Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar.


Shaidai malam bilya miqewa yayi ya kade babbar rigarsa ya qara gaba,saidai koda ya isa gida kasa shiga yayi,yayi zaune anan qofar gida lamarin na masa kai kawo,yana jujjuyashi cikin ransa tare da hasashen meke iya faruwa nan gaba,wala'alla hakan ya qara masa daukaka da girma na hada jini da masarauta,wala'alla kuma ya sake fadawa wata daban.


Dukkaninsu shi da umma luban a wannan daren basuyi wani isashen barci mai dadi ba,kowa da zancan ya kwana a ranshi yana juyashi tare da taraddadin meye zai biyo baya?.


Washegari sam bata da agender na shiga masarauta,a yadda ta tsara sai jibi,amma zuwan ya zame mata tilas don isar da wannan saqo zuwa kunnuwan fulani,don haka tun goma na safe ta gama shirinta ta doshi masarautar kaisa.


Sanda taje akwai baqin da fulanin ke ganawa dasu,tadai shaidawa jakadiya zuwanta,ita kuma ta shaidawa fulani,sai kuma tayi zaman jiran ayi mata iso.


Lokacin da aka bata izinin shiga ita kadai tasan yadda ta dinga ji,gumi ya dinga karyo mata,qafafunta babu qwari ta dinga kutsa kai falon,cike da taraddadin sakamakon da maganar zata bayar.


Sanda ta shiga tana zaune saman daya daga cikun kujerun alfarma dake wajen,fuskarta a sake take duban luba harta qaraso,ta zube cikin girmamawa a gabanta
"Allah ya taimakeki....ya baki yawan rai...Allah ya iya miki yakuma dafa miki,ya danqwafar da maqiyanki,ya qasqantasu a gabanki.....barka da warhaka ranki ya dade" murmushi tayi har cikin ranta tana jin dadin addu'ar da luba tayi mata
"Yauwa sannu luba,barkanmu....ya iyali"
"Kowa lafiya Allah ya baki yawan rai"
"To madalla,haka mukeso" shuru umma luba tayi tana jujjuya maganar,harsai da fulani ta fuskanci akwai magana bakinta,ta dago tana gyara zamanta sosai sannan tace
"Lafiya dai ko?" Kanta zuwa gefan fuskarta ta shafa,tana jin wani irin rashin sukuni
"Lafiya amma ba lau ba"
"Uhmm,gaggauta sanar dani,meye yake faruwa?" Zama tayi sosai dirshan,don a jikinta tana jin cewa maganar ba qarama bace
"Wato Allah ya baki yawan rai,jiya da daddare bayan sallar isha'i,mahaifin yarinyar nan da aka yiwa auren shekara daya da yarima Allah ya qara masa lafiya.....yazo ya taddani har cikin gida..." Saikuma tayi shuru,cikin sakanni da basu wuce biyu ba yanayin fuskar fulani ya sauya,ta zuba luba idanu tana kallonta
"Uhmmm,ina jinki,ina fatan jin badai wani abunne zai biyo baya ba,tunda mun riga da mun gama tsarawa da kuma qulla dukkan wata yarjejeniya dasu ko?"
"Allah ya taimakeki,tuba nake,amma kusan kamar baya ce ta haihu"
"Ki hanzarin fayyacemin komai,baya ce ta haihu kamar yaya?" Ta sake tambayar luba kamar mai shirin miqewa tsaye
"Yarinya dai juna biyu gareta" ta fada a hankali kamar batason fadar.



Wani irin rugugin aradu ne ya gifta saman kan fulani aisha,zuciyarta ta wani damqe waje guda na sakanni
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?,garin yaya haka ta faru?,ya akayi haka?,ya akayi wannan kafar ce kawai.suka bari basu tosheta ba?,saboda tayi tunanin yariman zai kauce mata da.kanshi,tayi tunanin ko bata toshe ta ba shi xai toshe da kansa,tunda yasan irin auren da nau'insa,amma ya akayi basira ta bace mata bata jaddadawa sodangi ba?,me yasa basira ta bace mata bata gayawa ita kanta luba din ba?,ya akayi basira da wannan tunanin aka daukeshi cak daga kwanyarta?,me yake shirin faruwa?,tonuwar asirinsu?.


