Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yadda suke ta janta a jiki da nuna mata kulawa yasanya dole tadan sake a cikinsu,don ma yarima ya hanata sakat da mayun idanuwan shin nan,duk.inda ta motsa yana biye da ita,batasan me yakeso ba hakanan,amma ita kanta zuwa yanzu tasan cewa mahaukaciyar qaunarshi ta mata mugun kamu,kamun da take zaton ba yau jiya ko shekaran jiya ya kamata ba,ta rasa yaushe ne?,a ina?,kuma a wanne lokaci?.


Sun dade sosai a wajen,don basu tashi ba sai sha daya saura,qiri qiri suka riqe twince suka ce wajensu zasu kwana,hakanan tana ji tana gani tana kuma jin nauyi tabi azeez din suka wuce sashensa,zuciyarta cike da fargabar wanne dare zata fuskanta a yau din?.


Tun daga farkon sassan ya baiwa duk barori dake hidimawa sashen hutu sannan suka wuce zuwa ciki,suna isa falon ya harde hannayensa yana dubanta da narkakkun idanunsa
"Zabi bedroom din da kikeso,wanda zaki kwanta ki huta sosai" maganar da yayi tadan kwantar mata da hankali,tadan dauke kai kamar ba zata nuna ba,murmushi ya saka,ya nufi wani wanda ke daura da nashi dakin
"Na zaba miki nan"
"Na gode" ta furta qasa qasa,ita gaba daya yadda yake kallonta yana sanyata cikin wani yanayi ne mai nauyi,gami da kunya,gabanshi gadi yake komai,dazun har gulmarsa uswa da afnan sukayi,saidaya jefesu da harara sannan suka guntse bakunansu.


Tana jiyo qarar wayarshi sanda take shiga dakin,duk da batasa dawa yake magana ba,amma taji takun fitarsa daga falon gaba daya,hakan ya bata sukunin sauya kayanta zuwa na bacci masu kauri yalwatattu,bata da sauran abunyi,saboda haka ta nade tsakiyar gado,ta jawo wuyarta daya mata kyautarta dazu me azabar kyau da tsada ta soma dudduba cikinta.


Cike da mamakin ha durfafi sashen fulani adama,yayi mamaki qwarai da yau ta daga waya ta kirashi da kanta wai tana son ganinsa,baya ga haka wai a daren,a daren ma qarfe shadaya da wani abu na dare?,abunda bazai iya tunawa sau nawa ya faru ba a rayuwarsa,hakanan ya danne mamakin har ya isa ainihin sassan nasa,ya kuma samu baiwa daya tana jiransa,tayi masa jagora har ainihin falon da fulani adama ke zaune tana jiransa.


Da mamakinsa da murmushi ta tarbeshi,harda miqewa tsaye tana fadin
"Maraba da yariman kaisa....sannu da zuwa" saiyadan dubeta kadan cikin mamaki sanda take nuna masa wajen zama
"Zauna mana,bari a kawo maka abunci da abunsha,na tabbata da qyar idan ka samu saka wani abu a cikinka saboda hidimar jama'a" kai ya girgiza yana soke hannayensa a aljihun wandonsa
"Bana buqatar komai,naci abincin dare tare da ammi na" cikin yaqe da boye takaici tace
"Ai amminka badai qoqari ba,duk damu an waremu ba'a gayyacemu ba" cikin zaquwa dason jin dalilin kiran yace
"Uhmmm" kawai,don dukka wadan nan maganganun nata baiga ma'anarsu ko muhallinsu ba face salo na batawa kai lokaci
"Ka zauna mana yarona,idan kaqi cin abinci ai bazaka qi shan komai ba" kafin yace komai ta kira daya daga cikin hadimanta,ta bata umarni ta kawo tatattaccen ruwan inibi kamar yadda tasan cewa azeez din yafi sonshi.


"Allah yasa lafiya dai ko?" Ya fada yana kafeta da idanu,saboda kame kame da yaga tanata yi
"Eh lafiya....amma saurin me kake ne,ka bari a kawo maka lemon mana"
"A qoshe nake,kiranki ne kawai ya fiddo ni"
"To...to ai shikenan.....dama akan abubuwan da suka faru ne wunin yau,yanzu ace shekaru har takwas abdul'azeez kana da mata harda yara biyu amma babu wanda ya sani a cikinmu?,aiko babu komai dai mudin kamar iyayenka muke,idam yau babu ranta mu xaka ci gaba da kallo a matsayin iyaye ko?,sam banji dadi ba,saiya zamana kenan bamu da maraba da sauran jama'ar waje dama talakawan gari ko?" Dan qaramin murmushi ya sake na gefan baki yana yada kanshi gefe kadan,sam baiga muhallin maganar ba,a yadda ma take magana kamar bata shirya yin maganar ba kawai yin kanta maganar take,ya jima da gama karantar halayyar matar tsaf,tun yana ganin kamar amminsa na daukan tsattsauran matakin nesantasu harya fahimci gaskiyar mahaifiyarsa,ya sani,makira ce ta gaske,maida dubansa gareta yayi
"Kinsan komai sai Allah ya nufa,to sai yanzu ya nufa ku sani"
"Eh hakane,amma duk da haka maganar gaskiya bamuji dadi ba,don innarka fauziyya ma don tabar nan wajen ne,amma fada ta dinga yi kamar zata ari baki,da qyar na tausheta" haka ta dinga soko maganganu marasa kan gado da sam bashi da alaqa dasu.


Bilkisu kuwa na tsaka da saita wayarta taji an turo qofar,da mamakinta tasa kai don taga waye,tasan cewa kamar ya mata sallama a fakaice ne sanda take shigowa dakin,to meye ya dawo dashi.


Saidai wanda ta gani din abun ya mugun kadata da razanata,wata fuska da batasan ga wacece ba tsaye gabanta tana qare mata kallo.


A hankali ta aje wayar gefe itama idanuwanta qur a kanshi tana son inda ta sanshi
"Malam lafiya?,waye kai,ta yaya zaka shigo dakin matar aure haka kai tsaye ba tare da neman izini ba?" Ba amsa illa ci gaba da qarewa surarta kallo da yake,wanda kallon ya bata tsoro sosai,saita soma sauka ta daya barin don ta dauko.mayafi ko hijabi ta qara suturta jikinta,Allah ya taimaketa ma kayan ba masu fidda tsiraici bane.


Tafiyarsa taji a bayanta sanda take sanya hijabin,tayi hanzarin juyawa tana daidaita shi a jikinta
"Ka fitar min a daki,baka da hankali ne?,ko kai mahaukaci ne?" Ta fada cikin qaraji da tsawa.


Wani shu'umin murmushi ya saki
"Dukka ina jinki,kuma ni ba tashin hankali ya kawoni ba,wala'alla ke bazaki gane ni ba,amma ni bazan taba iya mantaki ba,tun shekaru takwas dana taba ganinki zuwa watannin baya zuwa yau,na dade ina kishi da baqinciki da yarima,duk abinda nake buri a rayuwata sai naga shi ya samu ni kuma ban samu ba ciki kuwa harda ke,nayi burin aurenki,nayi burin samunki amma sai gashi lokaci daya yarima ya sameki,duk neman da nake shekara da shekaru ya tashi a banza,saboda haka nazo cikin salama ki bani na dandana yadda shima ya dandana,ko hakan zai ragemin zugin asarar rasaki da nayi,ki bani hadin kai,don har mu gama bazai dawo ba,idan kuma kinqi zan amsa ta qarfin tuwo,don naci alwashin bazan barshi wannan karon ya tsira dake ke daya ba".


