Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar yana da wata matar daban wadda dukkaninsu basu san da zamanta ba,tabdijan,turqashi!,qaqa qara qaqa,Allah ne kadai yasan yawan kudin data sadaukar ta kuma sarayar,haka ta dinga takawa qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba.


Fulani aisha ce kawai tayi saura a wajen,saiya dubeta
"Har ke,kema ki bamu waje" kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta miqe itama,amma saita kasa tafiya bayan ta fita,ta zauna a falo na farko kafin wannan falon,ita kadai shuru,tana jin kamar ana yamutsa duniyarta,ta riga data sani a yau kam babu wani sauran rufa rufa ko boye boye,lallai yau komai zai bayyana,kamar yadda Allah ya yiwa azeez din kwarjini to ya gada ne daga mahaifinsa,ta tabbatar tunda ya sallamesu yana son jin gaskiyar komai ne daga bakinsa,wanda ta riga ta sani da wahala ya maka irin wannan titsiyen ka iya boye masa gaskiya,saidai ta wani sashen tana ji a zuciyarta tamkar gata ya mata,kamar wani rufin asirine ya mata daya sallamesu gaba daya,wannan tonuwar qatoton asirin ba'a yishi ba gaban adama da saratu.


"Koda baka tambayeni ba,koda komai bai bayyana gareka ba ayau nayi niyyar shaida maka komai,amma ina mai neman afuwa daga gareka nida ammi akan dukkan abinda zakaji"
"Sanar dani komai,ban buqatar ka boyemin komai" ya fada kansa taaye,cikin ranshi cike da addu'ar Allah ya sanya ba babbar kwaba da zata rusa lahirarsu gaba dayanta suka aikata ba.


Babu abinda abdul'azeez din ya boye masa,ya bayyana masa dukkan wani abu daya faru a can baya din
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,lahula wala quwwata illa billah" shine abinda kawai mai martaba yake iya furtawa,kansa da idanunsa na kallon qasa,shuru ya ratsa falon,kowa da abinda ke kai kawo a ransa.


Sosai abdul'azeez yakejin wani abu mai nauyi yana ratsashi,kunya da nauyin mahaifin nasa na sake dabaibayeshi,amma wani sashe na zuciyarsa yana jinsa sakayau,wani nauyi da zuciyarsa ta dade tanaji a yau din sai yakejinta fayau,sai yakejinta empty kamar babu wani sauran nauyi daya rage a cikinta,amma kuma wani sashe na zuciyar tashi cike yake da fargaba tashin hankali gami da taraddadin irin hukuncin da zai yanke masa.


Yasan halinsa sarai,bashi da sauqi ko kadan,hakanan baya qyalewa idan har ka aikata wani abu na ba dai dai ba,komai kuwa kusancin da yake tsakaninka dashi.


A qalla sun kusa kwashe mintuna a shirin a zaune a haka ba tare da wani canjin yanayi ba,daga bisani ya tsinci muryar mai martaba yana cewa
"Tashi kaje abdul'azeez,tashi ka bani waje" bashi da wani zabi daya wuce ya tashin,don idan ya zauna ma bashi da sauran wani abu da zai fada,ko kuma wani abunda zai iya kare kansa ko ya kawo masa sassauci daga wajwn mai martaba,haka ya miqe yana takawa gami da laluben hanya da idanunsa da sukayi jajur,adam's apple dinsa ba abinda yake sai motsawa sama da qasa,alamun akwai wani abu daya taba zuciyarsa shima.


Tana zaune ya giftata amma saita kasa ce masa komai harya wuce,da alamu ma bai lura da zamanta a wajen ba,sai daya bacewa ganinta sannan ta miqe cikin wata iriyar tafiya tana harhada hanya ta koma ciki.


Tun kafin ta qarasa sallamarta ya daga mata hannu gami da yi mata nuni kan ta fice,bata musa ba ta juya wani abu yana tokare mata wuya.

*_tofa!_*


*_Bilkeesu_*


Kai tsaye garinsu abbaa kawai suka wuce a mota bayan jirgi ya saukesu a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano don su fara duba jikin mama.


