Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kansu,saita duqa saitinsu ya hadesu gaba daya cikin jikinta tana shafar kan amatu tana cewa
"Shikenan ya isa,kiyi shuru" cikin lokaci qanqani suka ware,ta sake musu wanka ta sauya musu kaya,sannan sukaci abinci suka fita falo,don yau gidan babu kowa,ateeq da najwa already suna makaranta,sai weekend suke zuwa hutu,abeed sun fita tare da babanshi,sai khadija dake barci abinta saboda ta rigasu dawowa daga makaranta,ba makaranta daya suke ba,nurain kuma yana bayan anty zuhriyya din.


Sai da suka fita sannan tayi nata wankan,ta zauna gaban madubi tana shafe lallausar fatarta da mayukanta da take amfani dasu,masu azabar taushi qamshi da tsada,tana duba saqon dr adam
"Na gode qwarai da kika gudu kika barni,amma dai duk da haka na godewa Allah daya bani ikon ganinki a yau,ina dokin zuwan gobe don na sanyaki a idanu na,ina kuma addu'ar ranar da zaki aminta na kawo miki ziyara koda sau daya ne a tarihin rayuwata" baki ta tabe,cikin ranta tana mita,tana kuma ganin iska na wahal dame kayan kara ne kawai.


Tana gama sanya rigarta tana shirin fita anty zuhriyya ta iskota
"Sannu da aiki bilkisu" tace da ita,koda batace komai ba tasan tana mata magana ne kan amatu,yaran na gaban goshinta ne fiye da kowa,ba'a tabasu a kwan lafiya,wani irin so take musu,kamar yadda hakanan suke da tarin farinjini wajen kowa dake baiwa bilkisu mamaki.


Bata amsata ba harta zauna gefan gadonta sannan tace
"Yanzu har amatu ta isa wannan fadan a wajenki?,yarinyar da batasan komai ba,batasan wacece ita ba?,nasha gaya miki dole kiyi haquri da wasu abubuwan da zaki dinga gani,ko munqi ko munso jinin sarauta ne su,akwai wannan jinin dake yawo a jikinsu kullu yaumin,zamu iya ganin halayya da dabi'u na izza da sarauta tattare dasu,wanda mu bamu isa mu cire musu ba tunda ahalin abunne,haka Allah S W T yaga dama ya haliccesu......so pls ki daina zafafawa da yawa haka,basusan komai ba su din,kada gudun gara ki fada zago,kici gaba dayin abubuwan da zasu sanya su saka ayar tambaya akan kansu"


Hakane kalaman anty zuhriyya,to amma itama bayin kanta bane,wani abun batasan tana wuce gona da.iri ba akansa har sai ta gaya mata,ita din kamar uwa take mahaifiya a wajenta,cikin sanyin jiki tace
"Zan gayara mami in sha Allah"
"Allah ya yarda,bari na qarasa naga kema kaman fitowa zakiyi"
"Eh mami yanzun nan,zan baki labarin wani yaro dana duba yau,ciwonshi akwai ban mamaki da daure kai" murmushi anty zuhriyyan ta saki
"Banga abinda a yanzu kikeso sama da aikinki din nan ba,kullum akwai sabon labari,kamar ba'a nan muka dinga dambarwa muna qoqarin tanqwaraki nida abbaa ban kan ki zabi bangaren" dariya sosai bilkisu tayi har herarrun fararen haqoranta suka bayyana kana tace
"Mami banda tuna baya fa"
"Oho dai" ta fada tana dariya gami da ficewa,itama saita juya gaban mudubin nata tana murmushi,ta jawo wani turare me kama da cream.ta lakata ta soma shafe hannayenta fatar cikinta zuwa wuyanta dashi,wani qamshi mai taushi ya soma tashi cikin mintuna qalilan,ta maidashi inda ta dauko kana ta dauki wayarta ta fito.
7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 50

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070




Kusan koda yaushe ta zauna takanyi tunanin me yasa ya kasa mantawa?,me yasa lamarin ya gaza gushewa daga tunaninsa duk da shekarun da suka soma gangarawa?.


