Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaka iya wucewa ba,ke kanki duk sanda kuka hadu laushi kike qara yi bare ni da nake a matsayin suruki,yana da kwarjini da cika ido" tasan da hakan sarai,amma saita tura baki
"Duk kwarjininsa amma dai qanina ne ko?,shi ya kamata idan ya ganka ya soma gaisheka" dariya yayi yana kada kai,ita kanta yasan ta fada ne kawai,amma ba abinda zai yiwu bane,haka ya lallabata sukaci gaba da takawa.


Har aka gama serving dinsu babu wanda yace uffan,sai data gama zubawa ta tafi sannan fulani taja nata abincin gabanta tasoma ci,maimakon taga yaja nashi abincin sai taga ya janyo babban jug din tangaran wanda yake cike da ruwan tattacen inibi yahau zubawa yana dirkawa cikinsa,bata ce masa komai ba har taci kusan rabin abincin
"Hala a qoshe kake kenan?" Kai ya jinjina
"Banajin yunwa ne..." Bata kuma cewa komai ba,amma tana karance dashi har ta kammala sannan ta dubeshi
"Batun ci gaba da karatunka....har yanxu baka kammala zabar universty din da zaka ba?" Kwata kwata a yanzun bashi da wata sha'awa ta tafiya wata qasar again,uwa uba ma dukka wani buri da shima ya ciwa karatunsa a yanzun babu shi,tamkar wanda aka zarewa dukkan wata sha'awa da burinsa,amma a yanzun yana da yaqinin furta hakan ga ammi ba qaramin qalubale bane,tunda ba abunda take son ji ba kenan.


Boyayyiyar ajiyar zuciya yasaki yana hade hannayensa waje guda
"Zan duba in sha Allahu"
"Baka kai ga soma dubawa ba kenan?"
"Sai nan gaba" ya fada don mutum ne shi da abune mawuyaci,ta riga data sanshi,don haka saita gyada kai kawai tana dubanshi tare da karantar sauyin yanayi muraran tattare dashi.
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 40

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*
*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*
*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070



Zaune take tsakiya ateeq da najwa da suka baza litattafansu tana koya musu assigment,yayin da hisham yake zaune saman cinyarta yana wasa da wani abun wasan yara da ake daura musu a hannu,haule kuma na kitchen tana hada kayan girkin da anty zuhriyya ta sata ta hada din kafin ta sauko daga sama,saboda abune mawuyaci kaga ta sakarma haule dukka girkin gidan idan ba wani babban uzurine ya taso mata ba wanda bata kusa ko bazata dawo gida da wuri ba.


A hankali ta daga hannunta ya dafe bayan wuyanta dashi,saboda yadda takejin jikinta na wani irin ciwo,qashinta kamar ana sassara mata shi,yayin da takejin zazzabi nason kamata,saisai babu alamunsa saman fatarta,da alama zazzabin cikin qashine,daurewa ta dinga yi ganin sun kusa gama assigment din,a haka a anty zuhiryya da a yanzun take kiranta da mami kamar yadda yaranta ke kiranta ta sauko daga saman nata tana dubansu.


"Kinga ta kanki daughter,wai har yau ba's gama aikin bane" idanunta ta daga cikin wata iriyar kasala da dandatsar da takeji a qashinta tace
"Eh....mun kusa amma" fuska anty zuhriyya tadan yamutsa tana kallon bilkisu
"Daughter....anya lafiya kuwa,kinga yadda idanunki suka sauya kala" itama yamutsa fuskar tayi
"Banajin dadi ne,kamar zazzabine yakeson kamani" da hanzari ta taho inda take tana dauke hisham daga saman cinyarta
"Ashsha...tun yaushe kuma amma kika tsaya kina wani aikin daban,maimakon ki samu waje ki kwanta,maza tashi ki dauko paracetamol guda biyu kisha ki kwanta,zuwa anjima kadan mu gani,idan baki samu relief ba ki shirya nasiru driver ya kaiki kiga likita" bata musa ba ta miqe,sai a sannan taji da gaske ashe jikin nata babu dadi,ta dinga takawa a hankali harta shige dakin da suke ajiyar magunguna,ta balli paracetamol din guda biyu tasha sannan ta wuce dakinta.


Kai tsaye gado ta fada taja duvet ta lulluba sosai tana sakin ajiyar zuciya saboda yadda taji qashinta na mutstsuka,tadan jima a haka sannan bacci yayi awon gaba da ita.


Sanda ta farka taji dama dama,don harma ta sake wanka don ta kuma jin dadin jikinta,takuma shirya ta sauko qasa akaci abincin dare da ita,lokacin kwanciya yayi ta dauke najwa tace tare zasu kwana suka wuce dakinta.


Saidai tsakiyar dare ciwon ya dawo mata sosai,harta kasa jurewa,ta dinga sakin nishi tana murqususu,ga wani dan banzan zazzabi mai kama da an kara mata wuta,hatta da numfashinta huci yake bayarwa,najwa nata bacci batasan me yake faruwa ba,sai gab da asuba da fitsari ya tasheta sannan ta gani,abinka da yarinta dakuma rashin sabo duk sai ya rude,ta juya da sauri ya fice daga dakin don sanarwa mamin nasu,duk da bilkisu tayi yunqurin tsaidata kada ta tashesu suna bacci.


Minti biyar yayi yawa suka dawo tare ita da anty zuhiryyan,sanye da hijabi da alamun bacci take ta tasota,a hanzarce ta isa inda bilkisun take tana riqeta,yadda taji zafin da jikin nata ya dauka ya daga mata hankali,saita saketa tana cewa
"Bari na yiwa abbaa magana,inaga gwara kawai mu wuce asibiti" bata da sauran qarfin da zatace komai saboda yadda taketa rawar dari,kai kace an sakata ne cikin kogin qanqara.


Cikin daren ya fidda mota suka wuce asibiti,sukabar yaran a gida su da haule,wanda suna zuwa cikin sauri aka karbeta,sannan aka bata dukkan taimakon daya kamata,cikin awa guda saiga bacci ya sureta,sai a sannan hankalin anty zuhriyya yadan kwanta.


Da safe likita ya bada test na malaria da typoid yace ayi mata bayan ya tambaya tana da aure antyn tace aah,baccin da take yasa aka jinkirta yin test din har zuwa sanda zata tashi.


Bacci tayi sosai saboda allurai da ruwan da aka saka mata,bata farka ba sai kusan azahar,anty ta taimaka mata saboda jirin da tace tana ji,ta shiga bandaki ta wanke bakinta,tayi alwala tazo ta rama sallar asuba data kubce mata,sannan ta dora da azahar,sai a sannan antyn ta zuba mata farfesun kifin da haule tayi da dankali jifa jifa a ciki,ya dahu sosai yadda zaiyi dadin ci,ta matso da kwanon kusa da ita
"Bismillah,ungo" ta fada tana miqa mata cup mai dauke da ruwan tea mai zafi bayan ta tura mata kwanon kifin gabanta,kanta ta dauke tana kada kai
"Bakina babu dadi ummee,kuma bana jin yunwa ma kwata kwata,cikina a cushe yake"
"Idan kika ci ko babu yawa zakiji dadin bakinki,sannan bazai yiwu ayita baki magani ba amma babu komai a cikinki,likitan dama yace idan kin tashi kici wani abu,kema.kya dan sake jin qwari,don lab zamuje yanzun za'a miki test".


Batason mata musu,don haka ta saka hannu ta karbi ruwan tea din,kurba uku tayi mishi taji cikinta na juyawa,hakanan ba zata iya ci gaba da sha ba,saita dire tana cewa
"Ummi wallahi kaman xanyi amai,don Allah ki qyaleshi" yadda ta fara yunquri ya nuna mata da gaske take,don haka ta qyaleta,bata yi mata maganar test bama sai data kwanta tasake hutawa sannan sukaje lab din.


Washegari result ya fito,malaria din ne da typhoid,saidai malaria yafi yawa,nan anty zuhriyya ta dinga sababi
"Dama a wannan gidan kowacce irin cuta ma ba samunta za'ayi ba tunda babu mai kula dakai,mun godewa Allah daya sanya iya tsahon shekarun ciwon da kika samu kenan".


Kulawa sosai ta samu a asibitin,satinta guda sa'annan ta samu sauqi suka bata sallama suka dawo gida.


*_BAYAN KWANA BIYU_*


Babu bata lokaci anyy zuhriyya tayi ma bilkisu registration na waec da neco,hakan ya sanya gaba daya bilkisu ta maida hankalinta kan karatu,duk wani buri nata ya sake dawowa sabo,kwadayin karatunta da karsashinta suka sake dawo mata,ta bude can wani saqo na zuciyarta data tattara dukkan burin karatunta ta cusashi a ciki ya zaqulo abinta ta sabunta shi,tunda a yanzun tana ganin ta samu dukkan wata dama data dace,hakanan babu wata sauran matsala da zata dakatar da ita.


Lafiya qalau ta zana waec dinta,cikin sauqi,don duk yadda ta zaci abun zaizo mata da wahala ta dinga jin tsoro duk da karatun da tayi sai taga duka ba haka bane,tazarar kwanaki suka soma neco.


Ranar farko lafiya lau taje itama ta dawo gida,saidai a komawa ta biyu ta soma jin jikinta babu dadi,kamar rashin lafiyar datayi a kwanakin baya tana son dawo mata,don haka ta fidda magungunanta da dama basu qare ba tun wancan lokacin ta sha,ta danji dama dama,sun kuma taimaka mata ta qarasa zana jarabawarta,har zuwa ranar da suke da paper qarshe.


Tun a makarantar da take zana jarrabawar ta soma jin kanta na juya mata,hakanan qafafunta basu da wani isasheshen qwari,a daddafe ta dinga amsa tambayoyin,tana yi tana dakatawa ta huta,a haka harta kammala,inda Allah ya taimaketa tuni drivern anty zuhriyya yana waje yana jiranta,don haka bata wani tsaya ba ta tattara ya nata ya nata ta fito,tunda dama babu wanda ta sani,kuma iya zuwanta bata bari tayi sabo da kowa ba,abinda ya kaita shi kadai takeyi,data gama take tafiyarta.


Tunda ta shiga motar take dafe da kanta,don tana daga zaunen amma jiri takeji,hakanan numfashinta na mata nauyi,Allah Allah take su isa gida ta samu waje ta kwanta sosai ko zata samu relief.


Suna isa ta bude motar ta fit,tana tafiya tana hada hanya,kallo daya zaka mata kasan ba lafiya qalau take ba,a haka ta isa falon gidan,anty zuhriyya ce kadai zaune tana kallo,duka yaran na makaranta lokacin tashinsu baiyi ba,sai hisham dake zaune a gefanta yana shan madara.


Yanayin sallamarta ya sanya anty zuhriyya dubanta tana amsa sallamar
"Yadai daughter?" Ta tambayeta tana qare mata kallo,ba zata iya wani dogon tsaiwa ba don kada ta fadi,saita doshi dakinta tana cewa
"Bab....ba komai ummi" saidai kafin takai ga isa tuni jiri ya debeta tayi luu zata fadi,cikin mugun hanzari anty zuhriyyan ta nufeta ta tallafota tana kiran sunanta,idanunta nakan fuskar antyn sanda numfashinta ke qoqarin daukewa,sannan a hankali dukka idanun nata suka lumshe.


Abinda yayi masifar daga hankalin antyn kenan,tasoma qwalawa drivern daya kawota kira ba tare da tayi la'akari da cewa babu lallai ya jita ba,ganin babu alamun yana jinta ya sanyata riqe bilkisun ta kwantar da ita saman kujera,sannan ta fita harabar gidan cikin hanzari tana sake qwala mishi kira,tunda babu kowa gidan ta aiki haule kasuwa.


Allah yasa yadan tsaya magana da me gadi a qofar gate din kafin ya fice yaje dauko su najwa,yanayin kiran ya alamta mishi ba lafiya,saiya taho da hanzarinsa
"Maza bude mota,daughter ya fadi" ta qarasa fada tana komawa cikin gidan cikin gudu gudu sauri sauri,sai data sake duba bilkisu cikin tsoro da firgici sannan ta haura dakinta ta yayibo hijabin sallarta tazo ta sake kamata zuwa cikin mota,sai data kwantar da ita sannan ta dawo ta dauki hisham daketa qwala kuka,ya zaci tafiya zatayi ta barshi,hankalinta a matuqar tashe,don ko abbaa batasamu damar gayawa ba saida suka isa asibitin aka karbeta sannan ta daga waya ta gaya mishi.


Jiki a sanyaye ta isa office din likitan tana fargabar wanne ciwo kuma keda bilkisun har haka,rabbi kada yasa wata mummunar cutar ce kuma ta daban ta kamata.


Cikin qwarara gwiwa abbaa da suka shigo tare ya dan taba kafadarta yana nuna mata wajen zama,don daya tashi daga office nan ya biyo,yaran kuwa tunda aka daukosu daga makaranta tasa aka wuce dasu gida wajen haule,ta isa inda ya nuna matan ta zauna abbaan yana binta da kallo,yasani cewa indai akan bilkisu ne raguwa ce,bata da wani jarumta ko qwarin gwiwa ko kadan,qaunar da takewa 'yaruwarta ce gaba daya ta tattarata ta koma kan bilkisun,batason duk wani abu da zai sameta,ya dade da shaida hakan tun bilkisun batakai haka ba,shidin bai zauna ba,saiya tsaya kawai saman kan zuhriyyan suna sauraren bayanin likita.


Dukka test test din da akayi mata ya tattara ya zuba cikin file dinta sannan ya dubesu
"Mara lafiyarku tana da aure ne?" Cikin mamaki anty ta dubeshi
"Me yasa ka tambaya likita?" Kafadarshi ya daga sannan yace
"Eh,na ganta da unifoarm ne,sannan sakamakon gwaje gwajenta kamar bai dace da yanayinta ba" cikin daure kai ta sake amsa mishi
"Bata da aure" saiya dafe goshinsa sannan yace
"Ya salam" kusan abbaa yaso gano meke faruwa,don haka yayi gyaran murya
"Amm,likita ta taba aure,sannan bata jima da rabuwa da mijin ba" yanayin fuskarsa ya sassauta,saiya saki goshin nasa ya dago yana dubansu
"Good....to tana dauke da juna biyu na sati goma sha biyu"
"What!" Anty zuhriyya ta fada cikin wani irin tashin hankali,har tana miqewa idanunta dukka a waje tana duban likitan,duk da shima abbaa sakamakon ya bugeshi,amma sai yayi hanzari kama hannun zuhriyyan
"Relax zuhra....likita" ya kirashin yana dubanshi
"Bilkisu bilyamin muke magana fa?" Kai ya gyada
"Yes,ba wadda kuka kawo da azahar ba student?,shi yasa na soma tambayarki before na gaya muku sakamakon,ba typhoid yanzu a jikinta,sai malaria 'yar kadan da kuma juna biyun da take dashi" ya sake karanto musu sakamakon bayan ya sake bude file dinta yana sake karanto bayanan da aka rattaba jikin takardar,sai daya qare sannan ya daga kai yana dubansu
"Bada ubanshi ba?" Yakuma tambayarsu cikin mamakin tashin hankalin daya gani saman fuskar anty zuhriyya,murmushi abbaa yayi
"Da ubansa,kasan shiriritar mata,saboda nasa tare da mijin kuma ga ciki shine abinda ya daga mata hankali" murmushi ya saki
"Hajiya qaddarar ubangiji ai tafi gaban haka,babban abun godiyar shine daya kasance ba shege bane"
"Hakane kam....mun gode likita" ya fada yana bashi hannu sukayi musabaha,sannan yaja hannun anty zuhriyya da tuni da daina ganewa ko jin abinda suka tattaunawa a kai.


Kuka ta fashe mishi dashi suna fita daga office din,ta dora kanta saman kafadarsa tana jin wani abu yana sukar zuciyarta,wannan zalunci ne,zalunci ne mai yawa,me yasa basuyi amfani da matakan kariya ba tunda sunsan ba zama zasuyi da ita ba donsu sauqaqe mata wahala,ta gama wancan zaman da yafi kama dana fursuna,sa'annan yanzu ga wata sabuwa ta bullo?
"Kiyi haquri zuhra hakanan don Allah,kaman yadda likita ya fada ne,mu godewa Allah daya kasance ba shege bane da ubansa"
"To meye marabar dambe da fada abbaa!" Ta fada a zafafe tana daga kanshi daga kafadarsa kai kace shine ya aikata dukkan komai,saiya saki murmushi,yasan kan kayarshi sarai,ya janyeta zuwa cikin motarsa yazaunar da ita seat din baya shima ya zauna gefanta,hannunshi ya saka cikin nata yana dubanta
"Nidai zuhrar dana sani jaruma ce gsky ba raguwa irin wannan ba,kin taba ganin bawa yayi kokawa da qaddararsa?,baki godewa Allah daya saka dan halas ne?,duk tsiya saida aka biya sadaki aka shafa fatiha sannan aka samar da cikin?,sannan wannan kukan da kike shi xaki ci gaba dayi har yarinyar ta farka ta gani,ki karya mata gwiwa kisake sata a zulumi,maimakon taga qarfafa gwiwa a fuskarki da rashin damuwa,wanda hakan shi xai qaranta tata damuwar da rungumae qaddararta,har a samu yadda akeso" cikin hikima da sanin makamar matarsa ya dinga gaya mata kalaman da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sanya mata kwanciyar hankali,sun jima cikin motar sai daya tabbatar yayi cooling temper dinta sannan ya qyaleta,saidai daga qarshe ta dubeshi
"Amma abbaa dole susan da zaman cikin nan" kai ya gyada
"Eh,wannan ya zama dole,kuma haqqinsu ne dama su sani saboda gaba" wannan din itama yayi mata,don haka ta gyada kai tana sauke ajiyar zuciya,saidai can qasan ranta tana jin zafi tare da baqincikin yadda suka sanya rayuwar 'yarta cikin walagigi bisa tsarinsu da kuma son zuciyarsu.


Bata koma dakin ba sai data tabbatar zuciyarta cikin kaso dari kaso hamsin ya sanyaya,don ko abbaa bai amince ba batajin wannan karon za'a musu shuru,gwara susan da abinsu,kuma koda ta haihu su dauki abinsu ita kuma taji da rayuwar 'yarta.


Tana tura qofar dakin idanunta akan bilkisu,ta waiwayo suka hada idanu,yadda ta kalletan sai taga kamar tasan yanayin data kuma fadawa,hakan ya karyar mata da zuciya,qwarin gwiwarta ya ragu,tausayinta ya kamata,ta fito daga wata jarrabawar yanzu gashi katsam ba zato ba tsammani ta fada wata,me yasa tun sanda ta dawo bata kawota an dubata an tabbatar babu ciki ba,da ta sani tun kafin abun yayi nisa da wala'alla an samu mafita akansa,qaddara ta tabbatar ita ta hana kawo bilkisun a bincikar mata lafiyarta da kyau.


Ta farka idinta biyu,saidai tana kwance a yadda take bata motsa ba,murmushi tayi mata sanda take tambayarta ya jikin nata
"Da sauqi ummi" yanda tayi.maganar sai ta sake ganin ta koma mata maimunatun ta,da sauri ta miqe daga kan kujerar da take kai jin qwalla na shirin zarto mata,ta isa ga drower din da abbaa yayi musu siyayyar kayan tea tana fito dasu,saida ta saisaita kanta sannan ta dawo.inda take tana duban ruwan da aka saka mata sannan ta maida kanta gareta
"Ya kusa qarewa,bari na musu magan suzo su cire miki ki samu wani abun kici" kai ta gyada mata ta juya ta fice ba jimawa suka dawo da wata nurse ta cire mata,ta taimakawa bilkisun ta tashi,duk da jirin da takeji ya ragu sosai.


Sai data kaita bandaki tayi alwala sannannta dawo ta shinfida mata abun sallah,yanayin anty zuhriyyan data canza ya bawa bilkisu mamaki,duk da batace komai ba amma ta lura komai da takeji jikinta a sanyaye yake,itadai bata tambayeta ba tahau abun sallar ta tada salla.


Sai data gama dukka sallolinta sannan ta zuba mata abinci tace ta matso taci,kaita soma kautarwa sabida wani tashin zuciya da amai data soma ji sanadin shaqar warin abincin,ta girgiza kai
"Bazan iya ci ba ummi" fuska ta bata
"Dole kici daughter,ta yaya zaki zauna ba abinci,kina so muyi fada kenan?" Kainta girgiza qwalla na cika mata idanu,tunda take bata taba jin irin wannan feeling din ba na batason ganin abinci kojin qamshinsa ba sai yanzu,kamar an nuna mata bindiga haka taji
"Kiyi haquri ummi,wallahi bazan iyac....." Bata qarasa ba amai ya taso mata,tahau yunqurin aman da babu abinda ya fito saboda babu komai cikinta,sosai ta galabaita,don har sai da nurse din ta dawo,ta mata wata allura sannan aka sake maida mata ruwa,ta lumshen idonta tana sauke ajiyar zuciya sanda take akwancen,don babu abinda tafi buqata irin kwanciyar,gefe guda kuma tana mamakin wanne irin ciwo ne haka takeyi?,azaba da wahalar da takeji bata taba jin irinta ba,a haka bacci ya sake daukanta,anty zuhriyya na zaune gefanta tana ta qoqarin boye hawayenta.
7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 42
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*
*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*
*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070




Tsayin lokaci yana firfitar gamida mai maitaba innalillahi,ita kuma tana zaune tana kallonshi tare da mamakin rudewar tasa,shi duka baiyi wannan lissafin ba,ko tsabar rainin hankali ne kawai.


A hankali ya aje hularshi gefe sannan yace
"Yanzu meye abunyi?" Baki ta tabe
"Bansan muku ba,tunda badani aka qulla ba,abinda na sani kawai shine,ta inda aka hau tanan ake sauka,kasan dukka hanyar da zakabi ka sanarwa da uban cikin ajiyarsu dake jikin 'yata,bama buqatar wani abu face su kwana da sanin akwai jininsu a jikinta" daga haka ta yunqura ta miqe,sai yayi saurin dakatar da ita
"Ya zaki tafi kuma?" Kallon banza tayi masa
"To ce maka akayi dama zama nazo yi?,saqo nazo isar maka,kuma tunda ya isa shikenan" daga haka ta juya tayi ficewarta daga falon,ta tsaya ta kirayi bilkisu suka wuce.


Tashin hankalin da bai tana zaton zaijishi ba shi yakeji,gumi ne kawai ke yanko masa ta kowanne sashe da loko na jikinsa,bai taba hasashe ko tsammanin faruwar hakan ba,bai taba kawo hakan zai iya faruwa ba,ko kallon mama ladi dake faman tambayarsa abinda yake faruwa cikin salon bugun ciki baiyi ba.


Zumbur ya miqe yana maida hularsa dake ajiye dafa'an a gefe saboda hasashen da qwaqwalwarsa ta bashi
"Ina zaka haka kuma malam?,wai wanne irin jarababben albishir wannan masifaffiyar matar tayi maka daya daga maka hankali haka,bayan nasan babu kalar abinda baka gani ba"
"Rayuwar 'yata....." Kawai ya fada yana yin gaba.


Yana tafe shi daya yana zancan zuci da qananun sumbatu,tabbas ta inda aka hau tanan ake sauka kamar yadda zuhriyya tace mishi,dole susan da zaman cikin,saidai bashi da wani yaqini ko tabbacin xasu amshi maganar,tunda sun riga tunda fari sunzo da dukkan sharudda nasu,shi kuma ya karba hannu bibbiyu ya amince musu,a lokacin da idanunsa suke a rufe,matsera yake nema kawai da hanyar da zai kubuta daka dukan da talaucin yake masa tako ina,bai tsaya wani dogon nazari ko tunani ba,sai gashi yau wannan al'amarin ya sameshi bagata tan.


Baiyi burki ko ina ba sai qofar gidan umma luba,wanda idan ka ganshi a yanzu ba zakace shi bane,saboda rushe mata shi akayi gaba daya aka sake mata sabon gini me bene,aka qawatashi da qaramin gate da fenti mai kyau harda shukoki,bayan umarar da sukaje tare da malam bilya din,da kuma kudade da aka danqa mata wanda suka isheta jari,bayan matsayi da fulani ta sake qara mata a masarautar kaisan.


Bakinsa cike fal da addu'ar Allah yasa tana nan ya sake gyara tsaiwarshi ga qofar gidan,ya kirayi wani yaro dake shirin giftawa,ba musu yaron ya qaraso da hanzari
"Shiga gidan nan maza kace ana sallama da luba" ya amsa mishi sannan ya tura gate din gidan ya shige,babu jimawa ya fito ya gaya masa tana zuwa.


Shudewar mintuna biyu aka taba qofar sannan aka budeta,umma luba ta bayyana,ganin malam bilya saita saki murmushi,har haqorin makkan data maqala yana bayyana
"A'ah,dama kaine.....aida ka shigo daga ciki ko?"
"Shigowar nan kuwa zata yiwu?,don gsky a gaggauce nake" cikin mamaki take dubanshi
"Koma meye ai shirin zaune yafi na tsaye ko?" Bai sake tankawa ba yabita a baya,basu tsaya ba har zuwa madaidaicin falon gidan,da aka qawata da kayan zamani.


Suna zama ta kira mai aikinta ta kawo masa lemo,don yanzun me aiki gareta,wadda take kula mata da gidan idan ya tafi gidan maimartaba
"Bar lemon nan luba.....babban tashin hankali ne ta tunkaroni ko ince ya tunkaromu" qirji ta dafe cikin razana ta fidda idanu
"Mun shiga uku!,wani abune ya faru?" Sai daya sanya gefan babban rigarsa ya sharce gumin fuskarsa,duk da sanyin acn dake falon wanda umma luba ta qure tana morewa jin dadin duniyarta,takan ce sai tayi qara'i yadda ya kamata,tunda hutun baizo mata a quruciya ba,yanzunma da yazo mata duk daya wai mamaci ya karye.


"Bilkisu 'yar wajena,mai gado,juna biyu gareta....juna biyun yarima"
"Tashin hankali!" Umma luba ta furta tana zama sosai saman kujera gamida fidda idanunta waje sosai,kamar wadda bata gani,zallar tashin hankalin data furta a bakinta yana bayyana qarara saman fuskarta
"Wannan wanne irin bahagon lamari ne,ya akayi haka ta faru?,me yasa dukkanmu bamuyi tunanin yuwuwar afkuwar hakan ba?" Ta qarashe maganar tana kallon malam bilya,karon farko a bigiren farko da yaji kishin jininsa,don haka saiya hade rai tsam,shima yaso yadan motsa qwanjinsa wannan karon ko yaya ne,kamar yadda yaga zuhiryyar tayi
"Oho,wannan kuma bani zaki tambaya ba,abu daya ne,kawai ki shaida musu abinda ke faruwa,so ake su sani kawai,bawai wani abu ake bida daga wajensu ba" shuru tayi tana juya maganarsa cikin ranta,kowanne daya cikin biyun zai iya yiwuwa,imma dai idan tayi shuru nan gaba har aka haife abinda aka samu ta shiga sahun masu laifi wajen fulani,wanda hakan zai jawo mata matsala,inma kuma taje ta shaida mata hakan ya zama tashin hankali ko kuma ya ballo da wani ruwan,to kowanne tayi ciki tana zato da kokwanton babu mafita,amma kuma da ace shurun tayi wani abun ya bullo bayan watanni suyi kuka da ita,gwara ta shaida musu tun yanzun sunsan da

Please Login or Register in order to submit comment