Batasan ta miqe tsaye har tana safa da marwa ba saida kalaman umma luba suka dawo da ita hayyacinta
"Allah ya huci zuciyarki,ki dade ki qarko,babu abinda zai faru fiye da abinda kike son ya farun"
"Kije zan nemeki" shine amsar kawai data iya baiwa umma luba,saboda ba al'amari bane da zata yanke hukunci da hanzari ba,akwai buqatar tayi zuzzurfan tunani akai,tunanin da ita daya take buqatar yinsa,ta kuma yanke shawarar abinda zai fishsheta,don wannan karon bata da buqatar kowa yaji ko yasan me ya kuma afkuwa.


Da hanzari umma luba ta miqe tana godiya,sallamar data mata a lokacin tayi mata dadi,don dama Allah Allah take ta matsa daga wajen,saboda kwarjinin fulanin dake sake sanyata cikin firgici da dimuwa.


Wunin ranar kaf cikin wani mawuyacin hali tayishi,maganar taketa maimaitawa tana dorata bisa mizani iri daban daban,duk hukuncin data bata sai taga batayi mata ba,tabbatuwar cikin da wanzuwarsa tamkar barazana ce ga duk wani sirri nata da kuma rayuwar azeez,zubewar mutuntakarta taba qima sa darajarta data ahalinta gaba daya.


Ranar kaf bata sake bari kowa ya ganta ba,har zuwa dare sanda take zaune gefan gadonta sanye da kayan bacci,hannunta dauke da cup tana kurbar tea wanda ta tilastawa kanta sha don kada ta kwanta da yunwa,maganar ce dai a ranta take sake juyata gami da yi mata fashin baqi.


Dire cup din tayi da sauri,saboda wata magana da tayi amsa kuwwa cikin kanta
"Karki zama shashasha mana.....daga sun fadi magana ki dauketa gaske..." Maganar ta shigeta sosai,sai tayi tsam da hankalinta tana dora maganar kan ma'auni
"Tabbas talakawa ne wadanda basu da komai,mahaifinta ma'abocin son abun duniya ne,babu wanda yake irin yanayin da suke ciki,wanda xai shiga daula irin haka kuma lokaci daya ayi handing over dashi ya yarda ya karba,ya kuma fita salin alin ba tare daya qirqira wasu abubuwa da zasu biyo baya ba,kudi qalilan sukan ruda irinsu,su kuma sauya musu hali da alqibla,ba shakka zasu iya komai saboda komai yaci gaba da tabbata tsakaninsu,waya sani ma ko sun qirqiro maganar ne don suyi blackmail dinsu.


Murmushi ya kubce mata,sanda ta tattara dukkan bayanan da kwanyarta ta bata na cewa qarya suke,babu wani ciki,sunaso ne kawai suyi amfani da wannan hanyar su dinga tatsar dukiya daga garesu
"Da sun sani bata haka suka biyo ba,tabbas basu san wace aisha ba,da sun fadi abinda sukeso kawai cikin girma da an basu,albarkacin igiyar auren data taba gittawa tsakanin d'ana da d'iyarsu" ta furta a sarari,tana miqewa,sai a sannan taji duk wani nauyi da kanta yayi,da cushewa da cikinta yayi ya warware,har taji wata yunwa,sannan taji tana buqatar abinci,don haka tamiqe ta fito don bada umarnin a gabatar mata da abinci.

¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

Hakanan cikin daren bacci suka qauracewa idanuwansa,ya takurawa kanshi da tuhuma da tambayar me yake damunshi ne haka a kanta,sau nawa ya ganta da zata zauna haka cikin zuciya ruhi da kuma gangar jikinsa,har yake jin kamar yabar wani abu nashi tattare da ita?,kodon itace mace ta farko daya soma sharing ainihin abinda ake kira da rayuwa da ita?.


