Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya cika zaya maidata.


Kamar wanda akace daga kanka ya daga kanshi yana dan duban area din,yana son ganin ko samira ta fito?,saidai....maimakon yaga samira saiya hangi wata halitta daya jima yana neman inda take,wata halitta daya dade yana jin ita kadai ta dace da rayuwarsa,ita kadai ta dace ya aura,wanda a qalla shekara bakwai kenan da ganinta bai kuma sake sake ganin nata ba,shekaru bakwai baya a mexico.


Ba tare da dogon nazari ko tsinkaye ba ya cusa wayarshi a aljihu ya kuma tunkareta,zuciyarsa fari tas yana jin wata annashuwa
"Hey baby" maganar data firgitata jin sautin namiji dab da ita,ta waiwaya a razane,sai kuma taja baya da hanzari tana binsa da wani irin kallo,yayin da yake qare mata kallo zuciyarsa na sake tabbatar masa da cewa eh tabbas itace,saidai wannan ta hadu sosai,ta hadu fiye da shekarun baya,ta sake zama babba kuma cikakkiyar mace fiye ma da yadda yakeso
"Ya kike baby?....sunana....." Da sauri ta daga mishi hannu tana qarewa yanayinsa kallo dake nuna gogagge ne kuma mai budadden idanu
"Inajin kayi makuwa ne,bani kake nema ba" daga haka ta juya da hanzari,gabanta na faduwa tsoro na cikata ta wuce ciki.


Baiyi qasa a gwiwa ba ya bita,saidai kafin yakai har ta shige elevator,nan ya tsaya ya saki baki cikin takaici.


Ya sani koda yasan dakinta bashi da ikon zuwa har sai da ixininta,to amma babu wanda zai hanashi zaman jiran sake fitowarta,tunda dai yasan ba zata dawwama cikin dakin ba,daga nan zuwa safiya zuwa yammacin gobe dole ta sake fitowa,don haka saiya fita,ya samu samira na jiransa
"Munyi da wani abokina zaizo nan zamu tattauna kan business dinmu,don haka ga mota nan zata maidaki.makaranta zamuyi waya" tabe baki tayi tana dubanshi
"Amma dai ba haka mukayi dakai ba,sanda ka daukoni kana rawar qafa shine yanzu zakace na koma ni kadai?"tsawa ya daka mata wadda ta bata tsoro,dole ta rufe bakinta tayi shuru sannan tayi yadda yace din.


Gabanta na wani irin faduwa ta isa dakin,ta samu waje ta zauna tana rufe idanunta tare da sauraren bugun zuciyarta,wannan wacce iriyar tafiyace mara sa'a?,da wadanne irin mutane take gamuwa ne tunda tazo garin?,me yasa?,su waye saisu dinga binta haka?,tana wannan tunanin kiransu salwa ya shigo wayarta wanda shi ya katseta,ta bude idon nata tana amsa kiran
"Mun iso amma bamu ganki ba"
"Na sauko naga baku qaraso ba,na riga dana koma daki,banajin dadi ne sosai"
"Ayya yi xamanki,zamu samu wani cikin ma'aikata ya taimaka mana"
"Ok" kawai tace tana aje wayar sannan ta koma ta kwanta rub da ciki tana kiran sunayen Allah don gaba daya tunaninta a birkice yake.
7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 58
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070



Kusan awa guda kenan yana tsaye qofar shiga da fita na hotel din yana jiran ganinta,wayarshi na hannunsa,lokaci lokaci yakan maida kanshi ya danna na wasu sakanni sannan ya sake daga kanshi idan yaji qarar fita ko shigar wani abun hawan.


A irin hakanne motar da suke ciki ta durfafi gate din,yayi jinkirin daga kanshi wannan karon sai da suka kusa giftashi,a sannan idanunsa suka sauka kanta daga,tana zaune daga gefan hannun hagus saitin da yake,kafin yayi wani yunquri tuni sun harba titi,hakan ya sanya baiyi qasa a gwiwa ba shima ya tsaida taxi ya rufa musu baya don yana son cimmata a duk inda zata je.


