Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kunnenta ya gaya mata wani abu daya sanyata qwace jikinta da sauri bayan ta saka hannuwanta ta rufe fuskarta,ta yaya zata manta wannan lokacin,lokacin da asannan takejin tafi kowacce halitta baqinciki a duniya,tafi kowacce halitta rashin sa'ar rayuwa,ta kuma fi kowacce halitta asara,saidai a yanzun tunaninta nata sauya mata dararen guda biyu zuwa darare masu tarihi arayuwarta,daren farkon daya bambanta da kowanne daren farko.na kowanne ma'aurata,tana danne kunyarta da boye dariyarta tace
"Lalala nifa ba haka nace ba,kuma ni ba haka nake nufi ba" wani murmushi yake jifanta dashi hade da wani kallo da zai gaya ma mutum cewa ya dade da narkewa cikin duniyar qaunarta
"Zoki gayamin to yaya ne?" Ya fada yana qoqarin kai mata cafka,saidai knocking din da akayi a bakin qofar ya tsaidashi,ya kalli qofar saiya basar kamar baiji ba,ya sake maida hankalinsa a kanta yana sake takawa zuwa inda da durqushe,bai qarasa ba aka sake qwanqwasawa,tsaiwa yayi cak,kana cikin qasaitacciyar muryar shin nan yace
"Afnan!....zaki bar wajen ko sai nazo na bata miki?"
"Ba afnan bace,uwar afnan dince" ya tsinkayi muryar fulani,saiya dafe goshinsa da tafin hannunsa,ya salam,asirinsa ya tonu?,bilkisu kuwa tuni ta miqe ta bude bandaki ta shige ta maida qofar ta rufe,da wanne ido zata iys kallon ammin idan fa shigo ta gansu tare.


Qofar ya nuna ya bude,tana tsaye tana kallonshi,ta tsareshi da ido.sosai,kunya ta kamashi amma saiya maze ya rabeta zai wuce
"Ina bilkisun?"
"Tana toilet" ya amsa mata yana wucewa
"Ka jirani anan" ta amsashi tana shiga ciki.


Dakin tadanbi da kallo har saman gadon,a gyare yake ba alamun wani ya hau,saita saki ajiyar zuciya,batason yakai ga tabata yazun,harsai ta gama shiryata tsaf ta yadda zai sake raina kanshi
"Idan kin gama.boyon ki sameni falo" ta fada tana dake dariyarta,don taga alamun jinta ne ya sanyata kulle kanta a bandakin,ta juya ta fice tana jin sanyi cikin ranta da Allah ya azurtata da suruka irin bilkisun,tana tuna abinda ya faru awa daya data shude tsakaninta da safwa da iyayenta.


Ta shirya ne da kanta zataje ta zayyane musu komai ta kuma kawo gyara kamar yadda tayi na bilkisu,tunda ita ta shirya komai,lokacin data iske mahaifiyar safwa suna tare da safwan,kanta na saman cinyarta uwar na shafa kan nata kamar wata jinjirar goye,da alamu ma kuka ta gama yi,shigowar fulanin ya sanyata yin zumbur ta miqe,bata ko tsaya gaidata ba ko mata magana ta haye sama abinta,inda katafaren sashinta yake kamar dama can a gidan take zaune,bawai aure take a wani waje ba.


Sama sama suka gaisa da mommyn safwan,itama tana ta wani cin magani,bata boye mata komai.ba ta fayyace mata tare da neman suyi haquri safwan ta koma dakinta ta zauna kamar kowacce mace,cikin daure fuska take amsa mata
"Amma dai wannan abun hajiya aisha ke kanki kinsan zallar cin amana ce da rashin gaskiya,ya za'ayi yana tare da yarinyarmu amma har a zagaye a aura masa wata?,kuma harda yara tsakaninsu,ace kuma waike bakisanma suna tare ba,hakanan bakisan da yara tsakani ba sai bayan wasu shekaru,ai hankali ma bazai kama ba,gaskiya bazan boye miki ba,naji zafin wannan abun sosai,kuma bawai ni kadai ba,hatta da daddynta yaji ciwo sosai,kuma ni bani data cewa sai abinda yarinya tace,saboda haka zan turota kuyi magana tsakaninku" daga haka ta miqe ta haura dakin safwa,wanda sai data kusa minti arba'in zaune tana jiransu,da alama bayan ta gama bata labarin komai sai data sha kanta da qyar kafin ta yarda ta fito,sai gata ta sauko tana wani kumbure kumbure.


