu attah"
"The attah's daughter?" Humaina daya daga cikinsu tambaya tana zare idanu,waiwaya afnan tayi ta dubeta sannan ta kada kai
"Qwarai" saita sauke ajiyar zuciya tamaida jikinta ga kujerarta tana cewa
"ƙarshen magana?"
"Kaman yaya?" Hanan ta tambaya da alama maganar batayi mata dadi ba
"Zan gwada sa'ata indai zaki hadamu" tasake cewa da afnan,dubanta tayi kana tace
"Da zan baki shawara dasai nace its better ki haqura,nasan ya azeez farin sani,daya daga cikinmu ina da yaqinin ba zata taba burgeshi ba,nasan halayenshi da tsarinsa,even safwa ammi ce ta hadasu...,bayaga haka ma....ya azeez hanan am sorry to say yana da tsada mai yawa,tun a yanzunma da yake da shekara 25 ya kike tunanin gaba,he's belong to mata masu aji da tsada,ina da tabbacin zai rainaki ne saboda yana da kamar safwa....duk fadin makarantar nan wa kike tunanin tafi kowa kyau?" Dukkaninsu kuma lokaci daya idanunsu yakai kan bilkisu,hakanan cikin jikinta taji idanuwa barkatai a kanta,hakan yasa lokaci daya taji wata irin tsarguwa da takura.


Dariya afnan tasaki saboda ta karanci inda suka maida hankulansu
"Koda za'a maidata cikin sahun wasu a duniya,banajin zatayi attaracting dinshi...he's diffrent kamar yadda na gaya muku a baya".


Tsam bilkisu tamiqe bayan ta aje littafinta tasoma ficewa daga ajin,don gaba daya hirar tasu tasoma gundurarta duk da bada ita akeyi ba,amma ta fuskanci wasu al'amuran an soma jefata a ciki wanda ba huruminta bane.


Bata dawo ajin ba har sai data tabbatar malami yashiga sa'an nan takoma,ta tattara hankalinta dukka kan karatun,saidai wata sabuwa kuma,yunwar dake sakadar cikinta ta hanata fuskantar wasu abubuwan,saboda jiya abincinta su hauwa'u ta barwa,don a jiyan baban nasu baiyi cefane ba,da safe ma bata samu abinda zataci ba,amma yau tana saka rai,saboda umma luba tadawo zata leqa gidanta aiki,a haka taci gaba da daurewa har lokacin tashi yayi.


A gajiye tulus ta isa unguwar tasu,kamar ko yaushe ta karya layinsu cike da fargabar yau kuma wanne sabon abu zata tarar a gidan nasu.


Karaf kuwa sai idanunta suka sauka kan 'yar qurqurar anata sauke kaya da sukafi kama dana jere ana shiga dasu cikin gidan nasu,hakanan gabanta ya yanke yafadi,baban nasu bazaidai haqura ba kenan,tunda yadaura niyya sai yayi kamar yadda yasha maimaitawa kullum kwanan duniya?.


Jiki a salube ta isa qofar gidan sanda masu qurqurar suka tasheta da niyyar qarawa gaba,tafidda wani dunqulallen farin hayaqi daya wuce kai tsaye zuwa hancin bilkisu,ta shaqeshi har huhunta,wanda a take yasake murda mata ciki yakuma tashi yunwar dake sakadarta.


Tana shirin shiga gidan saiga umaima da bushira dauke da babban faranti,samansa kwanuka ne jere reras a kai,idanu tazuba musu tana dubansu har suka qaraso,take ta fahimci daga ina suke,ranta yabaci qwarai,ta tsuke fuska tana dubansu sannan ta jeho musu tambayar
"Daga ina kuke?"
"Umma kattice tace mudaukar mata abinci mu zaga mata dashi yau bazata siyar a gida ba" cikin bacin rai ta daka musu tsawa tana dubansu
"Talla?,tallah umaima?,mena gaya muku game da talla?," shuru sukayi dukkaninsu,jikinsu yayi sanyi sosai,a rayuwarta babu abinda ta tsana irin tallar diya mace,ta yarda suyi dukkan wani aikin wahala a biyasu amma banda talla,tallan ma yara qanana kamar umaima da bashira da basu gaza shekara takwas goma ba?,kawai saita isa gabansu ta debe kwanukan daga kansu tamiqa musu jakar makarantarta tanufi cikin gidan suka rufa mata ba.


Bayaga sallama bata qara kan komai ba,saboda ranta dake bace hatta masu jeran amaryar baban nasu ma bata duba ba,wanda bakajin komai cikin gidan sai karadinsu,ga kular abinci da lemon roba baja baja da alama sunci sun hantse,sai data isa qofar dakin umma kattin sannan ta aje kwanukan gabanta,suka dakata daga hirar da suke ita da baquwarta da alama tana labarta mata abinda ke faruwa ne
"Ina kudina?" Abinda tasoma tambaya kenan tana miqawa bilkisu hannunta,saita waiwaya kawai ta miqawa itama su umaiman hannu,sunsan mai take nufi,don haka suka miqa mata kudin tamiqawa umma kattin taja hannunsu,bata tsaya jin mitar da take ba nasun dawo mata da saura,hala ma hamshaqiyar yayar tasu ce ta hanasu.