A qalla azeez ya kusa shafe rabin sa'a a bakin dakin taron,duk bayan wasu mintuna saiya duba agogon hannunsa yana jiran lokacin zuwan nasu ya cika,dubawa ta qarshe agogon ya nuna masa nan da mintina biyar zasu iya isowa,hakan ya sakashi fitowa daga cikin hadaddiyar motar tasa,ya haye samanta ya zauna,ta saitin daya tabbaatr idan ta fito babu lallai ta ganshi,saidai shi yana iya ganinta.


Dukkan wata mota da zata shiga kota fita tana kan idanunsa,sanye yake da wasu baqaqen qananun kaya wadanda aka yiwa rigar manyan rubutun manyan haruffa da launin jaa,hakanan rufaffen takalmin qafarsa adon jiki gami da zaren jiki duka jaa ne,hatta da fuskarshi ya toshe qwayar idanunsa da baqin sun glasses,hannayenshi harde a qirjinsa,fuskar nan babu walwala ko misqala zarratin,sak ya fito a babban boss.


A hankali motar tayi parking daura sa tashi ba tare data kula da waye a wajen ba,itace qarshen fitowa saboda tsaiwa da tayi ta sallami me abun hawan,ta fito tana saqala jakarta kamar jiya hannunta riqe da takardu.


Cikin taku na nutsuwa ya sauko daga baya motar ya dosheta
"Assalamu alaikum,da fatan kin wayi gari lafiya" kalmar daya fada kenan saitin kunneta,wanda hakan ya sanyata zabura har takardun hannunta suna watsewa a wajen,kana ta juyo suka hada idanu,duk da cewa ita din bata iya ganin qwayar idanunsa,amma shinyana iya ganin tata,qwayar idon data masa wani mugun kyau,ta kuma yi tasiri cikin gangar jiki da zuciyarsa.


Baki ta bude da niyyar jefa masa magana amma sai ya rigata
"Kada kice komai,don tuni na soma haddace kalaman da kike jerantawa kullum kina bitar gayamin,idan kikace baki sanni ba inajin kamar kina kashene ni bilqees".


Lokacin da yakai qarshen kalamansa lokacin kamal ya iso,yasauka ya sallami mai motar kana ya juyo da niyyar tunkarar wajen,saidai me?,ga mamakinsa ita ya hango tsaye da yarima abdul'azeez din,abunda yaso yadan daure mishi kai,saidai kuma daya tuna saboda shi dama ya soma ganinta sai mamakin nasa ya ragu,amma abun tambayar dama har yanzu suna tare?,wacce irin alaqa ce haka mai girma tsakaninsu da tayi lasting har tsahon shekaru bakwai?,tambayar da yayiwa kansa kenan,yana dan sake matsawa kusa dasu gami da zuba musu idanu.


Harara bilkisu ta balla masa,saiya sake matsawa dab da ita yana son kashe duk wanu karsashi nata da kaifin idanuwansa,bayan ya zare glass din fuskarshi,har tana jin qamshin mayen turarensa sosai fiye da da.


Wannan matsawar ta darsa wani abu a zuciyar kamal,shawara ce kai tsaye daga wani sashe na zuciyarsa,wanda shawarar tayi masa dari bisa dari,tabbas idan ya aiwatar da abinda ranshi ke raya masa burinsu na shekara da shekaru zai cika cikin qanqanin lokaci,babu jinkiri ko kuma daga qafa cikin hanzari ya zaro wayarsa ya kuma shiga camera.


Ga bilkisu kuwa ganin yadda ya matse tazarar dake tsakaninsu sai kawai ta juya da sauri da niyyar barinsa a wajen,don bata jin zata iya ci gaba da tsaiwa dashi yana mata famin wasu sabbin al'amura da suka riga suka shude mata,duk da akwai burbushi cikin ranta,wanda dama shi ciwo ko rauni koda ya warke yakan bar gurbinsa jikin dan adam.


Caraf yayi yunqurin kama mayafinta,saidai maimakon haka sai yayi nasarar kama hannunta,tattausan singalalin hannunta ya ratsa tafin hannunsa,kamar yadda lallausan tafin hannunsa ta jiyo duminsa har cikin jijiyarta.


