Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakai kan qaramin bakinta dake dauke da pink lips,wani shock yaji wanda ya sanyashi yasoma tafiya da baya da baya,har sai daya dangana da muhallin daya soma tsaiwa farkon shigowarsa dakin yana ci gaba da kallon baby face dinta.


Cikin baccinta tasoma jin wani irin yanayi,yanayin da yayi mata kama da wani yanayi wanda ta taba shiga watanni biyu baya da suka shude,a firgice tabude idanunta sannan ta waresu gaba daya,duk da babu abinda take iya hange sai qaramin hasken da fitilar gefan gadon take iya bayarwa,wanda bai isa yasa taga komai ba,tattausan qamshinsa da hancinta ya sheqo ya aikawa qwaqwalwarta shi ya bata amsar tambayar dake zura gudu cikin kwanyarta,lokaci guda tayi wani mugun laushi,tashin hankali ya sauko mata wanda hakan ya sanya zuciyarta ta qara gudu kan gudunta na qa'ida,bata da sauran wani abunyi illa zubawa sarautar Allah idanu,tanajin lokacin bautarta ne yayi kamar yadda sauran bayi suke,abu na qarshe daya faru shine saukar zafafan hawaye daga kuncinta.


Ta cikin qaramin hasken take iya hango inuwar takunsa zuwa qofar dakin da niyyar ficewa bayan shudewar wasu mintuna,saita lumshe idanunsa sauran hawayen da suka cika mata idanu suka sake kwaranyowa karo na barkatai,wani irin tsanarsa taji tana ratsata karo na farko,ta wani gefe na zuciyarta taji xallar laifi mai girma akan mahaifinta,shi dinma karon farko a rayuwarta,taji zuciyarta tana jefa mishi tuhuma da zargi mai girma,abinda bata taba jin zuciyarta tayi masa ba duk da girman laifin daya ringa musu tun daga quruciya har girma sai a wannan karon.


Wannan karon da kanta ta tashi ta gyara kanta,ko mama sodangin bata bari ta sameta a wani hali ba,saidai wanda ya rigaka kwana dole saiya rigaka tashi,yanayin qunci da rashin walwalar data ga bilkisun a ciki ya fayyace mata komai,sannan ganin yariman a gidan ya qara mata haske,wanda kwana yayi a gidan kana ya qare wuninsa gaba daya a samanshi,bai bar gidan ba sai qarfe wajen shidda na yammaci.


Tunda yafita kamal ke ankare da yaushe xai dawo?,a wanne yanayi kuma zai shigo kamar yadda ya saba mishi,baiga shigowarsa ba sai yammaci,hakan ya qarfafa zarginsa a kansa,yakuma ci alwashin sake matsa masa lamba kozai karanto komai.


Tun daga ranar saiya zamana indai ya fahimci azeez din zai fita saiya qirqiri wani abun da zai sanya su fita tare,koda ba waje daya zasuje din ba kuwa,sam bai kawo komai cikin ranshi ba,illa iyaka ya dauka kamal din yasoma tattara hankalinshi kan abubuwa masu muhimmancin da suka kamata dashi.



Shudewar wata guda da sake faruwar lamarin tsakaninta dashi,a wani dare azeez din ya shirya kamar yadda yasaba lokaci zuwa lokaci don zuwa gidan yadauki abinda yake da buqata cikin gidan.


Falon yau kamal dinne kawai zaune,wanda dama yazauna ne kawai saboda azeez din
"Zaka dan ragemin hanya mana idan babu damuwa" sai daya waiwaya ya dubeshi sanda yake daukan muqullin motar daya arawa jabir,yadda yake yawan takurashi da rage hanya masa hanya abun yasoma ankarar dashi,harya soma shan jinin jikinsa azeez din ya janye qwayar idanunsa yana yin gaba,ya fidda ran xai amsashi sai yajishi yana cewa
"Taho mu tafi".


Duk yadda kamal din ke sanyo hirarrki azeez din bai tankashi ba,daya fuskanci yau 'yan wulaqancinne saman kanshi dole ya kama kanshi shima ya tsuke bakinsa,babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu,saima azeez din daya tura plate din waqa,wanda cikin sakanni yasoma tafiya.


