Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta soma aikinta.


Gaba daya falon ya dauki shuru,kowa ya bada hankalinsa ga computer din cike da mamakin abinda suke gani din,dai dai gurin da kamal din ya fincike mata hijabi me martaba ya rintse idanunsa gami da bada umarnin a dakatar da recording din.


"Oh ni adama naga ikon Allah,yanxu kamalu matar aure matar dan uwanka zaka yiwa fyade,wannan wanne irin lalacewa ne?" Ta fada tana zabgo salati gamida nuna tsantsar alhininta,duk a shirinta na fidda kanta daga wannan tarkon
"Meye banbancina dake?,ni xuwa nayi kawai na aikata,amma kome da saninku da shawararki akayi ko?" Ya fada cikin fushi dajin haushin yadda ta soma luguiguita maganar tun me martaba ko yan fadarshi basuce komai ba,inda yake kallon hakan a matsayin tunzuri kawai dason sanya me martaba ya yanke hukunci me tsauri akansa.


Maganar kamal din ta sanya kallo ya koma sama,sai kowa ya zubawa fulani adama ido,wadda ta zare idanu ta dafe qirjinta da hannu biyu kana tace
"Sharri?,sharri zaka yimin kamal?,fauxiyya kina jin danki?,yanzu irin sakayyar da zakumin kenan?" Yatsina baki tayi tana jin komai ta fanjama fanjam,ba zata bari sunan danta shi kadai ya lalace ba
"Eh to ai gaskiya ya fada,ba sharri yayi miki ba da kiketa wani haqiqancewa" sarai ta fuskanci kai sukeson hade mata su turota rana,don haka taga gwara kawai ayi mutuwar kasko
"Kice dai da saninmu duka,ku daina magana kuna ingizamin laifi na kada mana fauxiyya" shewa hajja fauziyya tayi,ta soma ratttabo.irin shawarwarin da fulani adaman tasha bayarwa akan yariman da uwarshi,ganin tana kwance mata zani a kasuwa yasanya itama ta soma lissafo nasu shirye shiryen,sai kowa yayi tsit kawai aka zuba musu idanu suna tonawa juna asiri kamar zasu doki juna.


Tsawa me martaba ya daka musu ganin abun yana neman wuce gona da iri
"La'ilaha ilalallah,muhammadurrasulullah" me martaba ya maimaitawa,hatta fulani aisha da wasu shirye shiryen tasan dasu amma ba qaramin mamaki tayi dajin wasu abubuwan ba,da hannu me martaba ya sallami fulani aisha da iyalinta,suka baro su adama zaune a gabanshi.


Shuru ne ya ratsa tsakani a lokacin da suke komawa zuwa sassansu,kowa da abinda ke mamayar zuciyarsa,imani ya sake ratsa zuciyar fulanin,tabbas ta sani cewa addu'a ce ta tare mata dukkan wannan masifa da bala'in da sukaso sanyata ita da iyalinta a rayuwa,ba shakka addu'a babu abinda ta bari,amma meta musu a rayuwa haka?,kawai donta hada miji dasu?,kawai don ta fisu siyasar iya zama dashi?,shin ita meye laifinta?,me yasa basuyi tunanin makomarsu a wata rana mai zuwa irin wannan ba?,lallai sau tari bawa shike xabawa kansa qarshensa sakamakon irin ayyukan daya gabatar da hannuwansa.


Ajiyar zuciya azeez ya sauke sanda sukaxo hanyar da zata kai kowannw sashensa,ya bude baki zaiyi magana fulani ta daga masa hannu
"Duk wata magana ta qare abdul'azeez,Allah ya fitar daku,ya fitar dani ya kuma fidda kowa,kuje kawai ku huta,ku samu hutun da baku sameshi ba" murmushi yadan fidda,koda yaushe yana sake jinjinawa mahaifiyarsa,koda yaushe tana hidimawa farincikinsu,tsayayyar uwace daya tamkar da dubu
"Inaso ki bani izini zuwa yammacin yau mu wuce saudiyya....already na siya mana ticket,kuma yau dama a qa'ida tafiyar zata kasance,so banyi tunanin komai zai warware a qanqanin lokaci haka ba,sai nayi tsammanin zamuyi missing tafiyar yau shi yasa nabar maganar"
"Na muku izini abdul'azeez,Allah yaci gaba da tsaremin ku a duk inda kuke,bari nasa afnan ta shirya ma su amatullahi kayansu" daga haka ta janyo bilkisu jikinta
"Kiyi haquri daughter,an bata muku ranakunku masu dadi ko?,amma ina da tabbacin yarona zai maida miki mafiyansu" wata iriyar kunya ta kama bilkisun,saita sunne kanta a kafadar fulanin,yayin da azeez shima ke fidda wani qawataccen murmushi yana jifan bilkisun da wani narkakken kallo,anan fulani tayi gaba ta barsu,saiya matsa kusa da ita ya sanya hannunshi cikin nata a tausashe suka fara takawa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace
"Kinji abinda ammi tace,kinaso na maida miki madadin kwanakinki wadanda suka fisu taushi da dadi?" Shuru tayi ta kasa amsa masa har suka kusa isa sashensu,saiya saki ajiyar zuciya sannan yace
"Nayi alqawarin nuna miki zallar so da zai saki ki nutsu da soyayyar da abdul'azeez ke miki ta gaskiya ce,tarayyarmu zata fara ne daga sanda kika bani amanna da kanki" bata gama fahimtar zancanshi ba amma saita share,gudun kada ya sanyata a kunyar da zata kasa sukuni.


Basu wani zauna ba da kanshi ya shiga hada musu duk abinda suke da buqata don tafiya,abinda ya bata mamaki yadda taga sassan nashi akwai komai da zata iya buqata a ciki,kamar dama can ta taba zama a ciki.


Kamar yasan abinda ke ranta ya biya da ita gida ta yiwa malam bilya sallama,dukkansu suka shiga

Adaren yayiwa me martaba sallama suka wuce filin jirgi bisa rakiyar uswa sumaira aafiya da afnan,wadanda suma a gobe suke saka ran wucewa gidajensu tunda komai yayi settling.


Kamar yasan abinda ke ranta ya biya da ita gida ta yiwa malam bilya sallama,dukkansu suka shiga suka gaidashi cikin girmamawa da karramawa,wanda hakan yayima bilkisun mahaifinta harma da 'yan uwanta dadi,saboda girman da sukaga sun bashin sam.basu zaci haka ba.


Ta tadda 'yan uwanta maza biyu cikin su ukun da Allah ya baiwa malam bilya sun waiwayo gida,babu wani cikakken lokaci na doguwar magana,amma tace su jirayi dawowarta,dama tana da qudurin nemansu koda su basu waiwayo gidan ba,ranta duka babu dadi,don dukansu babu wani gagarumin ci gaba ga rayuwarsu,kawai dai anata nemawa kai na rufin asiri ne,amma dai jiya iyau haka suke.


Suna hanya bilkisu na kusa da afnan,afnan din cikin murya qasa qasa tace
"Layinki fa da akayo swapping,wannan baturen likitan ya addabeni fa da kira,zan sunna masa rashin mutunci wallahi,baisan yanzun kinfi gaban wasa ba?" Ta fada cikin hade gira,murmushi bilkisun ta saki
"Karki masa rashin mutunci don Allah,ni da nakeso kiji dashi" ido afnan ta zuba mata cikin rashin fahimta
"Kamar yaya naji dashi?,gashi nace zan masa rashin m kince a'ah" dariya tadan kamata,saita dan daki cinyarta
"Haba qawata,ki fahimta mana,kiji dashi kawai nace fa" dan janye cinyarta tayi
"Rufan asiri ki daina kirana da qawarki,karki jamin balbalin bala'in mijinki yace na raina mishi mata,barni dai a qanwarki"
"To naji" ta fada tana dariya,sai maganar bilkisun tadan jefata a tunani,kimanin minti ashirin kuma saita saki murmushi tana gyara zamanta.