A fusace ta waiwayo tana watsa masa wani irin kallo
"Ka sakeni malam"
"Kiyi haquri,cikin girmamawa da lallashi kije muyi magana ta fahimtar juna ni dake"
"Idan naqi kuma fa?" Bai barta kalmar ta gama fita daga bakinta ba ya sunkuceta gaba daya ya nufi motarsa,abinda zuciyarsa ta jima tana gaya mishi daya aikata,abinda ya jima yana tunanun shibe mafita guda daya da zai kebe da ita,ya kuma bi hanyar data kamata don ta saurareshi.


Wannan daukar nata da yayi shinya qarawa kamal qaimin daukar hotunansu a hakan lokacin da take yunqurin kufcewa,saidai ingarman sadaukin yariman ya nuna mata qashun sam.ba daya bane,hakanan akwai banbanci mai girma tsakaninsu,yayin da su fadwa daje tsaye dan nesa kadan dasu suna kallonsu cike da sha'awa,saboda yadda sukaga sunyi matuqar yi musu kyau suka kidime gaba dayansu,ganin ya sanyata a mota gamida rufewa,ya kuma zagaya yana niyyar shiga sit dinsa,da sauri salwa tabar fadwa anan ta shuga ciki kiran dr adam,wanda ya rigasu yin gaba,hakanan babu yadda baiyi dasu su taho tare ba amma bilkisu taqi,ta gaya mishi ya riga yasan tsarinta ai tun bayau ba,tun a brasil.


Saidai fa dr adam yazo a makare,don ko qyallin motar yarima basu samu ba sai sawun tayar motar,fadwa ke shaida musu tuni ya wuce.


Tsaye sukayi cirko cirko cikin tashin hankali kowannensu,duk da cewa he's familia amma kuma basusan ina zaya kaita ba,kuma kusan a gaban idanunsu ya dauketa cikin qarfin tuwo ya sanyata a motar,hakan ke nuna ba tafiyar dadi bace kenan bare suce dason ranta akayita.


Hankalin dr adam ya sake tashi sanda fadwa ke gaya mishi daukanta yayi da hannunshi,tashin hankalinsa ya hadu ya cakudu da kishi mai tsanani,har baisan ya rufe su fadwan da fada ba kamar ma sune yariman,saiya fidda wayarshi ya soma jera mata kira babu qaqqautawa.


Sosai take mishi hayaniya da masifa cikin motar,ranta a matuqar bace ganin yadda ya maidata kamar wata 'yar tsana,hakanan ya zubda mata mutuncinta da qimarta a idanun mutanen da suke ganin girmanta.


Idan set din da suke kai ya tanka to yarima ya tankata,yasan kome zata fada yana fita ne tare da zafi da qunar dake cikin ranta,maganganun da take fada tamkar tana samun wani dan qaramin sauqi ne cikin zuciyarta,shi yasa ya zabi yayi shuru,ta fadi dukkan abinda takeson fadar,matuqar hakan zai sama mata salama cikin ruhinta.


Tafiyar minti arba'in har suka iso masaukinsa batayi shuru ba,iya gajiya bakinta ya gaji,wanda isowarsu wajen ya sanyata dole yin shuru.


"Ranki ya dade sauka muje" ya fada a tausashe cikin nuna girmamawa,da idanu takebin wajen da kallo,akwai jama'a nata kai kawo kowa yana sabgar gabanshi,saita dauke kanta gami da jan wani dogon tsaki
"Ba zani ko ina ba....ka mayar dani inda ka daukoni"kai ya girgiza cikin matuqar rauni
"Kiyi haquri,amma bazan iya maidake ba,inason kasancewa dake,inason inasan ina diyata take,yaya ta rayu ke da ita tsahon wadan nan shekarun?"
"Zamu shekara anan kenan" ta sake fada a harzuqe,kai ya girgiza
"Ba zamu shekara ba,saidai xan daukeki da hannuwana kamar daxun zuwa ciki,inda zamufi tattaunawa cikin nutsuwa" ya fada yana cire sit belt din dake daure dashi,da alama yana shirin daukar nata kamar yadda yace kenan.
"Idan ka daukeni zan maka ihu,in kuma gayawa duniya satoni kayi" murmushin gefan baki da yayi masifar qara masa kyau da kwarjini yayi
"Ko zaki shekara kina fada babu mai yadda dake...."
"Saboda kana taqama kaidin me arziqi ne?,kana da madafan iko da sarauta,kana da dukiya,Ka siye kowa?....ni kuwa talaka ce ba diyar kowa ba?" Ta jefeshi da tambayar cikin katsar numfashinsa ba tare data bari yakai qarshen maganarsa ba.


Qaramin murmushin ya kuma saki ba tare daya shirya ba,duk da kalamanta qona masa zuciyasa sukayi,yasan ta fadi daya daga cikin abinda ke damunta ne a zuciya,kai ya kada
"Ba wannan ba,ke zakiso duniya ta kira uban 'yarki da barawon mutane?" Sai kalmar tayi mata gingirin aka,ta kuma sake maimaita cikin zuciyarta,take fuskar amatu ta dawo cikin idanunta,sai taga kamar amatun ce a gabanta sanda ta fuskarshi,bai sake cewa komai ba ya sanya kai ya fice.


Har ya bude qofar tayi hanzarin ce masa
"Dakata!,kada ka soma tabani" saiya tsaya din kamar yadda tace ya goye hannuwansa a qirji yana kallonta,murmushi da baisan dashi ba yana subucewa daga fuskarshi.


Banzar harara ta jefa masa,bayan tayi kamar ba zata fito din ba,sannna taja qafafunta ta fito tana jan dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta.


Tunda ta shiga kanta yana a qasa,duk yadda yakai gason tayi magana amma bata daga kai ta dubeshi ba bare tace mishi uffan,tsahon wani lokaci haka ya tashi ya miqe ya barta,babu jimawa ya soma jere mata kayan motsa bakinkala daban daban.


Wani irin bacin raine ya cikata,me yake nufi?,an gaya mishi yunwa ce ta kawota ko mene ne?,ji tayi ba zata iya shuru ba tare data tanka mishi ba
"Ka maidani inda ka daukoni,don bance maka yunwa nakeji ba bare ka jere min wadan nan kayan a gabana" ta fada cikin matuqar hade rai,murmushi ya sakar mata yana jifanta da wani irin kallo
"Baqonka abun girmamawa ne a wajenka,duk da cewa kinqi cewa komai dani kinqi bani hadin kai....ko meye nayi miki a rayuwa babu abinda zai sanya ki fahimceni,idan na miki dai dai ko akasin haka,da gangan na miki ko ba cikin sanina bane sai zama mu tattauna,karki manta zuri'a ta shiga tsakaninmu,dole mu nemi makomarta,wanda bazai taba yiwuwa ace mace tayi ciki ita kadai ta haifa ba ba tare da uba ba,kiyi tunani,akwai wata rana da zata zo zata buqaceni,zata buqaceni koda baki so,zata buqaci sanin waye ni,zan baki mintina kiyi tunani akai"saiya miqe yana juyawa
"Bana buqatar yin wani tunani akan komai,na jima ina tunani akai,hakanan qwaqwalwata ta dade tanayin tunanika wadanda suka jima da gajiyar da ita,ta nemi hutu hutu irin na har abada,don haka bata buqatar yin tunani kan ire irenku da matsalar daya shafeku" murmushi kawai ya juyo ya jefeta dashi kana yayi gaba zuwa uwar dakin dake manne da falon,yayin da ita kuma ya bishi da harara,tana ganin baiken kanta da bata gwada ma yi masa ihun ba tun a can,komai ta fanjama fanjam.


Yana shiga dakin ya tura qofar yana dafe goshinsa gami da sauke numfashi,ba shakka ba qaramar badaqala bace a gabanshi,amma duk yana ganin komai zaizo masa da sauqi matuqar zata dinga tsaiwa tana saurarensa,koda ba zaga amsashi ba kamar yadda tayi masa yanzun.


Numfashi ya furzar mai dumi daga bakinsa,ya soma takawa zuwa cikin dakin,dai dai nan wayarshi tayi tsuwwa,ya zarota a kasalance yana duba mai kiran,fulani ce,don haka cikin girmamawa ya daga wayar yana karawa a kunnanshi.


A ladabce ya gaidata,sannan ta isar da saqon da takeson isarwa din
"Wai sai yaushe zaka dawo ne?,cikin satin sama upper week za'a gabatar da hawan daba na al'ada fa,kowa da kowa zaizo,dukkan wani wanda yake jinin masarautar kaisa ne wannan karon zai halatta,harda wadanda basa a qasar,kasan kuma kusan shekara biyu rabonka da zuwa,ya kamata a wannan karon ka halarta,saboda inason koda yaushe ka dinga zama a hannun daman mai martaba,saboda shekaru suna sake turawa,ya kamata ace ana ganinka a dukka al'amuransa,tunda bashi da kamar yakai"
"Inason nima na dawo,saidai uzurin da nakeyi din ne yanzu ma na fara bare ayi maganar kammalashi"
"Wanne irin uzurine haka?" Kanshi yadan shafa yana duban qofar falon daya barta
"Kidai tayani da addu'a ammi" ga zatonta sha'ani ne daya shafi harkar business dinsa,wanda indai ta fannin ci gaban da daukakar da yake samune kulli yaumin hakan na mata dadi,saidai kuma ta wani fannin tana da damuwa sosai akanshi yariman,akwai abubuwa da yawa na rayuwarshi da take ganin bai dace da ra'ayinta ba,kamar yadda yake wofintar da matarsa da lamuranta,bai fiya damuwa da sha'aninta sosai ba,yadda yake jimawa bai waiwayi masarauta ba,bare abokan adawa su dinga yawan ganinsa,suna kuma tunawa da matsayinsa tare da tunasar da kanau cewa wataran akwai mai amsar sarauta,wataran zata amsa sunan 'yar sarki jikar sarki matar sarki kuma uwar sarki,amma tana ganin tunda har ya cika mata dukkan buri da wani sharadi data kafa masa,ya kamata ta qyaleshi hakanan kuma yayi rayuwarshi yadda yakeso shima,akwai lokacin da komai zai daidaita,akwai lokacin da zai canza wasu abubuwan a qashin kanshi
"Shikenan,Allah yayi jagora"
"Amin summa amin,godiya nake" daga haka ta sauke wayar tana sakin ajiyar zuciya.


Tana daga kai suka hada idanu da afnan,saita dan tsareta da idanu kamar yadda ta fahimci itama tun dazun ita take kallo,ta rasa dalilin sauyawar afnan din tun dawowarsu daga brasil
"Lafiya kike?" Ammin ta tambayeta tana kallonta,saita dauke kanta ta maida kan wani qaramin littafi dake hannunta,a son ranta mama sodangi ta barta tayima ammin magana,kullum idan ta tuna da abun sai taji zuciyarta na azalzalarta ta tari ammi da maganar,amma mama sodangi ta gaya mata akwai lokaci,yin maganar a yanzun ta hangi babu abinda zai haifar sai tabarbarewar al'amuran da suke saka ran gyaruwarsu.


"Babu komai....kawai,ina tunanin,anya ba wani abu wanda ba dai dai muka aikata ba Allah ya jinkirta min aure na?" Ta qarashe maganar tana zube idanunta kan ammi fulani.


Hakanan taji maganar banbarakwai,ta kuma rasa muhallin da zata aje maganar,cikin rashin fahimta tace
"Kamar yaya afnan?,me kike nufi?" Wani murmushi mara ma'ana tayi tana kada kai
"Babu komai,kawai inajin hakanne cikin raina,ban sani ba koba dai dai bane" shuru ne ya ratsa tsakaninsu cikin falon,ta saka ammin cikin tunani,wanda kafin ta fita ita kuma ta miqe da litattafanta ta wuce ciki,hakanan sai ammin ta bita da kallo harta bacewa ganinta.


Ita daya tasaki nannauyar ajiyar zuciya,sai mafarkin da tayi jiya ya fado mata,mafarkin yarinyar sosai,yadda ta bugeta a asibitin kuma taci gaba da tafiyarta,abinda ta sake gani kenan,saidai wannan karon ta tsaya ta kalleta sosai a cikin mafarkin kafin tayi gaban abinta,idanunta ta rufe tana girgiza kai,tafi zargin saka abun da tayi cikin ranta ne shi ya sanyata mafarkinta a jiyan,ko kuma kewar suhaima ce.


*_KAMAL_*


Saboda tsabar zumudi bai iya bari ya isa gida ba ya koma cikin motarshi ya zauna sosai,sannan ya bude data dinsa bayan yahau watsapp ya tura dukka hotunan wa hajiya fauziyya mahaifiyarsa,kana ya sauka ya lalubi lambarta ya kirata.


Sai data kusa tsinkewa sannan ta daga,zuwa lokacin har ya qagu
"Wai ina kika shiga ne mom?"
"Baqi gareni ban lura da kiran naka ba,saida husna ta miqo min.....ya akayi?"
"Babbar jarida zan siyar miki...sa'annan babbar nasara dake alamta mana cikar burinmu nan da wasu 'yan kwanaki" baki ta tabe
"Nina yanke qauna dakai kamal,tunda har yau burinmu na shekara bakwai ka kasa cika mana shi,bayan mun sanya dukka burinmu da fatanmu saman wuyanka" wata banzar dariya ya saki sa'anan yace
"Idan nace miki nan da sati daya burinki na farko zai soma cika kafin zuwan na biyu zaki yarda?" Kai ta girgiza cikin nuna rashin tabbas
"Wai kana nufin bacin sunan yarima a duniya da kuma masarauta gaba daya?,kai anya kuwa,abun da kamar wuya,mutumin daya wuce saninmu a yanzu,ka kasa komai a sanda yake da qananun shekaru kuma shidin ba kowa bane a idanun duniya bare yanzu?"
"Wait mom....jeki watsapp dinki,amma da zarar kin kammala duban saqon...ina da buqatar jin alert na kudade masu nauyi a accnt dina kafin mu dora daga inda muka tsaya" tsaki taja
"Da gaske kamal lalacewa kakeson yi,banda haka duka duka yaushe mahaifinka ya tura maka kudade masu yawa?"
"Mom...wai kamata ta yaya bazan buqaci kudi ba,komai nawa fa saida kudi nake iya tafiyar dashi"
"Kamar wani ya hanaka tsaida hankalinka ka kammala karatunka,koka kama kasuwancin babanka da kyau,ba irin yadda kake riqon sakainar kashi dashi ba a yanzu"
"Yanzu mom na faranta miki amma zaki sakamin da haka?" Tuna batun da sukeyi ne ya sanyata cewa
"Sorry son,bari na duba" daga haka ta katse wayar,sai shima ya kashe tashi yana qunquni gami da kumbura,ya aje wayar gefe yana zaman jiran ji daga gareta.


A hankali sai kuma yaji kamar bai kyautawa bilkisu ba idan ya bari fuskarta ta bayyana a idanun jama'ar masarautar a matsayin wata lalatacciya mai mummunan aiki,amma saidai kuma.....babu wata hanya data rage masa wadda zai iya samunta ta ruwan sanyi a amatsayin matarsa saita hakan,saboda kallo daya ya yiwa idanun yarima ya karanci wata iriyar soyayya mai kaifi da yakewa yarinyar,wanda da alama shidin baisan tana fita daga idanun nashi ba....da wannan tunanin ya kwantar da kujerarsa yana jiran kira ko saqon kudi daga mom din tasa haj fauziyya.....
7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 59
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070


Tun kafin ta gama ganin hotunan ta miqe tsaye cike da zallar farinciki,haqiqa ba shakka lokaci yayi,lakaci yayi na tarwatsa fulani da iyalanta,lokacin da zasu soma cimma burinsu kan sarautar qasar kaisa yazo,irin hotunan da sukeso,irin hotunan da suke da buqata,wadanda komai bincike idan za'ayi zai tabbatar da cewa na gaske ne,ba hadin computer ba.