A hankali ya dauko wayarshi dake dake aje a gefe,hakanan saiya samu kanshi da bude tsohon saqo,tsohon saqon da bai sake bi ta kansa ba tunda aka turo mishi,tsohon saqon da bai taba tunanin xai waiwayeshi ba,sai gashi yau ya samu kanshi da budewa,saqon da ammi ta tura masa na hotonta tun lokacin da ake zancan hada aurensu,yana tunanin idan ya gan hoton zai samu relief.


Saidai tunaninsa ya saba,wani irin abu yaji yana ratsa zuciyarsa,wani irin feeling mai kama da kayi kewa da abinda kayi matuqar sabawa dashi,hankalinsa ya sake tashi fiye da dazun,don haka ya aje wayar ba tare daya fita daga gun hoton ba ya miqe.


Bandaki ya fada kai tsaye,ya sakarwa kansa ruwa,wanka yayi cikin mintina ashirin,sannan ya fito ya soma shiryawa.


Cikin lokaci qanqani ya gama shirinsa cikin wani kyakkyawan yadi da yaji aikin sarauta,yayi masifar dacewa dashi hakanan ya fidda ainihin shi din waye,sai da yagama feshe jikinsa da turarukansa sa'annan ya duba agogo,ya tabbatar yanzun ammi batayi bacci ba,idan ma ba abincin dare take ci ba,to bata jima da gama ci din ba,mai yiwuwa suna falonta ita dasu afnan,kamar yadda takan zauna dasu a yawancin lokuta.
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 41
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*
*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*
*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070
___________________________





Cikin sati guda rak wani irin laulayi mai azabatarwa ya rafeketa ba tare da ita kanta tasan laulayin take ba,don sam anty zuhriyya ta kasa gaya mata,gani take abun saiyayi mata yawa,babu abinda take iya ci ya zauna cikinta qalau,koda ruwa ne sai anci babbar sa'a bare akai ha abinci,hakan ya sanya koda yaushe cikin qarin ruwa take,ta zabge ta sake yin wani fari bau,gefe daya ga wata rama ta musamman datayi,dukka kayanta basa zaunar mata a jiki sun mata yawa,don wani lokaci rigunan najwa zuhriyya ke kawo mata ta saka,saboda tana da dan jiki,hakanan batanson hayaniya ko hasken rana mai yawa,wani irin azababben laulayi daya sanya anty zuhriyyan ta dinga mata kuka a boye,idan ka ganta saika zaci ba zatayi raiba saboda yadda take azabtuwa,itakam.har fatan cikin ya zube anty zuhriyya takeyi cikin ranta
"Wannan baqar qaddara taki Allah ya yanke miki ita bilkisu" haka take yawaita fada,saboda ganin irin yadda takeshan wahala da cikin da batasan ma yana maqale a jikinta ba.


Wata guda cur da satittika wajen uku sukayi a asibitin,sannan aka dan fara samun sauqi,har zuwa sannan batasan da wani ciki ba,saboda bata cikin nutsuwarta bare hankalinta da har zata lura da wani sauyi ko wata alama.


Da wani yammaci ta farka a bacci da wani irin fitsari daya matsota,a lokacin anty zuhriyya tana sallah,idan tana wajen duk sanda zata bandaki saita rakata,qaunar ummin na sake qaruwa cikin zuciyarta dakuma tausayinta,yadda take mata ko najwa ce iyaka abinda zatayi mata kenan a matsayinta na uwa,ta aje dukkan wasu harkokinta ta tattara a wajenta,hatta da gida saidai taje lokaci bayan lokaci ta dawo asibitin,duk hankalinta da kulawarta tana kanta.


Ganin yau jikin nata da qwari qwari ya sanya ta zuro qafafunta qasa a hankali,ta saka takalmanta ta miqe zuwa bandakin,don yau itama ta tabuka ta ragewa ummin aiki.


Tana zuwa fitsari sai taga jini,batayi wani mamaki ba,ta kawo a ranta period dinta ce tazo
"Dama naga kamar tayi jinkiri wannan karon bata zo akan kari ba,ko saboda ciwon nan ne" ta fada tana yin tsarki sannan ta miqe,amma sai taji mararta ta riqe,tadan cije bakinta,ikon Allah,tasan bata ciwon mara idan tana al'ada,amma yaya akayi yau mararta ke mata ciwo?,ta tambayi kanta tana fitowa daga bandakin a daddafe.


Sanda ta fito ummi zuhriyya ta gama sallar carbi take ja,ta zuba mata ido ganin yadda ta fito a duqe,da sauri ta tambayeta
"Lafiya daughter" saidata zauna gefan gadon sannan tace
"Marata ce take ciwo ummi,kamar period ne inaga"
"Periode?" Ta tambaya cikin fargana da faduwar gaba,saita gyada kanta
"Eh"
"Jini kika gani!" Ta fada tana miqewa a hanzarce har bilkisu na mamakin dalilin rudewarta haka,saita sake gyada mata kai
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta furta sannan ta durfafi qofa da hanzari,binta kawai tayi da kallo cike da mamaki,toko bai kamata ace tana period bane?,tayiwa kanta guntulalliyar tambayar da bata da amsa.


Sanda likita ya iso ya dubata saiya tabbatarwa da anty zuhriyya wahalar data sha ne bakin mahaifar ke niyyar budewa,saboda haka dole su bata bedrest again kona wata daya ne su gani.


Lokacin da suke bayanin kawai kallonsu take,kanta a daure tamau,ta kasa fahimtar komai,mahaifar waye zata bude?,waye keda ciki?,kuma wa za'a bawa bedrest?,duk da tambayoyin dake cin kanta bata iya furta ko guda daya ba,taci gaba da binsu da kallo ne harya gama abinda zaiyi ya fice,dakin ya rage daga ita sai anty zuhriyyan.


Ta lura da dimuwar da bilkisun ta shiga,da yadda take dan kallonta,da alamu tambaya ce fal kanta,tasan dama dole hakan zata kasance,tunda taji wasu magangun da bata gane kansu ba daga bakin likitan,don haka saita janho kujera zuwa bakin gadon da take kwance,ta zauna idanunta kan bilkisun,tana wassafa tare da tsara yadda zata mata bayanin da zai kwantar da hankalinta,duba da yanayin da take ciki,saboda rufewar ba zata amfana komai ba,face sanyata cikin tunani da kuma wani rudanin na daban.


"Daughter....nasan a rayuwa,daga sanda nake tare dake zuwa sanda bama tare,kin fuskanci abubuwa da dama arayuwarki,kin kuma rasa abubuwa da dama,kuma dukka kin juresu,rayuwa mataki mataki ce,kowanne mataki na jarrabawa idan yazo.maka kayi haquri kana iya cinyeshi yakuma wuce kamar ba'ayi ba,komai yayi farko tabbas yana da qarshe,kiyi haquri bilkisu....kina da juna biyu,wanda shine kusan silar ciwonki" wani irin abu taji yazo ya cake mata a maqoshi,ba don babu wasa tsakaninta da anty zuhiriyya ba da sai tace wasa antyn take mata,amma tasan babu wannan tsakaninsu,wani irin abu takeji yana mata yawo saman ka,kalaman antyn suna bangazar juna kamar xasu wargaza maya qwaqwalwa,saita rintse idanunta tana furta
"La haula wala quwwata illa billa" daga haka bata sake furta komai ba,bata sake cewa komai ba,saidai wani abu daya tsaya mata a wuya bata samu ya sauka ba har sai ranar da aka sallameta daga asibiti,sanda ta isa dakinta ta kwanta saman gadonta ita kadai,tana lissafin abinda yake cikinta,cikakken dan halas ne ko kuwa akasin haka?,ina ubansa?,tananda tutiya ko zarrar da xata nuna ubanshi harta furta shine yayi mata cikin da take dauke dashi a yanzu?.


Kuka ne mai wani irin nauyi a qirji da zuciya ya kubce mata,ashe haka matan dake yin cikin shege suke ji?,ashe haka suke tsintar kansu?,wanne irin bayani zata yiwa 'ya ko dan cikinta a duk sanda ya girma ya nemi mahaifinsa,shin ta yiwa rayuwasa ko rayuwarta adalci?,ta hanyar data cancanci a samar dashi kenan?.


Wadanne irin mutanene wadan nan da babu halin girma ko dattako cikin jininsu?,wadanne irin azzalumai ne su da suka zabi rayuwarta cikin miliyoyi suka tarwatsa ta,meta musu ne haka suka hanata cimma dukkan wani buri na rayuwarta,matsalarsu dai a kullum ita ke dakatar da ita daga samun duk wani ci gaba,a duk lokacin data yunqura don ci gaban rayuwarta saisun daqileta,wancan karom sune silar karatunta,wannan karonma dukkan alamu sun nuna sune zasu zame mata tarnaqi.


Tayi kuka mai yawan gaske,irin kukan data kwana biyu bata yishi ba,har zuwa wayewar gari,yadda idanunta suka tasa ya sanya anty zuhriyya ta fahimci irin kukan data yi,fada sosai ta dinga yi tana bala'i,saboda har yanzun ranta a bace yake itama,wani da bilkisu take kan me yasa zata zauna tana kuka,yayin da mafi yawa kuma dukka kan masarautar kaisa ne,wanda basusan halin da ake ciki ba.


Sai data gama son ranta sannan ta sauko,taci gaba da lallashin bilkisun tare da kwatanta mata illar bacin rai da damuwarta ga lafiyarta.


Ba qaramin jajircewa anty zuhriyya tayi ba wajen ganin ta daidaita lamari da yanayin bilkisun,wanda sai bayan kwanaki data tabbatar ta sake warwarewa ta nemi abbaa ya bata izini zataje tayi magana da malam bilya,daga nan su sanar da masarauta,don ta inda aka hau ta nan ake sauka,bai musa ba mata ba ya amince mata,don haka ta sanya lokaci yammaci liqis sanda tasan za'a iya samunsa a gida ta sanya bilkisu ta shirya suka nufi gidan.


Cikin doguwar riga take purple,saqar qasar dubai,ta yafa mayafin doguwar rigar kawai saman kanta ba tare data nannadashi ba,mai kawai da turare ta sanyawa jikinta,amma idan ka kalleta sai kaga ta qara wani kyau na musamman,kai kace an mata amfani ne da wasu kayayyakin gyaran fata na musamman,saidai tana nan babu qiba ko kadan tattare da ita,plate din takalmi kawai ta zira,ko wayarta da anty zuhriyya ta sauya mata zuwanta gidan bata dauka ba ta fito suka wuce,daga ita sai antyn sai hisham wanda bilkisu ke riqe dashi saman cinyarta,antyn tana tuqi.


Sanda suka isa gidan ana kiraye kirayen sallar magariba,wasu da yawa sunata daura alwala suna tafiya zuwa masallaci don samun jam'i.


Suna shiga gidan bayan sun faka motarsu qofar gidan malam bilya yana fitowa daga cikin gidan,cikin hanzari jikinsa jiqe da ruwan alwala,yana ganin zuhriyyan gabanshinya fadi
"Jarababbiya masifaffiya,ko dame kuma tazo" ya fadi,amma gefan ranshi yana jin dadin yadda bikisun ta warware sarai fiye da sanda ya ganta a asibiti.


Itace ta soma magana
"Munzo ganinka,gashi kuma kana shirin fita" tayi maganar fuskarta a daure tamau,wannan furucin ya sake sanyawa gabanshi ya fadi
"Da wata aqasa kenan" ya fada a ranshi
"Ku shiga ku jirani,zanje nayi sallah na dawo" bata amsa mishi ba ta juya tayi ciki,tabar bilkisu na gaidashi kafin itama ta biyo bayanta.


Umaima da aminatu ne a falon da alama salla suma zasuyi,,suna ganinta kowacce tasoma rige rigen isa wajenta,suka rungumeta cikim jin dadi,itama rungumesun tayi tana jin dadi,don tayi kewarsu sosai,tunda tabar gidan anty zuhriyya bata sake barinta tazo gidan ba,saidai tayi musu dukkan abinda tace zata yi musun,kuma taga alamun sauyi da canji tattare dasu,bata taba kawowa cewa qaddara zata sake rabasu ba,ba zata sake barinsu su zauna tare ba.


Murnarsu ta fiddo da hannatu dake cikin bandakinsu tana musu wankin unifoarm,itama murna ce ta cikata,suka baibaye bilkisun kowa yana son bata labarai gami da tambayoyi,anty zuhriyya na zaune saman kujera tausayinta na ratsasu,ta wani fannin kuma suna bata matuqar sha'awa na yadda suke qaunar junansu da kuma yadda suka saba,bata ankara ba taga tuni sun janyeta zuwa dakinsu,saita saki murmushi kawai tana kada kai.


Murmushin nata ya katse sanda anty ta shigo falon,sai anty zuhriyyan ta hade ranta tsam,don ta gama karanatar kowaccensu,itama antyn bataga wajen wargi ba,don haka ta gama abinda ya shigo da ita kawai ta fita.


Babu jimawa umma katti ta shigo,saita soma washe baki ganin zuhriyya,ita kuwa babu abinda ya sauya dangane da yanayin fuskarta
"A'ah,zuhriyya ce a gidan namu?"
"Nice" ta bata amsa a taqaice
"Maraba lale,kyazo ki zauna shuru ke kadai,aiko bamu zauna da maimunatu ba kya nemeni" wani kallo tayi mata tana tabe baki,rainin hankalinta ma yaso zarta na kowa,saidai duka zataji dasu,sa'arsu daya ma yanzu bata tasu take ba,da kowacce saita kwashi kashinta a hannu,don tanajin ciwon riqon da sukewa diyoyin mijin nasu,riqo na zallar jahilci qauyanci da kuma son kai.


Banza ta baiwa ajiyarta harta gama sunadin surutunta,wanda yafi kama da tabarmar kunya tabata waje sanda malam.bilya yake shigowa ya umarci a bashi ruwa yasoma sha tukunna,mama ladi dake da girki ta nufi kitchen don kawo masa.


Tana daga zaune anan ta qwalawa bilkisu kira,ta kuma jiyota,sai gata ta fito,ta qaraso a hankali ta samu gefan anty zuhriyya ta zauna,kanta a qasa,batasan yaya baban nata zai amshi lamarin ba,kuma ta yaya za'a samu warwarar qullin.


Duban gefanta tayi ganin mama ladi xaune dafa'an,bisa dukkan alamu tana nufin gabanta za'ayi zancan kenan,don haka ta dubi malam bilya
"Kaman baka shirya zaman ba,don naga wadanda ba ahalin maganar ba zaune a wajen" ya gane sarai dawa take,don haka ya dubi ladi
"Ladi...bamu waje" haushi ne ya cikata,haushin zuhriyya take ji,don ta fuskanci bata daukar raini,hakanan bata daukesu a bakin komai ba
"Kome meye muna zaune zamuji" ta fada tana shirin fita
"Daga baya kenan,wai anyi sadaka da karuwa" anty zuhriyya ta bata amsa.


Sai data fice sannan ta dawo da dubanta kanshi,takaici yana cin ranta tace
"Malam bilya,shukar da kayine nazo shaida maka lokacin girbinta yayi,wala'alla babu wannan cikin tsari hasashe ko shirinka ko?" Dubanta yake cikin rashin fahimta,sai kuma ya hade rai wai karta kawo masa wargi ko raini
"Kamar yaya,me kike nufi?,kefa baki rabo da jarfa,idan zakimin bayani kiyimin" gyara zamanta tayi yana amsa mishi
"Shi zan maka yanzu" sai taga baima kamata aci gaba dayin maganar a gaban bilkisun ba,saboda haka tace tatashi ta koma,cikin matuqar mutuwa da sanyin jiki ta miqe ta fice daga falon.


"Diyarka kuma diyar maimunatu da ka bada hayarta...don haya shine sunan da yafi dacewa da aurenta,taje ta kuma dawo maka da tsarabar jika,in sauqaqe maka dogon nazari,yanzu haka juna biyu gareta" wani irin gumi ne me dumi ya karyo masa,idanunsa dukka a waje yace
"Kamar yaya zuriyya,me kike fada ne?"
"Abinda kunnuwanka suka jiye maka" ta maida masa cikin gatse da matuqar jin haushinsa. Baisan sanda ya zame hular kanaa ba yahau firfita gami da ambaton
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".


_afwan,kuyi manage yau yayi guntuðŸ™ðŸ½ðŸ™ðŸ½_

_ale bilya na gaisuwa,yace ku tayashi da addu'a🤲ðŸ½ðŸ˜_
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 43
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070



Kamar yadda ya zata din kuwa,sanda ya isa sashen ammin tana saman katafaren dining din da aka cika da nau'in girke girke tana cin abincin dare,afnan kuwa na saman kujera zaune riqe da handout tana dubawa,daya daga cikin bayin dake aiki a sassan tana duqe gabanta tana gyara mata qafarta,sai sumaira dake kwance saman kujera tana charting,sanyin ac ne gaba daya ke ratsa falon,sai tv dake aikinta ita kadai ba tare da kowa ya damu da ita ba a cikinsu,don kowa da akwai abinda ya sanya a gabanshi.


Sallamarshi kadai ta saka kowa cikin taitayinsa,baiwar ta zube ba tare data iya kallonshi ba ta soma gaidashi,hannu ya daga mata,kana ta miqe cikin sauri da hanzari ta soma tattare kayan amfaninta,don dama ta gama yiwa afnan din
"Barka da warhaka yaya" duka suka hada baki wajen fada tsakanin afanan da sumaira,cikin qasaita muryarsa can qasa ya amsa musu,afnan ta kare fuskarta da littafi kana murguda baki tana hararar sashen da ya nufa wato wajen ammi fulani,cikin ranta tana mita
"Wannan duk randa ya zama sarkin ma ai mun kade,kullum fuska kamar kashin shanu,amma duk da haka ya sake dado wani daurewar fuskar saboda mugunta". Sumaira kam tuni ta sauko ya kwashe headphone dinta da charger dinta ta wuce daga falon da nufin sauya falon,sai afnan din kawai ta bari,wanda dama yawancin lokaci ita kadai ce ke iya zama waje idan yazo wajen ammin tasu.


"Barka da warhaka ammi" ya fada bayan ya zauna kan kujerar dake fuskantarta
"Ka yini lpy" ta jefa masa tambayar tana sake mamakin yadda gaba daya cikin lokutan take ganin sabbi da baqin al'adu tattare dashi,duk da ta sani cewa shi din miskili ne,wanda bayason yawan magana,mai qarancin fara'a,amma dukka wadan nan halayen nasa sun sake qaruwa tare da daukan sabon salo
"Lafiya alhmdlh" ya amsa mata,saita aje cokalin hannunta,tana hade hannayenta waje daya
"Kullum nakan qaryata lafiyarka da kwanciyar hankalinka,don yanayinka da fuskarka basu nuna hakan" sai daya dan kalleta,kana ya kauda kai
"Babu komai fa" shuru tayi kamar mai tantama akan maganar,sannan tayi ajiyar zuciya,ta dauki cokali ta soma ci gaba da cin abincinta ta sake cewa
"Amma....meya hanaka har yanzu ka zabi makarantar da zaka ci gaba da karatunka?"
"Ina nazari ne har yanzu" tsaida taunar da takeyi ta dubeshi
"Nazari kamar yaya?....kaga....na baka nan da jibi,lallai lallai kazomin da sunan makarantar daka zaba,kuma ba'a qasar nan ko maqociyarta ba"
"To" kawai yace mata,don ya kauda yanayin saiya miqa hannun ya dauki tataccen ruwan inibi dake cup,wanda ammin ta zuba da niyyar sha ya soma kurba.


Rabin kofin yasha sannan yadan kira sunan afnan,ta amsa tana aje handout dinta ta taso,da hannu ya mata nuni ta zuba masa abinci,ta tsani wannan miskilancin nasa,dom haka saita nuna kamar bata fahimta ba,maimakon ya bata amsa saiya dauki wayarshi ma ya soma latse latse ya barta nan a tsaye,saida ammi tace
"Ki zuba mishi mana kin tsaya saman kan mutane" qafa tadan buga sannan ta zumbura baki ta soma zuba mishin,ta gama

Please Login or Register in order to submit comment