Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amaryar dan bature" ta saketa tana cewa
"Harna soma fushi da ya yarima wallahi"
"Au hakama kikace?,saina koma,da ameer din nawa zaki fushi"
"To matar amir,ayimin afuwa" sai suka saki dariya a tare tana tambayarta shirye shirye tana laluban wajen zama.


"Wai bilkisu ce wannan?" Cewar wata mace dake xaune da yaro a cinyarta,duka suka waiwaya tana murmshi bilkisun tace eh,afnan ta qaraso
"Baki ganeta bane?" Kai bilkisu ta kada mata
"Farha ce fa,ga halima kuma" ta fada tana nuna mata su,cikin farincikin haduwa dasu suka fara gaisawa,kowacce cikinsu kallon bilkisu take tana qarawa,tare da mamakin yadda Allah ya sauya komai,har farha ta kasa daurewa sanda bilkisun ta musu sallama kan zata leqa gida taga ya shirye shirye suke saida ta tambaya afnan
"Ikon Allah ne,Allah ne ya hadasu bani ba" itace amsar data bata.


Yanayin da bilkisun ta samu gidan nasu ya mata dadi sosai,kallo daya zakawa gidan kasan suna cikin wadata,yayunta sun tsaya sosai kan gidan,Allah kuma ya akbarkaci kasuwancinsu qwarai,don yanzu malam bilya yana gida ne kawai yana hutawa,bayaga gini na alfarma da aka buge gidan aka qara masa girma akayi.


Sai data gama duba komai ta tabbatar babu matsala sannan ta kebe da amare hannatu da hauwa'u suma ta tabbatar basu da wata matsala sannan ta sake dawowa cikin gida aka shiga hidima sosai da ita,tuni aka soma shirye shiryen tafiya dinner wadda fulani ce ta dauki nauyi aka hade duka data afnan,bilkisun nata tsokanar hauwa'u da amaryar assadiq,itadai batasan ya akayi na,sai da za'a amshi kudin aurensu sannan ta samu labarin shi ya samu nasarar dauke kuluwar tata.

Tun kafin a tashi daga wajen dinner din tasa aka dawo da ita gida saboda tasan halin yarima sarai,duk da ta gama sakankancewa zata kwana a gida ne,hakan yasa su ahmad ma wajen umma katti ta barsu,taji dadin zuwan saboda sun tattauna sosai da anty zuhriyya,yanzu haka duk dawainiyar yaran ta karatu ta daukewa abbaa shi,duk da yana da qarfin dauka amma tana tuna zallar halaccinsa shi da umman tata,wanda bata da abun biyansu,anan taji zancan kawowa najwa kudi da akesonyi cikin satin,taji dadin hakan sosai,don tasan tana nan kenan za'a kawo din.


Saida driver dinta yana sauketa taga motoci a fake kamar na yarima,tayi mamakin me zai kawoshi goma da rabi na dare nan,tunda tasan dole zai barta ta kwana,sai gobe zata koma masarauta,saidai tana fita a motar aka bude daya daga cikin qofofin motar,a nan ta fahimci yariman ne,don haka ta doshi motar sannu a hankali.


Sit din gaba ta bude kamar yadda ta fahimci shike jan motar da kansa,tana shiga kafin tace komai ya rufe qofar ya kuma tashi motar da gudu yana barin layin,baki sake take kallonshi
"Abban amatu....ya haka?" Fuska a hade yadan dubeta sannan ya kauda kai
"Kamar yaya fa?"
"Ni da zan kwana gida kuma ina zaka kaini?"
"Ni kika tambaya nace na barki?,ina cewa ammi kika tambaya ko?" Zata sake magana ya dora hannunsa saman labbansa
"Shashshsh" sai tayi shuru bata yi maganar ba kamar yadda ya buqata,amma kuma fuskar nan a hade tana zumbura baki.


Motar ta dauki shuru na wasu mintuna,sai kuma ya saki nannauyar ajiyar zuciya,kana ya miqa hannunsa daya ya danja hancinta
"Cikin kowanne yanayi kyau kikemin,princess kema kinsan ba yadda za'ayi muna qasa daya gari daya na iya kwana babu ke a gefena,bazan iya barinki kwana ko inaba,idan nayi hakanma na tabbatar bazanyi bacci ba a ranar,ki gafarceni,kinfi kowa sanin haka nake".


