Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana aikinta,rabin hankalinsa na kanta,yayin da wani rabin hankalin nashin ya tafi wani tunani na daban.


Shuru sashen nashi yake babu motsin kowa,don tun kwanaki ukun da suka gabata ya sanya sunusi ya sallami dukkan hadimai da barorinshi,saboda baya buqatar kowa bare a dameshi,dukka ammin tasan da wannan amma tayi biris dashi,labarin abinda ya aikata din yazo mata,abu daya take tsoro gami da fargaba,sannan kuma bata da amsar hakan,me azeez yake nufi?,meye nufinsa na damuwa da yarinyar?,me yasa take ganin wasu alamu da take take nason soma kaucewa umarninta?,tambayoyin da takan kwashe lokutta tana yiwa kanta,saidai bata da amsar ko guda daya,tabbas matuqar ya zamanto cewa ra'ayin azeez ya soma sauyawa babu shakka akwai gagarumar matsala da take hasashen zata iya afkuwa,bata fata da ko burin abinda aka shiryashi na wani taqaitaccen zamani ya zama tarnaqi ga rayuwarta,ko ya lalata dukkan wani shiri data dauki tsahon lokaci tana yiwa rayuwarsu.


Gyara kwanciyarsa yayi,ya soma gajiya da kwanciyar,ya lumshe idanunsa yana sake matsawa qwaqwalwarsa zuwa ga tunanin mafita.


Kamar wanda aka tsikara ya bude dukkan idanunsa da sauri,sannan ya miqe a sukwane ya zauna sosai saman kujerar,a sarari cikin daga murya yace
"Yes!" Saiya soma lalubar wayarshi wadda tun kwana uku take a kashe ya kunnata,babu jimawa ta daidaita,saqonnin safwa ne suka fara shigo masa iri daban daban,saina abdulrashid jabir da sauran makusantanshi.


Duka baibi ta kansu ba,ya soma lalubar lambar sunusi,bugu daya tak ya daga,cikin girmamawa ya soma miqa masa gaisuwa,bai amsa ba ya gaya mishi saqon da ya sanya yayi kiranshi
"Kana ta ina?"
"Ranka ya dade,ina can bakin sassa kamar yadda ka umarta"
"Ka qaraso ciki,inason ganinka" daga haka ya katse kiran,sa'annan ya miqe ya soma barin wajen.


Bedroom dinshi ya tura ya shiga,ya qawataccen toilet dinsa,ruwan wanka ya hada mai dumi sosai yayi wanka,kana ya fito ya shirya kansa cikin wasu qawatattun kaya dake nuna ainihin wayeshi,sun matuqar karbarshi da kuma dacewa dashi,ya gyara sumarshi da kyau ya sanya hula data sake qawata adon nashi,sannan ya feshe jikinsa da turare baya ga na jiki daya sanya kamar yadda ya saba,ya zura takalmansa da suke mahadi da kayan,sannan ya duba agogo,zuwa yanzun yasan sunusi ya jima yana jiransa,don haka ya fito.kai tsaye zuwa falon da sukan zauna su jirayeshi a duk lokacin daya buqaci ganinsu.


Kamar yadda ya zata din kuwa ya sameshi xaune saman kilishi yana jiransa,yana daga tsaye yayi magana dashi
"Ka nemo min sodangin,ka shaida mata ina buqatar yin magana da ita cikin sirri,sannan kuma a gaggauce"
"An gama ranka ya dade" ya fada yana ficewa da hanzari,kamar yadda ya fuskanci buqatar ganawar tasu ta musamman ce,hakanan ya samu kanshi da kasa zama,burinsa kawai sodangi ta iso,ya tabbata komai zaizo cikin sauqi,yana da yaqinin a yau zata kaishi gidansu,zaije ya ganta,sannan ya tabbatar da gaskiyar wanzuwar jininsa tattare da ita ko akasin hakan.


Tana daga tsaye a katafaren kitchen na alfarma da ake amfani dashi wajen samar da abincin sassan fulani aisha,dukkan wani abinci da fulanin xata ci kusan yana qarqashin kulawar sodangi ne,daya daga cikin manyan amintattun ta ,wadanda takanyi amfani da shawarwarinsu,musamman idan suka dace kuma sukayi dai dai da ra'ayinta.


