Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

illa billah!. Ta sani dama tasan xa'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,tasan cewa matuqar wannan batun yashiga kunnuwan mahaifinta to magana ta riga data qare.


Dukkaninsu sunga hawayen dake zirya a fuskarta,hakan yasanya mama ladi gyara zama gami da dora nata sharhin
"Duk É—a nagari burinsa shine ya farantawa iyayensa yacika burinsu,kuma alhmdlh kedin kin samu shaida a wajen mahaifinki,don kaf Æ´aÆ´ansa babu wanda yake naci da damuwa dayimin zancanshi shida mahaifiyarsa irinki,shi yasa muke da kyakkyawan fata dakuma zaton ba zaki watsa mana qasa a idanunmu ba,don ke kanki basai an gaya miki ba cewa babbar masarauta ce take nemawa babban yaro kuma magaji a wajenta aure,kinga wannan bama lamari bane da za'a ce an tsaya ana jayayya akai ko tantama ba" duk da hawayen dake idanunta hakan bai hanata duban umma ladi ba,ba abun mamaki bane donta fadi hakan,saboda sama taka ta ganta,batasan cinta shanta ba bare sutturarta,ba'a maganar lafiya da ilimi harta kawo wannan minzalin,idan akwai wanda zata zarga shine mahaifinta,da har ya amshi wannan wasan yaran hannu bibbiyu yake da muradin wanzar dashi,ba tare daya tuna cewa diyarsa bace ita jininsa ce,dukiya ta rufe masa ido,koda baisan komai na dawainiyarta ba,baison ciwo da zafinta ba amma ai tsatsonsa ce
"Kayi haquri baba,karka bada aurena ta wannan sigar don Allah,hanyar da duk wani mutumin qwarai yaji zaiyi Allah wadai da ita,idan ka matsu ne na matsa daga gabanka,kana iya neman wanda zai aureni saboda Allah,ya riqeni saboda Allah,yaqaunaceni saboda Allah,yakuma zauna dani saboda Allah,wanda zaiga girma da mutuncinka martaba dakuma qimarka,ka duba maganata don Allah" ta qarashe fada cikin rauni,duk da cewa tafada ne koda wani abu zai iya taba ranshi ya waiwaya yadubi abinda yakamata,tasanshi sarai akwai kafiya da tsaiwa kan maganar da yakega tayi masa kuma itace dai dai,ba kasafai ake sauko dashi daga dokin naƙi ba idan yahau.


Cikin hargagi da kaurara murya yace
"Ke bilkisu!,naji duk abinda kikace da uwardakinki,nasan kuma dama ra'ayinki kenan,to ba yardarki nake nema ba,hakanan ba shawartarki nake ba,na yanke hukunci ne a matsayina na mahaifinki wanda yake da iko dake,ki yarda kokar ki yarda wannan ya rage naki,tashi ki fita ki bani waje".


Wani irin duhu duhu da hajijiya take gani,haka ta dinga laluben hanya,a daddafe takai kanta dakinsu,tazube tana sakin wani marayan kuka,karo na barkatai tasake fadawa cikin halin bege da fatan inama ace anty zuhra tana nan,inama ace anty zuhra zata dawo kafin mai afkuwa ta afku,tasan idan da tana nan zatayi dukkan maiyiwuwa ta hana faruwar lamarin,duk da matsananciyar Æ´ar tsamar dake tsakaninta da mahaifin nata.


Ranar za'a iya cewa ba ita kadai ba,hatta da ƴan ƙannenta babu wanda ya runtsa,ta kasa boye tashin hankalinta sam,kuka tayi mai yawa wanda ya qara yawan zazzabin da tayi tunanin yatafi kenan ashe yana labe,yasamu mafaka kuwa yasake rafketa.


************


Washegari bayan duka qannenta sun wuce makarantar Allo,tana kwance a daki ita daya,tanaji tana gani makarantar data ci burin taje yau hakanan tabi ruwa,don bata da ƙwarin jikin da zata iya niƙar uwar tafiyar data saba.