Gefan titi yaga ya gangara kana yayi parking din motar ya waiwayo ya dubeshi sai kuma yadauke kai
"Iyakata nan,kana iya sauka" bashi da sauran abun cewa,duk da baiso sauka anna din ba,yaso ne yaga yau maqurar inda yake zuwa,amma gudun tonuwar asirinsa yasa yace
"Ohkey,ba case,thanks,saimun hadu a gida ko?" Kai kawai ya kada masa,ya tashi motar yayi gaba,yayin da kamal.yaci gaba dabin motar da kallo,yana fatan Allah yakawo taxi da zai samu damar binsa kafin ya bace masa.


Daga nesa yasoma hango tahowar wata taxi,cikin sauri ya sanya hannu yasoma tsaidata kamar ance mishi wucewa zaiyi bazai tsaya ba,a gabanshi ya tsaya,sai daya shiga sannan cikin nuna alamun yana hanzarine ya nuna mishi motar azeez data kusa qulewa,yace ita yakeso yabi,bayaso suyi missing,yayi mantuwar wasu abubuwa nashi masu muhimmanci a ciki,motar drivern ya tayar kana yasoma bin motar azeez cikin qwarewa,da alama tsohon driver ne.


Yana tuqinsa yana dan tunane tunanensa har ya shiga unguwar,a nutse yasamu waje ya aje motar,dai dai lokacin da kamal yayiwa drivern umarnin yasaukeshi nesa kadan da inda azeez ya tsaida tashi motar,ya zaro kudinsa bayan ya gaya mishi adadin kilomitres din ya biyashi sannan ya fito.


Cikin sanda yake bin jikin varender da bishiyoyin dake titin har ya isa wani gida dake kallon gidan da yaga azeez ya shiga,ya lafe sosai a bishiyar dake wajen gamida bada hankalinsa kan gidan yana nazartarshi,gami da xuba mishi ido,yana karantar yanayin gidan dakyau,tare da fatan samun wani abu da zai zama hujja a gareshi.


Ya jima tsaye a wajen,babu abinda bai saqa ba cikin ranshi,zargin da zuciyarshi tafi bashi shine,azeez din ya aje zuqa zuqan 'yammata ne yana hutawa dasu,shine yake boyewa bayason su sani,tabbas haka zatonshi yake babu shakka.


Fitowar azeez ta sanyashi sake lafewa,ta gabanshi yaja motarshi yafice,sai daya daina ganinsa sannan yafiti yana bin inda motar tawuce da kallo,kai.ua girgiza yana wani shu'umin murmushi,sa'annan ya maida dubanshi ga gidan.


Har ya nufi gidan gadan gadan kanshi tsaye,sai kuma ya dakata jin wayarshi na ringing,denial ne abokinsa,ya amsa kiran na wasu mintuna sannan ya maida wayar aljihunsa,ya sauya akalar tafiyar tashi yasoma neman taxi,hannu daya kuma yana laluben lambar wayar mom dinsa da niyyar shaida mata abinda yasamu gani.


Bugu biyu ya dauka,tamkar dama tana kusa da wayar ne
"Son,ya akayi"
"Mom,breaking news!"
"Me yafaru son?,mun cimma nasara ne?" Sai daya gyara zamanshi yana murmushi sannan yace
"Alamunta dai sun fara bayyana....kinsan me yake faruwa?" Kai ta gyada cikin qaguwa
"A'ah,yi sauri ka gayamin da Allah,banason wannan kauce kaucen".


Dukkan abinda yafaru ya gaya mata,wanda hakan yayi masifar faranta mata,harta kasa zama
"Na jiyo qamshin nasara,wulaqanci da tozarci suna gab da tabbata kan abdul'azeez da uwarsa,amma meya hanaka qarasa cikin gidan ka ganewa idanunka badalar da yake tafkawa?"
"Da zan shiga,so wani abokina yana jirana,zamuje wani waje,saina bari kawai nasoma shaida miki daga baya na koma" fada sosai tasoma yi masa
"Wanne irin shashancine wannan?,ko meye ake jiranka kayi yakai girman wannan ne?,wannan fa rayuwarka ce gaba daya akeso a gina maka ita"
Cikin nuna qaguwa da takura da fadan da take masa yace
"No mom,ba zaki gane bane,wajen da zamuje alqawari nayi,idan na saba kuma zasu dinga kallona as qaramin mutum....dole dole zanje,dole zan shiga gidan naga me yake aiwatarwa,ai kin sanni mom,meye na daga hankalinki kuma ha'an?"
"Is ok shikenan,amma duk rintsi karka wuce gobe"
"Relax mom,dole saina dai daici lokacin da nasan bazamu hadu ba,u know azeez very well,dole sai mun kula fa"ajiyar zuciya tasauke,wannan kafirin yaron tun kafin yakai wadan nan shekarun yake basu wahala
"Shikenan....saina jika" da haka sukayi sallama da juna,kamal ya aje wayar yana taune lips dinsa na qasa,saqa kawai yadda zai.kama abdul'azeez dumu dumu yakeyi,yana kuma qissima irin tonon silili nacin mutunci da zasuyi masa.
7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 31


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070



Wani irin yammacine mai cike da wani irin yanayi mai dadi,dai dai lokacin da sukan xauna karatu a gidan,yauma hakkane,tana zaune da littafi a gabanta tana budawa shafi bayan shafi tana dan nazari tana jiran rakiya data tafi duba girki tadawo su dora a karatunsu,yau mama sodangi bata nan,ta fita siyo musu fruits na gidan da suka qare,amma bawai nisa tayi ba,don basu da nisa da wajen da ake saidawa.


Wani lallausan yadine da akayi mishi dinkin doguwar riga da hijabinta,butter colour ne,haka yake zuwa readymade,kayan sun amsheta sosai,sun fidda kamarta qwarai,banda dan duhun fata da take da ita zaka tsammaci ba 'yar nijeria bace,uwa uba kuma yadda fatarta tayi kyau saboda cima me kyau dakuma zaman waje daya.


Dai dai sanda kamal ke tsaye qofar gidan,yana duban qofar gami da sakin murmushi yana kuma shafan gemunsa zuwa gefan fuskarsa,yana cikin farinciki mara misaltuwa idan yatuna ayau zai toni asirin azeez,mutumin da a rayuwa ya tsaya masa a wuya fiye da kowacce halitta,a hankali yadora hannunshi kan qararrrawar dake shaidawa masu gidan cewa suna da baqo ya dannata.


Doorbell ce tayi qara har sau biyu kusan a jere,hakan yasanya bilkisu daga kai ta dubi bakin qofar,saita dubi kitchen inda rakiya ke ciki,tasan babu lallai taji,kuma wala'alla mama sodangi ce,ta tsaya kiran rakiyar kamar bata lokacine,tunda maman tana da dan ciwo qafa lokaci zuwa lokaci,kuma a kwanakin yadan tasar mata,saboda haka rufe littafin ta miqe da sauri ta doshi qofar.


Murmushine akan fuskarta sanda tabude qofar,tashin farko idanuwansu ya hadu da kamal dake tsaye,murmushin fuskar tata saiya gushe ganin baquwar fuska,tana masa duban rashin sani,yayin dashi kuma hakan yabashi damar qare mata kallo tun daga sama har qasa.


"Wow....wow" yasamu bakinsa da furtawa ba tare daya shiryawa fadan hakan ba,ya dora da fadi a zuciyarsa
"Shege azeez...komai nashi na dabanne?why?"ba qaramin razana yayi ba da ganin bilkisun,baiyi zaton ganin halitta irin wannan ba mai kyau quruciya dakuma kwarjini a wannan muhallin ba.


Sakin qofar tayi ta juya zata koma ciki,ganin ta tambayeshi har sau biyu bai amsa mata ba,sai wani kallo da yake binta dashi,abinda ta tsana a rayuwarta kenan mugun kallo irin wannan,uwa uba ma sai taji sam bai kwanta mata ba
"Hey babe" ya fada da sauri,saita tsaya gamida waiwayowa tana dubanshi,fuskarta a gintse,sai yaga hakan yayi masifar qara mata kyau
"Sorry baby...baki sanni ba ko?,muje ciki zan miki bayani,i think yarima bai miki bayani na ba" wani muguwar faduwar gaba taji ta saukar mata,tashin farko bayan rashin kwanta matan da taji bai mata ba sai taji tsanar data yiwa wannan mai suna yariman tana shafarsa,bata ce masa ci kanka ba taci gaba da tafiya,ya take mata baya yana ci gaba da qare mata kallo,gamida lashe lips kamar tsohon maye,ba shakka bayan komai ya kammalu saiya tabbatar da cewa ya mallaki wannan babyn.