Da harshe irin na uwa fulani aisha tayi magana da ita cikin lallashi da fahimtarwa,saidai tana bude bakinta cikin tsanar sakalci da sangarta tace
"Nifa yanzu na tsaneshi ma,saboda maci amana ne mayaudari,na bashi amana dari bisa dari amma yamin wannan yaudarar tsayin shekarun da muke tare dashi?,ni bazan koma gidansa ba saidai.idan har zai saketa ya rabu da ita,ni kadai na rayu a gidanmu kamar yadda momy na take ita kadai wajen daddy,so ni banga wani dalili da zai sani in zauna da wata ba" tadan murguda bakinta ta miqe ta koma inda ta fito,yayin da fulani ta bita da kallo cikin mamaki da takaici,saidai batason bacin rai ya kaita ga yanke hukunci da sauri,ko meye itace sila dole ta daure koma me zata gani ta kawo gyara iya iyawarta,haka ta miqe ta iske barorinta suka bar gidan.


Sai data iske mai martaba ta sanar mishi da komai,yayi shuru yana mamakin irin nasu dattakon su kuma a matsayinsu na iyaye,sai yayi ajiyar zuciya kana yace
"Zan samu lokaci nida kaina na iske ibrahim din,komai zai daidaita in sha Allah" da wannan ta baro wajensa,saidai ranta cike fal yake da mamakin abinda sukayi matan.


A falon ta iske azeez tsaye hannayensa zube a aljihu,idanunsa saman tv,saidai ba ita yake kallo ba,duka tunaninsa na ga bilkisu ne,zama tayi sannsn tace dashi
"Xauna" hannayen nasa ya cire kana ya zauna saman kujerar datafi kusa dashi,a nutse ta soma masa magana
"Inason kome safwa zata ce da kai,kayi haquri har sai al'amura sun daidaita" shuru yayi yana juya maganar aransa,hakanan jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa,amma dai saiya amsa mata dato,kana ya miqe ya nufi fita daga sassan.


Baiyi wani nisa ba yaji kamar muryar afnan na kiranshi,ya dakata ya waiwayo yana dubanta harta iso,sai data qaraso kuma sai tayi laushi kanta a qasa tace
"Yaa azeez....ammi ta boye maka ne,bata gaya maka komai ba" nan ta gaya masa dukkan abinda ya faru kamar yadda fulanin ta bata labari bayan ta dawo.


Wani irin bacin rai yaji yana hudashi,har wani tururi yakeji saman fuskarshi,idanunsa kafe jikin wata bishiya daura dasu,saidai a badini ba ita yake kallo ba.



Bazai taba lamunta wata halitta ta wulaqanta masa mahaifiya ba,bare mace macen ma matarsa,wadda a musulunce take a qarqashinsa,bayan ita din harda mahaifiyarta itama?,uban me suka musu?,duk iskanci da sakalcin da yarinyar takeyi bai taba daga kai ya duba koya dauki mataki mai tsauri ba duk sabida darajar ammin da takeci su basu gani ba?,bazai taba lamunta ba,koda da ruwan gold daka qerata kuwa bata isa ta taba mishi.mahaifiya ba,inda yasan ma inda ammin ta tafi da bai barta ba,don ko sabon aurene ya qara baida laifi a irin rayuwar d sukeyi da safwa din,wadda sam batasan muhimmancinsa ba bare auren dake kanta,tsabae sakacinta ya bada gudunmawa wajen mutuwar gudan jininsa suhaima,ko sun dauka ya manta ne?,ko zuba musu idanun da yayi suna zaton shi sauna ne ko baison ciwon kanshi ba?,kai kawai ya jinjina bai iya cewa afnan komai ba ya soma takawa yana barin wajen.


