Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taga shigowar wasu matasa,wanda da alama ma'aikata ne,kamar a inuwar taga ana fidda dukka kayan gado da aka qawata dakin dasu,eh kamar inuwa zata ce,tunda hankalinta bai jikinta bare ta tantance inuwa ne ko zahiri ne.

Tamkar mutum mutimi haka take zaune cikin falon gidan,daga kunnuwanta har idanuwanta basa iya ganin komai,basa kuma gane kome face mai rayuwarta ta gaba zata haifar mata.


Hannunta na dama dunqule yake da takardar data zamto tamkar wani mubudi ne na rayuwarta ta gaba,takarda ce da saqon dake ciki take jinsa daidai da saqon ranar mutuwarta,riqonta kawai zafi yake mata tun daga tafin hannunta har zuwa qwaqwalwa da zuciyarta,yakuma zarce zuwa ilahirin jikinta gaba daya.


Duk da cewa tana tsammanin zuwan ranar,duk da cewa tasan cewa lallai lallai komai daren dadewa irin wannan ranar tana tafe,takuma shirya zuwanta tun daga ranar da aka soma lissafin kasantuwar kwanakin har zuwa randa zata risketa,saidai batasan me yasa ba,meye dalilin data tabata har haka ba,batasan meye dalilin da jikinta da zuciyarta suka girgiza har haka ba,sabone?,ko kuwa tunanin me gobenta zata haifar mata ne?,meye matsayinta meye sakamakon rayuwarta?,wanne sabon shafin zata bude?


Karo na qarshe ladingo tafito tafito da akwatinta da take jin shine abu na qarshe a cikin dakin data mallaka,ta qarasa inda take aje musu kayansu shima ta ajeshi,ta qarasa gaban bilkisu ta tsaya cikin rusunawa
"An gama fitar da komai,ance jirgin qarfe sha biyu zamu bi,yanzu haka mai motar dazai daukemu zuwa filin jirgin yana kan hanya...."


Qwaqwalwarta tajiyo wani sashe na maganarta,saidai bata fahinta duka ba,cikin jimla guda ta tattara maganartata,qwaqwalwarta ta sake aika mata da saqon
"Tafiya zakuyi,zaku koma nigeria,zaki kuma cikin gidanku".


Tamkar wadda ake bawa umarni sai kawai tamiqe,cikin qarfin hali tasanya hannu tagyara zaman qaramin hijabinta,kana tasoma takawa a hankali kamar mai tafiya saman qayoyin da aka shimfidawa hanyarta tayi hanyar bedroom din daya zama shine matattarar dukka wani tarihi nata.


Idan ka kalleta a sannan zaka iya rantsewa tashigo dakinne tana son fayyace da ainihin qasar wanne waje aka gina dakin saboda yadda takebin kowacce kusurwa ta dakin da kallo sama zuwa qasa da kallo har na tsahon wasu daqiqu.


Sauke idanunta tayi awani sashe can na dakin,tasoma takawa a hankali kamar wadda maganadisu yake janta zuwa arean,tasa hannu tasoma shafa wajen,yana yawan tsaiwa a wajen duk da cewa cikin duhu take ganinsa,yana son wajen sosai duk da bata taba ganinsa muraran ba,saita sake matsawa da jikinta wajen,ta lumshe idanunta tana shaqar daddadan qamshin da wajen yake fitarwa,tabbas qamshinsa ne,abinda duk cikin rayuwar datayi mai kama da mafarki tafi riqewa,saikuma qaqqarfar ajiyar zuciya wadda tasaka dukkan gabbanta suka saki,hawayen da uta kanta batasan na meye ba suka ziraro daga idonta guda daya.


Kamar wadda aka tsikara tajuya da sauri tanufi qofar ficewa daga dakin,dakin da zuwa yanzu yakoma zallar kangonshi babu komai ciki tamkar wasu rayuka basu taba wanzuwa a ciki ba,batasan inda kayan suka koma ba tunda dama ba mallakinta bane.


Girgiza kanta take dasauri tana gayawa kanta,tabbas bata tsira da komai ba,babu abinda ta tsira dashi koda kuwa hoton fuskarsa ta zahiri ne face ragowar qamshinsa daya barwa hancinta da qwaqwalwarta tabonsa.


Cak ta tsaya tana duban gabanta,kana ta duqa a hankali takai hannunta tadauki zoben daya dauki hankalinta qwarai,zobene da tasha ganinsa a yatsunsa,abun guda daya tak datake iya banbance dangane da duk wani abu daya shafeshi,cikin sauri tadauki zoben ta damqe a hannunta kana cikin sassarfa tafice daga dakin ta zarce da ficewa daga gidanma gaba daya don tanaji cewa izuwa yanzu itama ya kamata ta yanke dukka sauran abinda yayi saura.


Tanajin ladingo na mata magana saidai bata ko tsaya ba bare ta waiwayo ta dubeta,fatanta shine ta raba kanta da komai daya wanzu a shekara guda,ta yanke dukkan wani abu dake da alaqa da shekarar........


********** ***** ********


Tana zaune daga guri na musamman da aka tanada saboda xaman baqi,daga gefanta kuma maimartaba ne sarkin qasar kaisa,daga hannunshi da nata hannun yaransu kowanne zaune a mazauninsa,dukkaninsu sun bada hankalinsu dari bisa dari kan taron da ake gudanarwa,farinciki ya lullube zuciyar kowannensu na ganin yadda dansu kuma yayansu yaketa karbar lambobin yabo da girmamawa kala daban daban.


Kamar yadda a tsarin shiga kyan halitta,kwarjini da kuma wata irin ginshira tasa ya fita daban da sauran daliban,hakanan ma ta fannin hazaqarsa suna gamida shahararsa cikin makarantar,farinjininsa daga wajen malamai har zuwa dalibai.


Fuskar fulani aisha tamkar gonar auduga,zuciyarta fes kamar dutsen qanqara,har hakan ya gaza boyuwa ya bayyana saman fuskarta,jerarrun fararen haqoranta irin na azeez sun bayyana kansu saboda irin murmushin da takeyi,ko iya yanzu ta tabbatar da cewa azeez din yayi zarra,yakuma fara taka irin matakin da takeso ya taka,tauraruwarsa ta haska ta danne ta kowa,sunansa ya shahara yakuma fantsama ko ina,inama ace adama tazo wajen batayi qaryar bata jin dadi ba?,koda yake koda adama batazo ba,ta tabbatar afra zata bata labarin dukkan abinda ke faruwa,uwa uba akwai waya a hannunta tana nadar komai.


Wasu qwallar farinciki ne suka so fitowa daga idanuwanta a lokacin da aka buqaci mahaifinsa ya taso makaranta zata girmamashi saboda irin gudunmawar daya bayar,da kuma kyakyyawan misali daya baiwa dalibai,hakanan yasa makarantar tasake samun daukaka da suna,bayan maimartaba ya isa wajen sai azeez din ya nemi alfarmar mahaifiyarsa ta taso,sosai ta dinga jin farinciki,tana jin cewa taqi kadan ya rage burinta ya gama cika.


Awa biyu cur akayi kwashe ana gabatar da taron kafin a kammala,har yanzu farinciki yaqi barin zuciyarta,cikin sigar xolaya mai martaba ya dubi fulani aisha
"Ke ko 'yar karan nan ma babu,kinga fuskarki kuwa kamar gonar qanqara?" Cikin dan jin nauyinsa tadan sunne kai kadan tana dariya qasa qasa kana tace
"Bazan iya boye farinciki na ba,don abdul'azeez bai bamu kunya ba,yayi dukkan abinda yakawoshi qasar nan,harma fiye da abinda muka zata" kai.ya jinjina shima yana sake jin dadi,alfahari da tilon dan nashi namiji yana ratsashi.


Daga mazaunin dalibai maza kuwa kamal ne zaune kamar ruwa ya cishi,duk wani motsi na azeez din yana kan idanunshi,jin zuciyarsa yake kamar zata babbake ganin yadda yaketa samun lambobin yabo daga bakunan malamai kala kala,ya tabbatar wannan labarin bamai dadi bane akunnen mahaifiyarsa,ya rasa kuma meye hana fulani adama zuwa wajen,bayan mom ta shaida mishi tana qasar,kuma zata zo.


Can wani sashen kuma daga rukunin mazaunin daliban dai minal ce zaune,ita dinma idanunta hankalinta da tuaninta yana ga azeez din,wani daci take ji cikin ranta da zuciyarta na yadda tayi loosing oppurtunity dinta,na yadda ta rasa azeez din,duk da ta taki babbar sa'a da bai sake tada case din ba,bai kuma sake nemanta kobi ta kanta ba,duk da cewa a hakan tana boye kanta daga gareshi,kada wataran su hadu ya tuna allura ta tono garma,wai shin me zatayi azeez ya sota kamar yadda take buri?.


"Guy din nan ya gama haduwa,komai yaji,Allah ya masa komai" ta tsincin furucin na fitowa daga bakin wasu 'yammata dake zaune gefanta,saita waiwaya tana dubansu,ji tayi wani abu ya tokareta,kamar ta miqe ta shaqesu ganin yadda suke binsa da kallo duk inda ya motsa kamar wasu tsaffin mayu,dole ta janye idanunta daga kansu tana jan tsaki mai qarfi a fili,wanda sai daya sanya qawarta ta waiwayo tana dubanta gamida tambayarta,saidai bata bata amsar komai ba.


Lokacin tashi nayi kamar yadda aka tsara a rubuce aka qarqare komai,a nan dalibai suka soma musayar adress da lambobin waya gamida daukar hotuna a tsakaninsu.


Haka ce ta faru ga azeez,mutanen dake son daukar hoto dashi....musayar lambar waya da amsar adress suna da yawa,harda 'yan shishshigi,harda wadanda shi bai taba hulda dasu ba,iya mutanen da suke selective a wajensa ya tsaya sukayi wadan nan abubuwan ya qara gaba wajen da motocinsu ke fake ya barsu a wajen.


Me martaba ne cikin motar,sai ammi a ciki,sauran duka suna wata mota ta daban,yana shiga maimartaba ya dubeshi cikin murmushi
"Wadan can mutanen da suka jiraka fa?" Sai daya waiwaya ya dubesu ta window sannan cikin girmamawa yace
"Allah ya taimakeka.....na gama sallamarsu" murmushi kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba,ya riga da yasan hali xanen dutse,har yanzu halayyarsa tana nan a jininsa,tun zamanin shekaru qananu har yanuzu da aka doshi shekara ta ashirin da shida.


Lokacin da drivern ya tada motar suka fara tafiya mai.martaba yayi gyaran murya,kana cikin sautin muryarshi dake nuna tsantsar hikima,dattijantaka da kuma kamala yace
"Babu shakka duk baiwar da dan adam yaga ubangijinsa yayi masa....yayi masa itane bawai don yafi kowa ba,a'ah,yayi masa itane saboda shi din mabuwayin sarki ne,yakanyi abinda yaso a sanda yaso a kuma lokacin da yaso,dukkan wata baiwa a rayuwa tamkar jarrabawa ce ga bawa,yakan iya cinyeta,yakan iya kuma afkawa zuwa ga halaka idan baiyi takatsantsan ba,abdul'azeez...,zuwa yanzu girma ya soma hawa kanka,tunda gashi har ka soma aje wani mataki na karatu,shekarunka kuma sun bar ashirin da biyar sun soma tsalle zuwa da shida,ina fatan zaka zama mai nutsuwa da nazari a duk yanayi matsayi ko matakin daka samu kanka,ka zama cikakken mutum mai kamala da adalci,sannan kuma adali a duk wani sha'aninsa,hakan zai baka dama ta gina inga tacciyar rayuwa,ka samu iyali na qwarai,ka auri matar da bazata zalunceka ba kamar yadda kaima ya haramta ka zalunceta,wannan shine matakin rayuwarka ta gaba" hakanan yaji wani irin yanayi ya shigeshi,cikin girmamawa ya furta
"In sha Allahu".


Murmushi fulani aisha tayi tana qoqarin danne yanayin data shiga
"Allah ya taimakeka nasihar tun yanzu?,da ka bari ai mun qarasa gida kun huta tukunna sai kuyi xama na musamman" dubanta yayi shima yana murmushi
"Kinsan hausawa sukace da zafi zafi akan bugi qarfe,kuma kowacce magana akwai muhallin daya dace ayita" kai ta jinjina kawai tana kau da kanta gefe,sai takejin kamar wata qusa ya kafa mata.


Tans jinsu suna magana jifa jifa da azeez din har suka qaraso gidan,wanda babu kowa ciki sai fulani adama da fafur ya qirqiri ciwon qarya,saboda baqinciki da bacin rai mai martaban da kanshi ya tako zuwa bikin,saboda tsantsar soyayya d kulawar da yakewa azeez din kenan?.
7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 37
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*
*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*
*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070
____________________________


A duban farko idan kayi masa,zaka tsammaci wani ciwon ne yake damunsa,saboda yadda yaketa safa da marwa cikin dakinsa,daga wancan bangon zuwa wannan,lokaci lokaci yakan sanya hannunsa saman sumarshi ya shafi kansa,yanajin qwaqwalwarsa tana matuqar daukar dumi da caji.


"Why?,me yasa?,me yasa?,me yasa ta kasa barin tunani da qwalqwawarsa?,me yasa tun bayan nan bai taba kwanciya peafully ba ya tashi haka?,me yasa duk wani motsi nashi second ko minti saita ratsa ta ciki ta tuna mishi da kanta?,yana tsammanin komai is over kuma komai ya wuce,amma baisan me yasa wannan ya kasa wucewa ba,me yasa wannan memory din ya kasa shafewa ba.


A hankali ya maida akalarsa zuwa bandakinsa,ya tsaya gaban famfo ya watsawa fuskarsa ruwa mai sayi sosai,har sai dayaji zuciyarsa na kwanciya,sannan ya jawo daya daga cikin qananun towel din dake jere raras ya goge fuskarsa da kyau ya wurgashi gefe ya fito.


Yana shirin komawa yazauna don ya ragewa kansa kai da kawon da yake kamar sojan dake fareti yaji ana knocikin qofar dakin nasa,ko waye ma yasan wani makusancinsa ne kuma mai muhimmamci,tunda har ya ratsa dukka falukan ya qaraso bedroom dinsa,don haka yana daga tsayen ya bada damar a shigo.


Abdulrashid ne,wanda shima cikin satin ya kammala nashi karatun ya dawo qasarsa garinsa kaisa,idanunshi saman azeez yana dubanshi bakinsa dauke da sallama,saiya waiwayo shima yana dubanshin lokaci guda kuma yana amsa sallamar.


"Ya na ganka haka ko shiryawa bakayi ba?" Kanshi ya daga yaduba lokaci sannan yaja qaramin tsaki,ya soma takowa bakin gado inda abdulrashid ya yiwa kansa mazauni
"Nayita kiranka kafin na shigo ina wajen ammi,itama ta kiraka amma no answer....."
"Bacci nayi" ya amsa mishi a taqaice yana miqa hannu ya janyo wayarsa dake gefan filon daya tashi akai,abdulrashid ya bishi da kallo sanda yake buda wayar yana duba miscal din dake ciki
"Ammi ta gayamin cikin kwanakin nan kamar kana cikin damuwa?....what's going on?" Ya tambayeshi still yana kallonshi,saidai shi hankalinsa na bisa waya,miscal dinsa dana ammi ya soma tararwa,saina wani abokin karatunsa sannan na safwa,yakuma sakin tsaki kana ya maida wayar ya aje,banda ya mata alqawarin zuwa yau din,baijin akwai abinda zai fiddashi,hakanan yakejinshi cikin mode din da baison magana da kowa
"Just thirty minutes,yanzu zan shirya" ya fadi a maimakon ya amsa mishi tambayarsa yana nufar bandakin,sake dai binsa yayi da kallon,ba shakka akwai abinda yake damun nashi,duk da dama tsabar miskilancinsa yasa idan baku dade ba ko baka karanci yanayinsa ba zaka tsammaci ko yaushe cikin damuwar yake.


Sai daya shafe kusana wanni guda sannan yasoma shiryawa cikin wani tattausan yadi mai kyau da tsada,wanda yabi lafiyayyar fatarsa ya kwanta dakyau,yana cikin fesa turare abdul yasake masa tambayar,saidai baice mishi uffan ba,alamun dake nuna baida sha'awar su tattauna kenan,sai daya gama sa'annan suka fito gaba daya.


Abdul dinne ke tuqa motar,tuqi yake cikin nutsuwa,saboda shikam yanayin garin ya masa dadi sosai,saidai shurun dake cikin motar yayi yawa,a hankali yace
"Zuwanka kenan fa na farko tunda ka dawo,babu wani abu da za'a kai mata" tsaki yakuma ja sannan yace
"Share kawai letter".bagarar dashi abdul din yayi yaci gaba da tuqinsa.


Ba'a jima ba dai still yakuma sakin wani tsakin,abdul.ya taka burki da qarfi uana dubanshi cikin bala'i bala'i
"Kaga malam,bafa zaka zo ka sanyani a gaba da tsaki ba hakanan babu gaira babu dalili,ban maka uban komai ba,ban kuma san meke damunka ba". A maimakon ya amsa mishi saiya bude murfin motar da wani irin hanzari ya fice kawai yana buga mishi qofar,binsa yayi da kallo baki bude,tsahon minti biyu ya tuna suna saman titi ne ashe bawani parking din arziqi yayi ba,don haka ya balle murfin motar ya biyo bayanshi.


Saman motar ya sameshi zaune abinsa dafa'an,kamar ya manta suma saman titi ne,ga motocin dake zuwa wucewa sunata saka musu haske dake nuna wrong parking sukayi,kuma koda yaushe zasu iya hada goslow ma
"me kake haka?,baka gani saman titi muke?" Wani kallo ya masa,kana ya dauke kansa baice masa komai ba
"Oh god" abdul ya fada a ranshi,baison wannan side din na azeez,indai yasoma haka to 'yan taurin hade da uban miskilancin suna kusa kenan,zaka sha wuya idan ya taurare.


Waiwayawa yayi yadubi titin,da gaske sun fara hada cunkuson ababen hawa da yawancinsu suka soma zuba uban horn,ya dawo da kallonshi kansa
"Ka gani ko?,pls ka sauko mu wuce muna sake bata lokaci anan" sai da yayi kamar bazai magana ba sannan yace
"U better keepquite,kar ka sake damuna"
"Naji" ya amsa mishi a kaurare yana jifansa da harara,wani kallo shima yayi masa sannan ya sauko yakoma cikin motar.


Kansa jingine da kujera idanunsa a lumshe,yanajin sanda ya tashi motar suka soma yin gaba,bayajin koda yaje wajen safwa zai iya tabuka abun arziqi,may be ma ya qare da nuna mata halinsa,don haka yace
"Maidani gida" kallonsa yayi sannan yadauke kai yaci gaba da tuqinsa
"Kai din banza,baka isa ba Allah,minti biyar yayi yawa mu isa,ka sanya mata kuma rai,sannan yanzu kace na maidaka gida" jin abinda yace ya sanyashi yin shuru bai sake cewa komai ba har suka isa.


Ta juya ta kalli kanta a madubi sau babu adadi,ita da me aikinsu ne wadda taketa biye mata,kwalliyar data kira takanas akazo har gida aka mata take dubawa,yau ranar ta kusamman ce,karon farko tunda ya dawo zaizo wajenta
"Halima inane baiyi ba don Allah?"murmushi tayi
"Ai tako ina kwalliya tayi,ina da tabbacin shi kansa idan ya ganki yau saita Allah,saiya susuce fiye da yadda kike tsammani" dadi ya kamata,tayi dan tsalle gami da ihu tana mata godiya,dai dai lokacin da mahaifiyarta ta leqo dakin.


Tsaki taja ganin irin quruciyar da safwa ke yi,ita kuma halima na tayata
"Bansan se yaushe xaki gama girma ba safww,saiki fito kije suna jiranki a falon baqi" daga haka ta saki labulen ta juya,tana jiyo kwakwazonta da muryarta,dama tasan za'a rina hakan zata faru,saita saki murmushi tana addu'ar Allah dai ya nuna mata ranar auren tilon diyar tata da muradin ranta abdul'azeez.


Sai data sanya masu aikinsu suka kai komai sannan ta qara gyaggyarawa ta fito,a qofar falon ma ta kusa minti uku tana dudduba inda baiyi na,sa'an nan ta daga labulen dakin ta shiga.


Akan azeez din idanuwanta soka fara sauka,wani sanyin dadinya saukar mata,ason ranta idan itace zata so ya taso.da sauri ne ya iskota,kana su rungume juna kamar yadda turawa kanyi a duk sanda sukaga abun sonsu da suka dade basu ganshi ba,saidai ita din bata samu haka ba,amma idan ta lura dakyau kallonta yake ta qasan idanu,wato miskilancinsa bazai barshi ya bude dukkanin idanunsa ya kalleta sosai ba.


Sam shi ba wannan bane cikin kwanyarshi,idanunsa da zuciyarsa ne bijiro masa da ita kamar yadda take masa lokaci zuwa lokaci,sai yake ganin fuskarta gefan ta safwa har tazo ta zauna.


Kusan rabin hirar da abdul suka yita,ya karanci damuwa qarara saman fuskar safwa saboda yadda ta ciwa ranar da lokacin buri,don haka saya miqe ya zagaya ta bayanshi ya sunkuya dai dai kunnensa cikin rada
"Don't be a silly pls....bai kamata ba,kayi abinda ya kamata" sai ya daki kafadarsa sannan ya qara gaba ya fice.


Ci gaba sukayi da kallon juna kawai shuru yana sake ratsa dakin,sai data gaji sannan ta saki ajiyar zuciya,ta taso zuwa kujerar da yake kai a hankali idanunta a kanshi,tana jin kamar taje ta rungumeshi cikin jikinya,saidai bata manta da sharadin daya sanya mata ba kafin ya iso,don kada ma tayi yunqurin aikatawa.


Hannun kujerar da yake kai ta xauna,hakan ya kawo kusaci sosai tsakaninsu,cikin sanyin murya da shagwaba tace
"My prince" shanyayyun idanunshi dake sakr narkar da ita a soyayyarshi ya daga ya kalleta dasu,ya kafeta kuma dasu yana ci gaba da kallonta,itama kallonshi take,ta daga hannunta a hankali xata shafi idanun nasa,sai kuma ta tuna warning dinsa,don haka tayi saurin janye hannun nata da sauri
"Gaba daya ka ciremin zumudin zuwanka dana kwana inayi,idan wani laifi nayi maka pls prince ka gayamin..." Wani murmushi ya saki na gefan baki yana kada kai
"Babu wani abu....just bana jin dadi ne...." Ya qarashe maganar yana miqewa idonsa still a kanta
"Zan dawo wani lokaci" ya fadi yana tattakawa a hankali harya fice daga falon,daga inda take xaune ta bishi da kallo kawai,tana jin idanunta na tara qwalla,me yasa zai mata haka?,saita miqe cikin sassarfa tayi cikin gida tana gab da rushewa da kuka.


A harabar gidan yasamu abdulrashid tsaye jikin motar yana amsa waya,baice masa komai ba ya bude gidan baya ya shige maimakon gaba,galala ya bishi da kallo yana sauke wayar daga kunnensa,tsahon minti biyar yaji baice masa komai ba,kamar ma bai cikin motar,don haka saiyayi sallama da wanda yake wayar ya maida aljihunsa,yabude kawai ya shiga ya tada ita shima still bai cewa azeez din komai ba.


******** ***""""*** *******


Ƙarfe biyar da mintuna ne na yammacin ranar,zaune take saman abun sallarta wanda tunda tayi sallar azahar kusan take kai bata tashi ba,kiran sallar la'asar ne kawai ya tadata,ta ajjiye qur'anin hannunta tashiga bandaki ta daura alwala tayi sallar la'asar din,ko data idar qur'anin tasake dauka taci gaba da karatunta,don a yanzun indai tana ita kadai cikin dakin shine babban abokin hirarta,cikinta babu komai,tun shayin safe data samu ta kukkurba a tsaitsaye cikin qannenta,don batason ta fita daban cin abincin tayi karo da mama ladi ko anty wani ya samu maganar dazai gaya mata wadda zata sake dagula lissafinta.


Jin yadda hanjinta ke murdawa saboda yunwa ya sanyata aje qur'anin gefe,sannan ta miqe a nutse ta taka ta fice zuwa kitchen.


Kamar baquwa ko barauniya haka take takawa cikin sanda,don bata fatan ta tadda kowa a ciki,addu'arta ta karbu,babu kowa din kuwa,ta samu plate ta bude tukunya ta xuba dafadukan shinkafar da akayi a matsayin abincin rans,ta saka spoon ta fara tsakura,don gaba daya cin nata tamkar na yara haka yake,cikin nata ba wani babban space ne dashi ba.


Gabanta yayi mummunar faduwa sanda take kai lomar abincin bakinta saboda jiyo muryar anty tana shigowa kitchen din,faduwar gaban data sanyata qwarewa,saita saki cokalin tahau tari tana dafe qirjinta.


Dubanta anty tahau yi sanda ta qaraso tana tabe baki,sannan taja dogon tsaki
"Qaryar banza qaryar wofi,dama kin lallabo kina satar abinci babu cas ba as ba dole alhaki ya sakaki ki qware ba,jarababbiya kawai....ni wallahi bansan me yasa ubanki ma ya zuba miki ido kike ci gaba da xama tsakanin matan babanki ba,bayan babu abinda baki sani ba,mu dake yanzu duka sammakal" munanan maganganun da basu dace ba taci gaba da fada,wadanda suka haddasa tsaiwar tarin cak ba tare da tasha ruwa ba,sai kuma zafafan hawaye suka biyo gurbinsu.


Kai ta kada ta juya da niyyar bar mata kitchen din saiga mama ladi itama ta sako kai,tun daga bakin qofar kitchen din ta tsinci meke faruwa,itama saita dora nata
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta furta wasu sabbin hawaye da har suka sanya bata ganin gabanta sosai suka kwaranyo mata,taci gaba da tafiya kawai taba laluben hanya,amma hakan baisa sun rabu da ita sun qyaleta ba,saima leqowa da mama ladi tayi ta kitchen din ta dora
"Wato muna magana ga shashashai kina ci gaba da tafiya ko?,da yake babu uwarki ciki mu duka bamu haifeki ba,koda yake tunda kika yi mana uwar takima haka zaki.mata tsaf kuwa,tunda kin balaga kinsan namiji kinsan dadinsa kamar yadda muka sani,kinga kuwa dole kiga ai kanmu daya,daya daga cikin illolin xama da bazawara kenan,muna fada malam yana ganin ba haka ba,to yau zaizo,ni ko shi a cikin gidan nan,kwana biyu sai anyi magana ya wani ce jinin maimunatu ce ke,ina ruwanmu da wata maimuna,shi ya santa,da can baisan hakan ba sai yanzu"


Sosai kalaman suka mata girma a qwaqwalwarta,duk da haka bata fasa daga qafarta ba,burinta daya ta isa dakinsu kunnuwanta su tserewa muna nan kalaman da mama ladi da taci gaba da tsaiwa tana jifanta dasu,me ya kawo zancan mahaifiyarta a wannan maganar?,baiwar Allahr da batasan me yake faruwa ba?,batasan da wanzuwarsu ba?,ta jima kwance cikin kushewarta cikin salama shine yanzun zasu ambatota cikin haukan kishinsu da batasan meye manufar yinsa ba?,shin wai sun manta cewa itace sila na dukka wannan daula da suke ciki?,ko iya haka bata cancanci samun dagin qafa ba daga garesu?,tana jin qirjinta na mata wata irin suya,tana jin wani irin xafi cikin qirjinta,numfashinta kamar an dora mata dutse a qirjinta yana son ya fara yi mata nauyi.....


Kamar daga sama,kamar cikin daya daga cikin

Please Login or Register in order to submit comment