Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki nasara"
"Akwai mutane guda biyu a gidan nan da tabbas basa cikinsa,kuma hadiman gidan nan ne,baya ga haka suna aiki ne a sassan aisha...." Saita tsagaita gami da yin shuru,yayin da ita ta jinjina kai
"Auta inason a bincikamin cikin sassanta su waye basu nan?,idan an samu ina suka tafi,auta...." Ta sake kiran sunanta,ta amsa mata tana sadda kai
"Banason wannan karon acemin ba'a samo wani bayani game da aikin nan ba,inason kota halin qaqa nasamu wani bayani da zai gamsar dani" kai ta jinjina
"Da ikon Allah wannan karon ranki ya dade sai inda qarfina ya qare,Allah ya baki nasara zakiyi farinciki da samun baya nan"
"A tashi a bamu waje" ta fada tana juyawa autan baya.


Koda ta fice zurfin tunani ta fada,tana tuna yadda abubuwa suke son su jagule musu,tako ina aisha ta toshe kowacce kafa ko qofa da za'a samu wani abu daya danganceta,bata taba shiga matsi da wahala kan wani abu data sanya gaba ba irin wannan lokacin,dan ko fulani saratu bata wani bata wahala ba,a yanzunma mantawa take da ita da abinda ya shafeta,don tasan ta rufe babinta,aisha yanzu itace target dinta.


Cikin sati guda auta ta dinga shige da fice ta kowanne fanni don gano su waye basa nan din?,sannan ina suka tafi?,me suka tafiyi din?,saidai dukka qoqarinta ya cimma tura,abu qwaya daya tal tasamu ganowa shine,sodangi da rakiya ne basa nan,dole haka ta tattara abinda tasamu ta shaidawa fulani adama.


"Allah ya tsinewa yarinyar nan,Allah ya isa tsakanina da ita" fulani adama ke fada wanda batasan harya fito fili ba saboda takaici da baqincikin daya mamayeta,tuni ta kora autarma,wadda ita tana ganin tayi namijin qoqari,saboda dukkan hadiman fulani aishan 'yan amana ne,samun wani bayanai daya danganceta daga wajensu ba qaramin aiki bane,tana da wani tsari,ba dukkan komai zata gudanar bane take bari ya fita har a sani,hakan ya sake sanyawa ta zama mai ciakakken sirri akan dukkan al'amuranta.

****** ******* *********


Sannu a hankali kwanaki suka dinga tuawa,lokuttan da sukayi musu saura na barin qasar mexico bai wuce sati takwas ba watanni biyu kenan masu zuwa.


Ta fannin mama sodangi da kadan da kadan take tattara dukkan wasu kayansu da tasan cewa zasu tafi dasu,dakuma wadanda zasu barsu a nan inda suka samesu.


Bata taba yin zancan da bilkisu ba,hasalima wani irin tausayin yarinyar takeji sosai har cikin ranta,tana jinta tamkar diyar cikinta data haifa,takan zauna sau tari ita kadai tayi ta tunanin yadda rayuwarta zata kasance a nan gaba,bayan anci moriyar ganga a yarda qauronta,dukkan wani fata nata da burinta na ganin manufar auren ta sauya sai taga ko kadan babu alamu dake nuna samuwar hakan,taso ace inama inama wannan zaman nasu ya haifar da shaquwa da soyayya mai matuqar qarfi,wadda zata zama silar wanzuwarsu a matsayin miji da mata har gaban abada.


Tasan azeez tsaf ciki da bai,tunda itadin tamkar uwa ce a wajensa,daukar ciki da naqudarsa ne kawai batayi ba,amma ita tayi rainonsa kaf,hakanan bilkisu,adan zaman da sukayi na watanni goman nan ta karanci wasu daga cikin halayenta,wadanda dukka masu kyaune,bataga guda mara kyau ba ko abun tur,taga dacewarsu da azeez fiye da yadda ta zata,tana da tsammanin cewa tabbas babu shakka fulani aisha batasan wacece bilkisu ba,a iya nata nazarin da hangen,da kuma karantar yanayi da halayyarta da tayi,bilkisun itace irin macen da kowacce ywa zatayi kwadayin ta zama suruka a wajenta,tana da halayya da dabi'u masu kyau nagarta da kuma jan hankali.


Abinda bata sani ba shine,itama bilkisun ta nata fannin tama irge da duk kwana daya data ragu cikin kwanakin da suka rage mata,zumudinta na komawa zuwa gida yana qaruwa,ba don komai ba,sai don tazo taga 'yan uwanta,jininta,wanda kullum kwanan duniya dasu take kwana take kuma tashi dasu,saidai kuma karsashinta yakan ragu idan ta tuna meye makomarta anan gaba?,ta rasa karatunta,ta rasa mutuncinta,sunanta bazawa a yanzu?,eh tabbas!,wannan shine sunan da zata ci gaba da amfani dashi.


Cikin satin da ya zamana shine satinsu na qarshe cikin qasar,sai dukka yanayinta yasake canzawa,hakanan take jin wani iri a dukka.jikinta da zuciyarta,duk wata walwala tata ta tafi,sai takejinta wani iri,tamkar ranar da zata taho daga nigeria zuwa qasar,tafison zaman kadaici fiye da komai,tafison zama shuru ita daya,duk sanda ya kadaice din tana zaman takurawa kanta ta hasasowa kanta meye makomarta,dukka mama sodangi na lura da ita,tsananin tausayin bilkisun ne ke sake kamata,don ta riga data sani,koma wace macace akayiwa rayuwarta haka daga mai manufa zuwa mara manufa zataji fiye da abinda bilkisun takeji,musamman idan tasan rayuwa fiye da bilkisu,ma'ana shekarunta sun daranma nata.


******* ****** ********


Gagurumin shiri take na tarbar yaron nata,wanda takejinsa daya ne tamkar da dubu,shiri tayi na kece raini na bikin murnar dawowarshi tare da kammala karatunsa,saidai a wani sashe na zuciyarta tana jin cewa,koda ya dawo din zai dora ne daga inda ya tsaya,bawai zaizo yayi zama na dindin bane a masarautar,saidai tana sa mishi ran zan dan zauna dasu adadin kwanakin daya jima rabon da yayi irinsu.


Wannan karon kusan duk wani wanda ya kwana yatashi a masarautar kaisa yasan da dawowar yarima azeez,bama masarautar kawai ba,duk wanda ke cikin garin na kaisa harma da maqwaftansa,saboda shiri fulani aishan take dan gaske,irin shirin da akecewa tsone idon maqiya.


Kamar yanxun da take xaune gaban mai martaba,cikin ado na kece raini,har yau bata bar ado wa mai martaba ba,hakanan dabi'arta take,macace mai masifar tsafta da son ado da kwalliya,shi yasa har kwanan gobe tauraruwarta take haskawa a zuciyar mai martaba,har kullum aishansa ta dabance,tasan kanshi hakanan tasan yadda take tafiya dashi.


Dan gyaran murya yayi yana gyara zamanshi,idanuwansa bisa kanta
"Yanzu uwar abdul'azeez da akazo aka tsareni har haka me ake buqata?,ni naga alamun ma fa anasone gaba daya a ture gwamnatina daga zuciyar yarona,tako.ina kinbi kin dha gabana a wajensa ba tare dana ankara ba?" Wata qawatacciyar dariya tayi tana lanqwasa wuyanta,tana mishi wani kallo da duk duniya shi kadai yake samunsa
"Ni na isa Allah ya baka yawan rai,abdul'azeez ai naka ne,bama shi kadai ba,uwar sa taka ce bare shi" murmushi ya fidda wanda ke nuna kalamanta sun mishi dadi,ta iya lafazi mai kyau da kwantar da zuciya,duk cikin matansa babu mai irin harshenta,shi yasa ko zaman hira yafi jin dadin yi da ita fiye da kowacce a cikinsu,duk da yana qoqarin boye fifikon kowaccensu a cikin zuciyarsa.


"Kamar nawa zan bayar?,amma fa kada a manta,nidin almajirin dan kasuwa ne....kece hajjaju guda,don naga saida komai yazo qarshe aka nemi na bada nawa kason" murmushi tasake yi wanda yasake fidda kyanta duk da shekaru da suka fara ja
"Ko nawa ran sarki ya dade ya bayar fulani tana maraba,amma kada ya manta,kome fulani tayi da bazarsa take rawa" harar wasa ya jefa mata sanda ya dauki wayarsa
"Dadin baki ko?,salon na miki transfer duka kudin account din nawa ba tare dana ankara ba" dariya tayi
"Da na zama daya daga cikin jerin miloniyoyi mata matuqar dukiyar cikin accnt din sarkin kaisa ta dawo hannuna" dariya ta bashi sosai,yana murmushi ya mata transfer kudade masu nauyi,har tayi mamakin yawansu ta dubeshi,saiya daga mata gira shima yana duban nata yace
"Kina mamakine?,kaman ban taba hidima me yawa haka kan lamarin abdul'azeez ba kamar yau ba ko?" Kai ta gyada,saiya gyara zamanshi yana murmushi
"Nima inason yarona sosai aisha,wala'alla ma fiye da yadda ke kike sonshi,amma dole a matsayina name iyali da yawa,wanda Allah ya wajabtamin yin adalci a tsakaninsu,dole na dinga takatsantsan da kuma qoqarin daidaita matsayinsu cikin zuciyata,koda ace wani yafi soyuwa a zuciyata fiye da wani,inason abdul'azeez bawai don matsayinsa na da namiji ba,a'ah,inasonshine saboda soyayyarsa daga Allah take a zuciyata,bugu da qari a yanayin da Allah ya azurtani dashi koda daga wanne jinsi ya fito,inajin xan soshi fiye da kowa cikin 'ya'yana,ubangiji ya daukemin mahaifina a ranar daya musanyamin dashi" sai ya tsagaita yana sauke ajiyar zuciya.


Kai fulani ta gyada,har cikin zuciyarta tana jin dadin yadda yau yake sake jadda da mata soyayyar shalelenta,iya wannan kawai ya isheta alfahari gami da farinciki tsakanin abokan zamanta
"Allah ya yiwa mai martaba raham,ya kyauta makwanci,yasa can tafi nan"
"Amin,amin ya Allah indona" ya fada yana murmushi,itama saita murmusa tana jin yana bata kunya.


"Amma ina ganin zuwa yanzu da abdul'azeez zai dawo gida,ya kamata ace anyi maganar aurensa,saboda shekaru suna tafiya,inason ya zama babban mutum kamili,hankalinsa yasake game jikinsa,don shine magajina anan gaba kamar yadda kowa yasani" maganarsa sai tadan sanya zuciyarta rawa da yayi zancan aure,saita tuna da nata plan din duk da yake kwanaki qalilan suka rage a gamashi,hakanan ta gama shirya komai akansa shima.


A karan kanta itama tana lissafin zuwa yanzu ya kamata ayi magana tsakanin magabatan abdul'azeez din dana safwa,a qalla asan da xaman juna,amma furucin me martaba shi yanke zaren tunaninta ba tare data shirya ba,yakuma so daga hankalinta
"Kinsan diyar wajen professer Amk?,wadda tazo kwanaki hutu ko?" Da sauri ta gyada kai,duk da bata shaida yarinyar wani can can ba,don data zo din ta sauka ne sassan fulani saratu a matsayinya na uwar gida kamar yadda shi mai martaban ya tsara,saidai kawai ta shigo ta gaidasu,sa'annan data tashi tafiya tabiyo ta mata sallama,ita kuma ta mata halin girma kamar yadda ta saba da kyaututtuka kala daban daban,tana sone taji abinda ya dauko xancan yarinyar,kamar yasan me take saqawa kuwa saiya dora
"Da mun fara magana dashi professor din,kan yiwuwar hada aurensu da abdul'azeez..." Ai yana ajewa ta kama,don ita sam maganar ma bata tsaru a kunnenta ba,ina 'yar professor ina azeez din?,tana ganin kwata kwata ba ajinsu bane
"Ai Allah ya taimakeka.....abdul'azeez tuni yana da wadda yakeso,kuma sun jima da fahimtar juna,maganar karatunsu duka ita dashi shiya kawo tsaikon shigar manya maganar" Da dan mamaki yadubeta kana yace
"Af...kice na kusa tafka kuskure....to amma,ya akayi haka?,bamu taba maganar dashi ba"
"Ni na dakatar dashi saboda karya hada karatunsa da soyayya" murmushi yasaki
"Kamar yaya?,saikace wani mace" murmushi tayi tana son sauya akalar zancan
"Kasan halin yaran nan sarai,matuqar suka sanya soyayya cikin ransu karatunsu saidai addu'a kawai,basu iya daukar abu da sauqi ba" kauda wannan zancan yayi ta hanyar cewa
"Diyar wacece ita?"
"ƴar alh ibrahim khalilu attah,diyar qawata kuma" idanu sosai mai.martaba ya zuba mata,wanda hakan yayi mata kwarjini sosai,saita dan basar kana ya jeho tambayarsa
"Ni dake kusan dukka musan waye alh attah....ina fata aisha ba auren hadi zaki masa ba saboda 'yar aminiyarki ce?,don kinsan na soke auren hadi a tsarina gaba daya,kaf yarana babu wanda zan sake yiwa auren dole?" Kai ta girgixa
"Sam ba haka bane Allah ya baka yawan rai,abinda kake tunani bashi bane" shuru ya ratsa tsakani sa'an nan yace
"Shikenan....duka mu ajjiye maganar tawa da taki,idan yadawo zan tuntubeshi naji nashi ra'ayin"
"Allah ya nuna mana" ta furta tana sauke boyayyar ajiyar zuciya.


Dukkan wani abu da azeez din zai buqata ta riga data kammalashi,hatta da dukkan wani furniture na bangarensa tasa an musanya masa da wasu,ko tsinke bata bari ba,duk da cewa ba tsufa sukayi ba,tayi hakanne da biyu,na farko tasa an caje dukkan sassan nasa lungu da saqo,an tabbatar babu wani abun cutarwa a rataye ko a bunne,kana ta sanya aka qara matakan tsaro bayan an gama shirya komai tsaf.


Hatta da gidan da mai martaba ya bashi kyauta sukutum da guda sai data sanya aka tsarashi aka kuma gyarashi yadda zai dace da tsarinsa dakuma son ranshi.


Kyautar gidan da yafi kowanne gida qawatuwa cikin gidajen da mai.martaba kedashi ya jawo cece kuce tsakanin matan nashi,gwara adama tayi qoqari ta boye tsananin bacin rai da kuma adawarta cikin kirsa da munafurci,amma fulani saratu dake abunta gaba gadi takanas ta iske mai martaba da zancan,murmushi yayi sanda ta gama jawabinta
"Banda abinki saratu.....shifa yaron nan da kike gani dole idan yatashi aure idan bashi da yadda zaiyi na bashi gida,idan ta kama ma harda auren inyi masa dungurun gum,qannenshi kuwa daga daya wataran shine a makwafin mahaifinsu,babu wani abu dana gaza tsakanin yarana,kowanne ina bakin qoqarin biya masa buqata da sauke nauyinsa daya rataya a wuyana,hakanan ina qoqarin ganin na daidaita komai tsakaninsu,babu son kai ko fifici" jikinta ya danyi sanyi,saboda tasan cewa hakanne,tabbas yana bakin qoqarinsa na ganin yayi adalci yakuma daidaita matsayin kowannnesu,to amma tana matuqar kishi da aisha ne,da yadda akomai ta fisu,tun daga farinjini cikin gidan da kuma yawan masoya,duk da cewa wasu da yawa suna boyewa ne saboda ganin idanunsu.
"Kayimin afuwa Allah ya baka yawan rai,amma maganar gsky wannan kyauta sam batayi ba" murmushi yasake yi ganin ta kasa bada cikakkiyar hujja
"Kinga saratu...na riga na bawa abdul'azeez gida,bawai don baya da,wannan kawai ra'ayina ne,kamar yadda nake hidimtawa gamida kashe kudi wa qannensa a duk sanda zan aurar dasu,ba kuma tare da tashi mahaifiyar tayi qorafin na musu abu banwa nata yaran ba" hakanan ta qaraci qananun mitocinta da gunguni tamiqe ta fita,tanajin kamar taci wuta saboda bacin rai kishi da masifa dake cinta.


Tsanar abdul'azeez na sake qaruwa a zuciyarta,tana jin gaba daya ya zame musu qarfen qafa,ko qadangaren bakin tulu,kullum kwanan duniya sai taji ko taga wani abu game dashi dazai sanyata bacin rai,bazata iya tuna mutum nawa ta hukunta cikin barorin sassanta ba akan abdul'azeez da tsohuwarsa,sukan manta su kirashi da sunan da tuni ta haramtashi ta kuma yi jana'izarsa a sassanta,ko suyi subutar baki su yabesu,da wannan bacin ran ta qarasa sassanta tana qulla abunyi a zuciyarta.
7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 33

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070



Ƙarfe biyu da mintuna ne na rana a qasar ta mexico,tun daga unguwar zuwa gidan gaba daya ya dauki shuru,baka jin motsin komai saina abubuwan da ba'a rasa ba,saboda qarancin zirga zirgar al'umma cikin unguwar da kewayenta,wanda dama ba kasafai kake jin hayaniya sosai cikinta,har dama dama ranakun qarshen mako.


Dai dai lokacin da bilkisu ke zaune a falon gidan ita da rakiya,wayarta ce a hannunta tana danne danne,wanda ita kanta bata ce ga abinda takeyi a ciki ba,duk da tasan tana duba wasu hadisaine data sauke su take bibiya kullum har ta kusan kammalawa su duka,saidai a yau bata gane karatun,yinsa kawai take,yayin da rakiya wadda ke zaune a gefanta take kallo a tv plasma din dake girke a falon,mama sodangi kuwa tana daki tana ci gaba da tattara kayayyakinsu waje gida.


Qararrawar dake qofar falonsu ta dauki qara,dukkansu suka kalli bakin qofar,sam babu wani kuzari a jikinta saboda haka rakiya ta rigata miqewa ta nufi qofar don budewa.


Hausa taji rakiyan tanayi na wasu sakanni,ta saki qofar ta dawo ciki,saita wuce kai tsaye zuwa dakin mama sodangi,bata jima ba suka fito ita da maman,rakiyan takoma inda ta tashi ta zauna,mama kuma ta zarce bakin qofa
"A'ah,lawal.....shigo mana,ya zaka tsaya a nan?" Tayi maganar tana dawowa ciki,babu jimawa sai gashi ya bayyana a falon.


Kakkauran matashi mai duhuwar fata,yana da tsaho dakuma jiki,da alamu shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas zuwa da tara ba,kallo daya zaka masa kasan baiyi kala da zallar bahaushen nijeria ba,yayi zubi da 'yan mali sosai,da alama jinin can ne.


Bata zauna ba sai data gabatar masa da ruwa da lemo sannan ta zauna suka gaisa sosai,ya karkata ya zura hannunsa a aljihun wandonshi yafito da passport da kuma ticket yana miqawa mama sodangi
"Wannan passport dinku ne da ticket dinku,an kammala komai"
"Hala fulani ta iso"
"Eh suna can tare da yarima,sunzo bikin kammala karatun nashi,kuma ina tsammanin duka tare zasu kom....." Da sauri bilkisu tamiqe ba tare data tsaya jin sauran maganar ba,tunda taji an ambaci sunayensu ta gundura da xaman falon,tun can batasan ma meye ya zaunar da ita ba,a hankali ta taka tashige dakinta.


Gefen gadonta ta zauna cikin wani irin kasala da mutuwar jiki,tana ci gaba da danna wayarta,wanda zuwa yanzu ta daina fahimtar komai,sai wani nisan kiwo da qwaqwawarta tayi cikin duniyar tunani.


Mintina wajen ashirin kyawawa tana zaune a haka,bata motsa ba sai lokacin da aka turo qofar sa'an nan ta daga kanta,mama sodangi ce take takowa cikin mutuwar jiki da kasala,bata ce komai bs itama harta iso gefan bilkisun ta zauna,sannan ta miqa mata wani dan koren littafi da wata paper,sai data kalli abinda take miqo matan sannan ta sanya hannu ta karba tana juyasu
"Passport ne da ticket,na fitarmu daga mexico,nan da kwanaki biyar masu zuwa idan Allah ya yarda".


Ba zata iya tantance mai taji ba,saidai abu guda da zata iya ganewa wani sashe na zuciyarta ya cika da farinciki da murnar samun 'yanci,yayin da wani sashen ya cika fal da fargaba da tsoro,ga wani irin cushewa da qirjinta yayi wanda batasan na meye ba
"Allah ya kaimu" ta fada cikin sauri sauri tana lalubar lambar wayar umma katti wanda kusan yawancin lokuta da wayarta take magana da ƙannenta

**************

A hankali doguwar motar ta alfarma wadda ke dauke da iyali da kuma ahalin masarautar kaisa,wanda ya hada da fulani aisha,da yaranta duka,Aarifa uswa sumaira da afnan,tana tare da amintattun hadimanta har mutum hudu,sai kuma fulani adama wadda ta buqaci zuwan itama,tana tafe da hadima daya sai diyarta da bata aurar ba afra.


Ko kadan fulani aishan bataso zuwan adaman ba,amma saita dake,ko a fuska bata nuna ba,tunda mai martaba da kansa ya buqaci hakan.


Da fari adaman itama zuwan sam bai mata dadi ba,amma daga bisani da sukayi magana da haj fauxiyya saitace da ita
"Aikamar dama ce kika sami,dama da xaki nunawa duniya dashi kansa yaron kina qaunarsa,dama ta biyu kuma zaki iya sanya idanu qwarai da bin diddiginsa har zuwa ranar da zaku dawo,wala'alla idan ska dace ki samu wani hujjan kamawar komai qanqantarta". Wannan magana ta fauziyya ta sauko da ita har ta saki murmushi,tana kuma sake tabbatarwa kanta maganar fauziyya haka take bayan tayi nazari.


Gidane wanda zai ishesu sauka su duka,babu matsi ko takura,falo ne yalwatacce mai dauke da dakuna a wani corridor na daban,fulani aisha daki daya ita da autarta afnan,uswa sumaira da Aarifa da yaran uswan biyu daki daya,daya dakin kuma fulani adama ce da afra wadda taqi xama dakinsu uswa ta koma dakin mamanta,sai wami spare dakin Kuma dake falon gidan daura da kitchen sauran barorin da suka taho dasu suka sauka a ciki.


Kowa dakinsa ya shiha ya kintsa yakuma huta gajiya,dai dai lokacin fulani aisha data gama wanka tana zaune saman daya daga cikin tuntun dake dakin,uswa na zaune a gabanta tana sake gyara musu kayansu,gamida jerasu yadda zasu musu dadin sawa,afnan na amsa tana jerawa cikin wardrobe din dakin.


Ita daya tayi nisa a zurfin tunani,duk da cewa ta gama tsara yadda zata kauda dukka tunanin adama,tasan cewa anzo gabar qarshe,kuma hausawa sukace aski idan yazo gaban goshi yafi zafi,idan batayi wasa ba komai zai iya kwabe mata ta hanyar adama,a wannan lokacin da akazo gangara,sam bata tsara plan na tafiyarta da ita ba,amma dole tayi shuru da maimartaba ya buqaci hakan,don kada ta tsammaci wani abun,tuntuni ta kula,ta kuma karanci halayen fulani adama da kyau,tana da sanya idanu dabin diddigi,shi yasa take takatsantsan da duk wata mu'amala da zata sanyasu su xama a bigire daya.


Duk da cewa hankalinta yadan kwanta data aikawa sodangi da ticket dinsu na komawa,amma dole ta tabbata sunbar qasar ba tare da fulani adama taga daya daga cikinsu ba.


"Afnan....maza kiramin yayanku" ta fada bayan takai qarshen tunaninta gamida suke ajiyar zuciya,dan tsaiwa da abinda takeyi afnan din tayi sannan ta bata rai
"Amma gaskiya ammi saidai a wayarki,kinsan halinsa,yanzu dana cika kiranshi zaimin halin nasa"ta qarasa fada a shagwabe,kai ammi ta gyada,kafin ma tayi magana uswa ta rigata
"Nima na kirashi,amma baiyi picking ba,yamin tex dai suna school suna qarasa wasu abubuwa"
"Ohkey,babu damuwa,rabu dashi ma,nasan zai shigo gidan nan da anjima".


Babu jimawa kukun gidan ya shaida musu ya kammala abinci,ya kuma shiryashi saman babban dining na gidan,kusan kowa a buqace yake da abinci,hakan ya sanya lokacin fitowrsu cin abincin yazo dai dai da juna.


Kowacce jinta take ta cika ta kuma hamshaqa,fulani aishan na tsakiyar yaranta suna tsaka da cin abincin sanda fulani adama tafito,kamar zata maze itama yadda taga fulani aishan taga tayi,sai kuma ta tuna cewa ita din me nema ce wanda aka ce baya gajiyawa,don haka bayan ta zauna tasoma zuba abincin ta dubeta
" har yanzu abdul'azeez bai samu damar shigowa ba hala?" Cikin izza da sarauta ta amsa
"Eh...bai samu ba" sam amsar bata mata ba,amma saita danne,tsanarta da haushinta na ninkuwa a ranta,fatanta na zuwansu hannu yana sake qaruwar mata.


Fulani adama din ce tafara tashi daga zaman ta wuce dakinta,sai fulani aishan da yaranta,sai kuma afra dake zaune tana charting gami da cin abincin ba tare data kula kowa ba.


Sallamarshi cikin muryarshi dake cike da sarauta ta ratso falon,yanayin tafiyarsa ne kawai zai gaya maka tabbas a gajiye yake,waiwaya tayi tana amsa sallamar,fuskarta ta cika da fara'ar ganin gudan jinin nata,shima kai tsaye teburin cin abincin ya nufo,kowacce tasoma qoqarin shiga taitayinta,yayin da afra ta kasa zama ganin yaja kujera yana niyyar zama,saita yiwa kanta qiyamullaili ta miqe,badon taso ba tace
"Barka da yamma"
"Yauwa" ya amsata a taqaice,ta juya tawuce tana tura baki bayan ta tabbatar bazai ganta ba,cikin ranta tana ta jero mita,dama tasan koya amsa amsawar tashi bata wuce haka.


Afnan da sumaira suma miqewa sukayi bayan sun gaidashi,don kowa yasan hali,sai wajen ya zamana daga shi sai uswa sai fulani aisha,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa tana tambayarsa
"Lafiya lau.....ya shirye shiryen?" Ya murxa goshinsa da tafin hannunsa
"Alhmdlh....komai ya kusa zuwa qarshe"
"Ma sha Alla" ta fada tana jin dadi har cikin ranta na yadda komai yake tafiya dai dai kusan dai dai da yadda ta tsara.


"Me zakaci?" Uswa ta tambayeshi cikin kulawa bayan ta kammala cin nata abincin,so take kuma ta rashi ta basu waje,don tunda taga ammin na nemansa tasan zasuyi magana ne,baice komai ba sai daya gama kallon duka abincin dake wajen,sannan ya mata nuni da abinda xata zuba masa,sannan yace
"Ba mai yawa ba" kai ta jinjina,sai data zuba mishi komai ta tura gabanshi sannan ta miqe tana duban ammi
"Ammi zanje na shirya zandan fita,munyi da abban aira zan je gidan anty umma mu gaisa" kai ta jinjina mata,daga haka tasauka tashige ciki itama.


Shuru ne ya ratsa tsakani lokacin da yake tsaka da cin abincin,fulani aisha tayi gyaran murya sannan tace
"Na aikawa sodangi da yarinyar nan passport dinsu har da ticket na komawa nigeria....zasu wuce daga can,don babu yiwuwar mu hadu,na gama tsara komai,da zarar sun sauka zasu danqata ga mahaifinta,abu daya yanzu ya rage takardarta,ka rubuta yau ko.zuwa gobe da safe,ahmad xaizo ya karba yakai musu,idan muka koma gida komai zai dora,mai martaba yayi magana kan yiwuwar fidda macen aure,nasan za maka magana kan diyar abokinsa prof,basai mun maimaita zance ba,ka san bayanin da xaka yi masa,da zarar ka gaya masa kuma abinda zai faru shine xai aika ga iyayen safwa....wannan shine mataki na gaba na rayuwarka da nake saka rai,kafin

Please Login or Register in order to submit comment