Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunan da akeson mana,shine ke kuma zaki shigomin da wasu kalaman banza" murmushi ta saki
"Kimin afuwa,ki kuma yafemin,ba yarfe ko bata suna bane ya kamata ace ya dameki ba ammi,saboda dama duk nisan jifa qasa zai fado,hakanan komai daren dadewa dole wannan sirrin ya fito....abinda yafi dacewa ki damu dashi shine,yadda kika sarrafa rayuwar baiwar Allah ta hanyar da kikaso,sannan kuma yaya rayuwar tata ta kasance bayan nan?,naga bakya qauna ko kusa atuna miki ta taba zama surukarki ko ammi?....to yanzu dai hanyoyi guda biyu suka rage mu daga ragowar martaba da qimarmu...na farko....inma ki fita ki shaidawa duniya cewa wannan din tsohuwar matarsa ce da suka taba aure,an dauki hoton sanda suke a matsayin ma'aurata duk da nasan ba haka bane,to amma ta yaya zaki musu bayanin yadda auren ya gudana?,shin zasu gamsu?,tunda basu da masaniyar sanda aka qullashi?,.....wa imma kuma ki bar mutane kowa yaci gaba da tofin alatsine garesu gami da aibatasu,ana mata kallon karuwa da kwartonta,wanda aikata hakan kamar qarin wani zunubinne akan wani,kuma shizai qarasa rugurguza martaba da qimar da kiketa mana tattalinta....." Tsawa tayi saurin dakawa afanan,tanajin kanta ya soma yamutsewa,dukkan idea na kubuce mata daya bayan daya,saita nuna mata qofa da yatsa
"Fita ki bani waje tun bsn bata miki ba" murmushi afnan ta saki ta soma takawa zata fita din kamar yadda ta buqata
"Ke mahaifiyata ce da bani da kamarki,hakanan bazanso naga kin shiga kowanne irin hali ko yanayi mara kyau ba shi yasa na tunkareki da wadan nan maganganun,kiyi haquri ki dubasu dakyau tun lokaci bai qure mana ba" daga haka ta fita din kamar yadda ta buqaceta.


"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ta soma ambata a fili,kana ta zame ta zauna gefan gadonta tana zame dankwalin kanta da takejin ya mata nauyi,yaya akayi tayi sake haka lamura suka kwabe mata ne?,wannan itace babbar tambayar da take jifan kanta da ita.
7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 64
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070



Kusan cikin dakin ta wuni,har sanda akayi sallar la'asar,ta soma jiyo muryar mai martaba cikin masallacin dake cikin gidan,yana daura auren wasu daga cikin barorin gidan maza da mata da suka samu mazajen aure,wanda yake kamar aikinsa ne,ya dorwa kansa alhakin aiwatar da haka duk shekara indai aka samu masoyan da suka daidaita kansu,yakan sanya a hada bikin daba din da bikin auren nasu,hakanan shike musu komai na aure,yakan ce Allah ya sanyasu ne qarqashinsu domin muma muyi musu hidima,ya sanya wasu daga cikinsu sun zama bayi a garemu,bayan ga mahaliccinsu kawai wannan bauta take,kyautatawarmu a garesu shike nuna zallar godiyarmu ga mahaliccinmu kan ni'imomi da baiwa daya mana masu tarin yawa.


Kusan duk abinda zaiwa barori matan da shawara da kuma sanya hannun fulani aisha yake aiwatarwa,wanda kusan ita ta qarfafi wannan shawarar tashi tun shekarun baya,takan kuma sanya itama nata kason a cikin hidimar masu kayan aure,badon mainartaba ya gaza ba,a'ah,tana yine da sunan sadaka da kuma neman lada,saidai a wannan shekarar kusan komai saidai taji labari,don bata da wannan nutsuwar,illa kudin dai data saba bayarwa bata fasa ba.


Sai da aka gama daura auren kaf a kunnunta sannan ta miqe da qyar ta shiga bandakinta dake cikin dakin ta daura alwala ta tada salla,koda ta idar tana saman abun sallar tana tunane tunane,ta duba lokaci,taga akwai sauran kusan awa guda daga sanda zasu isa wajen maimartaba,don haka taci gaba da xama saman abun sallar tata.