Dudduba yadda ake gudanar da girkin take cikin nutsuwar nan tata da kamalarta,daidai lokacin data gama duba tattasan da aka gama markadawa,kubra ta qaraso bayanta,cikin girmamawa murya qasa qasa
"Shugaba yarima yayi aike,ya aiko sunusi,yana da buqatar ganawa dake yanzu" shuru ta danyi tana tunani,don kusan tun dawowarsu daga mexico fulani ta karbi fiye da rabin aikinta a sashensa ta dora wasu,batasan me yasa ba,amma tana tunanin hakan bai rasa nasaba da tarayyarsu da bilkisu,tanason sai tafiya ta sake nisa komai ya daidaita kafin lamuranta gaba daya su koma can,don kada ya zamana suna yawan ambarta ta kasa bacewa daga bakunansu,tana hasashe dukka dalilinta baya wuce wannan.


Ba tare da dogon nazari ba tace
"Muje" saboda jikinta ya gama bata cewa tabbas akwai abinda ke faruwa,cikin kwanakin taga yariman ya kusa sau uku,kallon farko tasan akwai abunda yake damunshi,a matsayinta na wadda ta sanshi tun daga yarinta zuwa girma.


Kamar yadda ta xata kuwa daga fallon farko ta fuskanci matsala da damuwa kwance saman fuskarshi,falon ya dauki shuru bayan fitar kowa,ya zamana daga ita saishi,cikin nuna kulawa da tausasawa tace
"Allah ya taimaki yarima,ko meye yake faruwa zanso najishi daga bakinka,dom ns tabbatar akwai alamun matsala da damuwa tattare dakai".


Dukkan abinda bata sani ba ya gaya mata,bai boye mata komai ba,da buqatarsa nayin tattaki da kansa zuwa gidansu bilkisun don tabbatar da gaskiyar lamarin.


Idanunta na kallon qasan carfet din,saidai sun cika fal da hawaye,tausayin bilkisu matsananci yana ratsata,inama ace tasan gidansu bilkisu,inama ace tasan inda zata ganta,lallai ba shakka koda zuwanta ko kai yarima zai zama sanadin qarshen zamanta a masarautar kaisa da sai taje,tana hasashe da tunanin yadda rayuwa zata kayawa yarinyar,rayuwar da zatayi dauke da cikin da bata da iko isa ko qwarin gwiwar nuna ubanshi,zata raini ciki cikin al'ummar da basusan da zama ko labarin ta taba aure ba,me zasu kalli cikin,shege kenan fa?,tanaji a jikinta zancan cikin gaskiya ne,tunda ita din kusa shaida ce na dukka abinda ya faru,meya sanya fulani ya ta sauya haka?meya qeqasar da zuciyarta ta zama wata iri bayan ba haka dukka suka santa ba?.


Yatsunsa tasa ta dauke hawayen da suka gaza boyuwa sannan tace
"Iyakar zamana na jima banga yarinya kamar bilkisu ba,yarinyar dake da dattako da kyawawan halaye da sukafi shekarunta yawa,shekara sha shida amma zaka tsammaci ta mallaki shekaru É—ai É—ai har gda arba'in ne,quruciyarta me kyau ce da burgewa duk da rashin gata da wanda zai damu da ratuwarta,inaji a jikina zancan cikinta gaskiya ne,ba shakka tana da ciki,saidai.....ina neman afuwarka....ina kuma mejin dadin shaida maka cewa....bansan koda hanyar gidansu ba,mun rabu tun a airphort da ita,bansan ya akayi ta isa gida ba,ladingo da luba su sukasan ainihin gidansu,saidai suma na jima da daina ganin gilmawarsu cikin masarautar nan".


Idanunsa kawai ya rufe tsahon wasu mintuna ya gaza budesu,haka nan itama shuru tayi tana taya bilkisu jin ciwo,saboda tasan cewa Allah ne kadai yasan ciwon da a yanzun yarinyar takeji a ranta.


Izini aka nema na shigowa,bai iya bada amsa ba sai sodangi ce ta bada,saboda ta fuskanci dan aiken daga sassan me martaba yake
"Mai martaba yana son ganinka,yayo aike daga sassansa" sodangi ta shaidawa azeez,sai a sannan ya bude idanunsa da suka sauya kala,haka kawai yaji aiken ya sanya gabanshi faduwa,abinda ba kasafai hakan ke faruwa gareshi ba,ya motsa labbansa da qyar yana amsawa,sannan ya miqe yana sallamar sodangi yasake shige ciki.


Ya jima zaune yana qoqarin controlling kansa don ya samu zuwa kiran me martaba,baya son yaje masa a wani yanayi na daban wanda zaibar ayar tambaya a zuciyar maimartabar.


Tsahon wani lokaci sannan ya samu rage kaso hamsin na mode din da yake ciki sannan ya fito,ya samu wasu daga cikin barorinsa acan qofar waje,sunso masa rakiya kamar yadda aka saba amma ga dakatar dasu,shi kadai ya durfafi sassan mai martaban.
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 45
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070
__________________________
*_kina da burin koyon sana'a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*

*_kin jima kina sha'awar yadda yake hada BIRTHDAY CAKE DA DECORATION amma kin rasa wajen da zaki koya?,ko FARASHIN YA MIKI TSADA?_*

*TOFA MATA!*

*_Ga dama ta samu_*

*_UMMU AYMAAN KITCHEN ta shirya tsaf don koya muku yadda ake hada gangariyar BIRTHDAY CAKE wanda ya gama hada dukkan gamayyar kayan dadi masu sanya harshe su motsa,gefe guda kuma ta koya miki yadda zaki qawata waje da walwali da kuma walainiyar KAYAN ADO DA QAWA na wajen gudanar da SHAGALIN BIKI SUNA TARON BIRTHDAY WEDDING ANNIVERSARY da sauransu_*

*_ba'a nan UMMU AYMAAN KITCHEN YA TSAYA BA,tana da ajujuwa na musamman don koyar da mata nau'in girke girke MAIDA TSOHUWA YARINYA,hakanan tana karbar kwangilar abincin taro kowanne iri_*

*_ta fannin kayan maqulashe na fulawa ta samar da abubuwa kamar haka_*
Cake perfait
Cup cake
Samosa
Springrolls
Meatpie
Doughtnout

*SIYAN DAYA KO SARI*

*_za'a koyar dake BAKING AND DECORATION QIRI DA MUZU ta sigar zancan nan da hausawa kance GANI YA KORI JI,gani ga malama_*
*_sa'an nan kuma akwai tanadi na musamman ga masu sha'awar koya ta hanyar yanar gizo wato ONLINE,duka kan farashi mai rangwame_*

*_ZA'A IYA SAMUNTA A UNGUWA UKU,LAYIN MAI FATA ZARIA ROAD*

KO A TUNTUBETA A WANNAN LAMBAR WAYAR
08032964266

*_ZA'A GUDANAR DA KOYARWA NE ON 5&6,GARZAYA MAZA KI REGISTER*ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸ðŸƒðŸ¾â€â™€ï¸





Sashe ne da kusan yafi kowanne sashe dake cikin gidan tsaro kyau tsaruwa da kuma yawan ma'aikata,hakan ya sanya tun kafin ya tunkari qofa barori dake kai kawo kowanne ke qoqarin aika gaisuwarshi cikin kirari da nuna qauna da kuma girmamawa,saidai a duk sanda sukayi kirarin sai ya dinga jinsa cikin kwanyarsa,tamkar suna gaya masa cewa sarauta zata zama kota zama sanadiyyar rushewa duk wani tsari na karan kanshi da rushewar rayuwarshi,don haka ya soma daga musu hannu yana dakatar dasu,da haka har ya isa ga me martaba.


Kayan jikinsa kawai zasu nuna maka bai jima da barin xaman fada ba,kaya ne nashan iska,saidai fuskarshi da wani sassan na jikinsa akwai sauran damshin ruwa dake nuna wanka yayi bayan shigowarsa,fulani suratu na zaune daga gabanshi tana bare mishi ayaba,bayan kofi data miqa masa wanda ta cika mishi shi da sassanyar lemo.


A fakaice ta yiwa azeez din wani kallo kana ta dauke.kanta tana ci gaba da yin abinda take,ta tsani ya dinga kiran yaron haka a lokacin kebewa irin wannan,lokacin da take gani su kadai ya cancanta su kasance tare dashi.


A qasan shima ya zauna,kansa a qasa cikin girmamawa ya gaida mai.martaba,ya amsa mishi cikin kulawa,fuskarsa dauke da fara'a,ya waiwaya ya dubi fulani saratu
"Barka da warhaka mama" ya gaidata itama,murya can ciki,cikin dakiya da kuma shariya ta amsa
"Barka kadai" duka mai martaba yana ankare,saiya murmusa kawai cikin ranshi,shi yana mamakin kishin qarfin hali irin na mata,a iya saninsa da abdul'azeez bai taba wani abu da zai nuna raini garesu ba,kowacce yana bata girmanta bakin gwargwado,shidai kawai barshi da miskilancinsa,qarancin fara'a da rashin son yawan magana.


"Ranki ya dade....ki aramin wasu lokuta daga lokutanki mana" mai.martaba ya fada cikin fara'a,ta watsa mishi idanunta,duk da taso yin qorafi amma yanayin yadda yayi maganar dole ta sallama,saita aje abinda takeyi din kawai ta miqe ta basu waje.


Bayan ta fita ya tashi ya zauna sosai daga kashingidar da yayi,yasa hannunsa ya shafi fuskarsa yana aje numfashi sannan ya kira sunan abdul'azeez,kiran daya sanya gabanshi faduwa ya amsa mishi yana sake nuna tsantsar ladabi
"Wato bansan mutane me suka dauki zalunci ba a wannan zamanin....kusan kowa ya zama azzalumi ba tare da ya sani ba,kowa burinsa ya samu wata dama komai qanqantarta ya zalunci dan uwansa,bansan wanne gardi ko dadi yakewa al'umma cikin ruhinsu ba,nayi tsammanin kowanne muminin qwarai zaiyi qoqarin gudun fanfalaqi wa zalunci iyakacin numfashinsa,komai qanqatar wannan zaluncin kuwa,koda na mummunar magana ce bare na aiki a aikace,a rayuwa zalunci na daya daga cikin manya manyan laifuka,saboda girman laifin Allah daya halicci komai da kowa yace ya haramtawa kansa da kansa shi,ya tauna tsakuwa don aya taji tsoro,ya nunawa bayi shi da yake da ciakken iko da izza ya haramtawa kansa,hakan yana nuni da cewa matuqar wani cikin bayi ya aikata wa wani dan uwanshi wannan zaluncin...bazai barshi ba saiya fidda masa haqqinsa....abdul'azeez,wallahi wallahi wallahi dukkan bawan daya zalunci dan uwansa koda da bawon rake ne bazai shiga aljanna ba sai Allah ya fiddawa wannan wanda ka zalunta haqqinsa,koda kuwa arne ne ba musulmi ba baka ci bagas ba"


"A yau na yanke wani hukunci da naso ace kana wajen na zartar dashi,wanda har cikin zuciyata inajin cewa shine dai dai....bazan daga qafa ga duk wanda na kama da laifin xalunci ba!,ko waye shi!". Sosai kalaman maimartaba suka dakeshi qwarai,bawai kalamanshi na qarshe ba,tunda ya soma magana suke shigarsa,saiya soma hada maganarshi data sodangi,indai har da gaske ne rashin gata ne!,indai har da gaske abinda zuciyarsa ke ayyana amasa haka ne,hakan na nufin an zalunceta?,hakan yana nufin ammin tayi zalunci?,shima zai iya fadawa ciki?,to amma zaluncin cikin sani ne ko cikin rashin sani,idan har ya tabbata zalunci ne ta yaya zai kubutar da ita a matsayinta na mahaifiyarsa da yake burun ganin tsiranta,ci gaba da yi mata biyayya irin wannan tamkar bata qofa ne naci gaba dayin abubuwan da basu dace ba?.


"Zanyi tafiya ethopia gobe,akwai taro da zamuyi a kamfanin dana sanya hannun jarina,naso ace muje tare dakai ko,kafin nan da shekara hudu da nake saka ran ka cika shekara talatin ka soma wakilatata,nima na soma ragewa kaina wasu al'amuran,to amma hakan bazai yiwu ba don lokaci ya qure,naso magana dakai kwanaki uku baya amma ka bace sam ba'a ganinka,don haka gobe zaka rakani airphort...zan bar riqon masarauta hannun waziri,saidai daga wannan karon inason ka soma sanin wasu abubuwa kaima,zaku riqe qasar tare,zaka zama tamkar mataimakinsa,har zuwa sanda Allah yayi na dawo".


Baya jin xai iya cewa wani abu illa
"In sha Allah ranka ya dade,Allah ya saka da alkhairi" baya son yawan qorafi,don yasan cewa saratu na qididdige da lokacin da aka shigar mata,don haka basu dora kowacce hira ba ya sallameshi,ya kuma gaya masa lokacin da zasu fita din zuwa airphort.


******* ***** *********


Akwatuna ne a gabanta a bubbude wasu da kaya da ajere a ciki wasu kuma yanxun ta soma jerawa,bisa dukkan alamu aiki takeyi ta katse ta zauna kallon takardun hannunta guda biyu.


Wani murmushi take fitarwa dake nuna farincikin da zuciyarta take ciki,duk da tayi katatu tuquru amma bata taba tsammanin kyawun sakamakon nata zaikai har haka ba,ko kusa ko alama,dukkan jarabawarta guda biyun sakamakon sun fito mata a ba zata.


"Kai bilkisu,basan wanne irin qauna haka kikewa karatu ba" sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta daga kai tana duban ummi anty zuhriyya,ta sake sakin murmushi
"Inason karatu sosai ummi,inason naga ina karatu a rayuwata" murmushi ummi tayi
"Karki damu daghter,zakiyi karatu in sha Allah,har sai kinji a karan kanki kin qoshi dashi" murmushin itama tayi mata tana kada kai
"Na gode ummi sosai,na gode" yatsanta ta dora saman lips dinta
"Shshsh,Allah xaki godewa,amma nikam na sha gaya miki karki sake godemin ko?" Saita rufe fuskarta da hannunta,ummi ta bita da kallo daga fuskarta zuwa cikinta daya fito cikin tausayi,wani irin mahaukacin girma yake,wata shidda amma saika tsammaci yayi watanni tara ko goma,abun har mamaki yake basu,hakan ya sanya likitan dake ganinta yace idan ta cika wata bakwai zai sake mata ultrasound scan a sake ganin lafiyar baby,duk da cewa tace bata jin komai,hakan shima yana alamta komai lafiya yake,don badon hakan ba da zata ga wata alama ko sauyi a jikinta.


Kusan ummi zuhriyya ce ta tayata qarasa hada kayan nata,tunda su nasu dama ba wani abu zasu dauka ba,tunda komai nasu yana can,banda ma zasu soma sauka ethopia din da babu abinda zasu dauka
"Duk abinda fa kikasan kina da buqata ki dauka abinki,don idan muka tafi din babu lallai mu dawo nan kusa,har sai sanda abbaa ya kammala abinda ya kaishi"
"Toh ummi" ta miqe tana sake laluba kayanta dakyau,dai dai sanda hisham ya callara qara,da alamu ya tashi a baccin da yake ne,ya samu babu kowa kusa dashi,da sauri ummi ta miqe
"Ga dam gidanki can ya tashi,bari na duba shi" murmushi tayi
"A shafamin kanshi,yanzu zan fito na wanke shi tas ko yaji dadin wasa da kyau" harara ummi ta jefa mata
"A haka da wannan turtsi billin naki" tayi daroya tana ficewa,ita kuwa murmushi ta saki,a hankali kuma murmushin nata saiya yanke sanda ta dora hannun nata saman cikinta,ta soma shafashi daga sama zuwa qasa,har yanzu bata ji qauna ko shaquwar da akan fada ba wai tun yaro yana ciki,bata sani ba ko tata qaddarar kenan?,ko kuma sai yazo duniya?,ko abinda mahaifi da ahalinsa suka mata ne ya danne wannan feeling din?,duka bata da wannan amsar.


Ƙoƙari tayi ta watsa wannan tunanin gefe,kamar yadda ta yiwa kanta alqawarin mantawa da komai,ta kuma fuskanci rayuwarta ta gaba,don haka ta miqe,taci gaba da lalubar sauran abinda yake da muhimmanci a wajenta tana hadasu waje guda gami da ci gaba da shiryasu a kwatin nata.


Washegari ana ya gobe zasu tafi wunin gida tayi tare da qannenta,sabanin daa a yanzu damuwarta kadan ce,ba kamar lokuttan baya da takanyi tafiya ba,saboda ta gamsu a yanzu da yanayin da suke rayuwa,yanayi mai kyau,wanda anty zuhriyya ta tsaya musu da gasken gaske,hakanan ko cikin gida ga mahaifinta taga wasu sauye sauye da bata zata ko tsammata ba,duk da tayi mamaki amma ta barwa Allah lamarinsa.


Bayan la'asar ne,ta idar tana saman abun sallar hannatu ta qaraso gabanta da baqar leda ta ajiye maya,bin ledar tayi da kallo tana duban hannatun,don bata gane ba,sai daya zauna sannan tace
"Kudadenki ne da aka baki ranar da kika dawo din nan?" Sai a sannan ta tuna da batun,ta miqa hannu a hankali ta daukesu gamida yaye ledar tana kallonsu,kudaden da suka zama tamkar fansa ga mutuncinta fansa kuma ga duk halin da zata tsinci kanta a gaba,badan Allah yaji qanta ba ya aiko mata ds uwa a gareta.


Maidasu tayi tamkar yadda suke sannan ta miqawa hannatu,tsayawa tayi tana dubanta,da alamu tana neman qarin bayani
"Kuyi amfani dasu keda sauran qannanki,ki kula da kanku" yawan kudin yasa hannatun ta dinga ji kamar ba zata iya dasu ba,sai suka zauna ita da bilkisun tana kwatanta mata yadda zasuyi amfani da kudin,da doguwar takards me cike da list,wanda hakan ya daukesu lokaci mai tsaho kafin su gama.


Suna gamawa din hannatu ta dubi bilkisu da idanunta wadanda suka cika taf da ƙwalla
"Ba shakka yaya me gado kin zama uwa kuma uba a garemu,jigon rayuwarmu,ba don ke ba bansan ya rayuwarmu zata kasance ba" saita qarasa fashewa da kuka,sanyata bilkisu tayi a jikinta tana rarrashinta,itama tana qoqarin boye tata qwallar
"Kowanne bawa yana qarqashun kulawar ubangijinsa ne,babu wanda yake rayuwa saboda wani na raye,ko babu ni zaku rayu,hannatu,a yanzun kin soma bin sahun 'yammata,tunda kinkai shekara ta sha biyar,ina horonki daki kame mutuncin kanki,ki kula da kanki da kyau,kada ki yarda rashin mahaifiyarki gaban idanunki yasa ki aikata abinda yake kinsan ba dai dai bane,gwargwadon iko nasan cewa na doraku bisa turba mai kyau,wanda kunsan dai dai kunsan kuma kasin haka,koda bani kusa daku in sha Allahu ba zaku rayu cikin tsanani ba yadda kuka rayuwancan karon,ki kula dakanki da qannenki,idan hauwa'u bata dawo ba har zuwa sanda zan dawo qasar nan,nayi alqawarin in sha Allahu zan nemo mana ita a duk inda take" sallama sukayi mai karya zukata,bata bar gidan ba sai bayan sallar isha'i driver yazo ya dauketa,tabar gidan cike da kewarsu.



******** ****** **********


Jeri gwanon motocin masarautar kaisa masu kyau tsari da daukan hankali ne suka ci gaba ratsawa manyan titunan garin kaisan,wanda zai sadasu da filin sauka da tashin jiragen sama dake garin.


Duk wani titi da motocin suka gilma sai an samu jama'a da zasu daga musu hannu gami da kyakkyawan fatan alkhairi ga adalin sarkin nasu,daya tamkar da dubu,basu damu da cewar yana ganinsu ko baya ganinsu ba,burinsu addu'o'insu da fatan alkhairinsu ya riskeshi a duk inda zashi.


A dai dai lokacin da yake xaune cikin motar data É—arawa duka sauran motocin kyau da tsada,gefanshi kuma azeez ne zaune cikin shigar sarauta shima,yayi kyau har ya gaji da haduwa,duk da cewa baya cikin wannan mode din,amma duka yayi hakanne don ya faranta ran mahaifinsa,ya kuma kautar da idanunsa daga gano damuwa tattare dashi.


"Abdul'azeez" mai martaba ya ambaci sunanshi cikin kulawa,cikin girmamawa ya amsa mishi
"Inason idan Allah ya bamu aron rai,na dawo daga tafiyar nan,zamu zauna da iyayen yarinyar nan 'yar wajen alh ibarahim,a tsaida magana me kyau kan aurenku,ya kamata zuwa yanzu a san inda aka nufa kan aurenka,bai kamata magajin sarki ya zaman bashi da future me kyau kan tara iyali ba..." Ya qarashe maganar cikin raha,wanda sam bai lura da yanayin da fuskar azeez ta fada ba,ya dora da cewa
"Sannan idan karatun ya isheka hakanan,inaga ya kamata kayi magana,kawai sai nayi reforming kan dukiyoyina da kadarorina kaci gaba da gudanar dasu,na samu na huta hakanan nima na tattara hankalina kan abu guda,duk da ita kanta sarautar ta soma gundurata,amma munyi magana da mahaifiyarka kan haka...saidai nata ra'ayin ya nuna,kana da tarin kadara wadda ta mallaka maka ita da mahaifinta,da kuma nawa wanda nake saka ran miqa maka su,tafi sha'awar ka gudanar da taka,ta yadda zaka ci gaba da tashi cikin hazaqa kishin kai neman na kai da sanin ciwon nema,duk da hasashenta na a bigire me kyau,amma dole ya kamata a duba wasu abubuwan,wanda duka ba damuwa bane,idan na zauna duk xamu tattauna kan hakan a samu matsaya" duka baice komai ba har sai da maimartaba ya kammala sannan yace
"Alla ya taimakeka,na gode bisa wannan zabi da aka yimin da kuma karramawa,ina da maganganu biyu masu alaqa da juna,zancan zuwa gidansu safwa....ina roqon alfarmar a dakata a yanxun sai zuwa nan gaba,maganar kula da harkokinka kuma Allah ya taimakeka idan Allah ya dawo dakai lafiya,saikayi tunani a nutse,ka zartars da dukkan abinda kaga ya dace"
"Allah ya bamu aron ran,amma meye dalilinka na tsaida maganar aurenka?,baka da labarin dukka 'yan uwanka nasa sun fidda miji?,inason wai da na hada aurenku dasu lokaci guda....amma...bansan naka tunanin ba,na baka lokaci,saidai kada ka bari ya tsawaita baka zomin da gamsashshen bayani ba"
"In sha Allah" ya fada yana lumshe idanu,a wannan qadamin da yake ciki baison ya sake qarawa kanshi matsala,baiyi solving ko daya daga cikin matsalolinsa ba tukunna.


Dai dai lokacin da anty zuhriyya da nata ahalin suka isa cikin filin sauka da tashin jiragen saman,duba daya zaka musu kasan cewa happy family ne,hatta da bilkisun yau fuskarta a sake take cike da walwala,idan ta tuna inda zasu,tana fata walwalarta ta dore,tana fatan tabar dukkan wata damuwa da matsala tata a kaisa,kowa janye da akwatinsa suka shige ciki,bayan driver ya ajjiyesu ya juya da motar zuwa gida.


Basu sake wata doguwar tafiya ba motocin nasu suka isa airphort din,suka samu wuri na musamman suka ajjiye motocin nasu,sanda maimartaba yake shirin fitowa sukayi kacibus da waalin kaisa,shi yadan kawo tsaiko saboda tsayawa gaisawa da sukayi,har aka soma screening na matafiya,ganin lokaci na shirin qwacewa yasa abdul'azeez matsawa bayan maimartaba cikin girmamawa ya sanar dashi,don haka basu sake jimawa ba sukayi sallama,maimartaba ya wuce ciki,abdul'azeez na take masa baya,bayan sun baro dukka dogaran a waje,don shi kadai zaiyi tafiyar,sai mutum daya da zai masa rakiya cikin amintattunsa.
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 46


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070




Saida komai ya kammala azeez

Please Login or Register in order to submit comment