Inda tatashi takoma tazauna,tasake jan littafinta tana ci gaba da dubawa,yayin da shi kuma yasamu saman kujera yazauna idanunsa a kanta
"Dole azeez dole,ashe babbar harka ya samu irin wannan ya aje yana hutawa?,a ina yasamo wannan halittar?,a hakan ma ba'a ganin komai sai fuska da hannaye?,inaga anga sauran?" Saiya sake lashe labba gamida hadiye yawu muqut.


Ya bude baki zaiyi magana rakiya tafito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa tazube tana gaidashi,don tasan wayeshi,ya amsa mata yana mamakin me kuma ya kawota gidan ita?,me takeyi?,yaushe tazo qasar?,duk da baisan fuskarta sosai ba amma ya tabbata daga masarautar kaisa take,zai dan iya shaidata.


Bai gama wannan mamakin ba aka sake taba qofar,rakiya ce tamiqe da hanzari taje ta bude,mama sodangi ce dauke da ledojin siyayya,rakiyan ta amsa kana ta matsa mata don tasamu damar shigowa.


Da mamaki suke kallon juna ita da kamal,saboda duk sunsan juna farin sani,saidai ita maman ta boye mamakinta qwarai,saita maye gurbin fuskarta da murmushi gamida miqa mishi gaisuwar barka da zuwa,ta sanya rakiya ta cika mishi gabansa da drinks da kuma fruits din data shigo dasu.


Duka sai hankalinsa ya kasu kashi kashi,ya gaza fahimtar komai,ga sodangi da rakiya daga masarautar kaisa,ga kuma wata baquwar fuska da baisan wacece ba,sannan alamu sun nuna dukka suna zaune ne a gidan,bakuma zuwan shekaran jiya jiya ko yau bane bisa dukkan alamu,to amma me azeez keyi a gidan?.


Kusan mintuna talatin ya kwashe a gidan yana karantar komai da idanunsa,yana kuma sauraren karatun su bilkisu,yayin da mama sodangi taketa takatsantsan,don tayi yaqinin wannan zuwan da yayi babu masaniyar fulani aisha ko kuma yarima,tunda kusan tana daga cikjn mutane na gaba gaba da suka san dukkan abinda yake wakana,hankalinta bai kwanta ba har sai daya miqe da zummar tafiya,idanunsa akan bikisu wadda bata sake daga kai ta kalleshi ba tun kallon farko har zuwa sanda yafice daga gidan.


Ajiyar zuciya mama sodangi tasaki,tana ankare da irin kallon da yake jifan bilkisu dashi,wanda sam bata gamsu dashi ba,tana ganin babu wata mafita datayi saura face ta shaidawa fulani zuwan kamal din,don koma meye a dauki.mataki,uwa uba kuma batason wani mummunan abu dazai shafi bilkisu ya bullo.


Zaman dirshan a ranar kamal yayi yana dakon dawowar azeez din,saidai kuma ya daki gurbi,don daga makaranta ranar saiya wuce gidansu mama sodangi,can dinma bai shiga da wuri ba,ya tsaya a makaranta duba wasu karatuttuka,abinda yasa ya gagara kenan kaf cikin makarantar,sunansa yakuma tumbutsa,hakanan farinjinsa ya kere na kowanne matashi dake ji da samartaka,tako ina azeez din ba baya bane,baya ga baiwar kyau aji izza da miskilanci da yake dashi,sai baiwar qwaqwalwa,wanda nacinsa da yawan maida hankalinsa kan karatun ya maidashi haka,sau da dama yakanyi mamaki idan akace wane daqiqi ne ko kuma baya ja,saboda a iyakacin saninsa yasan Allah bazai tana halittar dan adam daqiqi ba,saidai ace kaifin ganewarka tafi ta wane,hakanan dabi'ar karatu tanason mutum mai maci da jajircewa,shi kuma haka yake,baya wasa da dukkan wani abu da yasan mai muhimmanci ne,hakanan duk abinda ya sanya a gaba saiya kaishi.