Batasan lokacin data daga hannu ta zabga mishi mari ba,tunda take a duniya bata taba jin tashin hankali irin wannan ba,tuni bacin rai zallah ya bayyana saman fuskarta
"Wanne irin jakin mutum ne kai?,wawa wanda baisan darajar aure ba,ko karuwa idan kana da kunya bai kamata ka gaya mata wannan maganar kai tsaye ba,bare matar aure mai mutunci,kayi gaggawar barin sassasan nan gaba daya,tun kafin na tara maka jama'a!" Murmushi ya saki yana shafa wajen yana sake matsowa inda take tsaye
"Naga alamar dai ba zaki bani hadin kai ba,saidai na yimiki fyade na karba ta qarfi" yana gama fadar haka ya danqi.hijabinta cikin zafin nama yana neman rabata dashi,kafin kace meye wannan kokawa ta kaure tsakaninsu,bilhaqqi ya sakar mata dukka qarfinsa da mazantakarsa kan sai ya keta haddinta,yayin da take dukka qoqarinta wajen ganin ta kare kanta ta tsira da mutuncinta.
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 78

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070




Miqewa yayi daga dosana dawawunshi da yayi saman hannun kujerar daya zauna akai tun dazun yana duba agogonshi,yaga alamar surutun nata bamai qarewa bane,kimanin minti arba'in da zuwanshi kenan amma babu wani abu me muhimmanci data gaya masa,sai soki burutsu da kwashe kwashen zance
"Allah ya bamu alkhairi" ya fada yana durfafar qofa,tanason ta sake tsaidashi ta bata mishi lokaci amma kuma ya mata kwarjini da yawa yadda ya hade fuska,hakanan tana kallonshi har ya fice
"Ja'iri,wannan baqin ran naka yau za'ayi maganinsa,gwara a soma tarwatsaka,muga qaryar fadin rai da izza,dan banza shi da uwarsa".


Haka kawai ya dinga ji gabanshi na wani irin faduwa,irin faduwar gaban da bai taba jin irinta ba,ya lumshe idanunsa kana ya bude a hankali kuma a fili ya furta
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,wala udwana illa alazzalimin" saiya danji faduwar gaban ya ragu,yaci gaba da tafiya a hankali yana dosar sassan nashi,yana kallon yadda sawu ya soma daukewa a gidan,kamar ba shine yayi cikar kwari dazu ba,da alama kowa ya nufi makwancinsa.


Sosai ya galabaitar da ita ya kuma qarar mata da sauran kuxarinta,hijabin jikinta ya tsarge,cikin tashin hankali tasa hannunta ta cukuikuye hijabin sosai ta hanashi sauka daga jikinta,cikin qarfin hali tasa qafafunta ta harbi cikinsa,yayi baya yana dafe da cikin saboda yadda ya qulle masa,hakan ya bata damar yunqurawa ta durfafi falo,shima ya miqe ya rufa mata baya.


Qafa ya sanya mata ya tadeta a tsakiyar falon,ta tafi luuu tayi qasa,wanda kafin takai qasa ta sanya hannunta,hakan yasa ta fadi akan hannun,wani irin zafi ya ratsa qwaqwalwarta,wanda batasan sanda ta saki wani gigitaccen ihu ba.


Kamar a mafarki yaji sautin murya kamar ta bilkisun tana fitowa daga sassansa,cak ya tsaya yana son tantance abinda yaji,sai kuma ya qara sauri zuwa ciki saboda wani bugu da zuciyarsa ta fara yi harya wuce na dazu.


A gaggauce yake ratsa falukan har zuwa sanda ya isa falon da bilkisun suke,daidai sanda yake tura qofar daidai lokacin daya sanya hannu ya fincike hijabin jikinta da taketa faman riqe dashi yana fadin
"Baki isa ki tseremin ba,har sai na cika burina a kanki,bazan zuba idanu yayita yin nasara a kaina ba tsahon......." Maganar da bai samu damar qarasata ba kenan yaji saukar wani irin naushi a bakinsa,tsananin zafi yasa ya kasa tantance daga inda dukan yake,sai wasu taurari da suka soma kewaye kwanyarsa zuwa cikin idanunsa,kafin ya koma hayyacinsa yaji wata kyakkyawar shaqa data kusa wucewa da duka sauran numfashinsa da yayi saura,sai a sannan idanunsa suka sauka kan azeez,wanda launin fuskarsa zuwa idanunsa gaba daya suka sauya tamkar an watsa musu ruwan barkono
"Me...mmee......" Yaketa qoqarin yin magana,saidai azeez din ya riqe dukkan wata kafar numfashinsa,har sai da numfashin ya kusa katsewa sannan yayi jifa dashi waje guda
"Me kakeyi cikin dakin iyalina?,me kake shirin aikatawa kamal?" Ya fada a zafafe yana durfafarsa,cikin qarfin hali kamal din ya miqe yana son nuna nashi qarfin halin
"Me kake haka?,karka kuskura ku sake dukana malam na gaya maka" ya fada yana nunashi da yatsanshi,zallar haushinsa da yakeji shekara da shekaru a yanzu suna taso masa,tsana da qiyayyar yariman.


Bai kuma ankara ba ya wankeshi da wasu zafafan marin kuncin hagu da dama,sannan ya sake kaiwa fuskarsa naushi,wanda hakan ya baiwa haqoransa na gaba guda biyu da tun naushin farko suka soma girgidi damar xubowa qasa.


Duka tako ina yake kaiwa kamal din,wanda tun yana yunqurin yaga ya rama harya fuskanci zarrarsu ba daya bace ya soma qoqarin qwatar kansa ta hanyar bude qofofi yana neman hanyar da zai kubuta,yayin da azeez ke biye dashi bai fasa ka masa duka ba duk inda ya samu a jikinsa cikin tsananin fushi kishi da fitar hayyaci.


A haka har suka fito zuwa babbar farfajiya,daidaikun masu giftawa wadanda basu kai ga zuwa makwancinsu ba suka soma labewa cikin mamaki,suna kallon yadda azeex din ke jibgar kamal cikin hasken fitilun gidan.


Hannu daya yasa ya damqi wuyan rigar kamal din ya tayar dashi tsaye,kana ya soma janshi zuwa sassan da mahaifiyarsa hajja fauziyya ke sauka.


"Kiramin masu horon gidan qasa su sameni a wancan sashen yanzu yanzu" ya fadawa wani bawa da sukayi arangama dashi a hanya ba tare daya dubi sassan da bawan yake ba,wanda cikin hanxari da zallar biyayya ya wuce don isar da saqon yariman nasu.


Daidai lokacin da hajja fauziyyan ke zaune a katafaren falon dake sashen,sam hankalinta ba'a kwance yake ba tunda fulani adama ta gaya mata abinda kamal din ya tafi aiwatarwa,sam shirin da tsarin baiyi mata ba,har sukaso sudan haura da fulani adaman,saboda tana ganin don ba danta bane shi yasa ta aikashi aikata wannan alfashar,abinda kawai yadan kwantar mata da hankali idan ta tuna cewa idan suka cimma muradinsu to wannan zai bude musu wata qofa da zasu iya cimma muradinsu,amma matuqar komai ya daidaita xata cire adama me daga tafiyar,daga ita sai yaronta xasu amfana.


Bugun qofar da wani irin qarfi,da kuma faduwar wani abu kamar kayan wanki a gabanta shiya dawo da ita daga tunanin data lula,azeez ta gani tsaye a gabanta yana fidda huci da wata irin kama da bata taba ganinsa da ita ba,ta duba gabanta da kyau,sai taga kamal yashe cikin jini dake fita daga hanci da bakinsa.


A razane ta dora hannu aka ta kurma ihu,koda ba'a gaya mata ba tasan cewa lamari ya lalace kenan,idanunta a warwaje a matuqar tsorace tace
"Na shiga uku ni fauziyya,me zan gani haka?,abdul'azeez dan uwan naka zaka kashe?,jama'a kuzo ku tayani gani,yariman kaisa zaiyi kisa" ta soma kwaroroto wanda ya janyo hankulan jama'a,na nesa dama wadanda ke tsaitsaye saman hanya suna jimantawa gami da tattauna abinda suka gani din yanzu.


Tuni qofar sassan ya soma cika da 'yan ganin qwaf
"Na kawo miki shine ya gaya miki meyaje aikatawa kafin a wuce dashi" azeez ya fada cikin fushi yana fidda idanunsa
"Meya maka haka abdul'azeez?,ashe shaye shayen naka da ake fada dai da gaskene?,to wallahi bazan yarda ba,abinda kayi masa saika karbi sakamakonka" ta fada tana matsar qwallar qarya.


Dai dai lokacin da masu gadin gidan qasa suka qaraso(masu kula da sashen manyan laifuka na prison din masarauta)
"Ku kamashi kuje ku kullemin shi" ya basu umarni yana mai juyawa don barin falon,yana jin yadda hajja fauziyya ke maganganu tana kurin ba wanda ya isa ya fita dashi,saidai sahun giwa ya take na raqumi,haka suka qwamusheshi suka ingizashi inda yariman ya buqata.


Zabura tayi daga inda take takure tana kuka sanda ya tura qofar ya shigo,tana ganin shine saita maida kanta taci gaba da kukanta,ya isa inda take ya dagata gaba daya ya sanyata a qirjinsa ya rungumeta tsam yana sakin wata nannauyar ajiyar zuciya,yana jin wani irin ciwo da qunci idan ya tuna yadda yaxo ya tadda kamal na shirin cin zarafin bilkisun,banda doka da shari'a tabbas sanda ya riqe wuyan kamal bazai sakeshi ba har sai numfashinsa ya wuce,yana jin wani irin zafi tun daga zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,kamar ana masa feshin wuta,huci kawai yake fiddawa yana sauraren sautin kukanta da yakejin kamar ana yanka mishi zuciya ne.


Tsahon lokaci suna a haka,sannan ya janyeta zuwa ciki,bandaki ya wuce da ita,ya zaunar da ita a toilet sit ya hada ruwan mai dumi sosai sannan ya iso inda take,idanunshi cikin nata yana nata qwarin gwiwa ya soma cire mata rigar baccin jikinta,sai daya rabata da komai sannan ya sanyata cikin ruwan zafin,ya tabbatar jikinta ya gasu yadda ya kamata sannan ya sake mata wanka banda wanda tayi daxu sannan ya maidota cikin dakin.


Wasu kayan ya sauya mata marasa nauyi masu taushi sannan ya suka koma saman gadon ya sake sanyta cikin jikinsa,kanta na saman qirjinsa,har yanzun kuka take,hakanan shima ya gaza furta mata komai bare ya hanata,don wata gobara ce take tashi daga zuciyarsa,yana wassafa hukuncin daya dace da kamal ne kawai,tsattsauran hukuncin da baiga abinda zaisa ya sassauta mishi ba,tunda yayi gigin shiga gonar data masa nisa,ta masa zarra,kwatankwacin nisan da tazarar dake tsakanin sama da qasa.


Sai can tsakiyar dare ya jita shuru bayan kukan ya dauke gaba daya,ya daga fuskarta daya tasa saboda kuka,yayi kissing kyakkyawan lebanta zuwa goshi,sannan ya gyara mata kwanciya a jikinsa yana jin wani qaunarta da kishinta na sake ratsashi,ya sake matseta gam cikin jikinsa kamar wani zai qwace masa ita.


Kwanan zaune yayi,saida aka kira sallar asuba sannan yayi yunqurin zuwa bada farali,zuwa lokacin ita dinma ta farka,sai data fara shiga tayi alwalar sannan shima yayi,shiya jagorancesu sukayi jam'in sallar tare suka idar,tsahon wasu mintuna bayan idarwar tasu sannan ya waiwayo yana fuskantarta,hannuwansa ya miqa mata,batayi jinkiri ba ta isa jikinsa,habarshi saman kanta ya soma lallashinta cikin taushi har zuwa sanda ta sauke ajiyar zuciya tana jin nutsuwa na shigarta,don jiya har barawon baccinya saceta bakinta na dauke da addu'a zuwa wayewar garin yau.


Wayarshi dake daura dasu ta dauki ruri,daga inda yake zaune ya miqa hannunsa ya jawota,sam yama mance da ita tun jiya,daya duba sai yaga me martaba ke kiransa.


Cikin girmamawa ya daga ya soma gaidashi,ba tare daya amsa ba yace
"Duk abinda kake ka barshi kaida iyalinka kazo ka sameni yanzun nan a babban falo" bai jira amsarsa ba ya katse kiran,saiya aje wayar kawai,ya miqe zuwa ma'ajiyar kaya dake dakin ya budeta,ya fiddo yalwatacciyar jallabiyya da wadataccen hijabi ya miqawa bilkisu
"Ki saka,zamuje wajen me martaba" alamun tsoro ya gani qarara saman fuskarta,saiya durqusa gabanta,ya kama hannayenta ya saka cikin nashi ya matse,idanunsa cikin nata
"Baki da buqatar ki tsorata ko ki raxana,zaki gaban managarcin mutum ne mai adalci,indai kuma ina tare dake babu wata halitta data isa taci zarafinki kota tozartaki matuqar ina numfashi a doron qasa" wannan ya bata qwarin gwiwa,saita miqe ta soma shiryawa,shima ya sauya kayan jikinsa sannan suka fito.


Yayi mamakin ganin mutanen dake hallare a wajen kamar ba safiya ba,kamal da mahaifiyarsa wanda yake zaune jikinta,da alamu sai daya ziyarci asibiti,cikin daren ne ko kuwa bayan sallar asuba ne bai san mishi ba,fulani adama,amminsa da babbar diyar me martaba yarinyar fulani saratu.


Cikin girmamawa ta gaida kowa sannan ta samu waje ta zauna,bayan shudewar wasu mintuna me martaba ya fara magana
"Me dan uwanka kamal ya aikata maka har haka cikin dare kahau dukansa kamar wanda Allah ya aiko,ka masa jina jina irin haka?".


Wani abu me tauri da daci ya hadiye,baison ma ya maida maganar,amma dole ya fadeta,bai boye komai ba ya zayyanewa mai martaba,yana kaiwa aya fulani adama dake zaune gefe,wanda tun jiya da lamari ya baci take cikin taraddadi da tunanin yadda zata fidda kanta,tayi gudawa tafi sau a qirga,saboda ta tabbatar indai wannan abu ya fito da sunanta to Allah ne kadai masanin hukuncin da zai biyo baya,salati ta saka mai qarfi da salallami
"Kai kuwa kamal meya kaika aikata wannan tabargazar,matar dan uwanka?" Da mamaki hajja fauziyya ta dubeta,tabbas banda yau din tana tsoron tonuwar asirin fulani adama nata tonuwar asirinne da ba shakka saita bankadata.


"Kai kamal...anyi haka?" Me martaba ya tambayeshi,cikin hali na ciwo ya gyada kai
"Eh anyi haka,amma ita ta kirani,ita ta nemeni" kalmar data kusa ruguza zuciyar azeez da bilkisu,wadda batasan sa'adda data daga kanta ba,cikin zare idanuwa take kallon kamal din,tana jin jinin jikinta kamar ya daskare
"Qarya yake!" Fulani aisha ta samu kanta da furtawa cikin fushi,duk yadda taso ta hana kanta magana amma wannan karon ta kasa.


Basu ankara ba har azeez ya isa inda kamal ke jingine jikin babarsa,yasa qafarshi ya take qafar kamal din,ta bada wata qara da yake bada tabbacin babu makawa ya karye,idan bai karye ba to ya samu mummunar gocewar qashi
"Gaya musu gaskiya!" Ya fada cikin qaraji
"Abdul'azeez!!!, agabana?" Me martaba ya fada cikin tsawatarwa,dole ya koma ya zauna ya fidda hucin bacin rai yana jin kamar yasa bindiga ya fasa kan kamal.


Shuru ne ya biyo baya na tsahon lokaci kana ya gyada kai
"Zanyi bincike....zanyi bincike kuma duk wanda na samu shike da laifi bazan daga masa qafa ba dai dai minti daya ba" maimartaba ya fada cikin kaushin murya,saiya waiga ya dubi Aafiya
"Ya ake ciki da likitan saratu" kanta a qas cike da alhini tace
"Sakamakon ganin abinda ya razanata da tayi,yace ta samu mummunan stroke wanda yake da wuyar magani,bugu da qarima wai jini yahaura qwaqwalwarta,akwai yiwuwar lokaci zuwa lokaci a dinga samun wasu dabi'u mabanbanta tare da ita"
"Ya salam" me martaba ya fada yana lumshe idanunsa,ya budesu a hankali yana musu umarnin tashi su tafi.


A yanayin da taga yariman ya shiga wunin ranar sai ta soma tausayinsa fiye kanta,zallar bacin rai qarara,bata tana tunanin haka yake da zafi da kuma fushi ba sai yau,kusan wunin ranar haka suka wuni suka kwana.


Ta fannin su hajja fauziyya kuwa sun cika da farinciki,saboda suna ganin sun samu hanya sassauqa da zata kawo musu qarshen komai,hakanan babu wani abu ko wata hujja da zata kubutar da bilkisu kota wanketa.


A kwana na biyun ana ya gobe kwanakin da me martaba ya diba na zai sake nemansu su cika,wajen goma na dare taga ya tashi zumbur daga inda ya maida wajen kwanansa wato dogiwar kujerar falon dake daura da dakin gadon,ya zura slippers dinsa ya fice,saita bishi da kallo cikin mamaki,don tun daxun take lallamarshi ya tashi yasha koda fresh milk ne,saboda babu abinda yaci wunin ranar,duk da fulani itama tayi iya yinta yaci wani abu.


Ba'a jima ba sai gashi ya shigo da wata laptop riqe a hannunsa,ya zauna bayan yaja qaramin table gabanshi ya dora akai,ya daga hannu ya mata nuni akan tazo,jiki a sanyaye ta iso,sai yaja hannunta ya zaunar da ita gefanshi,gami da dora kanta saman kafadarshi,dukkansu fuskokinsu na kallon laptop din.


Bata gane ne yakeyi ba,illa taga kaman ya rubuta wani kwanan wata ya shigar,sai vedio ya fara motsawa,tsayin mintuna kadan ta fahimci cctv camera record ne,sai kuma ta gane date din ranar da akayi wedding anniversary dinsu,tun daga rana yana wucewa har zuwa sanda duhu ya fara shigowa.


Sannu a hankali saiga gilmawar mutum cikin sanda,yayi zooming hoton saiga kamal quru quru cike da alamu na rashin gaskiya,saiya tafi next camera da zata kaishi daga falo na qarshe zuwa qofar bedroom din,take ta soma nuna masa gilmawar komai ciki harda kai kawon kamal,labewarsa,shigowarsu shiryawarsu da fitarsu dawowarsu da sanda azeez din ya sake fita,fitar data bashi damar afkawa zuwa cikin dakin.


Tsayin mintunan da suka kwashe suna gwagwarmaya a ciki saiga fitowarsu falon again yana yunqurin rabata da hijabin jikinta da qafa daya sanya mata ta zube a qas,fincike hijabin da shigowar azeez din,anan ya tsaida record din,ya sanya tafukan hannayenda duka saman fuskarsa yana shafa fuskar,a hankali ya furta
"Alhmdlh,na godewa Allah daya tunasar dani akwai camera a sassan nan,na godewa Allah zahiri da badini" ita kanta ajiyar zuciya ta sauke me nauyi,wata nutsuwa na ratsa zuciyarta,ita kanta wannan shine abu na biyu daya taba gigita rayuwarta lokaci guda,tana tunanin ta inda gaskiya zata bayyana,kana ta kubuta,amma da yake Allah mabuwayin sarki ne,sai gashi ya kawo musu warwarar komai.


Ranar dukkansu baccinsu ragagge ne,kowanne na tsumayin ketowar alfijir saboda bayyanar da gaskiya.


A yau din zaman ya sauya salo,saboda samun qaruwar amintattun memartaba cikin xaman,gudun kada yaje ya zartar da hukunci kan kuskure,hakan ya sanya dole ya sakosu cikin lamarin.


Dukkansu tsakanin su ukun shi bilkisu ko amminsa ba wanda yace musu ta tafas sanda suka zage suna maida yadda akayi cike da son rai,da kuma son yiwa qarya kwaskwarima su fidda kansu,dukka saida duka gama zancansu damar magana ta dawo bangarensu sannan ya miqe da laptop din,yayiwa me martaba bayani a taqaice sannan ya kunna

Please Login or Register in order to submit comment