Saidai me?,bata jima ba saqo ya risketa ta hanzarta zuwa sassan mai martaba da gaggawa yana da buqatar ganinta,ta zuba jakadiyar idanu gabanta na wani matsanancin faduwa,yanayin yadda aka kawo mata saqon yana nuna kamar ba lafiya ba.


Alkyabbarta kawai ta zura wadda ke aje tun daxun a gefe,sabanin daa da saita tsaya ta sake wanka,ta kuma fesa ado na qasaita,irin adon da tasan mai martaba na mutuwar so,irin adon da tasan zai tafi da hankalinsa,saidai a yanxun duka bata jin wannan nutsuwar.


Tun a hanya ta lura da yadda masu satar kallonta suka yawaita,tun a nan dukka wani karsashi da qwarin gwiwa da take baiwa kanta ya soma bajewa yanayin nasa guri,tana tattaroshi amma yana sake sulalewa,da haka ta isa ga sassan mai martaba,kana ta qarasa kai tsaye ga turakarsa.


"Wannan babban abun tashin hankali ne a garemu baki daya.....abun kunya tur da ala wadaine,tun sanda nasamu saqon na kasa samun nutsuwa bare barci,abdul'azeez fa Allah ya taimakeka?" Abinda ta soma tsinta kenan daga muryar adama,wadda ke zaune gaban mai martaba tana sharce qwalla.


"Ya Allahu,ya naseru"ta furta cikin ranta,tana neman daukin ubangiji sanda suke hada idanu da maimartaba,wanda bisa alamu shigowarsa sasaan nasa kenan,ya soma rage kayan jikinsa adaman ta cimmasa,don bai gama fidda kayan da yayi hawan gaba daya ba.


Karon farko a rayuwarta dataji ya mata wani mugun kwarjini,irin kwarjinin da takanji jama'ar da yake mulka wadanda suke qarqashinsu suna labari lokaci zuwa lokaci,gwiwa a matuqar sanyaye ta dauke kanta daga adama daketa hada hawaye bilhaqqi,ta isa gabanshi ta zube cikin sanyin jiki qwarai da sanyin murya tace
"Barka da warhaka"
"Barka kadai aishatu" ya amsa mata cikin kulawa yana jin tausayinta a ranshi,saboda ya lura da yadda jikinta yayi sanyi qila itama ta samu labarin komai katsam kamar yadda ya samu,yake raya haka a ranshi,saidai kuma,akwai alamun bacin rai a muryarshi da yake dannewa sanda yayi maganar.


Kai tsaye ya miqa mata hotunan data tabbatar cewa sune,ta kuma soma gajiya da kallonsu,don ba azeez da yake danta ba,hatta da bilkisun ta haddace dukkan surori da kuma kamanninta tsabar kallon hutunan.


Kamar ba zata karba ba,sai kuma ta tuna aikata hakan kamar bada wata qofa ko dama ce ga adama dake zaune a gefanta ta zuba mata idanu kamar tsohuwar mayya,wanda ta tabbatar tanason ganin reaction dinta ne kawai,don haka tasa hannu biyu a hankali ta karbi hotunan,ta dawo dasu gaban idanunta,tayi kamar ta kalla kana ta kifasu saman cinyarta tana fadin
"La haula wala quwwata illa billah" tana rufe idanunta saboda yadda taji zuciyarta na wani irin bugawa



"Hmmm...ana zaton wuta a maqera,sai haquri,yaran yanzune ka haifesu amma baka haifa halinsu ba" adama ta soma zuba,mai martaba ne ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana kallon aisha
"Kina da masaniya kan wani abu daya danganci hoton?" Ta yaya zata amsa masa gaban wannan makira kuma azzalumar matar,wanda daga shigowarta zuwa yanzu ta fahimci ita ta shirya komai,sannan tayi tattaki ta kawo masa hotunan har dakinsa,don haka kawai saita girgixa kai alamun a'ah.