Yana tsaka da hutawa bayan yayi ɗai ɗai saman tattausan gadonshi yana amsa wayar safwa kiran amminsa yashigo a daya wayar tasa,daga can bangaren tana tsaye ne cikin qawataccen falonta,duk da tarin kujerun da aka qawata falon dashi amma ta kasa zama,jira take kawai ya daga kiran nata
"Barka da warhaka ammi"
"Abdul'azeez,kana cikin hankalinka kuwa?" Yanayin yadda tayi maganar ya tabbatar masa lallai babu lafiya,kawai abinda ke faruwa,don haka saiya zauna sosai saman gadon fuskarshi na nuna alhini da mamaki,ko kadan baya qaunar abinda zai tashi hankalinta,har abada ammin ta musammance a wajensa,sama take da duk wata mace dake duniya,ya janyo daya wayar da yake amsa kiran safwa dashi,wanda daa yace karta katse kiran bari ya amsa wayar ammi,yayi qasa qasa da murya yace mata
"I wil cal u back,bani wasu mintuna" ba tare da ya jira amsarta ba ya katse kiran ya tattara hankalinsa kan ammi
"Nace kana cikin hankalinka kuwa?"
"Ammi....me hake faruwa?"
"Ta yaya zaka bari har kamal!....kamal yasan muhallinku,yakuma sako qafafunsa har gidan yashigo?" Boyayyar ajiyar zuciya yasauke yadda ba zata jishi ba,ya zaci wata gagarumar matsala ce,shi a wajenshi sam wannan ba wata damuwa bace mai girma
"Ammi meye a ciki?" Cikin muryar dake nuna maganarshi ta sake tunzurata tace
"Au,meye ma a ciki?,bayan kafi kowa sanin abinda yake gudana?,kasan nasan halin uwar kamal sarai....hakanan kaima kasan halin kamal din,kanason komai ya tarwatse ya lalace a lokcin da bamu shiryawa hakan ba kenan?" Idanunsa ya lumshe yakuma budesu lokaci guda,ha fuskanci me take tsoro,kada su karanci wani abu,har suje su shaidawa mai martaba
"Relax ammi....cool down please...,a sanda yazo bana nan,kuma ko ina nan na tabbatar bazai fuskanci komai ba,tunda ba'a rubuce yake a goshi ba,kin manta?" Shuru yadan ratsa tsakani,hakan yana nuna maganarsa tadan saka mata nutsuwa,jin hakan yasa ya dora
"Amma duk da haka,i wil take a seriouse action,bazan kuma bari qafarsa tazo gidan ba,kin gamsu da hakan?" Kai ta girgiza kamar tana gabanshi
"Hankalina ya tashi azeez,i know fauziyya na daya daga cikin mutanen da basu qaunata,basu qaunar su bude ido su ganni nida abinda na haifa,bare ace har nakai wani mataki ni ko su....hankalina yadan kwanta amma kadan,inajin kawai zan canza muku wani gidan ne" duk sai yaji hukuncin bai masa ba,sai passing passing ake dashi duk don aci gaba da boyeta,cikin son yardar da ita yace
"Believe me ammi,babu wani abu dazai faru,babu abinda kamal.ya isa yayi,beside ma duka duka baifi saura watanni uku komai ya qare ba,kin manta?" Da qyar da dabara yasamu yasha kanta,bayan tayita zabga mishi warning din ya kula yakumayi taka tsantsan.


Ta bangaren kamal kuwa bayan ya gama xaman jiran nashi,har zuwa wajen biyu na dare yaji shuru,saiya miqe yana tsaki yanufi dakinsa,gefan gadonsa yazauna yaciro wayarsa yana yunqurin kiran mom,don baiyi maganar da ita ba,ya kuma tabbatar tana can tana jiransa,daya kintata lokaci yasan a lokacin bazai wuce tara na safe ba nigeria.