Ba shakka gaskiya ya fada,tafi kowa sanin halayyar yarima akanta,baya iya jurema rashinta ko qaqa,tun bata saba ba tana qorafi harta saba,anty zuhriyya tasha gaya mata hakan wata daraja ce a wajen mace,wata da wanzuwarta da babu duka dayane wajen miji,sai a yanzun take sake gasgatawa,kafin tace wani abu kuma taji sautin muryarsa kamar me qunquni yana cewa
"Idan kuma abun hakane kawai saina sake lalubawa ko zan samu wadda tayi koda kwatarki ce na samu na dinga ragewa da ita tunda nan an fara gajiya dani".


Harara ta jefa masa mai tafe da kallon so,sai ta fasa mishi kukan shagawaba,ba shiri yayi parking ya hau lallashi,sai data ja ajinta abinta son ranta sannan tayi shuru,ya sauke ajiyar zuciya duk da yasan na wasane amma baya fatan wata rana tazo dazai bata mata da gangan tayi kuka kansa irin haka
"Kin dagamin hankali fa" murmushi ta sake masa
"Afuwa nake nema,bana fatan na zama silar hakan a rayuwarka" yana shirin sake tada motar yace
"Na sani,amma duk da haka yau saikin biya bashin wannan kukan da kika saka na bata lokutta ina lallashinsa,a daren nan ina buqatar qarin twince,dukka yammata pls" murmushi ta kuma sakewa tana sake jin sabuwar qaunarsa,bata taba ganin mutane masu son yara irin jinin fulani aisha ba,duk da yadda ta gaji amma batajin zata iya hanashi yayi yadda yaga dama da rayuwarta
"Baka da case in sha Allah,afnan ta gayamin har yanzu jikokin basu ishi ammi ba" saiya waiwayo cikin fara'a yana dubanta
"Na dade da sanin bilqeesa ta jaruma ce,ina fata Allah yasa yarana su dauki halayyarta,yasa kuma ta zama min uwargidana har a aljanna" hannyenta ta daga sama alamun addu'a
"Nima fatana kenan,Allah ya barmin yarimana har a aljanna...." Tun kafin ta qarashe ya cafe ya amshe da amin,hakan harya baya dariya shima ya biye mata yana tayata cike da zallar qaunar juna da farincikin rayuwa.



*TAMMAT WALHAMDULILLAH*🥰🥰🥰🥰

_Anan na kawo qarshen wannan littafi nawa na siradin rayuwar bilkisu,ina fata Allah ya yafemin dukka kura kuran dake ciki,ya hadamu a ladan_


_duk inda akace zo mu zauna zo mu saba,ina neman afuwa ga duk wanda na sabawa kona masa ba dai dai ba,ta hanyar lafazi ko aiki,zan iya cewa ajizanci ne irin na dan adam,da fatan zaku gafarceni,Allah ubangiji ya sadamu da rahamarsa,yasa idan muka tsaya gabanshi zamu tsaya ne don amsar lada da kyawawan ayyukanmu,ba domin tuhumar juna ba_🤲ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½


_ina mai barar addu'arku da bakunanku masu albarka kan wata buqata tawa,ina fata ubangiji ya cikamin ita alfarmar ma'aiki S A W nida sauran dukka al'ummar musulmi_


_Saqon jinjina da godiya ga mabiya ZAFAFA BIYAR 'YAN AMANARMU wanda kullum basa gajiya da patronizing dinmu,ubangiji yaci gaba da buda muku da yauqaqa arziqinku,yabarmu cikin amana da aminci_


_muna muku fatan alkhairi,sai haduwa ta gaba idan ubangiji mai kowa mai komai ya yarje mana lafiya da tsahon rai,haqiqa muma zamuyi kewarku🥰🥰🥰_


_SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASHHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA_🤲ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½ðŸ¤²ðŸ½


©ï¸Â®ï¸ *ZAFAFA BIYAR 2021*
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment