Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

goma da ashirin,saita dafe goshinta da tafin hannunta tana jin kamar kuka zai qwace mata,babban takaicinta batasan yadda akayi ta manta wayarta a motarshi ba,da kira daya zata yiwa adam ta tabbatar babu bata lokaci zai bayyana a wajen,dolenta ta koma da baya ta zauna,tana wassafa irin babban abunda zata masa wanda zai tursashi barinta ta tafi,bayan yayi zuciya gaba daya ya bar bibiyar rayuwarta ita da yaranta.


Minti a qalla takwas ya bude qofar ya shigo,yana dauke da jakar tata,saidai daya hannun nashi wayarta ce,yake riqe da ita,wadda yana shirin maida qofar ya rufe ta dauki tsuwwa.


Ita dake zaune da shi da wayar ke hannunsa dukka hankulansu ya karka ga wayar,sunan Dr adams daya gani na yawo saman screen din nata shi shi ya sanya qwayar idanunsa soma sauya launi nan take,saboda sanda yake qoqarin dauko wayar ya lura da tarin miscal da irin wannan sunan,wane kishi na masifa yaji ya motsa masa,saiya bar abinda yakeyi din ya daga wayar ya kara a kunnenshi
"Sweet angel.....ina kika shiga haka?,ina ya kaiki,kin barmu hankali tashe munata nemanki" kalaman da suka soma dukan kunnenshi kenan,cikin wata iriyar kakkausar murya fuska kamar hadarin gabas,ya dawo da wannan kamar tashi,kamar bashine ke magana cikin taushi ba a dazun yace
"Kada ka sake kiranta,domin tana tare da mijinta,idan kuma ka qiya,ba shakka tsautsatsauran hukunci zai hau wuyanka,qaton banza kawai" ya cikashe da tsaki yana sauke wayar daga kunnenshi kana ya datse kiran.


Niyyarsa ya shiga cikin wayar ya sanyata a flight mode,saida me?,hoton amaturrahman da abdurrahman dake saman wayar a matsayin homescreen walpaper dinta yaso tafiya da numfashinsa,iskar dake fita ta kafofin hancinsa ta masa qaura na wucin gadi,har ya dinga kokawar nemota saboda barazanar tafiya da take gaba daya.


Bai ankara ba yaji am wafce wayar,kana muryarta ta maye gurbi
"Wai waye kai da zaka dinga gayawa mutane cewa kaidin mijina ne?,wanne irin mutum ne wai kai ehenn?" Ta fada tana tsaye a gabanshi.


Sam bai fahimtar me take fada,tunaninsa ba'a kan wanann yake ba,tuni qwaqwalwarsa tayi nisa wajen gaya masa
"Yaranka biyu ne,tabbas 'yan biyu ta haifa maka" baisan lokacin daya rarumota gaba daya ita da wayar ba ya sanyata cikin jikinsa ya matseta gam,bai damu ba,hakanan bai kulaa da yadda take kai mishi duka tako ina ba gamida yi masa gargadin ya saketa.


"Alhmdlh,alhmdlh" shine abinda yaji bakinsa yana maimaitawa,kafin daga bisani yace
"Na godewa Allah da bai qyaleni na tafi a yadda tsarin yazo ba,na godewa Allah daya sanya wani lamari mai girma a zuciyata game dake,na godewa daya hukunta min haka cikin rayuwata,cikin sati guda kacal da nisantarki da rayuwarmu....ashe ke din wata alkhairi ce da kika shigo rayuwata,wanda dukkaninmu bamusan da haka ba?,ashe har yara biyu na bari a jikinki ba yare dana sani ba?" Ya fada yana dora hannunshi saman cikinta yana shafawa,wanda cikin hanzari ta buge hannun nasa qwalla na sauka saman kuncinta,saboda yadda ya riqeta tsam,kuma babu alamun zai saketa,ga kalamanshi dakeson dawo da komai sabo cikin rayuwarta.

Birkitota yayi suna fuskantar juna,yana duban tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka dade da sauya launi,wannan karon dukka kafadunta ya kama ya riqe sosai yana ci gaba da maganarsa
"Ashe har yara biyu Allah yayimin kyautarsu ba tare dana sani ba,suna rayuwa a wata duniyar ina rayuwa a tawa duniyar daban?" Bata ankara ba ya zube gaba daya a gabanta saman gwiwoyinsa yana riqe da dukka qafafunta
"Kimin alfarma ki bayyana min 'ya'yana,koda zakimin wani hukuncin na yarda zan karba...." Da qarfin tsiya cikin kuma sauri ta janye qafafunta daga gareshi,duk yadda taso nuna juriya da jarumtarta amma ta gaza,don tuni kuka mai nauyi da qarfinya qwace mata
"Wadanne 'ya'yan?,ai kai da dui wani makusanci naka ku saka a ranku cewa baku da wasu yara a duniya sama da wadanda ke gabanku,yaran da tun a ciki kuka baiwa banza a jiyarsu?,kuka yiwa duniya kyautarsu?,dasu rayu da kada su rayu ba damuwarku bace,kuka qaryata wanzuwa da samuwarsu,to kamar yadda kuka qaryata samuwarsu,inason har duniya ta nade kuci gaba da raya wannan cikin ranku,don har abada ba zasu taba zamowa naku ba".


Ta soma yunqurin zame kafadunta daga hannunshi,tayi nasara saidai kuma ya kama hannayenta da sauri ya saka cikin nashi
"Ba laifina bane bilqess,anfi qarfina ta hanyar da sabawata zai iya zama babbar illa ga rayuwata...."
"Da bai zama illa ga rayuwarka ba yanzun ka gani ya zama illa ga jininka ko?...." Kai ya gyada
"Tabbas hakane....amma ki yarda dani....bani da laifi,koda ina dashi laifin nawa kadanne,nasan zakimin uzuri matuqar kika zauna kika saurareni...." Hannayenta ta zame ta qarfin tuow,ta cimma nasara kuwa saboda jikinsa dake a mace laqwas,yana jin zuciyarsa na masa wani irin zafi zugi da kuma quna
"Kada ka sake tabani,ka matsa daga kusa dani,sannan ka budemin qofa na koma inda na fito,idan kai bakasan illa da zunubin haka ba ni na sani"
"Babu wata illa,hakanan babu zunubi a kanmu,DOMIN KUWA KE MATATA CE" Idanu dukka ta zaro,don ga zatonta yabar wannan maganar ne,ya kuma fadeta ne a baya saboda kawai ya samu damar tsaidata.


Idanunsa cikin tsakiyar nata qwayar idanun,kai ya gyada mata yana mai sake son tabbatar mata
"Yes...har yanzu ke matatace" nata idanun ta janye saboda yadda yake kallontan ya mata nauyi da yawa,ta saki wani malalacin murmushi da batasan yadda akayi ta qwaqwaloshi bama,ba tare da tace komai ba ta soma takawa zuwa bakin qofa kana ta soma bashi amsa
"Kabar wannan tatsuniyar kazo ka budemin qofa,domin koda jikina dukka kunne ne bazan taba yarda da wanna tazo mu jita din ba,koda zan yadda da kowacce ta tsuniya takan wannan kam bata da gurbi ko kuma muhalli" takowa yayi zuwa dab da bayanta ya tsaya
"Ba tatsuniya bace...hakanan yadda na fadi haka maganar take,inda shaidu har guda uku,wadanda na tabbatar koda a gaban alqali sun isa su zama shaida" saiya kewayeta ya bude qofar,ba tare daya dawo ba yayi gaba.


Jinta take kamar mutum mutumi,jinta take kamar ba'a duniya ba,qafafunta kamar ansa wani abu mai qarfi an bubbuge mata su,babu qwari sam tattare da ita haka itama ta taka ta fice.


Tun daga wannana rana ba ta sake fita wajen taron ba,wuni take kwance a gida,tana jin tamkar bata da lafiya,inda Allah ya taimaketa dr adam yana tsaye akan komai,rashin zuwan nata na sauran kwanakin bai zame mata wata illa ko asara ba,kusan duk abinda aka gudanar zata ji daga wajensu tare da gamsashen qarin bayani da 'yan qananun jotting dake sake bata haske.


Zamanta a dakinsun sai yafi mata kwanciyar hankali,saboda tasan babu ta yadda za'ayi ya iya ganinta ba tare data fita ba,tana kuma da yaqinin yana can yana fama da zirga zirgar neman ganinta,don ta fuskanci halayyarsa cikin wani qanqanin lokaci.


Saidai wani abu dake bata mamaki saqonnin gaisuwa dake tafe a jejjere a wayarta da wata baquwar number da batasan ta waye ba,saqonni ne dake nuna zallar kulawa da kuma bege,bata taba damuwa tasan lambar waye ba,iyaka idan ta karanta ta goge taci gaba da sabgarta.


Ta fannin yarima bai boyewa azeez komai ba ya shaida masa,ya sake qarfafa masa gwiwa tare da fatan nasara.


Tabbas rashin ganinta ya sanyashi a damuwa qwarai,har yanzu baikai ga ji ko samun dukka abunda yake da buqata ba,saidai abu biyu na debe masa kewa da kwantar masa da hankali.


Abu na farko ya riga da yayi connecting wayarta da nashi,duk sanda ta tashi barin wani gari ko wata qasa zuwa wata zai sani,hakanan da zarar ta koma brasil a sauqaqe zai ga adress din inda take zaune,ta wannan fasahar kuma ya samu damar shiga gallery dinta,ya debi dukka hotunanta wadanda sukayi masa,nata dana amaturrahman da abdurrahman.


Ranar kwana yayi yana kallonsu,ya kalli hotunan kamar zasu gudu su barshi,ya kallesu kamar ba gobe,ya kallesu kamar mai shirin yin sallama da duniya,hakanan duk tsananin jarumtarsa dakiya gami da juriya amma ya gaza daurewa wannan karon sai daya zubda qwalla sanda yake kallon hotunan yaran,yake kallon tsantsar kama ta ban mamaki dake tsakaninsu,babu wanda yake hangowa a wannan lokacin sai fulani,ko yaya zata karbi lamarin?,ya zata kaeshi?,da wanne irin ido ko zuciya zata amshi yaran,tabbas ba shakka a wannan karon ya shirya tara dama qalubalantar ko meye zai faru,ko meye zai biyo baya.

¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶


Safiya ce mai cike da wani irin ni'ima da lullumi,shi daya qwal cikin dakin yana maqale da waya a kunnenshi yana amsa kiran da safwa tayi mishi,yayin da yake ta cike wasu takardun kwangiloli,ayyukane suka taru sukayi yawa kan harkar kasuwancinsa,amma ya tare komai ya kasa komai,bilkisu ta tsaida komai cak cikin rayuwarshi,yana lissafe da yau kwanaki bakwai rabon daya sanyata a idanunshi,yanajin matuqar wasu kwanakin suka sake biyo baya,tabbas zaiyi dukkan mai yiwuwa ya isa har dakin dake masaukinsu cikin hotel din,saboda zuciyarsa ta soma gazawa.


Maganar da safwa tayi ne yasa yadan dakata da rubutun da yakeyi
"Ina saka ran ganinka a hawan daba na wannan shekarar.....kowa da kowa zaizo,nima wannan karon zanzo,inason ganinka don nayi kewarka".


Yasan cewa tana sonshi,hakanan tana da muradin kasancewa tare dashi,saidai wasu abubuwa da suka sanya sam zaman nasu bai fiya armashi ba,hakanan akwai tsarukansu da sam basuyi dai dai ba,bakuma su dace da ra'ayinsa ba,amma ko meye yasani cewa tarsa ce dai,hakanan tana da haqqi a wuyanshi,don haka cikin yanayi na kwantar da hankali yace
"Kada ki damu,wani babban aiki ne ya tsareni anan din,wanda bani da tabbacin zuwa din,saidai da zarar komai ya kammala zan taho ayi komai dani in sha Allahu" murya ta kwabe sosai tana jin babu dadi
"Kace kawai ba xakazo ba" kai ya girgiza
"Ba haka bane,babu tabbacin rashin zuwa kamar yadda babu tabbacin zuwan" xatayi magana ya dakatar da ita,sakamakin wani haske da sauti d wayarshi daya ware ta musamman tayi,yace zai kirata yana zuwa.


Alama ce dake nuna mishi cewa bilkisu ta isa filin tashi da saukar jirage,hakan na nufin zata sake barin qasar,baida matsala yana da jama'a dake aiki a filin jirgin,don haka yasa aka laluba mishi inda jirgin da zai tashi yanzu ya nufa,aka tabbatar masa brasil ne.


Already yana da visa dinsa,saboda haka yasa aka duba mishi jirgin da zai sake tashi zuwa qasar,aka tabbatar masa saidai gobe da yammaci,duk da ba haka yaso ba amma dole haka ya haqura,ya shiga shiri cikin zafin nama gamida shirya dukkan abinda yake saka ran zai wanzar idan ya isa brasil din.


Cikin shiga dake nuna tsantsar alfarma isa mulki da kuma qasaita take nufar sassan mai martaba,wanda ta samu kira ne na musamman daga gareshi.


Daga ita sai manyan hadimanta guda biyu,kubra da yaha,wadanda suta zaba suyi mata rakiya.


Sau uku tana wuce gungun mutane wadanda dasun hangota suke zubewa su miqa mata gaisuwa,ta amsa musu cikin nuna zallar sarauta kana ta wuce.


Gungu na uku da suka tadda bayan sun dan gota su ne ta tsinci muryar kubra
"Ranki ya dade,Allah ya taimakeki"
"Uhmmm,ya akayi kubra?" Dan jim tayi har sai da fulanin tace da ita
"Ina saurarenki mana,fadi buqatarki"
"Allah ya baki yawan rai....shin kin lura da yadda gungun dukka jama'ar da muka wuce ke boye wani abu da zarar sun ganki?" Cak ta tsaya da tafiyar da takeyi,tsahon sakan uku kana ta waiwayo tana duban kubra,wadda tuni suka sadda kai qasa ita da yaha cike da girmamawa
"Kamar yaya kenan?" A ladabce ta amsa
"Kamar akwai abinda suke gani,wanda ganin giftawarki ba zato wala'alla yasa suke boye abun....kin kula da haka yaha?" Kai ta gyada
"Qwarai kuwa,nima na gani har karo biyu kafin isowarmu nan".


Dogon tunani maganar tasu ta sanya fulanin,tayi shuru na wasu mintuna ba tare da tace komai ba,kalaman kubra suka dawo da ita daga duniyar tunanin data fada
"Amma uwar gijiyata,kina iya sanya idanu a gaba koda zamu sake ganin wasu mutanen" kai ta jinjina cikin gamsuwa,kana ta juya taci gaba da tafiya tana sake nutsuwa da sanya idanu ga hanya koda zata ga abinda su kubran ke fada.


Ilai kuwa idanunta suka gane mata,cikin barorin gidanne kimanin su hudu,maza biyu mata biyu,idan ta lura ma da kyau kama sun razana ne da ganin nata,daya daga cikinsu dake can baya kuma hannayensa na boye a bayansa suka zube suna miqa mata gaisuwa.


Bata amsa ba,saita soma takawa zuwa inda suke zuben,babu wanda ya motsa a cikinsu jin bata amsa ba hakanan bata tafi ba,saita isa gabansu tana qare musu kallo,idanunta ya sauka akan na bayan dake goye da hannayensa a baya.....
7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 60
*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*
_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*
0903 234 5899
Ko
09033181070


Har ta bude baki da zummar yin magana,sai kuma ta tuna ba girmanta bane,don haka ta juya taci gaba da tafiya ba tare data ce da kowa komai ba,sai su kubra suka rufa mata baya suma ba tare da sun tanka ba,jin batace komai din ba.


Zuzzurfan tunani ta shiga,ba shakka akwai abinda ke faruwa,akwai abinda ke faruwa wanda ita din bata sani ba,kuma koma meye yana da alaqa da ita,lallai abun ya shafeta,amma zata bincika cikin hikimarta kamar tadda ta saba.


Saida sukazo iyaka,wanda su kubra basu da izini ko ikon darawa daga nan din sannan tayi magana a sanda suke juyawa
"Na lura da abinda ke faruwa,kuma ba shakka abun bisa dukkan alamu ya jibanceni ne.....ku isa sassana ku jirani,kada ku tafi,ku kuma kira sodangi da lubabatu suma suyi dakona,zamu tattauna bayan na fito"
"An gama uwar gijiyarmu" suka amsa mata a kusan tare,ba tare data waiwayo ba ta saka kai zuwa ainihin sassan mai martaba.


Cikin qasaita da nutsuwa tayi sallama a katafaren falon daya kasance yana ganawa da iya iyalinshi kawai,ba'a amsa mata ba,hakan ya bata mamaki,saita ware idanu tana kallon wadanda ke zaune cikin falon.


Uwar gida sarautar mata ce fulani saratu,saman cinyarta daya daga cikin jikokinta ne maza,hakama gefanta jikan nata ne wanda dukkansu ba zasu haura shekara hudu da biyar ba.


A daya kujerar kuma maibi mata ce wato fulani adama,itama tana zaune da nata jikan guda daya a gafanta tana tsinke mishi inibi cikin kayan marmarin dake jibge a falon tana bashi yana ci,shima bazai wuce shekara shida ba.


Batayi mamaki ba don saratu bata amsa mata ba,adama ce cikin salo na kissa tadan tada kai ta amsa mata babu yabo ba fallasa.


Ganin kamar yau din kowa akwai abinda ke cikin ranshi sai itama ta nemi tata kujerar cikin hakimcewa ta zauna,ta kuma kama kanta da kyau ba tare da tabi takan kowaccensu ba.


Tsahon mintuna falon ya dauki shuru,bakajin komai sai darar su fulani saratu kowacce da jikanta.


Abunda fulani aisha ta lura dashi da kyau shine,kamar abinda sukeyi din sunayi ne da biyu,don haka saita sake baiwa banza ajiyarsu.


Jikan adama keta wasanshi cikin falon yana zagayewa,ya hau wanann kujerar ya fada kan waccan,yayin da fulani adaman ta shiga masa tafi tana masa waqa,kana ta dora da cewa
"Tattaka da kyau....yauwa,cikin ikon Allah wataran sai kaga kaine mamallakin wannan wajen....eh mana,tunda su magadan sun kasa kawo nasu magajin...duk inda aka kai magaryar tiqewa ai dole a miqo mana mu masu jikoki maza,ahaaann....ai wani hanin ga Allah baiwa ne".


Sosai maganar ta taba fulani dake danne dannen wayarta,ta taba ranta sosai,saboda tasan bada kowa suke ba sai ita,hakanan suna magana ne kai tsaye akan abdul'azeez dinta,harta daga kai zata magantu sai kuma taga ba girmanta bane,hakanan tafi kowa sanin ta yadda take maida musu amsar magangununsu irin wannan ta qona musu rai cikin ruwan sanyi fiye da yadda sudin sukayi mata,don haka saita share taci gaba da abinda take,duk da zancan ya tsaya mata sosai cikin ranta.


Batasan me yasa fulani adaman ta sauya cikin shekarun nan ba,kishin nata da ada take dannewa ta cinye yanzun ga kasa,takan mata gugar zana a lokutta masu yawa,saidai abinda ta lura dashi sam bata kwatantawa gaban maimartaba,akasin fulani saratu da bata iya boyewa gaban kowa ma.


Wannan bai bar kunnuwa da qirjinta ba fulani saratu ta daga qaramin jikanta dake kan cinyarta tahau masa rawa
"Idan Allah ya baka babu me hanaka.....wani hanin ga Allah baiwa ne" sunan Allah ta ambata can qasan ranta,sa'annan taci gaba da danne dannen wayarta kamar basu dameta ba,daya daga cikin dabi'unta dake qona musu rai,na yadda bata taba buda baki ta nuna musu bacin ranta kan wani aiki nasu,saidai su gani a aikace.


Allah ya taimaketa ba'a qara second goma ba maimartaba yayi sallama cikin falon ya bayyana,cikin shigar da yakanyi idan yana cikin iyalinsa yana kuma buqatar ya sake sosai.


Fulani aishan ce ta soma amsawa,wanda hakan yaja hankalinsa matuqa a kanta,adonta ya qayatar dashi,don dama babu qarya,gwanace ta wannan fanni,tun yarinta zuwa girma yanzu daya cimmata.


Ita ta soma miqewa ta aje wayar hannunta,ta isa inda yake tsaye,ta saka hannayenta ta soma karkade mishi kujerar da yake da niyyar zama a kai,duk da ba wani datti ko qura ko qanqani akai
"Barka da fitowa ranka ya dade" ta fada tana kallonshi cikin wani salon murmushi mai qayatarwa,dolenshi ya maida mata martani ba tare daya shirya ba,duk da yadda yaso ya daure kodon su saratu dake wajen
"Barka kadai aishatu.....da fatan kin wuni lafiya" murmushi ta sake masa tana duqawa gamida soma zuba mishi abun sanyi dake cikin jug jug na alfarma na tangaran dake jere a wajen
"Lafiyata tana tattare da yadda ka wuni lafiya yallabai" ta qarashe fada tana miqa masa kofin,fuskarsa dauke da murmushinya karba sannan yace
"Ma sha Allah,na gode qwarai aishatu"
"Babu godiya tsakaninmu,amfanina kenan" da haka ta juya tana sakin murmushi zuwa mazauninta,ko iya haka tasan ta rama wani sashe daga abinda sukayi mata.


Sai data zauna sannan ya dubi saratu
"Sarautar mata...,kuna lafiya?" Ya tambayeta yana miqawa daya jikan nata dake zaune gefe hannu,saiya sauko da gudu ya nufi inda yake,da alamu akwai sabo da shaquwa tsakaninsu,bata iya danne bacin ranta ba,don gashinan saman fuska da muryarta haka ta amsa mishi,saiya waiwaya ga adama
"Ranki ya dade?,to kefa?" Tayi qoqari ita din tadan sakaya da murmushin yaqe,ta amsa mishi a taqaice
"Lafiya".


Sai daya gama shanye lemon da fulanin ta zuba mishi shi da jikokin nasa,yana yi yana jansu da wasa,wanda wannan shi yadan sauko dasu daga dokin da suka hau,sannan ya fara maganar data tarasu.


Gida biyu hankalinta ya kasu,daya yana ga maganar da suke da mai gidan nasu,yayin da dayan ya lula zuwa ga tunanun abinda ya afku dazun,shin meke faruwa?.


Awa daya da wasu motsi suka shafe sa'annan ya sallamesu,nan ma sai datayi abinda ta tabbatar zasuji ba dadi sannan ta fito abinta,tama rigasu barin wajen,don yanzun hankalinta ya tafi ga lalubo abinda ke shirin faruwa.


Sanda take fitar da wani irin kallo adama ta bita,ta kuma saki shu'umin murmushi,duk da abinda tayin ya qona mata rai,saidai bacin ran nata ragagge ne,takan kuma cika da farinciki,idan tuna nan da wasu awanni da idan sunyi nauyi awa 78 rayuwarta ita da ahalinta zasu shiga cakwakiya,don tana da yaqinin saqon data bada ya soma bazama lunguna da saqunan masarautar,a iya yau kadai Allah ne kasai yasan adadin jama'ar da suka gani.


Kamar yadda ta buqata haka taje ta samesu suna jiranta,cikin girmamawa kowanne ya miqe tsaye harta samu waje ta xauna,kana suka gaisa da mama sodangi saboda yau din duka basu hadu ba.


Shuru na dan mintuna sannan tace
"Nasan zakuyi mamakin taraku da nayi anan,duk da cewa yaha da kubra sunsan dalili,amma kudin nasan baku sani ba"
"Gaskiyane" suka amsa mata,saita gyara zamanta sosai sannan ta zayyane musu abinda ke faruwa.


Shiru ne ya ratsa falon babu wanda yace wani abu,saita shiga nazartar fuskarsu tare da shiga nazarin amsa da mafita da kowanne zai bata.


K'an kame hannunta umma luba tayi,wanda ke dauke da daya daga cikin hotunan data samu tsinta itama cikin masarautar tun gefin magariba,hotunan data fuskanci sun fara yawo cikin masarautar,don wannan shine na biyu data tsinta,tun dazun take ta tunanin hanyar da zatabi ta nunawa fulanin,ta kuma ankarar da ita abunda ta fuskanci ya soma wanzuwa,dalilin jimawarta kenan cikin gidan har kawo wannan lokacin ba tare data tafi gida ba.


Sosai fulanin ta ankare da mutsu mutsun da umma luban keyi,hakan ya sanya ta zuba mata idanu,ta kuma gano yadda hannuwanta ke dunqule kamar yadda ta dinga ganin hannuwan dai daikun mutanen data wuce dazun.


"Lafiya lubabatu?,ya akayi?" Ta tambayeta tana sake tsareta da kallo,ta dago da niyyar ce mata babu komai,to amma kwarjininta ya sanya ta kasa fadar hakan,saita soma inda inda irin ta marasa gaskiya,sa'anna daga bisani akan kanta dole ta fiddo hotunan guda uku ta miqa mata.


Ji ta dinga yi kamar a mafarki sanda take kallon hotunan,yarimanta yaronta rungume da mace cikin jikinsa,har daya daga cikin hotunan ma yafi kama da kiss yake mata,don ya rufa fuskarshi ne saman tata sosai,babu wani batun almara ko zane,yariman qasar kaisa yarima abdul'azeez ne sosai.


Wani mummunar faduwar gaba gamida fargaba ta rusketa sanda ta tuna fuskar yarinyar,qwaqwakwarta kuma tayi mata tariyar wacece ita,kaddai ace tsahon shekarun suna tare,kaddai ace data rabasun tsayin shekarun basu rabu ba suba tare da juna suna zaman haramc......


Saita hana zuciyarta qarasa wannan mummunan tunanin,ta miqe tsaye qirjinta na suya,zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,a matuqar rude ta miqawa mama sodangi hotunan tana jifan umma luba da kallo bayan ta yiwa kubra da yaha nuni da hannu kansu fita hade da tambayar umma luban
"Wannan ba yarinyar nan bace da kika samo sukayi aure da yarima na shekara daya ba?" Kan umma luba a qasa ta gyadashi
"Tabbas itace uwar gijiyata"
"Ban fahimta ba,a ina suka hadu,ko dama suna tare basu rabu ba?" Tayi tambayar wannan karon tana maida dubanta ga mama sodangi tana jin duk wani dabara da hikimarta suna toshewa.


Mama sodangi da tunda ta dora idanunta akan hotunan taji wani sanyi yana kwarara cikin ranta ta daga kai tana duban fulanin,kai tsaye tace da ita
"Tabbas basa tare,canzawar yanayin yarima kawai na tsahon shekarun ya isa ya shaida maka hakan"
"Ta yaya zan tabbatar da gaskiyar hakan,bawai pretending yake min ba?".


A wannan karon babu wanda ya bata amsa a cikinsu
"Tabbas indai abinda nake tunani ne abdul'azeez ya tafka babban kuskure,kuskure mafi girma a rayuwarsa" ta fada cikin gsananin bacin rai.


A wannan karon kasa shuru mama sodangi tayi,cikin nuna girmamawa tace
"Ina ganin kibi komai sannu a hankali....abdulazeez yarone mai biyayya matuqa da gaske da duka duniya ta shaida,karki zafafa wannan karon,kada ki shiga raywarsa da yawa"
"Dakata sodangi!" Ta daga mata hannu cikin

Please Login or Register in order to submit comment