Ringing daya kacal tayi ya daya,tamkar dama tana zaman jiran kiran nashine
"Ya ake ciki?" Kansa ya shafa yana qiyasta inama ace xai bata labarin ya kama azeez dinne cikin qazantaccen yanayi
"Naje mom....saidai kusan basu samu wani abuba,hakanan banga wani abu baqo ba,sai baquwar fuskar yarinya guda daya dana gani" cikin son lallai sai sun kamashi da laifi tace
"Kaman yaya?,ita baquwar fuskan itace dadiron nashi duk da ban gani ba" goshinsa yahau murzawa yana tuna zazzaqar muryar bilkisu sanda take karantawa rakiya iziyya,wadda saura qiris su sauketa,da yadda kyakkyawar fuskarta ke hade tsaf
"Bana tunanin haka mom,don karatun qur'ani natarar sunayi" shuru hajja fauziyya tayi,fadin hakan da yayi ya warware mata dukkan tunaninta,saita koma ta zauna tana sakin ajiyar zuciya
"Sauran dake cikin gidan su waye da waye"
"Daga masarautar kaisa suke,babbar mace da yarinya,kamar naji yarinyar ana kiranta da rakiya,babbar mace kamar..." Sai yadanyi jim yanason tuna sunan,daga bisani yace
"Sodangi".


Shuru tayi tan gyada kai,sannan daga bisani tace
"Dakyau hakanma,zansa amin bincike cikin masarautar kan su waye,meye kuma dalilin barinsu masarautar kaisa zuwa mexico" daga haka ya katse kiran,bai damu ba ya cilla wayae gefansa yana shafa kanshi da hannu daya,bilkisu na mishi yawo cikin idanunshi,saiya saki murmushi a hankali yana mamakin yadda yakeso ya jarabtu da ita cikin qanqanin lokaci haka.


Misalin hudu da arba'in ne na yamma agogon nigeria,tara da arba'in na safe agogon mexico sanda ya shiga gidan,kusan a gaggauce yake sauri yake ya debi wasu takaddu nashi zai wuce makaranta,don qarfe goma yana da lacture.


Dai dai lokacin da kamal yake zaune a falon gidan yana kallon news,hannunsa daya kuma yana kurban ruwan baqin tea.


Bin azeez yayi da kallo sanda yake sallama a gaggauce yana shigowa falon,saiya aje cup din hannunshi murmushi yana subucewa fuskarshi,yana ganin ya kamata yace wani abu,ya kamata azeez din yasan yaje gidan,ya kuma kamata yaji wani abu ko yasan wani abu komai qanqantarshi akan yarinyar,don haka yamiqe bayan ya bada tazarar mintuna uku da shigar azeez dakin nasa ya rufa mishi baya.


Da mamaki ya waiwayo sanda yaji an turo qofar dakin ba tare da sallama ba ana kuma shigowa,saboda kusan kowa ya sani,dokarshi ce,bai yadda da shigar mishi daki haka sakaka ba kai tsaye ba tare da neman izininsa ba,hakanan shima bai shiga dakin kowa cikinsu,idan ma ya shiga din to tabbas lalura ce ta kaishi ko ta kama yashiga din.


Ganin kamal ne ya sanyashi ci gaba da gyara takardun dake saman mirrow dinsa,dama koda bai shigo ba shi zai sameshi ya masa warning,don yadan fuskanci tamkar bibiyarsa yakeson ya dinga yi,wanda shi bazai lamunci hakan ba.


Cikin muryarsa da saman fuskarsa dukka zaka fahimci akwai nishadi da walwala a ciki,ya qaraso cikin dakin sosai yana dan qarewa dakin kallo a fakaice
"Shegen....komai nashi saiya banbanta dana kowa,kamar yana zabawa kanshi rayuwarshi" yayi maganar can qasan ranshi,amma a fili saiya tattaro dukkan juriya da dakiyarsa yace
"Hey man" banza yayi dashi kamar baiji ba,har sai daya gama abinda yakeyi ya riqe takardun sosai sannan ya juyo yana dubanshi,idanunsa ya sanya sosai cikin na kamal din,yana masa wani kallo dake qara fidda kwarjininsa,tsahon wasu sakanni,shima kallon nashi kamal yake,duk da yadda kwarjininsa keson dakusar da duk qoqari da yunqurin masa magana da yakeson yi.
7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 32

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________



"Nakai maka ziyara a gidan ajjiyr baqinka na musamman,duk da ban shaida maka ba,but....amma naso nayi suprising dinka ne,tunda na fuskanci akwai abinda ake boye mana,kuma da naje din sai naga hakane,ashe akwai abun boyewar...." Ya qarasa fada yana daga gira irin na 'yan duniya,yana fidda murmushi.


