Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

alhaji" yatsanshi ya ciza yana kada kai
"Kumafa wallahi kin kawo shawara lami,dadina dake hankali,kinga waccar dosoruwar bata taba bani irin wannan shawarar ba wallahi,to amma yanzu ai tunda takusa gamawa kudin da sukayi sauran basu taka kara sun karya ba....".


Miqewa kawai bilkisu tayi ba tare data tsaya ta qarasa jin cecekucen dasuke ba,ta sanya takalmanta tafice daga gidan tanajin iska na yawo da ita.


Tana tafe a hanya amma sam hankalinta baya tattare da abunda ke gudana kan hanyar,tayi matuqar nisa a duniyar tunani,wani irin quntata zuciyarta tayi,tanajin hucin hakan har saman fuskarta,kukan zuci take mai ciwo,wanda yafi na fili radadi da yankar zuciya,tana jajantawa yara da yawa cikin fadin duniya masu mahaifi irin nata,tayi amanna marayu da yawa sun fisu gata,marayu da yawa sun fisu daraja da kima,ya ilahi mahaifinsu meya hau kanshi haka?,Allah yayi masa daraja da baiwar 'ya'ya amma shi baisan da hakan ba,meye marabarsa da matacce?,wanne abu zasu iya adarwa kan gata da wani abu mai muhimmanci da uba ya yiwa 'ya'yansa,dame zasuyi tutiya?,da ire iren wadan nan tunanukan ta qarasa gidan umma luba.


Taje ta sameta a hargitse da tulin hirarta,bakinta har kunne yau Allah ya yarda zata daga daga qasar nijeria masarautar kaisa zuwa mazako,duk da yanayin da take ciki hakan bai hana murmushi subucewa daga fuskar bilkisun ba,na yadda tafadi sunan qasar,dakuma yadda taketa lodar kaya kamar zata ta shekara a can
"Mexico ake cewa umma....sannan wadan na kayan da kika diba ai sunyi yawa,idan zaka wata qasar ba kaya kake loda ba,idan sati biyu zakuyi kala bakwai ma ya isheki" baki tasaki tana kallon bilkisu
"Ke 'yar nan,tafiya cefa ta alfarma,ga qafata ga qafar fulani fa,a qalla muyi sati biyu ko uku" murmushi takuma yi
"Duk da haka umma"
"To yo ai gwara da kikazo,don ni niyyata iya adadin kwanakin zan diba harda qari ma,matso ki zabarmin" tafada tana bata waje.


Anutse ta shirya mata komai,hakan kuma yayi mata dadi har tace
"Bude store dina ki daukar muku taliya goma,macaroni goma,shinkafa kwano biyu,samambita yakusa qarewa dauke ragowar kwa dafa kuci keda qannenki" sosai hakan yayiwa bilkisu dadi,tasan da yardar Allah bazasu galabaita ba sosai.


☀ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸


*_MEXICO CITY_*



Tsaye takan gaba gadon da aka kwantar dashi,hannayenta saman kanshi idanunta qur akan fuskarsa,kana ganinsa kasan cewa lallai da gaske bashi da lafiya sosai,har cikin zuciyarta takejin ciwon nashi tamkar ita dince babu lafiya,sakin ajiyar zuciya tayi tana sauke hannun nata daga saman kanshi kana ta juya a hankali tafice daga dakin zuwa office din likitan don suyi magana,tana son jin cikakken bayanin abinda yake damun azeez din.


Dukka hankalinta yana kan likitan lokacin dayake rubuce rubuce jikin file din azeez,harya gama kana ya daga kai cikin harshen mutanen qasar mexico yasoma mata magana,saita sauya harshe zuwa turanci
"Am sorry" ya fada yana murmushi,don shaf ya mance da cewa ba 'yar qasar bace,saiya koma mata bayani zuwa yaren englishi
"A yanayin halittar yaronki a bincinkenmu mutum ne mai matuqar buqata,wanda baya biyan buqatarsa takowacce hanya dazai rage yawan ruwan halittar dake taruwar mishi,a maimakon hakan saiyake amfani da wasu qwayoyi da zasu gusar masa da dukkan wata sha'awa da zata taso mishi,wanda sannu a hankali suka zame mishi jiki suka bi jikinsa,har aka kai matakin da basa iya mishi aiki sosai a jikinsa,saiya koma yin allurar da ake ta jijiya,wadda tafi qwayoyin saurin isa inda akeso.....to,bayan hakan gaba daya,bamu sani ba tunda bama tare dashi,amma a shekaran jiya an kawoshi ranga ranga,mun karbeshi mun kuma bashi taimakon gaggawa,wanda daga qarshe bincikenmu ya tabbatar mana da cewa yasha maganin ne daya wuce qa'ida,wanda har hakan yanaso ya masa illar,illar da idan ba aure yayi ba to komai zai iya faruwa dashi".


