Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta saka mishi cokali ta sauka ta dauki handout dinta itama ta fice kamar yadda taga sumaira tayi dazun.


Jan plate din yayi gabansa yasoma ci,akwai tambayar da yakeson mata amma baisan yadda zata amshi kota kalli tambayar ba,haka ya dinga cin abincin yana gwada ta yadda zai tambayetan,kafin daga bisani ya tattara dukkan gwanintarsa yace
"Sun aiko sun fadi adadin abinda suke buqata kuwa?" Ya jefa mata tambayar,saboda ya tabbatar kudi ne suka rudesu har suka yarda suka aikata abinda suka aikata din,don haka zasu biyo ba'asi daga baya na kudin da akace su fadi nawa sukeso,qila ta wannan hanyar zaiji wani abu,ko yaya daga garesu.


Mutum ne shi da bayason mutum mai kwadayi ko son abun duniya,amma baisan me yasa ita bai ganinta da wannan abun ba,baisan me yasa ya kasa mantawa da ita ba.


Cikin rashin fahimta ammi ta dago tana dubanshi
"Wa kenan kake nufi?" Rasa yadda zai mata bayani yayi,sai daya hade lomar bakinsa sannan yace
"Yarinyar da aka turan mexico" wani irin hade rai da bai taba gani saman fuskarta ba ammin tayi,ta wani gefen gabanta yadan fadi,ta kafeshi da ido,yaji a jikinsa kallonsa take,amma saiya basar yaci gaba da cin abincinsa kamar bai gani ba.


Dama ta kusa qoshi da abincin,maganarsa tasa sauran wajen da zata zuba abincin ya cike,saita ja kujerarta baya tana ci gaba da tsareshi da ido,a hankali cikin muryar dake bayyanar da bacin rai tace
"Meye hadinka dasu?,meye damuwarka da sun aiko ko basu aiko ba?,abdul'azeez,ina fata baka manta da maganarmu ta qarshe ba kafin in turo maka ita,ka sakata a idanunka banda zuciyarka,karka yadda ko gefen zuciyarka taje,idan taje din akwai matsala,saboda ita din ba kininka bace,sannan ita din ta wucin gadi ce a wajenka,abdul'azeez...koda wasa banason na sake jin wata magaba makamanciyar wannan daga bakinka....har abada"
"Afuwan" ya fada cikin girmamawa,daga haka shuru ya biyo baya,saita miqe tana sauka daga wajen,da alamu ranta ya baci ne.


Shima bai wani ci gaba da cin abincin ba,cokali biyu ya qara ya miqe ya sauko daga wajen,ya mata sallama ya fito.


Kan hanya ya dinga jin kansa yana wani daukan zafi,ranshi yana baci,baisan ainihin dalilin ba,amma yakan tuna bai samu jin komai daga wajen ammin ba,yana jin wani feeling mai qarfi nason karya zuciyarsa,irin feelings din da baisan menene ba.


Maimakon ya zauna a sashensa kamar yadda ya tsara,sai yaji ya kasa zaman,ya dauki wayoyinshi kawai ya fito,ya soma takawa cikin gidan sarautar yana nufar sassan da xasu fiddashi daga gidan,ya dinga wuce qofa qofa gate gate,akwai tazara mai dan yawa tsakanin ainihin sassansu zuwa babbar qofar da zata fitar dakai daga gidan sarautar gaba daya,amma haka yaci gana da takawa,yanajin tafiyar kamar zata debe masa kewa ne,yana tsaka da wannan tattakin wayarshi ta dauki tsuwwa,sunan safwa ya bayyana,sai yayi rejecting kiran sannan ya kashe wayar gaba daya ya jefata a aljihun wandonsa.


****** ***"""***** *******


Kasa zama tayi lokacin da fulani aisha ta yi kiranta,tana son taji wacce amsa ce zata fito daga bakinta?,idan har ta amshi cikin ne tasan cewa lallai ita din tazo duniya a sa'a,ta soma aiki a masarautar kaisa da qafar dama,hakanan kakarta ta kuma sake yanqe saqa kenan,zata samu arziqi da alherin daya ninka na baya,idan kuma akasin hakan ta faru to dole kowannensu ya amshi hukuncin,don basu da qarfi ko qwanjin da zasuce zasu ja da hukuncin.


Yau din cikin matuqar daurewar fuska ta fito,wanda hakan ya sabbaba faduwar gaba wajen umma luba,tun fulanin ma batace komai ba.


Sai data gama dukka tattakinta sannan ta tsaya gabanta,ta dubeta da kyau cikin kaushin murya
"Ki gaya musu cewa wannan maganar cikin labarin qanzon kurege ce,qirqirarren labari ne da aka samar dashi saboda ayi wasa da hankalin masarauta,ki gaya musu,basusan wacece fulani ba,ki shaida musu sunyi kuskure,da sun sani kansu tsaye sun fadi adadin kudaden da suke da buqata...komai yawansu fulani tafi qarfinsu,amma bawai su biyo ta wannan hanyar ba,ki sake shaida musu cewa....ban tura ta mexico na hadata da yarona don tayi ciki ba,ban tura bilkisu mexico don ta dace dashi ba,na turata ne tamkar ma'aikaciya ta wucin gadi,saboda sanin kansu ne ce cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,saboda haka ki jadda musu,hawainiyarsu ta kiyayi ramata,kudi kuwa ko nawa suka yanke suna da buqata su shaida miki,gari bazai waye ba zai tabbata a gabansu,kudin da zai zamo abu na qarshe da zai shiga tsakaninmu kamar yadda muka tsara bisa yarjejeniya....kije ki shaida musu...ruwansu su haqura da batun ciki....ruwansu suci gaba dayi....".


Kamar daga sama ya dinga jin tashin maganganun ummin sanda yake hanyar shigowa wajen ummin,da alama cikin bacin rai take maganar,sunan data kira kawai yaji tamkar an jefeshi da wani abu,kalaman da suka biyo baya kuma suka so birkita masa kwanya da kuma tunaninsa gaba daya,har ya kasa tantance ainihin furucin dake shigowa kunnuwansa yake ji ko kuwa,don haka ya kutsa kanshi kai tsaye cikin falon,burinsa kawai ya isa yaji abinda kunnuwansa suke jiyo masa hakanne?.


Dubanshi tayi sanda ya shigo,saita dauke kai ta maida ga luba
"Kije ki shaida musu dukkan abinda na gaya miki,hakanan ki dawomin da dukkanin amsar da suka bada"
"Da izinin Allah kuwa ranki ya dade....Allah ya huci zuciyarki....a tashi lafiya" daga haka ta miqe ta fice daga falon.


"Ummi....ciki?,waye yake da ciki?" Ya samu bakinsa da furta mata kalaman ba tare daya shirya ba,dukkan kallonta ta maida kanshi,cikin matuqar hade rai tace
"Sun shirya qara tare da tsara cewa tana da ciki,saboda idanuwansu sun rufe,suna tunanin shashashai ne mu,suna so yi amfani da wannan damar don suyita tara dukiya damu,bayan sun amince da dukkan yarjejeniyar da mukayi dasu" Hakanan yaji batun cikin ya samu kyakkyawan matsugunni cikin zuciyarsa,ya kuma zauna daram bisa kansa,hakanan yaji baida sha'awar ci gaba da zama,don haka ya qaraso tsakiyar falon,ya samu kujera daya ya zauna
"Amma ammi....bincakawa ya kamata ki soma yi,ki tabbatar da ainihin sahihancin maganar ko kuma akasinta" karon farko ya samu kanshi da musawa hukuncinta,karon farko daya soma fadin ra'ayi da views dinsa kan wani hukunci data zartas.


Sosai take dubanshi itama,kafin daga bisani ta motsa bakinta
"Wacce jami'a ka zaba?" Ta jefa masa tambayar ba tare data bi takan qorafinsa ba.


"B U K kano" ya fada yana motsa labbansa,kamar wanda aka yiwa dole wajen furta lafazin,wani kallo ta watsa masa
"Kana da hankali kuwa?,ka manta wacce jami'a ka gama?,ko kuwa ka manta gargadin da nayi maka na cewa banda duk wata jami'a dake cikin qasar nan?" Baki ya bude zai mata magana,cikin fusata ta daga mishi hannu gami da cewa
"Ya isheni....tashi ka bani waje tun bai gama fusata ba" tsam ya miqe ba tare daya furta abinda yayi niyya din ba,yana jin ranshi a jagule,bacin rai na mamaye zuciyarsa.


Har ya kusa fita ta kirayi sunanshi
"Abdul'azeez" ya tsaya kana ya waiwayo,ta baiwa qofa baya don haka bai ganin fuskarta
"Idan wani abun ke damunka,ka gayamin tunda wuri mu maganceshi,idan kuma wani abu kake saqawa cikin ranka,ina mai baka shawarar kayi gaggawar cireshi....saboda bazai taba haifar maka da d'a mai ido ba".......

******** ****** ********

Tunda umma luba ta shaidawa malam bilya saqon fulani aisha yaji ranshi yana baci,a karon farko kenan,bai taba kawowa ko tsammanin zasu ture ko su qaryata maganar cikin ba,shi kadai zancan ya dinga damu yana masa kai kawo cikin zuciyarsa,yana son shaida zuhriyya saidai baisan gidanta ba,bai kuma san inda zai sameta ba,yasan cewa koda zatayi fada masifa da tashin hankali a qalla ya samu sassauci ya gayawa kowa,haka maganar ta dinga damunsa taba sanyashi bacin rai da baqinciki.

*****************


Misalin bakwai da rabi ne na safiyar ranar,anty zuhriyyan ta shirya don takai najwa da ateeq tahfiz da suka sanyasu dan iyakacin lokacin zamansu a kaisa kafin su tattara su koma inda suka fito,saboda gudun kada karatunsu ya samu tasgaro kafin su koma.


Yawancin lokutta abba ne yake kaisu,amma yau anty ce zata kaisu sakamakon fita da yayi tun sassafe.


Da kanta ta iske bilkisu a daki,ta sanyata ta shirya zata rakata takai yaran makaranta,sabanin daa da ita da haule suke bari a gidan,amma yau tace tare zasu,saboda har yanzun walwalar bilkisun bata dawo ba,duk da cewa tadan samu sauqi,amma laulayi kam har yanzu bai barta ba,don wani lokaci idan ya waiwayeta haka take wuni akwance,ba tare data kai komai bakinta ba,wala ruwa ko abinci,wani lokaci kuma ka ganta da 'yar lafiyarta.


Yawan tunane tunane da anty zuhriyyan ta fuskanci tana yawan zama tayi shike damunta,don haka ta sake zage damtse wajen janta a jiki,hanata zaman kadaici,da qirqiro mata abubuwa da tasan zasu janye mata hankalinta.


Da fari tayi shawara da abbaa kan zata sama mata skyline universty,yace aah,yanaga yanzu abu mafi kyau shine suyi tattalin lafiyarta tukunna,tunda har yanzu ba wani cikakkiyar lafiya ne da ita ba,sannan shi yafison idan sun koma brasil tayi karatunta a can,inda babu wani wanda ya santa bare ta samu takura ko wani abu makamancin haka,ta yarda da shawararsa don haka ta jingine wannan batun,saita sauya mata waya da laptop,hakanan lokaci lokaci takansa ana dauko mata qannenta su wuni wajenta,hakan saiya sake rage mata damuwar da take ciki sosai,duk da cewa zuciyarta har yanzu a quntace take,ta cika da tsana da zargin ahalin kaisa,hakanan ta boye wani quduri cikin zuciyarta.


Da yake duk sanda ta tashi sallar asuba sai tayi wanka saboda ta samj temprature din jikinta ya mata dadi,yanzun ma da wankanta,kaya kawai ta sauya zuwa doguwar riga,saboda yanxun tafi ta'ammali dasu,sakamakon cikinta daya daga ya soma fitowa,don ya shiga wata na biyar,ta samesu tuni suna cikin mota.


A hanya surutu ateeq da qawarta najwa suketa mata tana biye musu,motar bata zauna shuru ba har sai da ummin ta saukesu suka juyo iya su biyu kawai,suka daukon hanyar komawa,saidai wannan karon a hankali ummi take tuqin.


Basuyi wani nisa ba ummi zuhriyya tace
"Inaga ya kamata mu leqa gidanku ko?,muji meye feedback na mutanen can kan batun cikinki" boyayyar ajiyar zuciya kawai bilkisun ta sauke ba tare data ce komai ba,don ita gaba daya bata qaunar tunasu ma bare maganarsu,ta ajesu can wani sashe daban na rayuwarta mai nisa,wanda take fatan watan watarana ta mance da babinsu,saidai ko hakan zai yiwu?,tunda ga wata igiya mai qarfi ta ratsa tsakaninsu?.


Har suka je gidan bilkisun bata tanka ba,sukaci sa'a baban yagama shirin fita kasuwa kenan yana tsaye a falo yana baiwa umma katti kudin cefane,wanda cikin satin ya sake gyara lamarinsa,tare da gyara abubuwa masu yawa cikin gidan,harda wadanda ma baya yi.


Daga yanayin yadda ya karbesu bilkisu taga wani irin sanyi da laushi mai yawa tattare dashi,ba ita ba,hatta da anty zuhriyya abokiyar burminsa ta lura da hakan,saidai yace musu su xauna minti goma yanzun zai dawo,tabe baki kawai antyn tayi batace masa komai ba har ya fice.


Qofar gida ya tsaya yana neman yaron da zai aika gidan umma luba,saboda nashi yaran duka basa nan sun wuce makaranta,bayajin zai iya gaya musu wannan saqon da bakinsa,yana jin zuwa yanzu ya kamata ya sauya daga asalin bilya zuwa bilyaminu,ya kamata ya dainda dabawa diyarsa wuqa haka a zuciyarta,ya tabbatar dole amsar da zata biyo baya ta taba zuciyar kowacce mace,ki dauki ciki kina wahala dashi,sa'annan wadanda keda alhakin hakan suce basu yarda da batunsa ba?,ba qaramin mummunan xance bane ga kunnuwan kowacce diya mace.


Da qyar ya samu yaro ya aika,saiya tsaya nan qofar gidan yana jiran dawowarsa,Allah ya taimakeshi sai gata da yaron,cikin mamaki take tambayarsa lafiya?
"Maigado ce da mariqiyarta,wadda take da alhakin jin komai sukesu suji amsar da masarauta ta basu" ita kanta wannan karon abun saiya mata nauyi,amma ba yadda ta iya dole ta isar da saqon,don tana da buqatar amsar da zata kaiwa fulanin,don haka ta cije suka shige tare.


Sau daya bilkisu ta daga kai ta kallesu ta dauke kanta,mutum biyun da kullum idan ta gansu sai taga kamar taga wadanda suka sanya gatari suka rinqa sassaqar rayuwarta har zuwa qarar da ita.


A sanyaye umma luba ta gaida anty zuhriyya datayi mata kwarjini,ta amsa mata ba yabo ba fallasa,don batasan wacece ba
"Sannu maigado" ta sake yiwa bilkisu sannu,bata iya dubanta bama bare ta amsa,saita gyara zama cikin dan da wurwura,ta gaya musu dukkan abinda fulanin ta fadi.


Ƙololuwar fushi anty zuhriyya ta shigeshi,yayin da bilkisu ta shiga wani irin yanayi wanda batasan wanne iri bane,abu daya kawai taji jiki da zuciyarta na gaya mata,basason zamansu a wajen,basason ci gaba da sauraren bayanan umma luba,duk da alamu sun nuna ta gama fadin abinda zata fada din,saita miqe tsam.idanuwansu dukka suka rakata,kowa yana jin wani yanayi game da ita a zuciyarsa.


Haka ta dinga sanya qafarta kawai duk inda ta fuskanta,bata tsaya ba sai data isa jikin motarsu,ta sanya hannu ta bude ta shiga ta zauna,gamida curewa waje daya,taso cusa fuskarta tsakanin qafafunta ko zataji salama,amma babu damar haka,saboda cikin dake jikinta,don haka sai taja mayafin rigarta ta lullube fuskar tata,sannan ta dora ta saman tafin hannunta,tana sakin ajiyar zuciya a jejjere kamar zuciyar tata zata fito.


Tamkar zatayi aman wuta daga qirjinta haka takeji,batason ta yanke hukunci babu yawun abbaa,amma tanajin dole ta aikawa da fulanin saqo,saqon da zai isa jikinta da zuciyarta yadda ya kamata
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 44

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070



"Inason nima ki shaida mata,ni zuhriyya qanwa ga mahaifiyar bilkisu,kuma uwa a yanzu a gareta....auren danta da bilkisu qaddara ce....wata qaddara wadda ta sanyani nayi nesa da 'yata,wata qaddara wadda a yanzun bata isa ta zama sanadin maimaituwarta ba,ki gaya mata....bilkisu ta yiwa danta nisa,tayi masa tazara kwatankwacin yadda sama ta yiwa qasa nisa,ki shaida mata ashe shi arziqi bawai kudi bane kawai....arxiqi yana a zuciya ne ba'a hannu ba,ki shaida mata,munfi qarfin dukkan wata dukiya tata da take tunanin ta mallaka,komai yawanta,ciki kuwa dan duma ne,yado yakeyi,da kansa zai fasa kansa,wala'alla kuma sanda zai fasa kan nashi,yafi dukkan qarfinta da tunaninta,ya mata nisa ya mata zarra,ki sake shaida mata dai,ta rubuta ta ajjiye,akwai ranar nadama,akwai kuma ranar qin dillanci....ki jadda da mata,ta sanyawa ranta bata taba alaqa da wata mai suna bilkisu ba,bare tayi zaton ta taba hada dangantaka da wani d'a nata,wannan shine saqona" daga wannan bata qara cewa komai ba,hakanan bata sake waiwaya ta dubi daya daga cikinsu ba ta fice,don hankalinta gaba daya yana kan bilkisu tunda ta fice.


"Kukan me kikeyi?,bai kamata kiyi kuka ba daughter kina da uwa kamata,share hawayenki" ta fada tana daga bilkisu,saidai yanayin da ta ganta ya kadata gamida daga hankalinta,duk yadda taso shawo kan abun ya gagara,dole sai data danganata da asibiti,wanda sai data kwana biyu sannan tasamu shawo kanta,wannan dalili ya sanya ita da abbaa suka yanke shawarar fara shirye shiryensu su koma inda suka fito,amma da farko zasu fara yada zango a ethopia don kaita taga tarin dangi da 'yanuwa wadanda bata sansu ba,suma basu santa ba.


Cikin qanqanin lokaci komai ya kammala na bilkisu,su dama ticket kawai zasu siya,don suna da visas dinsu kuma basu qare ba.


********* """"""""" *********



"Shaida min abinda suka sake aikoki dashi" fulani dake tsaye ta fada tana duban wani guri daban,kamar yadda ta umarceta haka ta gaya mata komai dalla dalla,bata boye komai ba.


Ga mamakinta murmushi fulani tayi tana jijjiga kai,sannan tayi tattaki mai dan dama kafin ta dakata,tana mamakin yadda saqon ya samu muhalli me kyau a cikin zuciyarta,amma duk da haka ta bari son rai yayi mata jagoranci,ta bude baki tace
"Wannan kadai ya isa ya zamemin shaida kan cewa qarya suke,idan har da gaske suke...zasu tsaya iyakacin tsayawarsu suga sun tabbatar da gaskiyarsu,mu rubuta duka mu ajiye,maga wanda zaiyi dana sanin....tashi kije luba" ta fada tana takawa tabi wata siririyar hanya.


********** ***********


Tsit falon yake wanda sai kayi tsammanin babu wata halitta a cikinsa,qarar ac ne kawai ke tashi sai na sauran na'urori dake da alaqa da dakin.


Mutum biyu ne zaune saman lausasan kujerun da aka yiwa falon qawanya dasu,azeez ne da abdulrashid,wanda shurun ya afku ne sanadiyyar maganar da suka gama yi yanzu tsakaninsu.


Gauruwar ajiyar zuciya abdulrashid yasaki sa'an nan yace
"Babu wanda ya zaci al'amarin zaizo a haka,yanzun maganar ta canza,ana maganar jininka ne wani sashe na jikinka,abdul'azeez's photocopy,tamkar wani copy naka ne ajiye a wani waje,wanda bai cancanci koda kowa ya wofantar dashi ba kaika aikata hakan" wata iriyar ajiyar zuciya dake nuna gazawarsa da gajiyawarsa ya saki yana duban abdulrashid,da wani irin amo a muryarsa ya sake bude baki karo na biyu
"Wannan shine the same tunani na abdul.....indai har da gaske ne,yanzu ana magana ne ta jini,ana magana ta zuri'a....ban damu da amincewarta ta yadda da shirin da duk akaje mata dashi saboda kawai dukiya ba,ina duba da jinina ne,jini na ne a jikinta...but...fulani ta kasa fahimtar hakan,taqi yarda nayi mata bayani,taqi tsayawa ta saurareni,infact tama qaryata maganar,if maganar gaskiya ne me zai faru a gaba?".


Duban azeez din sosai abdulrashid yake,yana karantar wasu emotions dake saman fuskarsa,yana maganar ne deep inside him,akwai kuma wani babban lamari mai girma tattare dashi,bai taba ganin azeez din tunda suka taso daga quruciya zuwa yanzu ba ya damu da lamarin wata mace ba,bai taba ganinsa yana maimaita batu kan wata diya mace ba sai yanzu,koda ya take dashi kuwa idan ka dauke mahaifiyarsa,sai yanzu gashi wasu emotions na tashi daga saman fuska da kuma muryarshi,lallai wani abu na shirin faruwa.


Ajiyar zuciya abdul ya saki sannan yace
"Ni ina ganin kawai ka shaidawa mai martaba...." Idanu azeez ya zuba masa,sannan a hankali yace
"If idan qarya ne fa,maganar ba gaskiya bace?" Shuru yasake yi na wasu sakanni sannan yace
"Akwai fahimtar juna da qauna mai yawa tsakanin fulani da mai.martaba,idan har na shaida masa ni nasan girman abinda zai biyo baya,bazai yiwa kowa dadi ba,kuma ya zamana maganar ba haka take ba...yaya kenan?,na watsawa fulani qasa a idanu,na tozartata gaban maqiyanta,na bata tsakaninta da mijinta,akwai abubuwa masu tarin yawa da zasu iya biyo baya" kai abdul ya kada,tabbas shima ya hango cakwakiya mai tarin yawa cikin aikata hakan,shuru yayi yana lalubar wata mafitar,wanda kafin yakai qarshen nazarin nasa maganar azeez din ta katse masa hanzari
"Akwai hanya guda daya da nake tunanin zata bullemin"
"Waccece?"
"Zan binciki sahihancin maganar ta hanyar matar data kawowa ammi saqon"
"Good...amma a ina zaka samu matar?"
"Ma'aikaciyar masarautarmu ce,zanyi magana da sunusi,yasan kusan fiye da rabin barori da ma'aikatan gidan,zan dorashi ya bincika min komai..." Ya qarashe maganar yana miqewa tsaye,yana jin tamkar an warwareshi daga wani sasari da aka sanya masa,kai tsaye dakin abdulrashid din ya shige,yanason ya samu bacci don ya sake samun nutsuwa na aiwatar da komai.


Sanda abdul ya shiga dakin ya tadda shi tuni yayi nisa a kwanciyarsa,daga shi sai dogon wandon rigarsa,da fara qal din singlet,ya ware ac da fanka gaba daya,murmushi mai hade da dariya ya saki
"Problem solved"
"In sha Allah" ya amsa mishi yana lumshe kyawawan idanunsa da sai yanzu yaji bacci nason rinjayarsu.


******* ***** ***** *****


Hannayenta goye a baya take kai kawo,tabbas babu wanda zai sanya sunusi binciken inda luba take sai azeez,tunda shine shugaba kuma babba a masu kula da sassansa,akan yana nufin kenan ya take maganarta,gaba daya lamarin me yake nufi?,binciken luba yana da alaqa da yarinyar nan,ko kuwa wani issue ne na daban.


Sosai hankalinta ke a dage,karon farko data soma cin karo da wani abu da yayi kama da saba umarni daga azeez din,ba shakka zata nuna masa qarfin qwanji,da qarfin kasancewarta uwa,bata so kuma bata fata abinda zuciyarta ke qissima mata ya tabbata,ko a mafarki bata buri ko tunanin haka.


Cikin gaggawa tasa a nemo mata azeez din tana nemansa duk inda yake,saidai kuma aiken nata bai sameshi da wuri ba,sakamakon yana wurin mai martaba suna tattaunawa,yana son xaiyi tafiya marocco,kuma a qalla zai dauki kusan sati guda a can,duk da cewa yakanyi tafiye tafiye,amma bai fiya zama ko ya dade ba saboda mutanensa.


Lokacin daya fito daga wajensa,saqonta shine abu na farko da aka gaya masa,duk da yadda yakeso ya watsa ruwa a jikinsa amma haka ya yanke dukkan wani uzurinsa ya nufi sassanta.


Yanayin daya taddata yasa hankalinsa ya daga,ta jefa masa wani kallo da zai iya cewa bai taba ganinsa irinsa cikin idanunta ba,sannan cikin kakkausar murya ba tare data amsa gaisuwar da yake miqo mata ba,murya mai cike da gargadi tace dashi tun bai ida zama ba
"Wannan shine karo na qarshe da zan maka magana kan wani batu daya shafesu indai nina haifeka....ka dakatar da duk wani lalube da bincike da ka sanya ake maka kan luba,don ko ka samu luba ba zaka sake samun komai ba daga gareta,abdul'azeez!....karka sake ka tsallake gonata,karka sake mu sanya qafar wando daya dakai,a karo na biyu ina sake gaya maka....ka ajjiye duk wani abu daya dangancesu daga kwanyarka,tun baka shigo gonata ba,ka fuskanci abinda yake gabanka!,wannan shine umarni na" bata bashi damar cewa komai ba tayi gaba tabarshi a nan,shi dinma baijin koda ta bashi dama zai iya cewa wani abun,saboda yadda kwanyarsa gaba daya ta dinke,ya juya cikin wani irin yanayi yana takawa shima ya fice daga farfajiyar.


Wani irin juyawa yaji kansa yana yi,yanajin gangar jikinsa kamar ba tashi ba,karon farko da yaji har cikin zuciya da gangar jikinsa umarnin ammi bai samu masauki ba a qwaqwalwarsa,yakejin kamar bazai iya biyayya wa umarninta ba,ya miqe a hankali kamar me ciwon laka ya soma takawa,gaba daya zuciya da qwaqwalwarsa tayi nisan zango a tunani.


Kwananshi biyu ko ammin bata ga idanunsa ba,yana cikin wani irin yanayi da iya tsahon rayuwarsa bai taba shiga ba,ya qure tunaninsa gaba daya kan hanyar da zaibi ya kawowa kanshi mafita,yafi kowa sanin ammin nashi kaifi daya ce,gaba daya 'yan hamayya da abokan adawa sun gurbata tunaninta,tabbas duk wanda ya santana shekarun baya ba haka ammin take ba,to amma kusan shi a kansa komai yakeso ya qare,shin wannan soyayya ce?,kuma gata ne?,zai iya cewa eh,amma bisa hasashe da tunanin mahaifiyarsa,saidai akwai tarin kusakurai masu yawan gaske cikin dukkan hukuncinta da take yankewa,wanda takan dora komai ne bisa mizanin ramuwa da ganin ta cimma gaci,ta cusa baqinciki da bacin rai cikin zuciyar maqiyanta,amma hakan gashi yanason shafar rayuwa da walwalarshi.

********* ***** *********


Kamar kowanne lokaci yau cikon kwana na uku,yana kwance shi daya a falonshi sanye da singlet da dogon wando,idanunshi saman tafkekiyar tv dake girke

Please Login or Register in order to submit comment