Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,yayin da shima ya tsaya daga rufe motar da yakeyi,idanunshi fes bisa kanta,zuciyarsa na wani irin bugu garwaye da wani matsanancin sonta da yaji yana taso masa.


Tayi masifar kyau cikin shigar da tayi,babu wanda zai kalleta bai sake kallonta ba,saboda yadda tayi fresh,kana kuma kallonta zata tabbatarwa kanka ruwa biyu ce,chaculet colour din fatarta ta sake fita sosai ta qara haske,wanda sauran kadan ka kirata da fara idan ta shiga jinsin wasu masu choculet colour skin din.


Takowa yasoma yi yana burin ya cimmata a inda take tsayen,saidai tun kafin ya qaraso din ta kuma ciki da sauri kamar wadda taga dodonta.


Koda ta buda falonma bata tsaya a nan ba,sai data dangana da bedroom dinta,sannan ta samu kujerar madubi ta zauna tana maida numfashi,takaici ya kamata,tana ta murnar kwana biyu bai zuwa,ko yayi zuciya ne ya dauke qafa,sai kuma yau gashi katsaham,sai taja tsaki tana dora jakarta saman madubin bayan ta ciro wayarta.


Koda ya tafin bq zata fita yanzu ba,saita tabbatar da yayi nisa da unguwarsu,don haka ta kira number hauwa'u,ta sabuwar wayar data siya mata,tace kada suji shuru,sai zuwa anjima zata shigo,sannan ta kashe ta kira anty zuhriyya itama tace sai rana ta qara yin sanyi sannan zata zo,ta kashe wayar tana jan tsaki gami da dora wayar saman madubi,sai kawai ta miqe ta zare takalman qafarta,ta kuma ware rolling din kanta,take gashinta da yasha gyara yake qyallin ya bayyana,doguwar rigar jikinta data fidda shape dinta sosai daga sama ta sake qara mata kyau,saita haye saman gadonta tayi ruf da ciki bayan ta runtse idanunta,tana addu'ar Allah yasa yabar qofar gidan da wuri.


A qalla wajen minti goma tana a haka,ta soma gajiya da kwanciyar,ta sake gyara kwanciyar tata zuwa rigingine tana jan tsaki,gami da soma qunquni saboda takaicin bata mata lokaci da yayi,kamar a mafarki ta hangi kamar inuwar mutum wanda hakan ya razanata,ya kuma sanyata bude idanunta da sauri.


Ji tayi zuciyarta na neman faso qirjinta ta fito sanda idanunta suka hango matashi,tsaye bakin qofar shigowa dakin,ya jingina da qofar bayan ya budeta,ya harde hannayensa duka a qirji,bayan yaui crossinh qafafunsa,tamkar mai shirin daukan hoto.


Zumbur ta miqe cikin razana,tare da mamakin yadda ya iya ratso harabar gidan,ya qaraso har falon gidan,ya kuma riski dakinta,duk da cewa ba abun mamaki bane tunda babu kowa cikin gidan,amma babban abun mamakin shine,girman qarfin halinsa da har ya iya hakan.


Kasa magana tayi,sai wani zama da tayi tsakiyar gadon bayan itama ta zuba mishi idanu,kamar dabbar dajin da aka kawowa farmaki tana jira taga motsin wanda yakeso ya farmaketan.


Minti guda kafin ya saki hannayen nasa,sannan ya soma takowa cikin dakin,wanda hakan ya sanya itama ta soma motsawa sannan ta fara magana cikin hayaniya,duk da a cike take da tsoro
"Karka soma shigomin daki,ka fitarma mutane daga gida malam,nan gidan matan aure ne,don me zaka shigo musu gida babu izininsu?".


Bai kulata ba,illa gadon daya durfafa idanunshi a kanta,yana qarewa shigar jikinta kallo,wani shauqi daya jima baiji irinsa ba na neman tasiri cikin ranshi.


Karar wayarta dake saman madubi ya dakatar dashi,dukkansu suka dubi wayar lokaci daya,saiya sauya akalarsa zuwa inda wayar take
"Karka tabamin waya mana,meye hakan?" Ta fada da sauri cikin jin haushi,bai juyo ba bare ya tanka,yasa hannu ya dauki wayar yana duba me kiran.


Dr adam ne,tuni ya gane waye,saboda number waje dake nuna daga qasar da aka kira,wani abu yaji ya soki ranshi,sai yayi rejecting kiran.


Yana qoqarin maida wayar yaga sms saman screen din wayar,da sunan ASSADIQU,ya latsa kai tsaye ya sadar da kanshi ga akwatunan saqonninta

_gimbiyar duka kyawawan duniya,banason na cika damun wannan kyakkyawan ruhin mai cike da aminci,amma ina buqatar a tabbarmin da zuwan nawa,yayi ba matsala?_


Idanunsa ya runtse na wasu sakanni,yanaji taba sake bashi umarnin ya ajemata waya,sai kawai ya kashe wayar gaba daya ya sanyata cikin aljihunsa,sannan ya juyo yaci gaba da nufar gadon da take
"Wai kurma ne kai,bakajin me nake cewa?gidan matan aure ka shigo musu baka nemi izni ba" Ta sake fada cikin tsiwa.


Bai amsata ba har sai daya qaraso bakin gadon,ya kuma zauna a gafensa a nutse,sannan cikin narkakkiyar muryarsa yace
"Na sani,kuma nima tawa matar auren nazo gani"
7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 70

https://youtu.be/-kbsWo6IjOo

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________
*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903 234 5899
Ko
09033181070


Wani kallo tayi masa na tsiwa,wanda shi kuma ya jishi har jinin jikinsa
"Wace matar auren naka?,idan zaka farka daga wannan mummunan mafarkin naka ka farka,ada dai qaddara tasa na zama matarka,bada amincewata ba,ba kuma don ina sonka ko qaunarka ba,sai don......".


Gaba daya ya fincikota zuwa cikin jikinsa da hannunshi qwaya daya tal,ya kuma haura gadon dasu gaba daya ya turmusheta,bayan ya azq mata dukka nauyinsa,abinda bata zata ko tsammata ba,hakan yaso wucewa da numfashinta na wucin gadi.


Cikin sakanni qalilan dumin jikinsu ya gauraya,suka soma musayar numfashi duk da yadda nata numfashin yake mata wahalar jaa da kuma fitarwa saboda yadda yake a samanta ya aza mata nauyinsa,fuskarshi saitin nata,idanunshi da suka sauya launi cikin nata,duk da sun rage girma hakanan launinsu ya sauya,amma sai taji sun mata nauyi,wani yanayi can daya taba shudewa da dadewa memory dinsa yazo cikin qwaqwalwarta a take,saita birkice masa,ta soma tureshi da dukkan qarfinta,tana magana da qyar
"Ka dagani ko in maka ihu"
"Bismillah" yace da ita,alamun ya bata damar yin ihun,sai kawai ya sanya bakinsa saman dogon wuyanta,bayan ya saka hannunshi ya sauke jelar gashinta,ya soma aika mata da wasu saqonni da suka sanyata mutuwar wucin gadi cikin salo na babu zato bare tsammani.


Hankalinta ta maida jikinta cikin sauri,ganin yadda tsigar jikinta ta soma zubawa,saboda yadda ya canza waje daga wuyan nata zuwa kunnenta,tun tana tureshi harta soma gajiya,tun tana cewa zata masa ihu harta soma cewa zata masa Allah ya isa,amma baima nuna yasan tanayi ba.


Babban abun tsoron yadda taji jikinta na sauyawa,mood dinta yana canzawa zuwa wani yanayi mai wahalar fassarawa,duk da yadda zuciyarta take a zafafe amma hakan bai hana gangar jikinta amsar saqonshi ba.


Hankalinta ya sake tashi ganin yana nemam shiga wata gona ta daban,taji kamar sama zata rikito mata data tuna gidan babu uban kowa bare ta nemi maceci,sauran qarfin daya rage mata ta sanya dukka ta turashi,ya motsa,saidai bai sauka daga samanta ba,saidai kamar allura ta masa ko wata tunatarwa,donshikansanya soma manta a inda yake.


Ya tsaya cak da abinda yakeyi din,ya kifa kanshi saman qirjinta yana maida numfashi da sauri da sauri,yana kuma jin yadda itama take maida numfashin har qirjinta yana dagawa,sautin bugun zuciyarta ya fito muraran.


A hankali ya soma saita nutsuwarshi,baiso ya daga fuskarshi a haka ta ganshi a ayanayin da yake ciki,ita dinma bata sake wani yunquri ba,don da qyar take fusgar numfashinta,tana kuma son daidaita nutsuwarta,ta yadda zata iya masa qwaqwqwaran kashedi.


A hankali ya mirgina gefe sannan ya tashi ya zauna sosai na wasu sakanni,hakan ne ya bata damar gajin yadda ya yiwa rigarta,saita juya itama da sauri tayi rub da ciki,haushi da takaici gami da matsananciyar kunya tana kamata.


Tana jin takunsa amma ta kasa juyowa bare ta masa tsiwa ko jan kunnen da tayi niyya,taji tsaiwarsa bakin madubinta na minti kusan daya sannan taji ya nufi qofa,sai kuma ya dakata.


Ba tare daya juyo ba cikin wata shaqaqqiyar murya yace
"Ban zama lusari ba,ba kuma zan taba zama ba,sassaucina da sanyina ya ta'allaqa ne kan laifin da nasan mun aikata miki,har a yanzun ke matatace har a wajen Allah,ina da kishi matsananci,bazan lamunci shigar kowa gonata ba ko wucewarsa ta gefenta ba,duk wanda ya aikata hakan zai gane bani da dadi,nafi namijin goro daci,ki masa kashedi,ki kuma ja masa kunne da babbar murya cewar kada ya sake ya sake nuna ya taba saninki ko a hanya,indainyana son tsira da mutuncinsa da lafiyarsa,idan kuwa ke kika kulashi....to ban yafe ba koda ban gani ba" daga haka ya taka a nutse yayi gaba.


A zabure ta miqe da niyyar gaya masa cewar bai isa ba,kuma shi yasan da wani igiyar aurensa a kanta,ita batasan da wannan ba,saidai kallo na qarshe daya jefeta dashi,ya kuma ja qofar ya rufe shiya kashe bakinta murus,tsahon minti guda tana zaune saita koma ta kwanta rigingine tana jan tsaki.


Maimakon taji haushinsa sai ta soma jin haushin kanta lokacin da qamshin mayen turarensa ya soma buwayar hancinta,data bincika da kyau sai taji jikinta ke qamshin kamae ya fesa mata turaren ne,hatta da fatarta data shanshana qamshin take,hakanan bedsheet dinta,haushin kanta ya cikata,saita miqe ta zauna tana tuhumar kanta,ya akayi tayi sake haka har ya cimmata,me yasa sanda ya shigo bata shiga bandaki ta kulle ba?,wani dogon tsakin taja ta sauka daga gadon,ta isa bakin qofa ta murza muqulli sannan ta nufi bandaki,don ta tabbatar idan ba wanka tayi ba ba zata daina jin qamshin ba.


Ita kadai a toilet tana wanka amma taja tsaki yafi cikin kwando,takanji haushin kanta ya sake kamata idan ta tuna yadda ta ruski jikin sanda tazo yin tsarki
"Allah ya isa na" ta ambata qasa qasa,bata taba tsintar kanta a yanayi irin wannan ba sai yau,kuma duk silarshi.


Kayanta ta maida data fito,duk da sun yamutse,ta isa gaban mudubi ta kalli kanta,duk sai taji haushin rigar ya kamata,don haka ta zage zip din ta cireta ta cillata cikin kayan wanki,ta dauko wasu ta sanya.


Tana shirin barin gaban madubi taga qaramar takarda da bironta data yi rubutu dazun aje a gefe,saman takardar memory card ne akai,ta dauke memoryn ta warware takardar.


Lafiyayyen rubutu ne cikin tsari kamar haka
_banda a gidan wasu nake,wasunma dana shigo gidansu ba tare da izininsu ba,wanda hakan ya taka dokar addini,da yau saina kaiki duniyar da zaki gane shayi ruwa ne,ki kuma sake sako wasu twince din part two,amma ko a yanzun nasan na bar miki tambarin da zaki dinga shafawa,kina kuma tuna cewa kedin mallakin wani ce,mallakin abdul'azeez shi daya,kuma har duniya ta nade....,ga memorynki idan kina da buqata,wayarki kuma da layukanki kunyi sallama dasu,nama yi gwari da tuntuni ban rabaki da ita ba,don bansan gardin daya saya miki ba,nima na tafi da memory mai dadi a ruhina,duk da kin cakawa zuciyata mashi,kishinki zai iya halakani kafin safiya,karki kuma sake fita bada iznina ba._

_yarimanki ne,uban 'ya'yanki kuma_


Yayyaga takardar ta hauyi tana masifa ita kadai
"Aikin banza aikin wofi,gwara ka nema matarka tun dare baiyi maka ba,don ban yarda da wannan tatsuniyar ba,kuma abinda kayin yanzun alhaki a kanka wallahi,baka isa kamin shamaki da yin mu'amala da duk wanda naga dama ba,wayata kuma dole a adawomin da abata,tunda ba wani ne ya siya min ba ehe" haka ta dinga masifa ita kadai cikin gidan,ta koma gadon ta kwanta bayan ta canza zanin gado,sadai bata dade da kwanciyar ba taji sam kwanciyar babu dadi,hakanan ta dinga tariyo mata abinda ya faru dazu,don haka ta kuma jan tsaki,sannan ta sauko daga gadon taja dankwalinta ta daura,tama fice daga dakin gaba daya zuwa falo,da niyyar daukar landline ta kira anty zuhriyya,don yadda takejinta sam a yanzun bata son fitar
"Kodai gargadinsa ne ya miki tasiri" wata zuciyar ta tambayeta,kamar ita da wani tace
"Haba,shi din banza,bai isa ba"Ta baiwa kanta da kanta amsa,tana isa wajen wayar ta zauna sannan ta janyota ta fara kiran.


Anty zuhriyya cewa tayi tayi zamanta ma kawai,sa biya su dauko yaran duka saisu dawo tare,hakan itama ya mata dai dai,saboda wata muguwar kasala da takeji,kuma hakanan taji fitar ta fice mata aka.


Har zata tashi sai kuma ta koma ta zauna ta kira assadiq,tambayar abinda ya samu wayarta ya fara yi,saita rufe masa kan cewa babu chargy ne,ta sanyata a chargy,sannan ta gaya mishi amincewarta na zuwanshi a goben.


Hira yake janta dashi,amma sai taji sam hiran bata mata dadi,don haka ta dauki uzuri ta aje wayar,sai kawai ta zame a nan ta kwanta,don gaba daya batason komawa cikin dakin,saboda qamshinsa da har yanzu bai bar dakin ba.


Anan dinma bawai ta tsira bane,haka abun ya dinga fado mata arai,ta dinga juyi tana canza kwanciya gami da jan tsaki ita kadai.


Tun a hanya yana tuqi yake jinsa cikin wani irin nishadi mara misaltuwa,kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka karanci hakan,a lokacin ya dinga tuhumar kansa,mai yasa ma ha tsaya yana kallonta a baya bai mori lokaci irin wannan ba?.


Yanayin ya dawo masa da memory masu yawa da suka shude a wancan lokacin,ya tuna first night dinsu,wani irin baudadden first night,wanda ko a labaru shidai bai taba jin irin nasu ba,saiya saki murmushi,ya saka hannunsa guda daya da baya tuqi da shi ya shafi qirjinsa
"Zan qawata darenmu na farko da zamu sake rayawa fiye da tunaninki,na miki tanadin soyayyar da sai ta kusa zautaki ta kuma zauta tunaninki" ya furta haka shi daya cikin zuciyarsa,da wannan yanayin ya isa gida,kana kai tsaye ya wuce sassansa.


Toilet ya fada yayi wanka,sannan ya dawo ya fada saman gadonshi bayan ya fito,bai jima a duniyar tunani ba bacci yayi awon gaba dashi,baccin dake cike da wata irin nutsuwa daya jima bai sameta ba,baccin daya cika da.mafarkai,shida bilkisu cikin wata rayuwa mai dadi irinta ma'aurata,wajen da baikai ba a mafarkinsa sai daya kai,hakan ya sanya bayan ya farka dole ya sake wanka,zuciyarsa ta sake cika fal da shauqinta bege da wata iriyar zazzafar qauna,hakanan ya fito shi daya yana shawagi cikin wani lambunsa dake sassansa,yana jin zuciyarsa fayau,sai nishadi da soyayya da suka cikata maqil.


Bayan ya koma daki abun mamaki saiya tadda miscal din safwa jingim,tsaki yasha yana gyada kai ya aje wayar baibi ta kanta ba,ya rantse wannan karon zaka ga ainihin kalarsa da bata taba gani ba,zai saita musu tunani tunda su ya fuskanci basu dashi.


¶¶¶¶¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶ ¶¶¶¶¶¶¶


Tsaye take gaban mudubinta riqe da soson hoda da take shirin shafawa fuskarta amma ta kasa,saita buge da kallon kanta,ta rasa me yasa hakanan batajin wani karsashi a jikinta,farinciki ko dokin zuwan assadiq sam,bayan ita ta bashi iznin zuwan,komawa tayi saman kujera ta zauna riqe dai da soson
"Ko gargadinsa ke razanar dake?,ko don maganar da yayine kikeson ki fasa fita?" Zuciyarta ta tambayeta,saita kada kai da sauri
"Allah ya sawwaqe,shi din wa?" Tayi maganar tana fara shafa hodar a fuskarta.


Turare tadan dake fesawa kadan,sannan ta zura hijabinta mai hannu dark pink,wanda ya haskata sosai,ta zura slippers sannan ta fito.


Suna falo dukansu suna kallo,anty zuhriyya ta fita kitso tun daxun,daga ita saisu cikin gidan ta dubesu
"Najwa,akwai girki a kitchen,ki duba kafin na dawo"
"Tohm mami" ta amsa mata tana sake gyara zamanta saboda yadda kallon yayi mata dadi.


Amatu ce ta nace saita bita,hakanan badon taso ba ta barta suka fita tare.


Yana daga qofar gidan saman motarshi,cikin mamaki ta dubeshi
"Ya baka qaraso ciki ba?" Murmushi ya saki
"Nishadi nakeji yaukam,sai naji nafison zaman nan din,kona bude miki motata mu zaua ciki?" Wani kallo ta jefa masa mai kama da harara,saiya qyalqyale da dariya,don yasan kwanan zancan,ba abinda tafi tsana irin zance cikin mota,shi yasa shima ya tsokaneta da hakan.


Shirmen amatu ya tsaya biyewa har sukaci lokaci kafin ta shiga gida ya kuma saurareta
"To ya akayi?" Ya fada cikin murmushi yana dubanta,saita daga kai daga wasa da take da yatsunta tun daxu data fada duniyar tunani duk zaman hirarshi da amatu,murmushi kawai ta saki
"Kai za'a tambaya" gyara zamanshi yayi
"Kinsan meye?"
"Saika fada"
"Hajiya na bala'in son na kai mata ke ta ganki,tunda na soma mata zancanki itama kullum maganar kenan,ta matsu taga nayi aure,saboda na soma mata zancan rabi'a,har ta saka rai kuma taji shuru" murmushi tayi ta kada kai
"Lokacine,zamuje idan yayi".


Daidai lokacin anty zuhriyya ke dawowa daga gidan kitson ita da abeed,suka gaisa da assadiq,saidai yanayin fuskarta a yau ba kamar yadda suka saba gaisawa ba,hakanan tayi gaba tana dan binsu da kallo wanda hakan ya sanyawa bilkisu tsarguwa.


Tun safe yake fama da kanshi kan yadda yakejin matsanancin son ganinta,duk yadda yaso hana kanshi ya kasa,saboda haka daga masallaci da yayi sallar la'asar kawai yasaka cikin hadiman gidan mutum biyu suka daukoshia mota suka kawoshi.


Suna dosar unguwar farincikinsa na daduwa,yauma kota halin yaya yana jin saiya ganta koda bataso,saidai kuma me?,suna kusantar gidan fara'arsa tana raguwa,tun idanunsa na ganin masa kamar ba dai dai ba har ya tabbatar ita dince dai tsaye,tsaye tare da wani.


Wani bala'e'en wutar kishi ce ke ruruwa cikin ransa da zuciyarsa,lokaci daya kamanninsa suka canza,ya dinga furzar da huci,tun kafin su qarasa ya sanya suka faka motar,yayi shuru zaune a ciki yana kallonsu daga inda yake.


Da qyar ya iya daidaita numfashinsa sannan ya dakatar da hadimin dake yunqurin bude masa qofa,ya bude da kansa,qafafunsa ya soma zirowa kafin gangar jikinsa ya biyo baya,hannayensa zube cikin aljihunsa yake takawa zuwa inda suke tsaye,idanunsa a kansu harya cimmasu.


Sam basu ganshi ba,tana bashi amsar wata tambaya da yayi mata,wadda tambayar tayi matuqar bata dariya,sai suka hada idanu da ita.


Cak dariyar ta tsaya mata,gabanta yayi wani mummunan faduwa da batasan dalilin hakan ba,hakanan taji dukka gwiwoyinta sunyi sanyi,koda batasan fuskarshi sosai ba amma tasan cewa zallar bacin raine a saman fuskarsa.


Sauyawar yanayinsa ya sanya assadiq juyawa shima,suka hada idanu da yariman,saiya dan zuba mishi idanu,shahararren dan kasuwan da ya jima yana ganin tarin kama mai yawa tsakaninsa da yaran bilkisun,abu biyu ya hanashi mata maganar koya tambayeta,abu na farko yana tsoron amsar da zaiji daga gareta,tace masa eh shine mahaifinsu amatu,wanda indai.hakan ya kasance,bayajin matar data taba mallakar mutum kamar azeez din zata soshi so na qauna har zuciyarta,ta kuma aureshi da zuciya daya,a ma'aunin cancanta da kaiwa mizani ko kusa ko alama bai isa ya hada kafada da yariman ba,tako wanne fanni ya mishi shal,babu bigiren da zaya iya tsaiwa ya hada qualitynsa da nashi,tun daga kyau,ilimi,zati cikar halitta da haiba,uwa uba dukiya da nasaba.


Abu na biyu kuma idan ya tuna tun asali,auren dole akayima bilkisu,wanda bayajin akwai macen da za'a aura mata mutum kamar abdul'azeez kaisa din ta kira auren da sunan auren dole,mutumin da tarin cincirindon 'yammata ke buri da fatar ya waiwaya ya dubesu koda sau daya ne,koda bada batun aure ba,koda iya friendship ne kawai amma basu samu wannan damar ba,sannan bayajin mutum kamarshi zai auri macen da baiso ko bata sonshi,saboda dama da Allah ya bashi na iya auren duk irin nau'in macen da yakeso,daga kowanne irin nau'in jinsi yare ko qabila,wadan nan tunane tunanen da yake yawanyi su suke gaya masa ba abinda ya hada bilkisunshi da shi,face kama kawai daga Allah,wadda ke nuna zallar qarfin ikonshi,isarshi qudirarsa da iradarsa,kamar yadda yaji ana cewa,kowanne dan adam akwai masu kama dashi a doron duniya mutum saba'in.


Kallo daya tak ya yiwa assadiq yasha jinin jikinsa,hakanan ya sake tsaida hankalinsa tsam,a hankali ya bude bakinsa cikin izza da qasaita yace
"Banason in cutar dakai,amma kada ka yarda ka qara minti biyar qofar gidan nan" yana kaiwa haka ya damqi hannun bilkisu yayi gaba.


Turje turje ta fara yi tana fadin ya sakar mata hannu,amma baiko waiwayeta ba har ya isa bakin motarsu,ya baiwa hadiman umarnin su fita subar mishi key din a jiki.


Haka kuwa akayi,ya sanyata a mazaunin kusa da driver ya rufeta,sannan ya zagaya daya set din ya zauna ya rufe sannan ya tashi motar da wani irin mugun gudu daya tsorata bilkisu ya fice daga layin.


Tafiya sukayi ta wajen mintina talatin kafin yaja wani wawan burki daya sake tsoratata,ba tare daya kashe motar ba ya waiwayo yana dubanta,ya zuba mata rinannu kuma narkakkun idanunshi,cikin jikinsa can qashinsa yakeji kamar zazzabi nason kamashi,yayin da yaketa controlling fushinsa,saboda baiso yayi abinda bai kamata ba,ko ya wuce gona da iri.


Dauke nata idanun tayi daga irin kallon da yake mata,cikin hade girar sama data qasa tace
"Ina kake shirin kaini,ka maidani inda ka daukoni,koka budemin na fita kaji ko?".


Shuru yayi mata kamar baxaiyi magana ba,sai daya tabbatar ya rage kaso mafi yawa ma fushin dake cinsa sannan ya bude baki,cikin murya mai sanyi kaman an sanyashi a ruwan qanqara,saidai kuma cikin fushi dake bayyane qarara cikin muryarshi yake cewa
"Bakisan ainihin waye azeez ba....nayi imani da hakan,kozan lamunci komai bazan lamunci wasa da izgilanci da igiyar aure na ba,kiyi komai saboda an taba ranki,amma banda wasa da martabar aurena....idan da naso,zan iya daukarki,na kaiki wani waje wanda ba wanda yasani,tunda kedin mallakina ce,amma bazanyi hakan ba,saboda aikata hakan kamar nayi amfani da qarfina ne maimakon neman yarda da aminci afuwa da kuma shafe laifuka da mantawa dasu,amma ki kiyaye,ki kiyayi aikata ire iren wadan nan abubuwan,na rantse daga yau duk wanda na sake kamawa yazo wajenki da sunan tadi sai na masa daurin da babu wanda ya isa ya fito dashi,sai nasa ya bata,bacewa ta har abada...." Sosai kalamansa sun shigeta,kuma daga yanayinsa ba shakka zai aikata sama da hakanma a kanta,to amma batason ta nuna mishi weekpoint dinta bare yaci gaba da amfani da hakan,saboda haka cikin tsiwa tace
"Saboda kuna da mulki?,kuna da kudi?,kuna da fada aji?,saboda kai wanine?" Bai amsa mata ba,hakanan bai fasa tada motar ba,illa dai kawai yayi wani qaramin murmushine na gefan baki,idanunsa na akan titi,yayi ribas din motar ya koma titin daya baro,sai a sannan yayi magana guda daya
"Lokaci ne....kibi a sannu 'yammata" yayi furucin yana qoqarin cooling mind dinsa,don ba qaramin zafi yakeji qirjinsa yana masa ba,kamar ana kara masa garwashi.


A qofar gidan ya sauketa,fit ta fice ba tare data waiwayoshi ba,ya bi takunta da kallo harta shige,sannan ya lumshe idanu yana jin yadda qirjinsa keci gaba da zafi,ya sake juya akalar motar a hankali ya fita a layin ya harba titi.


A bakin falo ta tadda anty zuhriyya tsaye,kamar dama tana dakon shigowarta ne tace
"Ina kikaje?,na aika qofar gida kizo akacemin baki nan,babu motar assadiq din kuma a wajen" duk sai ta dibibice,ta rasa yadda zatayi mata bayani kuma me zatace mata?.


"Ta dawo?" Ta jiyo muryar abbaa dake saukowa daga sama,saita waiwaya ta dubeshi
"Eh gata nan"
"Yauwa maigado,ki qarasa dakin baki kina da baqi" ya fada sanda yake qarasowa cikin falon riqe da wasu takardu.


"Baqi kuma?" Ta fada cikin ranta cikin mamaki,tabbas taga baqin wasu kyawawan motoci a harabar gidan,amma bata taba kawowa cewa baqinta bane,to baqi daga ina?,kuma su waye?,ganin babu wanda zata yiwa tambayar sai kawai ta juya ta fice zuwa dakin

Please Login or Register in order to submit comment