Shuru yayi yana maida numfashi,cak tunanin fulani aysha ya tsaya,don ko kusa ko alama bata taba kawowa kanta wannan ba cikin jerin abubuwan daka iya zama sila ko sanadi na ciwon azeez din ba,mganar likita tasake katse mata tunaninta
"Saboda an kai matakin da magungunan sun daina aiki a jikinsa,banda ma yana da qarfin jini da tuni sun kashe masa sha'awarsa gaba daya,a yanzu kuwa idan yaci gaba da shansu komai yana faruwa dashi" saita lumshe idanunta tana jin maganganun likita na sauka É—ai É—ai cikin kwanyarta
"Godiya muke likita" ta fada a taqaice tana miqewa a nutse tabar office din.


Duk da sunyi waya maimartaba amma bata shaida masa asalin ciwon dake damun azeez din ba,kamar yadda take da yaqinin daga ita sai abdulrashid suke da masaniyar haqiqanin abinda yake damunsa da abinda yayi silar shigarsa cikin ciwon,ta fannin abdulrashid sam baiyi mamaki ba,duk da cewa ba qasa daya suke karatu ba amma yasan azeez din na yawan ta'ammali da magungunan duk sanda lamura suka ci tura,don yana yawaita zuwa wajensa akai akai musamman qarshen mako,kamar yadda shima azeez din yakan ziyarceshi duk lokacin daya bushi iska.


Duk da cewa su abdulrashid din suna tsaye a kanshi amma kasa tafiya tayi masauki anan dakin da aka kwantar da azeez din ta kwana,duk motsi ko wani juyi da zatayi idanunta na kanshi tana tunanin mafitar daya kamata ta sama mishi mafi sauqi kuma cikin sirri.


Cikin dare yafarka sau daya,suka hada idanu yasaki murmushi,yana tason ya mata magana bacci yasake rinjayarsa,bai sake farkawa bai sai washegari da asuba.


Sati guda cif ya kwashe cikin yanayi na jiyya kafin yasoma watstsakewa,a kwana na goma kuma ya watstsake sarai,har zuwa sannan bata nuna mishi tasan komai game da ciwon nashi ba,hakanan basuyi magana dashi ba,saima ticket data siya musu na tafiya qasar mali,wanda ta diba musu zasuje suyi sati biyu a can,badon komai tayi wannan tunanin ba,tayi hakanne don zuwa ta shawarta da makusanciyarta abokiyar shawararta kan lamarin azeez din,don batason ta koma kaisa ba tare da wata qwaqwqwarar mafita ba da zata zama maslaha ga rayuwarshi.


A sannan saida ya kwana uku kamal yaje dubashi,da sunan cewa baya garin da suke makaranta sun turashi wani bincike kan course din da yake a wani gari daban,tunda yashigo azeez din ya kafeshi da ido,hakanan yaji ya dora alamun tambaya a kanshi,duk da cewa bai dora dukkanin zarginsa da zato akan kamal din ba,amma haka kawai yanayin daya nuna yakejin bai masa ba.

*****************


Karfe goma da rabine na safiyar ranar talata,cikin falon alfarma dake babban sashe da aka tanadarwa fulani aisha cikin masarautar qasar malin wadda take qarqashin sarauta da jagorancin mahaifinta.


Duk da cewa tayi rashi na uwa amma hakan sai bai sauya komai game da gata dakuma qimarta cikin gidan na,matan uban suna mata kallo ne irin wanda sukewa 'ya'yansu.


Su biyune tak cikin falon,tunda sukazo anan tasauka ita da azeez din,saidai akwai tazara sosai tsakanin dakinshi da nata,yayin da 'yan rakiyarta suma suke wani sashe na musamman maicin gashin kanshi.


A gaban fulani saratun yake zaune saman lallausan carfet da yayiwa falon qawanya,yana sanye da wando wanda yawuce qaurinsa da kadan bai kuma kai har can qasa ba,farine tas sai rigar jikinsa wadda ta kasance ruwan toka me haske.


Farfesun kayan ciki yake sha a hankali da cokali,kana dubanshi kasan yasamu lafiya dakuma cikakken nutsuwa,yayin da fulani aysha ke jefa yankkiyar kankana a bakinta duk da cewa safiya ce.


Duk wani motsinsa yana kan idanunta har zuwa sanda tagama shan tata kankanar ta aje cokalin da farantin,tazauna sosai cikin wani salo dake karantar damai kallo tsantsar izza da isar mulki dake yawo a jininta.


Tafin hannayenta ta hade waje guda kamar yadda tashigar da yatsunta cikin na juna, anutse ta furta
"Me yasa ka yanke shan qwayoyin da zasu iya kassara maka rayuwarka ta d'a namiji har abada azeez?" A bazata tambayar tazo masa,don bai taba tsammanin maganar ta isa kunnenta ba,da yaji shuru yayi zaton likitan ya saya komai ne,saboda haka saiya nemi ya qware da da romon farfesun,har sai daya aje bowl din hannunshi,ya nemi ruwa ya kwankwada sarai sannan yaji dama dama,ya aje gorar ruwan yana maida numfashi,gami da tattaro irin amsar da zai bata saman harshensa.


Ya daga idanunsa a hankali ya motsa bakinsa da zummar yin magana
"Dakata....bana buqatar kalaman kariya daga bakinka,ka kasa jurewa azeez,ka gaza ka daure ka isa ga matakin da nakeso ka isa a duniya.....,ba yadda zanyi dakai,nawa shine inyi iya abinda zan iya,sauran naka ne,tunda rayuwarka ne,dole saida gudunmawarka komai zai gudana yakuma tafi dai dai yadda ni da nake gefe na tsara maka" bashi data cewa sam,tunda komai yariga ya bayyanar mata,sai yayi shuru yana saurarenta kawai,idanunsa saman kofunan da suka yi amfani dasu yanzu.


"A matsayin da kake kai yanzu,dole ne a matsayina na uwa na sama maka mafita ta dukkan hanyar da zata kasance mafitar ce a wajenka....." Sai tayi shuru da alama magana mai muhimmanci zata fada,yayin da abdul'azeez yayi shuru yanajin wani sanyi yana ratsashi tun daga saman kanshi zuwa qafafunsa,wani nauyi na raguwa daga qirjinsa,fata sa kawai shine kunnuwansa su jiye masa kalaman amincewar ammi na yarjewarta kan yaje yayi aure
"Zakayi aure abdul'azeez" shuru tasake tana qara tariyo dukkan abinda suka tattauna da shawarar data bata cikin daren jiya,wanda taji ta gamsu da shawarar dari bisa dari,wata qaqqarfar ajiyar zuciya yasauke,wani munafukin qaramin murmushi nasan ratsowa ta saman miskilar fuskarsa ya bayyana kansa,saidai ya hana hakan faruwa,sai taci gaba da cewa
"Zakayi aure amma ba irin auren dana tanadar maka ba,zakayi aure amma AUREN KASHE GOBARA".


Da sauri yabude idanunsa fes kan ammin don bai fahimci abinda take fada ba,sam bai fahimci hausarta ta qarshe ba,yaci gaba da kallonta kamar yadda itama take kallonshi,tasan cewa yashiga duhu ne kuma yake da buqatar qarin bayani,tasan kuma dama zai buqaci hakan.


Sake gyara zamanta tayi tana sakin ajiyar zuciya,itama idanunta a kanshi tace
"Zakayi aure abdul'azeez kamar yadda buqatar hakan tataso,saidai ba safwa zaka aura ba a halin yanzu ba" kadan fuskarsa tasauya saboda ta sake jefashi cikin duhune,maimakon yafita zuwa haske saiya sake shigewa cikin duhun
"Eh,a yanzun zan aura maka yarinyar da xaka zauna da itane iya tsahon adadin zaman rayuwar karatunka harka kammala,sannan daga bisani zaka auri safwa a lokacin da muka tsara ni da mahaifiyarta,irin auren da nake buqata,irin auren da mukayi tanadi dakuma buri,ina fatan ka fahimci abinda nake nufi?".


Gaba daya sai komai yazo mishi a baibai,dukka bayananta suka cunkushe mishi waje daya,kamar ya fahimta abinda take fada wani sashe kuma sai yakejin kamar bai fahimta ba,ya hadiye yawun bakinsa da qyar yana duban ammin,yamotsa bakinsa zaiyi magana ta daga mishi hannu tana miqewa
"Ba shawararka nake nema ba,wannan shine kawai mafita azeez,no way face mubi wannan,so kawai abinda yarage shine kajira,zan shiga ciki wajen maimartaba..." Daga haka tasoma takawa tafice daga falon.


Wani zazzafar iska yafitar daga bakinsa ya nutsa dukka yatsunsa cikin sumar kanshi yana yamutsawa,kanshi na wani irin yamutsawa.


Me yake shirin faruwa ne?,saiya miqe ya koma saman kujera yakwantar da bayansa sosai a makarar kujerar yana ci gaba da barin idanunshi a rufe,sarrafa maganganun ammi yake yadda zasuyi daidai da qwaqwalwarsa da kuma tunaninsa
"Auren kwangila?,ko auren yarjejeniya?,ko kuma me?" Yadinga maimaita tambayar kansa shi daya cikin makeken falon.
7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: *S R B*

16

*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,gamai buqatar mallakar nashi saiya tuntubi wadan nan numbers din_*

0903 234 5899
Ko
09033181070
_______________________________

*Ina mata 'yan birni 'yan qwalisa masu burin sanyaya gidansu da daddaɗan ƙamshi mai tsayawa a zuciya da ruhin maigida?,shin kina da labarin ANNUR PERFUMES?,wadanda bayan sun gyara miki waje da ƙamshi su kuma gara miki ciki da kayan matsi?sannan su rabaki da infection?,WOHOHO wani kaya sai amale,ANNUR PERFUMES sun shara wajen saida*

*HADADDIYAR HUMRA*
*KWALACTURE*
*TURAREN WUTA*
*MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)*
*DECORATIONS NA TSINTSIYA*

*_UWAR GIDA DA AMARE KUZO GA NAKU_*

*_MAZA GARZAYA GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!_*

*KO A NEMESU TA LAMBOBIN WAYA KAMAR HAKA*

07086341096 ko 07069037534

_muna maraba da masu siyan ɗai ɗai ko sari_🤗🤗

*INGANCI KYAU RAHUSA DA KUMA INGANCI SAI ANNUR PERFUMES*👃ðŸ½
________________________________

16



Kusan ranar wuni yayi shi kadai a sashen da aka saukeshi yana son daidaita tunaninsa da maganar,yanason aunata kan ma'auni da mizanin dacewar hakan ko rashin dacewar hakan,dukkan wasu 'yan uwa dakeson ganinsa dayi masa sannu babu wanda ya baiwa damar ganinsa,ya zabi zaman shi kadai wuni guda sur.


Sai daga bisani ys tabbatar da cewa yana buqatar abokin shawara,waye a ciki?,sufyan ko abdulrashid?,daga qarshe yaji zuciyarsa tafi amincewa da kiran abdulrashid din,shi tuni yakoma kwana biyu da zuwansu mali.


A iyakacin abincin da aka jera masa babu abinda ya iya sha sai tattacen gamayyar ruwan kayan marmari,bayan sallar isha'i yasamu yakira abdulrashid din.


Cikin nutsuwa da aminci ya fayyace masa duk abinda ake ciki,bayan shuru na wasu 'yan mintina kana yace
"Abdul'azeez,a rashin uwa akanyi uwar daki,babu wata hanya ko mafita data rage banda ka karbi wannan tsarin,tunda kana da yaqinin cewa matuqar akaci gaba da tafiya kan wannan tafarkin komai zai iya faruwa,ina ganin kawai ka bada dama shine"
"Amma....abdulrashid,mai martaba fa baisani ba bazai kuma sani ba a tsari na ammi" shuru yasake yi yana jinjina kai
"Matuqar yasani din kaima kasan dukka hakan ba zata taba faruwa da amincewarsa ba" shuuru kowannensu yasake yi kana daga bisani yayiwa abdulrashid din sallama saboda har yanzu yana da buqatar kadaici har zuwa yanzu.

***************

Ko cikin gidan kebantaccen wajene da babu wanda ke shigarsa sai an lamunce maka.


Fulani aysha ce zaune saman daya daga cikin kujerun dake wajen,hannunta riqe da wayarta,da alamu magana take mai matuqar muhimmanci,don ta bada dukkan hankalinta ga wayar.


Bayan tagama sauraran dukkanin bayanin aminiyartata saita sauke ajiyar zuciya
"Amma inda nake ganin matsalar take saudat.....inda zan samu yarinyar da zata dace da ra'ayin azeez,kinfi kowa sanin halayyar yaronki,donko safwa ma ke zaki bawa wani labarin yadda aka qarke,inason komai yazama cikin sirri,inason yazama tamkar auren sirri tun daga qullashi har zuwa sanda zai qare,kin sani sarai muna tsakiyar magauta da abokan adawa,kowanne yazuba idanu yana son ganin bullar wani abu da zai riqa wajen bata rayuwa da duk wani ci gaba da daukakarmu".


Shuru hajiya saudat tayi tana dan tunani kana ta amsa
"Haka zancenki yake,saidai ni a anawa ganin samun yarinyar bazai zama wani abu mai wahala ba,ta fanni daya ne za'a samu yarinyar da komai zai tafi mana dai dai,ba tare da an samu wata matsala ba,ko daga baya aje ana jeka ka dawo,za'ayi mai gaba daya ne,kuma komai bisa yarjejeniya da amincewar iyayen kansu da ita yarinyar..." Sai tayi shuru tana sauraren fulani aisha,wadda dukka ta qagu taji ya abun yake
"Ke nake saurare saudat,idan na fahimceki kamar kinason kice da farko dole yarinyar tazama diyar masu qaramin qarfi kenan marasa hali?" Kai ta gyada kamar tana kallonta
"Tabbas haka nake nufi"
"To amma ta ina zamu samu kenan?"
"Kina da amintattu aisha,wadanda suke kusa kuma suke rayuwa tare da talakawan qasar kaisa,a nawa tunanin....a cikinsu idan kika basu asirtacciyar cigiya to ba shakka za'a dace" murmushi ne ya kufcewa fulani aisha jin duk wani qulli ya kwance,har farincikin hakan ya bayyana saman fuskarta
"Qwarai qwarai aminiyata,wannan tsarin yayi,hakan kuma za'a zartar.....zan kiraki"
"Ohk....sai munyi waya"
"Ma sha Allah" ta fada tana sauke wayar daga kunnenta murmushi na shimfide saman fuskarta.


Tabbas idan tabi wannan tsarin komai zaiyi dai dai,hakanan komai zai tafi yadda ya kamata,saita miqe tana takawa cikin wajen a hankali tana sake zurfafa tunaninta kan yadda zata tsara komai bisa basira da fikra gamida kaucewa idanun 'yan adawa,yayin da wani sashe na qwaqwalwarta yasoma lissafo mata mutanen da zata tuntuba cikin amintattun nata wanda tasan ba zata samu matsala ba haihata haihata.......
_tofa masu karatu,ba'a fara wasan ba,muje zuwa_.


****************


Satinsu uku a mali azeez yakoma bakin karatunshi,yayin da fulani ayshan itama ta tattara tadawo nigeria.


Sai data huta sosai sa'annan ta buqaci ganawa da barorin nata,cikin matuqar sirri da takatsantsan,mutum uku ta kira a cikinsu harda umma luba,da zummar idan bata samu yadda takeso ba saita sake kebe wasu ukun ta sanyasu cigiyar da neman.


A nutse tayi musu cikakken bayani dazai gamsar dasu,bisa sharudda da dokokin irin yarinyar da take da buqatar a sama mata,shuru sukayi kowanne cike da fata da burin cewa asamu dacewa ta bangarensa,domin tabbas indai hakan ta tabbata ta bangaren mutum sun sani cewa kakarshi ta yanke saqa,basu bar wajen ba saida kowacce ta tabbatar wa da fulani aisha cewa zatayi iyakar qoqarinta wajen samo yarinyar data dace.


****************

Tunda fulani aishan tayi maganar umma luba tashiga dogon tunani da nazarin wadda zata kaiwa fulanin,zataso ace cikin jininta zata samo mata yarinyar,saboda romon domokaradiyyar da take da yaqinin yarinyar ita da danginta zasu kwankwada,bugu da qari ba qaramar daraja bace wajen mace auren yarima azeez koda kuwa cikin mafarki ne,koda cikin sirri ne kamar yadda xai faru a yanzu,ba shakka madaukakiyar daraja ce cikin kundin tarihin rayuwar diya mace hada auratayya da jinin gidan sarautar KAISA koda kuwa hada jinin na minti daya ne.


Washegari ba zata shiga gidan maimartaba ba,don fulani ta basu hutu na sati guda,kowacce taje tayi bincike takuma zo mata da labari mai dadi kafin zagayowar satin.


Tana zaune a faffadan tsakar gidanta tana ninke kayanta da jiya bilkisu ta wanke mata su tas,kamar yadda yake yanzu bata da matsalar mai wanki,saboda bilkisun duka ta hada harda wankin nata saboda kudin aikinta ya qara auki.


Sallamar bilkisun ita ta sanya daga kai tana duban qofar gamida amsa mata,fuskarta a washe kamar koda yaushe tana fadin
"Me gado,yana ganki haka dawuri" dan qaramin murmushinta tasaki tana isa gefan tabarmar umma uwalen tadan dosana,duk da sun debi shekara kusan uku tare amma kullum bilkisun kamar baquwa take a gidan,kasancewarta mutum bamai saurin sabo ba,umma luban tayi mitar tayi qorafi kan tadinga sakewa amma har yanzu jiya iyau.


"Yana ganki tun lokaci bai qarasa ba?" Tasake tambayarta
"Yau banje makaranta bane"
"Aiho,to,koda naji" saita miqe cikin qarfin hali tana qoqarin kama aikinta,duk da cewa sam yaudin bata jin dadin jikinta,kusan shine ma silar data sanya bataje makarantar ba yau,amma tadaure tazo aikin saboda batason tayiwa albashinta gibi,umma luba akwai kirki idan taso,amma fa tana da qaunar dukiyarta.


Jifa jifa tana ninkin tana duban bilkisun,yau shurun nata sai taga yasake yawa,amma tasan koda ta tambayeta ba gaya mata komai zatayi ba,mutum ce ita wadda bata iya bude baki ta fadi matsalarta ba,duk da tana tsammanin koma meye baya rasa matsala da yanayin da suke ciki a gidansu ba,tunda kusan umma luban tasan komai,duk da bilkisun bata taba bude bakinta ta gaya mata ba,kasancewar umma luban mutum ce mai dan shige shige da kuma jama'a yasa tasan komai.


Tana zaune dai a wajen tana karantar bikisun,gabanta yafadi sanda bilkisun ke rataye hijabinta saman igiyar shanyar dake tsakar gidan da niyyar daura alwala,gashinta mai tsaho santsi da sulbi ya bayyana tun daga gaban goshinta zuwa gadon bayanta,kamar tasan tana kallonta tayi hanzarin janyo dankwalinta mai santsi dake niyyar zamewa ta sake daureshi saman kanta,hakanan umma luban tasamu kanta da qarewa halittar bilkisun kallo.


"Tabbas wannan duk inda ake neman mace tacika mace,kuma koda fulani aisha nakaiwa ita na tabbatar zatayi mata dari bisa dari,banda rama dake jikinta ma da Allah ne yasan yadda za'a ga cikarta,wannan tayi kuma nasan zataja hankalin yarima azeez" haka umma luban tasamu kanta da nazartar yanayi halitta dakuma halayyar bilkisun harta kammala dukka ayyukanta tayimata sallama zata wuce,saita diba kusan rabin abincin data dafa tace tatafi dashi suci ita da qannenta,bataqi ba,don bata da tabbaci ko yaqinin abinda zasuci idan takoma,don hatta da amaryar gidan mai qyallin goshi yau sai da suka haura da baban nasu,da alama hantsi yasoma duban ludayi,sa'annan zani yasoma sanin mazaunai,saura kadan itama bisa dukkan alamu tabi sahu ,hannu bibbiyu ta saka ta amsa tayi mata godiya kana tawuce.


Tana jin hamza yana kiranta amma taqi ta tsaya,bakinta cike da addu'ar kada Allah yasa ta cimma babanta bare yaji aiken da zai jero ya tilasta mata tafita ta saurareshi ba,don a yadda take jin kanta din nan a yanzun kwanciya kawai buqata ko abincin bai gabanta.


Tana basu flask din kuwa tamaida haqarqarinta ta kwanta,duka sai yaran suka damu suka dinga tambayarta abinda ke damunta,cikin qarfin hali tayi musu dabara tace gajiya tayi,suci abinci maza suma su kwanta.


Ranar kusan kwana umma luba tayi tana auna dukkan matakai da sharuddan amsar macen da zasu kawo da fulani aysha ta gindaya musu da yanayin halin rayuwar da bilkisu take ciki,duk ta inda ta auna sai taga bilkisun tahau ma'aunin,cif da cif,bataga gibi tako ina ba,can qarshen dare daga qarshe ta yanke shawarar fara tunkarar bilkisun da maganar,don harkar zatafi kyau ace yarinyar tasan komai,kuma tayi amannar babu yarinyar da za'ayi wannan tayin tana cikin halin rayuwa irin na bilkisun da zataqi amsar wannan gwaggwaban tayin.

☀ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸â˜€ï¸


Duk yadda taso tayiwa bilkisun maganar amma dole ta haqura har tsawon kwana biyu,saboda ciwon dai saida yasanya bilkisun takwana biyun bata fita,duk qaunarta da aikinta dakuma makaranta amma dole haka ta haqura,sai qannenta ta turawa umma luban suka shaida mata bata da lafiya. A wakankin kuwa taji jiki sosai,rama tayi qwarai. Umma luban tayi amfani da wannan damar ta dinga aiko mata da dafaffen abinci mai yawa wanda tasan zai ishesu ita da qannenta.


Sosai hakan yayiwa bilkisun dadi,yakuma rage mata radadin ciwon,koba komai tana samun salama cikin ranta idan ta daga idanu taga qannenta suna da abincin da zasuci.


A kwana na uku ta sake qwarara jikinta don zuwa taci gaba da aikinta,don tana lissafe da kwanakin da bataje na,hakanan ta shirya tafito,tasamu babanta a tsakar gida ta gaidashi tawuce. Ajiyar zuciya tasaki,tsawon kwanakin bata samu arziqin paracetamol ko na naira biyar ba daga wajen mahaifinta,hasalima ciwo kanshi baisan tanayi ba,wannan kuwa bawai wani baqon abu bane a wajenta,kusan haka tasu rayuwar take.


"A'ah,mai gado,kin warke ne da kika iya fitowa?" Umma luba ta fada cikin nuna tsantsar kulawa,duk da babu wata matsala data taba ratsa tsakaninta da umma luban saboda tsantseninta da kiyayewarta da takeyi amma tayi mamakin yadda yau kulawar ta ninka ta baya tazama ta musamman
"Eh,naji qarfin jikina ne shi yasa nafito"
"Ai da kin bari kin sake jin dama dama"
"Babu komai umma"
"Allah to ya qara sauqi ya qara lafiya"
"Amin amin"
"Amma dai kinje asibiti ne ko?" Murmushi kawai tayi mata ba tare data amsa ta ba,hakan ya baiwa umma luban amsarta,saita kama haba tana dubanta
"Kai,maigado Allah ya fidda ku cikin wannan halin rayuwar,Allah ya kawo miki agaji ya dandasheki da miji da zai zama silar fitarki daga quncin da kike ciki keda 'yan uwanki,ki huta suma su huta...kiyi aikin daidai gwargwado yadda zaki iya kinji,Allah yabaki lafiya,ke abar tausayi ce bilkisu" ta qarashe fada cikin nuna jajjabi. Ita kanta bilkisun taji maganganun har tsakiyar zuciyarta,taji zuciyarta ta karye sosai har hawaye yana shirin zubo mata,ta danne zuciyarta ta soma aikinta a hankali kuma a nutse yadda ba zata jigata ba.


Kamar kowanne lokaci duk sanda

Please Login or Register in order to submit comment