Duban umma kattin baquwar tayi
"Wai wannan ma diyarsa ce?" Tabe baki umma katti tayi cikin takaici
"Hmmm,aiba lallai harki tafi ki gama shaida yaransa ba,don wasu ma basa garin sun bazama neman kudi"
"Amma kuwa tubarkalla ma sha Allah da ita,ashe yana da zankadediyar yarinya har haka?,wannan wallahi dazai bada ita akai aikatau ba qaramin kudi zaku samu ba" baki umma kattin tariqe
"Rufani ki sayani,wannan da kike gani da qanwar uwarta na kusa ma ba lalle kiganta a gidan nan ba,donma uban ya kafe kai da fata aida tuni bata a nan" nan tadan labartawa baquwar tata wani abu game da bilkisun.


A daki kuwa dukkaninsu sunyi shuru suna kallonta saboda ba kasafai suka fiya ganin fadanta ko bacin ranta ba,saiduk kowa jikinsa yayi laushi,don bacin rai bata bi takan danqararriyar dafa dukan da aka aje mata ba ta daura zani da hijabi tashiga wanka,sai data fito tasanya wata doguwar rigar atamfarta da itama tasoma nuna gajiyawarta sannan taja abincin ta tsakura
"Ku tashi ku shirya mu futa gaba daya" ta basu umarni sanda tature kwanon tanajin taste din bakinta babu dadi.


Daga shigowarta zuwa yanzu cikin gidan anyi guda anyi habaici har batasan sau nawa ba,sai taga haqurin umma katti yau daya da bata tanka musu ba duk da rashin haqurinta,kuma wala'alla baquwartace ta hanata.


Bata bar gidan ba duka sai data kada kansu takaisu har qofar islamiyya suka shiga sannan tawuce gidan umma luba.

****** ******

"Yar halak,yanzu nake zancanki balaraba kinganta ta iso" cewar umma luba dake zaune qasan rumfar dake qofar dakinta tamiqe qafafunta,gefanta wata matace wadda a qalla zasuyi shekaru guda itada umma luban,murmushi bilkisun tayi ta qaraso gefan shimfidar ta zauna tana cewa
"Ina hanya ai,makaranta,yau banyi sauri a hanya ba"
"Aiko tunda nadawo na kasa kauda koda tsinke ina zaman jiranki" murmushi kawai tayi wannan karon,ta gaida umma luban kana ta waiwaya da niyyar gaida baquwar tata,sai suka hada idanu,tun dazun da alama bilkisun take kallo,tadan kauda kanta itama bilkisun haka,ta gaidata ta amsa cikin sakin fuska,daga haka bilkisun tamiqe tasoma aikinta.
Duk giftawar da zatayi idanun matar yana kanta.


"Nikam lubabatu ina kika samo wannan yarinyar haka?" Baquwar ta tambayi umma luba
"Wai bilkisu?,can qasanmu take wallahi"
"Amma kinyi sa'ar yarinya ta iya aiki,saidai nayi mamakin yadda take dakyau haka luba amma aiki take"
"Wallahi balaraba,halin rayuwa,amma banda haka bikisu ai tafi kyau da babban gida,nikaina wani lokaci nakan kalleta na qara,a haka ma wai don bata kwalliya,kullum haka dai zaki ganta cikin tsummokaran kayanta"
"Ma sha Allah,gaskiya Allah yayi mata baiwa,wannan kyanta tasamu wani babban gidan ko wani babban mutumin yayi wuf da ita" dariya umma luba tasaka
"Tunanina da naki ya zama daya,yanzun duk wannan kyan idan ba'ayi wasa ba saiya tafi a banza,saikiga wani qaramin yaron daga can cikin loko ya kwashi garabasa,bayan matar manya ce" qarasowar bilkisu wajen yakawo qarshen maganar tasu.


Batafi awa biyu ba baquwar tayi musu sallama tatafi,saiya zamana daga bilkisun sai umma luba,bakin umma luban baya shuru,bata taba iya zama haka,haka tadinga jan bilkisun da hira kamar yadda tasaba,yau kusan duka hirar tata kan yariman kaisa ne,maganganun afnan na daxu zuka dinga dawo mata,kusan maganganun saunyi daidai da nata,sam hirar bata wani bata sha'awa ba,ita da zatayi shuru da bakinta tabarta ma tayi tunanin yanayin da gidansu da rayuwarsu zasuci gaba da kasancewa da yafiye mata wannan hirar.


Gab da magariba tagama komai da komai,saita sanya hijabinta tana yiwa umma luban sallama
"A'ah,bazaki tsaya kici abincin ba?" Murmushi kawai tayi,umman tasanta da alkunya,wala'alla tanaso amma bazata iya tsaiwa ci ba,saboda haka tace mata
"Dauki kwano ki diba kyaci a gida".