Mama ladi ce tayi sallama tashigo dakin dauke da kofin silba da faranti mai dauke da kunu da wainar gero
"Sannu maigado,tashi kisanyawa cikinki wani abun kinji,su iyaye haquri ake dasu ana musu biyayya don a wanye qalau" hakanan ta qaraci babatunta ta fice,batako daga kai ta dubeta ba bare ta tanka mata,kamar ta sanya qafa ta shure abincin haka gaji,abun sam babu Allah a ciki,yau da qyar tasamu ta hadawa qannenta abinda sukaci da safe suka wuce makaranta,babu wanda yadamu da basu koda danyar qwayar gero,amma ita din yanzu gashi ana bibiyarta da abincin har shimfidar kwananta.


Umma katti ce ta bankada labulen dakin tashigo,fuskarnan a dinke tsaf kamar hadarin kaka,wanu kallo takewa bikisun sannan tace
"Wai me yake hadaki da waccar matar da naga daga jiya zuwa yau sai wani haba haba takeyi dake?,ko wani sabon munfurcin da tuggun xa'a hada baki dake a qullamin?,to idanma hakane ina mai gargadinki dajan kunneki ahir dinki,kuma shima munafukin uban naku wanda nasan da saninsa ake shirya komai zanje yanzu nasameshi,don ba'a siya sai dana gama dawainiya daku daci daku sannan azo za'amin wannan iyayin ba ehe" daga haka tajuya tafice tana mita.


Batasan ya suka ƙarke ba,amma ga mamakinta da daddare itama saigata da nata abincin tana mata magana cikin lallama,inda ta dangwarar da wancan da wanda mama ladin tasake kawo mata a nan ta dangwarar da natan itama.

********* ***********


Kashingide take saman lallausan carfet din dake madaidaicin falon alfarmar tana amsa wayar sumaira,wadda ke karatu a qasar kano jami'ar bayero,tana hannun yayarta uswa dake aure a masarautar kanon.


Yanayin yadda take amsa wayar kawai ya isa ya nuna maka zallar yadda qaunar 'ya'yan nata,wanda dama hakan aqidartace,halayyarta ce son Æ´aÆ´a
"ƙarshen watan nan muke sanya ran zuwa ma ammi,mu duka harda anty uswa,su irfan zasu samu hutu" cikin jin dadi tace
"Allah ya kawominku lafiya,dama inason ganinku gaba dayanku" daga nan sukayi sallama kana ta maida kanta ga umma luba dake duƙe gefe tana jiranta
"Uhmm,ina saurare" gyara zama tayi tana fidda murmushi
"Ai Allah yabaki yawan rai,Allah ya dafa miki tuni an wuce wajen,don mahaifinta ma yace yabaku,ai babu mai iya ja daku,ya amince yabaku ita" murmushi fulani tasaki,sannan tatashi tazauna sosai
"Dakyau,aikinki yana kyau lubabatu,tun zuwanki nafarko naji dukka hankalina ya karkata kan naki zaben da kikayi,saboda na tabbatar ayadda kika kasa zama kikazo kika shaidamin komai yarinyar ta hau mixanin da nakeso,hakan yayi". Farinciki ya cika zuciyar umma luba,tana ganin kakarta gab take da yanke saqa cikin masarautar kaisa
"Allah yabaki yawan rai,godiya nake,na gode da yabon dana samu daga gareki,yanzun Allah ya taimakeki kina da buqatar ganin yarinyar ne a kawota?" Hannu ta daga mata kana tace
"Bani nake buqatar na ganta ba,inajin yarima shi yafi cancanta ya ganta,idan tayi masa shikenan sauran ayyukan sun gama kammaluwa,abinda kawai yarage sai daurin aure,dakuma biki daga can nasu bangaren,don a nan bangaren namu,bana fatan koda ƙadangaren gidan nan yasan da maganar balle jama'a" cikin girmamawa ta rusunar dakai
"Baki da wata matsala Allah ya taimakeki,yadda kika dama haka kowa zaisha,tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa....in shaidawa yarinyar su shirya tafiya can ƙasar da yarima yake kenan?" Kai ta girgiza
"Eh....su shirya cikin satin nan zan sama muku visa keda ita da mahaifinta da mahaifiyarta"
"Angama ranki yadade,Allah yasa ki gama lafiya,godiya nake,nizan koma don nasamu zarafin isar da saqonki" ta furta cikin zumudi da farinciki,don nata manta qasar ba,bata kuma manta irin dadi da kashe ƙwarƙwatar idanu da sukayi ba,duk da cewa dubiya sukaje amma sukam fes haka suka dinga jinsu,kamar wancan karon wannan karonma sai data wanke umma luba da kudi,ba tare data damu da cewa kwanaki kadan ta bata wasu masu yawa ba.


Zuciyarta fes,ranta fari qal,babu tunanin komai a ranta,saima hasaso yadda komai zai tafi dai dai take,yanxu abinda yarage shine tasoma nema musu visa kamar yadda ta gayawa umma luba,wayarta dake aje gefanta tadauka tasoma neman wata number,saikuma ta tsaya saboda wani É—an gajeran tunani da tayi,tasauya akalar kiran nata zuwa layin azeez,tana kiran tana mita can qasan ranta ita daya,tunda sukayi maganar da ita bai sake tada zancan ba,iyakaci idan yakira suka gaisa sukayi maganar data shafesu shikenan,kamar ma bai damu ba ko nashi da interest akan zancan,itakam babu abinda zai dakatar da ita,tasan gata ne zata masa,don ta yadda yake sharewa kuwa tasani da zarar taga matar a gefanshi zai ware ya manta komai.


Yanzun kam dole tasoma samunshi da maganar,tasan halin miskilancinsa,sai suje yaqi ganinsu harsu dawo suyi zuwan banza,wannan kadanne daga aikinsa.


Dai dai lokacin da azeez din suke zaune a wani wajen kebantaccen wajen shaqatawa,wajene da za'ace yana da tsarki akan sauran guraren shan iska dake mexico city.


Komai nashi farine da ratsin baqi dan kadan,kamar yadda na lura kusan dabi'arsa ce son farin abu,farin wando ne a jikinsa mai azabar kyau wanda ya zarce gwiwarsa amma baikai idon sahu ba,sai shirt me gajeran hannu,v neck wadda tafidda qirar halittarsa,kallo daya zaka yiwa dantsensa kasan yana daga qarfe,qafafunsa rufaffun takalma ne hightop suma farare qal dasu kamar ba'a taba sanyasu ba,sai kanshi dake saye da p_cap fara mai adon baqi a jiki,wadda ya jawota ne sosai tarufe fiye da rabin fuskarsa dake duqe kacokam kan farar laptop dake saman cinyarsa,yana latsata a nutse da hannunsa dake dare da baqin agogo rolex na fata wanda yazauna sosai a hannun nashi.


Saboda shi abokan nashi suka shirya wannan fitar bisa amincewarsa bayan ya tabbatar da tsarkin wajen,amma idan kaga yadda yayi shakulaton bangaro da hirar tasu saika zaci shidin bare ne a cikinsu ba tare suke ba,duk da irin shewa da suke bugawa irin ta zaratan samari da jini ke yawo a jikinsu,hakanan duniya ke gara musu yadda ya kamata.


Suma basu wani damu ba,tunda idan da sabo sun saba da halayyar azeez,ba kasafai zaka sameshi yana hira ba,ba qaramar sa'a ka taka ba duk sanda kuwa ka sameshi yana hirar,ba kowacce irin hira ke burgeshi ba,hakanan ba'a kowanne yanayi yake zama ya bata lokacinsa wajen yin hirar ba,koda yazauna a cikinsu zaka sameshi da waya ko tab a hannu yana wani abun daya shafeshi.


Iska da yanayin gurin daya mishi ma shine yazaunar dashi har tsahon wannan lokacin,baya ga haka da saidai kawai su taddashi gida yawuce abinsa.


A sannan wata budurwa ta iso,duk da cewa shigar doguwar riga tayi amma kuma hakan bai hana wasu daga sassan jikinta fitowa ba,yalolon mayafin data yafa dinma iyakarsa wuya,qafarta sanye da hill shoes,kallo daya zaka mata ka bata sunan 'YAR DUNIYA,saboda dukka yanayinta ya nuna hakan.


Kai tsaye gaban kamal ta tsaya,cikin nuna tsantsar rashin kunya da rashin tarbiyya tadubeshi
"Ka gama guje gujen naka?" Saiya dubi sashen da azeez yake,saidai da alama baima kosan da zuwan nata ba,baya fatan yasan da zuwan nata,don har yau kusan idanun azeez na kanshi,kuma sharudan daya gindaya masa suna nan,duk da yayi niyyar bijirewa amma mommynsa tace yayi haquri ya karba haka,suci gaba da zama tare,saboda akwai wani target nasu kan azeez din,matuqar yabari misunderstanding yasake shiga tsakaninsu to target dinsu zai samu matsala
"Pls lisma,kije zan sameki a gida,ko wani wajen" zare glasses din idanunta tayi tana cuna baki
"Baka isa kasake yaudarata ba ai,kayi na farko kuma kayi na qarshe,bari na gaya maka kamal,ni gaba nake dakai na rantse da Allah akan bariki da iskanci" tafada tana dan daga murya da alama temper dinta tasoma hawa.


Ganin haka cikin wadanda suka san tsakaninsu da lisma din suka soma bata baki,gamida lallabarta taje din kamar yadda yace,sun mata alqawari zai sameta kamar yadda yace.


Kusan duk abinda ake a kunneshi amma saika rantse baya wajen,ko baisan da zuwan nata ba,yana sauraren komai,yana tunanin ba sabgarsa bace ko abinda yashafeshi,hasalima yana ganin zubewar qimarsa ce kamarshi ya tsaya wani maida magana ta hadashi da watsatstsun 'ya'ya irin wadan nan,saidai kalaman data sake fada suka ja hankalinsa harta daga kai yana dubanta fushinsa yanason motsawa
"Ku rabu dani naci uwa da uban dan iska,maqaryaci macuci mayaudari kuma maha'inci,jinin asara haihuwar iska" idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kana yabudesu,yamiqe cak yana aje laptop dinshi daga inda yatashin yana kuma qoqarin controlling anger dinsa kafin ya isa gareta,saidai hakan bata samu ba saboda maganganun data ci gaba da fadi.


"Getout of there!" Yafada cikin wata kakkausar murya data ja hankalinsu dukka harda masu bata haqurin,waiwayowa tayi tana neman wanda ya bata wannan umarnin kai tsaye kamar ubanta ta yagashi shima,saidai suna hada ido saqon ya isa qwaqwalwarta,wannan ba kalar wanda ake iya yagawa bane,kwarjininsa kadai yana karya lagon koma waye kai,maimakon magana saita maida glasses dinta ta rabashi sum sum tawuce daga wajen bayan ta kalli kamal taja masa qwafa alamun zancan bai mutu ba.


Idanunsa qur bisa kamal wanda kallon yariman ya rudashi,baison yadda yake zubawa mara gaskiya idanu haka,ran azeez ke tafasa sosai,saboda yanajin xagin datawa kamal din kamar da familynsu gaba daya take,kusan laifin kamal yafi nata yawa a wajensa,tunda yasan cewa idan babu qira meye zaici gawayi?,idan bai kulata ba ina taga fuska da qwarin gwiwar zuwa ta tsaya haka a gabanshi tana gaya masa wadan nan muggan kalaman.


Akwai magana da yawa a bakinsa,amma saidai baison yace komai da zai tozartashi cikin bainar jama'a masu yawa,tunda dai jininsa ne,hakanan bugu da qari ammi ta masa magana kan yadinga controlling fushinsa akan kamal,tunda dan uwanshine,uwa uba kuma akwai 'yar tsama sosai tsakaninta da momi mahaifiyarshi,so kada tadinga ganin kamar ita ke sanya azeez din yana yiwa kamal din wasu abubuwan.


ƙoƙari yayi yasoma hadiyr fushinsa,harya isa inda ya aje system dinsa ya dauketa yakashe sannan yasoma takawa don ficewa a wajen,tunda sukaga hakan sunsan tafiya zaiyi,don haka babu wanda ya tsaidashi.


Yana gab da ficewar wayarshi tadauki tsuwwa,daya duba yaga ammi ce saiya qi dagawa,harsai daya isa motarshi yabude yazauna asit dinsa kana yabi kiran nata.


"Kana lafiya ko?,jiya banga kiranka ba"
"Lafiya qalau ammi,jiya duka wayar tawa a kashe take,muna da test ne,dana gama karatu sai kawai nabarta a kashe saida muka fito,sanda muka fito kuma dare yayi anan babu damar kira"
"To ma sha Allah....kan maganar nan ta aurenka.....yanzu haka nasa an samo maka yarinyar,ina tunanin cikin satin nan zan turo maka ita ka ganta,idan tayi maka shikenan,inaso ne ayi komai a gama within two to three weaks".