Saida jirginsu ya tashi sannan su afnan suka baro airphort din,suna saman hanya kowa na yaban bilkisun da yadda ta shiga ransu farat daya,tare da fadar bambance banbance masu yawa tsakaninta da safwa
"Dama tun da can bilkisu bilyamin ta dabance wallahi" cewar afnan,ta fara bata labarin rayuwarsu ta makaranta,da yadda a baya ta tsangwama mata,suka dinga dariya suna mamakin abun
"Yanzu gata sama dake,ta zama yayarki" inji sumaira,murmushi afnan ta saki
"Wallahi kuwa,dama bakasan matsayi da baiwar da Allah ya yiwa mutum ba,shi yasa akace kabar wulaqanta ko yima mutum kallon banza,saboda rayuwa wataran bakasan ya zata kaya ba,saika tsinci kanka a qarqashinsa watan watarana,duk da dani ni dama tun da can qasan raina ina sonta,miskilancinta ke bani haushi a wautata" haka sukaci gaba da tattaunawa har suka kawo gida.


¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶


Babban abinda ya kaisu qasa mai tsarki dama ibada ce,ibadar kuwa sukayi tayi tuquru baji babu gani,babu wanda keda lokacin wani a tsakaninsu,hatta da yaran sun sanyasu sun himmatu wajen addu'o'i,dukkan wanda bilkisu ta sani ba wanda bata saka a ciki ba baya ga kanta 'yan uwanta yaranta dama surukanta da iyayenta,kwanakin qarshe qarshe suna gab da komowa gida saita tsinci zuciyarta ta karkata ga yiwa aurenta addu'a kan Allah yasa ya zama silar farincikinta dana mahaifanta duniyarta da lahirarta,sai ta sanya afnan,cikin zuciyarta tana jin fata da qaunar haduwa da qulluwar soyayya tsakaninta da dr adam,tabbas da tafi kowa farinciki.


Duk da ibada sukaje amma a wata gudan sun sake fresh da kyau saboda kwanciyar hankali,bilkisun ta yita daukar hankalin azeez din amma yana dakewa yana son cika alwashin daya ci.


Daga saudiyya kai tsaye ya dauketa suka wuce dangin mahaifiyarta,abinda bata san ya shirya masa ba sai ranar da zasu tafi,hakan ba qaramin faranta ranta yayi ba sosai,don dama anty zuhriyya nata saka ran zasu,to amma saboda yawa da suka dada dole akwai buqatar qara samun kudi da zasuyi tafiyar dashi.


Sunyi farinciki qwarai na ganinta da mijinta dama yaranta,dama already suna da labarin maida aurenta,sunso zuwa a sannan,amma ciwon da mahaifiyar mahaifin nata tayi a sannan yasa basu samu zuwa ba,saboda ta galabaita kamar bazatayi rai ba.


Sun shiga dangi sosai kamar wancan karon,su zaga gidan 'yan uwa qwarai,sai daidaiku da sukayi nisa sosai,kuma duk inda ta sanya qafa tofa tare da azeez ne,hakan ya sanya kafin su taho dangin maman nata da yawa suka sanshi,sati daya suka musu suka musu sallama suka barsu cike da kewarsu,suma sukayi alqawarin zuwa musu nigeria duk sanda wani abu ya sake tasowa.


Ga wani mamakin nata daga can sai gasu a mali dangin fulani aisha,acan taga tarbar girma kamar yadda ta samu daga dangin mahaifiyarta,taga yadda mulki ke aiki,ta tabbatar da cewa sarauta da mulki ba qarya bane,lallai duk wata dagawa ko nuna isa da fulani ko ahalinta zasuyi basuyi qarya,bakuma suyi a banza ba,gada sukayi,ba takawa da hayewa ba,anan ta sake ganin zallar gata da azeez keda shi,kowa nan nan yake dashi da iyalinsa,wani lokaci idan ana lelensu kallo kawai take binsa dashi,saita ringa ji cikin zuciyarta anya batayi xari ba?,anya baifi qarfinta ba?,anya bai girmi ajinta ba?,daga baya da kansa ya karanceta,ranar tana masa wannan kallon ya kama hancinta mai tsaho da tudu yadan ja
"Karki shanyemin kyauna mana gaba kuma kice na miki tsufa kona miki muni,wannan kallon ki adanashi haka,yana son karya min qwarin gwiwata da hanani cika alqawarin dana dauka,ki cire duk wani shakku ko tantama dake ranki,abinda azeez ya sani kawai shine,yana miki zazzafar qauna har muddin numfashinsa,ba gama garin qauna da kika sani ba wadda kika saba jinya ba a bakin kowa" saiya girgixa kai yana sakar mata wani murmushi na musamman sannan ya dora
"zai kuma ci gaba da qaunarki har ranar da za'a tasheshi a qiyama,shi naki ne har abada,kamar yadda kike tashi har abada" ya sunkuya yayi kissing goshinta kana ya soma takawa zai fice,don dama ya gama shirinsa ne zaije su gana da kakanshi ya tsaya amsar breakfast daga hannunta,kamar yadda yanzu ya zame masa al'ada,baicin komai daga hannun kowa.indai har bilkisun bada kanta ta bashi ba,yakance yafi shiga cikinsa ya xauna yaddda ya kamata.


Kwanaki goma sukayi cikin dangi me dadi,a kwana goman nan itama taga dangi dangi sun ganta,sun kuma nuna mata qauna da kulawa kamar su riqesu suyita zama dasu karsu tafi,musamman su amatu da suketa daukan hankalinsu,don wani zubin saisu wuni bata gansu ba.


A kwana na sha daya ya tashi da wayar abdurashid
"To baban soyayya,abun nema ya samu,sai kayi haquri hakanan tunda an cimma buri,kaje ka duba babban kamfaninka,kawai matsala,nayi qoqarin gyara komai amma ya gagareni,dole saika shiga da kanka"
"Naji,kar a sake kirana a irin wannan lokacin" ya fada cikin dakiya yana katse wayar,saiyabar abdulrashid da waya galala,daga bisani kuma ha saki dariya,yarima ne,yasan xai aikata fiye da hakan.


Kusan kamfanin shine zuciyar duka kamfanoninsa,samun matsalarsa zai iya jawo durqushewar harkokin kasuwancinsa dama shuhurar sunansa,don haka ya maida hankali wajen samawa su bilkisu visa din shiga qasar.


Randa ya gaya mata sai tace
"Daka barmu mun koma gida,kai sai ka wuce,ka tarad damu a can" wata harara mai kashe jiki ya aikata mata dariya nason qwace masa,yaso ya dago dalilinta na fadar hakan,tanason kasancewa tare da mijinta amma har yanzu nunawa take baya gabanta,batasan idanuwanta da yanayinta na bayyana mishi komai ba,shi kuma ya zuba mata idanu ne kawai yanason yaga gudun ruwanta,to tana ganin kamar ba amfani kenan kasancewarsu tare shi yasa tace ya barsu su tafi shima ya wuce
"Naqi wayon,ai bari kiji.....wannan wata tatsuniya ce asanda nake abdul'azeez dina da bashi ga tsuntsu bashi ga tarko,yanzu kuwa cikakken magidanci nake me iyali,kisa a ranki duk inda na jefa qafata to akwai taki a wajen" idanu ta fidda
"Aikina fa....ka manta da aikina a brazil?" Yana tattare kayayyakin da sukaci abinci ya bata amsa,don idan dai yana nan kusan shike hidimar yaransa,harma ya hada da nata,abun yana matuqar daure mata kai,yakan zama wani na daban idan yana cikin iyalansa,kai bakace basaraken yariman nan bane,kuma fitaccen dan kasuwa na duniya
"A sanda kike qarqashin umminmu kenan ko?" Sai daya gama hade kayan yakai yara da sukayi bacci daki ya dawo sannan ya kuma dubanta
"Kina tunanin kamata matata zatayi aiki?,aikinma qarqashin wani kodadden bature daya taba sonta?,lallai ko da daga ranar sunana mahaukaci" rasa amsar bashi tayi,kawai saita bishi da kallo,ya dawo da baya ya hure mata idanun da iskar bakinsa.


¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶


Isarsu qasar yasa ya sake zama busy sosai,baida cikakken lokacin kansa ma,yana can yana gyara abubuwa da maidasu kan saitin tsahon lokacin daya kwashe baya cikin kamfanin baya kuma ziyartarsa.


Hatta da yara sunyi bala'in missing dinsa,sun riga da sun saba dashi,kusan kome shike musu,amma yanzu saidai maminsu tayi musu,wuni suke suna tambayarta shi,saidai ta kira musu shi a waya ta hadasu.


Lamarin bilkisun nata bashi dariya da kuma qayatar dashi,ita kanta batasan tana nuna mishi fushi da daukewa lamuranshi kai ba,emotio n ne naso da qauna tun daga zuciyarta amma batasan yana tasowa yana tambara kanshi ba,gamida bayyana muraran cikin ayyukanta ba,ita duk a nata zaton tana jan ajinta ne da nuna ko a jikinta.


Ranar da al'amura suka soma daidaita yayi qoqarin dawowa da wuri saboda yaran,ya cimmata a kitchen tana qarasa hada abincin dare,da yake tunda suka sauka tace tafi ganewa ta dinga musu girki,don haka ya musu siyayyar komai na iya adadin kwanakin da yake saka ran zasuyi cikin qasar.


Tunda ta amsa sallamarsa saita ci gaba da hidimarta,ya saki murmushi yana aje briefcase din daya shigo da ita,ya taka a hankali zuwa bayanta,ya kama qugunta da hannayensa suka biyun ya mannata da jikinsa.


Kusan tare suka saki ajiyar zuciya,saidai ita bata shiryawa hakan ba,hakan yasa ta sake hade rai
"Yarafa,kada su shigo" saiya dan rabata da jikinsa,ya sanya kanshi a bayanta ya kwantar sosai
"Bugun zuciyarki ya saba da yadda asali,hakan shike qaryata duk wani lafuzzan bakinki da kike furtawa,kina qaryata kanki da kanki ne kawai,koda baki fada ba na sani kema kinji dadin dawowata,right?" Zame jikinta tayi
"Kayine dama saboda yaranka,nasan kuma zasu fini jin dadin hakan,sannu da zuwa" ta fada a gajarce,saiya saketa yana sakin dariyar daya kasa danneta,shi kansa zuwa yanzun yakai bango,ya gaji yana buqatar akai qarshe,hakan ya sanya ya tsara nan da kwanaki hudu zaiyi qoqarin kammala komai su wuce qasarsu su samu isashen hutun da zai bude mata sabbin shafukan darussan madarar soyayya masu wahalar mantawa a duniyar ma'aurata
"Shikenan,bari na tafi inda ake maraba dani" ya fadi yana daukan jakarsa,kamar tace masa ya dawo yaci gaba da tsaiwa da ita amma saita kasa,tana daga kitcen din tana jiyo dararsu da yarab,saita saki murmushi data tuna wata interview da akayi dashi dazu data kalla a tv,kamar bashi ba yanzun,acan zallar kwarjini tsare gida da aji kawai take kallo daga hamshaqin matashin dan kasuwar,amma a yanzu ya koma magidanci mai samawa iyalinsa farinciki da walwala,kamar ba shine na cikin tv din ba,totally dabi'unsa suna burgeta dari bisa dari,wanda ita kanta batasan sa'adda daya shiga rayuwarta har haka ba.
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 79

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070





Tunda suka sauka a nigeria ita kanta tasan ranar ta musamman ce,wani sabon salon kulawa take samu daga gareshi,tsokana yake mata da gayya,kome zai mata zai mata shine in a romantic way,ta yadda zan taba har can cikin zuciyarta.


Kai tsaye masarautar kaisa suka fara sauka,suka kuma yada zango a sassan fulani aisha,wanda ta shirya musu walima,duk da gidan a dan cike yake sakamakon hidimar bukukuwan sallah da akeyi,akwai baqi a gidan da masu zuwa xiyara su fita.


Har bayan magariba tana tare da fulani,wadda a yanzun take daukar bilkisu kamar afnan babu wani banbanci,harma tafi gatanta bilkisun akanta,hakan ya qara sanyawa bilkisu ta saki jiki sosai,kuma take mata kallon uwa.


A wunin ranar ta shiga sassan fulani saratu don ta duba jikinta,har yanzu dai tana nan jiya iyau,ba wani abu daya sauya,komai sai an mata,hatta bayan gida da fitsari a wajen take sai an gyara.


Abun ya baiwa bilkisu tausayi sosai,me rai ba'a bakin komai yake ba,yanzu kake mutum yanzu kake ba mutum ba,gadai dukiya sarauta da asali duka tana da,amma basu isa su bata lafiya ba,kuma basu hana qaddararta fada mata ba,sai taji tsoron Allah ya sake kamata.


Baki afnan ta tabe sanda bilkisu ke mata zancan
"Dukkansu abinda suka shuka shi suke girba,itama ashe akwai nata boyayyen abun data aikata sai daga baya nauyin haqqi yasa take fallasa kanta itama,kamar yadda su mama adama sukayi,kinsan idan zunubi da haqqi ya yiwa mutum yawa Allah kuma yaso kamashi da kansa yake tonawa kansa a siri,yanzun haka ita mama adama bamusan ina tayi ba,tuni me martaba ya qara mata wuta da takaddar saki,wanda mu a masarautar nan indai kina matsayin matar sarki kuma akaga ya sakeki lallai kin aikata wani babban zunubi,koda ba'a san meye ba to zai zame miki abun kunya ne sakin daya miki,ba kuma lallai kowa ya aureki ba,baresu da dukka baqin dake cikin gidan nan a gabansu suka fita suna maida magana ita da anti fauxiyya suna ci gaba da tonawa kansu asiri,ita anty fauxiyya an nesantata da masarauta na shekara goma,kamal nacan yana jinya tun daga randa abun ya faru daga qarshe aka gano yana da cutar HIV ne,yanzu meye amfanin irin wannan rayuwar?,shi yasa koda yaushe akeson ka shuka alheri,don ba zaka taba shuka ƙaya ba sannan kace inibi kakeson cira,sam" sosai labarin ya sake kada bilkisu,ya kuma sake zame mata darasi,kusan duk wanda tasan ya aikata zalunci ko wani sharri sai taga qarshensa sakamakonsa baiyin kyau
"Allah kasa mufi qarfin zuciyarmu,kada ka bamu ikon zaluntar kowa dai dai da qwayar zarra" ta samu kanta da furtawa a sarari,afnan ta amsa da amin
"Amin"


Ba'a wani jima da idar da sallar magriba ba yashigo sassan fulanin,tunda suka dawo yau din yana tare da me martaba a fada,da yammaci kuma suka rabu abdulrashid ya janyeshi,sai yanzu ya samu ya yakice,don ya shiryawa ranar yau din sosai.


Daf da ita ya zauna har cinyoyinsu na gogar juna,ko kunyar afnan baiji ba
"Ina ammi" tana dan kauda kai tace
"Tana wajen me martaba" saiya maida dubanshi ga bilkisu cikin wani kallo me kashe jiki
"Tashi kawai mu wuce.....na gaji princess,ina buqatar na huta hakanan" kafada ta maqale kamar qaramar yarinya
"Bamuyi sallama fa da ita ba,sannan su amatu suna tare da ita,kaga dole saimun jira sun shigo"
"Nooo....ba wannan lokacin" ya fada yana miqewa yana zura mata wayarta a handbag dinta dake aje gefanta,da sauran kayan da yasan nata ne.


Dole badon taso ba ta miqe ta gyara yafen mayafinta tana duban afnan
"Muje ki bani ajiyata" batace komai ba ta miqe,saita waiwaya ta dubi azeez dake tsaye yana qare mata kallo
"Zan karbo saqo"
"Minti daya.....karki wuce haka" ya fada yana nuna mata da yatsa.


"Ungo,gwara ma ku tafi,anaso ana kaiwa kasuwa" afnan ta fada tana miqa mata leda mai kauri wadda fulani ta bata daxu,bata buda ba saboda haka batasan meye a ciki ba,fusga tayi tana jifan afnan din da hararar wasa
"Dama waye yace miki ba'aso din bare akai kasuwa,yafi qarfin a kaishi kasuwa,ko a gidama sai mai rabo" baki afnan ta rufe dariya na kamata cikin jin dadi
"Allah y bada haquri,ashe haka yayan nawa yake da bala'in tsada?" Tana murmushi dayafi kama da 'yar dariya dariya ta soma takawa zata fice sannan ta bata amsa
"Qwarai kuwa,idan baki sani ba gwara ma yau ki sani" dadi ya cika afnan din sosai na yadda ko yaushe soyayyar yayan nata da qawarta ke sake bayyana muraran a idanun kowa.