☀ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸


Sanye yake cikin wata jibgegiyar rigar sanyi baqa wadda taqara mishi qiba sosai,saidai ta masa kyau ainun,an nata wani irin adon zane da jan zare wanda yasake qara mata qawa,abun mamakin duk sanyin daje busawa a wajen yasaki hular rigar baya,bayan kanshi babu komai sai gyararriyar sumarshi daketa qyalli.


Wandon jikinsa sosai yadace da rigar jikinsa,sai rufaffen takalmi hightop wanda yasake qawata adon nashi.


Shi dayane zaune saman table din,gabanshi kwalabe ne na lemuka guda uku da kofuna guda biyu,duk da cewa darene amma wajen tarwai yake da haske kamar kayar da allura kuma kasunkuya ka dauki abarka.


Kallo daya zakayi mishi kasam cewa ranshi a bace yake,yazuba lemon yasha shi kansa baisan adadin kofi nawa bane.


Kusan dukkan yarinyar dake wajen babu wadda bai dauki hankalinta ba,matane kala kala a wajen birjik nau'in yare daban daban,kama daga turawa larabawa 'yan africa da 'yan asia,saidai akwai wani babban abu dake hanasu qarasowa inda yake,kwarjini!,kwarjininsa yacika wajen gaba daya,hakanan ya dusasar da kyau da qasaitar duk wani namiji dake wajen.


Ajiyar zuciya tasauke mai nauyi tana duban wayenta guda biyu
"Friends....gaskiya banjin zan iya haqura dashi a yau,nayifa qoqari,watanni nawa ina faman boye mishi kaina,haqurina ya qare,ya kamata na bayyana mishi kaina,sonshi yayimin yawa a raina,kullum cikin mafarkinsa nake,ya kamata koyaya nashiga jikinsa" cewar wata farar budurwa ma'abociyar tsayi,saidai matuqar kana wajen zakayi mamakin jin yaren hausa na fita daga bakinta,saboda kallon farko idan akace ka yanke mata addini ko qabila ba zaka taba dangantata da qabila ko yaren hausa fulani ba,caraf takusa da ita ta riqe mata hannu
"Minal....kibi a hankali,bakisan waye prince ba shi yasa kike tunanin tunkararsa kanki tsaye" zame hannun nata tayi tana miqewa
"Na sani,nasan ba ordinary bane kamar sauran samari da muka sani,anyway zanje na tareshi yau komai ta fanjama fanjan,tunda shima mutum ne ai kamar kowa ko?" Tafada taba dage musu gira,sun fahimci me take nufi saboda haka suka sheqe da dariya gaba dayansu itama tana tayasu,kana tasoma takawa tana nufar inda yake zaune cikin wani salo da sauya tsarin tafiyarta.


Abun haushin shine harta isa baimaga tahowar tata ba,wannan karon harya miqe tsaye yana duban agogonshi bisa dukkan alamu tafiya zaiyi
"Hey!" Ta fada a hankali lokacin da take tsaye dab da bayanshi,a nutse yawaiwayo sai suka hada idanu,take murtikewar fuskarshi ta ninka yadda take ada
"Ina fatan ban matsawa prince ba ko?" Tafada tana jifanshi da wani shu'umin murmushi gamida dan kada jikinta cikin dabara,har yanzu dai dubanta yake ba tare daya amsa mata ba,hakan kuma ita yayi mata,saboda haka still tana murmushi tamiqa masa hannunta
"Am minal abdulhamid" hannun nata yabi da kallo wanda sukaci fixing na faratan 'yan kanti zaqo zaqo dasu,sa'an nan aka bisu da jan farce aka lullubesu dasu,sai qyalli suke zubawa.


Dauke idanunshi yayi yamaida cikin nata,wani kallo daya sanyata faduwar gaba,da kanta tasauke hannun nata ganin yana niyyar qagewa ba tare daya maida mata martanin gaisuwarta ba
"Kaman baka da interest da gaisawa da mata b....."
"Hey!" Yafada cikin kaushin murya
"Getout of my sight" yafada calmly kamar bamai bacin rai ba,murmushi tasaki itama kamar maganar tashi bata dameta ba
"Calm down yarima.....niba fada nazo muyi ba,nazo ne....."
Wani mugun tsaki yaja wanda har sai daya janyo hankalin mutanen dasuke daura dasu,dukka suka waiwayo suna dubansu,hannunshi yasanya yadauki wayarshi yasoma takawa don barin wajen.


Gaba daya sai taji ta muzanta yadda aka zuba mata idanu,har kamar ma sauti sautin dariya take jiyowa daga wani sashe na wajen,ranta taji ya sosu,cikin kunya da sagewar gwiwa tasoma tattaki don barin wajen itama,saboda yariga daya gama kunyatata har a gaban wadanda take daga musu kai,bataga sauran abun zama tayi ba kuma
"Batasan waye prince bane" sanda tazo gifta wasu 'yammata fararen fata

Please Login or Register in order to submit comment