Dauke dubansa yayi daga gareta,kana kai tsaye ya janyo wayarsa ya soma laluben lambar abdul'azeez kai tsaye.


Daidai lokacin da yake xaune falonshi,kace kace tsakiyar takardu laptop da wayoyinsa,bayan ya gama tsara da jiran awannin tafiyarsa su cika.


Wayoyi yake amsawa tare da kira,yana kuma tsarawa kansa hutu da na tsahon wata guda daga dukkan kamfanoninsa da harkokin kasuwancinsa,yana tura takardun inda sukka dace su sani,yana kuma nada wakilansa,sabida a hasashensa yana saka ran zuwa wata guda mai zuwa ya gama settling komai,yana fatan hankalinsa ya soma dawowa jikinsa.


Da sauri sauri yake komai,saboda yana riqe da awannin da suka rage masa na tafiya airphort don sauka a qasarsa nigeria.


Wayar dake hannunsa ce ta dauki ringing,ganin sunan mai martaba ya sanyashi sake nutsuwa,ya ajjiye biron dake hannunsa ya kwantar da bayansa a makarin kujerar sannan ya daga wayar cikin girmamawa da nutsuwa.


Baice masa komai ba har suka kammala gaisawa,kana yace
"Inason a yau ka nemi jirgi duk inda yake,ka tabbatar ka kwana a masarautar kaisa" umarnin daya soma bashi kenan,duk da yayi mamakin hakan amma saiya danne yace
"In sha Allahu nan da awa hudu zan iso qasata"
"Allah ya nuna mana" ya fada yana katse wayar,idanunsa kan adama,tariyar maganganun da abubuwan data gaya masa masu yawa ke masa kai komo kan yaron nasa,bayason yace komai bisa zargi,bayason ya yanke komai bisa labari kawai,hakanan bayason wai wai da ance ance,amma magangun data gaya masa kan yariman ba qananu bane,duk da haka shidin babba ne mai hankali,kuma jagora shugaba,yana da buqatar nutsuwa da kwantar da hankali kan duk wani hukunci da xai yanke
"Dukkanku kuje,zan sake nemanku" ya sallamesu gaba dayansu,don yana buqatar yin nazari sosai.


Wayar azeez yabi da kallo bayan maimartaba ya katse,saiya saki ajiyar zuciya yana sake kwanciya sosai,gefe guda kuma yaji ya sake qaguwa daya isa nigeria,tuni ya gano inda bilkisu ta yada zango,yanajin kuma shine abu na biyu da xai gabatar bayan ya saurari mai martaba,sabida yana da yaqinin akwai dalilin da yasa ya kirashin ya kuma nemi tahowarsa again bayan wanda mahaifiyarsa ta buqata.

¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶


Ba abinda take sai kaiwa da kawowa tsakanin falukan nata ta dangane da daki cikin tsantsar tashin hankali,tashin hankalin da bata taba shiga makamancinsa kamar yau,ji take inama ace zata iya tsaida komai cak ta kuma sauyashi zuwa dai dai,zuwan abdul'azeez ba qaramar barazana bace a wajenta,gashi mai martaba bai gaya masa dalilin kiran nashi ba bare ya dauki haske,ko kuma tun acan ya gama tsara abinda zaya gaya mishi idan ya iso,uwa uba tanata kiran wayoyinsa gaba daya sunqi shiga,alamu ne dake tabbatar da cewar yana hanya kenan,koya gama shirinsa na baro qasar daga yanzu zuwa kowanne lokaci,idan da so samune zataso ace ita ta soma tozali da azeez din,don suyi magana,su kuma san ya zasu bullowa lamarin,ta yadda komai bazai kwabe ba.


A wannan yanayin taci gaba da kasancewa,har zuwa lokacin da akayi sallar magariba,sam yaranta sun kasa gane kanta,don basusan meke faruwa ba,bayaga afnan ita kadai,wanda itama babu wanda ta shaidawa banda mama sodangi.


K'arfe uku na dare agogon brasil,takwas na dare agogon nigeria ya taso zuwa nigerian,sam sai yakega kamar jirgin baya sauri,tafiyar awanni taran ya dinga jinta kamar tafiyar shekaru tara,duk bayan wani daqiqa yana jin kamar ana sake kusantashi da bilkisune da ahalinsa,yana ji a jikinsa wannan tafiyar kamar wani mabudi ne da warwara na dukka matsalolinsa.


Ga fulani kuwa kusan kwanan zaune tayi,dukkan wani tunani da idea nata sun watse,abu na qarshe data zabawa kanta yi shine,ta kira daya daga cikin malaman da suke mata sauka,ta shaida masa tana da damuwa ayi mata sauka daga nan zuwa safiya a yi sadaka,ta aika mishi da kudin saukar kamar yadda ta saba lokaci bayan lokaci.


¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶



Ana kiraye kiraye na sallar asubahin nigeria cikin masarautar kaisa motarsa ta soma shigowa babban ginin masarautar,wanda ke nuna zallar sarauta da alfarma gamida qarfin mulki da gidan sarautar keda shi tun tale tale,hakanan har yanzu yana nan bai gushe ba.


Kai tsaye sassansa ya nufa kamar yadda ya yankema ranshi,yana ganin yanzu yayi safiya da yawa ya nemi ganin wani cikin mahaifansa ko makusantansa,wanda yana da tabbacin zaije ya samu komai a sassan yadda ya kamata,duk da cewa safwa ta shaida masa ta koma tun shekaran jiya,amma akwai wadatar ma'aikata,barori da bayi.


Kamar kuwa yadda ya zata din,komai na killace cike da tsafta da tsari,sai ka zaci akwai dan adam a sassan,yayi masauki a katafaren dakin gadonshi wanda yake dai dai da aljannar duniya.


Abu na farko daya fara hada ruwan wanka mai dumi sosai wanda zai dace da yanayin da yakeso,yayi wanka sosai,yanayi yana duba lokaci,duk da yasan da wuya ya samu jam'in sallar asubar,don yaji sanda suka tayar.


Jallabiyya kawai ya sanya ya tada tashi sallar,bayan ya idar baiyi gaggawar tashi ba kamar yadda ya saba,saidai yau zaman nashi ya banbanta dana kullum,hakanan yaji ya dade saman abun sallar yana addu'o'i,qari akan wadanda ya saba,baibar saman abun sallar ba,sai daya duba lokaci,yaga yayi dai dai da lokacin da maimartaba kan zauna da duka ahalin nasa a irin wannan safiyar ta washegarin hawan daba,duk da baccin da yakejin yana fusgarsa sama sama amma haka ya yakiceshi,yahau shiryawa sosai cikin shigar dake bayyana gadon sarauta gaba da baya,jinin mulki da qasaita,shigar data qara masa kyau qima da kuma kwarjini qwarai da gaske.


Duk wannan abun dake faruwa tun daga shigowarsa masarautar har isarsa sassansa fulani adama nada labari daga mutanenta data baza,saboda ta tabbatar yariman zaya iso kamar yadda yace,daga sanda maimartaban yayi kiransa zuwa kowanne lokaci za'a iya ganinsa.



Murmushin jin dadi ta saki lokacin da ake shaida mata ya riga daya iso din,a hankali ta furta
"YAU ZATA FASHE!" Abun yana mata dadi sosai cikin rai,tana hango tozartar aisha ayau din,don haka ta janyo wayarta ta shaidawa haj fauziyya dake nata sassan wanda takan sauka duk sanda tazo,daga can ita kuma ta kira kamal,suka gama dukka tsare tsarensu ta hanyar wayar.


Cikin dauriya da dakiya,da kuma rashin son baiwa abokan gaba qofa da zasu fahimci galaba akan dukkan tsarinsu a safiyar fulani aisha ta shirya,cikin shigarta dai tayau da kullum ta qasaita dake tsone idanun abokan xamanta,saidai a yau din maimakon alkyabba,tsadajjen mayafi na musamman ta nade jikinta da lallausar atamfar da tayi adonta,ta kuma iso katafaren dakin cin abincin da aka tanada saboda ranaku ire iren wadan nan cikin yaranta da 'yan jikokin da aka haifa mata.


