Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tambaya.


Sai daya kai aya sannan azeez ya bude dukka idanunsa akan abdulrashid,cikin tattausan muryarsan nan da lafuzzansa masu kama da ana jera masa su yace
"Ragon maza nake akanta,hakanan banda wayo ko wata fikira indai akanta ne,jarumi nake kuma zaki tsakanin maza 'yan uwana,mai furgita duk yarinyar data nemi shiga gonata ko hurumina ba tare da yarda ko amincewata ba" saiya tashi ya zauna sosai bayan yakai qarshen xancan,idanunsa da suka jajjanye duka akan abdulrashid,hannunshi daya ya dora saman qirjinsa bayan ya dunquleshi,daidai saitin zuciyarsa
"Kasan me nakeji anan abdulrashid?,kasan kullum da yadda nake bacci?,kasan yadda zuciyata ke zugi?,amma sam taqi fahimtar haka,taqi ta bani dama,taqi ta gane cewa bayaga mahaifiyata itace mace ta biyu da nake tsananin so da qauna,macen da bazan iya sake jure rashinta ba,me yasa ba zata fahimta ba?" Ya fada a hankali launin qwayar idanunsa na sauyawa.


Nannauyar ajiyar zuciya abdulrashid ya saki,tausayin azeez din yaji yana shigarsa,lallai dukkan abinda zai saka azeez din ya zauna yaba tona asirin zuciyarsa haka ba qarami bane,tunda suke tsahon tasowarsu tare,bai taba ganin yana yiwa wani abu irin wannan son ba,jarumine na gasken gaske,lallai ya cancanci a tausaya mishi.


Bai ankara ba yaga ya miqe
"Zanje na samu me martaba,koda zaiyi gunduwa gunduwa da namana na roqeshi ya saita lamarin,shirunsa din nan abdul nasan yana nufin abubuwa ne da dama....ina zuwa" ya fada yana shigewa ciki inda zai sadashi da 'yar qoramar da aka tanada saboda wanka wadda tayi shige da swimming pool amma a gargajiyance.


¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶


Yayi mamaki lokacin daya ganshi cikin hakimai a fada,ya saje cikinsu cikin ire iren shigarsu shima,saidai ya dake ya kuma nuna kamar bai ganshi din ba.


Duk tsahon awannin da aka dauka din yana nan tare dasu bai motsa ba,har zuwa sanda aka gaman zaman,sarki ya miqe yayi ciki yana biye dashi,sauran 'yan majalisar sarki suma kowa ya wuce uzurin gabanshi.


Daga shi sai me martaba ya rage,har zuwa lokacin yana biye dashi ba tare da yace komai ba.


Waiwayowa yayi sanda yake niyyar shigewa turakarsa,suka hada idanu da azeez,a ranar sai yaji mahaifin nasa ya masa kwarjini matuqa kamar sauran mutane,saiya sadda kanshi qasa
"Lafiya dai ko?,inason na shiga ciki na huta" me martaba ya fada yana duban azeez din,duk da yasan da walakin goro a miya.


Zubewa yayi nan gabanshi saman gwiwoyinsa,cikin sanyi da matuqar nadama ya soma neman alfarma a wajensa gameda lamarin bilkisun,tare da alqawarin amsar dukka hukuncin da yace ya yanke a kanshi.


Shuru ya masa har ya kammala sannan yayi gyaran murya
"Saboda ni ka daukeni qaramin mutum ko?,bayan mutuncina da kuka gama zubdawa da saidawa a idanun al'ummata yanxun kakeso na sake zuwa na ɓarar da sauran da hannuna?,ai abdul'azeez ta inda aka hau ta nan ake sauka...kaje ka samu uwarka yadda kuka qulla ku warware,kasan kana sonta amma ka bari akayi wannan barnar da kai?"
"Afuwarka da yafiyarka nake nema,ba don ni ba,kodon albarkacin 'yan biyun dake tsakaninmu"
"Yan biyu!" Mai martaba ya furta ba tare daya shirya ba,ya kuma sake fadin
"Kana nufin akwai zuriyya tsakaninku?" Kai ya gyada yana sake tabbatar masa,shuru me martaba yayi bayan ya lalubi kujera ya zauna,kyawawan mintuna biyar bai iya cewa komai ba,daga bisani ya miqe bai cewa azeez komai ba ya wuce ciki ya barshi a nan.


Daren ranar gaba daya sarki abdallah ya qarar dashi ne wajen nazari da kuma neman mafita wadd zata zama adalci sulhu kuma alkhairi a gareshi da ahalinsa.


Jikinsa ya bashi tabbas wannan lamarin jarrabawarshi daga ubangijinsa,ya jarrabeshi kan macen da tafiso cikin matansa,da yaron da yafiso cikin yaransa,duk da tarin qoqarin adalci da biyewar da yake,hakan ya sanya daga shi sai ubangijinsa ne kawai sukasan da wannan sirrin.


Kwanaki biyu ya dauka qwarara dukkan bincikensa ya kammala a asirce,duk abibda azeez din ya fadi babu qarya a cikinsa,hakan ya kawo masa sassauci kan hukunci da matakin da yayi niyyar dauka a kansa.



A kwana na ukun bai samu sassauci ba sai daya ganshi kan hanyar gidan malam bilyaminu da kanshi ba aike ba,cikin mota qwaya daya mai baqaqen gilashi,dagashi sai amintattunsa mutum uku,cikin salo na bad da kama,don baka isa kace sarkin kaisa bane a motar.


*GIDAN MALAM BILYAMIN*


Tub dawowarsu kaisa din ya zamana kusan kullum yaran na wajen malam bilya,da hauwa'u wadda har kukan dadi mlm bilyamin din yayi da dawowarta cikin 'yan uwanta,domin yayi cigiyar yayi neman har ya gaji ya haqura,albarka babu irin wadda bai shiwa bilkisu ba,don a yanxun kusan yaranshi har mazan kusan suna gabanshi,su mazan biyu daga cikinsu suke kula mishi da shagunansa,tunda a yanzun shi babu damar fita kamar daa,jikin yaqi dadi,ciwo yaqi barinsa,yau da lafiya gobe babu.


Sau tari yakan zauna ya zubda hawayensa idan yaga yadda Allah yayi dashi,wato duk abinda kaga Allah ya hanaka mai yiwuwa akwai hikimarsa cikin hakan,me yiwuwa ya baka wani abun madadinsa wanda kai bakasan da hakan ba.


A da yana kukan talauci da babu,yana ganin Allah ya hanashi dukiya,ashe ya masa musayarta ne da cikakkiyar lafiya,daga baya ya amshe lafiyar ya barshi da kudin,wanda kudin gashinan sun gaza siya masa lafiyar,ga kudin da zaici duk abinda yakeso,zai saka duk suturar da yakeso amma rashin cikakkiyar kafiya duka ya hana wannan,saidai ya kalla iyalansa da kuma wasu a waje suci,ashe babu arziqin da yakai na lafiya.


Cikin wannan jimamin da alhinin ya kama mama ladida sabuwar amaryarsa sun hada kai suna kitsa yadda zasu masa gagarumar sata,saboda a cewarsu idan ya mutu ba zasu tsira da komai ba bayaga tuminin takaba,umma katti da 'ya'yansa su zasu wawashe komai.


Wannan ma ya tashi hankalinsa qwarai,ya dinga kuka bayan ya sallami kowaccensu da saki bibbiyu,saiya dinga tuno rayuwarsa da maimunatu mahaifiyar bikisu,ta fishi kyau,ta fishi nasaba ta fishi dukiya,amma ta yarda,ta zabi ta rayu dashi badon yana da komai koya mallaki komai ba,ta ajjiye dukkan wasu qualities nata,ta haqura da rayuwar gidanshi,harta mutu bai ajewa ba bai bawa wani ajiya ba barema ta saka rai,sai gashi yanzu wadanda ya tsincesu sama taka suna neman kassarashi ta sandin dukiyar da aka samu ta hanyar diyar maimunatu,dukiyar da ita maimunatun bata dandana ba.


Ashe duk tsiya duk masifa matar babu ba qashin yardawa bace,sabida tunda suke da umma katti bata taba yunqurin gwada hakan a gareshi ba,itadai barta da masifarta da bala'inta,son yaranta ta hana na wani,da nuna mishi yatsa,amma babu wannan mugun qullin a ranta,ranar yayi kusa sosai ya kuma yi nadama,tare da godewa Allah da yaketa haska masa gaskiya tunda sauran lokacinsa.


To a yau din ma kamar sauran ranakun,da kanshi yayi kiran bilkisun yace ta kawo mishi 'yan biyu,ta shirya da kanta,yaran kuwa suma sunata murna,don ba qaramin son zuwa gidan suke ba,saboda yadda kowa ke nan nan dasu,ta shiryasu sosai,tayi musu adon shadda ash,wadda abba ne ya dinka musu su biyu kawai.


Itakam babu abinda zata cewa Allah sai godiya,kowa son yaran yake,nuna musu qauna da kulawa yake.


Da kanta ta kawosu,ta zauna suka sha hira da malam bilya din,sannan ta shiga ciki wajen 'yan uwanta suka sha hirarsu suma bayan ta gaida umma katti.


Hirarsu suke gwanin sha'awa,duk sanda ta daga kai ta kalli yan uwannata taga yadda rayuwa ta musu kyau hakan na sake faranta mata,a yanzun haka zancan auren auren hannatu ma akeyi.


Awa biyu kawai tayi tatafi tabarosu acan,tasan akwai masu kawosu gida,idanma sun kwana duka ba damuwa,don tasan mawuyacine su qyalesu su dawo a yau din.


Bata rufa awa guda da tafiya ba motar maimartaba ta iso layin,a daidai qofar gidan suka faka,yasamu tabbaci yana nan,saboda a yadda aka bincika masa ba kasafai yakan fita din ba kamar yadda muka sani.
7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 69
https://youtu.be/NNr-vDOJzq8

https://youtu.be/NNr-vDOJzq8


*CI KA ZAUNA LAFIYA*
*_youtube channel_*

*TARE DA*

*DR KABIRU ABDULKARIM*

_Tashar youtube irinta ta farko,wadda ke dauke da tarin ilimi irin wanda al'ummarmu take da buqata_

_Tashar da zata koyar daku dimbin darussa,ta yadda zaku samarwa jikinku garkuwa ta cikin abincin da Allah ya yassare mana_

_zata koyar daku yadda zaku kare kanku daga kamuwa daga cututtukan da suka addabemu,ta hanyar ganyayyakin tsirrai da tsaba_

_hakanan akwai tarin sirrikan gyaran fata,gyaran gashi da gyaran jiki gaba daya,ta hanyar amfani da sarrafa abincinmu_

_tashar CI KA ZAUNA LAFIYA ke/kai/su/ita/mu kowa nada buqatarta,walau lafiya kake ko akasin haka_

*_garzaya maza kayi SUBSCRIBE sananna ka danna LIKE kayi SHARE ga iyaye,yan uwa da abokan arziqi don kada ayi babu su_*
_________________________
___
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070



Su biyu ne rak cikin falon,daga shi sai maimartaba,wanda ko a mafarki malam bilya bai tsammaci zuwanshi har cikin gidanshi ba.


A hankali maimartaba ya sauke ajiyar zuciya kana ya miqawa malam bilya hannu,hannun ya kalla kana ya kalli maimartaba,ya sakar masa murmushi gamida bashi qwarin gwiwa,hakan ya sanya malam bilyan miqa masa hannu sukayi musabaha yana tambayarsa iyali.


Shuru na sakanni ya biyo baya,sannan mai martaba ya soma magana cikin nutsuwa
"Da farko malam bilyaminu....banason ka kalleni da idanun sarki,inason ka kalleni da idanun uba ga mijin 'yarka,sa'annan kuma suruki a wajenka,inaso muyi magana takai tsaye,kowa ya fadi abinda ke zuciyarsa,banason kaji nauyina ko kayimin alfarma" saiya dan tsagaita yana duban malam bilyan sannan ya dora.


"Dani dakai dukkan munsan abinda ya wakana tsakanin yaranmu shekara bakwai baya basai anyi bita ba,saidai nidin shekaru bakwai da suka shude,sun shude ne ba tare da nasan wannan lamarin ba,wanda kuma bansan da wanzuwar tashi ba sai cikin shekarar nan,a shekararnan dinma cikin satin nan,da fari ina mai baka haquri a madadina matata da dana akan wasa da akayi da rayuwar diyarka,tabbas anyi maku abu mafi muni,zalunci cikakke wanda dukkan dan adam din da aka yiwa an cutatawa rayuwarsa,nayi matuqar girgiza dajin labarin da yadda aka wofantar da jinina da yake tattare da diyarka,wanda a yanzun Allah ya rayasu....inajin nauyin magana ta gaba da zan furta,amma kuma dana zauna nayi dogon nazari akai sai naga shine mafita a rayuwar ƴaƴanmugaba daya nida kai da kuma jikokinmu"saiya tsagaita yana sauke numfashi sannan ya dora
"Cikin labarin daya bani ya tabbatar min yarinyar na a matsayin matarsa ne har yau,da farko ban yarda ba na kuma qaryata,saboda ba lamari bane da hankali zaiyi saurin dauka ko ayi amfani dashi ba,amma daga bisani daya gayamin shaidun daya maida matar tasa a gabansu,saina tabbatar da ingancinsu da kuma adalcinsu,amma duk da hakanan ban tsaya a nan ba,sai dana kira kowannensu na tabbatar da cewa haka maganar yake,wanda daya daga cikinsu tana kamar a matsayin uwa a wajensa ne....alfarmar da nake nema a nan ayimin itace,bilkisu ta koma dakinta a matsayin matar abdul'azeez,bayan na tabbatar da nagartar halayenta daga bakin wadda ta zauna da ita,hakan ya alamta min tana daga cikin sahun mata na gari daya kamata a riqe da kyau,rabuwa da ita tamkar tafka wata hasara ce mai girma,hakanan ko babu wannan an cutatar da rayuwarta,babban adalcin da zanyi a yanzu a damar da Allah ya bani shine ta sake komawa a matsayin matarshi,wanda duniya duka zata shaida,shaidawar da a baya bata shaida din ba".


Ba qaramin burgeshi sarki abdallah yayi ba,bai taba zato ko tsammatar haka ba,labarin adalcinsa da sauqin kansa ashe ragewa ake?,inama ace dukka shugabanninmu zasu kasance kamar haka?,inama a ce na sama zai kasance mai tausayi da adalciwa na qasa kamar haka?,tabbas da duniya ta zauna lafiya,da mun rabu da tarin matsaloli da suke addabarmu a yau,ba shakka ya koyi tarin darasi a yau daga sarki abdallahn,wanda yake zaune tare dashi babu wani shamaki,da ace wani zaya shigo baha ga suttutar jikinsa kuma baisan fuskarshi ba.....babu abinda zai hana yace ba sarki bane wannan.


Ajiyar zuciya shima malam bilya ya saki,yana jin kunyar kanshi da kanshi,kowanne uba na gari yakan kauda son zuciyarsa ashe ya zabawa zuri'ar da Allah ya nashi nagartaccen abu da yasan shi dasu zasu kubuta har a gaban Allah,tabbas wannan babban darasine daya sake samu a yau
"Dukkan abinda ka fada na jisu na kuma fahimta,saidai komai bai gudana ba saida gudunmawata da goyon baya na,bawai sunsa qarfi bane sun dauki 'yar,saidai kwadayina da son tara abun duniyata da dukka shi ya janyo hakan,ba shakka nayi nadama,nayi nadama mara iyaka kuma ina kan yinta,ta yadda na dauki yarinya mafi biyayya cikin iyalina na sadaukar da rayuwarta da mutuncinta,yarinyar data fito daga mace mafi soyuwa,nagartacciyar mace daya tamkar da dubu,matar da har yau ban maida kamarta ba,amma kwadayin samun dukiya duka ya rufemin idanu yasa na manta wannan"
"Idan akwai abinda ya kamata ace raina ya baci guda daya ne,ina namen afuwa,naji baqinciki naci kuma alwashin cewa.....daga ranar da aka kore cikin dake jikin maigado,bakai ba....koma waye zayaxo da sunan sunaso daga baya,koma waye yazo da sunan zuri'arsa ne bai isa ya amshesu ba,ciki kuwa harda hukuma.....kai din mutum ne mai girma kuma adali,wanda na tabbatar dama can baka da masaniyar wannan kitimurmurar,zuwanka wannan waje a irin wannan yanayin ya sake tabbatar da kai din waye,na yafe iya haqqina,amma akwai abu daya..." Saiya dakata shima yana gyara zamanshi.


"Daga wancan lokacin dana gane kurena,na gane gangancin da karan tsayen da na yiwa rayuwarta,saina dauki alqawari akaran kaina,sa'annan na dauki alqawari tsakanina da ubangiji na cewa....bazan sake yanke hukunci irin wannan cikin rayuwarta ba har na koma ga Allah ba tare da amincewa ko lamuncewarta ba,bazan sake yanke hukunci irin wannan kan rayuwar duka yarana ba,koda yara maza bare matan....saboda haka,a yanzu bani data cewa,sai abinda ta zaba a karan kanta" murmushi mai martaba yayi yana jinjina kai
"Ai koda ka amince surukina bazan taba yarda a zartas da komai ba saita amince da kanta,saboda dukkaninmu nida kai ba haqqinmu bane ba nata ne,sannan koda ta yardan bazan taba nemawa abdul'azees ko mahaifiyarsa sassauci ko dukka hukuncin da taso yanke musu ba,matuqar dai ta amshi alfarmata shikenan,sauran hukunci duka nata ne,yanzu wannan magana ta rage tsakanina da 'yata ne,naka ido kawai"murmushi malam bilya shima ya saki,yana jin dadin yadda ya maida bilkisu 'yarsa sosai kamar azeez din,yana niyyar cewa wani abu amatur rahman da abdulrahman suka shigo da gudu abdul din yana biye da ita,da alama wani abu ne ya hadasu.


Tunda suka shigo gaba daya suka tafi da hankalin me martaban,numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi,ya zuba musu idanu babu ko qiftawa yana kallon hukuncin ubangiji,sak abdul'azeez dinsa.


Kabbara yake a zuciyarsa yana sake kadaita Allah,iya yaran kawai sun isa su zama ishara garesu,sun isa su bayyanawa kowa cewa wani babban lamarine can dama da Allah ya boye a tarayyar bilkisu da abdul'azeez din.


Yana zaune ya kasa magana har malam bilya ya raba gaddamar,sannan ya kalli me martaba fuskarsa qunshe da murmushi
"Wadan nan yaran kadai sun zama wani farinciki da garkuwa na zuciyata,su kadai idan na kalla nakan tabbatarwa kaina lallai alqawari Allah na haihuwarsu ne ya tabbata....amatu kuje ga kakanku can ku gaidashi" ya fada yana dagasu daga jikinsa.


Idanu suka tsura masa,sannan suka juya suka kalli junansu suka kuma kalli malam bilya,sannan suka maida dubansu again ga maimartaba da yaketa jifansu da murmushi,ya qagu yaji dumin jikokinsa,kamar ya janyosu zuwa jikinsa saboda tsabar zaquwa.


"Ku qaraso mana taurarin masarautar kaisa" ya samu kanshida furtawa tsabar tsananin farincikin da yakeji cikin zuciyarsa,sashe daya na zuciyarsa kuma yana jin takaici da kuma kaico na ba cikin masarautar aka haife musu suba,saidai duk da haka yana miqa godiya ga ubangiji me dumbin yawa daya sanya suka fito daga tsaftataccen tsatso,hanya ta gari,sunnar ma'aiki S A W ba haihuwar titi ba
"Ammi zata mana fada,rannan ta kusa zane abdul,sabida yayi irin abun kanka a kansa" duka shuru sukayi,suba yara bane,sun fahinci me yarinyar keson fada,sai maimartaba ya saki murmushi yana shafa nadin dake kanshin
"Idan na cire zakuzo?,kuma ba zatayi fadan ba?" Dukkansu suka gyada kansu,saiya sanya hannunshi biyu yana nufin cirewar.


Da sauri malam bilya ya dakatar dashi
"Karka biye musu ranka ya dade.....ke amatu,abdul....ku qarasa maza ku gaidashi,ni nace muku ai,don haka ba zatayi fada ba"


Dukkansu luf sukayi q irjinsa tamkar sun jima da saninsa,ba shakka jini ba wasa bae,sai yaji idanunsa suna son cikowa da qwalla,yau ga yaran abdul'azeez dinsa a jikinsa,jinin azeez dinsa,lallai Allah da girma yake.


Ya dan jima da yaran har sai da yaga sun saki jikinsu dashi,sannan ya musu kyauta mai yawa,ya kuma wuce gida da alqawarin zuwa yaga bilkisu da kanshi.


¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶


Dukkan abinda me martaba keyi babu wanda ya sani,hakanan ya nemi anty zuhriyya da abbaa da kanshi ya gana dasu.


Nauyinsa girma da kuma shekarunsa suka hana anty zuhriyya tuburewa,mutum ne shi mai fahimta da saurin gano mutum,ya fuskanci a bacin rai take,hakanan taci alwashi sosai kan abinda akayi musun,saboda haka ya saki murmushi
"Bazan hanaki daukan dukkan matakin da kike gani ya dace ba,matakin da kike ganin shine zaisa ki huce....duk da mantawa zaiyi wahala,saboda anyi muku dukkan abunda ya cancanci dan adam yayi fushi akai,wanda koda nine akaiwa bazan qyale ba....amma ni alfarma daya nake nema shine,a maidamin surukata tare da yaranta,ta koma cikin ahalina,duk duniya kowa yasan cewa itadin ta zama familyn marigayi sarki mu'az kaisa,jikokina susan asalinsu,hakanan aurensu yaci gaba...bayaga haka bana buqatar komai daga haka".


Ita dinma kamar shigen abinda malam bilya ya fada haka ta amsawa maimartaba cikin girmamawa
"Allah ya taimakeka....indai wannan alfarma ce mudai mun maka,adalcinka yafi gaban ka nemi abu aqiyi maka,saidai.....bilkisu marainiya ce,hakanan mun mata alqawarin cewa zata yanke dukkan hukuncin da yayi mata babu mai tursasata,saboda duk qalubalen rayuwarta ta fuskanceshi ita kadai ba tare da munsan me ta gani ba,don haka muma kuke roqon alfarmar cewa,zamu barta ta yanke dukkan hukuncin da taso" kai yake jinjinawa cike da gamsuwa
"Maganarku da hukuncinku yayi daidai,matuqar muka shigo da tursasawa cikin lamarin bamuyi adalci ba sam,hakanan ba lallai mu samu abinda muke nema ba....,a yanzun haka na baro ayyuka da yawa a fada,amma zan dawo da kaina rana ta daban na ganta muyi magana".


Ko bayan tafiyarsa zancan suka rinqa tattaunawa a tsakaninsu,sam bawan Allahn bai dauki mulkin da yake dashi a bakin komai ba,ya dauki rayuwa da sauqi qwarai da gaske,ko a mafarki basu taba kawo cewa zaiyi tattaki har cikin gidansu ba saboda diyarsu,basu taba zatan zai nema wata alfarma ba daga gurinsu,duba da irun girma matsayi da martaba da yake da ita.


Saidai duk da wannan babu abinda ya rage haushin fulani a zuciyar anty zuhriyyan,da kuma alwashin da taci a kanta na nuna mata kurenta koda sau daya ne tak cikin rayuwarta,tabbas saita aiwatar da wannan,saboda ta san itace kanwa uwar gami,kuma ummul'aba'isin na faruwar komai


Cikinsu babu wanda yayi zancan da bilkisu,itama kuma batasan meke wakana ba,tasan dai a ranar anyi baqi a gidan,kuma da alama manyan mutane ne,daga haka bata fahimta komai ba,kuma bata tamnaya ba,sabida dama tambayar abinda bai shafeta din ba ba dabi'arta bace.


*ABDUL_AZEEZ*


Duk da abinda mai martaba yayi masa na nuna halin ko inkula,da kuma korar da yayi masa hakan bai sanya ya haqura ba,ya sake iskeshi a dakin hutawarsa,bayan ya gama wani xama na musamman da dukka hakiman dake qasarsa.


Da kallo me martaba ya bishi,yana karantar sauyi qarara tattare dashi,ga duk wanda ya sanshi duba daya zai masa ya tabbatar da cewa lallai abdul'azeez din ya sauya,hakanan akwai abinda ke yunqurin kawo masa tarnaqi a rayuwarsa.


Bai dakata ba har sai daya isa gabanshi a lokacin da yake kashingide,ya zube bisa dukka gwiwoyinsa a gabansa kanshi a qasa
"Na sake kawo kaina Allah ya taimakeka,na sani cewa nidin me tarin laifi ne a wajenka,hakanan na cancanci dukkan wani hukunci daga wajenka,amma ina roqon yafiya da gafararka da kume neman alfarmarka kan ka shiga lamarina" ajiyar zuciya ya sauke a boye,yana mamakin yadda duk sanda zaiyi magana saiya tattarawa kanshi dukka laifin ya aza saman wuyanshi,sam baya ambata ma sunan mahaifiyarsa a ciki,kamar shi kadai ya aiwatar da abun,yanajin tausayinsa amma yana ganin bai kai stage din dazai janye horonshi haka tunda wuri ba shida uwarsa,cikin tsare gida irin wanda yakanyi lokaci zuwa lokaci,musamman idan yana shari'ar data bata masa a rai a fada yace
"Banga amfanin zuwa ka nemi yafiyata ba,bayan bani kuka zalunta ba,mai ciwo daban mai neman magani daban?,kuma ma da kake fadin na shiga case dinka azeez ashe ina da qima da mutunci har haka?,ai na zaci nidin ba kowa bane,hakanan bani da wata rawar da zan taka cikin rayuwarka,banason na sake jin komai daga bakinka,ka tashi ka nemi yafiwa wanda kuka batawa,don ni babu abinda xan iya yi maka".


Yafi kowa sanin cewa shidin kaifi daya ne,idan yayi gaba mawuyacine ya dawo baya,daya daga cikin halayen daya gada kenan daga gareshi,don haka gwiwa a sake ya miqe ya soma takawa a hanakali hannayensa goye a bayansa,fulani aisha tayi saurin komawa da baya kafin ya risketa,zuciyarta na wata irin quna,saita fasa shigowa,ta koma izuwa sashenta,tabbas dole tasan abunyi,basu taba samun sabani koda shigen wannan ba tsakaninta da maimartaba,bare abdul'azeez da yake lelensa,ya kamata ta farka,ta kuma lalubi abunyi.


Babu wanda ta kula koda barorinta da suka zube suna ta faman yi mata barka da dawowa,hakanan afanan data samu zaune a falo tana karatu,itama afnan bata ce komai ba,sai binta da kallo da tayi harta shige dakinta,ta dauke kai afnan ta maida ga littafinta,saidai kuma itama zuciyarta ta fada kogin tunani.


Kai tsaye ta tsaya a gaban mudubin dakinta,kanta take qarewa kallo sosai,ba zata iya tuna wani abu daya taba damun rayuwarta ya sanyata rama haka ba irin wannan lamarin,ra hasaso azeez a idanunta,ta kuma hasaso sanda yake zube gaban maimartaba yaba masa magiya,amma yayi burus dadhi,kwatankwacin yadda yake mata itama,ta sima gajiya,ta sima kaiwa maqura,wai shin ma me zai hanata ta tunkari yarinyar ayi me gaba daya?,me zaisa ba zata sake bin wata hanyar ba,ta jarraba koda kome zai daidaita?,da wannan tunanin ta samu relief,ta kuma zauna tana tsara yadda zata gabatar da komai.


¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶

Kalaman da memartaba ya gaya masa,sai yaji kamar yana bashi izinin ya sake yin dukkan me yiwuwa ne ya nemi yardar bilkisu,hakan ya sanya a washegari ya kuma shiryawa kamar kullum shi daya tak,bayan ya dakatar dakkan 'yan rakiyarsa ya nufi gidan anty zuhriyya.


Sanda take fitowa daga gidan da niyyar zuwa gidansu zata dauko su amatu da suka kwana a can,daga nan kuma ta biya ta gidan biki ta su taho tare da anty zuhriyya,wadda dukkansu yau suna gidan wunin biki daga ita sai mai gadi a gidan,a lokacin ne shima ya faka motarsa,ya kuma fito yana kulleta sukayi kacibus.


Cak ta tsaya ba tare data iya koda qara taku guda

Please Login or Register in order to submit comment