Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama a bakinta ta shiga,idanunta na saman gadon dake nuna akwai mutum kwance.


Can qasa taji anyi magana,bisa dukkan alamu amsa sallamar akayi
"Abdul'azeez" ta kirayi sunanshi tana tsaye daga gefe,yadan motsa kadan,sannan bayan shudewar minti guda ya yaye bargon daya rufa a hankali ya miqe ya zauna,bayan ya jingina bayanshi da makarin gadon.


Cikin tashin hankali take kallonshi,kamar ba azeez dinta ba,gaba daya ya feÉ—e,hakanan ya rame ya zabge,fuskarshi har ta soma tara gashi wanda batasanshi dashi ba,cikin hanzari ta qarasa gefan gadon a rude tana furta
"Ya salamu ya Allah,me ya sameka?" Tana kallon yadda qirjinsa ke dagawa da kuma fitar numfashinsa.


Idanunsa a kulle,shi kadai yasan ya yakejin jikinsa yace
"Banajin dadi ne"
"Bakajin dadi ko baka da lafiya kwata kwata abdul'azeez!" Ta fada a dan zafafe sannan ta sake cewa
"Tun yaushe ne baka da lafiyar amma babu wanda ka shaidawa?,kazo ka kwata ka kulle kanka kai kadai?,so kake ka mutu?" Ta sake fada cikin fada
"Qaramin yarone kai abdul'azeez?" Ta kuma tambayarsa.


Kasa amsa mata yayi saboda wani radadi da yakeji,ta fuskanci hakan,don haka hannunta na rawa ta ciro wayarta ta soma laluben wata lamba ta kira,umarni take badawa kan maza maza a fidda mota cikin sirri xa'a fita da yarima zuwa a sibiti,ta gama wayar ta kashe,saita rasa me zatayi banda sannu da take masa,ranta gaba daya a jagule kuma a tashe,meya sameshi haka amma bata da masaniya,Allah ne yasan kwanaki nawa yayi a haka,wannan matsalar gaba daya ta shiga rayuwarta,ta canzata,ta hanata aiwatar da komai yadda ta saba,ta zuba mishi idanu tana kallon yadda yake kokawa da numfashinsa.


Safwa ta fado mata a rai,haushi takaicinta ita da mahaifiyarta ya qarar mata a rai,ta zabawa azeez safwa ne saboda ya samu gata da kulawa irin wadda safwan taga ana bata a gidansu,ta zabeta ne domin ta zame masa macen aljanna,macen da zata zamar masa nutsuwa da hutu,sai kuma gashi tunda akayi auren ba abinda aka tsinta a zaman nasu,hakanan babu abinda xa'a dorar.


Cikin mitina qalilan aka fita da azeez din zuwa babban asibitin kudi kuma mallakin likitan gidan,tunda ta gaya masa bata yarda a dubashi ko a kwantar dashi cikin asibitin gidan ba,don ta tabbatar dukkan wadanda suke musu bita da qulli,da kuma binsu da sharri idanuwansu na kansu,don haka ta gwammace ya xauna a sibitin likitan,cikin dakuna da aka tanada na musamman mafiya tsada a asibitin.


Taso shaidawa maimartaba kafin tafiyarsu,to amma tasan cewa yanzun yana zaman fada ne,ba lallai ta samu ganinsa ba,don haka ta yanke tafiya ta shaida masa daga baya,don gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba.


Yanayin yadda yaga jikin yariman ya sanya aka fara bashi taimakon gaggawa,daga qarshe suka qara masa da oxcygyn saboda yadda numfashin ya soma masa wahala.


Cikin mamaki likitan ke tambayar fulani meke damun yariman?,a iyaka binciken da sukayi basuga wani ciwo ba,illa damuwa data masa yawa,da kuma yawan tunani daya sanyawa ranshi,wanda hakan ke neman yin barazana ga lafiyar zuciyarsa.


Cike da mamaki take kada kai
"Ban sani ba likita,bansan me yasaka har haka cikin zuciyarsa ba"
"Nina sani" afnan wadda ta biyosu asibitin daga baya ta fada,waiwayowa fulani tayi tana kallonta cikin mamaki,kanta tsaye ta soma magana
"Bilkisu,bilkisu ce a ranshi,ita ya saka cikin zuciyarsa,itace kuma silar ciwonsa da samuwar sauqinsa" daga haka ta miqe abinta ta soma takawa zata fice,da fulanin da likitan da baisan tushen maganar ba gaba daya suka bita da kallo harta fice daga office din
"Anyway....koma meye damuwarsa ya kamata a kawo qarshenta indai anason ya samu lafiyar zuciyarsa" maganar likitan data dawo da ita hayyacinta kenan.


Ita kadai a dakin da aka kwantar dashi take kai kawo tana tuna maganar afnan cikin qwaqwalwarta
"Bilkisu,bilkisu?" Ta maimaita sunan a hankali,sannan ta daga kanta ta dubi yadda yake kwance yana bacci da taimakon iskar oxcygyn.


Tunda take dashi bazata iya tuna sanda ya kwanya ciwo ba har haka,ace har gaon asibiti,mutum ne shi mai jumurin ciwo kowanne iri ne,yakan yi harkokinsa alhalin baida cikakkiyar lafiya,a haka zaiyi harkokinsa harya gama ciwo na cinsa a tsaitsaye ya kuma warke abunsa.


Amma da gaske bilkisun ce?,indai kuwa ita dince kamar yadda afnan ta fada bai haqura ba kenan?,idan kuwa bai haqura ba shin akwai shekaru ko wasu abubuwa da zasu zo su sanyashi haqurar?,idan ciwon nan ya zama ajalinsa fa?,qatotuwar tambayar data rufto kwanyarta kenan,ta sanya jikinta ya soma rawa,ba shiri ta samu sit ta zauna tana kiran sunan Allah,sai taji a jikinta kamar zata rasa yariman ne,sai taji kamar lokacin rabuwarsu ne yazo,cikin sauri da rawar jiki ta jawo jakarta,ta fidda wayarta ta lalubi lambar mai martaba.


A dake ya amsa sallamarta kamar yadda yake mata a wadannan kwanakin,cikin sanyin jiki da sanyin murya tace
"Saqona bai iske ba halan Allah ya taimakeka"
"Ya iskeni mana,amma me zan muku?,Allah ya bashi lafiya,inajin ke kika zabarma rayuwarsa hakan aiko?,kinga kenan ai babu matsala,saidai nayi fata da addu'ar Allah ya taimaka" daga haka qita ya kashe wayar.


Cikin mamaki tayi saroro,sai wayar ta sulale daga hannunta,ta saka hannayenya biyu tana rufe bakinta dasu gamida furzar da zazzafar iska,wani abu ya dunqule mata a maqoshi,bata taba zaton rana makamanciyar wannan na zuwa ba tsakaninta dashi,saita miqe da sauri ta isa gaban gadon tana duban fuskarsa data fada,zancan mai martaba na dawo mata
"Haka kika zabarwa rayuwarsa aiko?" Kai ta girgiza ta dora hannu saman kansa tana shafawa a hankali,kamar me neman amsar abinda ya dace tayi.


Ajiyar zuciya me qarfi mai martaba ya saka,bayan ya kashe wayar gaba daya sai yaji ya kasa nutsuwa,yanajin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a asibitin,amma dole ya dake ya kanne,harsai fulanin takai kanta da kanta inda yakeson taje din,harsai ta saitawa kanta hanya tukunna
"Allah ya bada lafiya,ya taqaita maka" yayiwa abdul'azeez din addua a fili can qasa yana jingina bayansa da dan gadon hutawar da yake kai,yana jin damuwa sosai cikin ranshi.


"Lafiya kuwa Allah ya taimakeka?" Ya tsinci sautin adama saman kanshi tana jeho masa tambayar,sam ya manta ya sanyata ta dauko mishi lemon tuffa a falo,sai ya miqa mata hannu yana amsar lemon ba tare daya amsa mata ba.


Bata haqura ba dai ta zauna daura dashi
"Kowa yaga fuskarka yasan kana cikin damuwa,idan don abinda yarima ga aikata ne saidai muce kayi haquri,kowanne bawa da jarrabarsa,dama ko cikin yaranka sai kaga Allah ya fitar maka da zakka a cikinsu,wani halinsa daban,shi yasa ba jinsi ake roqo ba da nagari,wasu matan sai suzo sufi mazan nagarta.....amfanin Allah ya baka yaran da yawa kenan,idan wani ya bata maka sai wani ya faranta maka aiko?".


Da mamaki saman fuskarshi ya sauke cup din yana dubanta
"Wani abun na gaya miki yarima yayi?" Sai tadan dirirce kadan
"Au...to ai na zaci abinda ya farune satittikan da suka gabata" bai sake cewa da ita komai.ba ya maida kofin bakinsa,wasu wasi fal ranshi yanata auna maganganu da ayyukan adaman cikin lokuttan nan,yayin da ita kuma tayi tsam da ranta,gefe guda na zuciyarta ya cika fal da haushi da takaici,duk yadda sukaso jin wani abu abun ya faskara,wani sashen kuma yana kwabarta na ta taka a hankali kada kwabarsu tayi ruwa,tunda tafi kowa sanin waye sarki abdallah din.
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 73

*_ina miqa saqon godiya a gareku,haqiqa na yaba da karamcinku,na kuma gode da addu'o'inku,wadanda suka yimin ta private da kuma wadanda sukamin cikin grp,na god sosai,Allah ya qaremu da lafiya,ya kuma rabamu da dukkan abun qi amin summa amin_*
____________________________
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070




Ranar ranta a bace haka anty zuhriyya ta wuni,bilkisu nacan gida batasan meke faruwa ba,don a can ta wuni,koda ta dawo batace da ita komai ba,sai da abbaa ya dawo take shaida masa abinda ya farun.


Murmushi yayi kawai sannan yace
"Na lura da abubuwa masu yawa,me martaba ya boyewa matarsa komai ne,batasan meke faruwa ba,akwai kuma abinda yakeson aiwatarwa,kada ki saka wannan abun cikin lissafin damuwarki,mu jira lokaci,nasan abinda ya shirya din xai bayyana"
"Kamar me abban najwa?" Ta tambayeshi
"Karki gaggawa,ki jira ki gani" ya fada yana bude foodflask din abincin data aje masa yana duba meta dafa,yayin da ita kuma ta shiga zurfin tunani sosai.

¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶


Yadda yake jin jiki a lokutan hakan yake samun kulawa daga wajen likitoci,sosai hankalin fulani yake a tashe kamar yadda hankalin me martaba yake,saidai shi ya danne ya kuma boye,bai bari kuma ta gane hakan ba.


Kamar wata safiya yana zaune dakinsa yana lazumi,saidai gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana kan azeez din dake kwance a asibiti.


Daga bakin qofar mihrabin da yakan zauna yayi sallah da lazumi yaji sallamar afnan,yayi mamaki qwarai jinta a irin wannan lokacin,don bata taba zuwar masa haka ba,sai daya amsa sannan ya bata izinin qarasowa.


Cikin nutsuwa kuma a ladabce ta samu waje ta zauna,ta gaidashi ya amsa mata cikin kulawa,shiru tayi na wani dan lokaci har sai daya tambayeta sannan ta soma magana cikin sanyi
"Abby....zuwa nayi na roqeka alfarma,don girman Allah kayi haquri,ka yafewa ammi da ya azeez kuskuren da suka aikata ko ince ganganci,ka daure ka shiga lamarin ya azeez,wallahi sosai yakejin jiki a asibiti,ina kuma da yaqinin cewa,inda ace bilkisu na tare dashi bazai shiga wannan yanayin ba" shuru yayi yana dan murmushi na wasu sakanni,sannan ya bude baki a nutse yace
"Haqiqa abinda aisha ta aikata yayi mugun bani mamaki da kuma girgizani,din ban taba kawo mata aikata hakan ba,laifin kuma bana kowa bane face na mahaifiyarkin,na riga dana yafe musu,amma yafiyar ba yana nufin karna dauki mataki akai ba,lamarin azeez na riga dana shigeshi tuntuni,saidai nabar sauran damar hannun yarinyar da aka zalunta,amma su ban basu damar su sani ba,saboda inason su gama horuwa,na baiwa mamarki haske na yadda zata gyara kurenta amma har yanzun bata dau hasken ba bare ta gyara,bani da yadda zanyi,iyakata nayita zama na zuba ido naga randa zata dauki haske,ta kuma dauki matakin gyaran,wanda gyaranta shi kadaine zai qarasa kawo qarshen wadan nan matsalolin" fuskar afnan ta fadada fara'a da kuma haske,cikin zumudi tace
"Kana nufin abby ka dawo ma da ya azeez matarsa?" Kai ya gyada
"Hakane,ban kuma lamunci ki gayawa kowa ba kamar yadda nima ban shaidawa kowa,nayi hakanne kuma bisa wani dalili nawa" kai take gyadawa tana sarawa salo da hikima irin na mahaifinta,tabbas ya cika cikakken adalin shugaba kuma jagora,sai yanzu take sake gane abinda yasa jama'arsa ke masa son so
"Allah ya saka da alkhairi,ya kuma qara girma abbi,amma don Allah kaje kaga ya azeez" murmushi ya kuma saki sosai yana dubanta
"Kin taba ganin an shiga tsakanin hanta da jini,dole zanje,amma sai bayan wani lokaci dana diba"
"Hakanma muna godiya" ta fada tana murmushi.


Hira suka taba wadda suka dan jima basuyi irinta ba,kana daga bisani sukayi sallama,harta kusa fita daga wajen yakira sunanta
"Karki manta,bance ki gayawa kowa yadda mukayi ba"
"In sha Allahu abbi....amma abbi inason naje naganta anty bilkisun" kai ya gyada
"Babu laifi....ki miqa gaisuwata zuwa gareta" ran afnan fes ta fita daga wajen maimartaba,hakanan hankalinta akwance yake yanzun,tasan na zasu rasa nagartacciyar suruka irin bilkisun ba.


¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶


Cikin zumudi da farinciki take shiryawa,bayan ta samu dan rakiya a sirrance zuwa gidansu bilksun,ta kuma nema rakiyar mama sodangi itama a sirrance,bayan ta shaida mata dukan abinda ke faruwa,wanda hakan ya yima mama sodangi dadi matuqa,kamar ta taka rawa haka ta dinga ji.


Babu wani jinkiri suka gama shirinsu tsaf,suka kama hanya.


Dai dai lokacin da bilkisun ke zaune saman wasu kujeru dake farfajiyar gidan,hannunta riqe da wani dan qaram littafi tana dubawa bayan tashin anty zuhriyya yanzun nan zuwa cikin gida.


Tsiya tayi mata ta kuma yi mata tas kan taqi gado taqi mawanka,duk kayan gyaran data kawo mata sai taqi amfani dasu,tace gyara dole kuwa babu fashi,kodon ta rikita musu yarima,ta kuma sake qular da aisha babarshi,itakam komaima jinsa take kamar a mafarki,hatta da komawar duk data amsa amma jinta take kamar wasan yara.


Batasan yadda zuciyarta da gangar jikinta suka dauki abun ba,itadai gata nan ne dai kawai ta zubawa sarautar Allah idanu,taga yaya qaddararta zata kaya.


Karar dage gate yadanja hankalinta,ta daga kai ta kalli motar dake shigowa,sai kuma ta maida taci gaba da karatunta,hakan ya sanya har suka fito bataga su waye ba,sai dataji takun tafiya sannan ta kuma daga kanta.


Sosai gabanta ya fadi sanda tayi arba da mama sodangi da kuna afnan a tafe,ta miqe tsaye cikin wasu wasi tana kallonsu,mama sodangi bata ganta ba,afnan ce ta hangota,saitayi wajenta da sauri hannaye bude cikin nuna zallar farinciki da kuma hargowa irinta farinciki sanda ta sake tabbatarwa lallai bilkisu classmate dinta ce
"Billy bilya!" Ta ambaceta da sunan da akan kirata dashi wani lokaci.


Haka kawai saita samu kanta da subucewar murmushi kan fuskarta,itama ta bude hannayen nata dukka tana dariya,har afnan ta qaraso suka rungume junansu,kowanne zuciyarsa na farincikin ganin dan uwansa.


"Wayyo Allah na,ashe da gaske dai kece,har taraddadi nake kar naxo.na samu ba kedin da nake tunani bane,bilkisu ina kika boye haka?,meye labari?" Da mamakin yadda bakin afnan din ya bude take kallonta,cikin dariya tace
"Mu qarasa ciki mana" saita juya sashen mama sodangi
"Mama....sannu da zuwa" ta furta a hankali,tana tuna wasu abubuwa da suka shude zamanin baya a rayuwarta,kai mama sodangin ta kada
"Bani amsawa,bayan an manta da nine a tsaye" dariya sukayi dukansu kana suka rankaya zuwa cikin gidan.


Ko daya a cikinsu anty zuhriyya bata gane ba tunda bata sansu ba,iyaka sun gaisa cikin mutunci,tasa najwa ta aje musu abunci da kayan motsa baki ta wuce ta barsu.


Hira sosai suka daka,tun daga labarin rayuwar makaranta,suns tuna yadda suka rayu,da yadda afnan din ta dinga qwarzabar billy,a nan wajen tace
"Kinsan wani abu?,alokacin fa burgeni kike,kawai so nake ki kulani muyi qawance,ke kuma kin qi,ni kuma inajin haushin na xubda daraja na fara zuwa wajenki,ina tsoron kada ki yarfani girmana ya zube,shi yasa nake miki haka" dariya sosai ta baiwa billy,ta karya wuya tana cewa
"Ni a sannan guguwar data taso rayuwata a gaba tasa bana ganin kowa sai ita,da kuma yadda zanyi na kawar da ita".


Sun dau lokaci sosai suna hirar,har sai da mama sodangi tace
"Kinga idan abinda ya kawoki dama kenan....ni matsa nayi abinda ya dameni" murmushi afnan tayi sannan ta tattara dukka hankalinta akan bilkisu
"Biko kashi na biyu muka sake zuwa yifa?" Bilkisu na dubanta ta tambayeta
"Bikon mefa?"
"Matar yayana" ta bata amsa kai tsaye tana dubanta,sai tadan matse fuska kadan sannan tace
"Awwnnn" daga haka kuma tayi shuru,tana tunsnin meya hana mahaifiyarsa sanya baki ne cikin maganar?,bayan itace qashin bayan komai?,sai wadanda bada su akayi ba keta zuwa,lallai ba shakka akwai matsala kuma akwai damuwa kenan.


"Bilkisu.....a matsayina na uwa ga yarima ba mahaifiya ba,bayan maimartaba nima gani nazo da kaina nema mishi afuwa a wajenki,don a yanxun bashi da ikon iya magana dake,yana gadon asibiti yana jiyya" waiwayowa tayi tana dubansu jin abinda sukace,sai afnan ta dage gira
"Yes...kin kwantar dashi,kuma komai.na iya faruwa da zuciyarsa....kima Allah kiyi haquri anty billy" ta qarashe fada tana hade hannayenta biyu waje daya.


Murmushin qarfin hali ta saki tana kama hannayen afnan kana ta sauke
"Bari....girman me martaba da darajarsa yafi gaban haka,ya riga ya roqa alfarma kuma na masa,so wannan ya riga da ya wuce"
"Indai da gaske ne to gaskiya ki tattara kayanaki ki tafi jinyar yayana" afnan ta fada tana langabewa cikin nuna alamun tausayi,dariya ce ta qwacewa bilkisun kana ta kada kai
"Bazai yuwu ba afnan,kiyi haquri" kamar zata saki kuka haka tayi,amma dole ta haqura,daga haka akalar hirar ta koma ga mama sodangi,ta soma tambayarta rakiya
"Rakiya ai tana gidan mijinta,yaranta biyu yanzu haka" murmushi ta saka tana mata fatan alkhairi,tare da tuna zaman shekara dayan da sukayi,zama me dadi a tsakaninsu,wanda sam ba zata mance dashi ba.


Suna tsaka da hirar dirvern gidan ya dawo dasu amatu daga tahfeez,ba afnan ba,hatta da mama sodangi sai data kusa narkewa a wajen saboda tsabar mamaki da wasuwasi,ai kafin kace meye tuni afnan ta isa wajen yaran tun kafin su qaraso ciki ta cafesu,basusan wacece ba,basusan dawan garin ba sai suka hau baza idanu,muryarta na rawa kamar zata saki kuka ta dubi bilkisu tace
"Don girman Allah kice wadan nan twince din ya yarima ne,kice nashine karkice aah" dariya da tausayin xallar soyayyar yaran data gani cikin idanunta ya kamata,murya can qasa ra furta
"Nakune" qatuwar ajiyar zuciya mama sodangi ta saki,ashe itama abinda takeson ji kenan,sai kuma dukka suka tattara duk wani attention nasu kan yaran.


Tun yaran suna baza idanu suna dari dari sai gasu sun sake,tana sake nanata musu ita din wace,kafin wani lokaci kuwa suka riqe radam a kansu,qarshe sai gasu suna qyaqyata dariya tare tana basu labarai ita da mama sodangi.


Ganin yaran ya hanasu tafiya da wuri har kusan sallar isha'i,koda suka tashi tafiya dinma kafewa afnan tayi da magiyar don Allah bilkisun ta bata su aro koda na iya yaune,gobe ta dawo mata dasu
"Kiyi haquri,bazai yuwu ba" tace da ita,hakanan jikinta a sanyaye ta saukesu suka wuce,bayan ta cika wayatta da hotunansu kamar ba gobe.


Cikin kwanaki biyu rak ta wanko hotunan,ta kuma cika sassan fulani dasu waje waje,wanda da ace wajene da kowa ke iya shiga ba shakka da.labari ya cika masarautar,randa fulanin ta soma gani ta jima tsaye tana qarewa yaran kallo,tun randa ta dora idanunta a kansu suka tsaye mata cikin xuciya da ruhi,taji wani abu mai kama da soyayya da qauna na ratsa zuciyarta,kwatankwacin yadda takeson mahaifin yaran,abu daya ya hanata kasa magana a kansu,duk da yadda kullum take kwana ta tashi dasu a ranta.


Batasan afnan na bayanya ba sai data yi gyaran murya,sai kawai tayi gaba ba tare data waiwayo ba,kamar ba kallon hotunan nasu ta tsaya yi ba,dariya ta kama afnan
"Uhmmm,ammi kenan,idanma zaki bi hanya tun wuri gwara kibi,saina taya abbi wannan yaqin wallahi".


¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶¶


Ko ina na jikinta rawa yake cikin tashin hankalin da bata taba riskar kanta a ciki ba,ba ita ba....dukkan wanda ke wajen hankalinsa a tashe yake,wasu daga ciki ma sun soma kuka,saboda yanayin da aka fita da yarima azeez.


Lambar mai martaba ta kira,tayi sa'a yana available,bugu uku ya daga
"Idan ma ba zaka zo ka ganshi ba,to na roqeka ka yafe masa,saboda yanayin daya shiga din,bamu da tabbacin samuwar ruhinsa......duk da cewa nice silar komai,dukka laifin yana wuyana a qa'ida....amma ina roqar masa afuwarka" kalamanta sunyi masifar daga mishi hankali,don haka bai iya maida mata amsa ba ya katse kiran,sannan ya bada umarni cikin gaggawa aka tada motoci ya nufi asibitin.


Fulani adama da fitar ta kasance kan idanunta saita jinjina kai,tana baiwa kamal umarnin bin ayarin motocin me martaba,yaga inda suka nufa,don sama bata yarda da yanayinsa a 'yan lokuttan nan ba,ta sakawa sauyawar mood dinshi ayar tambaya.


Yanayin daya samesu a ciki ya tabashi shima,tsahon awa guda kafin su maidoshi dakin,bisa qwararan dokikin banda hayaniya sam,hakan ya sanya maimartaba ya baiwa kowa umarnin komawa gida,abar mai jiyyar shi kadai,tunda akwai masu kula dashi,sai a sannan yake tambayar ina safwa?,ita ya kamata ta zauna dashi,tsananin bacin rai ya hana fulani bashi amsa,inda ace tana da iko ba shakka yau da ita da kanta zata sallami yarinyar,saboda ko kusa bata ga rana ko amfanin auren nasu ba.


Duk yadda yaso zuwa asibitin washegari bai samu dama ba,saboda baqin da masarautar tasu sukayi daga qasar jigawa,saidai ya samu bayanin cewa jikin nasa da sauqi sosai,don harma ya dan farka,hakan ya dan sake saka masa kwanciyar hankali.


Washegari ana idar da sallar asuba,gari yana yin shaa ya shirya zuwa sake dubashi ba tare da wasu mutane 'yan rakiya masu yawa ba.


Lokacin da ya tura qofar dakin saiya sameshi saman abun sallah,ya jingina bayanshi da bango,ya fada sosai ya qara haske,da alamar gyangyadi ne ya debeshi saboda tasirin allurai da ruwan da aketa saka mishi,wanda ciki akwai na bacci.


Saida ya tsaya ya gama qare masa kallo sannan ya saki murmushi,babu shakka ba'a cika baki a soyayya,hakanan babu wanda ya isa ya bugu qirji yace yafi qarfin soyayya,ko yace shidin jarumi ne a wannan fagen,ko wayeshi kuwa,bai taba ganin wani abu daya karya abdul'azeez din,ya cire masa dukkan wata jarumata tashi da qwarin gwiwa ba irin wannan lamarin,saiya ci gaba da takawa a hankali har yakai bakin daddumar ya xare takalmansa,sannan ya zauna a gabansa,kasancewar daddumar tana da yalwa,ya langwashe qafafunsa yana ci gaba da kallonshi,sannan a hankali ya saka hannunshi ya bugi cinyarsa........
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 74
*_kunsan me ake kira da ƘURE ADAKA?_*

_To ba kowa bane illa MAAB LUXURY HOME_

*_Wadanda suke a shirye kuma kullum a tafe wajen kawo muku ingantattun kayan qawata gida masu inganci da kuma kyan gaske_*

*idan matsalarki inda zaki samu kaya 'yan yayi masu inganci to kakarki ta yanke saqa,koda kuwa saqar qarfe ce,saboda zuwan MAAB LUXURY HOME*
_SUN TANADAR MUKU KAYA KAMAR HAKA_
_dinner set_
_serving trays_
_cutlery set_
_jugs_
_foodflask_
_thermoflask_

*kai dama dukkan wani nau'in kaya na qawata gida da maidashi aljannar duniya*
*_hausawa sukace gani ya kori ji,maza garzaya wadan nan shafukan namu don ganewa idanunku irin kayayyakinmu_*

*instagram* https://instagram.com/maabluxuryhome?utm_medium=copy_link

*facebook*:maab luxury home
*website*
http://maabluxury.com

_Ko ka tuntubesu ta lambar waya kamar haka_
+491521 4642007

*suna nan a garin kano,maza taho ayi daku*ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸
_____________________________
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070



"Tashi rago kawai" kalmar daya fada kenan,firgigit azeez ya bude idanunsa yana ambaton sunan Allah,saiya maida nutsuwarsa jikinsa cikin mamaki ganin me martaba zaune a gabanshi,kanshi ya sadda cikin jin nauyi,sannan a hankali cikin muryar marasa lafiya yace
"Barka da asuba" maimakon ya amsa mishi sai yace
"Ban taba tsammanin cewa kai din rago bane sai yanzu,shine ka zauna akan mace zaka mutu saboda tsabar ragwantaka?" Shuru azeez din yayi qirjinsa na bugawa,shi kadai yasan me yakeji,yana da tabbacin ba zasu gane ba,yayin da me martaba yaci gaba da kallonshi yana murmushi sannan ya kuma cewa
"Dago kanka ka kalleni"yayi maganar yana nade hannun rigar dake jikinsa me zubin alkyabba,dagowar yayi kamar yadda me martaba yace yana dubanshi
"ka ganni nan?" Ya fada yana nuna yatsarsa
"Ba'a tabani kasani akan mace ba,idan na qudirta a raina saina sameki saina samu.....ka tambayi mamarka....itace babbar shaida,mutum nawa na kasa a mali,na rabota dacan na kawota nan,amma kai mace daya ka kasa controlling tunaninta da soyayyarta zuwa kanka....koda yake,Allah baya goyon bayan zalunci"

Please Login or Register in order to submit comment