Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibiti ba,don anty zuhriyya ce zata biyo ta dauketa ita dasu amatun,zasuje bikin sunan wata matar abokin abbaa data haihu,to kasancewar suna garine da kowa baida wani nashi sai suka zama tamkar 'yan uwan junansu.


Tana gaban madubinta tana shafa tsadajjen manta saqo ya shigo wayarta dake aje gefanta tana chargy,saqo ne daga assadiq,ta sanya hannu ya shafa wayar kana ta bude saqon


_saqon fatan alkhairi gami da tashi lafiya zuwa ga sarauniyar kyawawan duniya,kuma mai mulkin zuciyata,da fatan kin wayi gari cikin qoshin lafiya,Allah yasa ana nan ana tunanin yiwa wannan zuciyar data kafu a donki adalcin da zai sanya ta dore ta kuma ci gaba da rayuwa,ki huta lafiya saraniya_


Murmushi ta saki,ire iren saqonnin dr adam kenan dake cike fal cikin wayarta,saita maida idonta ga madubin tana duban kanta gami da tuna maganar da assadiq din yazo mata da ita ranar data bashi izinin zuwa gidansu,bayan ta fito da hijabi dogo har qasa mai hannu ta tarbeshi,suna zaune saman wasu kujeru dake jere a yalwataccen balcony na gidan.


"Allah yasa sauyin rayuwa da tsahon xamani baisa kin manta cewa assadiq yana daya daga cikin tarin masoyanki ba,idan ma ke kin manta shi bai manta ba,kuma zai saki tuna miki da jaddada miki" saiya gyara zamanshi yana dubanta
"Kamar wancan karon ni assadiq naga bilkisu,kuma ina sonta,ina qaunarta har jinin jikina,hakanan inason na aureta ta zama matata ta sunna,ina buqatar hadin kanki qwarai da kuma soyayyarki,banason na sake rasaki kamar wancan karon,kimin alfarma don girman Allah" kalmarshi ta qarshe ta mata nauyi qwarai,saita sadda kanta qasa tana wasa da yatsunta,maza da dama sun sha neman soyayyarta,mutane iri daban daban,to amma tunda can tana jin wani nauyi na assadiq da qimarsa,don haka ta buda baki a hankali tace
"Na gode sosai da kaci gaba da daakon soyayyata tsahon wancan shekarun baka sauya ba har kawo yau,naji dadi sosai da soyayyarka gareni,idan so samu ne muci gaba da addu'a gaba daya nida kai,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi,yasa gobenmu ta haifar da kyakkyawar natija me kyau" duk da cewa bata fito kanta tsaye ta amsheshi kota koreshi ba,amma amsarta tafi masa kama da cewa yaci gaba da neman soyayyarta,duk da cewa ba'a bashi dama ta kai tsaye ba,amma hakanma yayi masa,yana fatan nan gaba ya samu amsa takai tsaye gamsashshiya.


Dai dai nan ta sauke ajiyar zuciya,ta miqe tana isa ma'ajiyar kayanta dake shaqe da dumbin suturu kala kala,masu mabanbantan kudade,ta zabi ta shirya cikin daya,cikin qananun mintuna ta shirya kanta tsaf,ta kalli kanta a mudubi,sai taga kamar yau tafi kyau fiye da kullum,ayau saita hangi kyau tsari kwarjini da ajin da maza ke yawan gaya mata tana dashi,harda wasu daga cikin 'yan uwanta mata.


Sakin wannan tunanin tayi don bataga amfaninsa ba,ta dauki duk tarkacen da tasan zata tafi dashi,sannan ta zira takalminta da jakar hannu wadanda dukkaninsu duka dace da sutturar jikinta ta fito.


Sanda ta gama parking motarta tana shirin kashewa ta hangi motar dr adam a gefenta,ta dauke kai da sauri tana addu'ar Allah yasa bai ganta ba,sai taci gaba da zama cikin motar tana so ya wuce ciki sannan itama ta shiga,don ta tabbatar idan ya ganta,zai tilastata saisun jera ne har ciki,ita kuma abinda bata so kenan.


Saidai kuma addu'ar tata bataci ba,don tana tsaka da zaman taji ana knocking glass din motar,tun kafin ta bude taga shine,bata da sauran zabi illa ta fito kawai,don idan bata fito din ba shi shigowa ciki xaiyi abinsa,don haka ta dauki kayayyakinta ta bude ta fito.


Fuskarsa cike da murmushi yake kallonta,ya bude baki cikin farinciki yace cikin harshen turanci
"Kyakkyawar laraba ce yau,naji dadi sosai da ganinki,yau inda bakizo ba,zansa mommy ne da kanta ta kiraki,ta kuma roqarmin alfarmar ki bawa danta adress din inda zaije ya ganki,tun kafin zuciyarsa ta buga" ya miqa hannu yana amsat kayayyakin hannunta,duk da bataso sakar masa ba,amma batason jan doguwar magana,dole murmushi ya subucewa fuskarta na furucin da yayi
"Bakajin kunyarta yanzu dr?" Idanu yadan fidda
"Au,ku a hausa fa abun kunya ne ko?" Sai ta soma takawa tana yin gaba ba tare data bashi amsa ba,tana bin kan tambayar tasa da gaisuwar ina kwana,ya biyota yana amsawa tare da qoqarin daidaita kafada da ita.


Abinda take gudu dai shi yayi,dolen sai daya jera da itan,suna tafe suna haduwa da ma'aikata,suna gaidasu cikin girmamawa da mutuntawa,tun daga lokacin da kowa ya fahinci soyayyar da yake mata suke bata wani irin girma,tamkar itace dr adam din,wannan ya janyo mata hamayya daga wasu daga cikin likitoci mata dake nacin neman soyayyar dr adam din basu samu ba,saidai ita din ko a jikinta,dukansu basu dameta ba,don a rayuwarta ta yanzun ba komai take bari ya dameta ba,tace ta gama samun damuwa tun asubar fari ta rayuwarta,yanzu kuwa da komai ya warware mata bai kamata ta bari qananun abubuwa irin wadan nan nason dagula lissafinta ba.


Bai barta ba kuwa sai da suka dangana da office dinta,don shi ya bude mata ma,yana aje mata kayan saman kyakkyawan table dinta ne yace
"Har yanzu mutanen nan basu karbi certificate na rasuwar yarinyarsu ba" ta daga kai ta dubeshi
"Na zaci tun ranar dana tafi ka sallamesu" kai ya girgiza
"Nima hankalina ba akwance yake ba,saboda yadda kika fita din na tabbatar ba lafiya ce ta kawo hakan ba" kafada ta gyada
"Ba damuwa,nan da awa daya komai xai kammala,koda sunzo zasu karba babu matsala" da qyar tasamu ya tafi nashi office din ya bata waje,bayan ya ritsata,ya kira mommynsa ya bata wayar suka gaisa.


Batura sosai,babu ruwanta da wata kunya ko kwana kwana,hira take da ita kai tsaye,tana kuma sake roqarwa danta soyayyarta,sun dan jima kan wayar kafin suyi sallama ta bashi wayarsa ya tafi tana masa mita shi kuma yana dariya.


Sai data gama rubuta certificate din,tayi waya daga dakin buga takardu na asibitin sukazo suka amsa sannan ta fita ita da nurses din dake team dinta,ta soma duba marasa lafiyanta,wadanda dr martin ne ya riqe mata su har zuwa yau data dawo.


Ta shafe tsahon lokaci sosai tana duba komai,sai data tabbatar komai da kowa lafiya lau,kuma komai ya tafi daidai sannan ta nufi komawa office din ta duba sauran ayyukan dake gabanta.


Tana shirin bude office dinnata taji ana dan kiranta da yanayi na girmamawa,ta waiwaya,daya daga cikin ma'aikatan dake buga takardunne riqe da certificate din,komai ya kammala kenan ya miqa mata,hannu tasa ta amsa tana masa godiya kamar yadda yake a al'adarta,ta tura qofar tana karanta rubutun jiki tare da lissafa adadin kwanakin da yarinyar tayi yau a qarqashin qasa
"Ranki ya dade akwai baqo" taji an fada da harshen qasar daga bayanta,ta waiwaya tana duban daya daga cikin ma'aikatansu ne
"Baqo daga ina?"
"Wai certificate xai karba" kai ta jinjina,mahaifin suhaima ne kenan,dama akwai maganar da takeson mishi,kan barin yarinyar da akayi babu uwa ko uba har wata uwa duniya,abun ya sosa mata rai,yana kuma ci gaba da sosa mata rai
"Ka bashi izini ya shigo" ta fada tana shigewa ciki shi kuma ya juya.


Saman kujerarta ta koma ta zauna tana dan juyata kadan kadan hagu da dama tana dakon shigowarsa,ganin wasu mintuna sun shude bai shigo ba saita ciro eye glasses dinta ta sanya,ta janyo takardar wani patient dinta ta soma dubawa saboda rage lokaci.


A hankali ya turo qofar office din bayan an bada izinin shigowa,sanye cikin trouser da shirt mai gajeran hannu,kalolin da suka masa kyau suka kuma bada ma'ana a jikinsa,qafarsa na saye da rufaffen takalmi,kanshi babu hula sai sumarshi da take zuba qyalli saboda kyau da tayi na gyaran da tasha,duk da ba mai yawa bace sosai,yanayin askin dake fuskarsa ya sake qawata zallar kyau da kwarjinin da Allah ya bashi,hannunshi daure da agogo rolex mai azabar tsada da kyau,sai gilashin idanu dake saman fuskarsa wanda ya kuma qarawa adonshi kyau da kwarjini,.


Tunda ya shigo yake daukan hankulan mata kala daban daban cikin asibitin,musamman wadanda suka san nauyi da tsadar motar daya fito daga cikinta,takunshi kawai abun daukar hankula ne,duka wannan bai dameshi ba,baisan ma me ake ba,fuskarshin nan babu ko digon fara'a a cikinta,ba zakace ya taba dariya a duniyarshi ba.


Maida qofar yayi yadda take saboda bin doka da qa'ida irin nashi,kana ya maido kansa cikin office din da niyyar yin salla.


Cak kalaman bakinsa suka tsaya saman harshensa,maqogwaronsa ya kada fidda wani sauti bare harshensa ya motsa,tamkar an kafe dukkan ganinsa saman fuskar dake kallon takardar dake riqe a hannunta,kamanninta suka dinga bayyana cikin idanunsa a wancan shekarun da kuma yanzu.


Sune dai,wadan nan kamannin daya jima da sani,wadan nan kamannin da suka hana rayuwarshi sukuni tsahon shekara bakwai da watanni,duk da cewa akwai bambamci mai tarin yawa,da suka bayyana qarara,tun daga yanayin fata,dressing da kuma yanayin ilimi gogewa da kuma wayewa.


Amma bayajin koda shekaru dubu ne suka shude matuqar ruhinsa yana cikin gangar jikinsa wannan fuskar mai tarin daraja qima da martaba idanunsa ba zata taba bace masa ba,yanajin koda an mata sauyin fuska jikinsa zai gaya masa cewa tana tare dashi,ruhinsa xaici gaba da gaya masa cewa itace a tare dashi.


Baisan ta yadda ya isa gaban table din nata ba,baisan yadda akayi yakai kanshi gabanta ba,yadai tsinceta tana daga fararen manyan qwayoyin idanunta dake ta walainiya kamar an diga musu mai ta dubeshi bayan qamshin turaren daya sanya mata matsananciyar faduwar gaba ya ziyarci hancinta,taso ta daure amma saita tsinci zuciyarta na gudu fiye da kima,bayan batasan daga inda qamshin ke kutso kai ba,hakan ya sabbaba mata dole ta daga kanta tana dubanshi,babban shahararren matashin attajirin dan kasuwar duniyar nan ta gani tsaye a gabanta,me ya kawoshi office dinta?,bata sani ba,saita tsuke fuskarta sosai tana ci gaba da kallonshi tanason jin me ha shigo dashi?.


Kamanni na zahiri data sake gani saman fuskarshi irin da twince din ta yasa wani faduwar gaban ta daban ta sameta irin wadda bata taba jinta ba,dole badon taso ba taji idanunta na lumshewa,cikin zuciyarta ta ambata da sauri
"Subhanallah....ya ubangiji....ka sanya baida alaqa da mahaifinsu ko wani nashi,Allah ka sake nisanta tsakaninmu dasu" saita kuma bude idanun nata da sauri.


Ta zaci zata sameshi a zaune ko kuma ya fita,saita sake ganinshi still dai a tsayen,hannayensa goye a qirjinsa,ya kafeta da idanunsa da takejinsu da wani irin nauyi a qirji da gangar jikinta,wani irin kallo da takejinsa ya bambamta da sauran kallo na kowa da kowa,qwayoyin idanuwa da bata taba ganin masu nauyi da kwarjini irinsu ba.


Can daga wane sashe na zuciyarta ya zaburar da ita,tayi hanzarin maida hankalinta tana janye idanunta daga kanshi tana daukar takarda ta gaba dake gabanta,tana kuma sake tamqe fuska,tare dajin haushin yadda yazo ya tsaya mata akai,kamar wani bodey guard,ba kuma tare da taji sallamarsa ba har ya zuwa yanzu,da harshen turanci tace dashi
"Lafiya malam?,ka shigo wajen mutane babu sallama,kuma ka tsaya haka a kansu ba tare dayin bayani ko fadin dalilin shigowar taka ba" ta qarashe maganar tana duba takardar,saidai zallar mamakin kamanni da razana dake tattare da ita suna nan,kunnuwanta kuma na gareshi tana son taji me zayace,saidai tsayin wasu mintuna shuru,hakan yasa ta fusata,ta sake daga kanta cikin masifa tace
"Kaga....idan baka da abun fada kana iya fita ka tafi,akwai tarin ayyuka gaba na".


Ga dimbin mamakinta sai taji ya damqi hannunta dake riqe da takardar,wanda yayi hakanne don son tabbatarwa da kanshi ire iren mafarkan daya saba yine ko kuma zahiri ne wannan?.


Cikin tashin hankali ta fincike hannunta tana dubanshi,kana ta miqe tsaye cikin fushi da fada
"Meye haka malam?,hankalinka daya kuwa?" Sakin hannun nata yayi,karo na farko daya buda bakinsa cikin tashin hankali bayan ya fahimci bilkisun nan dai daya shafe shekara da shekaru idanunsa na neman gani,zuciyarsa nason jinta kusa dashi,kunnuwansa na muradin jin duk wani abu daya shafeta itace dai,itace dai a gabanshi
"Am so sorry....kiyi haquri,wannan ce kalma ta farko da nake tunanin ya kamata na gaya miki".


Shuru tayi tana dubansa cikin mamakin kalaman da yake furtawa,me yayi mata,wayeshi?.


Kallon rashin fahimta da take masa ya tunasar dashi cewa,bata taba ganin wayeshi ba,batasan shi din yanzu akan me yake magana ba,cikin wata iriyar murya mai sanyi yace
"Abdul'azeez abdallah mu'az kaisa,yariman qasar kais......."


Bai qarasa ba saboda yadda yaga da mugun hanzari ta nemi kujerar data tashi dazun akai ta zauna,wutace ta dauke tsaffff! Na tsahon wani lokaci,wani irin tashin hankali taji yana rufto mata,indai kunnuwanta sunji daidai,yana son gaya mata cewa shine mutumin da yayi silar zuwan amaturrahman da abdurrahman duniya?,mutumin da yayiwa rayuwarta karan tsaye?,mutumin daya sauya qaddararta shida ahalinsa?,tome yake nema yanzu a gareta?,me yazo yi?,ko yazo ne ya qarasa tarwatsa rayuwarta?,don bata taba tunanin yazo bane domin 'ya'yansa,tunda tun suna tsiron da ba'asan ko meye ba a cikin cikinta suka nuna basu da buqatarsu,indai ko hakane yazo don ya tarwatsa sabuwar rayuwarta to qaryasa tasha qarya,ba zata taba bari suyi galaba ba koda waye gatanshi nan duniya.


Cikin lokaci kadan ta maida hankalinta jikinta,ta tattara dukkan nutsuwarta,ta miqe a hankali saidai cike da karsashinta,jifansa tayi da wani irin kallo sa'annan tace
"And so what?.....don kaine yarima abdul'azeez kuma sai me?,ehemmm?" Ta qarasa fada tana harde hannunta itama a qirji,tana kuma jifansa da wani irin mugun kallo.


Furucin nata ya dakeshi,bai taba zama ya tsara me zai iya biyo baya ba duk randa suka hadu,idanunshi a rufe suke,burinsa kawai ya ganta,yana tsammanin ganin nata shine abu mai wahala,idan ya gantan kome zai biyo baya sai yake ganin abune mai sauqi tattare dashi.


Takawa ya soma yi yana nufarta,cikin wata iriyar murya da zaka gaza fasara yanayin da yake ciki yace
"Karki ce zaki fusata don Allah....ki bani dama ta yadda zamu zauna mu...."
"Dawa?.....kaga malam nifa banma ganeka ba,inajin kana da ciwon tabin hankaline ko dake tashi lokaci bayan lokaci,ya kamata kabar nan,idan kuma ba haka ba zan kira securities su fita dakai" duk da cewa yana cikin hali na dimuwa amma saida yaji maganar tata kamar wasan yara,saboda ya sani cewa koda duka securities din qasar zata kira babu wanda zai iya kama hannunshi ya fiddashi,saboda sun riga da sunsan wayeshi shi,ko baya ga haka ma bayajin akwai wanda ya isa ya fiddashi daga office din daidai wannan lokacin,zamanin daya dade yana hana idanunshi bacci kan fata da burin zuwanshi,yana addu'ar Allah ya nuna mishi shi.


"Banajin ko duka duniya zasu taru sun isa su fiddani daga dakin nan bilƙess" cike da mamaki hakanan har tsakiyar kanta taji furta kalmar sunanta da yayi,saidai duka ba wannan ne a gabanta ba,yanayin yadda ya furta maganar ta tabbatar mata da cewa ainihin abinda yake cikin zuciyarsa kenan,magana ce data fito daga zuciyarsa,a bisa kuma saurin fahimta da gane halayyar mutane da Allah ya hore mata ta fuskanci yana da wani confidence tattare dashi.


Bata da buqatar ci gaba da tsaiwa dashi don haka bashi da wani amfani,hakanan tana jin zuciyarta na wani irin zafi duk sanda ta tuna waye tsaye a gabanta saman rufin daki guda daya,saboda haka ta soma tattara tarkacenta dake saman tebur din cikin hanzari da gaggawa.


Saiya sake matsowa dab da ita hakan yasa ta dago da sauri cikin kaushin murya tace
"Ka dakata malam,kada ka sake aikata irin kuskuren daka aikata daxun,domin ban sanka ba,bansan daga wacce duniya kake ba,kanme zaka nemi shiga rayuwata"
"Bilqess!"
"Karka sake ambatar suna na,don babu wani abu daya hadani dakai"
"Igiyar aurena....don har yanzu ke matatace!" Furucin da yaso tarwatsa qwaqwalwarta fiye dana daxu,yakuma so sumar da ita a duqen da take,har sai da tayi taga taga zata fadi,tallafin da yaso kawo mata ne yasa tayi hanzari tallafar kanta,ta dafe kujerar daje gefanta
"Qarya kike,kin manta su din mayaudara ne,azzalumai,da basu damu da damuwar kowa ba sai tasu?,me yasa zaki gasgata kalamansa don kawai ya fada?" Xuciyarta ke ankarar da ita,wannan tunanin ya sanyata namijin qoqarin aro juriya da jarumta ta azawa kanta,sannan ta dubeshi sheqeqe
"Wannan kuma kaita shafa,kaika sani,bansanka ba bare wata kalmar aure ma ta gilma tsakaninmu" daga haka ta rataya jakarta a kafadarta,duk da bata gama diban abinda xata diba din ba,burinta kawai tayi nesa dashi,burinta kawai ta tserema ganinsa,cikin wani mugun sauri da batasan tana dashi ba ta soma dosar qofa,baiyi qasa a gwiwa ba ya rufa mata baya
"Na hadaki da girman Allah ki tsaya ki saurareni koda na minti biyar ne,koda ba zaki yarda da dukka kalaman bakina ba,ki daina pretending kamar baki sanni ba,bayan babu wannan maganar" a fusace tana bude qofar tace
"Bazan daina cewa ban sanka ba,saboda ban sanka ba din!,donme zaka dinga bibiyata ha'ab?!"da sauri ganin tana niyyar ficewa yace
"Idan ke baki sanni ba nina sanki,na sanki sanin da babu mahalukin daya taba miki shi duka fadin duniya....idan har baki sanni ba,ina cikina?,ina yaro ko yarinyata dana bari jikinki?".


Ji tayi jiri na neman kayar da ita,dr adam ne tsaye qofar office din yana duban fuskarta,hakanan kalaman azeez na qarshe na shiga kunnuwansa,batasan sa'adda da ta danqa masa katin rufe qofar tata a hannunsa ba,har hannuwansu na gogar na juna,tabbacin ba cikin hayyacinta take ba
" ka rufemin qofar,bani da lafiya"daga haka ta qara wuta cikin sauri gudu gudu duk don ta tsere masa.


Bai tsaya bin takan dr adam.daya tsaidashi da tarin tambayoyinsa wadanda bai fahimtar ma me yake cewa ba,illa dai yaga bakinsa yana motsawa ba,ya rufawa bilkisu baya,yabar dr adam da binsu da kallo,baki sake,qwaqwalwarsa cike fal da tarin tambayoyi.


Saidai qaura wambai ya rasa bilkisun cikin harabar asibitin,bayan ya tabbatarwa da kansa cewa bata bar cikin asibitin ba,yayin da take tsakankanin wasu shukoki tana hango gilmawarsa,tanajin wani tsoro da fargaba da nashigarta,me zayayi cikin rayuwarsu daya dawo yanzu?,dame suka zo musu a wannan karon kuma?"ta yiwa kanta tambayar yafi cikim carbi.


Tayi dana sani mara iyaka kan rashin zuwanta yau da motarta,gashi anty zuhriyyan da zata dauketan har yanzu shuru basu qaraso ba,kafin wasu mintuna ta hada hawaye da gumi sharkaf saman fuskarta.


Cikin jikinsa ya dinga jin tana cikin asibitin,hakan yasa ya kasa fita,ya dinga zirya yana duba loko da saqo na asibitin,yanaji cikin zuciyarsa zaya ganta,ya dinga yawo tsakanin cikij asibitin zuwa harabarsa.


A karo na sau babu adadi yasake dawowa harabar asibitin,yanajin kamar zai zauce da bace masan da tayi,bayan ganinta da yayi karon farko na wasu 'yan mintuna.


Kamar ance masa ya juya ya hangeta cikin bala'e'en sauri tana nufar wata mota dake tsaye,wadda da alama ita suke jiran ta qaraso.


Abubuwa guda biyu duka dakeshi lokaci daya,shirin bace masan da takeyi,da kuma yarinya da yake hangowa 'yar kimanin shekara shida zuwa bakwai tana leqo da kanta ta window din motar,tana dubanta fuskarta cike da murmushi,tana zuro mata hannu gamida motsa bakinta da alama magana take mata.


Idan ba qarya idanunshi ke masa ba,fuskarshi yake gani kan fuskar yarinyar,banbancin shekaru kawai da kuma kasancewarta diya mace,banda haka zai iya cewa tashi fuskarce,a gigice cikin rashin sanin abunyi ya dora tafin hannunshi saman tashi fuskar yana shafawa a hankali,kamar wanda ya rasa hankalinsa,kai kace yanason tabbatar da gaskiyar abinda idanunsa suka gane masa ne..........


Bai ankara ya dawo hayyacinsa ba sai daya ga ta shige,an tashi motar ana shirin ficewa daga asibitin sa'annan ya zabura,cikin tsananin zafin nama da hanzari ya durfafi motar,sai ina tuni tayi masa nisa,har sun fice daga asibitin sun kuma harba kan titi.


Da saurinsa ya dawo inda tashi motar take,ya budeta yashige ya tayar da ita sannan ya tasheta da wani irin gudu ya rufa musu baya.


Da farko anty zuhriyya bata lura da yanayin da bilkisun ta shigo dashi ba,sai dataji yaran na mata surutu amma babu wanda ta kula a cikinsu,saita waiwaya tana dubanta
"Subhanallah!,daughter lafiya?,me haka?" Ta fada tana qoqarin sauka gefan titi,cikin muryar kuka tace
"Karki tsaya ummi muje don Allah" ganin yadda tayi maganar a gaggauce saita fasa tsaiwar,taci gaba da tuqin amma fiye da rabin hankalinta na kan bilkisun,tana karanto zallar tashin hankalin dake saman fuskarta.


Motar saita dauki shuru,dukka yaran kowa ya kama bakinsa,abdurrahman da amaturrahman damuwa ta bayyana qarara saman fuskarsu,ganin yadda dukka yaran sukayi tsuru suna kallonta saita kifa fuskarta saman cinyarta,don ta tabbatar ba zata iya hana kanta kukan ba bare ta tsaidashi.


Gudu yake zabgawa har ma ya wuce doka da qa'ida,saidai ko iri irin motar bai samu gani ba,haka ya dinga zagaye titunan dake daura da asibitin harma da maqwaftansa,shiga nan fita can,bayajin ko gajiya bata lokaci da kuma tsahon lokacin daya bata wannan aikin,tamkar wani zautacce,hatta da wayarshi dake aje gefan gear din motar daketa burari tana neman agaji bai jita ba bare ya saurareta,burinsa kawai yakai gareta,burinsa kawai ya cimmata,haka ya shafe lokaci mai tsaho yana zagaye saman titunan ba tare daya samu abinda yake nema ba,hakanan shima bai gaji da nema ba,yana fatan ko Allah zaisa ya ganta.....


Yayi yawo mai tsahon dashi kansa baisan adadinsa ba,sai daya zagaye dukka area da asibitin yake da sauran maqwaftan unguwanni,saidai babu alamun zai ganta.


Jikinsa ga soma mutuwa saboda yunwa da gajiya amma bai kulaa da wannan ba,zuciyarsa da qirjinsa ke masa wani irin zafi,roqon Allah yake tun qarfinsa ya tallafeshi,kada ya sanya ta subuce masa,kada ya qaddara masa wata doguwar wahalar kafin yasake ganinta,tilas daga qarshe ya gangara motarshi gefan titi,ya jingina bayansa da makarin kujerar yana lumshe idanunsa da suka sauya launi,yana fidda numfashi mai zafi,tun daga hunhunsa zuwa bakinsa da hancinsa,qwaqwalwarsa ta soma nisa cikin duniyar tunani tare da wassafa yadda al'amura zasu kaya anan gaba.


Ƙarar wayarshi a karo na barkatai shi ya sanyashi bude idanunsa yana bin wayar da kallo kamar wata baquwarsa,yanajin ringing dinta kamar tsaga qwaqwalwarsa yake,saiya sanya hannu da nufin dauka ya kashe,saidai kafin yakai ga haka ma ta katse don kanta,yana shirin kashewar dai kiran ammi fulani ya shigo,bazai iya kashe mata waya ba,don haka ya daga,saidai bai iya karata a kunne ba ya sakata a handsfree
"Ba zakaci abinci tare damu bane yau?"
"Akwai wani uzuri daya riqeni,kada na tsaidaku" sauyi taji sosai cikin muryarsa,to amma ta sani ya sauya ya zama wani mutum na daban cikin shekarun,koda yaushe mode nashi na iya canzawa,don haka cewa kawai dashi tayi
"Allah ya tsare hanya"
"Amin" ya amsa suna aje wayar dukkaninsu.


Tunanin daya fado mishi a rai ya sanyashi sake tada motar cikin hanzari,yana da hope da fatan xai samu cikakken adress dinta a a sibitin,adress din da zai zama silar kawo qarshen komai,ya kuma zama silar cimma burinsa na shekara da shekaru,don haka ya qarawa motar

Please Login or Register in order to submit comment