Batayi wani jinkiri ba bayan ta gama bin hotunan daya bayan daya da gaggawa ta kira kamal,shima baiyi jinkirin dagawa ba,tunda abinda yake jira dama kenan
"Haqiqa lokaci yayi,kayi qoqari sosai kamal,kayi qoqari ba kadan ba,duk da naso ace sunfi haka muni amma hakanma babu laifi,yanzu meye abu na gaba?,ta yaya za'ayi hotunan su shigo masarauta?"
"Kudina tukunna mom"
"Dalla can mayen kudi kawai,dan banzan yaro mai idanun cin naira,zan tura maka 100k"
"Kacal?"
"Au kacal ne ma?,kana zaune babu cas babu as ka samu 100k amma ka raina"
"Amma mom wannan ba aiki nayi ba?"
"Aikin da zaka fi kowa farinciki dashi ba,duk badon kai nake komai ba?,idan komai yayi daidai waye zai haye karagar?"
"Oh yeah,naji shikenan"
"Yauwa"
"Yanzu mom,hotunan ya kamata ne ace an wankosu da yawa,an kuma zuzzubar ko ina lungu da saqo na masarautar,yadda kowa zai samu gani"
"Hakane....amma so muke su isa gaban idanun ubanshi,kasan yadda jamar masarautar ke qaunar abdallah,za'a iya qin kai masa saboda kada ranshi ya baci....amma na tuna wata dabara....adama,ita ya kamata ta miqa hotunan zuwa gareshi,don banason aga fuskarsa a wajen,bare sunanka ya baci nan gaba,kafin lokacin da itama adaman aiki zai biyo ta kanta"
"Good,saiku qarasa tsara yadda za'ayi,nidai naji alert"
"Naji ubana.....inajin aikin nan lokaci mafi dacewa da farashi shine,lokacin babban hawan daba na qasar kaisa,lokacin da baqi zasu cika gidan,yadda maganar zatafi fantsama lungu da saqo na qasar kaisan.....inason ka halarci hawan kaima"
"Zanzo" ya bata amsa don akwai sabuwar yarinyarshi da yayi a katsina,dama yanason zuwa su hadu,da wannan mummunan shiri da qullin sukayi sallama kowa ya aje wayarsa cike da farinciki,saidai haj fauziyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,sai data lalubi adama don ta mata albishir.


Duk da ba cikin yanayin take ba amma hakan bai hana idanunta bin falon da take a zaune da kallo ba,tunda take bata taba ganin dakin hotel mai kyau da tsaruwa irin wannan ba,idan kana ciki ba zaka tsammaci cewa a hotel kake ba,saidai daga ganin yanayin yadda yake sake sosai a wajen dakin ya zamar masa kamar nasa ne,irin abin nan da masu hannu da shuni kanyi,su riqe daki ya zama na saukarsu ne duk sanda suka sauka a qasar,koda basu nan ba za'a sanya musu kowa ciki ba,saidai fa suma zasu dinga biyan kudi kamar suna kwana.


Abinda yasa ta gane hakan,qananun frames frames dake maqale a bango,wadanda sukafi kama da abun award,shaidar girmamawa da akan baiwa mutum sun kusa guda goma.


Janye idanunta tayi a hankali tana jan tsaki,wanda yayi dai dai da fitowar yariman daga daki,sarai yaji tsakin amma sai yayi kamar baiji din ba.


Wannan karon sanye yake jallabiyya mai azabar kyau da taushi,wadda duba daya zaka mata kasan kudinta ba kadan bane,yadda take da kyau haka tayi masa wani azababben kyau,ta fidda kyanshi mai sanyin nan da tafi da zukatan mata da yawa.


Ganin ya nufi qofa yana shirin fita ya sanyata miqewa da hanzari tana fadin
"Malam dakata...bafa kaya ka ajjiye ba"
"Tunda muka hadu dake bilqees kike kirana da malam,kin manta sunan mijinki kuma uban 'ya'yanki?,abdul'azeez abdallah,idan kin manta kuma ba laifi kina iya kirana da abban baby" ya bata amsa yana riqe da handle din qofar,yayin da take nufo qofar da sauri tana son cimmasa ta samu nasarar fita,saidai kafin ta qaraso yaja qofar ya rufe.


Koda ta isa taja sosai taqi koda motsi bare batun buduwa,hakan na nufin kulleta yayi kenan?,bacin rai

Please Login or Register in order to submit comment