Azeez na tsaye yana dubanshi harya gama,saiya soma takawa kamar xai fice,saidai ba fitar zaiyi ba,zai rage nisan dake tsakaninsa da kamal ne,har sai daya zo dab dashi sannan ya tsaya yana dubanshi.


Cikin muryarshin nan mai cike da izza mulki da kuma qasaita,wadda a wannan karon ta cika da gargadi da jan kunne yace da kamal
"U break my rules....kamal,nasha gaya maka...ka daina yunqurin shigomin daki ba tare da sallama ko neman izini na ba,secondly kuma....iam warning you,ka fita daga sha'anin rayuwata,abinda kaketa yunqurin shiga bazai maka da kyau ba,wannan itace shawarata" saiya ci gaba da takawa,harya wuceshi kamal na binsa da kallo,har yanzu baiji komai game da yarinyar ba don haka yace
"Idan banda akwai abinda kake boyewa meya hanaka ci gaba da zama damu ummm?....and ita din wacece ita?" Shuru ne ya ratsa dakin,azeez ya dakata daga tafiyar da yake,yana jefa masa tambayar bilkisu ta dawo masa tarwai a kwanyarsa,yana magana ne a kanta ko kuwa?.


Sake takowa kamal din yayi zuwa bayan azeez,sannan yasake cewa
"Ita kadai nakeson sanin wacece ita,coz she attract me,na kuma ji ina da interest a kanta,so pls ko zaka hadani da ita" karon farko yaji wani mugun bugun zuciya,wanda tsahon rayuwarshi bazai iya tuna when last da yaji haka ba,saiya juyo sosai yana jifan kamal da wani irin kallo,take yasha jinin jikinsa,yana jin yana masa kallon ne da fassara ta daban,don haka ya gyara tsaiwarshi
"Am seriouse man....sonta nake da gaske,ba irin soyayyar da kake min fassararta ba...." Dakatar dashi yayi ta hanyar nuna masa qofa da hannu,sannan ya motsa labbansa a hankali
"Get out pls...zan kulle dakina" fuskar kamal din akwai damuwa sosai,amma yasan halin azeez din,dama kadan daga aikinshi ne,don haka ya daga kafadunshi sannan yasoma takawa yafice daga dakin.


A zafafe ya rufe dakin,kana yazo yawuce kamal din dake tsaye a falo,ya tada motarsa cikin zafi kana yafice a layin.


Har saman fuskarshi yake jin zafin,yadinga shafa sumarshi zuwa sajensa yanason lalubo meya zafafa kanshi haka da yawa bayan yayi 'yar tafiya,iskar sassanyan bishiyun dake jere gefan titin sun bugeshi,fresh air ce mai kyau ta tatattciyar safiya,daga baya abinda yayi realising kawai shine,yana da kishi qwarai,ta yaya kamal zai nemi yayi tarayya dashi kan wani abu dashi ya taba tarayya dashi?,bawai don ya damu da wanzuwarta ko wani abu bane,a'ah,kawai.har zuwa yanzu tana qarqashin ikonshi ne,idan da bayan nan ne bashi da matsala dashi,sai daya qaraci yawonsa ya tabbatar duk wata temper tashi game da kamal ta sauka sannan ya shiga aji,a sannan malamin harya kammala yafice,sai saura ya taras.


****************

"Auta" fulani adama ta kira sunanta cikin izza tana mata wani duba dake nuna koma meye zata fada mai matuqar muhimmanci ne,tun kafin ma tayi magana yanayin wajen da suka kebance kadai ya isa ya gayawa auta cewa ba qaramar magana zasuyi ba. A ladabce ta masa mata
"Ranki shi dade,Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment