Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin motar,saiga drivern yafito cikin hanzari hannunsa dauke da ruwan roba manya guda biyu.


Baki tasake yadda taga afnan din ta balle ruwan roban takama gefan unifoarm din nata cikin rashin damuwa tana tittilewa a jiki tana wanke ruwan kwatar,saita kai hannu da sauri ta riqeta
"Zubamin zan wanke dakaina" murmushi ta sakar mata,bata musa din ba taci gaba da xuba matan tana wankewa,lokaci lokaci tana satar kallon bilkisun,harga Allah tausayi take bata,ta tsani kalmar auren dole,koda a littafine take karantawa tota aje littafin kenan,saboda bata manta dauki ba dadin da aka dinga yi cikin gidansu ba lokacin da maimartaba yaso baiwa arifa yayarta tabiyu wani ba,yadda arifan tashiga tashin hankali qwarai harsu kansu saida suka tayata shiga damuwa,daga baya dai Allah ya warware da yake wani baya auren matar wani.


Tas tawanke,ta kama inda zai matsu ta matse kana ta yarfe
"Na gode" tafada a sanyaye tana duban afnan,tare da mamakin meya sauyata haka?,don ko amafarkinta bata taba tsammanin afnan din nada tausayi da sauqin kai ba
"Ba komai,kishiga mota saimu saukeki a hanya" motar takalla kana ta kalli afnan,tana qoqarin hadiye wani abu dake taso mata,hala afnan tana cikin masarautar kaisa ne amma batasan dukkan abinda ke faruwa ba,da zata iya data gaya mata cewa a yanzun ta tsani dukkan wani abu daya shafi masarautarsu,saidai ko Allah ma yace kada laifin wasu mutane yasa ka kasa yi musu adalci,babu ruwan afnan cikin batun,don ga alamu sun suna batasan ma meke faruwa ba,wala'alla data sani ko kallon tsiya ba zata mata ba bare na arziqi,a yadda suke da ita abaya na rashin jituwa a tsakaninsu
"Ki barshi,zan iya qarasawa ai,kada na bata muku mota da danshi,kinga a jiqe nake,na gode sosai" saita soma takawa,tausayinta takeji sosai,ba zata iya barinta tawuce ba,saitasha gabanta
"Don girman Allah kishigo mu saukeki,bakyau maida alkhairi" ta kashe mata jiki,tilas tabita tabude mata murfin motar,sai data soma shiga sannan itama afnan din tashiga.


Wani sassanyan sanyi ne yasoma ratsa kowanne loko da saqo na jikin bilkisu yana busar da gumin da ada ta hada saboda tafiya a zafin rana data soma,sanyin da rabonta data jisa tun lokaci anty zuhriyya na rayuwa a kusa da ita,duk da yanayin da take ciki sanyin ya mata dadi,saita lumshe idanunta kawai tana jin yadda motar ke tafiya wani suuuuu kamar ba saman kwalta suke tafiya ba,kai kace a iska ko a sama suke tafiya.


"Kiyi haquri xan miki shishshigi bilkisu,duk da ina zaune aka gayamin,ban sani ba gaske ne koba gaske bane,amma indai da gaskene auren da bakiso za'a miki,kizo na kaiki wajen abbana,na tabbatar da cewa zai hana faruwar hakan,don tun daga cikin gidansa zuwa al'ummar qasarsa ya haramta auren dole tun daga kan yayata arifa" idanunta tabude akan afnan,ashe haifaffiyar sarkin kaisa din ce ita,hakan na nufin ita din 'yaruwa ce ga yarima wanda akeson bata?,uwa daya ko uba daya ko uwa daya uba daya?,rashin sani yafi dare duhu,batasan daga can zancan yataso ba take da yunqurin kaita don samun adalci,akwai adalci da gaske irin wannan a masarautar amma ya kasa biyowa ta kanta?,waishin ins matsalar take ne?
"Karki damu,babu damuwa,na gode da kulawa" abinda tace mata kenan,don koda ace ba daga gidan tushen matsalarta take ba bazata iya kai mahaifinta qara kan zai aurar da ita ga wani ba komai lalacewar mahaifin nata.


Basu sauketa a hanya ba kamar yadda da farko afnan ta fada ba sai da suka danganata da bakin layin
"Na gode" tasake maimaitawa tana duban afnan din,itama ita take kallo cikin murmushi tace mata
"Babu komai" koda sukayi gaba da kallo tadinga bin unguwar tasu,tana ganin tarin banbance babance qarara,wane sashe na zuciyarta yana sake cika da tausayin bilkisun,da kuma ganin kuskurenta qarara na sanya 'yar tsama ga innocent mutum kamar bilkisun,wadda bata taba taka mata ba bare ta zubar mata.


**************


Cikin irin kebantattun lokutta da take warewa ne domin iyalinta,tana zaune a falonta na musamman,sanye take da doguwar riga mai hade da hula na wani irin yadi mai sulbi da taushi,afnan ce kanta saman cinyarta,hannunta riqe da wayarta,saidai hankalinta bai kan wayar tata gaba daya,ta ta'allaqashi ne wajen bawa amminta labarin bilkisu,da abinda ta fuskanta daga rayuwarta duk da bata taba bude baki anyi magana makamanciyar haka da ita ba,har sai da fulani aysha ta soma gajiya dajin labarukan autar tata afnan tace da ita
"Baki da sauran abunyi mata ai afnan,tunda tace babu komai tagode" cikin shagwaba irin ta wadanda suke auta a wajen iyayensu tace
"Toni ammi tausayi take bani wallahi,da bama shiri amma yanxu tausayinta nake"
"Ai shikenan,saikiyitayi,daga min cinya hakanan na huta" tana dagawar jakadiya tayi sallama bakin qofar falon tana jiran abata izini tashigo,saita dubi afnan
"Idan kin fita ki mata ixini" amsawa tayi dato tana gyara yafen mayafinta,kana ta wuce jakadiya kuma tashigo.


"Allah yabaki yawan rai....an shaidawa ubabatu kuna son ganinta,gata kuma ta iso"
"Anyi mata izini tashigo"
"An gama Allah ya taimakeki" daga haka tajuya tafice,cikin qiftawa da bismillah umma luba ta bayyana cikin falon.


Babu jinkiri fulani aisha tasoma zayyana mata dalilin kiran
"Da farko munason ki shaida musu a sanda zasu tashi zuwa gidan zama nawucin gadi kafin a kammala musu ginin gidansu kafin lokacin da za'a daura auren....zamu dauketa zuwa gidan da za'a kebeta...inason ayi mata horo na musamman,ayi mata gyara na amare na musamman irin gyaran da aka jima ba'a yiwa wata diya ba,duk da cewa xabinmu ce zuwa wani lokaci amma ko babu komai zatayi tarayya da jininmu ne,sabida haka inason a sauyata amantar da ita wacece ita,a dabi'anceta da dabi'a ta gidan sarauta,halayyarsu yanayin maganarsu da sauransu saboda yarima yaji dadin zama da ita ba tare da yana tuna wani abu na daban ba,ko yaji damuwa cikin ranshi,bayan wannan inason ayi mata training na yadda zata kula kanta,babu buqatar takoyi yadda zata zauna dashi,don iya aikinta kawai zataje tayi,kula da komai nashi yana da masu yi masa shi,bana buqatarma takoya din saboda wasu dalilai nawa dana barwa kaina sani,abu na iko,inason ki shaida musu,su lissafa dukkan adadin dukiyar da sukeso a matsayin dukiyar auren 'yarsu,ko nawa ne zamu biya,su fadi ko nawa suke da buqata daga nan har zuwa ranar rabuwarsu,bisa sharadin idan an rabun,zasu manta cewa 'yarsu ta taba auren mai suna abdul'azeez,yariman masarautar kaisa,munason rabuwa tahar abada,ta rayu takuma ci gaba da rayuwa babu shi ko digo cikin tunaninta,wannan shine babban bangare kuma babban sharadi na tafiyar alaqarmu,samun akasin hakan kuma dai dai yake da faruwar kowanne abu...." Saita tsagaita tana maida numfashi
"Wannan sharadin kusan shine abu na farko dana fara shaidawa mahaifinta,yakuma yarda yayi na'am da hakan dari bisa dari" kaita gyada cikin nutsuwa sannan tadora
"Ko a mafarki bama buqatar su hado diyarsu da wani abu,itadin kawai zallarta muke da buqata....abu na qarshe shine,za'a daura aurensu cikin masarautar mali cikin ahalina ba'a qasar kaisa ba,daga nan zamu dauketa zuwa muhallin da zata zauna na tsahon shekara daya,ba zata bar wajen ba harsai sanda kwanakin suka cika"
"Allah yabaki yawan rai an gama,wannan saqo zai isa kunnensu da izinin Allah" kai tasake jinjinawa
"Da kyau,ina da buqatar hotonta wanda zai turawa yarima don yaga irin zabinmu....jibi zata bar gidansu zuwa gidan da muka tanadar mata tazauna,zamu aika da mai hoton can,inason a zaman ya kasance kina daya daga cikin masu kula da ita,har zuwa lokacin da zasu wuce mali,tukuicinki kuma kizauna ki zaba dukkan abinda kikeso a duniyar nan,matuqar mun mallakeshi xamu bakishi"
"Godiya nake Allah ya taimakeki,wannan karamcin naki da bashi da kwatankwanci bakina yayi kadan yayi miki godiya,kalmomin bakina sun qare fulani". Umma luba ta fada cikin rudewa da zallar farinciki.


Ƙarfe biyu da rabi na dare ne amma saika tsammaci tsakiyar rana ce tarwai saboda yadda idanunta suke a bushe kuma a soye raqayau,babu digon wani abu mai suna bacci tattare da ita,bata jin koda alamarsa duk kuwa da yadda ya qware wajen iya sata.


Ji take kamar zata zauce a duk lokacin data tuna kalaman da mahaifinta ya gama rattaba mata daxu bayan sallar isha'i,YA SAIDA ITA,YAYI CINIKINTA wannan itace kalma mafi sauqi daya kamata mahafinta ya gaya mata akan hanyar dayabi ta dogon sharhi kan buqataun masarauta akanta

Jin zantukan nashi take tamkar a shirin film ko kuma a qagaggun labari na hikayoyi,wadan nan sharuddan da dokoki dukkansu sunfi kama dana matar da za'a siyeta a matsayin baiwa ba 'ya ba,ta ina zata fara?. Ta ina lamarin zai yiwu?. Saita waiwaya tana duban qannenta dake kwance suna bacci ba tare da sunsan gagarumin tashin hankalin dake fuskantarsu ba. Ta ina zata soma barin wadan nan bayin Allahn da yafi kyau a kirasu da marayu?. Ta yaya zasu iya jurewa rashinta?. Wa zata barwa su?. Umma katti?,mama ladi?,koko mahaifinsu da yafi kowa rashin damuwa da rayuwarsu,wanda asanda take masa bayaninsu ma cewa yayi basu da wata damuwa tunda zasu samu sauyin muhalli,zasu kuma samu ci sha da suttura maikyau.


Wani abu dake mata yawo saman kwanyarta kamar ana mata tafiyar tsutsa haka tadinga ji,ta dinga kaikawo tana tafiya tsakanin qannen nata daga bango zuwa bango na dakin. Ji take kamar ta zura da gudu tabar gidan...tabar qasarma gaba daya,da sauri ta juya tafice daga dakin,saita tsinci kanta tayi hanyar soro tana muradin ficewa.


Sanda tabude qofar gidan babu abinda yasoma mata maraba sai zallar duhun dare,wanda ya cukudu da haushin karnuka daya cuka anguwar tasu
"Wa kika barwa su?" Daga qasan zuciyarta aka jefa mata tambayar data sanyata tsaiwa cak
"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim". Tasamu kanta da furtawa sau babu adadi,wanda wannan ya taka rawa wajen sanyayar jikinta,tamaida qofar ta kulleta kamar yadda take,kana ta janyo qafafunta zuwa cikin gidan.


Maimakon tanufi dakinsu kai tsaye saita durfafi bakin famfonsu gadan gadan,ta kunnashi kana ta duqa gami da tara hannayenta,saita bige da alwala.


Bata damu da neman abun salla ba,hakanan saman dandaryar sumuntin dakin ta tada sallar,sallar data jata har zuwa lokacin da akayi kiran assalatu,ta bada farali wanda daga wannan bata kuma sanin abinda ke faruwa ba,gwanin iya sata ya saceta duk da yadda take kokawa dashi da nuna mishi nata maraba da ziyararshi.


A kallon farko zaka san cewa babu wani abu da yayi kama da sukuni tattare da ita,duk wata wulgawar da yaran zasuyi binsu take da kallon zallar tausayi,bata ankata ba tuni mahaifinta yagama gaya musu cewa zai aurar da yaayarsu,wanda hakan yayi masifar dugunzuma hankulansu gaba daya,tana zaune tana saqa da warwara sai ganin yara tayi sun sata a gaba gamida zagayeta,gabanta na faduwa tana fatan ba abinda take hasahe bane ta tambayesu lafiya
"Aure wai zakiyi yaaya inji baaba,kema aure zakiyi ki tafi kibarmu mudaina ganinki yaaya?" Hauwa ce tajefa mata tambayar cikin matuqar mutuwar jiki dakuma saddaqarwa.


Da idanu ta dinga binsu da kallo dai dai da dai dai,tana jera kalaman da zata gaya musu,saidai yanayin dake saman fuskar kowannensu ya sagar mata da gwiwar kowanne yunquri nata,tausayinsu yasake ninkuwa cikin zuciyarta,qwarin gwiwarta da karsashin data tattaro suka baje,ta rasa abin cewa,sai kawai ta sanya musu kukan data jima tana boyewa,karo na farko a rayuwarta,karon farko data nuna gazawarta a gabansu,abinda komai girman nauyi da tsanani bata taba bari gazawarta ta bayyana koda saman fuskarta ba,saboda tasani itace kadai qwarin gwiwarsu,itace kadai hope dinsu,batason tayi abinda zata kashe musu fata da burinsu da dukka suka aza wuyanta.
7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: 20

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070
________________________________



Kuka take haiqan irin kukan dake nuna zallar tashin hankali da shiga taskun rayuwa,fuskarta kife a tafin hannun hannatu,yayin da dukka yaran suke kewaye da ita,kowannensu kuka yake kamar yadda yayar tasu take,kai...tama zarta yaya a wajensu,uwa ce kuma ubace gata sannan jigo cikin rayuwarsu.


A yau din da ake niyyar tsigeta daga cikinsu akaita can wata uwa duniya ji take kamar ana shirye shiryen zare ranta ayi jana'izarta ne,tana hasashen rayuwa babu qannenta,bayan babu wani tartibin hannu da zata barsu,dukka bayanan da mahaifinta yayi mata akansu basu gamsar da ita ba,me jiya tayi ballantana yau,meya tsinanawa rayuwarsu a baya bare a yanzu,ya ilahi me tasa babu wanda yaduba kokenta?,babu wanda yaduba quncinta?,babu wanda ya waiwaya yaduba uzurinta?,kowa yasanya buqatarsa gaba fiye data kowa?,kowa nashi muradin shine a gabansa?.


Dai dai lokacin data soma jiyo hargagin mahaifinta daga tsakar gidansu wanda yasoma zama filin Allah,saboda tuni akayi nisa wajen rugujeshi,yana zubawa umma katti masifa,wadda a yanzu take tsananin yi masa biyayya da takatsantsan,kan tashiga tafito da maigadon,ubanme takeyi mutane suna jiranta a waje?,kai kace irin amaren nan da ake shirin kaisu gidajen mazajensu a yammacin daurin aurensu.


Kafadarta umma katti ta dafa cikin tausasa harshe tace
"Haba maigado,kamar zaki barsu hannun bare?,bayan ga mahaifinsu gani da nake kamar uwa a wajensu?,ki kwantar da hankalinki,kamar yaune zakije ki dawo ki samesu lafiya kinji?,don Allah karki tashi hankalinki". Sai a sannan ta daga rinannun idanuwanta tana kallon umma katti,kallo take mata irin kallon da wanda aka cuta yakewa azzalumi,tsahon xamanta tare da ita zata iya cewa bata taba jin lafazi mai dadi daga bakin umma kattin ba sai a dan tsukinnan da aka fara wannan sabgar,bata daukan zamanta tare dasu a matsayin wami abu mai alfanu,tunda shekarun dukka da suka shude basu canza komai ba,sai yanzu?,amma yata iya,dole tayi magana da ita,cikin muryar dake nuna kuka ya suqeta tace
"Ga amanar Allah nan a hannunki,Allah shine shaida umma"
"Karki damu,qannenki ba zasu tagayyara ba,mu da zamu shiga rayuwar daula da hutu?,rashin abinci da suttura dukka fa zai zame mana tarihine a rayuwarmu" ta qarasa fada tana murmushi da alamu abun yana mata dadi,cikin qunci da takaicin umma kattin tadauke kai daga gareta,dole tayi farinciki tunda tasamu mafita ba tare da an taba martabar nata diyan ko guda daya ba,saita dubi hannatu,ta kama hannunta tariqe tsam hawaye naci gaba da kwaranya
"Hannatu,bayan babu ni kece makwafina....na baki dukka amanar qannenki....ina fata zaki zama jaruma,zaki sanya dukka qarfinki ki tallafesu a yayin da sukayi rauni" kuka tafashe dashi sosai,cikin sheshsheqa tace
"In sha Allahu yayaa,zamuyita miki addu'a Allah yadawo mana dake" saita dauke idanunya daga kan hannatun tamaida kan qannenta,kowanne da abinda ta gaya masa gwargwadon sanin halinsa da tayi,hauwa'u ce tashin hankalinta yafi nakowa,takuma sanyata kuka fiye da wanda tayi a baya,da lafuzzan bakin yarinyar tafice daga gidan ba tare data jira rakiyar da umma katti da mama ladi keta qoqarin yi mata ba,ba tare data jira ba tabude motar da kanta tashiga,kana ta cure waje daya saboda sanyin ac da bala'in da takeji yana gigita rayuwarta,tana sake fashewa da wani kuka mai azabar radadi dacin rai kamar ana yankar zuciyarta ta sake kame jikinta waje daya
"Shikenan yaaya idan kika tafi kema,kinga har yanzu ba'a ga mamata ba,bayan kince ko batazo ba ke zaki kaini gurinta,shikenan kema kin tafi ko yaaya?".


Batasan motar tatashi ba bare taji alamun tafiyarta,tunani ne kala kala fal cikin kwanyarta,zuwan abubukar saddiq tatuna,mutum na farko bayan afnan da taga yanuna damuwa qarara saman fuskarta kan yanayin datashiga,fuskarsa ta hango lokacin da babanta ke rattaba mata ya zaba mata miji,biki saura sati biyu,karya sake ganinsa qofar gidansa,data san da zuwan wannan ranar data tsaya ta saurari abubakar,wala'alla ya zame mata garkuwa,da tasan da afkuwar wannan mummunar qaddarar dako amanar qannenta tabari a hannunshi,duk da batasan wayeshi ba,batasan halayyarsa ba,amma hakanan jiki da zuciyarta suke bata gwara shi akan mutanen gidansu,jikinta yake bata zai iya,zai iya kula mata dasu,saidai dukka bakin alqalami ya riga daya bushe babu makawa.


"Ranki ya dade mun iso" taji ana fada daga gefanta,abinda ya sanyata dago kai kenan cikin mamaki tana duban mai maganar,umma luba ce,saidai wannan karon tana maganar cikin qanqan da kai da wani irin respect,kai kace ubangidane da yaronshi.


"Duk abinda akace kiyi bakiyi ba,ko kika musa tsahon wannan yarjejeniyar,Allah ya isa tsakanina dake ban yafe miki ba" taji zuciyarta na tuna mata kalaman mahaifinya na qarshe,wanda dasu ya sallameta,wata iriyar dakiya taji tazo mata,wai meye yaragewa saura a rayuwarta?,tabarsu kawai,tazuba musu idanu koma me zasuyi suyi,idan sunso su rabata da ranta.


Cikin mutuwar jiki ta zuro qafafunta tasauko daga motar,sai kuma ta tsaya cak tana duban gidan,tsoro yana son shigarta.


Wani irin qawataccen gida mai cike da ni'imar dake bayyana kanta tun daga farfajiyar gidan ba tare da kakai ga shiga cikin gidan ba,tasan cewa sanda suka baro gidansu rana ce tarwai mai zafi a sararin subhana,amma ga mamakinta gidan babu alamun rana tattare dashi,sai wata irin iska mai dadi dake kadawa,ko ina luf luf yake,kamar ka shiga wata qasaitacciyar gona,tafiyar da sukayi daga gidansu zuwa nan din a qiyasinta bazai wuce tafiyar awa daya ba bare tace kafin su isone yammaci lis tayi
"Ga hanyar da zamu shiga cikin gidan nan,ki kwantar da hankalinki,tun daga nan zaki gane kin soma samun sauyin rayuwa" umma luban ce dai tasake fada cikin taushi tana nuna mata hanya,ala wadai da sauyin rayuwa irin wannan,sauyin rayuwar da zai doraka bisa wani SIRADI da bakasan qarshensa ba,sauyin rayuwar da zai sanya asiyeta tataho bauta kwatankwacin yadda ake cinikin bayi ada,wanda banbancinsa da wancan kadanne,sauyin rayuwar daxai binne dukka wani buri nata,ya rabata da 'yan uwanta,ya katse mata karatunta,ita kuwa me zatayi da wannan sauyin?,dukka wadan nan maganganun tana yinsu ne a lokacin da suke takawa zuwa hanyar da zata sadasu da falon gidan.


Tun daga falon ta fahimci lallai akwai banbanci mai tarin yawa da sauyi da rayuwarta ke fuskanta,makeken falone wanda yake dauke da dukka abubuwan more rayuwa,saidai bata da nutsuwar xama ta kalli wani abu,a qalla ta tadda ma'aikata nata kawai kusan guda biyar,suna shiga suka soma zubewa cikin girmamawa suna gaidata,bata iya amsawa ba saboda abu uku,baqinciki haushi da takaici,abun sam bai burgeta ba ko kadan,umma luba bata barta anan ba sai data danganata da wani hamshaqin daki daya amsa sunansa,dakine da iya kallonshi ma wata ni'imace ta daban bare kasancewa a cikinsa,ko daya bai bata sha'awa ba duk da yadda aka tsarashi,aka kuma qawatashi,saita zabi zama qasan dakin tana ririta zuciyarta gamida wassafa yadda rayuwarta zataci gaba da gudana cikin wannan dakin.


Azahar tanayi umma luba ta gabatar mata da abinci har cikin dakin ba tare data nemi ta fito muhallin da aka tanada ba saboda cin abinci dake falon.


Wata iriyar lafiyayyar shinkafa ce da kaza da hadin salad,sai farfesun nama dana kifi kala daban daban,bayan nau'ikan lemuka,ko a idanu abincin yafi qarfin cikin mutum daya,amma dukka aka jere saboda ita daya,ko kadan abincin bai burgeta ba bare ya bata sha'awa,a sannan tunaninta shine,su hannatu sunci abinci?,idan sunci me sukaci?,waye yabasu?,waye yakula dasu?,sai wani kukan ya balle mata,a maimakon cin abinci saita sanya kanta tsakanin qafafuwanta taci gaba da rerashi.


Sosai umma luba tazauna tana bata baki gamida lallashi dason shawo kanta,ko daya batason ganinta kojin kalaman bakinta,don kusan itadin itace ummul aba'isin fadawarta kowacce musiba a rayuwa,banda ta zabeta...banda tazo har gida ta shaidawa mahaifnta....takuma yi masa romon bakan abinda zai samu....da tuni iyanzu tana csn cikin qannenta,duk da rayuwarsu babu wadata sai fatara qunci talauci da yunwa,amma tanajin tafiye mata sau dubu fuye da wannan rayuwar da batama soma fuskantarta ba,rayuwar da akayi cinikin 'yancinka na wasu watanni aka miqaka ga hannun wasu.


Ganin cewa umma lubar ba zatayi shuru ba saita miqe kawai ta durfafi inda ta nuna mata dazu bayan sun shigo a matsayin bandaki,tatura tashige kana ta maida qofar tarufe,saita samu gefan bathtube tazauna ta dora daga inda ta tsaya,sai datayi mai isarta,taji ta rage wani nauyi sosai daga qirjinta sannan ta dubi agogon data lura dashi cikin bandakin tun shigowarta,lokacin sallar azahar yayi harma yadan gota,don haka tazarce da daura alwala kana tafito.


Sanda tafito babu kowa cikin dakin,da alana tagaji da jira tafita,saita kintaci gabas kawai ta tayar da sallarta,ko bayan ta idar dinma bata kallo sashen da abincin yake ba,haka taci gaba da zamanta tunani kuma ya qulla qawance da ita.


Ƙarfe biyar da 'yan mintuna na yammaci taji an dan taba qofar,tsahon sakanni batace komai ba tana duban qofar,sai taji an turo an shigo,baquwar fuska ce da bata santa ba,hannunta riqe da wani abu,cikin girmamawa ta rusunar da kanta tana cewa
"Ranki ya dade,mai gyaran jiki ce ta iso,tace a shaida miki,daga wajen fulani take" jim tayi kamar ba zata amsa ba,saidai ko bata amsa din ba babu abinda zaya canza,don haka saita miqe kawai tana gyara hijabinta wanda tun daga gida ta taho dashi
"Ammm....afwa ranki ya dade,ga wadan nan kayan,su zaki canza kafin kifita" wani kallo ta watsa mata kana tawuceta tana shirin ficewa,saboda tsabar wulaqanci suturar da tazo da ita daga gidan uban nata ma sai an rabata da ita saboda tsabar raini,da sauri tace
"Ranki yadade kiyi haquri ki canxa,fitarki a haka zai janyomin matsala,ki taimakeni" tsaiwa tayi tana dubanta,yadda ta marairaice mata ya tabbatar mata da iya gaskiyarta ta fada mata,sai taji tausayinta ya tsarga mata,wala'alla itama bata da iko da kanta sai abinda aka bata umarni,saita dawo da baya ta amshi kayan daga hannunta,ganin haka yasanyata juyawa tafita daga waje don ta bata damar canzawar.


Saman gado tazube kayan kana tasoma daddagasu da ɗai ɗai da ɗai ɗai tana qare musu kallo,ko ba'a gaya mata ba tasan cewa kayane masu daraja da tsadane,wani santsi da sulbi suke,doguwar riga ce mai wani irin wadataccen mayafi,haka ta ware kayan ta sanya ba tare data damu da kyansu ko tsadarsu ba,kawai zatayine saboda matar kada ta gamu da matsala kamar yadda ta nemi alfarma a wajenta.


Wani kebantaccen dakine na musamman ta taras da matar zube ita da kayan aikinta,kana gani kasan ta kusamman ce,kuma takanas aka daukota saboda aikin,dukkan abinda ake bilkisu idanune nata,tsahon awanni biyu cas tuni an soma fidda ainihin kyan choculet colur skin dinta,an yashe duk wani datti ko gashi dabai dace da saman fata ba,hakanan gashinta tana kallo aka masa ɗai ɗai akayi masa wankan tsarki,duk da cewa shidin bawai datti ne dashi ba,saidai wani samfurin gyara da aka masa yasake masa tsaho santsi dakuma laushi.


***********


Kwanaki uku kenan tana cikin wannan gidan,wanda dukkan wani nau'in abubuwa na morewa rayuwa babu abinda ba'a aje mata ba,saidai iyakarta dakin sai dakin da ake mata gyaran jikin da babu abinda tafi tsana a duniya sama da yammaci yayi azo wannan hidimar,bata taba yarda ta taka wami wajena gidan na daban ba baya ga wannan dakunan guda biyu,abinci kuwa iyakarta na safe sai kuwa na dare,kowanne tsakurarsa kawai take abisa dole badon son ranta ba,gadon dake dakin kuwa iyakarta dashi kallo,ko sau daya bata taba kwatanta kwana akanta ba,yan uwanta ne tsaye a ranya fiye da komai,hatta da makarantarta yadda ta qwallafa rai tariga daga sallama amma tunanin qannenta bai bar ranta ba,kwanakin ajere ana mata wannan hidimar ta gyaran jiki,cikin jikinta a karan kanta tasan cewa akwai gagarumin sauyi,amma taqi baiwa kanta cikakkiyar damar karantar haka bare har takai ga duba xuwa wannan.


Ta dade da zubawa sarautar Alla idanu,takuma zama kamar mutum mutumi,saboda tasan cewa tawayenta babu abinda zai qareta dashi,kanayin tawaye ne a inda kasan kana da abin fada kana kuma da gata sa'annan za'a daga kai a dubi buqatarka.

***************


Wasu irin kalolin fitilune ke kamawa da kashe kasu a qaramar harabar da aka qawata

Please Login or Register in order to submit comment