Kusan kowa cikin walwala yake a wajen idan ka debe ita,duk da tayi qoqarin qaryata hakan akan fuskarta,da kuma qoqarin da tayi ta aro walwala ta saka fuskar tata,saidai kallo daya mai martaba yayi mata ya fahimci ainihin halin da take ciki,saiya alaqanta hakan da abinda ya faru jiya,wanda koshi din zuciyarsa ta cika da damuwa,damuwar kada ace gudan jininsa da yake saka ran xai gajeshi,gudan jininsa da duniya duka take kallo take kuma sake tambara sunanshi da matsayinsa ya jawo musu wani abun fada da zai rusa darajarsu da martabarsu,hakan har a ransa yaji tausayin aishan,saboda yasani cewa tana da tsaiwa kan 'ya'yanta,don haka saiya yawaita sakota a hirar tasu.


Duk da wajen akwai surutai na tashi,kowa na hirarsa da wanda tasu tafi zuwa daya,amma saratu da adama na ankare,kowacce kuma abinda take saqawa cikin zuciyarta daban.


Sallamarsa cikin dakin yasa surutan suka dauke cak kamar anyi ruwa an dauke,hakanan numfashin fulani aisha yaso daukewa cak itama,cak ta tsaya tana addu'o'i cikin ranta,addu'o'in Allah ya sanya bashi bane,Allah yasa kunnuwanta ke mata gizo,duk wannan addu'ar da take ta kasa waiwaya ta tabbatarwa idanunta abinda kunnuwanta suke ji din.


Daidaiku ne suka amsa sallamar tashi,ciki harda me martaba daya zuba mishi idanu cikin zuciyarsa shima yana addu'ar Allah ya sanya abinda ya gani din ya zama ba gaske bane,jikinsa yaji yayi sanyi sanda suka hada idanu da me martaba,kusan yana daha cikin mutanen da suka san halayyarsa tsaf,suke iya gane magana daga idanunsa kafin ya fadeta.


Kamal shike zaune kan kujerar da a qa'ida nan ne wajen zaman azeez din a duk lokaci irin wannan,yauma bai fasa nufarta,idanunsa cikin na kamal din,kamar yadda kamal din shima ke kallonsa.


Mai guri yazo dole me tabarma ya nade,hakanan yanaji yana gani ya miqe ya bashi wajen,ya koma kujerar dake kusa da ita,yana qwafa cikin ransa gamida fadin yau dai za'a yita ta qare ko?.


Cikin girmamawa ya gaida dukkan wanda ya girmeshi a wajen,saura dake qasansa kuma suka gaidashi harda yayyensa mata da tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,duk da ransu baison hakan amma dole suka gaidashin,musamman walida da takejin kamar ta ciji harshenta,batasan me yasa suke raina kwanaki arba'in da wani abu data bashi ba,duk tsiya aidai ta girmeshi.


Baima san me suke ba,don cikin kulawa ya maida hankalinsa ga iyayensa yana tambayarsu lafiyarsu,hakanan kowanne ya danne abinda ke ranshi ya amsa mishi,daga haka cin abincin yaci gaba da gudana,amma saidai hirarrakin dake tashi dazun sun ragu qwarai,hakanan shima dai yana zaune ne kawai ba tare daya dauki komai yaci ba,don dama haka al'adarsa take,ya riga daya saba,hakan zauna din,amma bai fiya cin komai ba har a tashi.


Dan gyaran murya kamal yayi kamar wanda ya qware bayan sun hada idanu da fulani adama,yasa tissue yadan goge gefan bakinsa badon ya baci ba sannan yace
"Ko yaushe sake zama manyan qasa kuke,sati biyu daya wuce na ganku a dubai a hotel kai da wasu baqi mata,hala abokan kasuwancinka ne kazo kama musu masauki?" Dago kanshi yayi daga amminsa da yake ta nazari tun daxun,ya lura akwai raguwa kuzari da walwala tattare da ita,yana fatan hotunan datace masa ta gani ba daukakar lamarin tayi ta sakashi haka cikin ranta ba,yana addu'ar wannan karon lamarin yazo da sauqi,ta tsaya ta fuskanceshi,komai yazo qarshe.


