Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya fada yana maida hannun rigarsa,wanda ya nadeta ne dama don ya nuna mishi qwanjinsa sanda yake masa misali da qarfin da yake dashi na qwatar soyayya.


"Tunda kai ka gaza yin komai mu munyi maka.....na maka bikon matarka amm...." Baiko jira yaji qarshen maganar ba gaba daya ya kama hannunshi ya riqe gam,bakinsa yana motsi ba tare da ya iya furta komai ba,dubanshi me martaba yake shima yana dariya
"Sakarmin hannu mana,yada saurin murna haka bakaji qarshen zancan ba" kunya ta kamashi,ya zame hannunsa daga cikin na me martaba
"Zata koma aduk sanda ta gamsu a karan kanta,wanda ni na bata wannan damar,saboda kada shiga haqqin nata yayi yawa" saiya sauya yanayin fuskarsa sannan ya koma sarki abdallahnsa sosai
"Abdul'azeez,abinda kuka shirya kuka aiwatar kaida mahaifiyarka yayi.masifar batamin rai da bani mamaki,ya nuna cewa bakusan daraja da qimata ba,hakanan baku daukeni a bakin komai ba,duk da cewa laifin mahaifiyarka shine kaso casa'in cikin dari,kai kuma kana da goma...."


"Abdul'azeez,nine uba kuma mahaifi a gareka,nine wanda nafi cancanta tun asali ka soma shaidawa cewa kana da buqatar aure,bawai mahaifiyarka kadai ba,dukkan wata dama ta sakin fuska da yadda zamu shaqu da juna na baku ita,sabida ire iren wadan nan abubuwan na rayuwa,bare kace babu fuskar da zaka shaidamin hakan,inda na godewa Allah ka shaida matan itama,baka shiga baragurbin rayuwa da matan bariki ba,irin yadda wasu daga cikin matasa da suka samu dama irin taku suke shiga ba,na godewa Allah daya zama kun hadune ta halastacciyar hanya,hakanan jikokina sun fito ya halastacciyar hanya"


"Abu na biyu shine,babu biyayya ga abun halitta wajen sabawa mahalicci,a duk sanda ka fuskanci mahaifiyarka takauce hanya,kayi qoqarin dawo da ita hanya ta mu'amala me kyau,da kuma tausasa lafazi,idan hakan bata samu ba kuma,itama tana dana gaba da ita,kayi qoqarin shaida musu saboda kauda ita daga fadawa halaka,wanda kai baka aikata hakan ba,sai kaci gaba da yi mata biyayya ba tare da kayi yunqurin shaida min ba"

"Na uku baka duba dukkan nauyin haqqin dan adam dake wuyanka ba,ka iya sakar musu yarinya don kawai mahaifiyarka ta baka umarni,wannan shine kuskure na qarshe mafi girma wanda ayanzu kaga ishara,saidai ka roqi Allah wannan jiyyar dakayi ya zame maka kaffarar zunubin dake tsakaninka da mahaliccinka,ita kuma yarinyar kayi qoqarin neman yafiya da afuwarta itama,ka kuma riqeta da kyau riqon tsauri,ka gyara duk wata baraka data taba giftawa tsakaninku,Allah ya gani,ni nayi iya nawa yin,sauran gyaran kuma ya rage naka".


Kanshi a qas,cike da gamsuwa da kuma nadama yakewa mai martaba godiya,qauna da qimar mahaifin nashi na sake qaruwa cikin ranshi,bai wani jima sosai ba yayi mishi sallama ya tafi.


Sosai ya shiga zurfin tunani bayan fitar me martaba,can qasan ranshi yanajin wani dadi da farinciki na musamman yana ratsashi,ji yake kaman ya fice daga asibitin a yanxu ya tafi ganinta,saidai kuma babu wannan damar,saboda wani plan da ya tsara ma ranshi,wanda itace ha ya mafi sauqi da zata kawo masa bilkisun har dakin asibitin ba tare da anja wasu dogayen kwanaki ba.


Daga dakin da aka kwantar da azeez din likitan dake ganin azeez din me martaba ya nemi gani,yaci sa's kuma aikij kwana yayi,kuma baikai ga tafiya ba.


Maganganu sukayi dashi har na wajen mintun ashirin,kana daga bisani yabar asibitin.


Cikin 'yan rakiyarta hadimai ta shigo cikin asibitin,wanda tun kafin takai ga shiga dakin da azeez din ke kwance likitan ya nemi ganinta idan ta iso,bata jira ya isketa ba,ita ta iskeshi a office dinsa,don dama cike take da fargaba da taraddi kan bayanan da zataji kan sakamakon da gwaje gwajen azeez din.


"Ranki ya dade kamar dai yadda na taba gaya miki ne a baya,babu abinda ke shirin illatar masa da zuciya ta hanyar gagarumin hawan jini irin damuwa,damuwace a zuciyarsa wadda da alama ba tun yau ba yake fama da ita,wanda idan har ba'a dauki matakin yaye masa ko kawo masa qarshenta ba yaci gaba da kasancewa a halin da yake ciki nan da kowanne lokaci za'a iya rasashi,naso boye muku amma naga babu amfanin hakan,na riga dana shaidawa me martaba ma wannan bayanin,saboda haka inaga abinda yafi kawai shine,ayi qoqarin ganin an kauda masa da wannan damuwar,idan ba haka ba komai na iya faruwa"


Duk da acn dake karade office din,amma hakan bai hana gumi yankowa fulanin ba,ta kasa furta komai illa
"Na gode dr" daga haka ta miqe ta fice daga office din.


Duk wanda suka taho tare yasan cewa ta sake ficewa daga hayyacinta,dakin da azeez ke kwance ta tura ta shiga,idanunta a kanshi,saitaganshi kwance miqe kamar yadda ta barshi a jiya,babu wani alamun sauyi,kada dai ace tun jiyan ba wani ci gaba da aka samu?"tayiwa kanta wannan tambayar,sai taji hankalinta ya tashi,ta qarasa bakin gadon ta tsura mishi idanu,ramar da yayi ta bayyana muraran,saita dora hannunta saman sumarshi a hankali.


Karon farko taji wani abu mai kama da tausayi da nadama suna shigarta,abinda ta aikata din ya dinga dawo mata tiryan tiryan,ya akayi?,garin yaya ta fice haka a hayyancinta,idan hadin auren da rabasun da tayi tana sane kuma akwai.manufa daga baya hujjojin da suka dinga bayyana kansu meya hanata karbesu?,azeez ne fa,yaron daya fita daban cikin 'ya'yanta,mutumin da tun daga quruciya zuwa girma bata bashi umarni ya tsallake ba,baisan cewa a'ah ba kan dukkan wani umarni nata ba,komai tace masa yakan ce to,komai tsananinsa ko rashin dacewarsa da nasa ra'ayin,me yasa zata katase masa farinciki cikin rayuwarsa?,me yasa ba zataso abinda yakeso ba?.



Saita tuna da twince dinsa,idan itace aka rabata dashi da afnan yaya zataji a ranta?,ta tuna dukkan wata gwagwarmaya da tayi cikin masarautar kaisa,wanda dukkanta ta yita ne saboda kare yaranta,saboda ta rayu dasu,amma shi me yasa ta zama silar rabuwarsu tsahon shekaru,amma duk da haka bai fasa mata biyayya ba,bai taba fasa kallonta a matsayin uwa ba,bai fasa mata biyayya ba,tabbas ya cika da na halas wanda ya cancanci samun aljanna,indai hakane....indai yayi dukka komai saboda ita itama ya kamata tayi komai saboda shi,idan tace komai din ciki harda dawo masa da bilkisun dama yaranshi cikin rayuwarsa gaba daya ba tare da jinkiri ba.


Tana kaiwa qarshen tunanin ta sauke hannunta daga kanshi,sannan ta juya da hanzari ta doshi qofar fita,abdul'azeez da tun tsayin tsaiwarta saman kanshi yana jinta,saiya bude idonsa guda daya a hankali ya bita da kallo,yana jin qamshin nasara cikin ranshi.


Ta bude handle din qofar ta jata baya ta zura jikinta zata fita suka kusa gware,safwa ce a gaba cikin yanayi na rudewa,mahaifiyarta na biye da ita,sai mai aikinsu wadda babba ce biye dasu da kwanduna na alfarma riqe a hannunta.


Kallo daya zaka yima fulanin kasan qasaitar ta motsa,san fuskarta babu wannan annurin da yanayin da takan tarbesu dashi,a tsaitsaye daga nan bakin qofar sukayi magana da bata wuce biyu ba da mmn safwa tayi gaba,tana kiran sunayen hadimanta da zata fita dasu din.


Yau din tun safe da suka tashi bilkisu ta hada kan matan zuwa kitso da gyaran gashi,anty zuhriyya kuma ta dauki samarin don su rakata siyayya kasuwa,saboda shiryen shiryen daukan azumin watan ramadan da akeyi a sati me zuwa,hakan ya sanya gidan babu kowa sai mai gadi da kuma me aikin anty zuhriyyar.


Tafiyar mintuna talatin fulani aisha ta yima gidan anty zuhriyyar tsinke,tun daga bakin gate me gadi ya gaya mata cikin girmamawa basunan saboda ya shaida wacece ita,amma saita zabi zama ta jira dawowarsu koda awanni nawa zasuyi.


A farfajiyar gidan ta umarci dukka hadiman nata su zauna su jirata,yayin data shiga gidan ita kadai.


Mamaki sosai ya kama mai aikin anty zuhriyya ganin wacece baquwar tasu,don wancan karan da tazo ita taje ganin gida batasan da zuwan nata ba,fuskar fulani aishan ba boyayya bace musamman ga ma'abota kallon tv ko yawaita karatun jarida,kasancewar tana da qungiyoyin tallafawa gajiyayyu da marasa qarfi,hakanan tana yawan bada tallafi a duk wani sha'ani da xai taso cikin qasar kaisa,hakan yasanya mai aikin yi mata tarba me kyau bayan ta shaida mata basu nan,amma sun jima da fitama,sunce kuma ba zasu dade ba,tace babu damuwa,zata jirayi dawowarsu.


Wayar dake cikin kitchen ta dauka ta kira anty zuhriyya don shaida mata tayi baquwa
"Wacece?" Ta tambayeta,cikin zumudi ta shaida mata
"Matar me martaba ce wallahi ummi"
"Matar me martaba?" Ta ambata cikin mamaki,tare da tunanin meye kuma ya sake dawowa da ita
"Eh wallahi,harma ta zauna tana jiran dawowarku". Itama anty zuhriyyan sai abun ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,to meke tafe da ita?,koma meye batason haduwarsu da bilkisu,don hakan kamar zai sake tarwatsa duk wata 'yar yarda da nutsuwa dake zuciyar bilkisun,don haka tace
"Ohk,shikenan muna hanya" daga haka ta katse kiran,saita lalubi sabuwar lambar bilkisun kan wayar data sauya.


Bugu biyu ta daga,tambaya ta soma jefo mata
"Kina ina?" Bata kawo komai a ranta ta amsa.mata
"An gama mana ummi,yanxu muka fito daga wajen,mun hau titi ma" ajiyar zuciya ta sauke,babu yadda zatayi ta maidata,hala yau din ya zama dole ne su hadu shi yasa Allah ya shirya hakan,jin tayi shuru yasa bilkisun cewa
"Lafiya ummi?"
"Babu komai,saikun iso,nima ina hanya" ta kashe wayar ta mayar jaka,saita haqura da sauran abubuwan da bata siya din ba,aka zuba mata sauran siyayyar a mota itama ta dauki hanyar gida.


A qofar gida me adaidaita ya saukesu bilkisun suka shigo gidan da qafa,amatu na shiga da gudu tana biye da ita tana qwala mata kira tare da matan fadan gudun banza.


Daidai lokacin da fulanin ke zaune a falon,jin sabbin muryoyi ya sanyata zubawa qofar shigowar ido bayan ta miqe ta sake matsowa tana jiran ganin masu shigowar cikin qaguwa.


Amatu ce first,don haka tayi caraf ta dauketa,wanda yarinyar bata zaci haka ba,hakan yadan bata tsoro,data kalli fuskarta kuma saita tuna lokacin data taba zuwa gidan,tayi wajensu,anty zuhriyya ta hanata tabasu,hakan ya sake bata tsoro,saita saki wani dan guntun ihu tana zillewa daga hannunta.


Tunda ta shigo farfajiyar tayi arba dasu jikinta taji sam bai bata ba,tunaninta daya daga ina suke?su waye su?,dan ihun amatun ya sanyata zabura itada najwa zuwa cikin falon gidan cikin gudu gudu sauri sauri.


Dai dai lokacin da me aikin anty zuhriyya ke dariya tana cewa
"Meye haka biyu?,baki santa ba ko?,ai dafa gareta dama,uwarta tafi ganewa fiye da kowa".


Cak bilkisun ta tsaya ana kallon kallo tsakaninta da fulani,fulani na qare mata kallo zuciyarta na gaya mata tabbas itace bilkisun,don ta jima da haddace fuskarta a tarin tulin hotunan da aka dinga ruwansu cikin masarauta,yayin da bilkisu zuciyarta ke bugawa da wani irin sauri,idan har dai dai idanunta ke gane mata fulani aisha ce a gabanta,matar me martaba,mahaifiyar yarima azeez,matar da takan ci karo da hotunanta ko ganin fuskarta a akwatunan tv na qasar nan,mai tarin bada tallafi da taimako ga mabuqata,matar da take ga halinta ya saba da ayyukanta,matar da kullum taga ana yabonta mamaki kan cikata,taga zallar rashin sanin wacece ita yasa jama'a ke yabonta,matar data zama silar wanzuwar komai cikin rayuwarta.


Sallamar anty zuhriyya ta karade falon wanda itama ta fado ne da hanzarinta,a hankali ta waiwaya suka hada idanu da anty xuhriyyan,saita dauke kai a hankali ta soma takawa zuwa hanyar dakinta ba tare data furta wata kalma ba.


Babu wanda ya tsaidata cikinsu,hakanan ba wanda yace mata komai harta bacewa ganinsu,sai data bace din kana anty zuhriyya ta qaraso zuwa cikin falon,fuskarta a tamke,murya a kausashe ta soma magana
"Me kuma ya sake dawo dake cikin gidan n......"
"Sulhu,sulhu nake nema domin girman Allah da darajar manzonsa" tayi maganar cikin matuqar sanyi tana hade hannayenta biyu waje daya,domin a yanzun ta shirya yin komai don ta daidaita lamura,don ta wanke kanta,don kuma ta maida komai kan muhalli da mixaninsa
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 75
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070




Duka qarfinta ta tattare ta turashi kana ta tashi daga rungumar da yayi mata tana kyabe fuska da hade rai,dariya ya saka sosai har ya bata mamaki,ta saki baki kawai tana kallonshi
"Ai na zaci baki gama kallon nawa bane shi yasa na riqeki da kyau saboda ki kalleni yadda ranki keso" kunya tadan kamata,saita soma sauka daga gadon,sannan ta durfafi qofa.


Saidai ina,tun kafin ta qarasa ya rigata,ya tura qofar ya murza key din dake jiki,sannan ya harde hannayensa a qirji ya zuba mata idanu da tsumammun idanunsa,wadanda ciwon da sukayi ya sake sanyawa suka zama wasu irin masu saurin narkar da zukata
"Tunani kike madam zaki fita dakin nan ta sauqi?,inaa na daina wannan saken,tunda kika shigoshi saikin samu ladan aure,kin kuma warkar da zuciyar dake cike da shauqi da qauna...." Yana kaiwa aya ba zato ba tsammani taji an sunkuceta,ta soma qoqarin qwacewa tana cewa ya sauketa amma ina,sai daya direta bakin gado
"Karka sake tabani,kuma da nasan ma ka warke da ban zuwa wlh" da baya da baya ya koma gefan daya gadon dake kallon wanda take kai ya zauna idanunshi a kanta,sai daya zauna ya dage mata gira daya
"Kiyi duk boren da zaki na yarda,kome xakiyi kiyi am ready,amma.ina mai.tabbatar miki baki fita dakin nan sai zuciyata ta warke" idanu ta fiddo
"Me hakane?,kasan dai bani kadai nazo ba"
"Yes,kamar yanda nasan babu me tuhumata game da xamanki nan din,tunda dai matata ce ko?" Shuru kawai tayi,ta fuskanci kome xata fada bazaya yadda ba,amma duk abinsa idan sun tashi tafiya ai za'a nemeta,kuma dole ya barta ta fita.


Shima shurun saiya masa,ya zuba mata idanu yana qare mata kallo,gami da tuna abubuwa masu yawa a kanta,tun tana mitsitsiyarta shekara sha bakwai,duk da ba wani gani ya mata.mai yawa ba,amma har yanzu hotunan moments din nanan a qwaqwalwarsa.


Batasan idanunsa tamkar dafi suke a gareta ba sai da kallon da yake jifarta dashi ya soma hanata sukuni,duk inda ta motsa saita dinga jinta a takure,cikin kwarjininsa tana jin ya cika dakin gaba daya,don haka cikin jarumta ba tare data iya duban qwayar idanunsa ba tace
"Ban fiye son kallo bafa gaskiya"
"Sorry ma" ya fada yana sakin wani sihirtaccen murmushi,sai kawai ya zame ya kwanta a gadon daya koma din,yaci gaba da kallonta ta qasan idanuwa,wanda wannan takejinsa har cikin qashinta,kamar yafi na daxun dafi,don haka ta gyara zamanta,ta juyawa sashen da yake baya,amma duk da haka bata fasa jin tasirin kallon ba cikin jikinta.


Mintina kusan ashirin,kamar babu kowa cikin dakin,qarar wayarta ya karade dakin,ta budeta da sauri tana duba mai kiran,anty zuhriyya ce,saidai kafin takai ga dagawa taji ya amshe wayar,baki ta saki tana binsa da kallo har zuwa sanda ya ansa wayar
"Ku tafi kawai anty,tace zata zauna,tana jin kunyar gaya miki ne" abinda taji yana fada kenan,wanda ya sanyata zaburowa zata karbe wayar tana fadin
"Ba haka nace ba Allah ummi" wanda ta makara,don tuni ya kashe wayar.


Sai yayi tsam, yana jiran isowarta,wanda bata ankara ba sai sake tsintar kanta tayi a jikinsa,yasa hannayensa gaba daya ya rungumeta cikin jikin nasa yana shaqar daddadan qamshinta da tun daxu ya tafi dashi.


Cikin kunnenta yake rada mata
"Relax mana.....relax" hakanan taji dukka jikinta ya saki sanda sautin maganar ya shiga kunnenta,saita daina kici kici din da takeyi,a hankali cikin sanyi yaci gaba da magana
"Ba mutum ne ni maison tashin hankali ko fada ba,pls ki taimakeni mu fahimci juna,ki sassauta fushinki da hukuncinki har sai na warke,na miki alqawarin zan dauki duk wani hukunci kome girmansa,na miki alqawari bazan sake tabaki ba tunda bakiso,amma kimin alfarma kiyi.jiyyata,wala'alla daga nan bazan sake rayuwa ba" haka kawai taji jikinta yayi sanyi,bata sake cewa komai ba,hakanan shima bai qara riqetan ba ya saketa,ta koma mazauninta na daxun,saiya sake kunna wayarta dake hannunshi ya soma latsawa yana cewa
"Bari na sake yiwa anty bayani....tunda dazun kince bake kika ce ba" idanunta a kanshi take dubanshi tana mamakin baijin kunya zai iya magana da ita haka kai tsaye?,bata gama mamakin ba muryar anty zuhriyya ya fito ta cikin wayar,saiya miqe ya nufi bakin wondow yana amsa wayar,ta bi bayanshi da kallo,verry giant and gentle prince taji zuciyarta na fada,dukka kamanninsa da abdul sun fito sosai,sai yanzu ta lura hatta yatsun qafa ma iri daya ne.


Idanunta ta lumshe sanda ya waiwayo manne da wayar a kunnensa,saidai tuni ya ganta tana kallonshi,baice komai ba ya miqa mata wayar,wanda sai daya hada da hannunta kadan sannan ya sakar mata,cikin sauri da yadda tsigar jikinta ta tashi ta kara wayar a kunneta
"Karki damu,kiyi xamanki,lada xaki samu,pls daughter ki saki jikinki,abinda ya faru ya ruga ya faru,kuma a yanxun muna da yaqini da kuma kyautata zaton ya wuce" kasa amsa mata tayi saboda nauyi da kunya,har sai data kashe wayar da kanta.


Sau uku fulani na aikowa a dubasu amma qememe yana jin knocking yaqi budewa,itama batayi magana ba saidai ta daga kai ta kalleshi alamun tanason a bude din,amma saiya wani lumshe ido kamar baisan me ake ba,yana kwance abinshi saman daya gadon yana qare mata kallo son ranshi shauqinta da begenta gami da wata qqaqqarfar soyayyar da bai taba zaton akwai irinta ba tana ratsa kowacce gaba ta jikinsa.



Wajen shidda na yammaci fulanin ta tako da kanta tare da likitan da yake dubashin,wanda shima zuwanshi na biyu kenan amma qofar na garqame,hakan ya sanya fulanin zuwa da kanta.


Mamaki sosai ya kamata sanda ta ganshi ya bude qofar sannan ya koma,sai kawai itama ta maze kaman bata gani ba,yayin da kunya ya hana bilkis sukuni.


"Toh fa...inaga ya kamata ayi sallama hakanan ai ko?" Likitan ya fada qasa qasa,ta yadda azeez ne kawai zaijishi,gira ya yamutse shima cikin qas da murya yace
"Haba likita...yaushe aka fara bikon bare a gama,da mun koma gida mutane ne zasu damemu" dariya taso kama likitan hakanan ya danne don kada fulani taji.


A ranar abbaa shima yazo dubashi,tana ji tana gani ya taho mata da madaidaiciyar akwatinta dauke da kaya,ta bata fuska tana kyabe baki,wato ta lura da gaske mutanen nan dai suke,yarima dake daga kwance yana kallon duk abinda ke faruwa,sai hakan yayi masa dadi,yakanji duniyarsa tamkar ta daidaita ne,sabanin daa da yake jinta a hargitse.


Kwana biyu rak tayi amma gaba daya ya gama narka mata jiki da wata iriyar soyayyarshi ba tare data sani ba,duk wani alqawari da yayi na ya daina tabata ya dade da karyashi,idan ta buda baki zatayi qorafi saiya langabe mata yace aishi patient ne,koda tayi niyyar nesantarsa saiya janyo abinda zai kawo kasuwancinsu,kamar sanyata ta zauna ta bashi abinci a baki,wanke mishi hannu tayashi shaving uban suman daya tara da sauransu,kuma koda a gaban fulani ne baiji kunya,idan bilkisun ta soma masifeshi kuma saiya wani koma mata kalan tausayi,wani sa'ilin fulanu saidai ta dauke kai idan yana tabararshi da baiko jin kunya,kai bakace shine wannan sarkin miskilancin hada gira da uban kwarjini ba,idan kuma taga ba zata iya ba tabar musu dakin,dataga ma ciwon nashi kamar na shaqiyancine saita rage zuwa ta dade,yawanci tafi zuwa daga yammaci zuwa bayan magrib ta koma gida abinta,ita kanta bilkisun ta soma rasa gane ma'anar xamansu a asibitin,don dai itakam bataga wata cuta ba,banda tablet da yakesha,wanda ta tabbata ko a gida ya zauna zaya iya shan abunshi basai cikin cikin asibiti ba,amma haka taja baki tayi shuru,ta zubawa sarautar Allah idanu.


Tun randa ya amshi wayarta ya hanata ita,yace tayi haquri amma bai bata sai randa ya siya mata wadda yaga dama da hannunshi,haka ta haqura tasa aka laluba mata wasu litattafai a kasuwa da zasu qareta kan fannin data karanta na likitanci,ga anty zuhriyya daga ita har yaran tun ranar da sukazo tare babu wanda ya kuma dawowa.

¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶


Yau kam tunda ta tashi take cin magani,duk da dama bawai wani fara'arta yake samu ba,saidai yau taci alwashin babu abinda xata yarda yasa ta hada jikinta da nashi,don ta karanci wayo kawai yake mata.


Ita kadai tasan yanayin da take tsintsar kanta duk yayin da hakan ta faru,duk da cijewa da qaryata kanta da takeyi,sau tari saidai ta shiga bandaki tayita maida numfashi harsai bugun qirjinta ya daidaita,sannan wani lokaci ta daura alwala ta fito,abinda bata sani ba shine,ya jima da karantar yadda moode dinta kan canza a wasu lokutan,yakanci dariyarshi shi kadaine kawai ba tare daya nuna mata ba,amma yanajin dadi sosai har cikin ranshi na yadda salonshi ke aiki.


Duk wani abu da tasan zaya buqata ta aje mishi kusa dashi,ta gama shirinta tsaf wanda dama nan cikin toilet din dakin take sanyawa muqulli ta shirya,ta yane jikinta da mayafinta mahadin kayan,ta haye kan daya daga cikin cusion din dakin ta nade a kai taja littafinta guda daya tahau karatunta.


Ta qasan idanu yake qare mata kallo,yau tayi masa kyau sosai fiye da kullum,jajayen lips dinta sunata qyallin lipgloss,saiya lumshe idanunsa kana ya sake budesu a kanta,duk da batasan yana kallonta ba,ya gama karantarta tsaf,saidai a yau din zaiso ace cikin jikinsa ta wuni kacokam gaba daya,yana sheqar wannan daddadan qamshin nata da baya gajiya dashi
"Bilqess" yayi kiranta da wani irin sauti daya ratsa jikinta sosai,saita daga manyan idanunta a hankali ta zubesu cikin nashi tana lumshe ido gami da budesu lokaci guda,alamun ina jinka.


Lallausan murmushi daya sake bayyana kyanshi ya sake mata yana sake nutsa idanunsa cikin nata
"Uhmm....yau kuma rowar maganar ma akemin?" Ya fada da wani irin salo daya sanyata tilas ta janye idanunta ta maida kan takardar dake gabanta,saboda wani irin kwarjini da nauyi da taji sun mata,ba zata iya ci gaba da kallonshi ba
"Breakfast dina fa?" Ya tambayeta cikin wani taushi
"Na shirya maka komai ai,gasunan kusa dakai" ta fada cikin siririyar muryarta,ya jima yana kallonta,sai yaja break din ba tare daya sake ce mata komai ba ya soma ci,don ya fuskanci a tuburenta take,amma zaya sauko da kayarsa.


Wunin ranar haka ya dinga takale takalen sakata abubuwan da yasan dole zasu kawo kusancinsu,saidai gaba daya taqi wayon yauta daki karatun,duk sai yakejinsa sukuku babu dadi,baison kanshi tsaye ya isa gareta ne,da tuni aikin gama ya gama,yasani dole yabi komai mataki bayan mataki.


"Ki taimaka ki wankemin qafata,tayi datti" ya fada yana dan jujjuya qafar kamar gaske,a lokacin tana saman abun sallah,saita daga kai kawai ta dubi qafar da yake maganar tayi dattin,dariyace ma taso kamata,qafar dako qura babu alamunta tattare da ita amma ita ake kirawa datti,tasan cewa kawai neman abun magana ne,kuma ba zata biyeshi ba,don yau lafiyar Allah ta wuni,to haka zataso ta kwana,jin taqi kulashi sai yace
"Shikenan,idan ammi tazo ta wankemin"
"Yaron ammi kawai" ta fada qasa qasa,sarai yaji me tace amma sai yace
"Na'ammm,in taso ki wankemin ne?"
"Ni bance ba" ta fada da sauri,dariyarsa ya qumshe kawai yana jinjina kansa,batasan wayeshi ba da taki kiransa da wannan sunan,soyayyarta ta maidashi duk yadda take ganin nasa a yanzu.


Ranar kuwa

Please Login or Register in order to submit comment