Su biyu ne rak cikin motar,bai yarda kowa ya bisu ba,domin yana buqatar kadaicewa sosai,tare da nuna mata ainihin abinda ke ranshi,duk da zuwa yanzu shi kanshi yayi amanna cewa bata tantamar komai a kanshi.


Hannunshi cikin nata sanda yake tuqin,yana dan murzawa a hankali,wanda hakan ya kuma kashe mata jiki,sai tayi laqwas cikin sit din motar,sanyin ac yana ratsata,ga wani feeling na daban kan mijin nata.


Juyawa yayi kadan ya dubeta akayi sa'a suka hada idanu,saiya saki murmushi yana maida kanshi ga titi,cikin tattausan muryarsa can qasa kamar wanda ya fara bacci yace
"Ina fata zaki marabceni zuwa sabuwar duniya,zaki jarabtu da soyayyata kamar yadda na dauki tsahon shekaru ina cikin jarabawar taki soyayyar" murmushi tayi tana sunne kanta,saiya dan tsuke fuska
"Princess....wannan kunyar...Allah ya gani zata cuceni,bana sonta wallahi indai a yanayin da muke daga ni sai kene,a rayuwar aurena gaba daya da matata ban rubutata cikin lissafi ba,pls ki barni naci duniyata da tsinke" dariya maganar tashi ta bata,saita rufe bakinta da dayan tafin hannun nata,tana ci gaba da sauraren maganganunsa,wanda babu komai ciki face zallar mayen giyar qaunarta,inda ita kuma suke qara ruguxa duk wani qwarin gwiwa nata,suna sake cusa mata soyayyarsa mai tsananin qarfi.


Da ido ta dinga bin gidan sanda duka isa,village ya kaita,tun daga harabar gidan yanayinsa ya dinga saukar mata da wata nutsuwa ta musamman,komai anyi qoqarin yinsa ne bisa tsarin qauye da gargajiya,har wani qamshin qasa ke tashi na musamman,duk da dama damina ta soma sauka yadda ya kamata,hakan ya baiwa duk wani tsiro dake gidan damar fidda ainihin kalarsa,duk da dama ko da can kafin daminar haka zaka samu tsirran gidan,sakamakon samun ciakkiyar kulawa da sukeyi daga masu kula da gidan.


Rungumota yayi zuwa jikinsa,a hankali ya rada mata
"Inason irin wannan nature din,shi yasa nakeson gidan nan,idan ina cikin nishadi indai ina qasar kaisa,nakan zabeshi a matsayin wajen dazan huta" kaita gyada a hankali,itama zabinsu yaxo daya,don lokaci guda gidan ya mata sosai.


Tunda suka shigi ciki shike jan ragamarta,shike mata komai nata idanu,wanka suka fara yi suka hada da alwala sannan ya jasu jam'i suka gabatar da sallah,doguwar addu'a yayi musu,wadda ta sake ninka mamakinta akanshi,yanayin yadda yake addu'ar kawai ya isa ya shaida maka ya samu ilimin addini dai dai gwagwardo,suka kammala suka shafa,sannan ya waiwayo inda take zaune saman abun sallarta,fuskarsa dauke da fara'a ya matsa gabanta kadan
"Duk da wancan lokacin bamu samu damar yin salla da addu'a ba,har yanxu muna da dama aiko princess?" Murmushi kawai tayi tana tuna darenta a wancan rana,wani irin bahagon dare da bata taba jin koda labarin dare irin nata ba,saiya sanya hannunsa ga goshinta,ya karanto addu'ar da annabi yayi umarni akan kowanne ango ya yiwa amaryarsa.


Yunwa takeji sosai don bataci wani abun kirki ba,don haka ta langabe waje daya,kamar ya sani ya dubeta
"Muje mu samu wani abu muci ko?,dare na dada yi" ba musu ta miqe tabishi a

Please Login or Register in order to submit comment