"Gwara a gaya masa gaskiya,kada ta dawo tazo taci gaba da wannan iskancin banzan kamar wadda aka yaye daga nono" afnan ta fada tana juyawa tana barin wajen.


Kiran da taji ana mata ya tsaidata,daya daga cikin barorin gidanne,ta qaraso da hanzari hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando da aka saqa da hannu da wata iriyar ciyawa
"Ranki ya dade,mangwaro na tsinko a lambun gidan nan,irin wanda kikeso,naga yafi dacewa dake" murmushi ta saki,ta saka hannu tana yaye dan qyallen da aka rufe kwandon dashi,ta dauki daya tana cewa
"Amma kuwa kin kyauta asiya,a wanke yake?" Tayi tambayar tana kaiwa bakinta
"Fes ma uwar dakina" ta bata amsa tana murmushi itama.


Kai ta jinjina bayan ta gutsira
"Yayi,irin nawa ne kuwa har dandanon,muje ki ajemin,kin cancanci a baki tukuici" cikin farincikin yadda ta amshi kyautar tata tadan rusuna kanta
"Kinfi gaban haka mai hannun alkhairi irin na uwarta,godiya nake" daga haka suka rankaya tare suna taba hira abinsu,kai bakace asiyan qasa da ita take ba.


¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶


Cikin satin kyakkawan saqon katin da aka qawata adonshi da ruwan gold ya zagaya lungu da saqo na masarauta kaisa dama qasar kaisa gaba dayanta,tare da wasu qasashe maqwabta dana nesa da suke wannan duniya dama garuruwa baki daya,katin daya daga hankalin maqiya da abokan adawa da yawa,katin daya faranta ran wasu,katin daya sanya ayoyin tambaya cikin ruhi da zukatan wasu,ya sanya wasu rayukan kuma cikun zumudi da son ganin zuwan wannan rana.


Katine dake dauke da gayyata ta musamman zuwa babban bikin taya yarima Abdul'azeez abdallah mu'az kaisa da mai dakinsa Bilkisu bilyamin murnar cika shekara takwas cif da auren wedding anniversary,sunan dake manne saman katin shi ya sanya al'umma da dama tambayar wacece?,tunda da yawansu sunsan safwa ne,babu wanda yasan da wanzuwar bilkisun.


Duk da cewa fulanin da fari ta dauka komai zai daidaita tsakaninsa da safwa ta hadasu dukka ta musu,rashin samuwar hakan da gudun bata lokaci yasata kawai aiwatarwa.


Sanda kyayykyawan katin daketa sheqi ya isa hannun safwan kamar tayi qaramin hauka haka taji,ta dinga koke koke kaman qaramar yarinya tana sake tabbatar da cewa azeez yaci amanarta,kuma babu ta yadda zata koma masa,babu bata lokaci ta dauki waya ta tura masa tex,ya gani ya karanta,ya kuma yi murmushi kawai sabida ya riga ya wuce wannan babin,yaci kuma da irgen kwanakin daya bata kawai,duk da bai fahimci wasu daga cikin kalamanta ba,don baisan me fulani ke shiryawa ba a lokacin.


Cak ta tashi fulani adama hajja fauxiyya da shalelenta kamal a tsaye,hankalinsu a matuqar tashe suka hadu domin tattaunawa kan lamarin,kowa ya kawo tashi shawarar,wanda suke hasashen cikin biyu abu daya ne zai faru,imma dai taron ya zamewa aishar abun kunya da tonuwar asiri gareta da iyalanta,ko kuma ya zama wankuwar laifi da fidda kai daga zargi a idanun al'umma,wanda daga qarshe sukaga babu wata mafita,illa dai kawai su zuba idanu suga yadda taron xai kaya,daba bisani sai susan matakin dauka na qarshe,don na zasu bata zuba idanu ko lamuntar wahalar da suke da fadi tashi na shekara da shekaru ya tashi a banza ba.



Ta fannin fulani saratu itadinma cikin dimuwa da tashin hankalin take,ya tabbata dai yana da wata matar kenan bayan safwa?,duk kudin data zuba kan amata aiki akansu ya tashi abanza kenan?,hakan bai sanya ta saduda ba,kudi ta sake zubawa masu ciwo duka akan azeez din,saidai kowa ya amshe kudinsa ya kuma kalmashe,sannan ya bita da qaryar ta zuba idanu daga nan zuwa bayan taron,zataga abinda zai faru,bayan kowa ya bincika yaga aikin yafi qarfinsa,amma babu wanda ya gaya mata,saboda yana tsoron rasa kwasar ganimar kudaden data je musu dashi.


Tayi imani dasu,ta kumayi imanin duk abinda suka fada haka yake,don haka tadan samu 'yar nutsuwa kadan ta sama ranta zata jira din daganan zuwa ranar taron taga me zaya farun kamar yadda suka alqawarta mata,harta samu damar qarfafawa su walida gwiwar su halacci taron da suka shaida mata gayyatar da fulanin tayi musu,don tana ji a jikinta suke da nasara a ranar.


Abinda bata sani ba,tun farkon lamarin fulani aishan ta bada kudin sadaka masu tarin yawa kan ayi mata sauka babu adadi kamar yadda ta saba,wannan karon kan Allah ya daidaita komai cikin hikimarsa da ikonsa,ya kuma karesu ita da dukka ahalinta daga sharrin mai sharri mutum ko aljan.


Yadda al'amura ke gudana da shirye haiqan,kai kace auren afnan zatayi shi yake sake daga musu hankali,shiri take na qasaita isa ixxa da nuna zallar mulki da sarauta daga inda aka gajeta ba taka haye ba,hatta wasu sassan na gidan ta saka an sake gyaresu domin saukar baqi.


Duk abin nan azeez bai sani ba sai daga baya,shi daya ya dinga murmushi yana shafa kanshi,qaunar mahaifiyar tasa da tausayinta na sake ratsashi,farincikin da yaji a lokacin ba dan kadan bane,don haka shima saiya soma shirya nashi gagarumin walimar sanyawa auren albarka,ya kuma soma tura katin gayyata ga dukka wani abokin arziqi ko na huldar kasuwanci nashi dake fadin duniya,tare da shirya musu tafiya umara suyi azumin ramadan acan shi da ita dasu amatu,ba tare da sanin kowa ba banda anty zuhriyya.


Duk wani jini ko ahalin me martaba sai data tabbatar da goron gayyata ya isa gareshi,ciki harda yaran su fulani adaman da kanta ta aika musu ba tare data bi takan iyayen ba,hakanan nata yaran sumaira uswa da aafiya dukkansu kowacce ta dokantu tazo gidan,don basu taba haduwa da bilkisun ba.


Ga me martaba kuwa sanda ta miqa mishi katin ya gama karantawa saiya saki murmushi,yasani cewa tayine domin ta sake wanke kanta a idanunsa,tayi ne donta wanke yaronta daga zargin masu zargi,sannan tayine donta daga hankali ta dugunxuma hankalin abokan adawa yadda ta saba,hakanan tayine donta wanke kanta ta kuma bayyanawa duniya abinda ada ta boyeshi da hannunta,ta kuma qarasa aikinta,wanda takeji har jiki da zuciyarta shine abunda yayi saura da zatayi ta qarasa gyara dukkan alaqar data bata a baya,bawai kawai zallar manufar WEDDING ANNIVERSARY bace kawai,kamar zata jefi tsuntsaye da yawa ne da dutse daya
"Aishatunnabiyyi.....Allah ya nuna mana,ya bamu aron rai da lafiya" murmushi tayi tana amsa mishi.


Shi a karan kansa yakejin abun yayi dai dai,ya kuma burgeshi,shima saiya samu kansa da dokin zuwan wannan rana.


Bilkisun batasan dukan yadda aka shirya abun ba,duk da tasan da taron,harma ta gayyaci farida ita kadai,saidai yadda afnan ta kasa zaune ta kasa tsaye abun ke bata mamaki,a hankali kuma ta gano ba qaramin shiri sukema abun ba,ita abunma daure mata kai yake,yadda fulanin ke nuna mata qauna tare da qoqarin karbe fadar anty zuhriyya qarfi da yaji
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmussalihat" takan furta lokaci lokaci kawai,saboda tasan banda Allah babu wanda ya isa ya mata hakan.

*_na gode da uzurinku gareni,kuci gaba da haquri har zuwa sanda zamu rufe littafin,fatan alkhairi🙋ðŸ¾â€â™€ï¸ðŸ™‹ðŸ¾â€â™€ï¸_*
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 77



Cikin dimuwa sukayi gware da juna lokacin da hajja fauxiyya ke kai kawo tana jiran shigowar fulani adama,dukkansu goshinsu ya bugu sosai,kowanne ya hau sosawa amma sam ba wannan bane damuwarsu ba,tsantsar tashin hankalin da suka gani yanzu a wajen gudanar da taron weddinga anniversary din ya shafe komai,ya shafe duk wani zafi da radadi da zasuji.


Cikin zallar tashin hankali adama ta kama hannun fauziyya
"Da gaskene wai fauxiyya abinda idanuna suka ganemin kuma naji ana fada?,abdulazeez keda wadan nan 'yan biyun masu kama da juna?,don Allah kicemin mafarki nake" ta fada tana jijjiga hannun fauxiyya wadda itama gaba daya tashin hankalin da take ciki take jinta kamar ba cikin duniya ba
"Adama....adama na fiki shiga tashin hankali" ta fada tana buga cinyoyinta da hannu,duk yadda fulani adama taso daure kukanta wannan karon ta kasa,sai kawai ta dafe kanta da hannu biyu ta saki kuka tana fadin
"Wallahi aisha ta cucemu,ta shammacemu,tako ina tasha damu,ta zarcewa tunaninmu,aure tayi masa a boye da hadin bakin maimartaba,ta yadda ba zamu iya cutar dashi ko abinda suka samu ba,tanuna mana wannan kodaddiyar yarinyar a zuwan ita kadaice matarsa,Allah ya isa aisha,kin kadar da tunaninmu na tsahon shekaru,inda muka nufa daban kema inda kika nufa daban" saita sake kukanta sosai,saboda yadda abun yake mata ciwo a zuciya,duk wata hanya da take ganin ta dace tabi don tarwatsa matar da ahalinta amma ya gagara,tsayin shekaru aishan bata taba barin tunaninta ya huta ba da laluben hanyar daukar fansa mafi ciwo ba,sai gashi yanzu dukka dararen data bata a rayuwarta sun tashi a banza,hannun agogo ya sake komawa baya fiye da yadda yake ma a da.


Hajja fauxiyya sam ta kasa zama,sai kaiwa da kawowa takeyi kamar wanda ta hadiyi tabarya,gumi kawai ke yanko mata,tana jin abun kamar mafarki take wanda za'a iya tashinta kowanne lokaci.


Daga can dakin taron kuwa 'yan qananun gulmarmaki ke tashi,mafi yawa daga bakin munafukai ne,kowa yana tattaunawa da abokin zamansa,yayin da mafi yawa mamaki yafi cika zukatansu,musamman wadan da zukatansu ke cike da alkhairi da kuma qaunar fulani aisha na yadda ta fita zakka cikin dukka matan me martaba wajen tausayawa da sauraren matsalolinsu,tunaninsu yafi karkata kan akwai babban dalili da yasa auren ya zama a rufe har zuwa yaran da suka samu,sun ta'allaqa hakanne saboda samun tsaro a rayuwarsa data yaran daya samun,wanda qilan sai yanzun ne suke ganin lokaci yayi da ya kamata a bayyanawa duniya su.


Tun tana zaune tana ganin zata jura,tana danne gudun da zuciyarta ke qarawa tare da ganin al'amarin kamar almara ce har juriyarta ta gaza,a hankali fulani saratun ta sulale daga inda take zaune ta zube a qas ba tare data shiryawa hakan ba,tsabar razana da ganin yaran da tayi baya ga matarshi bilkisu,hankalin yaranta yakai gareta,suka isa wajen da gaggawa suna girgizata,idanunta na kansu saidai babu baki ko damar motsa hannu,haka aka dauketa zuwa cikin gida cikin tashin hankali,yayin da yarima azeez da bilkisu harma da fulani aisha ke can suna gaisawa da jama'a cike da zallar farinciki,wanda hatta da bikisun a yau tana jin kanta ya daban kuma ta musamman.


Duk inda suka gitta sai idanun kamal ya musu rakiya,yana daga zaune a inda yake tunda yazo,zallar kishi wanda hassada tafi yawa a ciki ke cinsa,kanshi yakewa tambaya,waishin me yasa duk abinda ya burat a rayuwarsa saiya zama mallakin azeez dinne,yaso suna daukaka dukiya da uwa uba kudi,dukka ciki babu wanda ya samu,amma sai gashi azeez din ya mallaka,yaso bilkisu tun ranar daya soma ganinta,sai gashi ta zama matarsa harda kyawawan yara biyu.


Idanu ya lumshe yana gayawa kansa tabbas wannan karon bazaiyi faduwar baqar tasa ba,sai ya dasa baqinciki a rayuwarsu,wannan murmushin saiya juyashi ya koma kuka da alhini,saiya miqe da hanzari,cikin qarfi da zallar bacin rai yake takawa yana barin gurin,tare da ayyana da kuma tsara yadda zai gudanar da komai a daren yau basai gobe ba.


Sosai taro ya bada ma'ana,hakanan ya qawatar,ya kuma faranta ran zuciyar masoya masu qaunar fulani da ahalinta.



Gagarumin zaman cin abinci ta sake shiryawa tsakaninta da memartaba da duka iyalin nata a wani waje na musamman cikin gidan,saidai lalurar data samu fulani saratu bagatatan wadda ba'asan dalilin samuwarta ba ya sanya zaman ya kasance daga ita sai 'ya'ya da jikokinta.


Karfe bakwai na dare aka sanya zaman zai kasance,kusan tunda aka tashi daga wajen taron tana tare da fulani,anty sumaira uswa da aafiya,wadanda sukejin kamar su hadiyeta ita da twince,abun mamaki yadda bata zata ba yaran sun sake sosai cikin gidan,kamar dama can sun saba dasu,sai wajen bayan la'asar sannan fulani ta hadata da zababbun barori masu mata hidima zuwa qawataccen sassan yarima azeez dake gidan bisa rakiyar afnan.


Tunda aka tashi shima bai samu zama ba,hakan ya sanya basu kuma haduwa da ita ba,yana can wajen baqinsa,wadanda wasunsu ke masa sallama suna komawa inda suka fito,tunda tafiya ce ta jirgi,wasunsu kuma zasu kwana ne a qasar kaisan,su jira walimar daya shiryawa a washegari.


Tamkar baquwa haka ta zauna a sassan,gashi afnan ta koma ta barta,daga ita sai yaran,wadanda suma baqunta bata gama sakinsu ba.


Ana magariba afnan da kanta tazo daukan amatu da abdul,tare da kayan da za'a sanya musu,iri dayane sak kayan,sai bambancin danki na mata dana maza,kaya ne dake nuna zallar sarauta da kuma tsadar da suke dashi,ita kanta da aka gama shiryasu kallonsu kawai take,saita lumshe idanu,ta tsinci kanta da godiyawa Allah daya bata su a matsayin yaranta na cikinta,wani lokaci sai taga kamar ba ita ta haifesu ba,kamar ba daga jikinta suka fita ba,ana gama shiryasun afnan ta kalleta
"Anty saidai fa ki taho donmu munyi gaba,kowa twince yake jira" murmushi tayi
"Wariyar launin fata zakimun?,kafin ki sansu wa kika fara sani?" Dariya ta saki
"Ke,amma yanzun gsky sun qwace fadar,saidai kiyi haquri daga ke har ya azeez din" dariya ma ta bata,saita tura qofar toilet kawai ta shiga don tara ruwan zafi su kuma suka fice.


Tana tsaka da shiryawa ya turo qofar,a raxane ta juya,don bata taba tunanin shigowarsa dakin ba a lokacin,saboda taga dakuna da yawa,bata kawo zai shigo nan din ba.


Idanunshi a kanta yake takowa inda take,yayin da ita kuma zuciyarta ke bugawa da sauri,tama rasa inda zata nufa don ta boye har ya cimmata,a bayanta ya tsaya a hankali ya kuma jawota jikinsa ya rumgumeta tsam yana sakin ajiyar zuciya
"Barka da warhaka gimbiya" ya fada a hankali kamar meyin rada,idanunta ta lumshe,tsigar jikinta na tashi,ta kasa amsa mishi harya sake cewa
"Maimakon ki jirani inxo muyi wankan tare?,tunda baki jirani ba dole ki sake wani kam" kafin ta ankara ya sunkuceta yayi bandakin da ita,saita kasa musa masa ko qwatar kanta.


Cikin bathtube din cike yake da ruwan data tara,don haka zare dan towel din jikinta kawai yayi ya tsullumata a ciki shima yabi bayanta,kamar xata narke saboda kunya haka taji,ta dinga qoqarin ya fita ya bata koda towel dinne ta daura amma sam yaqi,yayi mursisi abinsa,kamar ma baisan tana yi ba,daga qarshe ma saiya sanyata a jikinta ya soma aika mata saqonnin da suka mantar da ita akan me take magana.


Sai daya gama aika mata da saqonni son ranshi sannan ya barta ya soma wanke jikinsa,ta runtse idanunta don bata son ganinsa a haka,yana ganinta saiya tari ruwa mai sanyi ya watsawa fuskarta data yi wani kyau da haske saboda gyaran data sha
"Zakima sabane,sannu sannu wataran ma ke zaki min wanka,gwara ma ki shirya" tana jinsa harya gama bata bude idanunta ba,sai daya daura nashi towel din sannan ya miqa mata hannu
"Taso na sa miki muje mu shirya,mun wuce lokaci,nasan mu suke jira" kafada ta maqale,don ba zata iya tasowar yadda yakeso ba,murmushi kawai ya sakeyi saiya ciro towel din ya aje mata gefan bathtube din ya juya baya,da sauri ta dauka ta miqe ta daura,tazo ta rabeshi zata wuce,saiya kamo.hannunta yasake janta zuwa jikinsa,daurewa kawai yakeyi,yanaso ne ya nuna mata ainihin qauna da soyayya wadda yake ganin kamar tana doubting samunta ko tabbatuwarta daga wajenshi,hakan yasa ya yima ranshi alqawarin sai ya gamsar da ita cewa yana mata so guda daya tak ne.


Duk yadda take dojewa bai barta ba,don kusan tare suka shirya,cikin kayan da itama batasan da zamansu ba sai daya bata,wohoho,zo kaga zallar kyau iya kyau,kamar kwatankwacin wanda sukayi a taron daxun,wanda ita da kanta sai data tofa addu'a ta shafa a daxun saboda maganin baki,yana riqe da hannunta suka baro sashen zuwa sassan fulanin.


Yana labe a inda ya tanada sukazo suka giftashi,ya bisu da kallo ranshi na sake quntata,zuciyarsa da shaidan na sake ingizashi tare da bashin qwarin gwiwa na aikata abinda ya qudirta,saiya ciro wayarsa ya turawa fulani adama dan gajeran tex
_sun fita zuwa wajen,ina da tabbacin ba zasu wuce awa guda ba,dasun dawo zan shaida miki,kiyi qoqarin kiranshi zuwa sassanki_

Daga haka ya maida wayar aljihunsa yana jan qwafa qasa qasa,gamida sake cin buri kan abinda zai aikata din.


Lokacin da suka isa tuni suka samu kowa ya hallara su kadai ake jira,cikin qauna da kulawa kowa ya taresu,sannan suka fara gabatar da abinda ya tarasu a wajen.


Kallo daya zaka musu kasan cewa ahalin na cikin zallar farinciki qauna da kuma fahimtar juna,zuciyar fulani aisha a wanke fes haka yau takejin kanta,idan ta dubi iyalin nata sai taga kaman tafi kowa sa'ar rayuwa,hakanan qima da qaunar bilkisu kowanne lokaci sake yawa take a ranta,kunyarta kawaici da girmama na gaba da ita,bambanci take gani muraran tsakaninta da safwa,wanda ada bata bambance ba sai a yanxu.




Please Login or Register in order to submit comment