Ko sau daya bata taba tuhumarsa ko sake tunkararsa da maganar ba,domin yabar maganar tun daga ranar data bashi zabi,ya kuma zabi yi mata biyayya,ya zabi ya faranta mata,ya zabi yabi abinda ta shimfida ta kuma tsara.


Bata manta irin wahalar da yasha a sannan shekaru bakwai baya,har hakan yaso karya zuciyarta,yaso yasa ta karya tsarin nata da hannunta,ya kusan sanyata ta maida hannun agogo baya ta kuma sauka daga kujerar naqin data hau,saidai daga baya ta qarfafawa kanta gwiwa,taci gaba da zama kan matsayin da take kai,duba da abubuwan da zasu biyo baya idan har ta biyewa son ran abdul'azeez din,cikin abubuwan da zata iya fuskanta din kuwa harda kunyata gaban abokan xamanta,wanda ta dade da sanin cewa bata da abokan gaba sama dasu,suna daga cikin mutane dake sahun farko farko dakeson ganin kunyatarta da tozartarta cikin masarautar.


Abu mafi girma kuma dayafi wannan tsanani shine.....hukuncin da zata fuskanta daga hannun mai martaba,wanda wala'alla dukkan wani buri daya dorawa azeez din ya karye bazai kuma sake dawowa ba.


Ci gaba tayi da kallon fuskar tashi sanda yake kusantowa inda take,tana ci gaba da tuna wasu daga cikin abubuwan da suka faru ya yarda ya kawo kanshi zai mata biyayya a sannan,saidai taci wahala ita kanta kafin zuciyarsa ta samu dangana,inda ta masa tukuici da abinda take ganin zai sake sanyashi yayi laushi ya kuma haqura,wato auren SAFWA,anyi auren irin wanda take buri,auren da labarinsa ya fantsama lungu da saqo na qasar,ya kuma bawa maqiya haushi da takaici,hakanan ya tayar da tarxoma tsakaninta da kishiyoyinta,suka dinga duban cewa kome akayi a bikin mai martaba ne ya tsaya musu,ya kuma yi musu barin dukiya fiye da yadda yakeyi aduk sa'ilin daya tashi aurar da diyoyinsa.


Murmushi kawai yayi,ba tare daya biyewa lamari na kishinsu ba,don ya fuskanci duk yadda zai musu bayani ba zasu fuskanta ba,dukkan wata gudunmawa daya dace ya bada ya bayar bakin gwargwado,sauran kuwa ya sani dukka tsarin aisha ne.


Abu guda ɗaya daya fuskanci basu fuskanta ba daga wajen aisha ba wanda yake da yaqinin da sun karanceta da abubuwa da dama.basu gallabi kansu ba dashi,wani irin salon kishi ta iya wanda takan iya dugunzumasu tunani a lokuta da dama,ta manna musu hauka ta kuma nuna kamar batasan ana yi ba.


Ako yaushe takan yi qoqarin yin abunda xai alamta musu cewa ita ce 'yar gaban goshinsa,koda a muhallin da ba hakan bane,aisha ce matarsa guda daya da bata taba yarda wani yagansu a rana shida ita,komai girman laifin da zai mata komai girman sabanin da zasu samu,zata fitowa ta nunawa duniya lau suke,basu da wata matsala,basu taba ma fuskantarta ba,yayin dasu kuma anasu bangaren basa iya haka,hatta da yaransu sukan samu masaniyar sabanin dake tsakaninsu,saboda qorafi rashin haquri da rashin iya yin shuru aduk sanda wani abu ya gitta tsakaninsu na rashin fahimtar juna,wanda ga aishan sam ba haka bane,bata iya yin haka,wannan yasa ta samu matsayi a wajensa da tazara mai girma tsakaninta da matansa,duk da cewa sun dan girme mata,sun kuma rigayeta kasancewa tare dashi.


Da fari ba safwa ba,ita kanta taci wuya da azeez din kafin a samu daidaito,su zauna zaman aure na haqiqa irin na kowanne ma'aurata,saboda canzawar hali da wasu daga cikin dabi'unsa,kafin daga bisani ta samu abubuwan su daidaita,saidai har a yanzun safwan bata samu kanshi dari bisa dari yadda taso ba,yadda kuma tasha qiyastawa zata samu,kamar bata gabanshi,kamar dole yake zaune da ita,kamar akwai dalilin da yasa yake zaune da ita,tayi dukkan abinda take ganin ya dace kuma zata iya amma har yau bata samu yadda takeso din ba,tayi haquri ta tattara ta zubawa sarautar Allah idanu,tana zaune dashi sabida darajar soyayyar da take masa wanda har yau bataga namiji kamarsa ba,hakanan babu wani haqqinta da bai saukewa,saidai akwai abubuwa da yawa da take da buqata daga gareshi fiye da wannan.



Kamar lokacinsa,kulawarsa tarairaya da soyayya ire iren wadda take gani ga turawa finafinai da litattafan turawa na soyayya,fara'arsa da walwalarsa ta zama wani abu mai tsada da wahalar samu a wajenta,amma dukka ta jure saboda soyayya.


Ajiyar zuciya fulani ta saki sanda yake isowa gabanta,ya qarasa a hankali yadan rungumeta ta gefab kafadarshi daya,tasa hannunta a bayanshi tadan bubbuga kamar qaramin yaro,tana jin babu dadi na yadda fuskarsa take a kullum babu walwala,ya saketa yana miqa mata gaisuwa cike da girmamawa,amsa mishi tayi cikin kulawa da fara'a,kafin daga bisani su wuce zuwa ciki daga ita saishi.


Katafaren teburin cin abinci ne da aka cikashi da kalolin abinci nau'i daban daban na alfarma,da kanta fulani take serving nashi duk kalar abincin dake wajen,harta kammala yana biye da ita da idanu baice komai ba,ta tura komai gabanshi taja kujera itama ta zauna bayan ta tsiyaya tataccen matsatstsen ruwan 'ya'yan itatuwa tana kurba a hankali,idanunta akanshi.


Sam bata qaunar wannan shurun nasa daya sake zame masa dabi'arsa kuma jinin jikinsa,ta aje cup din tana sakin boyayyar ajiyar zuciya
"Sai yaushe ne su safwan zasu wuce?" Cikin mamaki ya daga kai yana dubanta,kana daga bisani ya cire farin eye glasess din dake idanunsa,yana jin ranshi na baci kadan kadan,kada dai ace wucewarta tayi ba tare da sanin ammin ba
"Tun inacan mukayi waya da ita cewa jiya zasu tafi,ban samu dawowa a jiyan ba shi yasa na gama musu komai daga can.....bata shaida miki ba kenan?" Murmushi kadan ammi tayi,tana jin ranta yana son ya soma baci kan wasu baqin halaye da bata so daga safwan,amma batason ran nata yakai ga baci har azeez din ya karanci hakan,tunda ko babu komai tafi kowa sanin cewa zabinta ce ita din
"Eh to....wala'alla don kada suyi missing flight ya sanya bata tsaya munyi sallama ba" sosai ranshi ya sake baci,koda bata zo ba ai a qalla ta kirata ta gaya mata ko?,baice komai ba ya ciro wayarshi daga aljihun gaba rigar suit din dake jikinsa ya soma neman layinta na brasil,dai dai sanda ammi tace
"Ba wani matsala bace,dama kawai naso na hadasu da sodangi ne,saboda yanayin kula da suhaima din,fata dai Allah yasa aje a sa'a kawai" bai tanka ba yaci gaba da neman layin,duk da yasan cewa ammin tanason dakatar dashi ne.


Qin shiga layin yayi,yayita qoqarin nema bai samu ba,ya tabbatar idan da sun isa ko bai shiga ba zai nuna masa alamun suna qasar,to babu wannan alamar,don haka saiya sauya akalar kiran nashi zuwa ga lambarta ta qasar nan.



Ga mamakinsa sai gashi kiran ya shiga,cikin mamakin ya kasa kunne yana jira yaji me zai faru,babu dadewa aka daga,muryar safwa ce tas tana fadin
"My prince....ka iso kenan?"
"Kina ina?" Ya jefa mata tambayar akwai alamu na bacin rai cikin sautin muryarsa,cike da rashin damuwa da nuna halin ko in kula tace
"Ina gida"
"Wanne gida?"
"Gidanmu wajen mom" idanunsa ya lumshe kana ya budesu,yana son yayi controlling fushinsa
"Ina suhaima?"
"Urppp.....sun wuce ita da mama rahama....zuwa jibi zanbi bayansu,idan ban samu jirgi ba kuma next week,kafin sannan sun gama settling na komai ko?" Kamar zuciyarshi zata fito haka ya dinga ji,magana da itama tamkar bata lokaci ne,don haka ya kashe wayar kawai ba tare daya ce mata komai ba,amma ya sani cewa saiya hukunta tata.


Ya rasa wacce irin uwace ita da har yau batasan cewa ita din uwa bace,har yau kallon kanta take a safwanta,shagwababbiya 'yar lelen daddynta da mom dinta,bata iya raino nuna kulawa ko tattalin diyar da Allah ya bata ba,baya manta gwagwarmayar da aka sha kafin ta haife suhaima,kullum cikin kuka raki da tsoron ba zata iya haihuwa ba itakam,an gaya mata akwai wahala da ciwo,amma bai zaci wannan banzar halayyar shagwabar mara amfani zata ci gaba da bibiyarta ba,son jiki da rashin son yin komai,sai shegen son soyayya kamar wadda laila da majnun sukayi cikinta.


Duk idanunsa a lumshe yayi wannan tunanin,muryarshi can qasa yace
"Zan soke duk wani abu da nazo yi,zan bisu gobe in sha Allah"muryar ammi da tuni ta gama jin komai ta katseshi
"Ka qarasa dukkan aikinka....babu wata matsala,ka yankarwa kubra ticket zata bisu,bayan ta isa zan tura sodangi taci gaba da zama da ita,har sanda za'a sallamesu", kai kawai ya kada baice komai ba,wannan bacin ran ya hanashi cin abinci,duk da dama cin abincin nasa ya zama sai a hankali tun lokuttan baya,amma saboda ammin ya daure yadan tsakuri wani abun.


Kiran wayarshi da abdulrashid yayi shiya tadashi,ya yiwa ammi nuni da yana zuwa,ya fice yana amsa wayar.


Bai gama ba har ya isa sashensa,wanda yake a gyare tsaf bayan gyara na musamman da aka masa,aka kuma sauya fasalin tsarinsa da gininsa,ya sake dacewa da zamani,wanda ba qaramin kudi aka narkar ba
"Ka jirani kawai,fitowa dama zanyi yanzun" azeez din ya fada yana katse kiran,lokaci guda kuma yana cire kayan jikinsa sannan ya shige bandaki.


Gaba daya ya baiwa business dinsa muhimmanci da lokaci fiye da komai cikin rayuwarsa,yana jin shine abu guda daya da zai dinga debe masa kewa da rage masa damuwa.


Minti talatin cikakku ya fito cikin rigar wanka,ya samu wata kujera dake daura da gadonshi ya zauna yana goge ruwan jikinsa,a hankali idanunsa suka sauka kan wani dan mitsitsin frame mai matuqar qanqanta dake maqale jikin drower gefan gadonshi,idanu sosai ya zubawa frame din,tsahon wasu sakanni sa'annan ya lumshe idanunsa yana jin yadda bugun zuciyarsa ke dada gudu,ya miqa hannunshi a hankali ya dauki frame din yana dubanta.


Tsahon wadan nan shekarun babu wani abu da ya ragu tattare da ita a zuciyarsa da rayuwarsa,saima qaruwa da yayi,ya sake habaka zuwa wani mataki na daban,kullum yanaji wani sashe na zuciyarsa na faduwa yana rugurgujewa idan ya tuna da ganin da yayi mata na qarshe,duk da yadda kullum kwanan duniya yake qoqarin danne zuciyarsa to amma yana ji a jikinsa,yana kuma tsoron ranar da zuciyar tasa zata bijire,ranar da zata bi karbar umarnin ammin,ranar da zata bijirema dukkan wani umarni.


Cikin jikinta fa?,tambayar da idan ya yiwa kansa yakejin kamar zuciya da qwaqwalwarsa zata fashe,yana jin kamar zuciyarsa zatayi bindiga,dukkan wani bin diddigi da binciken inda take har yanzu bai samu komai ba,bai samu wani qarin bayani ba da zai masa jagora ko ya bashi hasken ina take?.


Jin ya soma shiga wani yanayi wanda idan ya shiga din yakan kwana biyu a birkice ya sanyashi maida hoton ma'ajiyarsa kana ya miqe yahau shiryawa,saidai duk da hakan qwayar idanunsa tuni ta jirkice ta sauya kala,wannan dalilin ya sanya koda ya gama shiryawa ma baqin glass ya sanyawa idanunsa a maimakon fari yadda ya saba,yana ganin kiran safwa ya share,ya sani idan har ya sake ya daga to sakamakon da zai biyo baya bazaiyi musu dadi ba dukkaninsu daga shi har ita,ganin kiran nata ma sake qona masa rai da dugunxumashi yakeyi,don haka ya antayata a black list,wanda ba wannan ne karon farko da irin hakan ke faruwa ba dama,da zarar yaga alamun zata shiga rayuwarshi,abubuwa da dama tana cin daraja da mutuncin ammi ne,da tuni ya sanya kakkaifan gatari ya datse duk wata igiyar alaqa da tayi saura a tsakaninsu,wanda hakan da zai faru sai yafi kowa samun sukuni tare da ci gaba da fuskantar rayuwarsa.


Nannauyar ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar azeez daga falon,tana mamakin halayen safwan wanda ada bata santa dasu ba sai a yanzun,tana jin ba dadi da yadda ta zama wata rabin mutum,wadda tsabar gata da sangarta yasa bata iya tsinanawa diyarta ko mijinta komai,komai zatayi saida taimakon ma'aikata da barori,gaba daya yarinyar kamar ba jininta ba,kamar ba ita ta haifeta ba,bata fiya damuwa da matsaloli da sabgoginta ba sai idan abubuwa sunci tura,gaba daya safwan tazo mata ba'a yadda ta zaceta ba,duk wani data xata daga gareta babu shi,badan badan ba.


Bata jima da jin zancan cewa ta gama haihuwa da safwan tace tayi ba,don tana tsoron mutuwa,mutum biyu ne suka mutu ranar da taje naqudar suhaima a gaban idanunta,to ba zata sake ba bare a wuce da ita,tun tana daukan abun barazana da tsoro da wasu matan kan shiga a lokacin da suka haihu,harta fuskanci da gasken gaske take,tunda har zuwa yau da yarinyar keda shekara hudu bata sauka daga kan qudurinta ba,babban burinta na gaba a yanzu shine ayita haifawa a zeez din yara maza,ta yadda ko nan gaba kambun sarauta da gadon maimartaba bazai bar jikinta ba,ta lura mahaifiyar safwan itama sam bata iya tsaiwa tayi mata wani fada,data soma taga ran ya baci koya sakar mata kuka shikenan an wuce wajen,ba don tana duba wasu abubuwa ba da babu shakka ta sakewa azeez din aure,saidai akwai abubuwan da take dubayya dasu,shi kamsa azeez din tana da buqatar ganin dawowarsa cikin mode dinsa na baya.


Daya daga cikin katafaren kamfaninsa dake da mazauni cikin garin kaisa ya nufa,ziyara ta bazata don babu wanda yasan da zuwanshi,hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,saboda sun san cewa qaramin kuskure zakayi a yau din yayi maka sanadiyyar rasa aikinka.


Ba wanda baisan halinsa ba tun daga sanda ka soma aiki dashi kama yau,mutum mai zafi fushi fusata da tsautsarar ra'ayi,sau da yawa abdulrashid kanyi mamakin yadda ya koma ayau,saidai idan ya tuna girman abinda ke damunshi a rayuwa saiya bashi uzuri,sauda yawa shike qoqarin fahimtar da ma'aikatan kan cewa ba haka halayyar yariman take ba,akwai abinda ya sauyashi,sukan jishi ne kawai,don a haka suka sanshi,kuma a haka suke ci gaba da ganinsa har kwanan gobe basu ga wani abu daya sauyashi ba.


Ya jima sosai cikin kamfanin yana duba abubuwan da suka dace ace ya duba din,a ranar wadanda tsautsayi ya rutsa dasu da yawa sun rasa aikinsu,saidai abdulrashid daya dinga fansarsu kamar yadda ya saba,ya sallamesu da jarin da xai ishesu su kama sana'a.


Sai dare suka koma gida tare da abdulrashid din,don basu gama tattaunawa ba kan abinda ya hadasun,har yanzu ranshi a jagule yake,baya ga mode dinsa na yau da kullum kuma sai case din safwa,abun yana damunshi sau tari,amma a gaban ammin wasu lokuta yakan nuna bai damu,tunda yasan kome ma zatayi zabin ammin ne,abinda ta zaba mishi kenan,duk da cewa duk lokacin da tayi katari yana kan tsininsa baya daga mata qafa ko yi mata da sauqi.
7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 51

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070



A gaggauce take fitowa zuwa ainihin falon gidan don ta samu abinda zata sanyawa cikinta kafin takai ga fita zuwa asibiti,wanda ayau din tana da tarin ayyuka,ciki harda aiki da zata yiwa yara uku,ba sabonta bane makara sam shi yasa gaba daya hankalinta yayi gaba.


Duk inda ta motsa qamshi ne mai taushi da sanyi yake fita a jikinta,musamman idan kana daura da ita,duk shigar da tayi kyau take mata,musamman shigar da takanyi wadda ke killace komai na jikinta,ba zaka iya ganin komai na jikinta ba,daga fuskarta sai hannayenta,koda qafafunta ma tafi ta'ammali da irin takalman nan da ake kira da half cover,dr bilkess kenan,mace mai aji,wadda ba iya maza kawai take tafiya da imaninsu ba,hatta 'yan uwanta mata takan burgesu qwarai,da yawa su buraci dama sune ita,ba tare da sunsan tsinin data taka ba kafin takai ga wannan bigiren da take kai.


Babu kowa a falon,dama ta zaci haka,saboda yayi safiya da yawa,don haka ta shiga kitchen ta samu ruwan zafi a kitchen,ta zuba mishi kayan qamshi,sannan ta bude fridge ta dauki samosa fresh one guda uku ta soya,tana daga tsaye ta soma gutsira tana ci,don idan ta fita din ba kasafai take cin abinci a waje ba,har sai ta dawo gida.


"Mamiiiii" taji an fada daga bayanta,ko bata juyawa ba tasan muryar amatu ce,ta waiwaya bayan ta gama wanke hannunta tana gogeshi da tissue tana dubanta,sanye da wani riga da wando pink,wanda yau tashin wurin data yi ya sanya tana gama wanka itama tayi mata ta shiryata,tace ne ta kwanta ta koma bacci abinta sai gashi ta sake biyota,tun daxun dama take nacin zata bita asibitin
"Ya kuma akayi?" Ta tambayeta tana tsareta da ido,saita langabe kai tana shirin sakin kuka
"Please mami,kinmin alqawari fa rannan....don Allah mami na rakaki don Allah" shuru ta danyi,sam batason fiya son zuwa dasu asibitin ba,wani irin farinjini yaran keda shi,wanda yawanci.idan taje dasu asibitin ma basa zama waje daya,daga wajen wannan sai wancan,shi yasa da wuya taje dasu din,saidai yanayin yadda amatun keta mata naci ya karyata,dole ta koma ta sauya mata kaya sannan suka fito tare suka fice.


Suna isa kuwa ta soma jawo mata idanun jama'a fiye da da,wadansun sun santa dama kuma suna son magana da bilkisun babu dama,wasu kuma ganin farko ne,da haka ta samu ta janyeta zuwa office dinta don karta bata mata lokaci.


Minti arba'in da wani abu ta gama shirin shiga surgery din,duk yadda dr adam yaso tabar amatu wajensa amma saita zame,ta hadata da wata nurse dinta mace,don ba zata iya barin mishi diyarta mace ba,duk da cewa bawai tana zarginsa bane,amma tarbiyya ba abar wasa bace,kuma sam bata taba wasa da tarbiyyar yaranta ko qanqani.


Cikin nasara kamar kowanne lokaci ta aiwatar da duka surgery din,bayan ta fito ta daura alwala cikin office dinta tayi sallar nafila raka'a biyu don nuna godiyarta ga Allah kamar yadda ta saba a duk sanda ta gama aiki haka successfully.


Bata jima da idarwa ba,amatu na gefanta tana wasa aka nemi izinin shigowa ta bayar,john ne,tunda ta ganshi tasan magana ce kan wani mara lafiyan,ta saki murmushi tana cewa
"Badai xaku barni na huta ba ko?" Shima martani ya mayar mata kana yace
"Naga kamar kin manta da patient din da kika ce idan sun iso a basu gado,kuma patient ce mai muhimmanci a wajenmu kamar yadda kika sani" baki tadan tabe kadan
"Wannan patient kuna ji da ita,ban manta ba,dole saina kammala komai kafin na ganta,yanzun haka ina dab da zuwa dakin,ba room 1 bane"
"Eh madam" ya amsa mata a ladabce,kai ta gyada yayin da shi kuma ya juya ya fice.


Sai data gama komai sannan ta maida kayanta,ta nada mayafinta da kyau ya zauna mata ta koma neat kamar yadda ta shigo asibitin sannan ta kama hannun amatu suka fito.


Dab da zata isa dakin wayarta ta dauki ruri,ta dakata tana duba mai kiran,nabila ce,qawa guda daya tilo aminiya datayi tsayin shekarun anan qasar brasil,wadda itama zuwau ce kamar ita,saidai Allah ya hada jininsu,ya saka qawance mai qarfi tsakaninsu
"Qawa kada dai ace ba zata kikamin kin dawo?" Inji bilkisu,daga can daya barin akayi dariya
"Kedai bari qawa,mamaki naso baki" daga haka suka soma hira wadda tadanja lokaci kafin suyi sallama,bilkisu ta aje wayar tana murmushi,a sannan ta lura da amatu bata wajen,tadan dudduba bata ganta ba,tasan wajen babu hanyar fita,tafi kyautata zaton ta shiga dakin da sukazo,don haka tayi gaba zuwa dakin,ta murda qofar ta bude kana ta tura kai ciki.


Tun kafin ta gama shiga ta jiyo muryar amatun rai rai,a hankali idanunta suka sauka kansu,su biyu ne zaune gefan gadon mara lafiyas,amatu da yarinyat da duka duka alamu ke nuna ba zata wuce shekara uku ba,sai nurse dinsu dake zaune gaban gadon saman kujera,riqe da cup da plate na abinci tana lallabar yarinyar ta karba,daga can wata kujerar kuma wata macace zaune tana fuskantarsu.




Please Login or Register in order to submit comment