Kusan wannan ne zuwansu amatu na farko tun bayan da sukayi wayo,hakan ya sanya sukaita baza ido suna kalle kalle tun a hanya har bacci ya daukesu.


Babban gidane gidansu abbaa,gidane na masu sukuni wanda ya qunshi mahaifi da mahaifiyarsa,sai kakanninsa wadanda suka haifi babansa,saidai tuni Allah ya yiwa kakanshin rasuwa,sai matarsa da har yanzun take raye suna kuma zaune tare da it,hajiya fatsima,tsohuwa mai ran qarfe,macace mai son jama'a da dattako,hakanan tasu tayi mugun zuwa daya da bilkisu tun ma tana qaramarta,da Allah ya sake hadasun yanzun kuma sai sabon nasu ya dora,don lokaci zuwa lokaci takan kira ta ko sanda tana brasil.


.

Sanda suka isa sashen maman abbaa din suka sauka gaba dayansu,macace itama mai kirki faran faran da son jama'a,alamu sun nuna cewa taji jiki sosai,amma ba laifi sauqi yana samuwa.


A yunwace suka qaraso,hakan ya sanya babu dadewa ma'aikatan gidan suka gabatar musu da abincin,saida sukaci suka qoshi sannan bilkisu ta wauce sashen hajiya fatsima da suke kira da hajiya.


Da murnarta ta tarbeta tana tsokanarta tamkar dai yadda ta sabawa jikokinta,bilkisun na maida mata cikin dariya ta zauna suka gaisa,sun sha fira sosai kafin ta sanya mai aikinta ta gyara mata daki daya cikin dakunan dake sassanta,wanda su biyune kadai a sassan daga ita sai wata jikarta data dauko take tayata zama.


Sanda ta miqe ta miqe da niyyar isa dakin hajiya ta fadi maganar data tsaidata
"Har yanzu dai 'yata babu maganar wani?,ina nan inata kasa kunne naji kin kawomin ango,ko yanzun ma dana ganku,na zaci abunne ya taso" murmushi kawai ta yiwa hajiyan,saboda ko wancan watan abbaa da kanshi ya soma tada maganar,ita kuma a yanzun babu abinda ke daga mata hankali irin zancan aure,da wanne fuska zata kalli dukkan wanda ta aura ta gamsar dashi irin auren da tayi a baya
"A tayamu dai da addu'a" ta bata amsar data fi yawan bayarwa,don ita kanta tasan babu yadda za'ayi dama su zuba mata idanu ko tace zata dawwama a haka,amma kuma yaya tafiyar zata kasance?,me goben zata haifar mata?,wadan nan sune tarin tambayoyin da batasan amsarsu ba.


Da zancan a ranta ta shiga dakin,wanka ta soma yi saboda huce gajiya,ta aika sassan mama akira su amatu suyi wanka aka shaida mata tuni sunyi,don haka saita qyalesu,ta bayar aka siyo mata sabon layi,don nata tsohon na ainihi yana gidan anty zuhriyya na nan,saisun isa kaisa sannan zata daukoshi ta dora,yanzun kuwa tanason yin waya ne.


Hannatu ta fara kira ta shaida mata sun iso,nan da kwanaki kadan zasu qaraso kaisa,murna kamar tayi me
"Yanzu kuwa zanje na gayawa baba,nasan zaiyi murna" murmushi kawai bilkisu tayi,tana mamakin sauyawar mahaifin nata haka,abun kamar a mafarki,bata zata zai canza ba sai gashi lokaci guda ya canza din.


Bayan ta gama da ita saita kira farida qawarta,ta shaida mata itama sun iso lafiya,suka sha hira sanna sukai sallama,tana niyyar ajewa saita tuna da assadiq,tasan yana nan yana tsimayen samun numberta tanan,ta jima bataga mutun mai haqurinshi ba,koda dr adam bai kama qafar assadiq wajen haquri ba,don haka ta laluba ma'ajiyar number dinta tayi kiranshi.


Sosai yaji dadin kiran nata,har ya kasa jurewa sai daya fadi
"Harna cire tsammani,ashe jan ajinne har haka,nidai a tausayamin don Allah,a jani a hankali" dariya ma ya bata,saita sake sosai ta bashi lakacinta suka sha hira,inda daga bisani ya barta ta huta.



Kwanansu biyu a ringim qanwar abbaa ta haihu,washegari anty zuhriyya tasa suka shirya gaba daya tace zasu rakata barka.


Acan suka kusan wuni saboda an dade ba'a hadu ba,yammaci lis suka taho,kan hanyarsu sunata hira yaran na hayaniyarsu,basuyi nisa sosai ba gungun shanun dake tsallake titi suka sanyasu tsaiwa dole,haka suka dinga wucewa kamar ba zasu qare ba
"Kai bafulatin mutum.baidai wayo ba,yanzu wadan nan shanun idan kinji biliyoyin kudinsu zaki mamaki,amma ya gwammace yayita bautata musu ya qare rayuwarshi a jeje,guda bazai iya yankawa yaci ba,ke idan yaga ma tana ciwon ajali zama yake yayita mata kuka harta mace don bazai iya yankata ba" dariya sosai anty zuhriyya ta bawa bilkisu,saidai batayi mamaki ba,don tasan wasu daga halayyarsu na qaunar dukiyarsu,sai kuma dariyar tata ta soma raguwa,saboda tuna hauwa'unta da tayi.


Duk tsayin shekarun nan yarinyar na maqale a ranta,da burin samota take kwana take kuma tashi,ya zuwa yanzun ta tabbatar ta sake girma ta zama budurwa,fatanta kullum Allah ya hada fuskokinsu da alkhairi,saita buda murfin motar tana cewa
"Na dade bansha madarar shanu ba irin tamu anty,don Allah minti biyar naje naji ko zasu tatsar min,wlh sha'awarta nake"
"Saikin dawo,saiki tfi da kudi,don kinsansu dason kwabo da sisi,bare suga daga mota kika fita yanzu zasu tsawwala miki kudi,Allah yasa su saida miki ma" ni huguma nace lol,fillo bayinmu,badai son kudi baðŸ˜ðŸ˜œðŸ˜œ,murmushi bilkisu tayi tana ficewa daga motar tana tsokanar antyn
"Anya anty ba kishiya fillo xa'a miki ba kuwa?"
"Haba shi yama fara" ta amsa mata tana gyara zaman qaramin yaronta dake saman cinyarta.


A hankali take dan bin bayan shanun da suka rage,ba jimawa ta soma hango wata 'yar qaramar rugga,da alamu anan suka yada zango,daga nesa tana hango yadda suke hada hada da shanun ana daure na daurewa,'ya'yan kuma da ba'a dauresu kowa yana daura da uwarshi.


Daga nesa ta hango budurwar bafulatanar tsaye riqe da qugunta,duk da ta juya mata baya bata iya hango fuskarta amma shanun take kallo da alama,saita qarasa bayanta a hankali ta tsaya sannan tayi sallama.


Waiwayowa tayi tana amsa sallamar da harshenta daya karye da fulatanci,bilkisu ta sakar mata murmushi tana ganin kamar ta taba ganin fuskar a wani wajen
"Sannu"
"Yauwa sannu" ta amsa mata da alamun kallo rashin sani
"Madara nakeso don Allah ko zan samu?,muna hanya ne zamu wuce" kanta tadan sosa kadan sannan tace
"Kash,gashi kuwa yanzu muka dawo daga kiwo....ba lallai a samu ta arziqi jikinsu,saidai akwai wadda adda ta tatsa dazu,idan kinaso saina kawo miki,ita ta sake tatsar wata"
"Eh inaso hakan"
"Shikenan....zo muje" ta fada tana nufar wata bukka bilkisu ta bita a baya.


Daga bakin bukkar bilkisu ta tsaya jiranta ita kuma ta dan yaye labulen zanin ta shiga,saidai daga inda bilkisun ke tsahe tana jiyo banbamin fada daga cikin bukkar,wani da fulatanci,fiye da rabinsa kuma da hausa,data saurara saita fahimci ana maganar yin aure ne da wata bataso.


Muryar da taji ta soma magana cikin kuka kuka hakanan taja hankalinta,ba al'adarta bace,amma saita matsa gaba kadan ko zata iya hango cikin bukkar saboda labulen daya dage ya maqale a jikin karan da aka gina bukkar dashi.
7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 66

*_NAFISAKABDULLAHI_*

*_Mai karatu nasan zaka ce meye wannan?_*

*_shin kai/ke ma'abociyar hawa duniyar yanar gizo ce?,kina daga cikin masu shawagi a manhajar youtube?_*

*_to maza matso,GA SABUWAR CHANNEL 'YAR YAYI DAKE DA ZAMA A MANHAJAR YOUTUBE MALLAKIN MAWAQIYA NAFISA K ABDULLAHI_*

*_CHANNEL DIN DATA HADA dukkan wani sinqi sinqin abubuwan sanya ruhi nishadi,kama da_*

*waqoqi*
*fina finai*
*da bidiyoyi masu qayatarwa*


*_GARZAYA maza ka shiga wannan link din https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg dannan maballin SUBSCRIBE don samun sabbin shirye shirye idan an dora,sannan ka danna LIKE kayi kuma SHARING_*

*_NAFISAKABDULLAHI YOUTUBE CHANNEL 'YAR YAYI_* 🥰🥰🥰

_ZAKU IYA MAGANA DASU KAI TSAYE A SHAFINSU NA FACEBOOK_
https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi


_KO KU TUNTUBESU TA WANNAN NUMBER WAYAR_
08071172003

*karku manta SUBSCRIBE,LIKE SHARE AND COMMENT*
*SAI KUNZO*🚶ðŸ¾â€â™€ï¸ðŸš¶ðŸ¾â€â™€ï¸ðŸš¶ðŸ¾â€â™€ï¸ðŸš¶ðŸ¾â€â™€ï¸ðŸš¶ðŸ¾â€â™€ï¸ðŸš¶ðŸ¾â€â™€ï¸


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070



Kyakkyawar budurwa ce zaune gefan gadon kara sanye da kayan saqi,kyakkyawar fuskar hauwa'unta data sha yabawa tana qissima girmanta,ba shakka hauwa'u ce,saboda babu wani sauyi da zai saka ta kasa gane fuskar daya daga cikin 'yan uwanta,musamman hauwa'un da kullum take kwana ta kuma tashi da begen son ganinta.


Batasan ta kirayi sunanta ba sai da taga mutanen dake cikin bukkar dukka sun waiwayo suna kallonta,har ita hauwa'un da kanta ke kallon qasa a dazun,miqewa taga tayi daga bakin gadon karan tana fiddo idanu
"Yaaya maigado!" Ta fada da sauri kana cikin wani mugun gudu tayo inda take,ba bata lokaci ta fada jikin bilkisun suka rungume juna,lokaci daya kuma suka fashe da kuka,wanda ya janyo hankalin na kusa dana nesa,suka tattaru a wajen suka tsaya carko carko suna kallon sarautar ubangiji.


Daidai lokacin da anty zuhriyya da kanta ke ratso wajen saboda dadewar da taga bilkisun ta danyi,gashi suna son wucewa,sai tsoro kuma ya kamata na yadda ta barta ta shigo wajen ita kadai,gashi bilkisun tabar wayarta a mota,don haka ta shigo da kanta dubata.


Itama tsaiwa tayi tabi sahun 'yan kallo don batasan meya faru ba,ganin sunata yaren fulatanci a tsakaninsu an rasa me musu magana sai ta matso
"Ke daughter meye hakan?,daga cewa zaki sayi madara saikizo ki samu waje ki tsaya?" Kanta ta dago fuskarta ta jiqe da hawaye,tana riqe da hannun hauwa'u daketa kallon bilkisun kamar zata bace mata tace
"Anty hauwa'una ce,kuluwa ta" hakan data fadi yasa ta fahimci komai,sai a sannan hauwa'un ta waiwaya dubi dattijuwar da suka fito daga bukkar tare tayi mata magana mara tsaho da yaran fullanci,taji dai ta fadi sunanta dana babansu malam bilya,sai tsohuwar ta dubesu tana murmushi
"Ma sha Allahu,ai sai kuyi bayani,don sam bamu ganeku ba,ke ɓingel,bamu abun zama" ta gayawa budurwar da suka fara haduwa da bilkisu,saita juya da sauri ta shige bukkar.


*_BAYAN WASU MINTUNA_*



Hauwa'un na zauna gefan bilkisu kamar zata haye cinyarta,labari take bata na yadda tayi kewarsu,da yadda tasha wahala kafin ta sake a nan din,duk da ta samu kulawa sosai anan fiye da nasu gidan,hakanan a hannun kakar tasu wadda ta gansu tare take,wadda ita ke riqesu ita da qanwarta da mamar tasu ta haifa a gidan data sake aure,ta auri bafulatani jinsinta,yanzu haka suna tare dashi da yaransu biyar harda wannan da ake kira da bingel.

.


"Nayi kewarku yaaya kamar me musamman ke ke dana saka rai da dawowarki,kullum ina cikin lissafin kwanakin da suka rage kidawo,ki cikamin alqawarin karatu da kikayi mana,katsam sukazo suka tafi dani bayan sunyi baram baram da baba,yanzu haka yaya maganar aurena ake da shehu,ni kuma bana sonshi yaya karatu nakeso har yanzu" ta qarasa maganar kuka na qwace mata.


Zancan auren ya taba bilkisu da anty zuhriyyan kanta,kai bilkisun ta kada
"A'ah bazai yiwu ba,ki daina kuka kulu na,babu me miki aure yanzu sai idan kece kika ce kinaso,aurenma na dole....ki kwantar da hankalinki,kinga mun taho da yara,amma gobe zan dawo,zanga dukkan wanda ya kamata na gani,zaki koma can gida cikin 'yan uwanki,kuma in sha Allahu zaki karatu yadda kikeso" murmushi ya kubcewa hauwan duk da hawayen dake saman fuskarta
"Zaki iya daukar nauyina yaaya?,duk da naga kin zama 'yar gayu sosai,kin canza daga yaya maigadonki kin zama kamar wata baturiya?" Murmushi tayi tana tuna yawan albashin da a yanzu take dauka
"Karki damu,harda bingel ma idan kinaso zan hada da ita" idanu ta fiddo
"Allah yaaya?"
"Da gaske nake miki kulu" shuru ta danyi sannan tace
"Amma ina tunanin koni dinma su yelwa barasu yarda ki sake daukata ki maidani gida ba sabida abinda ya faru tsakaninsu da baba,da irin riqon da suka samu labari yayimin,bare su hada miki harda bingel,kuma na sani burinmu nida bingel daya itama karatu takeso kamarni"
"Karki damu,daren yau kita addu'a,zasu fahimta in sha Allah" tayi maganar tana miqewa tare da amsarwa anty zuhriyya yaron hannunta,ta leqa su yelwa sukayi sallama ta shaida musu zata dawo gobe tanason magana dasu.


Har can bakin titin hauwa da bingel sukayi musu rakiya,tana riqe da hannun amatu da abdul kamar ta hadiyesu,tana jin qaunar yaran har ranta kamar yadda mamarsu ke sonta itama,tanata santin kyansu kamar kada su rabu.


Ko cikin mota hirar hauwa'u suka dinga yi ita da anty zuhriyya,ranar gaba daya da abinda ta kwana cikin ranta,washegari ta dauki najwa da amatu suka rakata rugarsu hauwa'u,daidai sanda tasan suna dawowa daga kiwo.


Ba qaramar gwagwarmaya tasha ba kafin su amince zata dauki hauwa'u,su kuma fasa aurar da ita ga wanda sukayi niyya da farko,don harta fidda rai ta haqura kafin su amince,amma bisa sharuddan zasu dinga zuwa ganinta duk sanda sukaga dama,hakanan itama zata dinga ziyartarsu duk sanda buqatar hakan ta taso,amma sam sunqi su bata bingel,babu musu ta amince,don tasan a yanzu dai babu wata sauran matsala,don baban nasu ba nada bane,ya sauya qwarai,kuma a yanzu bashi da abokiyar shawarar data wuce ita,ta saka a ranta zatasan yadda zata ja ra'ayinsu anan gaba su bata bingel dinma,tunda suka bata hauwa'un a yanzu.


Anan suka tsara zasu wuce kano nan da kwanaki ukun da suka rage musu a ringim,randa zasu tafin zasu biyo su dauketa saisu wuce,akan haka suka rabu.


¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶


Bata taba zato ko tunanin duniya zata mata qunci da baqi ba irin na wannan lokacin,bata taba tunani ko tsammanin akwai ranar da zatazo fara'ar mai martaba tayi mata wuyar gani ba,bata taba wassafawa a ranta irin wannan lokaci zaizo ba,dukkan wani abu bai mata taste a baki,kamar yadda babu wani abu dake burgeta sam a yanzun,idan ka qare mata kallo zakaga rama ta fara bayyana akan fuskarta.


Tun daga randa suka kebe da azeez dukkan wani walwala da sakin fuska qauna da kulawa dake tsakaninsu yayi qaura,abu mafi daga hankalima yadda yayi mata shuru,har yau baice mata uffan ba,bai kuma tada maganar ba kamar ma ba'ayi komai ba,kamar ba abinda ya faru,koda taje turakarsa da sunan kwana takan zauna kamar wata baquwar amarya a gareshi,tsakaninau babu wata hulda koda ta cikakkiyar magana dake hadasu,sai maganar data zama dole.


Ayanzun takai maqura,shirunsa kullum sake kasheta yake alhalin tana raye,tafison yayi fada,tafison ya dauki mataki akanta,tafison hukunci akan shirunsa amma yaqi tankawa ko yace komai.


*_AZEEZ_*


Daga nashi bangaren shima kusan hakan take,yanata kasa kunne da zuba idanu mai martaba yace wani abu,yanata saka kunne yaji kira daga gareshi,saidai har yau shuru maqatau malam yaci shirwa,babu alamun ma zaiyi wani zama dashi ko ya nemeshi.


Hakan yayi masifar daga masa hankali gami da qara masa damuwa mai yawa,saboda dukkan wani burinsa ya azashi ga mai martaba,ya danganta samun mafitarsa daga wajensa,saidai da alama tunaninsa ya saba,failure tana shirin samunsa,shi kuma sam baishiryawa hakan ba.


Kewar yaransa tana masifar damunsa,yana da buqatar sanyata cikin idanunsa koda zaginsa zatayi,ya tabbatar zai samu wani relief ko yaya yake,to amma bayason yaje mata alhalin baisan wanne hukunci mai martaba ya yanke ba,bayason ya aikata abinda yaci karo da shiri ko tsarinsa,duk da dukkan wani fatansa na samun matsera daga gareshi yanzu ya fara kwaranyewa,daga baya yaji dukkan haquri da juriyarsa ta qare,ya shirya kawai yayi nufin zuwa jigawa ya gansu.


Sanda ya shirya ya nemi ganin fulani bai samu ganinta ba,rabonsa da ganin nata tun randa ya bayyanawa mai martaba komai,haka ya wuce jigawa bayan ya barwa afnan sallahu,wadda binsu kawai take da idanu,tana jiran taga yadda lamarin zai qarke,amma koma meye batajin wannan zata zuba idanu rayuwar qawarta ta tasake tashi a tutar babu,tana jin har cikin ranta zata shiga wannan lamarin a wannan karon koda ammin zatayi fushi da ita itama.


.


Yammacine lis ya isa garin na jigawa tarin Allah,garin yayi luf luf saboda haramar shigowa da damina keyi,wanda ake saka ran wannan karon za'ayi azumin ramadan ne a cikinta.


Dai dai lokacin bilkisu na xaune a falon hajiya suna hirarsu abinsu,ana ya gobe zasu wuce kaisa,hajiyan na bata labarin yadda mata sukayi xaman aure azamanin daa da yadda suka bi mazansu,da kuma yadda suma mazan suka riqe iyalinsu da kyau kuma suka kyautata musu,bilkisu nata mamakin abun,daga qofar part din hajiyan su amatu ke wasansu abinsu saman kekuna.


Sallamar daya daga cikin ma'aikatan gidan qofar sassan hajiyan yaja hankalinsu
"Isa shigo mana" hajiya tace tana sake miqe qafofinta dake mata ciwo,ba musu ya shigo,ya duqa cikin girmamawa
"Hajiya maman 'yan biyu ce tayi baqo" ya fada fuskarsa cike da fara'a,sai itama hajiyan ta washe baki
"Malam isa,ya naga kanata washe bakine,ko ta samu ne?" Da yake hajiyan akwai barkwanci,babu ruwanta sam bata da matsala,saiya sanya dariya
"Ai hajiya baqonne baqon alkhairi ne" murmushi tayi tana cewa
"Alhamdulillahi....aimu haka mukeso,to yayi kyau,ka bude mishi dakin baqi maza,zan aiko yarinye ta kawo masa ruwa"
"To hajiya" ya fada yana juyawa da hanzari
"Hajiya bansan waye ba,bansan akwai wanda na sani daya san gidan nan ba" cikin nuna halin ko in kula da batunta tace
"Baqo ai duk inda yake rahamane,tunda ba maciyin naman mutane bane ai ba abun gudu bane,don baki sanshi ba yanzu tun kafin ki fita sai kice masa ba zakije ba ko ya koma ko kuwa yaya mai gado?,haba bilki aiba halin dattako bane" sai tayi shuru ta sadda kanta qasa,Allah ya sani hakanan takeji fargaba gamida mamakin wanne baqo zatayi a garin da take a matsayin baquwa,ba fita take ba,ba wani gu take zuwa ba,idanma wanine ya ganta ya biyota a ina?,kuma yaushe?,yana daya daga cikin abubuwan da yasa batason zuwa nigeria,ta tabbatar da cewa zata takura ne da zaryar manema,hakan kuma zai zama kamar tunzurine ga magabatanta,zasu sake damuwa ne da sanyata a gaba kan maganar aure,wanda ita kuma sam bata shiryawa hakan ba.


Tanaji hajiyan ta saka yarinye mai aikinta ta hada ruwa da lemuka harda dambun kaza ta fita kaiwa,daidai sannan hajiyan ta sake cewa
"Tashi ki daure ki leqa" bata musa ba ta miqe jiki a salube,ta shiga daki ta dauki wani mayafinta me kauri ta yafa sannan ta fito.


Tana fitowa yarinye na qoqarin komawa sassan hajiyan,data kalleta itama fuskarta a washe fiye da dazu,batace da ita komai ba ta wuce itama yarinyen saita wuce da saurinta kuwa.


Zata giftasu amatu taji kukan amatun,saita tsaya ta qarasa wajen tana tambayarta meya faru,ashe bigewa tayi da keken ta kurje hannunta,ta kama hannun ta duba,sai taga kujewar ba wani mai yawa bane rakine irin na amatu,wanke mata wajen tayi da ruwa tace taje wajen hajiya akwai robb ta shafa mata tabarsu a nan ta wuce.


Shaqar farko data yiwa iskar dake kai kawo bakin qofar falon taji gabanta ya yanke ya fadi,qamshi wani turare daya zama sananne a wajenta ke tashi,saidai kuma tako ta ina zuciyarta na gaya mata babu ta yadda wanda ta sani asalin mamallakin turaren ya iya riskarta a nan,don haka saita dake zuciyarta ta shiga cikin.


Idanunta basa iya ganin kowa a dakin,saidai kuma hancinta na jiye mata qamshin sosai fiye da daxu,kamar ma mai turaren na gab da ita.


Data gama dube dubenta bata ga kowa ba saita juya da niyyar ficewa ta koma inda ta fito,karab sukayi gware,taja baya da sauri numfashinta na niyyar qwace mata,sai data daidaitashi sannan takai dubanta gareshi.


Yana tsaye bayanta dab da ita harde da hannayensa ya zuba mata idanu yana qare mata kallo,ranta ya baci ganin yadda yake binta da kallo kamar ya samu majigi,taja dogon tsakin daya sanyashi dawowa hayyacinsa,saita durfafi qofa da hanzari zata fice.


Ina!,ta riga data makaro,don kuwa tuni yakai mata tattausar cafka,yayi kuwa nasarar danqota,ba tare da bata lokaci ba ya janyota zuwa cikin jikinsa ya lullubeta da kyakkyawan yalwataccen qirjinsa ta hanyar runguma.


Ajiyar zuciya yaketa saukewa ajejjere kamar wanda ya farfado daga dogon suma,sam

Please Login or Register in order to submit comment