Dayaji ta bagarar da zancan tun wancan lokacin ya zaci tabar maganar ne,sam ya manta shaf da batun,don har yashiga sabgoginsa,bashi data cewa kuma bashi da damar musu,tunda yasakar mata ragamar komai kuma tayi din bai isa ya canza ba,cewarsa a'ah kamar ya taso da wani case ko wata matsalar ne tsakaninsa da ammin,gwara ya amsa koda baiso,koda babu abinda zata amfana masa,amma ko daya baya da buqatar zuwan yarinyar,koma ya take ba matsalarshi bace shi
"No ammi....basai tazo ba,kawai ku qyaleta" sai tadan bata fuska kamar yana gabanta kana tace
"Kamar yaya?,dama an taba aure ba tare da anga juna ba?" Shuru yadanyi na wasu daqiqu sannan yace
"Ba wani matsala bace,itadinma bata ganni ba tace ta amince" kai ta girgiza
"Akwao banbamci tsakaninka da ita,saidai kuma idan akwai wani abu daka shirya kake kuma boyemin....ko kuma kana da wadda kake da muradi daban da kakeso ayi hadin da ita" shima kai ya girgiza kamar tana wajen
"Ba haka bane ammi,indai ke tayi miki nima na tabbata zatayimin,sannan bawai abu bane na dindin ba bare ace ana buqatar dogon nazari ko zabe,it was just like a game...babu damuwa" sai datayi shuru sa'an nan tace
"Is ohk,amma zan amshi koda pic dinta ne na maka sending ta email dinka saika duba" bayason yafiya mata musu,saboda tana da wani girma da daraja a idanunsa,hakanan tafi qarfin komai kamar yadda tafi gaban komai,don haka yace
"Alright ammi,na gode" ƙaramin murmushi tasaki
"Anything for you" tafadi,daga haka suka kashe wayoyinsu.


Sauke wayar yayi daga kunnenshi yana sauke ajiyar zuciya,kana ya waiwaya yana duban almustapha daya shigo motar sanda yake gab da gama wayarshi,mutum nabiyu rak a rayuwarsa da yasan abinda yake gudana,saidai shidin bai bayyana masa cewa shekara daya ne rak zaman nasu ba,tun kafin mustapha yayi magana azeez yarigashi
"She prepared anything" murmushi yayi yana dukan kafadarsa
"Dan gata" ganin yanason maida maganar wasa saiya saki qaramin tsaki yana fitowa daga sit dinsa ya zagaya zuwa inda mustaphan ke zaune yabude murfin motar yana cewa
"Kaimu gida da Allah" yana dariya mustaphan yafito saukayi exchanging seat,ya tada motar suka fice daga gurin,yayin da azeez yayi relax a kujerar motar kawai yanason yayi emptying qwaqwalwarsa daga kowanne irin tunani.
7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: 19


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_______________________________


*_kina buqatar kayan qwalama da kwadayi da kuma maqulashe😋😋,abubuwan motsa baki masu kyau tsafta da kuma inganci?_*

*_Garxaya ki nemi MRS SCHOOL TREATS_*

*_nasan zakuce to me kenan?_*

*_RUGUNTSUMIN GAMAYYAR WAJEN SAMAR MUKU DA KAYAN MAQULASHE IRI DABAN DABAN,DA SUKA HADA DA_*

*tuwon madara mai kwakwa da marar kwakwa*

*da kuma*

*Gullisuwa*
*_dukka na zallar madara mara algus_*🤗

*_cikin nagartacce tsafatatacce_kuma ingantaccen package mai kyau_*

*SIYAN DAYA KO SARI*
_Kar kuyi sanya,maza ku nemeta a tudun wada,hayin buba GUSAU_
_ko kuma akan numbar waya 08069706638_

*_SUNA AIKAWA KOWANNE GARI DA IZININ ALLAH CIKIN AMINCI_*

*_biyan buÆ™atar abokan hulda shine burinmu_*ðŸ¤ðŸ½ðŸ¤ðŸ½

19



Wani irin farinciki ne yake ratsashi tun sanda umma luba ta gama gabatar da saqon fulani aisha,bakinsa ya kasa rufuwa,lallai arxiqin daya dade yana mafarkin samu yanxu yasameshi,maganar hausawa gaskiya ce da sukance DARE ÆŠAYA ALLAH KANYI BATURE,yaushi malam bilya akewa albishiri din cewa za'a rushe gidanshi yazabi kalar irin ginin da yakeso ayi masa,yakuma zabi sana'ar da yake da sha'awar yi,hakanan yazabi irin motar da yakeso yadinga hawa,rawa ne kawai bai taka ba gaban umma luban,amma koda tatafi bai iya daurewa ba sai daya taka din,mama ladi tana tayashi,cikin ranta tana godewa Allah daya sanya batayi gaggawar barin gidan ba,ashe da ita za'aci arziqi,sai daya gama sa'an nan yasoma tambayar mama ladin
"Ina mai gadon take ne,kiramin ita na shaida mata tashirya,sati uku ya rage mata a gidan nan"
"Anya ko tana cikin gidan nan,tun sassafe naji karakainarta da yara tana shirin fita makaranta" idanu ya fidda waje
"Ai bataji ba kenan?,bata yarda da hanata zuwa makarantar da nayi ba?,zamu gamu,nida itane,har makarantar zanje yanzu kuwa" ya fada yana shura takalmansa yafice daga gidan cikin hanzari zuwa makarantar tasu,don yanajin kamar bilkisun nason jawo masa wata asara ce dashi kuma bazai iya jurarta ba.


Kwanakin gaba daya tunda take zuwa makarantar kusan babu abinda take tsinanawa banda kwanciya,koda yaushe zaka sameta kife da fuskarta saman tebur,tashin hankalin da take ji yana fuskanto rayuwarta jikinta ya bata ba qarami bane,ta yaya ya akayi mahaifinta ya aminta da wannan bahagon tunanin?,me yasa ya amincewa wannan wasan yaran saboda dukiya kawai?.


Hakanan tasamu kanta da yawan duban sashen da bilkisun ke zaune,duk da bamai yawan magana bace amma koda tana zaune ne shuru to zaka sameta da littafi a gabanta tana dubawa,koda ba zatayi hira da kowa ba,duk da basa shiri,babu wata magana mai dadi dake hadasu,amma saita tsinci kanta da rashin jin dadin sauyawar bilkisu,ko ba komai a baya sukanyi compatition a aji wajen bada amsa a subjects da dama idan malami yayi tambaya,sukanyi rige rigen miqa classwork tsakanin ita da ita,duk da talura badon ita bilkisun takeyi ba,amma rashin ganin hakan kwana biyu duka sai taji babu dadi.


Kasa shuru tayi ganin kusan awa guda bata motsa daga yadda take ba,ta tabo hanan dake gefanta
"Wai meke damun bilkisu kwana biyu" cikin mamaki hanan tadubi afnan din,don tunda suke bata taba jin takirayi sunanta ba saboda takun saqarsu,kai ta girgiza
"Oho mata,waya sanmata ne" idanunta kan bilkisun dake duqe saman benci
"Kamar tana cikin damuwa" sake daga kai hanan tayi daga kwafar note din da take ta dubeta
"Meye damuwarki a ciki ke idan hakanne" kafada ta daga
"Nima ban sani ba" daga haka tabar zancan,saidai batasan me yasa idanunta suka kasa sauka daga nahiyar da take ba,har zuwa lokacin da aka aiko kiran bilkisun daga office din principal.


Tayi mamakin kiran,don tunda take bata taba yin wani laifi ba cikin makarantar ballantana tace ko wani abun tayi akeson ganinta,hakanan tamiqe tana gyara hijabinta cikin kasala da mutuwar jiki taja qafafunta tafice.


Ba jimawa afra tafita fitsari,sai gata tadawo tana qunshe dariya,hanan ta dubeta
"Lafiyarki ke kuma?"
"Wallahi wani abun tausayi nagani kuma abun dariya,mutuniyar billy ana can ana sharbar kuka a office din principal,babanta yazo yacireta daga makaranta,aure zai mata,aurenma na dole,ke kinga baban nata kuwa?,kamar wani mai tallan agwaluma,ke wallahi me yanke flowers din gidanmu yafishi kyan gani,kuma kina gani kinsan babanta ne wallahi" dariya duka wadanda ke role din suka fashe dashi,ga mamakinsu afnan kallonsu kawai tayi ba tare datace komai ba,tausayin bilkisun taji ya saukar mata,ashe da gaske ne ita din ba diyar kowa bace?,ashe abinda yake damunta kenan cikin kwanakin nan?,shiko me yasa zai cireta daga makaranta,duk qoqarinta da himmarta nazuwa makaranta,kaf ajinsu itace take daukan na daya kowanne tearm,afnan din ke mara mata baya ata biyu,ko ya gaji da biyan kudin makarantar tasune?,tunda a yadda afra ta siffantashi tabbas ba qaramin namiji bane mai irin wannan qaramin qarfin dazai iya biyan kudin makarantarsu
"Wai bakiji mutuniyarki bane?" Hanan ta tabo afnan tana fada dariya tana cinta,wani kallo tayi mata sannan tace
"Naji mana,amma banga abun dariyar bane,tunda dai macace 'yaruwarmu,muma xamu iya fadawa irin qaddararta" shuru kowannensu yayi da mamaki suna duban afanan din
"Kuna mamakine?,bilkisu bata taba yi mana laifin komai ba,inda ace za'a titsiyemu da bulala ace mu fadi abinda ta taba yi mana duk cikinmu babu mai amsa,saimu da muke cusguna mata ma amma bata taba tsayawa ta biye mana ba...."


Shigowar bilkisun ajin yakatse sauran maganar tata,kallo daya zaka mata kasan tasha kuka bana kadan ba,tawuce seat dinta tazauna gamida maida kanta yadda yake dazun.


Har duka periods din suka qare aka tashi daga makarantar bata dago kanta ba,saida kusan kowa a ajin yafice yabarta kana ta hada jakarta da qyar tawuce itama.


Duk da uwar ranar da ake qwalawa ko kadan zafinta bai dameta ba,qunci da baqincikin dake cikin zuciyarta yafi ranar zafi da quna a gangar jiki da zuciyarta,da mahaifinta za'a gama hannu a tarwatsa rayuwarta?,wadanne irin azzaluman masu sarautane su?,wadanda basu damu da buqatar kowa ba saita qashin kansu,dama duka qarya ce da shaci fadin mutane da suke cewa
"Masarautar kaisa badai adalci ba,dukka mai neman adalci to kansa tsaye yanufeta" gashi ita yau adalcin take nema xalla daga garesu amma sun gaza dubanta,indai da gaske ne daga masarautar kaisa akeson shirya mata wannan abun,indai da gaske ne afnan jinin masarautar kaisa ce iya dabi'u da halayenta kawai sun isa su gaya mata cewa lallai sudin mutane ne masu dagawa zalunci da takura,inama ace wanda yamutu yana dawowa yau ummanta tazo taga halin data tafi tabarta a ciki,inama ace wanda yayi nisa yanajin kira anty zuhriyya tazo taga yanayin datake shirin afkawa ta tsamota,tasamo mata adalci da nutsuwar ruhi.


Tafiya kawai take ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,bata ankara ba tajita tsamo tsamo cikin wani ruwa,sai a sannan ta maida hankalinta,ta duba dakyau sai taga ashe kwatace,dai dai sanda motar dake dauke da afanan take dosowa wajen.


Tun daga nesa taga kamar bilkisun,a hankali ta bada umarnin ya gangara gefan titin,tana tsaiwa motar tabude murfin da kanta kana tafito tana qarasowa inda bilkisun ke tsamo qafafunta tana son ci gaba da tafiya ba tare data damu da tsaiwa tayi ratse koda a fanfunan gefan hanya bane ta gyara jikinta.


Riqotan da akayi ya sanyata tsaiwa
"Bilkisu bilyamin" taji an furta a hankali,yadda aka kira sunan yasanya tagene daya daga cikin 'yan makaranta ko ajinsune,saita waiwaya don taga waye,mamaki ya cikaya ganin afnan abdallah mu'az kaisa tsaye tana dubanta cikin alhini da mamaki
"Ya akayi kika fada kwata bilkisu,me yasa bakihau mota kin koma gida ba bayan baki da lafiya" kai ta kada
"Ba komai,yanzu zan isa gida" tasan ta fadane kawai,amma ko ba'a gaya mata ba tasan akwai tazara tsakanin unguwarsu da unguwar da makarantar tasu take
"Ki tsaya ki wanke jikinki,karki dinga tafiya ana kallonki" bata tsaya jin amsar bilkisun ba tayi magana daga

Please Login or Register in order to submit comment