Idanunsa masu cike da kwarjini ya xubawa kamal din yana mamakin meya kawo wannan zancan a irin wannan wajen,gaban qannenshi da yayyensa da yaransu,sannan uwa uba gaban mahaifi da mahaifiyarsa,baya ga haka baima fuskanci wadanne mata ya gansu tare ba,hasalima shi ba kasafai ya fiya qulla harkar cinikayya da mace ba komai kudinta ko qasaitarta,saidai ko ta hadashi da ɗa miji ko ɗan uwanta,don shi yace sam bazai iya jure musu ba,baya tolerating nonsenses.


"Kamal....kaima da tone tone kake,banda abinda mutum kamarshi,da dukiyarsa irin haka kyau da asali ka rabu da ganinsa da wasu....."
"Gaskiya fa....to ai wayewar kenan,zamanin ne yazo mana da haka" adama ta fada tana tsiyaya kunun acca a cup,tana bada amsa kamar wadda ke magana bilhaqqi.


Gyaran murya mai martaba yayi,wanda hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,kana ya shigo da wani xancan da kusan ya shafi kowa dake zaune a wajen.


Tsahon awa guda da rabi sannan ya sallami duk wani wanda yake qasan yariman ne,ma'ana azeez din ya girme mishi,sai sa'anni da wadanda suke shekaru guda ne kadai sukayi saura,kana ya buqaci kowa ya fito zuwa babban falon hutawar dake maqale da dakin cin abincin. A sanyaye fulani ke takawa,daqyar kuma ta samawa kanta mazauni waje daya tana qoqarin sake daidaita kanta da numfashinta.
7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 65
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070



Doguwar addu'a mai martaba ya fara jaa,sannan kowa dake wajen ya bashi hankalinsa bayan an shafa,da wanda yasan meya zaunar dasu a wajen,dama wanda bai sani ba,gyaran murya yayi,idanunsa kan azeez sannan ya fara magana.


Wanda fulani ta dinga jin kamar yana fita da numfashinta ne
"Abdul'azeez....iyakar abinda na sani kuma Allah shine shaida,munyi dukkan wani qoqari daya kamata ace munyi wajen baka tarbiyya,mun baka kulawa da tarbiyyar data dace dakai,mun sadaukar da komai namu saboda rayuwarka ta inganta,na tsaya tsayin daka na nuns maka me kyau da mara kyau,na nuna maka halas da haram,duk da nauyin dimbin al'ummata dake kaina hakan baisa na sarayar da haqqin tarbiyyarku daga wayuna ba,daga kai har 'yan uwanka.....amma abun mamaki....abun takaici abdul'azeez,sai gashi komai yana shirin tashi a banza.....giyar kudi ta soma dibanka,kanason watsa mana qasa a idanu,abdul'azeez me kakeson zama ko kuma meka zama?" Ya qarashe maganar cikin nuna takaicinsa qarara
"Allah ya baka yawan rai....akwai wasu abubuwan da kana gani ana aikata ba dai dai ba amma kake yin shuru,kusan wannan ba shine farau ba,banson yin magana ne kawai saboda kada ayi maka fassara ta daban.....amma kamal gashinan....tare suka zauna ai a gida daya a mexico,babu abinda bai gaya min ba kan irin lamuran da yaga yana gudana,nace babu ruwanshi ya cire idanunsa yayi tasa sabgar saboda gudun fassarar mutane" hannu sarki abdallah ya daga mata ba tare daya dubu sashen da yake ba,bayason ta qara masa wani ciwon kan wanda ke damunsa,kota dora zuciyarsa bisa bigire na zargi ko zato,sai ya saka hannunsa gefan tuntun daya dora hannun nasa akai,ya ciro hotunan da adaman ta bashi tun ranar ya miqa masa
"Wacece wannan abdul'azeez?"
"Saidai kace tun yaushe suke tare ai" adama wadda tunda aka fara batayi magana ba sai a sannan,saboda sam ba haka taso ba,babban tonon silili taso gaban su waziri da sauran 'ya'yan fada masu tarin yawa,amma ko a yanzunma indai ya ɓaci idanun mai martabar ai kwalliya ta biya kudin sabulu
"Saboda lamarin ya girgixani sosai....ina ganin hoton saiga kamal ya shigo,shiya shaida min sun jima tare,tun a mexico" ta fada tana sake kaurara maganar donta samu mazauni me kyau a zuciyar maimartaban.


"Bilkisu ce,kuma matata ce" abdul'azeez ya fada karon farko tunda aka fara maganar,cikin wata kakkurar murya dake cike da dakiya da kuma jarumta,idanunsa da suka juye suka sauya launi saman fuskar adama,wadda bai taba jin ya tsaneta ba irin yau,saboda muraran ya hango zallar qiyayyarsu cikin idanunta,qiyayyar daya jima yana jin amminsa tana fadin ita adaman tana musu.


Kusan dukkansu babu wanda wuta bata daukewa ba,saboda kalaman da suka fita a bakinsa babu wanda ya tsammaci jinsu,ta sashen abokan hamayya basu so samun amsa irin wannan da wurwuri daga bakinsa ba,inda unda sukaso a fara dashi,daga bisani a zarce da maganar DADIRONSA CE,duk da a yanzun ma basu yarda da kalmar mata daya fada ba,sunfi zaton ya fada ne kawai don ya kare kansa,ya rage girman laifinsa idanun sarki abdallah,shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,kafin sautin salatin hajiya fauziyya wanda ya taho da kukan munafurci ya gauraye falon
"La'ilaha illallahu....muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam......ke kuwa aisha kina me har dan cikinki xai wannan aika aikar baki sani ba?" Ta fada tana kama haba tana duban fulani aisha,wanda ba komai take fuskanta ba a wajen
"Tabdi,lallai inda ranka kasha kallo...abun har yakai ga auren dadi......".


Da sauri maimartaba ya daga mata hannu
"Ya isa!" Ya fada da kaushin murya,wanda ya sanyasu shiga taitayinsu,sai mai martaban ya dubi sauran wadanda ke gurin dukkansu ya basu umarnin tashi su fita,ha rage daga matan nashi sai haj fauziyya.


A hankali ya kuma sauke idanunsa da suka sauya kala kan azeez
"Kasan abinda bakinka yake fada azeez?" Cikin wata dakiyar ya gyada kanshi yana sadda kan nashi qasa,karon farko da wani irin kunya da nauyin mahaifinsa ya kamashi
"Afuwa nake nema,amma na sani,matatace,kuma har yanzu matatace" kalmarshi ta qarshe ita ta farfado da fulani ta daga nata idanun ta sauke akanshi.


Wani nannauyan numfashi mai martaba yake saukewa,kana ya maida dubanshi kansu su da sukayi saura
"Ku tashi ku bani waje,abdul'azeez kawai nake da buqatar gani a nan" dukkaninsu ba haka rayukansu suka soba,kada ma hajja fauxiyya da adama suji labari,amma babu wadda keda ikon musa masa,dole suka miqe suna kakkabe jikinsu,wanda fulani saratu ita tayi saura a qarshe,domin dukkan abinnan dake faruwa ganinshi take kamar a majigi,ita kadai tasan iya adadin kudaden data kashe akan azeez din,an riga da an mata albishir din cewa....tabbas babu makawa mace daya azeez din zai aura har qarshen rayuwarsa,macen kuma zata haifa masa diya mace qwaya daya itama,zai rayu bashi da baya,bashi da wani magaji,hakanan rayuwarshi ba zata yauqaqa ba bare tayi tsaho,sai gashi a yanxun ana

Please Login or Register in order to submit comment